Fussilat


حمٓ

Ḥ. M̃.


تَنزِيلٞ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Saukarwa (da Alƙur' ãni) dãga Mai rahama ne, Mai jin ƙai.


كِتَٰبٞ فُصِّلَتۡ ءَايَٰتُهُۥ قُرۡءَانًا عَرَبِيّٗا لِّقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

Littãfi ne, an bayyana ãyõyinsa daki-daki, yanã abin karantãwa na Lãrabci, dõmin mutãnen dake sani


بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا فَأَعۡرَضَ أَكۡثَرُهُمۡ فَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ

Yanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Sai mafi yawansu suka bijire. Sabõda haka sũ, bã su saurãrãwa.


وَقَالُواْ قُلُوبُنَا فِيٓ أَكِنَّةٖ مِّمَّا تَدۡعُونَآ إِلَيۡهِ وَفِيٓ ءَاذَانِنَا وَقۡرٞ وَمِنۢ بَيۡنِنَا وَبَيۡنِكَ حِجَابٞ فَٱعۡمَلۡ إِنَّنَا عَٰمِلُونَ

Kuma suka ce: "Zukatanmu nã a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da tsakaninka akwai wani shãmaki. sahõda haka ka yi aiki, lalle mũ mãsu aiki ne."


قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَٱسۡتَقِيمُوٓاْ إِلَيۡهِ وَٱسۡتَغۡفِرُوهُۗ وَوَيۡلٞ لِّلۡمُشۡرِكِينَ

Ka ce: "Nĩ mutum kawai ne kamarku, ãnã yin wahayi zuwa gare ni cẽwa abin bautãwarku, abin bautãwa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nẽmi gafararSa." Kuma bone ya tabbata ga mãsu yin shirki.



الصفحة التالية
Icon