A ranar da Allah Yake tãra manzanni sa'an nan Ya ce: "Mene ne aka karɓa muku?" (zã) su ce: "Bãbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake."*
____________________
* A nan hukunce-hukuncen alkawurra suka ƙãre a wannan sura daga ãyã ta sama da wannan. Kuma da wannan ãyã ta l09 Allah Yanã yi mana hikãyar abin da zai auku a Lãhira da bincinkenSa ga tsare alkawari, kõ rashin tsarewa. Ya fãra da AnnabãwanSa. Ya aiko, da ƙarin bãyani a kan irin muhãwarar da zã ta shiga a tsakãninSa da Annabãwa.Yã yi misãli da Ĩsã dõmin mutanensa nã nan a cikin wannan al'umma, anã kiran su zuwa ga musulunci, kuma domin shine Annabi na ƙarshen da ba a manta abubuwan da mutanensa suka yi ba a gabanin ɗauke shi ɗin.