Kuma Muka ƙẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutãne waɗanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: "Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa "* Ya ce: "Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta."
* Farkon faɗan ƙarya da gaskiya a tsakãnin Banĩ Isra'ila da Mũsã wajen son kõmawa ga al'ãdu da ƙãri a cikin addini ta hanyar bidi'a.
الترجمة الهوساوية