Kuma suka sayar* da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.— الترجمة الهوساوية
* Ãyarin, sun tafi da shi, sun sayar da shi a kan kuɗi kaɗan, dõmin sun sani, shĩ bã bãwansu ba ne, tsintõ shi suka yi. Sabõda haka kõme suka sãmu game da shi, rĩba ce a gare su. Kuma gudun kada iyãyensa su gãne shi, su rasa kõme daga gare shi gabã ɗaya.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَشَرَوۡهُ بِثَمَنِۭ بَخۡسٖ دَرَٰهِمَ مَعۡدُودَةٖ وَكَانُواْ فِيهِ مِنَ ٱلزَّـٰهِدِينَKuma suka sayar da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.