Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra* ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"— الترجمة الهوساوية
* Ibrahĩm yanã yi musu tambayã ne dõmin yanã ganin kamar sunã yi masa magana ta izgili ne a kan sãmun ɗã a bãyan tsũfansa da na mãtarsa. Sabõda haka suka gaya masa cewa sũ masu gaskiya ne.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationقَالَ أَبَشَّرۡتُمُونِي عَلَىٰٓ أَن مَّسَّنِيَ ٱلۡكِبَرُ فَبِمَ تُبَشِّرُونَYa ce: "Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"