Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba(6) a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."— الترجمة الهوساوية
(6) Wannan ƙissa tanã nũna haƙuri ga riƙon iyãli, mulkin ƙasã da mulkin gida duka daidai suke, sai yadda Allah Ya yi umurni a yĩ su. Haka mallakar rai idan mutum bai bi umurnin Allah ba a cikinsu, sai su buwãye shi tsarewa, kamar yadda mulkin ƙasa ke buwãya a riƙe shi tãre da kãfirci da zãlunci.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَٱذۡكُرۡ عَبۡدَنَآ أَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِنُصۡبٖ وَعَذَابٍKuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."