---
title: "ترجمة سورة القيامة - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/75/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/75/book/1999"
surah_id: "75"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة القيامة - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/75/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة القيامة - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/75/book/1999*.

Translation of Surah القيامة from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 75:1

> لَا أُقْسِمُ بِيَوْمِ الْقِيَامَةِ [75:1]

Bã sai Nã yi rantsuwa\* da Rãnar ¡iyãma ba.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
\* Wasu na fassarawa: lna rantsuwa da Rãnar Ƙiyama. A ganina, da tabbatar da rantsuwar da kuma kore ta duka ɗaya ne, maƙasũdi dai jan hankalin mai karãtu ga abin da yake a ciki, na hikimar Allah.

### الآية 75:2

> ﻿وَلَا أُقْسِمُ بِالنَّفْسِ اللَّوَّامَةِ [75:2]

Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin\* kansa ba.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Kowane rai na zargin kansa idan bai yi aikin alheri ba, ko kuma bai yi fiye da wanda ya yi ba, ko kuma bai aikata wanda ya fi kyãwo ba a lokacin aikinsa.

### الآية 75:3

> ﻿أَيَحْسَبُ الْإِنْسَانُ أَلَّنْ نَجْمَعَ عِظَامَهُ [75:3]

Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?

### الآية 75:4

> ﻿بَلَىٰ قَادِرِينَ عَلَىٰ أَنْ نُسَوِّيَ بَنَانَهُ [75:4]

Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.

### الآية 75:5

> ﻿بَلْ يُرِيدُ الْإِنْسَانُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُ [75:5]

Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.

### الآية 75:6

> ﻿يَسْأَلُ أَيَّانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ [75:6]

Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"

### الآية 75:7

> ﻿فَإِذَا بَرِقَ الْبَصَرُ [75:7]

To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).

### الآية 75:8

> ﻿وَخَسَفَ الْقَمَرُ [75:8]

Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).

### الآية 75:9

> ﻿وَجُمِعَ الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ [75:9]

Aka tãra rãnã da watã

### الآية 75:10

> ﻿يَقُولُ الْإِنْسَانُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ الْمَفَرُّ [75:10]

Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"

### الآية 75:11

> ﻿كَلَّا لَا وَزَرَ [75:11]

A'aha! bãbu mafaka.

### الآية 75:12

> ﻿إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمُسْتَقَرُّ [75:12]

zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.

### الآية 75:13

> ﻿يُنَبَّأُ الْإِنْسَانُ يَوْمَئِذٍ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ [75:13]

Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.

### الآية 75:14

> ﻿بَلِ الْإِنْسَانُ عَلَىٰ نَفْسِهِ بَصِيرَةٌ [75:14]

Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.

### الآية 75:15

> ﻿وَلَوْ أَلْقَىٰ مَعَاذِيرَهُ [75:15]

Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).

### الآية 75:16

> ﻿لَا تُحَرِّكْ بِهِ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِ [75:16]

Kada ka mõtsar\* da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Dangantakar wannan ãya da ta sama da ita, ita ce bambancin Annabi mai gaggawar karɓar umurnin Allah da ƙyamar kãfiri ga karɓarsa, da bayãnin sauƙaƙewar Allah ga mai bin umurninSa.

### الآية 75:17

> ﻿إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ [75:17]

Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.

### الآية 75:18

> ﻿فَإِذَا قَرَأْنَاهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ [75:18]

To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.

### الآية 75:19

> ﻿ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُ [75:19]

sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.

### الآية 75:20

> ﻿كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ [75:20]

A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.

### الآية 75:21

> ﻿وَتَذَرُونَ الْآخِرَةَ [75:21]

Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).

### الآية 75:22

> ﻿وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَاضِرَةٌ [75:22]

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.

### الآية 75:23

> ﻿إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ [75:23]

Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.

### الآية 75:24

> ﻿وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ بَاسِرَةٌ [75:24]

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.

### الآية 75:25

> ﻿تَظُنُّ أَنْ يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌ [75:25]

Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.

### الآية 75:26

> ﻿كَلَّا إِذَا بَلَغَتِ التَّرَاقِيَ [75:26]

A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.

### الآية 75:27

> ﻿وَقِيلَ مَنْ ۜ رَاقٍ [75:27]

kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"

### الآية 75:28

> ﻿وَظَنَّ أَنَّهُ الْفِرَاقُ [75:28]

Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.

### الآية 75:29

> ﻿وَالْتَفَّتِ السَّاقُ بِالسَّاقِ [75:29]

Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.

### الآية 75:30

> ﻿إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمَسَاقُ [75:30]

Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa\* take.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Ranar kora mutane, kamar ana gargaɗa tumãki, zuwa ga tsayuwa a gaba ga Allah, dõmin hisabi.

### الآية 75:31

> ﻿فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ [75:31]

To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!

### الآية 75:32

> ﻿وَلَٰكِنْ كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ [75:32]

Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!

### الآية 75:33

> ﻿ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰ أَهْلِهِ يَتَمَطَّىٰ [75:33]

Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.

### الآية 75:34

> ﻿أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ [75:34]

Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.

### الآية 75:35

> ﻿ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ [75:35]

Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.

### الآية 75:36

> ﻿أَيَحْسَبُ الْإِنْسَانُ أَنْ يُتْرَكَ سُدًى [75:36]

Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?

### الآية 75:37

> ﻿أَلَمْ يَكُ نُطْفَةً مِنْ مَنِيٍّ يُمْنَىٰ [75:37]

Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)

### الآية 75:38

> ﻿ثُمَّ كَانَ عَلَقَةً فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ [75:38]

Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;

### الآية 75:39

> ﻿فَجَعَلَ مِنْهُ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنْثَىٰ [75:39]

Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?

### الآية 75:40

> ﻿أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَادِرٍ عَلَىٰ أَنْ يُحْيِيَ الْمَوْتَىٰ [75:40]

Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?\*
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Ana son mai karãtu a nan ya ce: a ɓoye بلى وأنا على ذلك من الشاهدين.

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/75.md)
- [كل تفاسير سورة القيامة
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/75.md)
- [ترجمات سورة القيامة
](https://quranpedia.net/translations/75.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/75/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
