---
title: "ترجمة سورة النّمل - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/27/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/27/book/1999"
surah_id: "27"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة النّمل - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/27/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة النّمل - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/27/book/1999*.

Translation of Surah النّمل from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 27:1

> طس ۚ تِلْكَ آيَاتُ الْقُرْآنِ وَكِتَابٍ مُبِينٍ [27:1]

¦. S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa.

### الآية 27:2

> ﻿هُدًى وَبُشْرَىٰ لِلْمُؤْمِنِينَ [27:2]

Shiriya ce da bushãra ga mũminai.

### الآية 27:3

> ﻿الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ بِالْآخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ [27:3]

Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ, sunã yin yaƙĩni.

### الآية 27:4

> ﻿إِنَّ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ زَيَّنَّا لَهُمْ أَعْمَالَهُمْ فَهُمْ يَعْمَهُونَ [27:4]

Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa.

### الآية 27:5

> ﻿أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَهُمْ سُوءُ الْعَذَابِ وَهُمْ فِي الْآخِرَةِ هُمُ الْأَخْسَرُونَ [27:5]

Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra.

### الآية 27:6

> ﻿وَإِنَّكَ لَتُلَقَّى الْقُرْآنَ مِنْ لَدُنْ حَكِيمٍ عَلِيمٍ [27:6]

Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa\* ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Lãhira da ĩmãni da ita sunã a cikin ashĩran Allah. Haka karɓar Alƙur'ãni daga Allah yanã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana a Littafi. Ganin Mũsa ga wutã da abubuwan da suka auku a wurin game da maganar Allah a gare shi da jũyãwar sanda macijiya da kõmawarta sanda da jũyãwar hannunsa fari ƙal da jũyãwarsa zuwa ga asalinsa, duka sunã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana su ga wani mutum.

### الآية 27:7

> ﻿إِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِأَهْلِهِ إِنِّي آنَسْتُ نَارًا سَآتِيكُمْ مِنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ آتِيكُمْ بِشِهَابٍ قَبَسٍ لَعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ [27:7]

A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa "Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi."

### الآية 27:8

> ﻿فَلَمَّا جَاءَهَا نُودِيَ أَنْ بُورِكَ مَنْ فِي النَّارِ وَمَنْ حَوْلَهَا وَسُبْحَانَ اللَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ [27:8]

To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, "An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu."

### الآية 27:9

> ﻿يَا مُوسَىٰ إِنَّهُ أَنَا اللَّهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ [27:9]

"Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima."

### الآية 27:10

> ﻿وَأَلْقِ عَصَاكَ ۚ فَلَمَّا رَآهَا تَهْتَزُّ كَأَنَّهَا جَانٌّ وَلَّىٰ مُدْبِرًا وَلَمْ يُعَقِّبْ ۚ يَا مُوسَىٰ لَا تَخَفْ إِنِّي لَا يَخَافُ لَدَيَّ الْمُرْسَلُونَ [27:10]

"Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, "Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa."

### الآية 27:11

> ﻿إِلَّا مَنْ ظَلَمَ ثُمَّ بَدَّلَ حُسْنًا بَعْدَ سُوءٍ فَإِنِّي غَفُورٌ رَحِيمٌ [27:11]

"Sai wanda ya yi zãlunci, sa'an nan ya musanya kyau a bãyan cũta, to, lalle Nĩ, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."

### الآية 27:12

> ﻿وَأَدْخِلْ يَدَكَ فِي جَيْبِكَ تَخْرُجْ بَيْضَاءَ مِنْ غَيْرِ سُوءٍ ۖ فِي تِسْعِ آيَاتٍ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَقَوْمِهِ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا فَاسِقِينَ [27:12]

"Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta, a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance mutãne ne fãsiƙai."

### الآية 27:13

> ﻿فَلَمَّا جَاءَتْهُمْ آيَاتُنَا مُبْصِرَةً قَالُوا هَٰذَا سِحْرٌ مُبِينٌ [27:13]

To, a lõkacin da ãyõyinMu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan sihiri ne bayyananne.

### الآية 27:14

> ﻿وَجَحَدُوا بِهَا وَاسْتَيْقَنَتْهَا أَنْفُسُهُمْ ظُلْمًا وَعُلُوًّا ۚ فَانْظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ [27:14]

Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai. To, ka dũbi yadda ãƙibar maɓarnata ta kasance.

### الآية 27:15

> ﻿وَلَقَدْ آتَيْنَا دَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ عِلْمًا ۖ وَقَالَا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي فَضَّلَنَا عَلَىٰ كَثِيرٍ مِنْ عِبَادِهِ الْمُؤْمِنِينَ [27:15]

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: "Gõdiya\* ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Abin da ke hakkin ni'imar Allah a kan mutum, ya gõde Masa. Dãwũda da Sulaiman Allah Yã bã su ilmi na Annabci sun tsayu da gõdiyarsa a kan aiki da shi, da kuma iƙrãri da cewa nĩ'ima ce daga Allah, bã da wani aiki nãsu ba. Annabci da ilmi da sanin maganar tsuntsu da ta aljannu da taturũruwa duka sunã cikin ashĩrin Allah da Yake nũnãwa ta hanyar waɗansu bãyinsa Annabãwa.

### الآية 27:16

> ﻿وَوَرِثَ سُلَيْمَانُ دَاوُودَ ۖ وَقَالَ يَا أَيُّهَا النَّاسُ عُلِّمْنَا مَنْطِقَ الطَّيْرِ وَأُوتِينَا مِنْ كُلِّ شَيْءٍ ۖ إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ الْفَضْلُ الْمُبِينُ [27:16]

Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: "Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar (Allah) bayyananna."

### الآية 27:17

> ﻿وَحُشِرَ لِسُلَيْمَانَ جُنُودُهُ مِنَ الْجِنِّ وَالْإِنْسِ وَالطَّيْرِ فَهُمْ يُوزَعُونَ [27:17]

Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, to, sũ anã kange su (ga tafiya).

### الآية 27:18

> ﻿حَتَّىٰ إِذَا أَتَوْا عَلَىٰ وَادِ النَّمْلِ قَالَتْ نَمْلَةٌ يَا أَيُّهَا النَّمْلُ ادْخُلُوا مَسَاكِنَكُمْ لَا يَحْطِمَنَّكُمْ سُلَيْمَانُ وَجُنُودُهُ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ [27:18]

Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba."

### الآية 27:19

> ﻿فَتَبَسَّمَ ضَاحِكًا مِنْ قَوْلِهَا وَقَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِي أَنْ أَشْكُرَ نِعْمَتَكَ الَّتِي أَنْعَمْتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَالِدَيَّ وَأَنْ أَعْمَلَ صَالِحًا تَرْضَاهُ وَأَدْخِلْنِي بِرَحْمَتِكَ فِي عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ [27:19]

Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai."

### الآية 27:20

> ﻿وَتَفَقَّدَ الطَّيْرَ فَقَالَ مَا لِيَ لَا أَرَى الْهُدْهُدَ أَمْ كَانَ مِنَ الْغَائِبِينَ [27:20]

Kuma ya binciki\* tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?"
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Wannan ya nũna tsayuwar sulaimãn da binciken kõme da kõwa a cikin daularsa. Kuma da yadda yake yin tsanani a cikin sauƙi. Wannan ita ce hanyar mulki mai kyau.

### الآية 27:21

> ﻿لَأُعَذِّبَنَّهُ عَذَابًا شَدِيدًا أَوْ لَأَذْبَحَنَّهُ أَوْ لَيَأْتِيَنِّي بِسُلْطَانٍ مُبِينٍ [27:21]

"Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne."

### الآية 27:22

> ﻿فَمَكَثَ غَيْرَ بَعِيدٍ فَقَالَ أَحَطْتُ بِمَا لَمْ تُحِطْ بِهِ وَجِئْتُكَ مِنْ سَبَإٍ بِنَبَإٍ يَقِينٍ [27:22]

Sai ya zauna bã nẽsa ba, sa'an nan ya ce: "Nã san abin da ba ka sani ba, kuma na zo maka daga Saba da wani lãbari tabbatacce."

### الآية 27:23

> ﻿إِنِّي وَجَدْتُ امْرَأَةً تَمْلِكُهُمْ وَأُوتِيَتْ مِنْ كُلِّ شَيْءٍ وَلَهَا عَرْشٌ عَظِيمٌ [27:23]

"Lalle ni nã sãmi wata mace wadda tanã mulkinsu kuma an bã ta daga dukkan kõme, kuma tanã da gadon sarauta mai girma.

### الآية 27:24

> ﻿وَجَدْتُهَا وَقَوْمَهَا يَسْجُدُونَ لِلشَّمْسِ مِنْ دُونِ اللَّهِ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ فَهُمْ لَا يَهْتَدُونَ [27:24]

"Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya, sa'an nan sũ, ba su shiryuwa."

### الآية 27:25

> ﻿أَلَّا يَسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي يُخْرِجُ الْخَبْءَ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَيَعْلَمُ مَا تُخْفُونَ وَمَا تُعْلِنُونَ [27:25]

"Ga\* su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwada abin da kuke bayyanãwa."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* An kãyar da harafin kõrewa dõmin barinsa, da Hausa, yanã ɓãta ma'ana, dõmin shaiɗan bai kange su daga rashin yin sujada ba.

### الآية 27:26

> ﻿اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ ۩ [27:26]

"Allah bãbu abin bautãwa fãce shĩ Ubangijin\* Al'arshi, mai girma."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Ya siffanta Allah da cewa bãbu abin bautãwa fãce Shi, dõmin ya kõre cancantar rãnã ga ibãda, da Ubangijin Al'arshi dõmin ya ɗebe girman gadon Bilkisu daga zukãta.

### الآية 27:27

> ﻿۞ قَالَ سَنَنْظُرُ أَصَدَقْتَ أَمْ كُنْتَ مِنَ الْكَاذِبِينَ [27:27]

Ya ce: "Za mu dũba shin kã yi gaskiya ne, kõ kuwa kã kasance daga maƙaryata?"

### الآية 27:28

> ﻿اذْهَبْ بِكِتَابِي هَٰذَا فَأَلْقِهْ إِلَيْهِمْ ثُمَّ تَوَلَّ عَنْهُمْ فَانْظُرْ مَاذَا يَرْجِعُونَ [27:28]

"Ka tafi da takardata wannan, sa'an nan ka jẽfa ta zuwa gare su, sa'an nan kuma ka jũya daga barinsu, sa'an nan ka ga mẽne ne suke mayarwa."

### الآية 27:29

> ﻿قَالَتْ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ إِنِّي أُلْقِيَ إِلَيَّ كِتَابٌ كَرِيمٌ [27:29]

Ta ce: "Yã kũ mashawarta! Lalle ne, an jẽfo, zuwa gareni, wata takarda mai girma."

### الآية 27:30

> ﻿إِنَّهُ مِنْ سُلَيْمَانَ وَإِنَّهُ بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ [27:30]

"Lalle ita daga Sulaiman take, kuma lalle ita da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai ne."

### الآية 27:31

> ﻿أَلَّا تَعْلُوا عَلَيَّ وَأْتُونِي مُسْلِمِينَ [27:31]

"Kada ku yi girman kai a gare ni, kuma ku zo mini kunã mãsu sallamãwa."

### الآية 27:32

> ﻿قَالَتْ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ أَفْتُونِي فِي أَمْرِي مَا كُنْتُ قَاطِعَةً أَمْرًا حَتَّىٰ تَشْهَدُونِ [27:32]

Ta ce: "Yã ku mashawarta\*! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai yanke wani al'amari ba, sai kun halarta."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Allah bai keɓance hikima ga maza kawai ba har mãtã akwai mãsu hikima a cikinsu. Sai dai Musulunci yã hana shugabancin mãtã, sabõda galibinsu ãdifarsu tã rinjãyi hankalinsu, sabõda kyautata tarbiyyar yãra. Anã fahimtar cewa iya mulki shi ne rashin fallewa da ra'ayi ga shũgaba, sai a bãyan ya shãwarci mutãnensa, kamar yadda sarauniyar Saba' ta yi da Majalisarta.

### الآية 27:33

> ﻿قَالُوا نَحْنُ أُولُو قُوَّةٍ وَأُولُو بَأْسٍ شَدِيدٍ وَالْأَمْرُ إِلَيْكِ فَانْظُرِي مَاذَا تَأْمُرِينَ [27:33]

Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umurui (da shi)?"

### الآية 27:34

> ﻿قَالَتْ إِنَّ الْمُلُوكَ إِذَا دَخَلُوا قَرْيَةً أَفْسَدُوهَا وَجَعَلُوا أَعِزَّةَ أَهْلِهَا أَذِلَّةً ۖ وَكَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ [27:34]

Ta ce: "Lalle sarakuna idan sun shiga wata alƙarya, sai su ɓãta ta, kuma su sanya mãsu darajar mutãnenta ƙasƙantattu. Kuma kamar wancan ne suke likatãwa."

### الآية 27:35

> ﻿وَإِنِّي مُرْسِلَةٌ إِلَيْهِمْ بِهَدِيَّةٍ فَنَاظِرَةٌ بِمَ يَرْجِعُ الْمُرْسَلُونَ [27:35]

"Kuma lalle nĩ mai aikãwa ce zuwa gare su da kyauta, sa'an nan mai dũbawa ce: Da me manzannin zã su kõmo."

### الآية 27:36

> ﻿فَلَمَّا جَاءَ سُلَيْمَانَ قَالَ أَتُمِدُّونَنِ بِمَالٍ فَمَا آتَانِيَ اللَّهُ خَيْرٌ مِمَّا آتَاكُمْ بَلْ أَنْتُمْ بِهَدِيَّتِكُمْ تَفْرَحُونَ [27:36]

To, a lõkacin da ya jẽ wa Sulaiman ya ce: "Shin, za ku ƙãra ni da dũkiya ne? To, abin daAllah Ya bã ni, shi ne mafi alhẽridaga abin da Ya bã ku. A'a, kũ nekuke yin farin ciki da kyautarku."

### الآية 27:37

> ﻿ارْجِعْ إِلَيْهِمْ فَلَنَأْتِيَنَّهُمْ بِجُنُودٍ لَا قِبَلَ لَهُمْ بِهَا وَلَنُخْرِجَنَّهُمْ مِنْهَا أَذِلَّةً وَهُمْ صَاغِرُونَ [27:37]

"Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu."

### الآية 27:38

> ﻿قَالَ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ أَيُّكُمْ يَأْتِينِي بِعَرْشِهَا قَبْلَ أَنْ يَأْتُونِي مُسْلِمِينَ [27:38]

Ya ce: "Yã ku mashãwarta! Wannenku zai zo mini da gadonta a gabãnin su zo, sunã mãsu sallamãwa?"

### الآية 27:39

> ﻿قَالَ عِفْرِيتٌ مِنَ الْجِنِّ أَنَا آتِيكَ بِهِ قَبْلَ أَنْ تَقُومَ مِنْ مَقَامِكَ ۖ وَإِنِّي عَلَيْهِ لَقَوِيٌّ أَمِينٌ [27:39]

Wani mai ƙarfi daga aljannu ya ce: "Nĩ inã zo maka da shi a gabãnin ka tãshi daga matsayinka. Kuma llale nĩ a gare shi, haƙĩƙa, mai ƙarfi ne amintacce."

### الآية 27:40

> ﻿قَالَ الَّذِي عِنْدَهُ عِلْمٌ مِنَ الْكِتَابِ أَنَا آتِيكَ بِهِ قَبْلَ أَنْ يَرْتَدَّ إِلَيْكَ طَرْفُكَ ۚ فَلَمَّا رَآهُ مُسْتَقِرًّا عِنْدَهُ قَالَ هَٰذَا مِنْ فَضْلِ رَبِّي لِيَبْلُوَنِي أَأَشْكُرُ أَمْ أَكْفُرُ ۖ وَمَنْ شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِ ۖ وَمَنْ كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيٌّ كَرِيمٌ [27:40]

Wanda yake a wurinsa akwai\* wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne, Karĩmi."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Allah na bãyar da asirai daga littattafai, kõ da wahayi zuwa ga Annabãwa, kõ da ilhãma daga abin da aka bai wa Annabãwa. Waɗansu sun ce ilmin nan sũnan Allah ne Mafi girma. Allah ne Mafi sani. Sai dai sharaɗin aiki da ilmi ga ĩbãda, ya kasance daga Annabãwa kawai, a cikin lõkacin aiwatar da shari'arsu.Bã a iya amfãni da wani sũnan Allah wanda wani Annabi bai zo da shi ba a gabãnin Musulunci, kuma a bãyan Musulunci.

### الآية 27:41

> ﻿قَالَ نَكِّرُوا لَهَا عَرْشَهَا نَنْظُرْ أَتَهْتَدِي أَمْ تَكُونُ مِنَ الَّذِينَ لَا يَهْتَدُونَ [27:41]

Ya ce: "Ku canza kamar gadonta gare ta, mu gani, shin zã ta shiryu, kõ kuwa tanã kasancẽwa daga waɗanda bã su shiryuwa."

### الآية 27:42

> ﻿فَلَمَّا جَاءَتْ قِيلَ أَهَٰكَذَا عَرْشُكِ ۖ قَالَتْ كَأَنَّهُ هُوَ ۚ وَأُوتِينَا الْعِلْمَ مِنْ قَبْلِهَا وَكُنَّا مُسْلِمِينَ [27:42]

To a lõkacin da ta jẽ aka ce "Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?" Ta ce: "Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu sallamãwar (al'amari ga Allah)."

### الآية 27:43

> ﻿وَصَدَّهَا مَا كَانَتْ تَعْبُدُ مِنْ دُونِ اللَّهِ ۖ إِنَّهَا كَانَتْ مِنْ قَوْمٍ كَافِرِينَ [27:43]

Kuma abin da ta kasance tanã bautãwa, baicin Allah, ya kange ta. Lalle ita, tã kasance daga mutãne kãfirai.

### الآية 27:44

> ﻿قِيلَ لَهَا ادْخُلِي الصَّرْحَ ۖ فَلَمَّا رَأَتْهُ حَسِبَتْهُ لُجَّةً وَكَشَفَتْ عَنْ سَاقَيْهَا ۚ قَالَ إِنَّهُ صَرْحٌ مُمَرَّدٌ مِنْ قَوَارِيرَ ۗ قَالَتْ رَبِّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي وَأَسْلَمْتُ مَعَ سُلَيْمَانَ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ [27:44]

Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye\* daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Idan ĩmãni ya shiga a cikin zũciya, sai girman kai ya fita daga gare ta sarauniya Bilkisu tanã kuranye ƙafãfunta da niyyarta ta shiga a cikin ruwa dõmin ta nũna ɗã'arta ga umurnin Annabin Allah Sulaimãn kuma ta yarda da shiga gulbin da ba ta san tsawon zurfinsa ba, kõ da za ta mutu awurin ɗã'ã da taƙawa. Mace da sarauta iyakar girman kai ke nan, bãbu abin da zai gusar da shi sai ĩmãnin gaskiya.

### الآية 27:45

> ﻿وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ فَإِذَا هُمْ فَرِيقَانِ يَخْتَصِمُونَ [27:45]

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, mun aika zuwa Samũdãwa da ɗan'uwansu, Salihu (ya ce), "Ku bauta wa Allah." Sai gã su ƙungiyõyi biyu sunã ta husũma.

### الآية 27:46

> ﻿قَالَ يَا قَوْمِ لِمَ تَسْتَعْجِلُونَ بِالسَّيِّئَةِ قَبْلَ الْحَسَنَةِ ۖ لَوْلَا تَسْتَغْفِرُونَ اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ [27:46]

Ya ce: "Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama?"

### الآية 27:47

> ﻿قَالُوا اطَّيَّرْنَا بِكَ وَبِمَنْ مَعَكَ ۚ قَالَ طَائِرُكُمْ عِنْدَ اللَّهِ ۖ بَلْ أَنْتُمْ قَوْمٌ تُفْتَنُونَ [27:47]

Suka ce: "Munã shu'umci da kai, kuma da wanda ke tãre da kai." Ya ce: "Shu'umcinku a wurin Allah yake. Ã'a, kũ mutãne ne, anã fitinar ku."

### الآية 27:48

> ﻿وَكَانَ فِي الْمَدِينَةِ تِسْعَةُ رَهْطٍ يُفْسِدُونَ فِي الْأَرْضِ وَلَا يُصْلِحُونَ [27:48]

Kuma waɗansu jama'a tara\* sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa,\*\* shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Yawan mãsu ɓarnã bã ya hana gaskiya bayyana. Kuma mai mãkirci dõmin ya halakar da mai gargaɗin addinin Allah, yanã yi wa kansa sanadin halaka kawai ne. Waɗannan mutãne tara sun yi niyyar kashe Sãlihu ne, bã da sanin danginsa ba, a wurin dayake kwãna yanã salla a masallacinsa, a bãyan gari. A can Allah ya halakar da su. Wannan shĩ ne sakamakon mãkircin da suka ƙulla. \*\* Zã mu kwãnan masa, ai zãmu kwãna da niyyar kashe shi a cikin dare, a ɓõye.

### الآية 27:49

> ﻿قَالُوا تَقَاسَمُوا بِاللَّهِ لَنُبَيِّتَنَّهُ وَأَهْلَهُ ثُمَّ لَنَقُولَنَّ لِوَلِيِّهِ مَا شَهِدْنَا مَهْلِكَ أَهْلِهِ وَإِنَّا لَصَادِقُونَ [27:49]

Kuma suka ƙulla mãkirci, kuma Muka ƙulla sakamakon mãkirci, alhãli sũ ba su sani ba.

### الآية 27:50

> ﻿وَمَكَرُوا مَكْرًا وَمَكَرْنَا مَكْرًا وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ [27:50]

Ka dũba yadda ãƙibar mãkircinsu ta kasance lalle Mũ Mun darkãke su da mutãnensu, gabã ɗaya.

### الآية 27:51

> ﻿فَانْظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ مَكْرِهِمْ أَنَّا دَمَّرْنَاهُمْ وَقَوْمَهُمْ أَجْمَعِينَ [27:51]

Waɗancan, gidãjensu ne, wõfintattu sabõda zãluncin da suka yi, lalle ne a wancan akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke sani.

### الآية 27:52

> ﻿فَتِلْكَ بُيُوتُهُمْ خَاوِيَةً بِمَا ظَلَمُوا ۗ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَةً لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ [27:52]

Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sun kasance sunã taƙawa.

### الآية 27:53

> ﻿وَأَنْجَيْنَا الَّذِينَ آمَنُوا وَكَانُوا يَتَّقُونَ [27:53]

Da Lũdu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Shin kunã jẽ wa alfasha\* ne, alhãli, kuwa kunã gani?"

### الآية 27:54

> ﻿وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ وَأَنْتُمْ تُبْصِرُونَ [27:54]

"Shin lalle kũ haƙĩƙa kunã je wa maza da sha'awa baicin mãtã? Ã'a, kũ wasu irin mutãne ne kuna aikin jãhilci."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Alfãshar mutãnen Lũɗu, ita ce luwãɗi, namji yabi namiji a duburarsa wannan alfãsha, kõ dabbõbi bã su yin ta. Ga mutãnen Lũɗuta fãra bayyana. Allah Ya halakar da su kamar yadda Ya ambata. Sa'an nan kuma ba a ƙãra ganinta ba, sai ga wannan al'umma asĩirin da ke ciki, shĩ ne yadda Allah Yake jũyar da ɗabĩ'ar mutum ta zama bã ta mãsu hankali ba, tãre da dõgewar halittar jikinsa kamar yadda take ga zãhiri.

### الآية 27:55

> ﻿أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ شَهْوَةً مِنْ دُونِ النِّسَاءِ ۚ بَلْ أَنْتُمْ قَوْمٌ تَجْهَلُونَ [27:55]

Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata.

### الآية 27:56

> ﻿۞ فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلَّا أَنْ قَالُوا أَخْرِجُوا آلَ لُوطٍ مِنْ قَرْيَتِكُمْ ۖ إِنَّهُمْ أُنَاسٌ يَتَطَهَّرُونَ [27:56]

Bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa fãce suka ce "Ku fitar da mutãnen Lũɗu daga alƙaryarku, lalle sũ, wasu irin mutãne ne mãsu da'awar sunã da tsarki."

### الآية 27:57

> ﻿فَأَنْجَيْنَاهُ وَأَهْلَهُ إِلَّا امْرَأَتَهُ قَدَّرْنَاهَا مِنَ الْغَابِرِينَ [27:57]

Sai Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa,\* fãce mãtarsa, Mun ƙaddara ta a cikin mãsu wanzuwa.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
\* Mutãnensa mũminai. Ĩmãni da gaskiya idan gaskiya ta bayyana asĩri ne daga asĩran Allah sai wanda Ya bai wa. Kusanci ga wani Annabi da aure kõ zumunta, bã ya bãyar da shi. Ruwan azãba, shĩ ma asĩri ne na Allah.

### الآية 27:58

> ﻿وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ مَطَرًا ۖ فَسَاءَ مَطَرُ الْمُنْذَرِينَ [27:58]

Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa. To, ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.

### الآية 27:59

> ﻿قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ وَسَلَامٌ عَلَىٰ عِبَادِهِ الَّذِينَ اصْطَفَىٰ ۗ آللَّهُ خَيْرٌ أَمَّا يُشْرِكُونَ [27:59]

Ka ce: "Godiya ta tabbata ga Alah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa, waɗanda Ya zãɓa." Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi?\*
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Daga wannan ãyã ta 59 zuwa ƙarshen Sũra, duka tambĩhi ne ga abũbuwan fake na ilmin Allah, wanda ya shãfi jikunanmu, amma ba mu san yadda suke aukuwa a gare mu ba. Sa'an nan kuma da tambĩhi ga abũbuwan gaibi da suke zuwa dõmin mu yi ĩmãni da su.

### الآية 27:60

> ﻿أَمَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَأَنْزَلَ لَكُمْ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَنْبَتْنَا بِهِ حَدَائِقَ ذَاتَ بَهْجَةٍ مَا كَانَ لَكُمْ أَنْ تُنْبِتُوا شَجَرَهَا ۗ أَإِلَٰهٌ مَعَ اللَّهِ ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ يَعْدِلُونَ [27:60]

Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa (Allah da wani).

### الآية 27:61

> ﻿أَمَّنْ جَعَلَ الْأَرْضَ قَرَارًا وَجَعَلَ خِلَالَهَا أَنْهَارًا وَجَعَلَ لَهَا رَوَاسِيَ وَجَعَلَ بَيْنَ الْبَحْرَيْنِ حَاجِزًا ۗ أَإِلَٰهٌ مَعَ اللَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ [27:61]

Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba.

### الآية 27:62

> ﻿أَمَّنْ يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ السُّوءَ وَيَجْعَلُكُمْ خُلَفَاءَ الْأَرْضِ ۗ أَإِلَٰهٌ مَعَ اللَّهِ ۚ قَلِيلًا مَا تَذَكَّرُونَ [27:62]

Kõ wãne ne yake karɓã, kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni.

### الآية 27:63

> ﻿أَمَّنْ يَهْدِيكُمْ فِي ظُلُمَاتِ الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَمَنْ يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ ۗ أَإِلَٰهٌ مَعَ اللَّهِ ۚ تَعَالَى اللَّهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ [27:63]

Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku, kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi.

### الآية 27:64

> ﻿أَمَّنْ يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ وَمَنْ يَرْزُقُكُمْ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۗ أَإِلَٰهٌ مَعَ اللَّهِ ۚ قُلْ هَاتُوا بُرْهَانَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ [27:64]

Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita, kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: "Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya."

### الآية 27:65

> ﻿قُلْ لَا يَعْلَمُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ ۚ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ [27:65]

Ka ce: "Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su."

### الآية 27:66

> ﻿بَلِ ادَّارَكَ عِلْمُهُمْ فِي الْآخِرَةِ ۚ بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ مِنْهَا ۖ بَلْ هُمْ مِنْهَا عَمُونَ [27:66]

Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne.

### الآية 27:67

> ﻿وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَإِذَا كُنَّا تُرَابًا وَآبَاؤُنَا أَئِنَّا لَمُخْرَجُونَ [27:67]

Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne?"

### الآية 27:68

> ﻿لَقَدْ وُعِدْنَا هَٰذَا نَحْنُ وَآبَاؤُنَا مِنْ قَبْلُ إِنْ هَٰذَا إِلَّا أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ [27:68]

"Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko."

### الآية 27:69

> ﻿قُلْ سِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَانْظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُجْرِمِينَ [27:69]

Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi take?"

### الآية 27:70

> ﻿وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُنْ فِي ضَيْقٍ مِمَّا يَمْكُرُونَ [27:70]

Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci.

### الآية 27:71

> ﻿وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ [27:71]

Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi (zai auku), idan kun kasance mãsu gaskiya?"

### الآية 27:72

> ﻿قُلْ عَسَىٰ أَنْ يَكُونَ رَدِفَ لَكُمْ بَعْضُ الَّذِي تَسْتَعْجِلُونَ [27:72]

Ka ce: "Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta\* a gare ku."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Kuturi, shi ne a bãyan wani ya hau dabba ya kuma aza wani a kanta daga bãya gare shi. Kinaya ce na cewa abin yanã kusa gare su ƙwarai, kamar tsakãnin ɗan kuturi da mahayin dabba.

### الآية 27:73

> ﻿وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى النَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَشْكُرُونَ [27:73]

Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kanmutãne kuma amma mafi yawansu, bã su gõdẽwa.

### الآية 27:74

> ﻿وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَعْلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمْ وَمَا يُعْلِنُونَ [27:74]

Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa.

### الآية 27:75

> ﻿وَمَا مِنْ غَائِبَةٍ فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُبِينٍ [27:75]

Kuma bãbu wata (mas'ala) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne.

### الآية 27:76

> ﻿إِنَّ هَٰذَا الْقُرْآنَ يَقُصُّ عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ أَكْثَرَ الَّذِي هُمْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ [27:76]

Lalle ne wannan Alƙur'ãni\* yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Idan wannan Alƙur'ani ya ƙunsã ilmin asĩrai da yake iya gaya wa Banĩ Israĩla mafi yawan abin da sũ da kansu, suke sãɓã wa jũna a kansu, tãre da shahararsu da ilmi, da yawan Annabãwan da suka wuce a cikinsu, to, ga Lãrabãwa jãhilai hiyãka ke nan. Bãbu abin da ya wajaba a gare su, sai sallamawa ga abin da yake kiran zuwa gare shi. In abin da yake faɗa ba gaskiya ba ne, dã Banĩ Isrãĩla ne farkon mãsu nũna ƙaryarsa. Ammã ba su yi ba. Sabõda haka duka gaskiya ne. Sai kõwa ya bĩ shi ya tsĩra.

### الآية 27:77

> ﻿وَإِنَّهُ لَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِلْمُؤْمِنِينَ [27:77]

Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai.

### الآية 27:78

> ﻿إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِي بَيْنَهُمْ بِحُكْمِهِ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْعَلِيمُ [27:78]

"Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne Mabuwãyi, Masani."

### الآية 27:79

> ﻿فَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ ۖ إِنَّكَ عَلَى الْحَقِّ الْمُبِينِ [27:79]

Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya.

### الآية 27:80

> ﻿إِنَّكَ لَا تُسْمِعُ الْمَوْتَىٰ وَلَا تُسْمِعُ الصُّمَّ الدُّعَاءَ إِذَا وَلَّوْا مُدْبِرِينَ [27:80]

Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya.

### الآية 27:81

> ﻿وَمَا أَنْتَ بِهَادِي الْعُمْيِ عَنْ ضَلَالَتِهِمْ ۖ إِنْ تُسْمِعُ إِلَّا مَنْ يُؤْمِنُ بِآيَاتِنَا فَهُمْ مُسْلِمُونَ [27:81]

Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa (al'amari zuwa ga Allah).

### الآية 27:82

> ﻿۞ وَإِذَا وَقَعَ الْقَوْلُ عَلَيْهِمْ أَخْرَجْنَا لَهُمْ دَابَّةً مِنَ الْأَرْضِ تُكَلِّمُهُمْ أَنَّ النَّاسَ كَانُوا بِآيَاتِنَا لَا يُوقِنُونَ [27:82]

Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba\* daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa "Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Wata dabba ce anã kiranta Jassãsa an ce 'yar rãƙumar Sãlihu ce a lõkacin da aka kashe uwarta, ta gudu, ta shiga cikin dũtse' dũtsen ya rufe da ita. Tanã fitõwa daga dũtsen Safa a Makka da hantsi. Bãyan fitõwarta, bãbu sauran wa'azi. Mũmini ya tabbata mũmini kãfiri kuma ya tabbata haka. Tanã riƙe da sandar Mũsã da Hãtimin Sulaimãn. Tana fitõwa a bãyan fitõwar rãnã daga yamma. Allah ɗai Ya san gaskiyar yadda take.

### الآية 27:83

> ﻿وَيَوْمَ نَحْشُرُ مِنْ كُلِّ أُمَّةٍ فَوْجًا مِمَّنْ يُكَذِّبُ بِآيَاتِنَا فَهُمْ يُوزَعُونَ [27:83]

Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. (ga kõra)

### الآية 27:84

> ﻿حَتَّىٰ إِذَا جَاءُوا قَالَ أَكَذَّبْتُمْ بِآيَاتِي وَلَمْ تُحِيطُوا بِهَا عِلْمًا أَمَّاذَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ [27:84]

Har idan sun zo, (Allah) zai ce, "Ashe kun ƙaryata ãyõyinNa, kuma ba ku kẽwaye su da sani ba? To, mẽne ne kuka kasance kunã aikatãwa?"

### الآية 27:85

> ﻿وَوَقَعَ الْقَوْلُ عَلَيْهِمْ بِمَا ظَلَمُوا فَهُمْ لَا يَنْطِقُونَ [27:85]

Kuma magana ta auku a kansu, sabõda zãluncin da suka yi. To, sũ bã su da ta cẽwa.

### الآية 27:86

> ﻿أَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا اللَّيْلَ لِيَسْكُنُوا فِيهِ وَالنَّهَارَ مُبْصِرًا ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ [27:86]

Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa, kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.

### الآية 27:87

> ﻿وَيَوْمَ يُنْفَخُ فِي الصُّورِ فَفَزِعَ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَمَنْ فِي الْأَرْضِ إِلَّا مَنْ شَاءَ اللَّهُ ۚ وَكُلٌّ أَتَوْهُ دَاخِرِينَ [27:87]

Kuma da rãnar\* da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Bãyan fitõwar dabba, kuma sai bũsar ƙahõ na farkõ, sa'an nan na biyu sa'an nan Ƙiyãma.

### الآية 27:88

> ﻿وَتَرَى الْجِبَالَ تَحْسَبُهَا جَامِدَةً وَهِيَ تَمُرُّ مَرَّ السَّحَابِ ۚ صُنْعَ اللَّهِ الَّذِي أَتْقَنَ كُلَّ شَيْءٍ ۚ إِنَّهُ خَبِيرٌ بِمَا تَفْعَلُونَ [27:88]

Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi, Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa.

### الآية 27:89

> ﻿مَنْ جَاءَ بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ خَيْرٌ مِنْهَا وَهُمْ مِنْ فَزَعٍ يَوْمَئِذٍ آمِنُونَ [27:89]

Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita,\* a yinin nan, amintattu ne.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Firgita daga azãbar Lãhira, wannan firgita ba irin ta farko ba ce wadda aka ambata a cikin ãyã ta 87, dõmin wancan firgitar kwarjini ce a bãyan tãshi daga kaburbura.

### الآية 27:90

> ﻿وَمَنْ جَاءَ بِالسَّيِّئَةِ فَكُبَّتْ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ هَلْ تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ [27:90]

Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa?

### الآية 27:91

> ﻿إِنَّمَا أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ رَبَّ هَٰذِهِ الْبَلْدَةِ الَّذِي حَرَّمَهَا وَلَهُ كُلُّ شَيْءٍ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُسْلِمِينَ [27:91]

(Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari,\* Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Wannan Gari shĩ ne Makka. Sanya Makka hurumi ba a iya shiga cikinsa da yãki yanã a cikin ashĩrai na Allah. Shiryuwa da ɓata duka asĩrai ne na Allah. Tsãrin Alƙur'ani da abubuwan da ya ƙunsa duka asĩran Allah ne.

### الآية 27:92

> ﻿وَأَنْ أَتْلُوَ الْقُرْآنَ ۖ فَمَنِ اهْتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِهِ ۖ وَمَنْ ضَلَّ فَقُلْ إِنَّمَا أَنَا مِنَ الْمُنْذِرِينَ [27:92]

"Kuma inã karanta Alƙur'ãni." To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: "Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake."

### الآية 27:93

> ﻿وَقُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ سَيُرِيكُمْ آيَاتِهِ فَتَعْرِفُونَهَا ۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ [27:93]

Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu." Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/27.md)
- [كل تفاسير سورة النّمل
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/27.md)
- [ترجمات سورة النّمل
](https://quranpedia.net/translations/27.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/27/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
