Haƙĩƙa Allah ya faralta muku warware* rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima.— الترجمة الهوساوية
* An rubũta yadda ake warware rantsuwa da kaffãra wadda aka ambata a cikin sũra ta5, ãyã ta 89. Anã kaffãrar rantsuwa da ciyar da miskĩnai gõma daga matsakaicin abinci, mũdu biyu ga kõwane, kõ tufãtar da su tufar da za ta ishe su salla, idan bai sãmu ba, ya yi azumin kwãna uku.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationقَدۡ فَرَضَ ٱللَّهُ لَكُمۡ تَحِلَّةَ أَيۡمَٰنِكُمۡۚ وَٱللَّهُ مَوۡلَىٰكُمۡۖ وَهُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُHaƙĩƙa Allah ya faralta muku warware rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima.