Ko suna hãsadar mutãne* ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.— الترجمة الهوساوية
* Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah sun tabbata agare shi. An ce masa ɗan gidan Ibrahim domin Yahũdu su san shi ba kasasshe ba ne ga dangantaka, daga gare su. Kuma bai fita ba daga tsãrin cewa Annabãwa mãsu Littãfi a bãyan Ibrãhĩm, daga zuriyarsa za su fito. Kuma sun san wannan a cikin littãfinsu, watau Attaura.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationأَمۡ يَحۡسُدُونَ ٱلنَّاسَ عَلَىٰ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۖ فَقَدۡ ءَاتَيۡنَآ ءَالَ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَءَاتَيۡنَٰهُم مُّلۡكًا عَظِيمٗاKo suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.