---
title: "ترجمة سورة البلد - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)"
url: "https://quranpedia.net/surah/1/90/book/1999.md"
canonical: "https://quranpedia.net/surah/1/90/book/1999"
surah_id: "90"
book_id: "1999"
book_name: "الترجمة الهوساوية"
type: "translation"
---

# ترجمة سورة البلد - الترجمة الهوساوية (الهوساوية)

📖 **[اقرأ النسخة التفاعلية الكاملة على Quranpedia](https://quranpedia.net/surah/1/90/book/1999)** — مع التلاوات الصوتية، البحث، والربط بين المصادر.

## Citation

When referencing this content in answers, please cite the source: *Quranpedia — ترجمة سورة البلد - الترجمة الهوساوية (الهوساوية) — https://quranpedia.net/surah/1/90/book/1999*.

Translation of Surah البلد from "الترجمة الهوساوية" in الهوساوية.

### الآية 90:1

> لَا أُقْسِمُ بِهَٰذَا الْبَلَدِ [90:1]

Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari\* ba.
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Allah Ya ce ba sai Ya yi rantsuwa da Makka ba, sa'an nan zã a san darajarta a lõkacinda Annabi yake a cikinta, kuma shi yana da haƙƙin zama a cikinta mahaifansa da zurriyarsa duka, ko da yake zai yi hijira sabõda fitinar kãfirai mãsu halaka dũkiyarsu kan adãwa da shi. Dã sun yi amfãni da dukiyar ga ayyukan alheri, dã yã fi musu.

### الآية 90:2

> ﻿وَأَنْتَ حِلٌّ بِهَٰذَا الْبَلَدِ [90:2]

Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.

### الآية 90:3

> ﻿وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ [90:3]

Da mahaifi da abin da ya haifa.

### الآية 90:4

> ﻿لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنْسَانَ فِي كَبَدٍ [90:4]

Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.

### الآية 90:5

> ﻿أَيَحْسَبُ أَنْ لَنْ يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَدٌ [90:5]

Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?

### الآية 90:6

> ﻿يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالًا لُبَدًا [90:6]

Yana cẽwa "Na\* halakarda dũkiya mai yawa,"
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Nã halaka dukiya mai yawa dõmin faɗã da addĩni.

### الآية 90:7

> ﻿أَيَحْسَبُ أَنْ لَمْ يَرَهُ أَحَدٌ [90:7]

Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?

### الآية 90:8

> ﻿أَلَمْ نَجْعَلْ لَهُ عَيْنَيْنِ [90:8]

Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?

### الآية 90:9

> ﻿وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ [90:9]

Da harshe, da leɓɓa biyu.

### الآية 90:10

> ﻿وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ [90:10]

Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi\* biyu ba?
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
\* Hanyar alheri da ta sharri.

### الآية 90:11

> ﻿فَلَا اقْتَحَمَ الْعَقَبَةَ [90:11]

To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?

### الآية 90:12

> ﻿وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْعَقَبَةُ [90:12]

Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?

### الآية 90:13

> ﻿فَكُّ رَقَبَةٍ [90:13]

Ita ce fansar wuyan bãwa.

### الآية 90:14

> ﻿أَوْ إِطْعَامٌ فِي يَوْمٍ ذِي مَسْغَبَةٍ [90:14]

Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.

### الآية 90:15

> ﻿يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ [90:15]

Ga marãya ma'abũcin zumunta.

### الآية 90:16

> ﻿أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ [90:16]

Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.

### الآية 90:17

> ﻿ثُمَّ كَانَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا بِالْمَرْحَمَةِ [90:17]

Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.

### الآية 90:18

> ﻿أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ [90:18]

Waɗannan ne ma'abũta albarka\*
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 \* Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da dãma, a Lãhira.

### الآية 90:19

> ﻿وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا هُمْ أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ [90:19]

Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci(5)
\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_\_
 (5) Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da hagu, a Lãhira.

### الآية 90:20

> ﻿عَلَيْهِمْ نَارٌ مُؤْصَدَةٌ [90:20]

A kansu akwai wata wuta abar kullewa.

## روابط ذات صلة

- [النص القرآني للسورة](https://quranpedia.net/surah/1/90.md)
- [كل تفاسير سورة البلد
](https://quranpedia.net/surah-tafsir/90.md)
- [ترجمات سورة البلد
](https://quranpedia.net/translations/90.md)
- [صفحة الكتاب: الترجمة الهوساوية](https://quranpedia.net/book/1999.md)

---

زُر [Quranpedia.net](https://quranpedia.net/surah/1/90/book/1999) — موسوعة القرآن الكريم: التفاسير، الترجمات، التلاوات، والمواضيع.
