Kuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci* da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.— الترجمة الهوساوية
* Wannan ya nũna, cewa Mũsã an bã shi Annabci a gabãnin ya yi hijira zuwa Madyana. Kuma yanã ƙãra ƙarfafa wannan magana abin da ke cikin ãyã ta 16 inda ya rõƙi Allah gãfara, Ya gãfarta masa, da ãyã ta l7 wadda ta nũna ya san an yi masa gãfarar har yanã neman tsari dõmin kada ya kõma yin haka a gaba. Annabãwa sunã wahami ga abin da bã wahayi ba, sa'an nan Allah Ya gyãra kuskuren, Ya tabbatar da gaskiya.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَٱسۡتَوَىٰٓ ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَKuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.