---
title: "ترجمة سورة لقمان - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/31/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/31/book/1999"
surah_id: "31"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة لقمان - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/31/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة لقمان - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/31/book/1999*.

Translation of Surah لقمان from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 31:1

> الم [31:1]

A. L̃. M̃.

### الآية 31:2

> ﻿تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْحَكِيمِ [31:2]

Waɗancan ãyõyin Littãfin ne mai hikima.

### الآية 31:3

> ﻿هُدًى وَرَحْمَةً لِلْمُحْسِنِينَ [31:3]

Shiriya da rahama ne ga mãsu kyautatawa.

### الآية 31:4

> ﻿الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ بِالْآخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ [31:4]

Waɗanda ke tsai da salla kuma sunã ɓãyar da zakka kuma sũ, sunã yin ĩmãnin yaƙĩni, ga lãhira.

### الآية 31:5

> ﻿أُولَٰئِكَ عَلَىٰ هُدًى مِنْ رَبِّهِمْ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ [31:5]

Waɗannan sunã a kan shiriya ta daga Ubangijinsu kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.

### الآية 31:6

> ﻿وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَشْتَرِي لَهْوَ الْحَدِيثِ لِيُضِلَّ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَيَتَّخِذَهَا هُزُوًا ۚ أُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مُهِينٌ [31:6]

Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi\* dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Tatsũniyõyi sunã shagaltarwa daga ilmi mai sanya sanin Allah. Allah Ya hana a yi tarbiyyar yãra game da tãtsũniya mai ɗauke hankalinsu daga ibãda, Littattafan makaranta na zãmani da jarĩdu duka tãtsũniyõyi ne, sai abin da ya dãce da sunna.

### الآية 31:7

> ﻿وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ آيَاتُنَا وَلَّىٰ مُسْتَكْبِرًا كَأَنْ لَمْ يَسْمَعْهَا كَأَنَّ فِي أُذُنَيْهِ وَقْرًا ۖ فَبَشِّرْهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ [31:7]

Kuma idan an karanta ãyõyinMu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai, kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi.

### الآية 31:8

> ﻿إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّاتُ النَّعِيمِ [31:8]

Lalle, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljannar ni'ima.

### الآية 31:9

> ﻿خَالِدِينَ فِيهَا ۖ وَعْدَ اللَّهِ حَقًّا ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ [31:9]

Sunã dawwama a cikinsu Allah Yã yi alkawarin, Ya tabbatar da shi. Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.

### الآية 31:10

> ﻿خَلَقَ السَّمَاوَاتِ بِغَيْرِ عَمَدٍ تَرَوْنَهَا ۖ وَأَلْقَىٰ فِي الْأَرْضِ رَوَاسِيَ أَنْ تَمِيدَ بِكُمْ وَبَثَّ فِيهَا مِنْ كُلِّ دَابَّةٍ ۚ وَأَنْزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَنْبَتْنَا فِيهَا مِنْ كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ [31:10]

(Allah) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa.

### الآية 31:11

> ﻿هَٰذَا خَلْقُ اللَّهِ فَأَرُونِي مَاذَا خَلَقَ الَّذِينَ مِنْ دُونِهِ ۚ بَلِ الظَّالِمُونَ فِي ضَلَالٍ مُبِينٍ [31:11]

Wannan shĩ ne halittar Allah. To ku nũna mini, "Mẽne ne waɗanan da ba Shi ba suka halitta? Ã'a, azzalumai sunã a cikin ɓata bayyananna."

### الآية 31:12

> ﻿وَلَقَدْ آتَيْنَا لُقْمَانَ الْحِكْمَةَ أَنِ اشْكُرْ لِلَّهِ ۚ وَمَنْ يَشْكُرْ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِ ۖ وَمَنْ كَفَرَ فَإِنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٌ [31:12]

Kuma lalle haƙĩƙa Mun bai wa Luƙmãn hikima. (Muka ce masa) Ka gõde wa Allah, kuma wanda ya gõde, to yanã gõdẽwa ne dõmin kansa kawai kuma wanda ya kãfirta, to, lalle, Allah Mawadãci ne, Gõdadde.

### الآية 31:13

> ﻿وَإِذْ قَالَ لُقْمَانُ لِابْنِهِ وَهُوَ يَعِظُهُ يَا بُنَيَّ لَا تُشْرِكْ بِاللَّهِ ۖ إِنَّ الشِّرْكَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ [31:13]

Kuma a lõkacin da Luƙmãn ya ce wa ɗansa, alhãli kuwa yanã yi masa wa'azi, "Yã ƙaramin ɗãna! Kada ka yi shirki game da Allah. Lalle shirki wani zãlunci ne mai girma."

### الآية 31:14

> ﻿وَوَصَّيْنَا الْإِنْسَانَ بِوَالِدَيْهِ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ وَهْنًا عَلَىٰ وَهْنٍ وَفِصَالُهُ فِي عَامَيْنِ أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ إِلَيَّ الْمَصِيرُ [31:14]

Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa) "Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take."

### الآية 31:15

> ﻿وَإِنْ جَاهَدَاكَ عَلَىٰ أَنْ تُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا ۖ وَصَاحِبْهُمَا فِي الدُّنْيَا مَعْرُوفًا ۖ وَاتَّبِعْ سَبِيلَ مَنْ أَنَابَ إِلَيَّ ۚ ثُمَّ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ [31:15]

"Kuma idan mahaifanka suka tsananta\* maka ga ka yi shirki game da Ni, ga abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'a. Kuma ka abũce su a cikin dũniya gwargwadon sharĩ'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa gare Ni, sa'an nan zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* A bãyan haƙƙin Allah sai haƙƙin iyãye. Sabõda haka ba zã a yi ɗã'a ga iyãye ba ga abin da ya sãɓãwa Allah.

### الآية 31:16

> ﻿يَا بُنَيَّ إِنَّهَا إِنْ تَكُ مِثْقَالَ حَبَّةٍ مِنْ خَرْدَلٍ فَتَكُنْ فِي صَخْرَةٍ أَوْ فِي السَّمَاوَاتِ أَوْ فِي الْأَرْضِ يَأْتِ بِهَا اللَّهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٌ [31:16]

"Yã ƙaramin ɗãna! Lalle ita idan gwargwadon ƙwãyar kõmayya ce ta kasance, to, ta kasance a cikin wani falalen dũtse, kõ a cikin sammai, kõ a cikin ƙasã, Allah zai kãwo ta Lalle Allah Mai tausasãwa ne, Masani."

### الآية 31:17

> ﻿يَا بُنَيَّ أَقِمِ الصَّلَاةَ وَأْمُرْ بِالْمَعْرُوفِ وَانْهَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَاصْبِرْ عَلَىٰ مَا أَصَابَكَ ۖ إِنَّ ذَٰلِكَ مِنْ عَزْمِ الْأُمُورِ [31:17]

"Yã ƙaramin ɗãna! Ka tsai da salla, kuma ka yi umurni da abin da aka sani, kuma ka yi hani daga abin da ba a sani ba, kuma ka yi haƙuri a kan abin da ya sãme ka. Lalle, wancan yanã daga muhimman al'amura."

### الآية 31:18

> ﻿وَلَا تُصَعِّرْ خَدَّكَ لِلنَّاسِ وَلَا تَمْشِ فِي الْأَرْضِ مَرَحًا ۖ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخْتَالٍ فَخُورٍ [31:18]

"Kada ka karkatar da kundukukinka\* ga mutãne, kada ka yi tafiya a cikin ƙasã kanã mai nũna fãɗin rai. Lalle, Allah bã Ya son dukan mai tãƙama, mai alfahari."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
\* Karkata kundukuki ga mutãne, alamar wulãkanta su ne.

### الآية 31:19

> ﻿وَاقْصِدْ فِي مَشْيِكَ وَاغْضُضْ مِنْ صَوْتِكَ ۚ إِنَّ أَنْكَرَ الْأَصْوَاتِ لَصَوْتُ الْحَمِيرِ [31:19]

"Kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka runtse ga sautinka. Lalle mafi mũnin sautuka haƙĩƙa shĩ ne sautin jãkuna.\* "
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* A nan ne iyãkar wasiyyar Luƙmãn ga ɗansa. Sa'an nan kuma Allah Ya ci gaba da bayãnin yadda ake tarbiyyar mutãne.

### الآية 31:20

> ﻿أَلَمْ تَرَوْا أَنَّ اللَّهَ سَخَّرَ لَكُمْ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَأَسْبَغَ عَلَيْكُمْ نِعَمَهُ ظَاهِرَةً وَبَاطِنَةً ۗ وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يُجَادِلُ فِي اللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَلَا هُدًى وَلَا كِتَابٍ مُنِيرٍ [31:20]

Ashe, ba ku gani ba, cẽwa Allah Yã hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasã, kuma Ya zuba ni'imõminsa a kanku, bayyanannu da ɓõyayyu? Kuma akwai daga mutãne wanda ke yin jidãli ga al'amarin Allah, bã da wani ilmi ba, kuma bã da wata shiriya ba, kumã ba da wani littãfi mai haskakãwa ba.

### الآية 31:21

> ﻿وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّبِعُوا مَا أَنْزَلَ اللَّهُ قَالُوا بَلْ نَتَّبِعُ مَا وَجَدْنَا عَلَيْهِ آبَاءَنَا ۚ أَوَلَوْ كَانَ الشَّيْطَانُ يَدْعُوهُمْ إِلَىٰ عَذَابِ السَّعِيرِ [31:21]

Kuma idan aka ce musu, "Ku bi abin da Allah ya saukar," sai su ce: "Ã'a, munã bin abin da muka sãmi ubanninmu a kansa." shin kõ dã Shaiɗan nã kiran su ne zuwa ga azãbar sa'ir,

### الآية 31:22

> ﻿۞ وَمَنْ يُسْلِمْ وَجْهَهُ إِلَى اللَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَىٰ ۗ وَإِلَى اللَّهِ عَاقِبَةُ الْأُمُورِ [31:22]

kuma wanda ya mĩka fuskarsa zuwa ga Allah, alhãli kuma yanã mai kyautatãwa, to, lalle ya yi riƙo ga igiya amintacciya. Kuma zuwa ga Allah ãƙibar al'amura take.

### الآية 31:23

> ﻿وَمَنْ كَفَرَ فَلَا يَحْزُنْكَ كُفْرُهُ ۚ إِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ فَنُنَبِّئُهُمْ بِمَا عَمِلُوا ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ [31:23]

Kuma wanda ya kãfirta, to, kada kãfircinsa ya baƙanta maka rai, zuwa gare Mu makõmarsu take, sa'an nan Mu bã su lãbari game da abin da suka aikata. Lalle Allah, Masani ne ga abin da ke a cikin ƙirãza.

### الآية 31:24

> ﻿نُمَتِّعُهُمْ قَلِيلًا ثُمَّ نَضْطَرُّهُمْ إِلَىٰ عَذَابٍ غَلِيظٍ [31:24]

Munã jĩshe su dãdi kaɗan sa'an nan Mu tĩlasta su ga shiga zuwa azãba kakkaura.

### الآية 31:25

> ﻿وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ ۚ قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ [31:25]

Kuma lalle, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halĩtta sammai da kasa?" Lalle zã su ce: "Allah ne." Ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah" Ã'a, mafi yawansu ba su sani ba.

### الآية 31:26

> ﻿لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ إِنَّ اللَّهَ هُوَ الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ [31:26]

Abin da yake a cikin sammai da ƙasa duka na Allah kawai ne. Lalle, Allah Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde.

### الآية 31:27

> ﻿وَلَوْ أَنَّمَا فِي الْأَرْضِ مِنْ شَجَرَةٍ أَقْلَامٌ وَالْبَحْرُ يَمُدُّهُ مِنْ بَعْدِهِ سَبْعَةُ أَبْحُرٍ مَا نَفِدَتْ كَلِمَاتُ اللَّهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ [31:27]

Kuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su ƙãre ba.\* Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Wannan bayãni ne ga yawan ilmin Allah, watau yanã nũnawa mutãne cewa su yi aiki da ilmin da Ya bã su, mai amfãni zuwa gare su, kada su wuce shi zuwa neman wani ilmi daga wani abu, su bar Allah, su halaka a kan wani ilmi da bai umurce su da su yi aiki da shi ba. Ilmin da Ya bã su a cikin Alƙur'ãni shi ne sharĩ'a wãtau hanya mai kai su ga Aljanna. Sauran hanyõyi ɓata ne.

### الآية 31:28

> ﻿مَا خَلْقُكُمْ وَلَا بَعْثُكُمْ إِلَّا كَنَفْسٍ وَاحِدَةٍ ۗ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ [31:28]

Halittarku bã ta zama ba, kuma tãyar da ku bai zama ba, fãce kamar rai guda. Lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani.

### الآية 31:29

> ﻿أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ كُلٌّ يَجْرِي إِلَىٰ أَجَلٍ مُسَمًّى وَأَنَّ اللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ [31:29]

Ashe, ba ku ga, lalle, Allah Yanã shigar da dare a cikin rãna ba, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare kuma Yã hõre rãnã da watã kõwane yanã gudãna zuwa a ajali ambatacce kuma lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa?

### الآية 31:30

> ﻿ذَٰلِكَ بِأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ الْبَاطِلُ وَأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ [31:30]

Wannan fa dõmin Allah Shĩ ne Gaskiya, kuma abin da suke kira wanda bã Shi ba, shi ne ƙaryã, kuma lalle, Alah shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.

### الآية 31:31

> ﻿أَلَمْ تَرَ أَنَّ الْفُلْكَ تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِنِعْمَتِ اللَّهِ لِيُرِيَكُمْ مِنْ آيَاتِهِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ [31:31]

Ashe, ba ka ga lalle jirgin ruwa nã gudãna ba a cikin tẽku da ni'imar Allah dõmin Ya nũna muku daga ãyõyinSa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, mai gõdiya.

### الآية 31:32

> ﻿وَإِذَا غَشِيَهُمْ مَوْجٌ كَالظُّلَلِ دَعَوُا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ فَمِنْهُمْ مُقْتَصِدٌ ۚ وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلَّا كُلُّ خَتَّارٍ كَفُورٍ [31:32]

Kuma idan tãguwar ruwa, kamar duwatsu, ta rufe su, sai su kira Allah sunã tsarkakẽwar addini a gare shi. To, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudu, sai daga cikinsu akwai mai taƙaitãwa kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce dukkan mayaudari mai yawan kãfirci.

### الآية 31:33

> ﻿يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمْ وَاخْشَوْا يَوْمًا لَا يَجْزِي وَالِدٌ عَنْ وَلَدِهِ وَلَا مَوْلُودٌ هُوَ جَازٍ عَنْ وَالِدِهِ شَيْئًا ۚ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ ۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا وَلَا يَغُرَّنَّكُمْ بِاللَّهِ الْغَرُورُ [31:33]

Ya ku mutãne! Ku bauta wa Ubangijinku da taƙawa, kuma ku ji tsõron wani yini, rãnar da wani mahaifi bã ya sãka wa abin haifuwarsa da kõme kuma wani abin haifuwa bã ya sãka wa mahaifinsa da kõme. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Sabõda haka, kada wata rãyuwa ta kusa ta rũde ku, kuma kada marũɗin\* nan ya rũɗẽ ku game da Allah.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Shaiɗan.

### الآية 31:34

> ﻿إِنَّ اللَّهَ عِنْدَهُ عِلْمُ السَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ الْغَيْثَ وَيَعْلَمُ مَا فِي الْأَرْحَامِ ۖ وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ مَاذَا تَكْسِبُ غَدًا ۖ وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ بِأَيِّ أَرْضٍ تَمُوتُ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ [31:34]

Lalle, Allah a wurinsa kawai sanin sa'a yake, kuma Yanã saukar da girgije, kuma Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa.

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/31.md)
- [كل تفاسير سورة لقمان
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/31.md)
- [ترجمات سورة لقمان
](https://quranpedia.net/translations/31.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/31/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
