---
title: "ترجمة سورة الفيل - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/105/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/105/book/1999"
surah_id: "105"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة الفيل - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/105/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة الفيل - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/105/book/1999*.

Translation of Surah الفيل from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 105:1

> أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصْحَابِ الْفِيلِ [105:1]

Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa\* ba?
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* An yi Yãƙin Gĩwa shekarar haihuwar Annabi tsakãnin halaka su da haihuwarsa kwãna hamsin. Bayan shekara arba'in Annabi ya fara karantar da mutane. Ya karantar da su cikin shekara ashirin da uku, sa'an nan ya ƙaura. Bayansa da shekara hamsin waanda suka bi shi suka cinye duniya. Wannan yana nuna cewa mutane ba su samun daraja sai da riƙon addini da ilimi.

### الآية 105:2

> ﻿أَلَمْ يَجْعَلْ كَيْدَهُمْ فِي تَضْلِيلٍ [105:2]

Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?

### الآية 105:3

> ﻿وَأَرْسَلَ عَلَيْهِمْ طَيْرًا أَبَابِيلَ [105:3]

Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.

### الآية 105:4

> ﻿تَرْمِيهِمْ بِحِجَارَةٍ مِنْ سِجِّيلٍ [105:4]

Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.

### الآية 105:5

> ﻿فَجَعَلَهُمْ كَعَصْفٍ مَأْكُولٍ [105:5]

Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/105.md)
- [كل تفاسير سورة الفيل
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/105.md)
- [ترجمات سورة الفيل
](https://quranpedia.net/translations/105.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/105/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
