---
title: "ترجمة سورة عبس - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/80/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/80/book/1999"
surah_id: "80"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة عبس - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/80/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة عبس - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/80/book/1999*.

Translation of Surah عبس from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 80:1

> عَبَسَ وَتَوَلَّىٰ [80:1]

Yã game huska\* kuma ya jũya bãya.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Wani makãho, Abdullahi bin Ummi Maktũm ya je wurin Annabi dõmin ya musulunta, sai ya iske a lõkacin nan Annabi na ƙõƙarin shiryar da wasu manyan mutãne na Ƙuraishãwa, sai wannan makãhon ya yanke maganar Annabi da su, bã da saninsa ba, alhãli Annabi na bũrin su musulunta dõmin darajarsu ga idon mutãnensu. Saboda haka Annabi, (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ya ɓata Fuska, ya tafi dõmin ɓacin ransa, saboda rashin musuluntarsu. Bãyan haka Annabi nã girmama Abdullahi ƙwarai, idan ya je wurinsa sai ya ce masa "Maraba da wanda Ubangijina Ya zarge ni sabõda shi." Kuma ya shimfiɗa masa mayafinsa, idan ya fita tafiya, yakan sanya shi riƙon garin Madina, ƙissar tana nũna girmamawar Allah ga Annabi da Ya ce: "Ya game Fuska." Bai ce masa: "Domin ka game Fuska" ba, sai ya faɗa a cikin hali mai sauƙi.".

### الآية 80:2

> ﻿أَنْ جَاءَهُ الْأَعْمَىٰ [80:2]

Sabõda makãho yã je masa.

### الآية 80:3

> ﻿وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُ يَزَّكَّىٰ [80:3]

To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.

### الآية 80:4

> ﻿أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنْفَعَهُ الذِّكْرَىٰ [80:4]

Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?

### الآية 80:5

> ﻿أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَىٰ [80:5]

Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.

### الآية 80:6

> ﻿فَأَنْتَ لَهُ تَصَدَّىٰ [80:6]

Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!

### الآية 80:7

> ﻿وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ [80:7]

To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?

### الآية 80:8

> ﻿وَأَمَّا مَنْ جَاءَكَ يَسْعَىٰ [80:8]

Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.

### الآية 80:9

> ﻿وَهُوَ يَخْشَىٰ [80:9]

Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.

### الآية 80:10

> ﻿فَأَنْتَ عَنْهُ تَلَهَّىٰ [80:10]

Kai kuma kã shagala ga barinsa!

### الآية 80:11

> ﻿كَلَّا إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ [80:11]

A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.

### الآية 80:12

> ﻿فَمَنْ شَاءَ ذَكَرَهُ [80:12]

Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).

### الآية 80:13

> ﻿فِي صُحُفٍ مُكَرَّمَةٍ [80:13]

(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,

### الآية 80:14

> ﻿مَرْفُوعَةٍ مُطَهَّرَةٍ [80:14]

Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.

### الآية 80:15

> ﻿بِأَيْدِي سَفَرَةٍ [80:15]

A cikin hannãyen mala'iku marubũta.

### الآية 80:16

> ﻿كِرَامٍ بَرَرَةٍ [80:16]

Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.

### الآية 80:17

> ﻿قُتِلَ الْإِنْسَانُ مَا أَكْفَرَهُ [80:17]

An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!

### الآية 80:18

> ﻿مِنْ أَيِّ شَيْءٍ خَلَقَهُ [80:18]

Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

### الآية 80:19

> ﻿مِنْ نُطْفَةٍ خَلَقَهُ فَقَدَّرَهُ [80:19]

Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).

### الآية 80:20

> ﻿ثُمَّ السَّبِيلَ يَسَّرَهُ [80:20]

Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.

### الآية 80:21

> ﻿ثُمَّ أَمَاتَهُ فَأَقْبَرَهُ [80:21]

Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.

### الآية 80:22

> ﻿ثُمَّ إِذَا شَاءَ أَنْشَرَهُ [80:22]

Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.

### الآية 80:23

> ﻿كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَا أَمَرَهُ [80:23]

Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).

### الآية 80:24

> ﻿فَلْيَنْظُرِ الْإِنْسَانُ إِلَىٰ طَعَامِهِ [80:24]

To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.

### الآية 80:25

> ﻿أَنَّا صَبَبْنَا الْمَاءَ صَبًّا [80:25]

Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.

### الآية 80:26

> ﻿ثُمَّ شَقَقْنَا الْأَرْضَ شَقًّا [80:26]

Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.

### الآية 80:27

> ﻿فَأَنْبَتْنَا فِيهَا حَبًّا [80:27]

Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.

### الآية 80:28

> ﻿وَعِنَبًا وَقَضْبًا [80:28]

Da inabi da ciyãwa.

### الآية 80:29

> ﻿وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا [80:29]

Da zaitũni da itãcen dabĩno.

### الآية 80:30

> ﻿وَحَدَائِقَ غُلْبًا [80:30]

Da lambuna, mãsu yawan itãce.

### الآية 80:31

> ﻿وَفَاكِهَةً وَأَبًّا [80:31]

Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.

### الآية 80:32

> ﻿مَتَاعًا لَكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ [80:32]

Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.

### الآية 80:33

> ﻿فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ [80:33]

To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.

### الآية 80:34

> ﻿يَوْمَ يَفِرُّ الْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ [80:34]

Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.

### الآية 80:35

> ﻿وَأُمِّهِ وَأَبِيهِ [80:35]

Da uwarsa da ubansa.

### الآية 80:36

> ﻿وَصَاحِبَتِهِ وَبَنِيهِ [80:36]

Da mãtarsa da ɗiyansa.

### الآية 80:37

> ﻿لِكُلِّ امْرِئٍ مِنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ [80:37]

Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.

### الآية 80:38

> ﻿وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُسْفِرَةٌ [80:38]

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.

### الآية 80:39

> ﻿ضَاحِكَةٌ مُسْتَبْشِرَةٌ [80:39]

Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.

### الآية 80:40

> ﻿وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ [80:40]

Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.

### الآية 80:41

> ﻿تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ [80:41]

Baƙi zai rufe su.

### الآية 80:42

> ﻿أُولَٰئِكَ هُمُ الْكَفَرَةُ الْفَجَرَةُ [80:42]

Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/80.md)
- [كل تفاسير سورة عبس
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/80.md)
- [ترجمات سورة عبس
](https://quranpedia.net/translations/80.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/80/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
