---
title: "ترجمة سورة الأعلى - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/87/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/87/book/1999"
surah_id: "87"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة الأعلى - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/87/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة الأعلى - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/87/book/1999*.

Translation of Surah الأعلى from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 87:1

> سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَى [87:1]

Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.

### الآية 87:2

> ﻿الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ [87:2]

Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.

### الآية 87:3

> ﻿وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ [87:3]

Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).

### الآية 87:4

> ﻿وَالَّذِي أَخْرَجَ الْمَرْعَىٰ [87:4]

Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.

### الآية 87:5

> ﻿فَجَعَلَهُ غُثَاءً أَحْوَىٰ [87:5]

Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.

### الآية 87:6

> ﻿سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنْسَىٰ [87:6]

Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.

### الآية 87:7

> ﻿إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ وَمَا يَخْفَىٰ [87:7]

Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.

### الآية 87:8

> ﻿وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَىٰ [87:8]

Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.

### الآية 87:9

> ﻿فَذَكِّرْ إِنْ نَفَعَتِ الذِّكْرَىٰ [87:9]

Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.

### الآية 87:10

> ﻿سَيَذَّكَّرُ مَنْ يَخْشَىٰ [87:10]

Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.

### الآية 87:11

> ﻿وَيَتَجَنَّبُهَا الْأَشْقَى [87:11]

Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,

### الآية 87:12

> ﻿الَّذِي يَصْلَى النَّارَ الْكُبْرَىٰ [87:12]

Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.

### الآية 87:13

> ﻿ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰ [87:13]

Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.

### الآية 87:14

> ﻿قَدْ أَفْلَحَ مَنْ تَزَكَّىٰ [87:14]

Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.

### الآية 87:15

> ﻿وَذَكَرَ اسْمَ رَبِّهِ فَصَلَّىٰ [87:15]

Kuma ya ambaci sũnan(5) Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 (5) Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran.

### الآية 87:16

> ﻿بَلْ تُؤْثِرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا [87:16]

Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.\*
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira.

### الآية 87:17

> ﻿وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰ [87:17]

Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.

### الآية 87:18

> ﻿إِنَّ هَٰذَا لَفِي الصُّحُفِ الْأُولَىٰ [87:18]

Lalle ne, wannan\* yanã a cikin littafan farko.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko.

### الآية 87:19

> ﻿صُحُفِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَىٰ [87:19]

Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/87.md)
- [كل تفاسير سورة الأعلى
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/87.md)
- [ترجمات سورة الأعلى
](https://quranpedia.net/translations/87.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/87/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
