---
title: "ترجمة سورة الدّخان - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/44/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/44/book/1999"
surah_id: "44"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة الدّخان - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/44/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة الدّخان - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/44/book/1999*.

Translation of Surah الدّخان from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 44:1

> حم [44:1]

Ḥ. M̃.

### الآية 44:2

> ﻿وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ [44:2]

Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.

### الآية 44:3

> ﻿إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنْذِرِينَ [44:3]

Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.

### الآية 44:4

> ﻿فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ [44:4]

A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.

### الآية 44:5

> ﻿أَمْرًا مِنْ عِنْدِنَا ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ [44:5]

Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.

### الآية 44:6

> ﻿رَحْمَةً مِنْ رَبِّكَ ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ [44:6]

Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.

### الآية 44:7

> ﻿رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِنْ كُنْتُمْ مُوقِنِينَ [44:7]

(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).

### الآية 44:8

> ﻿لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ [44:8]

Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.

### الآية 44:9

> ﻿بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ يَلْعَبُونَ [44:9]

A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.

### الآية 44:10

> ﻿فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَانٍ مُبِينٍ [44:10]

Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.

### الآية 44:11

> ﻿يَغْشَى النَّاسَ ۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ [44:11]

Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.

### الآية 44:12

> ﻿رَبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ [44:12]

Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.

### الآية 44:13

> ﻿أَنَّىٰ لَهُمُ الذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مُبِينٌ [44:13]

Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?

### الآية 44:14

> ﻿ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّمٌ مَجْنُونٌ [44:14]

Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa\* ne, mahaukaci."
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Sunã nufin waɗansu mutãne ne ke gaya wa Annabi Alƙur'ãni, kõ kuma daga alãma watau wai Annabi taɓaɓɓe ne, mahaukaci. Taɓaɓɓe da mahaukaci duka ma'anarsu guda ce, watau marashin hankali,wanda aka yi wa alãma da rashin hankali.

### الآية 44:15

> ﻿إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَائِدُونَ [44:15]

Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).

### الآية 44:16

> ﻿يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَىٰ إِنَّا مُنْتَقِمُونَ [44:16]

Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.

### الآية 44:17

> ﻿۞ وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ [44:17]

Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.

### الآية 44:18

> ﻿أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ [44:18]

(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."

### الآية 44:19

> ﻿وَأَنْ لَا تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي آتِيكُمْ بِسُلْطَانٍ مُبِينٍ [44:19]

"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."

### الآية 44:20

> ﻿وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَنْ تَرْجُمُونِ [44:20]

"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."

### الآية 44:21

> ﻿وَإِنْ لَمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ [44:21]

"Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."

### الآية 44:22

> ﻿فَدَعَا رَبَّهُ أَنَّ هَٰؤُلَاءِ قَوْمٌ مُجْرِمُونَ [44:22]

Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.

### الآية 44:23

> ﻿فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلًا إِنَّكُمْ مُتَّبَعُونَ [44:23]

(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"

### الآية 44:24

> ﻿وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُنْدٌ مُغْرَقُونَ [44:24]

"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."

### الآية 44:25

> ﻿كَمْ تَرَكُوا مِنْ جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ [44:25]

Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.

### الآية 44:26

> ﻿وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ [44:26]

Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.

### الآية 44:27

> ﻿وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ [44:27]

Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.

### الآية 44:28

> ﻿كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آخَرِينَ [44:28]

Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.

### الآية 44:29

> ﻿فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنْظَرِينَ [44:29]

Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka \*a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Watau sama da ƙasa ba su girgizu ba sabõda halaka su da aka yi kamar ba a yi, kõme ba.

### الآية 44:30

> ﻿وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِ [44:30]

Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.

### الآية 44:31

> ﻿مِنْ فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُ كَانَ عَالِيًا مِنَ الْمُسْرِفِينَ [44:31]

Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.

### الآية 44:32

> ﻿وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَ [44:32]

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.

### الآية 44:33

> ﻿وَآتَيْنَاهُمْ مِنَ الْآيَاتِ مَا فِيهِ بَلَاءٌ مُبِينٌ [44:33]

Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna\*
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* An bai wa Banĩ lsrã'ĩla ni'imar ilmi na Taurãta, an ɗaukaka su, sabõda aiki da ilmin, a kan sauran mutãnen zãmaninsu, kuma aka bã su ãyõyin mu'ujiza kamar tsãge teku da mannu da salwa da sauransu, amma kuma dukkan waɗannan ni'imomĩn sai da suka gushe a lõkacin da suka sãɓawa umurnin Allah, sai kuma ƙasƙanci ya maye musu daga bãya. Wannan kuma wa'azi ne ga Musulmi waɗanda Allah Ya ɗaukaka su da Alƙur'ãni a kan sauran mutãne, idan sun kauce masa zã su wulãkantu.

### الآية 44:34

> ﻿إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَيَقُولُونَ [44:34]

Lalle waɗannan mutãne\*, haƙĩka, sunã cẽwa,
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Anã nufin mutãnen zãmanin Annabi Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, waɗanda ake kiran su zuwa ga Musulunci.

### الآية 44:35

> ﻿إِنْ هِيَ إِلَّا مَوْتَتُنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنْشَرِينَ [44:35]

"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."

### الآية 44:36

> ﻿فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ [44:36]

"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."

### الآية 44:37

> ﻿أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَالَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَاهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ [44:37]

shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.

### الآية 44:38

> ﻿وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ [44:38]

Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.

### الآية 44:39

> ﻿مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ [44:39]

Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.

### الآية 44:40

> ﻿إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ [44:40]

Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.

### الآية 44:41

> ﻿يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَنْ مَوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنْصَرُونَ [44:41]

Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.

### الآية 44:42

> ﻿إِلَّا مَنْ رَحِمَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ [44:42]

fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

### الآية 44:43

> ﻿إِنَّ شَجَرَتَ الزَّقُّومِ [44:43]

Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),

### الآية 44:44

> ﻿طَعَامُ الْأَثِيمِ [44:44]

Ita ce abincin mai laifi.

### الآية 44:45

> ﻿كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِ [44:45]

Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.

### الآية 44:46

> ﻿كَغَلْيِ الْحَمِيمِ [44:46]

Kamar tafasar ruwan zãfi.

### الآية 44:47

> ﻿خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَاءِ الْجَحِيمِ [44:47]

(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."

### الآية 44:48

> ﻿ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ [44:48]

"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."

### الآية 44:49

> ﻿ذُقْ إِنَّكَ أَنْتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ [44:49]

(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"

### الآية 44:50

> ﻿إِنَّ هَٰذَا مَا كُنْتُمْ بِهِ تَمْتَرُونَ [44:50]

"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."

### الآية 44:51

> ﻿إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍ [44:51]

Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.

### الآية 44:52

> ﻿فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ [44:52]

A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.

### الآية 44:53

> ﻿يَلْبَسُونَ مِنْ سُنْدُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُتَقَابِلِينَ [44:53]

Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.

### الآية 44:54

> ﻿كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُمْ بِحُورٍ عِينٍ [44:54]

Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.

### الآية 44:55

> ﻿يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَ [44:55]

Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).

### الآية 44:56

> ﻿لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَىٰ ۖ وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ [44:56]

Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.

### الآية 44:57

> ﻿فَضْلًا مِنْ رَبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ [44:57]

Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.

### الآية 44:58

> ﻿فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ [44:58]

Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.

### الآية 44:59

> ﻿فَارْتَقِبْ إِنَّهُمْ مُرْتَقِبُونَ [44:59]

Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.\*
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Mãsu jira ne ga abin da zai sãme su idan ba su yi ĩmãni ba, watau ni'imar da aka ba su zã ta gushe ke nan dõmin ba su aiwatar da ita ba a kan umuruin Allah.

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/44.md)
- [كل تفاسير سورة الدّخان
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/44.md)
- [ترجمات سورة الدّخان
](https://quranpedia.net/translations/44.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/44/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
