---
title: "ترجمة سورة التكوير - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/81/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/81/book/1999"
surah_id: "81"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة التكوير - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/81/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة التكوير - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/81/book/1999*.

Translation of Surah التكوير from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 81:1

> إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ [81:1]

Idan rãna aka shafe haskenta

### الآية 81:2

> ﻿وَإِذَا النُّجُومُ انْكَدَرَتْ [81:2]

Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).

### الآية 81:3

> ﻿وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ [81:3]

Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.

### الآية 81:4

> ﻿وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ [81:4]

Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna\* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Rãƙuma mãsu ciki ɗan wata gõma.

### الآية 81:5

> ﻿وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ [81:5]

Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.

### الآية 81:6

> ﻿وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ [81:6]

Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.

### الآية 81:7

> ﻿وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ [81:7]

Kuma idan rãyuka aka haɗa\* su da jikunkunansu.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Ko kuma, aka haɗa kõwane mutum da irin mutãnensa a Aljanna ko a wuta.

### الآية 81:8

> ﻿وَإِذَا الْمَوْءُودَةُ سُئِلَتْ [81:8]

Kuma idan wadda aka turbuɗe\* ta da rai aka tambaye ta.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* A cikin zãmanin jahiliyya Lãrabãwa bã su son a haifa musu 'ya'ya mãta dõmin haka har sukan turbuɗe 'ya'yansu dõmin kada su yi abin kunya ko kuma su talauce wajen yi musu aure.

### الآية 81:9

> ﻿بِأَيِّ ذَنْبٍ قُتِلَتْ [81:9]

"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"

### الآية 81:10

> ﻿وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ [81:10]

Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).

### الآية 81:11

> ﻿وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْ [81:11]

Kuma idan sama aka fẽɗe ta.

### الآية 81:12

> ﻿وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ [81:12]

Kuma idan Jahĩm aka hũra ta

### الآية 81:13

> ﻿وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ [81:13]

Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.

### الآية 81:14

> ﻿عَلِمَتْ نَفْسٌ مَا أَحْضَرَتْ [81:14]

Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).

### الآية 81:15

> ﻿فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ [81:15]

To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã\* ba.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
\* Masu tafiya suna kõmawa bãya.

### الآية 81:16

> ﻿الْجَوَارِ الْكُنَّسِ [81:16]

Mãsu gudu suna ɓũya.

### الآية 81:17

> ﻿وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ [81:17]

Da dare idan ya bãyar da bãya.

### الآية 81:18

> ﻿وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ [81:18]

Da sãfiya idan ta yi lumfashi.

### الآية 81:19

> ﻿إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ [81:19]

Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.

### الآية 81:20

> ﻿ذِي قُوَّةٍ عِنْدَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍ [81:20]

Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.

### الآية 81:21

> ﻿مُطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ [81:21]

Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.

### الآية 81:22

> ﻿وَمَا صَاحِبُكُمْ بِمَجْنُونٍ [81:22]

Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.

### الآية 81:23

> ﻿وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِ [81:23]

Kuma lalle ne, yã gan shi(5) a cikin sararin sama mabayyani.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 (5) Annabi ya ga Mala'ika Jibirilu ya san shi. Sabõda haka wani aljani bã zai yi kama da shi ba balle ya kãwo masa ƙarya.

### الآية 81:24

> ﻿وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍ [81:24]

Kuma shi, ga gaibi(6) bã mai rowa ba ne.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 (6) Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cewa daga Allah yake, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne.

### الآية 81:25

> ﻿وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَجِيمٍ [81:25]

Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.

### الآية 81:26

> ﻿فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ [81:26]

Shin, a inã zã ku tafi?

### الآية 81:27

> ﻿إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِلْعَالَمِينَ [81:27]

Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.

### الآية 81:28

> ﻿لِمَنْ شَاءَ مِنْكُمْ أَنْ يَسْتَقِيمَ [81:28]

Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.

### الآية 81:29

> ﻿وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَنْ يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ [81:29]

Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/81.md)
- [كل تفاسير سورة التكوير
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/81.md)
- [ترجمات سورة التكوير
](https://quranpedia.net/translations/81.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/81/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
