---
title: "ترجمة سورة الطارق - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/86/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/86/book/1999"
surah_id: "86"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة الطارق - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/86/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة الطارق - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/86/book/1999*.

Translation of Surah الطارق from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 86:1

> وَالسَّمَاءِ وَالطَّارِقِ [86:1]

Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.

### الآية 86:2

> ﻿وَمَا أَدْرَاكَ مَا الطَّارِقُ [86:2]

To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?

### الآية 86:3

> ﻿النَّجْمُ الثَّاقِبُ [86:3]

Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.\*
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Wannan ya yi kama da zuwan Annabi a cikin jahiliyya don ya haskaka duniya da ilimi kamar yadda girgije ke ba da ruwa saboda tsiron ƙasa, hantsar uwa ta ba da nono saboda jariri kuma maniyi ya zo lokacin Jima'i.

### الآية 86:4

> ﻿إِنْ كُلُّ نَفْسٍ لَمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ [86:4]

Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.

### الآية 86:5

> ﻿فَلْيَنْظُرِ الْإِنْسَانُ مِمَّ خُلِقَ [86:5]

To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?

### الآية 86:6

> ﻿خُلِقَ مِنْ مَاءٍ دَافِقٍ [86:6]

An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.

### الآية 86:7

> ﻿يَخْرُجُ مِنْ بَيْنِ الصُّلْبِ وَالتَّرَائِبِ [86:7]

Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.

### الآية 86:8

> ﻿إِنَّهُ عَلَىٰ رَجْعِهِ لَقَادِرٌ [86:8]

Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.

### الآية 86:9

> ﻿يَوْمَ تُبْلَى السَّرَائِرُ [86:9]

Rãnar da ake jarrabawar asirai.

### الآية 86:10

> ﻿فَمَا لَهُ مِنْ قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ [86:10]

Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).

### الآية 86:11

> ﻿وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الرَّجْعِ [86:11]

Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.

### الآية 86:12

> ﻿وَالْأَرْضِ ذَاتِ الصَّدْعِ [86:12]

Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,\*
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Dõmin fitar tsiro.

### الآية 86:13

> ﻿إِنَّهُ لَقَوْلٌ فَصْلٌ [86:13]

Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki\*
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Mai rabewa tsakanin ƙarya da gaskiya.

### الآية 86:14

> ﻿وَمَا هُوَ بِالْهَزْلِ [86:14]

Kuma shĩ bã bananci\* bane
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
\* Kãkãci.

### الآية 86:15

> ﻿إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا [86:15]

Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.

### الآية 86:16

> ﻿وَأَكِيدُ كَيْدًا [86:16]

Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.

### الآية 86:17

> ﻿فَمَهِّلِ الْكَافِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًا [86:17]

Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/86.md)
- [كل تفاسير سورة الطارق
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/86.md)
- [ترجمات سورة الطارق
](https://quranpedia.net/translations/86.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/86/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
