Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa* kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.— الترجمة الهوساوية
* Yahũdu da Nasãra sunã sanin Annabi Muhammadu tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da abin da ya zo da shi na Alƙur'ãni, kamar yadda suka san ɗiyan tsatsõnsu; kamar yadda Abdullahi ɗan Sallãmi ya ce wa Umar: "Lalle ne na san shi a lõkacin da na gan shi, kamar yadda nake sanin ɗãna, kuma lalle ne, ni, mãfi tsananin sani ne ga Muhammadu fiye da ɗãna.".
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡرِفُونَهُۥ كَمَا يَعۡرِفُونَ أَبۡنَآءَهُمُۘ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَWaɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.