Kuma sarki ya ce: "Lalle ne, nã yi mafarki*; nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da waɗansu ƙeƙasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa."— الترجمة الهوساوية
* Mafarkin sarki wanda zai zama sanadin fitar Yũsufu daga kurkuku. Wannan yanã nũna ba akeɓance yin mafarki ga Musulmi kawai, kãfiri ma yanã yin mafarki. Bã a iya fassara mafarki sai da ilmin Alƙur'ãni da Hadisi da kuma sanin al'ãdun mutãne. Mafarki bã ya zama hujja sai idan wani annabi yã fassara shi.
— Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translationوَقَالَ ٱلۡمَلِكُ إِنِّيٓ أَرَىٰ سَبۡعَ بَقَرَٰتٖ سِمَانٖ يَأۡكُلُهُنَّ سَبۡعٌ عِجَافٞ وَسَبۡعَ سُنۢبُلَٰتٍ خُضۡرٖ وَأُخَرَ يَابِسَٰتٖۖ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ أَفۡتُونِي فِي رُءۡيَٰيَ إِن كُنتُمۡ لِلرُّءۡيَا تَعۡبُرُونَKuma sarki ya ce: "Lalle ne, nã yi mafarki; nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da waɗansu ƙeƙasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa."