Kuma suka riƙi gumãka,* baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.— الترجمة الهوساوية
* Gunki, shi ne dukan abin bautawa wanda bã Allah ba. Wanda ya riƙi wani sãlihi ko malã'iki ko aljani, yanã bauta masa, to, yã riƙe shi gunki ke nan. Bauta ita ce bin umurni da barin hani. Wanda ya bi umurnin da bã na Allah ba, kõ ya bar abin banin da ba na Allah ba, to, ya bauta wa mai umurnin ko mai hanin, yã riƙe shi gunki baicin Allah.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةٗ لِّيَكُونُواْ لَهُمۡ عِزّٗاKuma suka riƙi gumãka, baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.