Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah* zukãta suke natsuwa.— الترجمة الهوساوية
* Ambaton Allah, shĩ ne bin hukunce-hukuncensa ga kõme. Umar ɗan Khattãb ya ce: "Mafificin ambaton Allah, shi ne wanda aka yi a wurin umurninsa ko haninsa. Wanda yake yin zikirin bãki ba da yanã aiki da hukunce-hukuncen Allah ba a cikin ibãdarsa da mu'amalarsa, to, shi mai izgili kawai ne da sũnan Ubangijinsa, ba mai yin zikiri ba ne.".
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَطۡمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكۡرِ ٱللَّهِۗ أَلَا بِذِكۡرِ ٱللَّهِ تَطۡمَئِنُّ ٱلۡقُلُوبُWaɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa.