Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku* game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya."— الترجمة الهوساوية
* Ya fara da siyãsa dõmin ya karkatar da hankalin mutãne daga ãyõyin Allah. Cewarsa yãyi nufin ya fitar da ku daga ƙasarku, shĩ ne siyãsa dõmin idan mutãne suka ji maganar fitarwa daga ƙasa, sai su manta da kõwace irin magana tawani alheri.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationقَالُوٓاْ إِنۡ هَٰذَٰنِ لَسَٰحِرَٰنِ يُرِيدَانِ أَن يُخۡرِجَاكُم مِّنۡ أَرۡضِكُم بِسِحۡرِهِمَا وَيَذۡهَبَا بِطَرِيقَتِكُمُ ٱلۡمُثۡلَىٰSuka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya."