An-Najm


وَٱلنَّجۡمِ إِذَا هَوَىٰ

Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.


مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمۡ وَمَا غَوَىٰ

Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.


وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰٓ

Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.


إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡيٞ يُوحَىٰ

(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.


عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلۡقُوَىٰ

(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.


ذُو مِرَّةٖ فَٱسۡتَوَىٰ

Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.


وَهُوَ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡأَعۡلَىٰ

Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.


ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ

Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.


فَكَانَ قَابَ قَوۡسَيۡنِ أَوۡ أَدۡنَىٰ

Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.


فَأَوۡحَىٰٓ إِلَىٰ عَبۡدِهِۦ مَآ أَوۡحَىٰ

Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).



الصفحة التالية
Icon