Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu,* sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.— الترجمة الهوساوية
* Kada Musulmi su fita zuwa yãƙi da nũna alfahari da kiɗe-kiɗe da giya da mãtã da maganganun alfãsha, kamar yadda Kuraishãwa suka fita zuwa Badar; ku fita da tawãlu'i da zikirin Allah.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ خَرَجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بَطَرٗا وَرِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ بِمَا يَعۡمَلُونَ مُحِيطٞKada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu, sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.