AlHadid


سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Abin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.


لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme.


هُوَ ٱلۡأَوَّلُ وَٱلۡأٓخِرُ وَٱلظَّـٰهِرُ وَٱلۡبَاطِنُۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ

Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme.


هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يَعۡلَمُ مَا يَلِجُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا يَخۡرُجُ مِنۡهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا يَعۡرُجُ فِيهَاۖ وَهُوَ مَعَكُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi, Yanã sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta, kuma Shĩ yanã tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.


لَّهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ

Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma zuwa gare Shĩ (Allah) kawai ake mayar da al'amura.



الصفحة التالية
Icon