Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba!— الترجمة الهوساوية
* Wannan yã nũna cewa Annabi Muhammadu yanã jin tsõron rashin ĩmãnin mutãnensa, kada ya zama shĩ ne ya gajarta daga abin da Allah Ya ɗõra a kansa, na iyar da manzanci. Haka mũmini yake, kullum girman Ubangijinsa yake dũbi, sabõda haka kõme ya yi na ɗã'a, sai ya ga kãsãwar kansa ga tsayuwa da hakkin Ubangijinsa, a kansa, ya ƙãra jin tsõro da tawãli'u.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationلَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ أَلَّا يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَTsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba!