{
    "id": 1999,
    "name": "الترجمة الهوساوية",
    "short_name": "الترجمة الهوساوية",
    "description": "ترجمة معاني القرآن الكريم للغة الهوسا ترجمها أبو بكر محمود جومي، نشرها مجمع الملك فهد لطباعة المصحف الشريف بالمدينة المنورة، عام الطبعة 1434. ملاحظة: ترجمات بعض الآيات (مشار إليها) تم تصويبها بمعرفة مركز رواد الترجمة، مع إتاحة الاطلاع على الترجمة الأصلية لغرض إبداء الرأي والتقييم والتطوير المستمر. ",
    "language": "هَوُسَ",
    "locale_code": "ha",
    "direction": "rtl",
    "ayahs": [
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 1,
            "page_number": 1,
            "translated_text": "Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 1,
            "page_number": 1,
            "translated_text": "Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 1,
            "page_number": 1,
            "translated_text": "Mai rahama, Mai jin ƙai;"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 1,
            "page_number": 1,
            "translated_text": "Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 1,
            "page_number": 1,
            "translated_text": "Kai muke bautawa, kuma Ka kadai muke neman taimakonKa"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 1,
            "page_number": 1,
            "translated_text": "Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 1,
            "page_number": 1,
            "translated_text": "Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Da cewa Ubangijin halittu ya tara ilmin tauhidi na Ilãhiyya da Rububiyya, Mai rahama Ya tãra dukan rahamar dũniya da rãyarwa da matarwa da ciyarwa da shãyarwa da tufãtarwa. Mai jin ƙai yã tãra ni'imar dũniya mai dõgewa zuwa Lãhira kamar ĩmãni da na lãhira. Mai mallaka ko Mai nũna mulkin rãnar sakamako, yã haɗa dukan wa'azi. Kai muke bautã wa kuma Kai muke neman taimako, ya tara tauhĩdin Ilãhiyya da ibãda amaliyya ko ƙauliyya. Hanya madaidaiciya, tã haɗa dukan sharĩ'a da hukunce-hukunce. Waɗanda aka yi wa ni'ima, yã tãra dukan tãrihin mutanen kirki. Waɗanda aka yi wa fushi, yã tãra dukkan tãrihin mãsu tsaurin kai. Ɓatattu, yã tãra tãrihin dukan mai aiki da jãhilci ko ɓata."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 2,
            "translated_text": "A. L̃. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 2,
            "translated_text": "Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yã sifanta Littãfi; watau Alƙur'ãni da kamãla ya ce \"Wancan\" maimakon \"Wannan\" dõmin mãsu son su yi aiki da shi, su ne mãsu taƙawa. Taƙawa na da sharuɗɗa biyu, su ne ĩmãni da aiki da abin da manzancin Annabi Muhammadu ya ƙunsa. Sa'an nan mutãne a farkon Musulunci ko a inda Musulunci yake sãbo, sun kasu kashi huɗu. Kashi na farko sũ ne mãsu taƙawa waɗanda aka faɗi sifõfinsu a nan."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 2,
            "translated_text": "Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 2,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 2,
            "translated_text": "Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta* daidai ne a kansu, shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba zã su yi ĩmãni ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kashi na biyu daga cikin jama'a sũ ne kãfiran da suka dõge akan kãfircin su, babu wani gisshi kuma Allah Yã san bã zã su musulunta ba. "
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna da wata azãba mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "Kuma akwai daga mutãne wanda* yake cewa: \"Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira.\" Alhãli kuwa su ba muminai ba ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kashi na uku su ne munãfukai da suka bayyana Musulunci da bãki amma zuciyarsu tanã a kan kãfirci. "
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã su sakankancẽwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "A cikin zukãtansu akwai wata cũta. Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "Kuma idan aka ce musu: \"Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa,\" sukan ce: \"Mũ mãsu kyautatawa kawai ne!\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su sansancewa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "Kuma idan aka ce musu: \"ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni,\" sukan ce: \"Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?\" To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni, sukan ce: \"Mun yi ĩmãni. \"Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu,* sukan ce: \"Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kashi na hudu su ne Yahudãwa waɗanda suke sun san gaskiyar Annabcin Muhammadu da Manzancinsa, amma hãsada ta hana su su bi shi, sunã ƙõƙãrin ɓãta abin da ya zo da shi ta hanyar jħfa shibhõhi a ciki, dõmin su kange mutãne daga shigarsa. Sabõda haka aka ce musu shaiɗãnu. Duk wanda ya san gaskiya amma kuma ya yi girman kai daga binta, to, shi ne shaiɗan, daga aljannu kõ daga mutane. "
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "Allah Yana yin izgili* gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Yanã mayar masu da sakamakon izgilinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 3,
            "translated_text": "Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi rĩba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 4,
            "translated_text": "Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa (na abin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 4,
            "translated_text": "Kurãme, bẽbãye, makãfi, sabõda haka bã su kõmõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 4,
            "translated_text": "Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai!"
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 4,
            "translated_text": "Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 4,
            "translated_text": "Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku!"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 4,
            "translated_text": "Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 4,
            "translated_text": "To idan baku iya yi ba to kuwa bazaku taba iya yin ba to kuji tsoron wutar da makamahinta Mutane ne da Duwatsu kuma an tanadeta ne ga Kafirai."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 4,
            "translated_text": "To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku aikataba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfurai."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 5,
            "translated_text": "Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cẽwa lallene, suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su,* sai su ce: \"Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka,\" Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Gõnaki kõ gidãjen Aljanna. "
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 5,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su ce: \"Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan* ya zama misãli?\" na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi, kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Misãli da kamar mãtan Aljanna mãsu tsarki. Ba mãtã ba kõ da sauro ko abin da ya fi, kõ ya kãsa sauro, to, akwai hikima a cikin halittarsa, wadda zã ta jãwo hankalin mai hankali ga ĩmãni da Allah sabõda ita."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 5,
            "translated_text": "Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sãdar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan sũ ne mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 5,
            "translated_text": "Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rãyar da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya rãya ku, sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku?"
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 5,
            "translated_text": "Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma Ya daidaita* zuwa sama, sa'an nan Y a aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ya daidaita, watau Ya yi nufi; \"Sa'an nan\" yana amfãnar da jeranta aiki bã jerantar nufi ba, dõmin sifõfn Allah dukansu, bã fãrarru ba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 6,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã'iku: \"Lalle ne, Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa,\" suka ce: \"Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma mu, muna yi maka tasbihi tare da gõde maka, kuma* muna tsarkakewa gareka\" Ya ce: \"Lalle ne, Ni Na san abin da ba ku sani ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Malã'iku sun yi tambaya ne irin ta mai neman ya rinjãyi mai jãyayya da shi ga neman haliftaka a kan ƙasa. Sun san hãlãyen jinn da bunn waɗanda suka fãra zama a kan ƙasa suka yi ɓarna da zubarda jini. "
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 6,
            "translated_text": "Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan malã'iku, sa'n nan Ya ce: \"Ku gaya mini sũnayen waɗannan, idan kun nasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 6,
            "translated_text": "Suka ce: \"Tsarki ya tabbata a gare Ka! Bãbu sani a gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Masani, Mai hikima.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 6,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ãdam! Ka gaya musu sũnãyensu.\" To, a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu, (Allah) Ya ce: \"Ashe, ban ce muku *ba, lalle Ni, Inã sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (Inã sane da) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ƙissa ta nũna cewa shũgabanci da ilmi ake yinsa, bã da yawan ibãda wadda mutum yake keɓanta da yin ta ba. Dõmin an nũna wa mala'iku fĩfĩkon Ãdam a kansu da ilmi,bã da ibãda ba. Kuma da wannan sifa zai zama Halĩfa, kõ dã Iblis bai fitar da shi ba, daga cikin Aljanna, zai fita ta wata hanya dõmin zartar da hukuncin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 6,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã'iku: \"Ku yi sujada ga Ãdam,\" Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 6,
            "translated_text": "Kuma muka ce: \"Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisa wadãta, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itãciyar, har ku kasance daga azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 6,
            "translated_text": "Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa. Kuma muka ce: \"Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe, kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 6,
            "translated_text": "Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa, sabõda haka ya karɓi tũba a kansa. Lalle ne Shi, Shĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "Muka ce: \"Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiriya ta to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "\"Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan sũ ne abõkan Wuta; sũ a cikinta madawwama ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "Yã Banĩ Isrã'Ĩla*! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyan kiran mutãne gabã ɗaya zuwa ga addinin musulunci, sai kuma ya keɓance Yahũdu da kira zuwa ga addinin, dõmin sun bambanta da sauran kãfirai, sabõda ilminsu ga gaskiyar Musulunci. Yã gabata cewa jama'ar, kashi huɗu ce; mũminai, da kãfiran Lãrabãwan da bã zã su musulunta ba, da munãfukai da Yahũdu. Ya kira Yahũdu da Bani Isrã'ĩla, dõmin Ya tunãtar da su, cewa anã kiransu ne zuwa ga addini irin na ubansu Ya'aƙũbu bawan Allah. "
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na saukar, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji tsõrõNa, Nĩ kaɗai."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi rukũ'i tãre da mãsu yin rukũ'i."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "Shin, kuna umurnin mutãne da alhẽri, kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi? Shin, bãzã ku hankalta ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri, da salla. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa, mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu, kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "ku Banĩ Isrã'Ĩla! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma kuma ni na fifita ku akan sauran Talikai."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 7,
            "translated_text": "Kuma ku ji tsron wani yini, (a cikinsa) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme, kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma bã su zama ana taimakon su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 8,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, su na taya muku muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 8,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 8,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da muka yi wa'adi ga Mũsa, dare arba'in, sa'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa, alhãli kũ, kuna mãsu zãlunci (da bauta masa)."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 8,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan, tsammãninku, kuna gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 8,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa, tsammãninku, kuna shiryuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 8,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: \"Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 8,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da kuka ce: \"Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane,\" sabada haka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 8,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, kuna gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 8,
            "translated_text": "Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; \"Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku.\" kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 9,
            "translated_text": "Kuma a lokacin da Muka ce: \"Ku shiga wannan alƙarya. San nan ku ci daga gareta, idan kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu'i, kuma ku ce; \"kãyar da zunubai\" Mu gãfarta muku laifukanku, kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 9,
            "translated_text": "Sai waɗanda suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu, saboda haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 9,
            "translated_text": "Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa, Muka ce; \"Ka dõki dũtsen da sandarka.\" Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo, haƙĩƙa, kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu. \"Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku, kuma kada ku yi fasadi, a cikin ƙasa, kuna mãsu ɓarna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 9,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da kuka ce: \"Yã Mũsã! Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: \"Kuna nẽman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. \"Kuma Muka dõka musu walãƙanci da talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Aannabãwa, bãda hakki ba. Wancan, sabõda sãɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 10,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba*, da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Waɗanda suka koma, watau Yahũdu, daga maganar Mũsa, \"Mun kõma garesu\" Sura ta 7 aya ta 156, kuma Makarkata, jama'a ce daga Lãrabãwa suka karkata daga addĩnin ubanninsu zuwa ga bauta wa malã'iku. A farkon Musulunci sunã cewa ga wanda ya musulunta, wai ya yi kama da su."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 10,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku: \"Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammãninku ku kãrekanku."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 10,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan, to, bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙĩƙa, dã kun kasance daga mãsu hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 10,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: \"ku kasance birai ƙasƙantattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 10,
            "translated_text": "Muka sanya ta (mas'alar) azãba, dõmin abin da yake gaba gareta, da yake a bãyanta, kuma wa'azi ga mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 10,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: \"Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya.\" Suka ce: \"Shin kana riƙon mu ne da izgili?\" Ya ce: \"Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 10,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?\" Ya ce: \"Lalle ne, Shi, Yana cewa: \"Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 10,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta.\" Ya ce: \"Lalle ne, Shi Yana cewa: \"Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 11,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana abin da yake ita, lalle ne shãnu suna yi mana kamã da jũna, kuma mu, idan Allah Yã so, haƙĩƙa, shiryuwa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 11,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne Shi, Yana cẽwa: \"Ita wata sãniya ce; ba horarra bã tana noman ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lãfiyayya ce: bãbu wani sõfane a cikinta.\" Suka ce: \"Yanzu kã zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba zã su aikata ba."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 11,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa,* kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Asalin ƙissar, wani mutum ne mai arziƙi da yawa daga cikin Banĩ Isra'ĩla amma bã shida magaji sai ɗan ɗan'uwan sa. Saboda yayi gãdo, sai ya kashe shi da dare, ya kuma ɗauke shi ya ajiye shi a bakin ƙofar wani mutum, a cikin su. Da safiyã ta wãye, sai suka tãshi dõmin su yi faɗa a tsakãnin dangin wanda aka kashe da dangin wanda aka same shi a ƙofarsu, sa'an nan suka haɗa ra'ayi ga su kai ƙãra ga Manzon Allah, Mũsã. Suka isa gareshi, suka ba shi lãbãrin. Sai yace musu: \"Lalle ne, Allah Yã ce: \"Ku yanka wata sãniya.\" Da sun yanke kõwace irin sãniya da buƙãtarsu ta biya musu, amma sai suka yi ta yin tambayoyi ana bã su amsa, kuma yanã ƙãra yi musu wuyã, har suka kai ga a sifantã musu sãniyar yãro mai ɗã'a ga uwarsa wadda aka ce: bã zã a sayar musu da ita ba sai da zĩnãriya cike da fãtarta ko dai dai da nauyinta sau gõma. Bayan sun saye ta suka yanka ta sai Mũsã ya ce musu, su dõki wanda aka kashen nan da wani juzu'i nata. Suka dõke shi da ƙashin ta kõ harshenta, sai ya tãshi ya ce: \"Wane ɗan ɗan'uwãna, ya kasheni.\" Sai suka kãma wanda ya yi kisar suka kashe shi. Tartĩbin Alƙur'ãni ya yi ishara da mas'alar tsaurin kan Banĩ Isra'ila da hikimar bin umurnin Allah, da ĩkon tãyar da matattu da gaskiyar Wahayin Annabawa, da asiran da Allah ke sanyãwa a cikin wasu abũbuwa dõmin su zama sanadi ga aukuwar wasu, da yadda yake azurta mãsu yi masa ɗã'a, da sauran su duk a cikin ƙissa guda, ba da ya ambaci tsarin asalinta ba. Tsarki ya tabbata ga Allah. "
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 11,
            "translated_text": "Sai Muka ce: \"Ku dõke shi da wani sãshenta.\" Kamar wancan ne Allah Yake rãyar da matattu, kuma Ya nũna muku ayõyinSa, tsammãninku kuna hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 11,
            "translated_text": "San'nan kuma zukãtanku, suka ƙẽƙashe daga bãyan wancan. Sabõda haka suka zamanto kamar duwatsu. Ko mafi tsananin ƙeƙashewa. kuma lalle ne daga duwãtsu, haƙĩka, akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su, haƙĩƙa, akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi, kuma lalle ne, haƙĩƙa, daga gare su, haƙĩƙa, akwai da yake fãɗõwa dõmin tsõron Allah, kuma Allah bai zama gãfili ba daga barin abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 11,
            "translated_text": "Shin fa kuna tsammãnin zã su yi imãni sabõda ku, alhãli kuwa, haƙĩƙa, wata ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su karkatar da ita daga bãyan sun gãne ta, alhãli sũ, suna sane?"
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 11,
            "translated_text": "Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni sukan ce: \"Mun yi ĩmãni,\" kuma idan sãshensu ya wõfinta zuwa ga sãshe, sukan ce: \"Shin, kuna yi musu magana da abin da Allah Ya buɗa muku ne dõmin su yi muku hujja da shi a wurin Ubangijinku?\" Shin fa, bã ku hankalta?"
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 12,
            "translated_text": "Shin, kuma bã su sanin cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da suke ɓõyẽwa da abin da suke bayyanãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 12,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu akwai ummiyyai, bã su da sanin Littãfi, fãce tãtsuniyoyi, kuma sũ bã kõme suke yi ba fãce suna yin zato."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 12,
            "translated_text": "To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sanã'antãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 12,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Wuta bã zã ta shãfe mu ba, fãce, 'yan kwãnuka ƙidãyayyu.\"Ka ce: \"Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai sãɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah?\""
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 12,
            "translated_text": "Na'am! Wanda ya yi tsiwur-wurin mũgun abu, kuma laifinsa ya kẽwaye shi, to, waɗannan su ne 'yan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 12,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan, 'yan Aljanna ne, sũ a cikinta madawwama ne."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 12,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka karɓi alkawarin Bani-Isrã'ĩla*: \"Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata, da mai zumunta da marãyu da matalauta, kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutãne, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, sa'an nan kuka jũya bãya, fãce kaɗan daga gare ku, alhãli kuwa kuna mãsu bijirẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Tunãtar da Banĩ Isrã'ĩla alkawurra gõma da Allah Yã yi da Mũsã a cikin Attaura a kansu. Na farko bã zã su bauta wa kõwa ba fãce Allah. Na biyu kyautata wa iyãye da dangi da marãyu da matalauta. Na uku, faɗin magana mai kyau zuwa ga mutãne. Na huɗu, tsayar da salla. Nabiyar, bãyar da zakka. Na shida, bã zã a kashe rai bãbu hakki na sharĩ'a ba. Na bakwai, bã zã a fitar da kõwa daga gidansa ba. Na takwas, bã zã a taimaki azzãlumi a kan zãluncinsa ba. Na tara, idan abõkan gãbã sun kãma wani daga cikinsu, su yi fansarsa. Nagõma, ɗã'a ga kõwane Manzon Allah wanda bai sãɓãwa Attaura ba ga aƙida."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 13,
            "translated_text": "Lõkacin da Muka riƙi alkawarinku; bã zã ku zubar da jininku ba, kuma bã zã ku fitar da kanku daga gidãjenku ba; sa'an nan kuka tabbatar alhãli kuwa kuna bãyar da shaida (a kanku)."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 13,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma, gã ku, yã waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidãjensu, kuna taimakon jũna a kansu da zunubi da zãlunci kuma idan kãmammu suka je muku kuna fansarsu alhãli kuwa shĩ fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna ĩmãni da sãshen Littãfin ne, kuma ku kãfirta da sãshe? To, mẽne ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku fãce wulãkanci* a cikin rãyuwar dũniya? Kuma a Rãnar ¡iyãma ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azãba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Aiki da sãshen wasu abũbuwa na addini da barin wasu kãfirci ne mai wajabta wulãƙanci a kan Musulmi."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 13,
            "translated_text": "Waɗannan su ne waɗanda suka sayi rãyuwar dũniya da Lãhira, dõmin haka bã zã a sauƙaƙa azãba ba daga kansu, kuma sũ, bã ataimakonsu."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 13,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Munbai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun biyar daga bãyansa da wasu Manzanni, kuma Muka bai wa Ĩsã ɗan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Rũhi mai tsarki*. Shinfa, kõ da yaushe wani manzo ya je muku tãre da abin da rãyukanku bã su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma wani ɓangare kuna kashẽwa?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Rũhul Kuds; watau ran tsarki kõ rai mai tsarki, shi ne Jibirilu, amincin Allah ya tabbata a gare Shi. Ya zauna tãre da Ĩsã inda duk yake sunã tãre. Ãyõyin da aka bai wa Ĩsã sũ ne rãyar da matattu da warkar da kutãre da makãfi da marasa lãfiya. Wannan ya sanya cewa mãsu da'awar bin sa suka fito da aikin maristan, watau asibiti."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 13,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Zukatanmu suna cikin rufi.\" A'a, Allah Yã la'ane su, dõmin kafircinsu kadan kwarai suke yin ĩmãni!"
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 14,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da wani Littãfi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, alhãli kuwa sun kasance daga gabãnin haka suna fãtar taimako* da shi a kan waɗanda suka kãfirta. To, a lõkacin da abin da suka sani ya je musu, sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka la'anar Allah ta tabbata a kan kãfirai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sunã cewa idan Annabin ƙarshen zãmaninsa ya zo, zã su yãƙi kãfiran Lãrabãwa da shi. Sunã zaton a cikinsu zai ɓullo. Sai ya fito a cikin Lãrabãwan."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 14,
            "translated_text": "Tir, da abin da suka sayi rãyukansu da shi; watau su kãfirta da abin da Allah Ya saukar sabõda zãlunci;* kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so daga bãyinsa. Sai suka kõmo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kãfirai akwai azãba mai wulãƙantarwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bisa ga zãlunci, watau hãsada. Sun yi hãsadar Allah Ya saukar da abin da Yake so na falalarSa a kan wanda Yake so, shi ne Muhammadu, a cikin Lãrabãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 14,
            "translated_text": "Kuma idan aka ce musu: \"Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar.\" Sai su ce: \"Muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu,\" kuma suna kãfircẽwa da abin da ke bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su (na Attaura) Ka ce: \"To, don me kuke kashe annabãwan Allah gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya?\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Waɗannan Annabãwan da kuka kashe ko kuka ƙaryata a cikinku suke kũ ne aka saukar wa da abin da aka bã su, sabõda haka da'awarku ta cewa kunã ĩmãni da abin da aka saukar muku ƙarya ce."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 14,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mũsã ya zo muku da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuka riƙi maraƙi* (daga bãyansa, alhãli kuwa kuna mãsu zãlunci.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Riƙo A nan ma'anarsa bautawa; watau kõmãwa ga maraƙi da ibãda, ku bar Allah, bãyan Musa ya nuna muku ãyõyin Allah, yana ƙãra ƙaryata maganarku, ta cewa kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku kawai. Dã kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku, dã waɗannan abubuwa ba su auku ba daga gare ku."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 14,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka riƙi(5) alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku, (Muka ce:) \"Ku riƙi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi kuma ku ji\" Suka ce: \"Mun ji kuma mun ƙi.\" Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu sabõda kãfircinsu. Ka ce: \"Tir da abin da ĩmãninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance mãsu ĩmãni!\"<br \/>\n____________________<br \/>\n(5) A lõkacin da aka bã su Attaura sai suka ƙi aiki da ita sai da aka ɓamɓari dutse aka ɗaukaka shi sama a kansu, idan ba su yi aiki da ita ba ya fãɗa kansu. Sai suka karɓa, sa'an nan daga bãya kuma suka warware dõmin haka Ya ce: \"Suka ce: Mun jiya kuma mun ƙiya.\" Hãsali dai Yahũdu sun ƙi aiki da Littãfinsu, Attaura."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 15,
            "translated_text": "Ka ce: \"Idan Gidan Lãhira ya kasance sabõda ku ku ne kadai, a wurin Allah babu sauran mutãne, to, ku yi bũrin mutuwa, idan kun kasance mãsu gaskiya.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ya shiga bãyanin ruɗuwar Yahũdu, da alfahari da iyãye, ya sanyã su har suka gina ransu, cewa sũ ne mafifitan mutãne a wurin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 15,
            "translated_text": "Kuma bã zã su yi gũrinta bahar abada sabõda abin da hannayensu, suka gabãtar. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 15,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, zã ka sãme su mafiya kwaɗayin mutãne a kan rãyuwa, kuma sũ ne mafiya kwaɗayin rãyuwa daga waɗanda suka yi shirka. ¦ayansu yana son dã zã a rãyar da shi shekara dubu, kuma bã ya zama mai nĩsantar da shi daga azãba dõmin an rãyar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 15,
            "translated_text": "Ka ce: Wanda ya* kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zũciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishãra ga mũminai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mai ƙin gaskiya kullum yanã neman dalĩlin da zai kãma ya zama wani uzuri a gare shi wajen ƙin aiki da gaskiyar. Yahũdu sunã cewa bã su son Jibirila dõmin shi ne ake aikõwa da azãba, yã halakar da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Luɗu, sunã nufin su ƙi abin da ya kãwo wa Annabi na Alƙur'ãni."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 15,
            "translated_text": "Wanda ya kasance maƙiyi ga Allah da malã'ikunSa da manzanninSa da Jibirĩla da Mĩkã'ĩla to, lalle ne, Allah Maƙiyi ne ga kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 15,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun saukar, zuwa gare ka, ãyõyi bayyanannu, kuma ba wanda yake kãfirta da su fãce fãsikai.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan ãya tana umurnin bin Alkur'ãni da aiki da shi kamar yadda ãyõyin da ke bin ta suke hana barin aiki da shi dõmin a kõma ga son zũciya kamar sihiri da surkulle waɗanda yake bin su kãfirci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 15,
            "translated_text": "Shin, kuma a kõ da yaushe suka ƙulla wani alkawari sai wani ɓangare daga gare su ya, yi jĩfa da shi? Ã'a, mafi yawansu bã su yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 15,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da wani manzo (Muhammadu) daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, sai wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, suka yar da Littãfin (Alƙur'ãnin) Allah a bãyan bãyansu, kamar dai sũ ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 16,
            "translated_text": "Kuma suka bi abin da shaiɗãnu* ke karantawa a kan mulkin Sulaimãnu, kuma Sulaimãnu bai yi kãfirci ba, kuma Shaidãnun, sũ ne suka yi kãfirci, suna karantar da mutãne sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan malã'iku biyu a Bãbila, Harũta da Mãrũta. Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: \"Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta,\" balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Shaiɗan shi ne dukan wanda ya san gaskiya kuma ya ƙi yin aiki da ita, mutum ne kõ aljani. Sabõda haka a nan anã nufin miyagun malamai mãsu ɗauke mutãne daga abin da Allah Ya saukar musu na addini zuwa ga abin da suke so dõmin su cũce su. Hanyar ɗauke mutãne daga addinin gaskiya ita ce a wajen jingina magana ga wani mutum sãlihi wanda aka yarda da shi a bãyan yã mutu kamar Sulaimanu, kõ kuma a jingina ta ga wanda bã zã a iya tambayarsa ba kamar malã'iku. A wannan ãyã an jingina asalin sihiri ga Sulaimãnu aka ce da sihiri ya kai ga mulkinsa, kuma aka ce asalin sihirin nan ilmi ne daga Allah Ya saukar da shi ta kan wasu mala'iku biyu waɗanda suke a garin da ake ce wa Bãbila a ƙasar Iraƙ, anã kiransuHãrũta da Mãrũta waɗanda suke, kãfin su gayawa mai neman ilmin sihirin daga gare su abin da yake so, sai sun yi masa gargaɗi da cewa: \"Kada ka yi kãfirci,\" sa'an nan su gaya masa abin dasuke iya raba miji da mãta da shi na sihiri. To, Allah Yã farkar da mu cewa Sulamiãnu bai yi sihiri ba, dõmin yin sihiri kãfirci ne. Sũ mãlaman mãsu faɗin haka, sũ ne suka yi kãfirci. Mai aiki da sihiri bai cũtar kõwa sai da iznin Allah. neman saninsa cũta ne, bãbu wani amfãni."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 16,
            "translated_text": "Kuma dã lalle ne sũ, sun yi ĩmani, kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa, da sakamako daga wurin Allah shi ne mafi alhẽri, dã sun kasance suna sani."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 16,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ce: 'Rã'inã'* kuma ku ce: 'Jinkirtã manã', kuma ku saurara. Kuma kãfirai suna da azãba mai raɗaɗi.<br \/>\n____________________<br \/>\n* 'Rã'ina,' magana ce mai ma'ana iri biyu ta yabo da ta zãgi. Ta farko ita ce a lõkacin; da Annabi ke karantar da Sahabbansa sai su ce, 'ra'inã' watau dãkata mana har mu gane wannan; ta biyu ita ce, ra'inã!, watau yã ruɓaɓɓe! To, idan Sahabbai sun ce, 'ra'ina,' sunã nufin ma'anar farko, sai Yahũdu da mushirikai su jũya musu magana da ma'ana ta biyu."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 16,
            "translated_text": "Waɗanda suka kãfirta daga Ma'abuta Littãfi, bã su son a saukar da wani alhẽri a kanku daga Ubangijinku, kuma mushirikai mã bã su so. Kuma Allah Yana keɓance da wanda Yake so da rahamarSa. Kuma Allah Ma'abũcin falala mai girma ne."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 17,
            "translated_text": "Abin da Muka shãfe* daga ãya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, zã Mu zo da mafi alhẽri daga gare ta ko kuwa misãlinta. Ashe, ba ka sani ba, cẽwa lalle ne, Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan ãya da abin da yakea bayanta sunã kõrewar shubuhãtu watau rikice-rikicen addini da maƙiyan addini suke sanyãwa a cikinsa, dõmin su sanya Musulmi a cikin shakka da ruɗu."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 17,
            "translated_text": "Shin ba ka sani ba, cẽwa lalle ne Allah, Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa kuma bã ku da, baicin Allah, wani majiɓinci, kuma bã ku da wani mataimaki?"
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 17,
            "translated_text": "Kõ kuna nufin ku tambayi Manzonku, kamar yadda aka tambayi Mũsã a gabãnin haka? Kuma wanda ya musanya kãfirci da ĩmãni, to, lalle ne yã ɓace tsakar hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 17,
            "translated_text": "Mãsu yawa daga Ma'abuta Littãfi sunã gũrin dã sun mayar da ku, daga bãyan ĩmãninku, kãfirai, sabõda hãsada daga wurin rãyukansu, daga bayãn gaskiya tã bayyana a gare su. To, ku yãfe, kuma ku kau da kai, sai Allah Yã zo da umurninSa. Lalle ne Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 17,
            "translated_text": "Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka. Kuma abin da kuka gabãtar dõmin kanku daga alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah. Lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 17,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Bãbu mai shiga Aljanna fãce waɗanda suka zama Yahũdu ko Nasãra.\" Waɗancan tãtsũniyõyinsu ne. Ka ce: \"Ku kãwo dalilinku idan kun kasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 17,
            "translated_text": "Na'am! Wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yana mai kyautatãwa, to, yana da ijãrarsa, a wurin Ubangijinsa, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 18,
            "translated_text": "Kuma Yahũdãwa suka ce: \"Nasãra ba su zamana a kan kõme ba,\"* kuma Nasãra suka ce: \"Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba,\" alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma, a cikin abin da suka kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mai gaskiya idan marasa gaskiya sun tãru sunã faɗa da shi, to, rashin jituwar tsakãninsu zai sanya Allah Ya kange shi daga sharrinsu, sũ duka, kamar husumar da ke tsakãnin Yahũdu da Nasãra da kuma tsakãnin sũ mushirikai, su duka mãsu yãƙi da Musulmi ne kuma mãsu sãɓãwa jũnã ne wajen aƙidõjinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 18,
            "translated_text": "Kuma wãne ne mafi zãlunci* daga wanda ya hana masallãtan Allah, dõmin kada a ambaci sunanSa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su? Waɗannan bã ya kasancẽwa a gare su su shigẽ su fãce suna mãsu tsõro. Suna da, a cikin duniya wani wulãkanci, kuma suna da, a cikin Lãhira, azãba mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Misãlin sãɓãni tsakãninsu; Nasãra suka taimaki Bukhta Nassara ga ɓata masallacin Baitil Maƙdis da jefa mũshe da shãra a ciki, dõmin ƙin Yahũdu. Wannan ƙiyayya tã bayyana har a cikin takardar alƙawari a tsakãnin Nasãra da Halifa Umar bn Khattãb suka ce kada ya bar Yahũdu su shiga Baitil Maƙdis. Sabõda haka idan wasu sun hana ku isa ga masallacinku kõ kuma suka jũyarda ku daga Alƙibla, to, kada ku ji kõme, sun yi irin aikin danginsu. Gabas da yamma na Allah ɗaya ne, duk inda aka jũyar da ku, to, a can yardar Allah take. A lõkacin Musulmi na dũbin Baitil Maƙdis ga salla a bãyan Hijira daga Makka, bã su son haka."
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 18,
            "translated_text": "Kuma Allah ɗai yake da gabas da yamma sabõda haka, inda duk aka jũyar da ku, to, a can fuskar Allah take. Lalle ne, Allah Mawadãci ne, Mai ilmi."
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 18,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Allah Yã riƙi* ɗã.\" Tsarki yã tabbata a gare Shi! A'a, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, dukansu, a gare Shi, mãsu ƙanƙan da kai ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Misãli na biyu Yahũdu na cewa Uzairu ɗãn Allah, kuma Nasãra sunã cewa Ĩsa ɗan Allah, Lãrabãwa na cewa Malã'iku 'ya'yan Allah. Wannan zai hana su jituwa har adãwarsu ga Musulmi ta yi tãsĩri."
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 18,
            "translated_text": "Mai kyautata halittar sammai da ƙasa, kuma idan Ya hukunta wani al'amari, sai kawai Ya ce masa: \"Kasance.\" Sai ya yi ta kasancewa."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 18,
            "translated_text": "Kuma waɗanda bã su da sani suka ce: \"Don me Allah bã Ya yi mana magana, ko wata ãyã ta zo mana?\"* Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka faɗa, kamar maganarsu. zukãtansu sun yi kamã da jũna. Lalle ne, Mun bayyana ãyõyi ga mutãne masu sakankancewa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Misãli ne ga irin rikicin mushirikai ga addini kuma da yadda suka yi kamã da Yahũdu, waɗanda suka ce wa Mũsã: \"Ka nũna mana Allah bayyane.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 18,
            "translated_text": "Lalle ne Mun aike ka da gaskiya, kana mai bãyar da bishãra, kuma mai gargaɗi, kuma bã zã a tambaye ka ba, game da abõkan Wuta."
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 19,
            "translated_text": "Kuma Yahũdu bã zã su yarda da kõme daga gare ka ba, kuma Nasãra bã zã su yarda ba, sai kã bi irin aƙidarsu. Ka ce: \"Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya.\" Kuma lalle ne idan ka bi son zũciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bã ka da, daga Allah, wani majiɓinci, kuma bãbu wani mataimaki."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 19,
            "translated_text": "Waɗanda Muka bai wa Littãfi suna karãtunsa a kan haƙƙin karãtunsa, waɗannan suna ĩmani da shi (Alƙur'ãni). Kuma wanda ya kãfirta da shi, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 19,
            "translated_text": "Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku* tuna ni'imaTa wadda Na ni'imtar da ita a kanku, kuma lalle ne Nĩ, Nã fĩfĩtã ku a kan tãlikai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kira na ƙarshe zuwa ga Yahũdu dõmin shiga Musulunci. An biyar da gargaɗi gare su da tunãtar da su cewa wannan addinin fa, shi ne addinin kãkansu Ibrãhim, dõmin kada su fanɗare daga addinin ubanninsu na ƙwarai. Kuma sunã da lãbãrin ginin Ɗakin Ka'aba da addu'ar da lbrahim ya yi alõkacin, wadda ta ƙunshi zuwan annabi daga cikin zuriyar Isama'ila a Makka, watau Fãrãna."
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 19,
            "translated_text": "Ku ji tsõron wani yini, (a cikinsa) wani rai bã ya tunkuɗe wa wani rai kõme kuma bã a karɓar fansa daga gare shi, kuma wani cẽto bã ya amfanin sa, kuma ba su zama ana taimakon su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 19,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ubangijin Ibrãhim Ya jarrabẽ shi da wasu kalmõmi, sai ya cika su. Ya ce: \"Lalle ne Nĩ, Mai sanya ka shugaba dõmin mutãne ne.\" Ya ce: \"Kuma daga zũriyata.\" Ya ce: \"AlkawarĩNa bã zai sãmu azzãlumai ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 19,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka sanya ¦ãkin ya zama makõma ga mutãne, da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙãmi Ibrãhĩm, kuma Muka yi alƙawari zuwa ga Ibrãhĩm, da Ismã'ila da cẽwa: \"Ku tsarkake ¦ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu lizimta da mãsu rukũ'i, mãsu sujada.\""
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 19,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da lbrãhĩm ya ce: \"Yã Ubangijĩna! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutãnensa, daga 'ya'yan itãcen, wanda ya yi ĩmãni, daga gare su, da Allah da Ranar Lãhira.\" Allah Ya ce: \"Wanda ya kãfirta ma Ina jiyar da shi dãɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tĩlastã shi zuwa ga azãbar Wuta. Kuma makõmar, ta munana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 20,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm yake ɗaukaka harsãshin gini ga ¦ãkin, da Ismã'ĩla (suna cẽwa:) \"Yã Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani."
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 20,
            "translated_text": "\"Ya Ubangijnmu! Ka sanyã mu, mu biyu, waɗanda suka sallama (al'amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al'umma mai sallamãwa zuwa gare Ka, Kuma Ka nũna mana wurãren ibãdar hajjinmu, kuma Ka karɓi tũba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tũba, Mai rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 129,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 20,
            "translated_text": "\"Ya Ubangijinmu! Ka aiko, a cikinsu, wani manzo* daga gare su, yana karanta musu ãyõyinKa, kuma yana karantar da su Littãfin** da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi Mai hikima.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Addu'ar an karɓa, ta aiko Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. ** Littãfin-ya bayyana cewa Alƙur'ãni ne, dõmin bãbu wani sai shi. Hikima kuwa ita ce shari'ar da ke a cikinsa. Zai tsarkake su daga dauɗar shirka idan sun bĩ shi."
        },
        {
            "ayah_number": 130,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 20,
            "translated_text": "Kuma wãne ne yake gudu daga aƙĩdar Ibrãhĩm, fãce wanda ya jãhilta ga ransa? Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe shi, a cikin dũniya, kuma lalle ne shi, a cikin Lãhira, haƙĩƙa, yana daga sãlihai."
        },
        {
            "ayah_number": 131,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 20,
            "translated_text": "lokacin da Ubangijisa ya ce da shi ka mika wuya sai ya ce na mika wuya ga Ubangijin Talikai"
        },
        {
            "ayah_number": 132,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 20,
            "translated_text": "Kuma lbrãhĩm ya yi wasiyya da ita ga ɗiyansa, kuma Ya'aƙũbu (ya yi wasiyya, suka ce:) \"Yã ɗiyãna! Lalle ne, Allah Ya zãɓã muku addini don haka kada ku mutu, lalle, fãce kuna Musulmi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 133,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 20,
            "translated_text": "Ko kun* kasance halarce a lõkacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙũbu, a lõkacin da ya ce wa ɗiyansa: \"Mẽne ne zã ku bauta wa daga bãyãna?\" Suka ce: \"Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrãhĩm da lsmã'ĩla da Is'hãƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi mãsu miƙa wuya ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Lamĩrin Yahũdãwan Madĩna ne na zãmanin Annabi, waɗanda ake kira zuwa ga Musulunci anã tunãtar da su abinda kakansu lsrã'ĩla ya yi wasiyya da shi zuwa ga ɗiyansa, kãfin ya mutu; watau wannan aƙĩda da ake kiran suyanzu zuwa gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 134,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 20,
            "translated_text": "Waccan, wata al'umma ce, ta riga ta shige, tana da abin da ta sanã'anta kuma kuna da abin da kuka sanã'anta, Kuma bã zã a tambaye ku ba daga abin da suka kasance suna aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 135,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 21,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Ku kasance* Yahũdãwa ko Nasãra, kwã shiryu.\"Ka ce: \"A'a aƙidar Ibrãhĩm dai, maikarkata, zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yahũdu suka ce: \"Ku kasance Yahũdawa ku shiryu\" Nasãra suka ce: \"Ku kasance Nasãraku shiryu\". Allah Ya nũna addinin Yahũdu da na Nasãra yã sãɓãwa abin da suke yi, su duka biyu, kuma yã sãɓawa na mushirikai."
        },
        {
            "ayah_number": 136,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 21,
            "translated_text": "Ku* ce: \"Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Musulmi ake yi wa umurni."
        },
        {
            "ayah_number": 137,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 21,
            "translated_text": "To, idan sun yi ĩmãni* da misãlin abin da kuka yi ĩmãni da shi, to, lalle ne sun shiryu, kuma idan sun jũya bãya, to, suna a cikin sãɓãni kawai sabõda haka Allah zai isar maka a gare su, kuma Shi ne Mai ji, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ĩmãni irin na Musulmi shi ne rinin Allah watau baptisma."
        },
        {
            "ayah_number": 138,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 21,
            "translated_text": "Rinin Allah! Kuma wãne ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, mãsu bautãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 139,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 21,
            "translated_text": "Ka ce: Shin kuna jãyayyar hujia ne da mu a cikin al'amarin Allah, alhãli kuwa Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku, kuma muna da ayyukanmu, kuma kuna da ayyukanku, kuma mũ, a gare Shi, mãsu tsarkakẽwane?"
        },
        {
            "ayah_number": 140,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 21,
            "translated_text": "Ko kuna cẽwa: Lalle ne, Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Ya'aƙũbu da Jĩkõki, sun kasance Yahũdãwa kõ kuwa Nasãra? Ka ce: Shin kũ ne kuke mafi sani kõAllah? Kuma wãne ne ya zama mafi zãlunci daga wanda ya bõye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 141,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 21,
            "translated_text": "Waccan, wata al'umma ce, tã riga ta shige, suna da abin da suka sana'anta kuma kuna da abin da kuka sana'anta kuma bã a tambayar ku daga abin da suka kasance suna aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 142,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 22,
            "translated_text": "Wãwãye daga mutãne zã su ce: Mẽne ne ya jũyar da su daga alƙiblarsu wadda suka kasance a kanta? Ka ce: \"Allah ¦ai ne Yake da gabas da yamma, Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 143,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 22,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya* dõmin ku kasance mãsu bãyar da shaida a kan mutãne. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla** wadda ka kasance a kanta ba, fãce dõmin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake jũyãwa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, tã kasance haƙĩƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tõzartar da ĩmãninku.*** Lalle ne, Allah, ga mutãne, haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ãdilai, kõ matsakaita ga kõmai, babu zurewa,babu kãsawa ga addini da rãyuwa da sauran mu'ãmalõli duka. ** A lõkacin da Annabi ya yi hijira zuwa Madĩna, alhãli a cikin mutãnenta akwai Yahũdu Allah Ya umurce shi da ya fuskanci Baitil Maƙdis. Sai Yahũdu suka ji dãɗi. Sai Manzon Allah ya fuskance ta wata gõma sha wani abu kuma Manzon Allah ya kasance yana son Alƙiblar lbrãhĩm kamar yadda ya gabata ga ãyã ta 115. Kuma ya kasance yana addu'a yanã dũbi zuwa ga sama, har Allah Ya saukar da hukuncin jũyãwa zuwa gare ta. *** Ĩmãninku watau sallarku da kuka yi wajen Baitil Makdis, dõmin kun yi ta ne a kan umurnin Allah da ĩmãni da Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 144,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 22,
            "translated_text": "Lalle ne, Muna ganin jujjũyãwar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yardã da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallãci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku jũyar da fuskõkinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littãfi, haƙĩƙa su, sunã sanin lalle ne, shĩ ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 145,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 22,
            "translated_text": "Kuma hakĩka, idan ka je wawaɗanda aka bai wa Littafi da dukan ãyã, bã zã su bi Alƙiblarka ba, kuma kai ba ka zama mai bin Alƙiblarsu ba, kuma sãshensu bã mai bin Alƙiblar* sãshe ba ne. Kuma haƙĩƙa, idan ka bi son zũciyõyinsu daga bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, lalle ne kai, sa'an nan, haƙiƙa, azzãlumi kake.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Alƙiblar Yahũdu ita ce falalen dũtsen da ke Baitil Maƙdis. Kuma ita ce Alƙiblar Nasãra a zãmanin Ĩsã. A bãyansa Alƙiblarsu ta kõma ga mafitar rãnã, da ƙãgensu sabõda St. Paul koõ Bulis el Ƙissi, ya ce musu bãyan an ɗauke Ĩsa cewa: \"Nã haɗu da Ĩsa yã ce mini lalle ne ranã tauraro ne wanda yake inã sonsa. Yanã kai gaisuwata a cikin kõwane yini sabõda haka ka umurci mutãnena, su fuskanta zuwa gare ta.\" Da haka ya karkatar da su daga alƙiblarsu. Kuma inã zaton haka abin yake ga girmamãwar Lahadi maimakon Asabar dõmin Rũmãwa, ranã suke bauta wa a rãnar Lahadi wannan kuwa shi ne ma'anar \"Sunday\" da Tũrancin, watau 'yinin rãna.'."
        },
        {
            "ayah_number": 146,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 23,
            "translated_text": "Waɗanda Muka bã su Littãfi, suna saninsa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Kuma lalle ne wani ɓangare daga gare su, haƙiƙa, suna ɓõyewar gaskiya alhãli kuwa sũ, suna sane."
        },
        {
            "ayah_number": 147,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 23,
            "translated_text": "Gaskiya daga Ubangijinka* take sabõda haka, lalle kada ka kasance daga mãsu shakka.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Jũyãwar alƙibla abu ne na gaskiya daga Allah dõmin rarrashin wanda Allah bai yi nufi da tsĩrarsa ba ya ƙãre. Bãyan rarrashi sai yankewa wannan shi ne matakin farko da Musulmi suka fara tsiraita da shi daga maƙiyansu bayyane. Yanzu kuma Musulmi sun zama dabam."
        },
        {
            "ayah_number": 148,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 23,
            "translated_text": "Kuma kõwane ɓangare yana da alƙibla wadda yake shi mai fuskantar ta ne. Sai ku yi tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri, inda kuka kasance duka Allah zai zo da ku gabã ɗaya. Lalle ne Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 149,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 23,
            "translated_text": "Kuma daga inda ka fita, to, sai ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma lalle tabbas, shi ne gaskiya daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 150,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 23,
            "translated_text": "Kuma daga inda ka fita, to, ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku jũyar da fuskõkinku a wajensa, dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kanku, fãce waɗanda suka yi zãlunci daga gare su. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõrõNa kuma dõmin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammãninku zã ku shiryu."
        },
        {
            "ayah_number": 151,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 23,
            "translated_text": "Kamar* yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ãyõyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littãfi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Jũyar da alƙibla da yankewa daga dukkan kãfirai da hani daga tsõronsu kuma Allah Ya farkar da Musulmi ga ni'imõmin da Ya yi musu game da aiko Annabi daga gare su, zuwa gare su, a cikinsu, dõmin ya tsarkake su, bayyane da ɓõye, daga dukan ƙurar kãfirci. Wannan ya nũna cewa sai an yi rarrashin mutãne wajen kira zuwa ga addini da kõwace hanya mai yiwuwa. Bãyan haka a yanke wa wanda ya ƙi bin gaskiya bayyane kuma kada a ji tsõronsa. Kuma aka umurce su da fuskanta zuwa ga Allah kawai da tunãwa gare Shi da gõdiya, da nisantar kafirci."
        },
        {
            "ayah_number": 152,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 23,
            "translated_text": "Sabõda haka, ku tuna Ni, In tunã ku, kuma ku yi gõdiya gare Ni, kuma kada ku butulce Mini."
        },
        {
            "ayah_number": 153,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 23,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda *suka yi ĩmãni! Ku nẽmi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Magana kuma ta fuskanta zuwa ga mũminai kawai dõmin a shirya zamansu."
        },
        {
            "ayah_number": 154,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "kada ku ce ga waɗanda ake kashẽwa a cikin hanyar Allah: \"Matattu ne.\" Ã'a, rãyayyu ne, kuma amma bã ku sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wanda ya tsiraita da kansa, to, maƙiyinsa bã zai bar shi ba, sabõda haka an fara ƙulla zukãtan mũminai ga tarbon wahalar tsiraita da dõgara ga kai, bãyan Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 155,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da 'ya'yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 156,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: \"Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 157,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu."
        },
        {
            "ayah_number": 158,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "Lalle ne Safã da Marwa* suna daga wurãren ibãdar Allah, to, wanda ya yi hajin ¦ãki kõ kuwa ya yi Umra, to, bãbu laifi a kansa ga ya yi ɗawãfi gare su, su biyu. Kuma wanda ya ƙãra yin wani aikin alhẽri to, lalle ne Allah Mai gõdiya ne, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Al'umma bã ta haɗuwa sai an wanke ta daga al'adun Jãhiliyya, har dai waɗanda suka haɗu da ibãda, sabõda haka aka fãra da Safã da Marwa dõmin a ije cewa ɗawãfi a tsakãninsu aikin Jãhiliyya ne, sũ suna cikin ayyukan ibãda da Allah Ya shar'anta kuma ɗawãfin mutãne da sa'ayi a kansu da tsakãninsu duka daidai suke Baƙuraishe da Balãrabe da Ba'ajame duka daidai suke."
        },
        {
            "ayah_number": 159,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suke ɓõyẽwar abin da Allah Ya saukar da ga hujjõji bayyanannu, da shiriya, daga bãyan Mun bayyana shi ga mutãne, a cikin Littãfi (Alƙur'ãni), waɗannan Allah Yana la'anar su, kuma mãsu la'ana suna la'anar su."
        },
        {
            "ayah_number": 160,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tũba a kansu kuma Nĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 161,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai, waɗannan akwai, a kansu, la'anar Allah da Malã'iku da mutãne gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 162,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "Suna madawwama a cikinta, bã a sauƙaƙa azãba daga barinsu, kuma ba su zama ana jinkirta musu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 163,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 24,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinku Ubangiji* Guda ne. Bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Mai rahama, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ubangiji Shi ne Mai rãyarwa da matarwa, Mai umurni da hani kuma Mai halattãwa da haramtãwa. Ãyar da ke bin wannan tanã nũna dalilan sãmuwarSa da kaɗaitarSa."
        },
        {
            "ayah_number": 164,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 25,
            "translated_text": "Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa, da sãɓãwar dare da yini, da jirãge wadaɗnda suke gudana a cikin tẽku (ɗauke) da abin da yake amfãnin mutãne, da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta, kuma Ya wãtsa, a cikinta, daga dukan dabba, kuma da jũyãwar iskõki da girgije hõrarre a tsakãnin sama da ƙasa; haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 165,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 25,
            "translated_text": "Kuma akwai daga mutãne wanda yake riƙon kinãye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma waɗanda suka yi ĩmãni ne mafiya tsananin so* ga Allah. Kuma dã waɗanda** suka yi zãlunci, suna ganin lõkacin da zã su ga azãba, da cewa lalle ne ƙarfi ga Allah yake duka, da cẽwa lalle neAllah Mai tsananin azãba ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* So mai kai ga karɓar umurni daga abin son, wanda ba Allah ba shi ne shirki da kãfirci. Amma so sabõda ihsãnin abin son, kõ dõmin zamansa sãlihi dõmin a yi kõyi da aikinsa na cikin haddõdin sharĩ'a, bã shirki ba ne, dõmin bai kai yadda mũminai ke son Allah ba. ** Ãyõyi na l65 da l66 da 167 duka ɗinke suke ga ma'anoninsu. Ãyã ta l66 zarafi ce ga ta l65, sa'an nan ta 167 an haɗa rabinta ga ãyã ta 166. Sa'an nan sauran ãyã 167 ta zama ta'aƙĩbi da bayãni gare su duka."
        },
        {
            "ayah_number": 166,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 25,
            "translated_text": "A lõkacin da waɗanda aka bi suka barranta daga waɗanda suka bi, kuma suka ga azãba, kuma sabubba suka yanke da su."
        },
        {
            "ayah_number": 167,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 25,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka bi, suka ce: \"Dã lalle ne muna da wata kõmãwa (dũniya) sai mu barranta dagagare su kamar yadda suka barranta daga gare mu (dã ba su riƙi kinãyen ba).\" Kamar wancan ne Allah ke nũna musu ayyukansu, suna da nadãmõmi a kansu, kuma ba su zama mãsu fita daga wutar ba."
        },
        {
            "ayah_number": 168,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 25,
            "translated_text": "Yã ku mutãne!* Ku ci daga abin da yake a cikin ƙasa, wanda yake halal, mai dãɗi. Kuma kada ku bi zambiyõyin* Shaiɗan. Lalle ne shi, gare ku, maƙiyi ne bayyananne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yã kira mutãne a nan, bai ce mũminai ba, dõmin ba dukan Musulmi yake mũmini ba, sai wanda ya tsĩra daga ãyõyin da ke tafe. A cikinsu akwai abin da zai mai da Musulmi kãfiri kõ mai bidi'a.  ** Hanyõyin Shaiɗan ga halattar da abin da Allah Ya haramta kõ haramtar da abin da Allah Ya halatta dõmin kãga hukuncin da bai zo daga Allah ba, shirka ne tãre da Allah. Yã ce zambiyõyin Shaiɗan, dõmin Shaiɗan bã ya da hanya miƙaƙƙiya."
        },
        {
            "ayah_number": 169,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 25,
            "translated_text": "Yana umurnin ku ne kawai da mugun aiki da alfãsha, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 170,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 26,
            "translated_text": "kuma idan aka ce musu, \"Ku bi abin da Allah ya saukar,\" sai su ce: \"Ã'a, munã bin abin da muka sãmi ubanninmu sun saba a kansa.\" ashe koda iyayen su sun zamanto basa iya fahimtar komai ballanta ma su shiriya ga gaskiya?,"
        },
        {
            "ayah_number": 171,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 26,
            "translated_text": "Kuma misãlin (mai kiran) waɗanda suka kãfirta kamar misãlin wanda ke yin me! me! ga abin da ba ya ji ne, fãce kira da ƙãra, kurãme, bẽbãye, makafi, sabõda haka bã su hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 172,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 26,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ci ku sha daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku. Kuma ku gõde wa Allah, idan kun kasance Shi kuke bauta wa."
        },
        {
            "ayah_number": 173,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 26,
            "translated_text": "Kawai abin da Ya haramta a kanku, mũshe da Jini da nãman alade da abin da aka kurũrũta game da shi ga wanin Allah. To, wanda aka matsã, wanin ɗan tãwãye, kuma banda mai zãlunci, to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 174,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 26,
            "translated_text": "Lalle ne waɗannan da suke ɓõye abin da Allah Ya saukar daga Littãfi, kuma suna sayen kuɗi kaɗan da shi; waɗannan bã su cin kome a cikin cikkunansu fãce wuta, kuma Allah bã zai yi musu magana ba a Rãnar ¡iyãma, kuma bã zai tsarkake su ba, kuma suna da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 175,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 26,
            "translated_text": "Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, kuma azãba da gãfara. To, me ya yi haƙurinsu a kan Wuta!"
        },
        {
            "ayah_number": 176,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 26,
            "translated_text": "Wancan dõmin lalle ne Allah Ya saukar da Littafi da gaskiya, kuma lalle ne waɗanda suka sãɓã a cikin Littãfin, haƙĩƙa, suna a cikin sãɓãni mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 177,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 27,
            "translated_text": "Bai zama addini* ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da ɗan hanya da mãsu rõƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne mãsu taƙawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin cewa Musulunci bã yin salla ɗai ba ne. A'aha! Musulunci tsarewar rãyuwane kamar yadda Allah Ya ce a tsare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 178,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 27,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta, a kanku, yin ƙisãsi* a cikin kasassu. ɗa da ɗa kuma bãwa da bãwa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga ɗan'uwansa to a bi da alhẽri da biya zuwa gare, shi da kyautatãwa. Wancan sauƙaƙewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To, wanda ya yi zãlunci a bãyan wancan, to, yana da azãba mai raɗaɗi.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin hukuncin ƙisãsi: Ana kashe namiji sabõda ya kashe mace, bã a kashe ɗa da Musulmi saboda kashin bãwa da kãfiri sai idan ya zama kisan gila ne kõ ƙwãce. Gila shĩ ne kashe mutum dõmin dũkiyarsa kõ mãtarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 179,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 27,
            "translated_text": "Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 180,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 27,
            "translated_text": "Kuma an wajabta,* a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dũkiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin hukuncin wasiyya: Sunna ta bayyana cewa bãbu wasiyya ga wanda zai yi gãdo, kuma wasiyya bã zã ta shige sulusin dũkiyar tarika ba."
        },
        {
            "ayah_number": 181,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 27,
            "translated_text": "To, wanda ya musanya masa a bãyan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan waɗanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 182,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 28,
            "translated_text": "To, wanda ya ji tsõron karkata ko kuwa wani zunubi daga mai wasiyyar, sai ya yi sulhi a tsakãninsu to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 183,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 28,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta* azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa,<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin hukuncin azumi da darajar watan Ramalãna wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 184,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 28,
            "translated_text": "Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhẽri to, shi ne mafi alhẽri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna sani."
        },
        {
            "ayah_number": 185,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 28,
            "translated_text": "Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde."
        },
        {
            "ayah_number": 186,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 28,
            "translated_text": "Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni.* Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin yin addu'a: Anã son addu'a a cikin ramalãna, yadda neman karɓar addu'a da aikin da'a yake bãyan imani. Aikin ƙwarai shine gõɗiyar addu'a."
        },
        {
            "ayah_number": 187,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 29,
            "translated_text": "An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i* zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, zã su yi taƙawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Abũbuwan da aka hana, a cikin azumi, da ranã, an halatta su da dare har zuwa fitar alfijiri wato sĩlĩli fari na hasken sãfiya da sĩlĩli baƙi na duhun dare. Bã a yin jima'i kõ da dare a hãlin itikãfi, kuma bã a yin itikãfi sai a cikin masallãci."
        },
        {
            "ayah_number": 188,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 29,
            "translated_text": "Kada ku ci dukiyõyinku* a tsakãninku da ƙarya, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Haramun ne cin dũkiyar mutãne da zãlunci. An haɗa wannan ãyã da ta gabãninta, ta azumi, dõmin haɗin hana ci da ya gama su. Sãduwa da mahukunta da dukiya, shi ne rashawa, Allah Yã la'ani mai bãyar da ita da mai karɓarta."
        },
        {
            "ayah_number": 189,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 29,
            "translated_text": "Kuma suna tambayar ka* daga jirajiran wata. Ka ce: \"Su lõkatai ne dõmin mutãne da haji, kuma bã addini ba ne ku je wa gidãje daga bãyansu: kuma amma abin da yake addini shi ne wanda ya yi taƙawa. Kuma ku je wa gidãje daga ƙõfõfinsu, kuma ku bi Allah da taƙawa: tsammãninku, ku ci nasara.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Shiga Musulunci yarda ne da barin al'ãdu da hukunce-hukuncen jãhiliyya, sabõda haka ake sãmun tambayõyi da yawa daga sãbon Musulmi kãfin ya kammala da canza tsõfaffin al'ãdunsa da sãbabbi. Allah Yã yi tarbiyar Sahabban Annabi a cikin rãyuwar Annabi, bãyan saukar wahayi."
        },
        {
            "ayah_number": 190,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 29,
            "translated_text": "Kuma ku yãƙi waɗanda* suke yãƙinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsõkana, lalle ne Allah bã Ya son mãsu tsõkana.<br \/>\n____________________<br \/>\n* An umurci Musulmi da tsare kansu da yãƙi ga duk wanda ya yãƙe su, a kõ'ina yake. Sai dai an hana su tsõkanar wasu, kuma an hana su su yi yãƙi a cikin Hurumin Makka sai fa idan an fãɗa su da yãƙi a cikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 191,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 30,
            "translated_text": "Kuma ku yãƙe su inda kuka sãme su, kuma ku fitar da su daga inda suka fitar da ku. Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga kisa. Kuma kada ku yãƙe su a wurin Masallãci Tsararre (Hurumin Makka) fãce fa idan sun yãƙe ku a cikinsa. To, idan sun yãƙe ku, sai ku yãƙe su. Kamar wancan ne sakamakon kãfirai yake."
        },
        {
            "ayah_number": 192,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 30,
            "translated_text": "Sa'an nan idan sun hanu, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 193,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 30,
            "translated_text": "Kuma ku yãƙe* su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to bãbu tsõkana fãce a kan azzãlumai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* An umurci Musulmi da tsõkana ga kãfiran da suke nũna musu ƙiyayya bayyane, dõmin su hana su yin addininsu da kyau, kamar yadda Allah Ya umurce su, suna fitinar su da wahalõli. Kuma kada ku bar su, su laɓe da wani watan alfarma kõ hurumi, duk yadda hãli ya yi, a yi haka nan, alfarmõmi nã da ƙisãsi."
        },
        {
            "ayah_number": 194,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 30,
            "translated_text": "Watan alfarma da wani watan alfarma alfarmõmi mãsu dũkar jũna ne. Sabõda haka wanda ya yi tsõkana a kanku, sai ku yi tsokana a kansa da misãlin abin da ya yi tsõkana a kanku. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Yana tãre da mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 195,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 30,
            "translated_text": "Kuma ku ciyar* a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bã a iya yãƙi sai da abinci, kuma bã kõwa ke iya zuwa yãƙi ba, kamar yadda yake bã kowa yake da abinci ba. Sabõda haka sai a ciyar da dũkiya, a tãra ta dõmin ɗaukaka kalmar Allah. Rashin bãyar da ita, to, halaka kai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 196,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 30,
            "translated_text": "Kuma ku cika* hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, waɗancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙũba ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hukunce-hukuncen hajji a cikin fitina kõ a cikin rashin lãfiya, idan sun auku a bãyan harama, da hukuncin wanda ya ji dãɗi da umra sa'annan ya yi hajji, kõ kuma ya haɗa su a cikin harama guda, watau ƙirãni, hukuncinsu ɗaya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 197,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 31,
            "translated_text": "Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji* a cikinsu to bãbu jimã'i kuma bãbu fãsiƙanci, kuma bãbu jãyayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alhẽrin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin abũbuwan da aka hana a cikin hajji da waɗanda ake son a yi."
        },
        {
            "ayah_number": 198,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 31,
            "translated_text": "Bãbu laifi a kanku ga ku nẽmi falala daga Ubangijinku. Sa'an nan idan kun malãlo daga Arafãt, sai ku yi ta ambatar Allah a wurin Mash'aril Harãmi kuma ku tuna Shi kamar shiriyar da Ya yi muku kuma lalle ne kun kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga ɓatattu."
        },
        {
            "ayah_number": 199,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 31,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma ku malãlo daga inda mutãne suke malalowa. Kuma ku nemi gafara ga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙKai."
        },
        {
            "ayah_number": 200,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 31,
            "translated_text": "To, idan kun ƙãre ayyukan hajji, sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, kõ kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutãne akwai wanda yake cẽwa: \"Ya Ubangjinmu! Ka bã mu a cikin dũniya! Kuma bã ya da wanirabo a cikin Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 201,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 31,
            "translated_text": "Kuma daga gare su akwai wanda yake cẽwa: \"Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar Wuta!\""
        },
        {
            "ayah_number": 202,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 31,
            "translated_text": "Waɗannan suna da rabo daga abin da suka sanã'anta; kuma Allah Mai gaggãwar sakamako da yawa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 203,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 32,
            "translated_text": "Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙidayayyu.* To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma ku sani cewa lalle ne kũ, zuwa gare Shi ake tãrã ku.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin kabbarõri, bãyan sallõlin farillai gõma sha biyar, anã fãrawa da sallar azahar ta ranar salla a ƙãre da sallar asuba ta rãna ta huɗu daga rãnar salla. Kwãnukan Mina uku ne daga rãnar salla, sai ga wanda ya yi gaggawa ya fita daga Mina bãyan fitar rãnar nan kuma gabãnin fãɗuwar rãna."
        },
        {
            "ayah_number": 204,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 32,
            "translated_text": "Kuma akwai daga mutãne* wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin munafuki da hãlayensa, a cikin jama'a, a san shi, dõmin kada a dõgara a kansa. Haka mutumin kirki shi ma ana son a san shi dõmin a dogara da shi kamar yadda yayi bayãninsa."
        },
        {
            "ayah_number": 205,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 32,
            "translated_text": "Kuma idan ya jũya sai ya yi gaggawa a cikin ƙasa dõmin ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya halaka shũka da 'ya'yan dabbõbi. Kuma Allah bã Ya son ɓarna."
        },
        {
            "ayah_number": 206,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 32,
            "translated_text": "Kuma idan an ce masa: \"Ka ji tsõron Allah,\" sai girman kai da yin zunubi ya ɗauke shi To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma haƙĩƙa, shimfiɗa tã munana."
        },
        {
            "ayah_number": 207,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 32,
            "translated_text": "Kuma akwai daga mutãne* wanda yake sayar da ransa, dõmin nẽman yardar Allah: KumaAllah Mai tausayi ga bãyi ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin mũmini sõsai a cikin Musulmi da halayensa, a sanshi dõmin a dõgara a kansa."
        },
        {
            "ayah_number": 208,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 32,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku shiga cikin Musulunci gabã ɗaya; kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan; lalle ne shĩ a gare ku maƙiyine, bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 209,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 32,
            "translated_text": "To, idan kun karkace daga bayan hujjõji bayyanannu sun zo muku to ku sani cẽwa lalle ne Allah, Mabuwãyi ne, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 210,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 32,
            "translated_text": "Shin suna jira, fãce dai Allah Ya je musu a cikin wasu inuwõyi na girgije, da malã'iku, kuma an hukunta al'amarin? Kuma zuwa ga Allah al'amurra ake mayar da su."
        },
        {
            "ayah_number": 211,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 33,
            "translated_text": "Ka tambayi Banĩ Isrã'ila, da yawa Muka bã su daga ãyõyi bayyanannu. Kuma wanda ya musanya ni'imar Allah daga bãyan tã je masa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 212,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 33,
            "translated_text": "An ƙawata rãyuwar dũniya ga waɗanda suka kãfirta, kuma suna izgili daga waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli waɗanda suka yi taƙawa suna bisa gare su, a Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, bã da lissãfi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 213,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 33,
            "translated_text": "Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin (Littãfin) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa. kuma bãbu wanda ya sãɓã, a cikinsa, fãce waɗanda aka bai wa shi daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu dõmin zãlunci a tsakãninsu. Sai Allah Ya shiryar da waɗanda suka yi ĩmani ga abin da suka sãɓã a cikinsa daga gaskiya da izninSa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so, zuwa ga hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 214,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 33,
            "translated_text": "Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misãlin waɗanda suka shige daga gabãninku bai zo muku ba? Wahalõli da cũta sun shãfe su, kuma aka tsõratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi su ce: \"Yaushe taimakon Allah zai zo?\" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!"
        },
        {
            "ayah_number": 215,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 33,
            "translated_text": "Suna tambayar ka mẽne nezã su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alhẽri sai ga mahaifa* da mafi kusantar dangantaka da marãyu da matalauta da ɗan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ciyar da mahaifa matalauta wãjibi ne haka ɗiya da 'ya'ya ƙanãna waɗanda bãsu da dũkiya har yãro ya balaga a kuma aurar da yãrinya ta tãre a gidan mijinta. Amma  mãtar aure da bãwan mutum ciyar da su wãjibi ne kõ dã sunã da dũkiya. Liyãfa ga bãƙo har kwãna uku gwargwadon bukãta wãjibi ne, sauran ciyarwa mustahabbi ce bãyan an fitar da zakka idan tã wajaba."
        },
        {
            "ayah_number": 216,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 34,
            "translated_text": "An wajabta* yãƙi a kanku, alhãli kuwa shi abin ƙi ne a gare ku, akwai fãtar cẽwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhẽri a gare ku, kumaakwai fãtar cẽwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin hukuncin yãƙi da wuri da lõkacin da aka hana yinsa, da dalilin yinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 217,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 34,
            "translated_text": "Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: \"Yin yãƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah.\" Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushẽwa suna yãƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma waɗannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne."
        },
        {
            "ayah_number": 218,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 34,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihãdi a cikin hanyar Allah waɗannan suna fãtar (sãmun) rahamar Allah kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 219,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 34,
            "translated_text": "Suna tambayar ka game da giya da cãcã.* Ka ce: \"A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu.\" Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: \"Abin da ya rage.\"** Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku; tsammãninku, kuna tunãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin hukuncin cãca da giya da ciyarwa ta alhħri. Cãca da giya harãmun ne dõmin cũtarsu tã fi amfaninsu yawa, ana hukunci da abin da ya rinjãya. Ayõyin wata sura sun bayyana haramcin. ** Abin da ya rage daga larũrarku da ta iyãlanku da wanda ciyar da shi yake wãjibi a kanku, saura shi ne afwu. Daga afwu ake sadakar taɗawwu'i."
        },
        {
            "ayah_number": 220,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 35,
            "translated_text": "A cikin dũniya da Lãhira. Kuma suna tambayar ka game da marãyu.* Ka ce: \"Kyautatãwa gare su ne mafi alhẽri, kuma idan kun haɗa da su (wajen abinci), to, 'yan'uwanku ne; kuma Allah Yana sanin mai ɓãtãwa daga mai kyautatãwa. Kuma dã Allah Yã so, dã Ya tsananta muku. Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin gama abinci da yãra marãyu mãsu dũkiyar kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 221,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 35,
            "translated_text": "Kuma kada ku auri mãtã* mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũminaita ce mafi alhẽri daga ɗiya kãfira, kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin irin maza da mãtan wani addini da bã zã a aure su ba sai sun musulunta, watau mushirikai, banda mãtan Mutãnen Littãfi, sũ kam anã auren 'ya'yansu tãre da kãfircinsu. Bã a auren wanda ya yi ridda daga addinin Musulunci."
        },
        {
            "ayah_number": 222,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 35,
            "translated_text": "Kuma suna tambayar ka game da haila* Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin hukuncin sãduwa da mãtan aure a lõkacin hailarsu; watau jima'i ya haramta a cikin haila kõ bãyan haila gabãnin ta yi wanka. Kõ da ta yi taimama tã yi salla duk da haka dai sai tã yi wanka sannan farjinta yake halatta ga mijinta. Amma anã iya mubãshara da rungumayya ko a cikin haila bãyan tã ɗaura gyauto, tã rũfe cĩbiya zuwa gwiwa."
        },
        {
            "ayah_number": 223,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 35,
            "translated_text": "Mãtanku gõnaki ne a gare ku,* sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. Kuma ku gabãtar (da alheri) sabõda kanku, ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle nekũ mãsu haɗuwa da Shi ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga mũminai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mutum na iya sãduwa da mãtarsa yadda yake so kuma yadda ya sauƙaƙa a gare shi, daga gaba kõ daga bãya, amma ga farji banda ga dubura. Ma'anar ku gabãtar da alheri dõmin rãyukanku, shi ne ku yi basmala ku nemi tsari daga Shaiɗan sabõda 'ya'yanku. Ba a jimã'i da mace alhãli tanã barci, ana son gabãtarda wãsa."
        },
        {
            "ayah_number": 224,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 35,
            "translated_text": "Kuma kada ku sanya(5) Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n(5) Bãyanin rantsuwa da hukunce-hukuncenta. Kada ku sanya rantsuwa da Allah sababin rashin aikata wani alheri, kõ wani aikin ɗã'a, kõ kuma sanya sulhu a tsakanin mutãne, kamar a rõƙe shi ga wani abu daga cikinsu, sai ya yi rantsuwa ya ce: \"Wallãhi bã zan yi ba,\" dõmin tsare kansa daga aikatãwar abin da aka nema gare shi. Yin irin wannan rantsuwa makarũhi ne kõ haram, gwargwadon nauyin abin da aka yi ta sabõda rashin yin sa. Kambu shi ne wurin gwada harbi."
        },
        {
            "ayah_number": 225,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 36,
            "translated_text": "Allah ba Ya kãmã ku da laifi sabõda yãsasshiya a cikin rantsuwõyinku. Kuma amma Yana kama ku sabõda abin da zukãtanku* suka sanã'anta. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yasasshiyar rantsuwa ita ce, a wurin Mãlik, rantsuwa a kan abin da mutum ke ganin sa tabbatacce ne, sai ya bayyana daga bãya akasin tunãninsa. Kamar ya ce Wallãhi bã ni da kuɗi, ga saninsa kuwa haka ne bã ya da su, bai sani ba ashe wani yã mutu, yã yi gãdo. A Shafi'i ita ce: ã'aha Wallahi, I, wallãhi, a cikin magana bã da nufi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 226,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 36,
            "translated_text": "Ga waɗanda suke yin rantsuwa* daga matansu akwai jinkirin watã huɗu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hukuncin ĩlã'i, watau rantsuwa a kan barin tãkin matarsa dõmin ya wahalar da ita, a jira shi wata hudu, idan yã ƙi kõmãwa a sake ta daga gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 227,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 36,
            "translated_text": "Kuma idan sun yi niyyar saki, to, lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 228,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 36,
            "translated_text": "Kuma mãtã waɗanda* aka saki aurensu, suna jinkiri da kansu tsarki uku. Kuma bã ya halatta a gare su, su ɓõye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifunsu, idan sun kasance suna yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma mazan aurensu su ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin gyãrawa. Kuma sũ mãtan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja a kansu (su mãtan). Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin iddar saki da hukunce-hukuncen da suka rãtayu da ita iddar tsarki uku ga mãtar aure ɗiya, baiwa tsarki biyu. Ƙwarƙwara tsarki guda. Istibrã'in zina kõ kuskure kamar idda yake."
        },
        {
            "ayah_number": 229,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 36,
            "translated_text": "Saki sau biyu* yake, sai a riƙa da alh ẽri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sakin aure da hukunce-hukuncen da suka rãtayu da shi. Wanda ya saki matarsa sau ɗaya ko sau biyu, yanã iya mayar da ita kõ dã ba ta so ba matuƙar ba ta kãre idda ba. Wanda ya yi saki uku, bã ya iya kõma aurenta, sai tã yi jimã'i da wani sãbon miji a cikin aure sahĩhi. Sakin bãwa biyu ne."
        },
        {
            "ayah_number": 230,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 36,
            "translated_text": "Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani."
        },
        {
            "ayah_number": 231,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 37,
            "translated_text": "Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 232,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 37,
            "translated_text": "Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 233,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 37,
            "translated_text": "Kuma mãsu haifuwa (sakakku)* suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin shãyar da mãma ga jinjirin da ubansa ya saki uwarsa a lõkacin shãyarwa ko kuma ta haife shi bãyan sakin yã auku."
        },
        {
            "ayah_number": 234,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 38,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke mutuwa* daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin iddar mutuwar maza; mace ɗiya za ta zauna wata huɗu da kwana gõma. Baiwa mãtar aure tanã a kan rabi. Wadda ke shakkar ciki sai ta zauna sai shakka tã ɗebe. Ana takaba watau mai iddar mutuwa ta nisanci ƙawa kõwace iri ce, sai tã ƙãre idda."
        },
        {
            "ayah_number": 235,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 38,
            "translated_text": "Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta* da shi daga nẽman auren mãtãko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cẽwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shia ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin hukuncin neman auren mace a cikin iddarta. An hana sai dai da bananci kamar ya ce mata, \"Ina zan sãmi kamarki?\"."
        },
        {
            "ayah_number": 236,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 38,
            "translated_text": "Kuma bãbu laifi* a kanku idan kun saki mãtã matuƙar ba ku shãfe su ba, kuma ba ku yanka musu sadãki ba. Kuma ku bã su kyautar dãɗaɗãwa, a kan mawadãci gwargwadonsa, kuma a kan maƙuntaci gwargwadonsa; dõmin dãɗaɗrwa, da alhẽri, wãjibi ne a kan mãsu kyautatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin sadãkin wadda aka saki gabãnin shãfa da yanka sadaki, watau mijin ya saki tun bai sãdu da ita ba kuma bai yanka sadãki ba. Bãbu sadãki gare ta sai kyautar dãɗaɗãwa kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 237,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 38,
            "translated_text": "Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa* kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin sadãkin wadda aka yanka wa sadãki amma kuma aka sake ta gabãnin shãfa, to, ita tanã da rabin sadãkinta, sai idan tã zauna a ɗakinsa shekara guda cikakkiya, to, sai a biya ta dukan sadãkinta."
        },
        {
            "ayah_number": 238,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 39,
            "translated_text": "Ku tsare* lõkatai a kan sallõli da salla mafificiya. Kuma ku tsayu kuna mãsu ƙanƙan da kai ga Allah.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin hukuncin tsare lõkutan salla a cikin kõwane hãli: aminci ko tsõro, da bãyar da salla yadda hãli ya bãyar duka; tsaye kõ da tafiya kõ gudãne. Hikimar sanya wannan hukunci a tsakãnin hukunce-hukuncen aure dõmin farkarwa a kan muhimmancin salla, dõmin kada mu'ãmala ta shagaltar da Musulmi daga gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 239,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 39,
            "translated_text": "To, idan kun ji tsõro, to (ku dai yi salla gwargwadon hali) da tafiya ƙasa kõ kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince sai ku ambaci Allah, kamar yadda Ya nũna muku abin da ba ku kasance kuna sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 240,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 39,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke mutuwa* daga gare ku, alhãli suna barin mãtan aure, wasiyya ga mãtan aurensu da dãɗaɗãwa zuwa ga shekara guda bãbu fitarwa, to, idan sun fita to bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Al'ãda idan ba ta sãɓã wa rukunin sharĩ'a ba bã a hana ta sai dai bãbu tilastãwa ga yinta. A zamanin Jãhiliyya mãtã suna iddar mutuwar mazansu shekara guda. Wanda ya yi wasiyyar kada matarsa ta fita daga ɗãkinta har shekara ana karɓar masa sai dai bãbu tĩlas a gare ta da ta zauna, dõmin an shãfe hukuncin iddar shekara ta al'ãdar Jãhiliyya."
        },
        {
            "ayah_number": 241,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 39,
            "translated_text": "Kuma waɗanda aka saki suna da dãɗaɗãwa gwargwadon hãli, wajibi ce a kan mãsu jin tsoron Allah.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin hukuncin dãɗaɗãwa ga mãtan da aka saki bãyan an yi zaman aure da su Tamattu'i gare su wãjibi ne a kan mazansu, gwargwadon hãli."
        },
        {
            "ayah_number": 242,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 39,
            "translated_text": "Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa; tsammãninku, kuna hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 243,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 39,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita* daga gidãjensu, alhãli kuwa sũ dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: \"Ku mutu.\" Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, haƙĩƙa Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wasu mutãne ne daga cikin Bani Isrã'ila annõba tã auku a kansu sai suka fita daga gidãjensu dõmin gudun mutuwa sũ dubũ huɗu kõ takwas kõ wanin wannan adadi, sai Allah Ya ce musu; \"Ku mutu,\"sai suka mutu kwana takwas kõ fiye da haka. Sa'an nan kuma Allah Ya tãyar da su dõmin Ya nũna musu cewa gudun mutuwa, bã ya hana ta, sai abin da Ya so, shi ke aukuwa. Wannan ƙissa tanã amfãnar da ƙarfafa rãyuka dõmin jihãdi, sabõda haka umurni da yãƙi ya bĩ ta; watau ita shimfiɗa ce ga umurnin jihãdi da fita zuwa yãƙi. Kuma sũrar na karantar da tattalin arziki daga nan zuwa ƙarshenta. Watau kafa gari wajibi ne ga tattalin arziki."
        },
        {
            "ayah_number": 244,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 39,
            "translated_text": "Kuma ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mai jĩ ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 245,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 39,
            "translated_text": "Wãne ne wanda(5) zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya riɓanya masa, riɓanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku.<br \/>\n____________________<br \/>\n(5) Bãyãni ga cewa jihãdi bã ya yiwuwa sai mutãne kõwa ya bãyar da taimakonsa na dũkiya kõ na ma'ana. Kuma duk wanda ya bãyar da taimako, to, rance ne ya bai wa Allah, Wanda yake Shi ne Ya bãyar da asalin dũkiyar, da yawa kõ kaɗan, kuma Mai sakamako ga wanda ya yi aiki da umurninSa da babban sakamako, bãyan an kõma zuwa gareShi. Jihãdi wãjibi ne ga tattalin arziki domin tsaro."
        },
        {
            "ayah_number": 246,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 40,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta* daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacinda suka ce ga wani annabi nãsu: \"Naɗã mana sarki, mu yi yãƙi a cikin hanyar Allah.\" Ya ce: \"Ashe, akwai tsammãninku idan an wajabta yãƙi a kanku cẽwa bã zã ku yi yãƙin ba?\" Suka ce: \"Kuma mẽne ne a gare mu, ba zã mu yi yãƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidãjenmu da ɗiyanmu?\" To, a lõkacin da aka wajabta yãƙin a kansu, suka jũya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan ƙissa tana nũna cewa ba a iya yin yãƙi sai da sarki' shũgaba. Kuma ta fadi dalĩlin da ke sanya jama'a su yi yãƙi; watau dõmin tsaron addini da rãyuka da nasaba da mutunci da dũkiya."
        },
        {
            "ayah_number": 247,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 40,
            "translated_text": "Kuma annabinsu* ya ce musu: \"Lalle ne, Allah ya naɗa muku ¦ãlũta** ya zama sarki.\" Suka ce: \"Yãya ne sarauta zã ta kasance a gare shi, a kanmu, alhãli kuwa mũ ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a bã shi wata wadata ba daga dũkiya?\" Ya ce: \"Lalle ne, Allah Yã zãɓe shi a kanku, kuma Ya ƙãra masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bãyar da mulkinSa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sũnan Annabinsu Shamwĩlu daga Sibt Lãwaya. A bãyan Mũsã Yũsha'u bin Nũn sa'an nan Kãlib, sa'an nan Hizƙĩl, sa'an nan Ilyas sa'an nan Alyasa'u, daga nan Bani Isrã'ila suka rasa mai jan su har Amãliƙa ɗiyan Amlĩƙ bn Ãd waɗanda ke zaune a Falastĩn suka rinjãyi Bani Isrã'ila, suka karkashe su suka kõre su daga gidãjensu suka kãma 'ya'yansu, har a lõkacin da wata mace daga Sibt Lãwaya ta haifi Shamwĩlu Annabi. Ya naɗa musu sarki Ɗãlũta.** Ɗãlũta yana a cikin gidan Binyãminu ɗan Ya'aƙũbu talakãwa ne sunã dõgara a kan sanã'a. Zũriyyar Yahũza, sũ ne sarãkuna dõmin haka sunansu ya rinjãya a kan Bani Isra'ila. Zũriyyar Lãwaya sũ ne Annabãwa da mãlamai."
        },
        {
            "ayah_number": 248,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 40,
            "translated_text": "Kuma annabinsu ya ce musu: \"Lalle ne alãmar mulkinSa ita ce akwatin* nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran kaya daga abin da Gidan Mũsã da Gidan Hãrũna suka bari malã'iku suna ɗaukarsa. Lalle ne a cikin wancan akwai alãma a gare ku (ta naɗin ¦ãlũta daga Allah ne) idan kun kasance mãsu ĩmãni.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Akwatin Natsuwa, an saukar da shi tãre da Ãdam a cikinsa akwai sũrõrin annabãwa, da gãdon riƙonsa ya kai ga Mũsã yanã sanya Attaura a ciki sabõda haka aka sãmi karyayyun allunan Attaura a ciki da rawanin Harũna da wani abu daga Mannu da Salwa. A lõkacin da Amãliƙa suka rinjãye su, sai suka karɓe wannan akwãti suka ajiye shi inda bai dãce da shi ba, har a lõkacin da malã'iku suka ɗauke shi zuwa ga Ɗãlũta."
        },
        {
            "ayah_number": 249,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 41,
            "translated_text": "A lõkacin da ¦ãlũta ya fita* da rundunõnin, ya ce: \"Lalle ne Allah Mai jarrabarku ne da wani kõgi. To, wanda ya sha daga gare shi, to, ba shi daga gare ni, kuma wanda bai ɗanɗane shi ba to lalle ne shi, yana daga gare ni, fãce, wanda ya kamfata, kamfata guda da hannunsa.\" Sai suka sha daga gare shi, fãce kaɗan daga gare su. To, a lõkacin da (¦ãlũta) ya ƙẽtare shi, shi da waɗanda suka yi ĩmani tãre da shi, (sai waɗanda suka sha) suka ce: \"Babu ĩko a gare mu yau game da Jãlũta da rundunõninsa.\"Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle sũ mãsu gamuwa ne da Allah, suka ce: \"Da yawa ƙungiya kaɗan ta rinjayi wata ƙungiya mai yawa da iznin Allah, kuma Allah Yana tãre da mãsu haƙuri.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sõja na bukãtar tarbiya, su sãbã da wahala da ƙishirwa da magana mai shiryarwa. Kõgin kuwa shĩ ne kõgin Urdun tsakãnin Urdun da Falastĩn."
        },
        {
            "ayah_number": 250,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 41,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da suka* bayyana ga Jãlũta da rundunoninsa, suka ce: \"Yã Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sãwayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Dãwũdu ɗan Ãisha ya gãji annabcin Shamwĩlu da mulkin Ɗãlũta, shĩ ne ya fãra haɗã su a cikin Bani lsrã'ila bãyansa sai ɗansa Sulaimãn ya gãje shi haka nan. Yawan mutãnen Ɗãlũta da suka yi yãƙi kamar adadin mutãnen Badar ne waɗanda suka yi yãƙi tãre da Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 251,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 41,
            "translated_text": "Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dãwudu ya kashe Jãlũta, kuma Allah Ya bã shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma bã dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne sãshensu da sãshe ba lalle ne dã ƙasa tã ɓãci; kuma amma Allah Ma'abũcin falala ne a kan tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 252,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 41,
            "translated_text": "Waɗancan ayõyin Allah ne: Muna karanta su a kanka da gaskiya: Kuma lalle ne kai, hakĩka, kana daga manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 253,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 42,
            "translated_text": "Waɗancan manzannin* Mun fĩfĩta sãshensu a kan sãshe: Daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya ɗaukaka sãshensu da darajõji; kuma Muka bai wa Ĩsã dan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafã shi da Rũhi mai tsarki. Kuma dã Allah Yã so dã waɗanda suke daga bãyansu, bã zã su yi yãƙi ba, daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu. Kuma amma sun sãɓa wa jũna, sabõda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni, kuma daga cikin su akwai wanda ya kãfirta. Kuma dã Allah Yã so dã bã zã su yãƙi jũna ba, kuma amma Allah Yana aikata abin da Yake nufi.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Yanã tunkuɗe ɓarna a cikin ƙasa da wãsiɗar karantar da mãsu alheri, dõmin su yãƙi mãsu sharri. Ya saukar da ilminSa da wãsiɗar manzanninSa waɗanda Ya tabbatar da cewa Muhammadu, tsira da amincinSa su tabbata a gare shi, yana cikinsu kuma shi ne ya fi ɗaukaka daga cikinsu. Daga wannan ãyã zuwa ƙarshen Sũra duka, ƙãrin bãyani ne da shiryarwa ga hukunce-hukuncen da suka gabãta da kuma yadda zã a zartar da aiki da su, kamar yadda tsãrin magana zai nũna in Allah Ya so."
        },
        {
            "ayah_number": 254,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 42,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda* suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gabãnin wani yini ya zo bãbu ciniki a cikinsa kuma bãbu abũta, kuma bãbu cẽto, kuma kãfirai sũ ne azzãlumai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyan tabbatar da manzancin Annabi Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sa'an nan ya sãbunta fuskanta da kira zuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni da Annabi, kuma ya farkar da su game da zuwan babbar rãna ta Ƙiyãma. Sa'an nan ya faɗi sũnanSa Ta'ãla, Allah Mai sifõfin da ke cikin ãyã ta 255."
        },
        {
            "ayah_number": 255,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 42,
            "translated_text": "Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 256,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 42,
            "translated_text": "Bãbu tĩlastãwa* a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da ¦ãgũta kuma ya yi ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Abũbuwan bautãwa, iri biyu ne; Ubangijin da Yã aiko Muhammadu da wannan gaskiya da shiriya Shĩ ne Allah, da sauran iyãyen giji mãsu dõkõkin kai da na son zũkãta kamar nafsu da Shaiɗan, na aljannu da mutãne, mãsu ƙãga abin da suke so, su ƙira mutane a kansa ana ce musu Ɗãgũtu. Ya yi bayãnin sakamakon mabiyin kõwane irin bautawar. Sa'an nan ya biyar da ƙissõshi uku dõmin bayãnin abin da wannan magana ta ƙunsa; ta farko Namarũzu tãre da Ibrãhĩm, tanã nũna cewa mai mulki anã umurtar sa da bin Allah da taƙawa, idan ya bi son zũciyarsa, to, ya zama Ɗãgũtu. Allah zai halakar da shi. Ta biyu ƙissar Uzairu, tanã nũna cewa bãbu abin da yake da wuya ga Allah. Ta uku ƙissar Ibrãhim da yadda Allah ke rãyar da matattu, tanã nũna cewa bãbu laifi ka roƙi Allah Ya gãnar da kai dukan abin da ya shige maka duhu dõmin ka ƙãrã ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 257,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 43,
            "translated_text": "Allah Shi ne Masõyin waɗanda suka yi ĩmãni; Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma waɗanda suka kãfirta, masõyansu ¦ãgũtu ne; suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai. Waɗannan abokan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne."
        },
        {
            "ayah_number": 258,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 43,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani* ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: \"Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa.\" Ya ce: \"Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa.\" Ibrãhĩm ya ce: \"To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma.\" Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ƙissar farko ta Ibrãhĩm da Namarũzu."
        },
        {
            "ayah_number": 259,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 43,
            "translated_text": "Kõ kuwa* wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: \"Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta.\" Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: \"Nawa ka zauna?\" Ya ce: \"Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini.\" Ya ce: \"A'a kã zauna shẽkara ɗari.\" To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma\", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: \"Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ƙissa ta biyu Uzairu da alƙarya matacciya, da jãkinsa, da abincinsa bãyan shekara ɗari."
        },
        {
            "ayah_number": 260,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 44,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: \"Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu.\" Ya ce: \"Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?\" Ya ce: \"Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu.\" Ya ce: \"To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 261,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 44,
            "translated_text": "Sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, kamar sifar ƙwãyã ce wadda ta tsirar da zangarniya bakwai, a cikin kõwace zangarniya akwai ƙwãya ɗari. Kuma Allah Yana riɓinyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 262,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 44,
            "translated_text": "Waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, sa'an nan kuma bã su biyar wa abin da suka ciyar ɗin da gõri, ko cũta, suna da sakamakonsu a wurin ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 263,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 44,
            "translated_text": "Magana mai kyau da gãfartawa su ne mafi alhẽri daga sadaka wadda wata cũtarwa take biyar ta. Kuma Allah Wadatacce ne, Mai haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 264,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 44,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ɓãta sadakõkinku da gõri da cũtarwa, kamar wanda yake ciyar da dũkiyarsa dõmin nũna wa mutãne, kuma bã ya yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. To, abin da yake misãlinsa, kamar falalen dũtse ne, a kansa akwai turɓãya, sai wãbilin hadari* ya sãme shi, sai ya bar shi ƙanƙara. Bã su iya amfani da kõme daga abin da suka sanã'anta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* 'Wabilin hadari' wãtau ruwan sama kamar da bakin ƙwarya."
        },
        {
            "ayah_number": 265,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 45,
            "translated_text": "Kuma sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyarsu dõmin nẽman yardõjin Allah, kuma da tabbatarwa daga kansu, kamar misãlin lambu ne a jigãwa wadda wãbilin hadari ya sãmu, sai ta bãyar da amfãninta ninki biyu To, idan wãbili bai sãme ta ba, sai yayyafi (ya ishe ta). Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 266,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 45,
            "translated_text": "Shin ɗayanku nã son cẽwa wani lambu ya kasance a gare shi daga dabĩnai da inabõbi' marẽmari suna gudãna daga ƙarƙashinsa, yana da, a cikinsa daga kõwane 'ya'yan itãce, kuma tsũfa ya sãme shi, alhãli kuwa yana da zũriyya masu rauni sai gũguwa wadda take a cikinta akwai wuta, ta sãme shi, har ta ƙõne? Kamar wancan ne Allah Yana bayyanãwar ãyõyi a gare ku, tsammãninku kuna tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 267,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 45,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sanã'anta, kuma daga abin da Muka fitar sabõda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhãli kuwa ba ku zama mãsu karɓarsa ba fãce kun runtse ido a cikinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mawadãci ne, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 268,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 45,
            "translated_text": "Shaiɗan yana yi muku alƙawarin talauci, kuma yana umurnin ku da alfasha*, kuma Allah Yana yi muku alƙawarin gãfara daga gare shi da ƙãri, kuma Allah Mawadãci ne, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Alfãsha ita ce ayyukan zunubi kamar zina da shan giya, alhãli ɓatar da dũkiya a nan, ya fi tsanani, kuma bãbu wani badali don sakamako, sabõda haka ƙin ciyarwa dõmin gudun talauci da umurninku da alfãsha sun sãɓã wa jũna, ga abin da shi Shaiɗan yake gaya muku; watau kada ku ciyar, dõmin gudun talauci, amma ku sha giya, ku yi zina!."
        },
        {
            "ayah_number": 269,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 45,
            "translated_text": "Yana bãyar da hikima (ga fahimtar gaskiyar abubuwa) ga wanda Yake so. Kuma wanda aka bai wa hikima to lalle ne an bã shi alhẽri mai yawa. Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abuta hankula."
        },
        {
            "ayah_number": 270,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 46,
            "translated_text": "Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, kõ kuka cika alwãshi daga wani bãkance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzãlumai bã su da wasu mataimaka."
        },
        {
            "ayah_number": 271,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 46,
            "translated_text": "Idan kun nũna sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa, daga barinku, daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 272,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 46,
            "translated_text": "Shiryar da su bã ya a kanka, kuma amma Allah Shi ne Yake shiryar da wanda Yake so, kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, dõmin kanku ne, kuma bã ku ciyarwa, fãce dõmin nẽman yardar Allah, kuma abin da kuke ciyarwa daga alhẽri zã a cika lãdarsa zuwa gare ku, alhãli kuwa kũ bã a zãluntarku."
        },
        {
            "ayah_number": 273,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 46,
            "translated_text": "(Ciyarwar a yĩ ta) ga matalautan* nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jãhilin hãlinsu yana zaton su wadãtattu sabõda kãmun kai kana sanin su da alãmarsu, ba su rõƙon mutãne da nãcẽwa. Kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, lalle Allah gare shi Masani ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Matalautan nan 'muhãjiruna'ne waɗanda suka bar dũkiyarsu da iyãlansu dõmin hijira. Kuma ba su sãmi wata matãka ba a Madĩna, sai aka yi musu rumfuna, sunã kwãna a ciki, suka tsare kansu dõmin jihãdi da yãƙi da karãtun Alƙur'ãni da ibãda kamar matsayin sõja a yanzu. Sũ wajen ɗari huɗu ne, shugabansu, shi ne Abdur Rahman bn Sakhar Abu Huraira el Dawsy."
        },
        {
            "ayah_number": 274,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 46,
            "translated_text": "Waɗanda suke ciyar da dukiyõyinsu, a dare da yini, ɓõye da bayyane, to suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu. Kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 275,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 47,
            "translated_text": "Wadanda suke cin ribã* ba su tashi, fãce kamar yadda wanda da Shaiɗan yake ɗimautarwa daga shafa yake tashi. Wancan, dõmin lalle ne sun ce: \"Ciniki kamar riba yake.\"Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa'azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'an nan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah. Kuma wanda ya kõma, to, waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ribã ita ce ƙãri ga adadi koga lõkaci. Amma ƙãrin adadi shi ne ƙãri a cikin mu'ãmala da zinãri da azurfa da abũbuwan ci ga rayuwa. Yana haramta ga jinsi guda kawai, kuma ana sharɗantawa ga abinci ya zama abinci kõ abin gyaransa, kuma anã iya ajiye shi, ban da 'ya'yan itãcen marmari da duma da ruwa. Amma ga jinkiri an hana riba muɗlaƙan. kõ dã ga 'ya'yan itãcen marmari. Takardun kuɗi kamar sil'õ'i suke dõmin haka ƙimarsu tana hawa kuma tanã sauka. Har yanzu malamai ba su yanke hukunci a kansu ba sõsai. Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: \"Ka bar abin da yake sanya maka shakka zuwa ga wanda ba ya sanya maka shakka.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 276,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 47,
            "translated_text": "Allah Yana shãfe albarkar riba, kuma Yana ƙãra sadakõki. Kuma Allah bã Ya son dukan mai yawan kãfirci, mai yawan zunubi."
        },
        {
            "ayah_number": 277,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 47,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 278,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 47,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance mãsu ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 279,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 47,
            "translated_text": "To, idan ba ku aikata ba to, ku sani fa da akwai yãƙi daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tũba to kuna da asalin dũkiyõyinku, bã ku zãlunta, kuma bã a zãluntar ku."
        },
        {
            "ayah_number": 280,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 47,
            "translated_text": "Kuma idan ma'abucin wahala ya kasance (mawahalci) to, jinkirtãwa ake yi zuwa ga sauƙin al'amarinsa, kuma dã kun yi sadaka, shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kuna sani."
        },
        {
            "ayah_number": 281,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 47,
            "translated_text": "Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su."
        },
        {
            "ayah_number": 282,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 48,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu'ãmalar bãyar da bãshi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubũta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubũtu a tsakaninku da ãdalci. Kuma kada marubũci ya ki rubũtãwa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubũta. Kuma wanda bãshin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsõron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bãshin yake a kansa yã kasance wãwã ne kõ kuwa rarrauna, kõ kuwa shi bã ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da ãdalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mãtã biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun dõmin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazãkũtar* da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙõsa ga rubũta shi, ƙarami ya kasance kõ babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi ãdalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gẽwayarwa da shi hannu da hannu a tsakãninku to bãbu laifi a kanku, ya zama ba ku rubũta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fãsiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kõme Masani ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Watau mãta biyu su zama kamar namiji guda ga bãyar da shaida. Kuma ana fassara shi da \"ta tunãtar da ɗayar\"."
        },
        {
            "ayah_number": 283,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 49,
            "translated_text": "Kuma idan kun kasance a kan tafiya, kuma ba ku sami marubũci ba, to, a bãyar da jingina karɓaɓɓiya (ga hannu). To, idan sãshenku ya amince wa sãshe, to, wanda aka amincẽ wannan sai ya bãyar da amãnarsa, kuma ya bi Allah, Ubangijinsa, da taƙawa. Kuma kada ku ɓõye shaida, kuma wanda ya ɓõye ta, to, shi mai zunubin zũciyarsa ne. KumaAllah ga abin da kuke aikatãwa Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 284,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 49,
            "translated_text": "Allah ne, da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma idan kun bayyana abin da yake a cikin zukatanku (na shaida), ko kuka ɓõye shi, Allah zai bincike ku da shi, sa'an nan Ya yi gãfara ga wanda Yake so, kuma Ya azabta wanda Yake so. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan ãyã ita ce ƙarshen bayãni a kan bãyar da shaida. A kan shaidar da mutum ya bayyana kõ ya ɓõye a cikin rai, Allah Yake yi masa bincike dõmin hakkin wani da ya rãtaya a kan wannan bayyanawar kõ ɓõyewar. Ita ayar da biyu na bayanta sun ƙunshi ilmin Baƙara dukanta."
        },
        {
            "ayah_number": 285,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 49,
            "translated_text": "Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: \"Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take* \"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Aya ta 285 da ta 286 sun ƙunshi aikin Annabi da waɗanda suka bi shi daga aƙida da magana da aiki da kyautatãwa da mayar da al'amari ga Allah, da addu'ar tsari da nema daga Ubangijinsu. Aya ta 286 ita ce mafi kyaun addu'a. Kuma ta nũna Musulmi sun sãɓa wa Yahũdãwa mãsu cewa 'Mun ji, munƙi!'."
        },
        {
            "ayah_number": 286,
            "surah_number": 2,
            "page_number": 49,
            "translated_text": "Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa, yana da lãdar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatãwa: \"Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Yã Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabãninmu. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da bãbu ĩko gare mu da shi. Kuma Ka yãfe daga gare mu, kuma Ka gãfarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, sabõda haka Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 50,
            "translated_text": "A. L̃. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 50,
            "translated_text": "Allah, bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Rãyayye Mai tsayuwa da kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 50,
            "translated_text": "Yã sassaukar da Littãfi a gare ka da gaskiya, yana mai gaskatãwa ga abin da ke gaba gare shi, kuma Allah Yã saukar da Attaura da Linjĩlã."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 50,
            "translated_text": "A gabãni, suna shiryar da mutãne, kuma Ya saukar da littattafai mãsu rarrabẽwa. Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, suna da azãba mai tsanani. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma'abucin azãbar rãmuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 50,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah bãbu wani abin da ke ɓõyuwa gare Shi a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 50,
            "translated_text": "Shi ne wanda Yake suranta ku a cikin mahaifu yadda Yake so. Bãbu abin bautãwa fãce Shi Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 50,
            "translated_text": "Shi ne wanda ya saukar da Littãfi a gare ka, daga cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littãfin, da wasu mãsu kamã da jũna. To, amma waɗanda yake a cikin zukãtansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kamã da jũna daga gare shi, dõmin nẽman yin fitina da tãwĩlinsa. Kuma bãbu wanda ya san tãwĩlinsafãce Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi sunã cẽwa: \"Mun yi ĩmãni da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake.\" Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abũta hankula."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 50,
            "translated_text": "Yã Ubangijinmu! Kada Ka karkatar da zukãtanmu bãyan har Kã shiryar da mu, kuma Ka bã mu rahama daga gunKa. Lalle ne, Kai, Kai ne Mai yawan kyauta."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 50,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijimu! Lalle ne Kai, Mai tãra mutãne ne dõmin wani yini wanda bãbu shakka a gare shi, Lalle ne Allah bã Ya sãɓãwar lõkacin alkawari.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 51,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu bã su tunkuɗe musu kõme daga Allah, kuma 'ya'yansu bã su tunkuɗẽwa, kuma waɗannan, sũ ne makãmashin wuta."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 51,
            "translated_text": "Kamar ɗabi'ar mutãnen Fir'auna da waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata ãyõyinMu, sai Allah Ya kãmã su sabõda zunubansu, kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 51,
            "translated_text": "Ka ce wa waɗanda suka kãfirta: \"Za a rinjãye ku, kuma a tãraku zuwa Jahannama, kuma shimfiɗar tã mũnana!"
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 51,
            "translated_text": "\"Lalle ne wata ãyã tã kasance a gare ku a cikin ƙungiyõyi biyu da suka haɗu; ƙungiya guda tana yãƙi a cikin hanyar Allah, da wata kãfira, suna ganin su ninki biyu nãsu, a ganin ido. Kuma Allah Yana ƙarfafa wanda Yake so da taimakonSa. Lalle ne a cikin wannan, hakĩƙa, akwai abin kula ga maabũta basĩra."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 51,
            "translated_text": "An ƙawata wa mutãne son sha'awõyi daga mãtã da ɗiya da dũkiyõyi abũbuwan tãrãwa daga zinariya da azurfa, da dawãki kiwãtattu da dabbõbin ci da hatsi. Wannan shi ne dãɗin rãyuwar dũniya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyãwar makõma take."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 51,
            "translated_text": "Ka ce: Shin kuma, in gaya muku mafi alhẽri daga wannan? Akwai gidãjen Aljanna a wurin Ubangiji sabõda waɗanda suka bi Shi da taƙawa, kõguna suna gudãna daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, da mãtan aure tsarkakakku, da yarda daga Allah. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 52,
            "translated_text": "Waɗanda suke cẽwa: \"Ya Ubangijinmu! Lalle ne mu, mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana zunubanmu kuma Ka tsare mu daga azãbar wuta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 52,
            "translated_text": "Mãsu haƙuri, da mãsu gaskiya, da mãsu ƙanƙan da kai, da mãsu ciyarwa da mãsu istingifari a lõkutan asuba."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 52,
            "translated_text": "Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa fãce Shi kuma malãiku da ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa face Shi, Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 52,
            "translated_text": "Lalle ne, addini a wurin Allah, Shi ne Musulunci. Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓã ba, fãce a bãyan ilmi ya je musu, bisa zãlunci a tsakãninsu. Kuma wanda ya kãfirta da ãyõyin Allah, to, lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako ne."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 52,
            "translated_text": "To, idan sun yi musu da kai, sai ka ce: \"Nã sallama fuskata ga Allah, kuma wanda ya bi ni (haka).\" Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai:* \"Shin kun sallama?\" To, idan sun sallama, haƙĩƙa, sun shiryu kuma idan sun jũya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ummiyyi shi ne wanda bai iya karatu da rubutu ba. A cikin Alƙur'ãni anã nufin Lãrabawa da wannan sunan, dõmin bã su da wani littãfin sama da suke da shi a lõkacin nan. Amma ba ana nufin bã su da rubutu ba. Haruffan rubutun Alƙur'ãni tun a zamãnin Ismã'ila ɗan Ibrãhĩma aka san su. Kuma a cikin Lãrabãwa da yawa sun san su, har sunã rubuta ƙasĩdu mãsu kyau, suna rãtayewa a cikin Ka'aba. Jahiliyya ita ce lõkacin da bã a aiki da wani littãfi na sama kamar yadda mafi yawan mutãne suke a yanzu, ƙarnin ishirin shi ma ƙarnin wata jahiliyya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 52,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suke kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Annabãwa bã da wani hakki ba, kuma suna kashe waɗanda ke umurni da yin ãdalci daga mutãne, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 52,
            "translated_text": "Waɗannan ne waɗanda ayyukansu suka ɓãci a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wasu mataimaka."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 53,
            "translated_text": "Shin, ba ka ga waɗanda aka bai wa rabo daga littãfi ba ana kiran su zuwa ga Littãfin Allah dõmin ya yi hukunci a tsakãninsu sa'an nan wata ƙungiya daga cikinsu ta jũya bãya, kuma sunã mãsu bijirẽwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 53,
            "translated_text": "Wannan kuwa, dõmin lalle ne su sun ce: \"Wutã bã zã ta shãfe mu ba, fãce a 'yan kwãnaki ƙidãyayyu.\" Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya rũɗẽ su a cikin addininsu."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 53,
            "translated_text": "To, yãya idan Mun tãra su a yini wanda bãbu shakka a cikinsa, kuma aka cikã wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhãli kuwa, sũ bã zã a zãlunce su ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 53,
            "translated_text": "Ka ce:* \"Yã Allah Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wato ka mayar da ĩkon kõme ga Allah, yana yin sa yandaYake so, bãbu mai iya hanãwa, sa'an nan kuma ka ce wa mũminai, kada su yi wata mu'amala da kãfirai, su bar yan'uwansu mũminai, sai dai a kan lalũra kawai. Wanda ya riƙi kãfirai ya bar mũminai, to, bã shi tãre da Allah a cikin kõme. "
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 53,
            "translated_text": "\"Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 53,
            "translated_text": "Kada mũminai su riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kãriya. Kuma Allah yana tsõratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makõma take."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 53,
            "translated_text": "Ka ce: \"Idan kun ɓõye abin da ke a cikin ƙirãzanku, kõ kuwa kun bayyana shi, Allah Yana sanin sa. Kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah a kan kõwane abu Mai ĩkon yi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 54,
            "translated_text": "A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata daga alhẽri, a halarce, da kuma abin da ya aikata daga sharri, alhãli yana gũrin, dã dai lalle a ce akwai fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin daya aikata na sharrin! Kuma Allah Yanã tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinSa."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 54,
            "translated_text": "Ka ce: \"Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 54,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku yi ɗã'a ga Allah da Manzo.\" To, amma idan sun jũya bãya, to, lalle ne Allah bã Ya son kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 54,
            "translated_text": "Lalle ne Allah Yã zãɓi Ãdama da Nũhu da Gidan Ibrãhĩma da Gidan Imrãna a kan tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 54,
            "translated_text": "Zuriyya ce sãshensu* daga sãshe, kuma Allah Mai ji ne, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sũ duka daidai suke ga mai da al'amari ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 54,
            "translated_text": "A lõkacin da mãtar Imrãna* ta ce: \"Ya Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin da ke cikin cikĩna gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mãtar Imrãna sunanta Hannatu ɗiyar fãƙũza, bã ta haifuwa, sai wata rãna ta ga tsuntsuwa tanã ciyar da tsãkonta, sai ta yi sha'awar sãmun ɗa sabõda haka ta rõki Allah Ya bã ta ɗa. Da mijinta Imrãna ya tãke ta sai ta sãmi ciki, dõmin murna sai ta yi alkwarin 'yanta shi da bakance ga Masallacin Baitil Muƙaddas dõmin ya riƙa yi masa hidima. To, a lõkacin da ta haihu sai ta sãmi ɗiya mace. Ga shari'arsu bã a 'yanta mace ga irin wannan aiki na hidimar masallaci, dõmin haka ta nemi uzuri da cewa ta haife ta mace, mace bã kamar namiji take ba. Har ta yi ruɗu ta jũya, ta ce, namijin bã kamar mace ba, dõmin namiji ne a cikin zũciyarta."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 54,
            "translated_text": "To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: \"Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace!\"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa.\" Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu* kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Maryam, ma'anarta mai ibãda. Abinci da ake kai mata a cikin Masallaci shĩ ne 'ya'yan itãce, irin na ɗãri, a lõkacin bazara, kuma irin na bazara a lõkacin ɗãri. Wannan kuma ya mõtsar da begen zakariyya ga sãmun ɗã, bãyan shi da mãtarsa sun tsũfa ba su haifu ba. Sai ya rõƙi Allah kuma Ya karɓa masa, Ya ba shi Yahaya Annabi."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 54,
            "translated_text": "Sai Ubangijinta Ya karɓe ta karɓa mai kyau. Kuma Ya yabanyartar da ita yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya rẽnonta ga Zakariyya. Ko da yaushe Zakariyya ya shiga masallãci, a gare ta, sai ya sãmi abinci a wurinta. (Sai kuwa) ya ce: \"Yã Maryamu! Daga ina wannan yake gare ki?\" (Sai) ta ce: \"Daga wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda Ya so ba da lissafi ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 55,
            "translated_text": "A can ne Zakariyya ya rõki Ubangijinsa, ya ce: \"Ya Ubangijina! Ka bã ni zuriyya mai kyau daga gunKa. Lalle ne Kai Mai jin addu'a Kake.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 55,
            "translated_text": "Sai malã'iku suka kirãye shi, alhãli kuwa shĩ yanã tsaye yana salla a cikin masallãci. (Suka ce), \"Lalle ne Allah yana bã ka bushãra da Yahaya, alhãli yana mai gaskatãwar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi daga sãlihai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 55,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijina! Yãya yãro zai sãmu a gare ni, alhãli kuwa, lalle tsũfa ya sãme ni, kuma mãtãta bakarãriya ce?\" Allah ya ce, \"Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da Yake so.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 55,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijinã! Ka sanya mini wata alãma!\" (Allah) Ya ce \"Alãmarka ita ce ba zã ka iya yi wa mutãne magana ba har yini uku face da ishãra. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbĩhi da marece da sãfe.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 55,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da malã'iku suka ce: \"Ya Maryamu! Lalle ne, Allah Ya zãɓe ki, kuma Ya tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan mãtan tãlikai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 55,
            "translated_text": "\"Yã Maryamu! Ki yi ƙanƙan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujada, kuma ki yi rukũ'i tãre* da mãsu rukũ'i.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan ya nũna muhimmancin salla tãre da jama'a a masallaci, kõ da ga mãta. Sai dai hãli ya nũna an fi son mace ta yi salla a ɗakinta."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 55,
            "translated_text": "Wannan yana daga lãbarun* gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin husũma**.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan yana daga cikin dalĩlan annabcin Annabi Muhammad, tsira da aminci su tabbata a gare shi, wajen faɗar lãbãrin abin da bai halarta ba. ** Uwar Maryamu tã ɗauke ta, tã kai ta ga Bani kãhin ɗan Hãrũna ɗan'uwan MũSã, a lõkacin nan, sũ ne suke tsaron Baitil Muƙaddas, ta mĩka musu ita, ta ce: \"Ku karɓa. Na 'yantar da ita, kuma mace mai haila bã ta shiga masallaci, kuma bã zan mayar da ita a gidanã ba.\" Sai suka ce: \"Wannan ɗiyar limãminmu ce kuma shugaban Ƙurbãninmu.\" Zakariyya ya ce: \"Ku bã ni ita dõmin innarta tanã tãre da ni.\" Su ka ce: \"Rãyukanmu bã su iya barin ta ga wani.\" Sai suka yi ƙuri'a da alƙalumansu da suke rubũtun Attaura da su. Sai Zakariyya ya rinjãya. An ce sun tafi kõgin Urdun ne suka jefa alƙaluman nãsu, a kan cewa wanda alƙalaminsa bai bi ruwa ba, ya tsaya, shĩ ne ya rinjãya. Sai Zakariyya ya rinjãya, ga shi kuma shĩ ne shugabansu, kuma malaminsu, kuma annabinsu, sai ya sanya ta a cikin bene, a cikin masallacinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 55,
            "translated_text": "A lõkacin da malã'iku suka ce \"Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 56,
            "translated_text": "\"Kuma yana yi wa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma lõkacin da yana dattijo, kuma yana daga sãlihai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 56,
            "translated_text": "Ta ce: \"Yã Ubangijina! Yãya yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba?\" (Allah) Ya ce: \"Kamar wannan ne, Allah yana halittar abin da Yake so. Idan Ya hukunta wani al'amari, sai ya ce masa, \"Ka kasance!, Sai yana kasancẽwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 56,
            "translated_text": "Kuma Ya sanar da shi rubũtu da hikima da Attaura da Linjĩla."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 56,
            "translated_text": "Kuma (Ya sanya shi) manzo zuwa ga Bani Isrãila'ĩla (da sãko, cẽwa), Lalle ne, ni haƙĩƙa nã zõ muku, da wata ãyã daga Ubangijinku. Lalle ne ni ina halitta muku daga lãka, kamar siffar tsuntsu sa'an nan in hũra a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu, da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka haifa makãho da kuturu, kuma ina rãyar da matottu, da izibin Allah. Kuma ina gayã muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyẽwa acikin gidãjenku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyã a gare ku, idan kun kasance mãsu yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 56,
            "translated_text": "\"Kuma inã mai gaskatãwa ga abin da yake a gabãnina daga Taurata. Kuma (nãzo) dõmin in halatta muku sãshen abin da aka haramta muku. Kuma nã tafo muku da wata ãyã daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 56,
            "translated_text": "\"Lalle Allah shi ne Ubangijina, kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan ce hanya madaidaiciya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 56,
            "translated_text": "To, a lõkacin da Ĩsa ya gane kãfirci daga gare su, sai ya ce: \"Su wãne ne mataimakãna zuwa ga Allah?\" Hawãriyãwa suka ce: \"Mu ne mataimakan Allah. Mun yi ĩmani da Allah. Kuma ka shaida cẽwa lalle ne mu, mãsu sallamãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 57,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijinmu! Mun yi imãni da abin da Ka saukar, kuma mun bi ManzonKa, sai Ka rubũta mu tãre da mãsu shaida..*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Masu shaida su ne Musulmi dõmin a cikin Attaura sũnansu mãsu shaida, mabiya Annabi Ummiyyi."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 57,
            "translated_text": "Kuma (Kãfirai) suka yi mãkirci, Allah kuma Ya yi musu (sakamakon) makircin, kuma Allah ne Mafi alhẽrin mãsu sãka wamãkirci."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 57,
            "translated_text": "A lõkacin da Ubangiji Ya ce: \"Ya Ĩsa! Lalle NĨ Mai karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kãfirta, kuma Mai sanya waɗanda suka bĩ ka a bisa waɗanda suka kãfirta har Rãnar ¡iyãma. Sa'an nan kuma zuwa gare Ni makõmarku take, sa'an nan in yi hukunci a tsakãninku, a cikin abin da kuka kasance kuna sãɓã wa jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 57,
            "translated_text": "\"To, amma waɗanda suka kãfirta sai In azabta su da azãba mai tsanani, a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wasu mãsu taimako."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 57,
            "translated_text": "Kuma amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sai (Allah) Ya cikã musu ijãrõrinsu. Kuma Allah bã Ya son azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 57,
            "translated_text": "\"Wannan Muna karanta shi a gare ka (Muhammad) daga ãyõyi, da Tunatarwa mai hikima (Alƙur'ãni).\""
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 57,
            "translated_text": "Lalle ne misãlin Ĩsã a wurin Allah kamar misãlin Ãdama ne, (Allah) Yã halitta shi daga turɓãya, sa'an nan kuma Ya ce masa: \"Ka kasance: \"Sai yana kasancewa."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 57,
            "translated_text": "Gaskiya daga Ubangijinka take sabõda haka kada ka kasance daga mãsu shakka."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 57,
            "translated_text": "To, wanda ya yi musu* da kai a cikinsa, a bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: \"Ku zo mu kirãyi, 'yã'yanmu da 'yã'yanku da mãtanmu da mãtanku da kanmu da kanku sa'an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa'an nan kuma mu sanya la'anar, Allah a kan maƙaryata.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wanda ya yi hujjacewa da Annabi a kan sha'anin Ĩsã; kamar Nasãran Najrãn, sun tafi dõmin su yi jãyayya da Annabi. Ya kira su zuwa ga mubãhala, suka ce: sai sun yi shãwara, suka ce wa jũnansu: \"Kun san gaskiya mutumin nan Annabi ne. Ku bar ra'ayinku na mubãhala, dõmin wani Annabi bai taɓa yin ta tãre da wasu mutãne ba, fãce sun halaka.\" Bãyan haka suka iske Annabi yã fito shi da Hasan da Husaini da Fãtima da Ali, kuma ya ce musu: \"ldan na yi addu'a ku ce, Ãmin.\" Sai suka ƙi mubahãlar, suka yi sulhu akan jizya."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 58,
            "translated_text": "Lalle ne wannan, haƙĩƙa, shi ne lãbãri tabbatacce, kuma bãbu wani abin bautawa fãce Allah, kuma lalle ne, Allah, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 58,
            "translated_text": "To, idan sun jũya bãya, to, lalle Allah Masani ne ga maɓannata."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 58,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã ku Mutãnen Littãfi!* Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa** a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah.\" To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: \"ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mutãnen Littãfi sũ ne Yahũdu da Nasãra kõ da yake an ƙãre magana ne a kan Ĩsã, dõmin kira zuwa ga addini mai aƙĩda sahĩhiya ya haɗa kõwanensu. ** Kalma mai daidaitãwa ita ce kalmar shahãda dõmin tã tabbatar da cewa bãbu abin bautãwa fãce Allah. Bauta ita ce bin wani ga hukunce-hukunce na wajabtãwa kõ haramtãwa kõ halattãwa ko sanya wasu sharuɗɗa waɗanda sharĩ'a ba ta zo da suba. Wannan ãyã ba ta tsaya ga Yahũdu da Nasãra waɗanɗa suka ɗauki Ahbãr da Ruhbãn da mãsu ƙirƙira wasu hukunce-hukunce ba. A'a tã kai har ga Musulmi mãsu raunin hankali da ĩmãni, waɗanda suke zaton waliyyai sunã iya cũtãrwa, kõ sunã iya amfãnin wani da zãtinsu, kuma sunã iya halattãwar abin da Allah Ya haramta, kuma sunã iya haramtãwar abinda Ya halatta, tãre da haka kuma sunã ƙãga bidiõ'ĩ mãsu girma waɗanda Allah bai saukar da wani dalĩli a kansu ba, sunã sanya waɗannan bidi'õ'ĩ su zama ɗarĩƙu ga waɗannan waliyyan. Sunã riya cewa sũ ne mãsu ceton mutum kõ da suke sunã sãɓã wa sharĩ'a, sunã zaton cewa sunã kan wani abu. To, sũ ne maƙaryata, Shaiɗan yã rinjãye su har ya mantar da su daga tuna Allah. Waɗannan sũ ne ƙungiyar Shaiɗan. (Dubi Sãwi)."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 58,
            "translated_text": "Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke hujjacẽwa a cikin sha'anin lbrãhĩma, alhãli kuwa ba a saukar da Attaura da injĩla ba fãce daga bãyansa? Shin bã ku hankalta?"
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 58,
            "translated_text": "Gã ku yã waɗannan! Kun yi hujjacẽwa a cikin abin da yake kunã da wani ilmi game da shi, to, don me kuma kuke yin hujjacẽwa a cikin abin da bã ku da wani ilmi game da shi? Allah yana sani, kuma kũ, ba ku sani ba!"
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 58,
            "translated_text": "Ibrãhĩma bai kasance Bayahũde ba, kuma bai kasance Banasãre ba, amma yã kasance mai karkata zuwa ga gaskiya, mai sallamãwa, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 58,
            "translated_text": "Lalle ne mafi hakkin mutãne da Ibrãhĩma haƙĩƙa, sũ ne waɗanda suka bi shi a (zamaninsa) da wannan Annabi (Muhammadu) da waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma Allah ne Majiɓincin mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 58,
            "translated_text": "Wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi sun yi gũrin su ɓatar da ku, to, ba su ɓatar da kõwa ba fãce kansu, kuma bã su sansancewa!"
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 58,
            "translated_text": "Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuka kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa kũ, kuna shaida (cẽwa sũ gaskiya ne)?"
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 59,
            "translated_text": "Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma kuke ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane?"
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 59,
            "translated_text": "Kuma wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi ta ce: \"Ku yi ĩmãni da abin da aka saukar a kan waɗanda suka yi ĩmãni (da Muhammadu) a farkon yini, kuma ku kãfirta a ƙarshensa; tsammãninsu, zã su kõmõ.\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 59,
            "translated_text": "\"Kada ku yi ĩmãni fãce* da wanda ya bi addininku.\" Ka ce: \"Lalle ne, shiriya ita ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi ĩmãni) cẽwa an bai wa wani irin abin da aka bã ku, kõ kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku.\" Ka ce: \"Lalle ne falala ga hannun Allah take, yana bãyar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadãci ne, Masani.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Maganganu sun shiga jũna dõmin a yi raddin kõwace guntuwar magana da jawãbin da ya dãce da ita tãre da ita. A lũra da kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 59,
            "translated_text": "Yanã keɓance wanda Ya so da rahamarSa, kuma Allah Ma'abucin falala ne, Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 59,
            "translated_text": "Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri,* zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, \"Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai.**\" Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ƙinɗar Shi ne ũƙiyya dubũ gõma sha biyu, kuma ũƙiyya ɗaya tanã daidai da dirhami dubũ biyu da ɗari biyar kõ dĩnari dubu. ** Bãbu laifi idan mun ci dũkiyarsu: Watau Bayahũde yana ganin cin dũkiyar wanda bã Bayahũde ba irinsa halal ne a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 59,
            "translated_text": "Na'am! Wanda duk ya cika alkawarinsa, kuma ya yi taƙawa, to, lalle ne Allah yana son mãsu jin Tsoronsa."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 59,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suke sayen 'yan tamani kaɗan da alkawarin Allah da rantsuwõyinsu, waɗannan bãbu wani rabo a gare su a Lãhira, Kuma Allah bã Ya yin magana da su, kuma bã Ya dũbi zuwa gare su, a Rãnar ¡iyãma, kuma bã Ya tsarkake su, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 60,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, daga gare su akwai wata ƙungiya suna karkatar da harsunansu da Littãfi dõmin ku yi zaton sa daga Littãfin, alhãli kuwa bã shi daga Littãfin. Kuma suna cẽwa: \"Shi daga wurinAllah yake.\" Alhãli kuwa shi, bã daga wurin Allah yake ba. Sunã faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa sunã sane."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 60,
            "translated_text": "Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya bã shi Littãfi da hukunci da Annabci, sa'an nan kuma ya ce wa mutãne: \"Ku kasance bãyi gare ni, baicin Allah.\" Amma (zai ce): \"Ku kasance mãsu aikin ibãda da abin da kuka kasance kuna karantar da Littãfin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantãwa.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan ya nũna karatun Alƙur'ãni kawai bã da sanin ma'anarsa ba, dõmin a yi aiki da shi, ba ya isar mutum. Amman wanda ya kõyi ibãda sõsai, sa'an nan ya karanta Alƙur'ãni, to, zã a bã shi lãda kõ dã ba ya fahimtar ma'anarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 60,
            "translated_text": "Kuma ba ya umurnin ku da ku riƙi malã'iku da annabãwa lyãyengiji. Shin, zai umurce ku da kãfirci ne a bãyan kun riga kun zama mãsu sallamãwa (Musulmi)?"
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 60,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin Annabãwa: \"Lalle ne ban bã ku wani abu ba daga Littãfi da hikima, sa'an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku; lalle ne zã ku gaskata Shi, kuma lalle ne zã ku taimake shi.\" Ya ce: \"Shin, kun tabbatar kuma kun riƙi alkawarĩNa a kan wannan a gare ku?\" suka ce: \"Mun tabbatar.\" Ya ce: \"To, ku yi shaida, kuma Nĩ a tãre da ku Inã daga mãsu shaida.\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 60,
            "translated_text": "To, waɗanda kuma suka jũya bãya a bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 60,
            "translated_text": "Shin wanin Addinin Allah suke nẽma, alhãli kuwa a gare Shi ne waɗanda ke cikin sama da ƙasa suka sallama wa, a kan sõ da ƙĩ, kuma zuwa gare Shi ake mayar da su?"
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 61,
            "translated_text": "Ka ce: \"Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da Isma'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 61,
            "translated_text": "Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 61,
            "translated_text": "Yãya Allah zai shiryar da mutãne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, kuma sun yi shaidar cẽwa, lalle Manzo gaskiya ne, kuma hujjõji bayyanannu sun je musu? Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 61,
            "translated_text": "Waɗannan, sakamakonsu shi ne, lalle a kansu akwai la'anar Allah da mãla'iku da mutãne gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 61,
            "translated_text": "Sunã mãsu dawwama a cikinta, bã a sauƙaƙa azãbar gare su, kuma ba su zama ana yi musu jinkiri ba."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 61,
            "translated_text": "Fãce waɗanda suka tũba daga bãyan wannan, kuma suka yi gyãra, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 61,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci bã zã a karɓi tũbarsu ba. Kuma waɗannan sũ ne ɓatattu."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 61,
            "translated_text": "Lalle ne wanɗanda suka kãfirta, kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai to bã zã a karɓi cike da ƙasa na zinãri daga ɗayansu ba, kõ dã ya yi fansa da shi, waɗannan sunã da azãba mai raɗaɗi, kuma bã su da wasu mataimaka."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 62,
            "translated_text": "Bã zã ku sãmi kyautatãwa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, kõ mẽne ne, to, lalle ne Allah, gare shi, Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 62,
            "translated_text": "Dukan abinci yã kasance halal ne ga Bani lsrã'ĩla, fãce abinda Isrã'ĩla ya haramta wa kansadaga gabãnin saukar da Attaura. Ka ce: \"To, ku zo da Attaura sa'an nan ku karantã ta, idan kun kasance mãsu gaskiya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 62,
            "translated_text": "\"To, wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah daga bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 62,
            "translated_text": "Ka ce: \"Allah Ya yi gaskiya, sabõda haka ku bi aƙĩdar Ibrãhĩma mai karkata zuwa ga gaskiya; kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 62,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, ¦aki na farko* da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka** mai albarka kuma shiriya ga tãlikai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ɗãkunan Allah a cikin ƙasa dõmin mutãne su yi ibãda zuwa gare su biyu ne; Ka'aba a Makka da Baitil Muƙaddas. An gina Ka'aba a gabaninsa da shekara arba'in. Dãkin Bakka kuwa Ibrãhĩma ne ya gina shi alhãli Yahũdu da Nasãra sunã cewa kan addininsa suke. Dã sunã faɗar gaskiya dã sun kõma a gare shi gabã ɗaya. ** Ana ce wa Makka Bakka."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 62,
            "translated_text": "A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 62,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ya kũ Mutãnen Littãfi! Don me kuke kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa Allah Mai shaida ne a kan abin da kuke aikatãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 62,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 62,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗã'aga wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, zã su mayar da ku kãfirai a bãyan ĩmãninku!"
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 63,
            "translated_text": "Kuma yãyã kuke kãfircẽwa alhãli kuwa anã karanta ãyõyin Allah a gare ku, kuma a cikinku akwai manzonSa? Kuma wanda ya nẽmi tsari da Allah, to, an shiryar da shi zuwa ga hanya miƙaƙƙiya."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 63,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, a kan hakkin binsa da taƙawa, kuma kada ku mutu fãce kuna mãsu sallamawa (Musulmi)."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 63,
            "translated_text": "Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da kuka kasance maƙiya sai Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtanku sabõda haka kuka wãyi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gãɓar rãmi na wutã sai Ya tsãmar da ku daga gare ta, Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayõyinSa, tsammãninku, zã ku shiryu."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 63,
            "translated_text": "Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alhẽri, kuma suna umurnida alhẽri, kuma suna hani dagaabin da ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu cin nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 63,
            "translated_text": "Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka rarrabu kuma suka sãɓã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu kuma waɗannan sunã da azãba mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 63,
            "translated_text": "A rãnar da wasu fuskõki suke yin fari kuma wasu fuskõki suke yin baƙi (zã a ce wa waɗanda fuskokinsu suke yin baƙin): \"Shin kun kãfirta a bayan ĩmãninku? Don haka sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 63,
            "translated_text": "Kuma amma waɗanda fuskõkinsu suka yi fari, to sũ suna cikin rahamar Allah kuma, su a cikinta, madawwama, ne."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 63,
            "translated_text": "Waɗannan ãyõyin Allah ne, muna karanta su a gare ka da gaskiya, kuma Allah bã Ya nufin wani zãlunci ga tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 64,
            "translated_text": "Kuma abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ake mayar da al'amurra."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 64,
            "translated_text": "Kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri kuma kunã hani daga abin da ake ƙi, kuma kunã ĩmãni da Allah. Kuma dã Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, lalle ne, dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su. Daga cikinsu akwai mũminai, kuma mafi yawansufãsiƙai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 64,
            "translated_text": "Bã zã su cũce ku ba, fãce dai tsangwama. Kuma idan sun yãƙe ku zã su jũya muku bãya, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 64,
            "translated_text": "An dõka ƙasƙanci a kansu a inda duk aka sãme su fãce da wani alkawari daga Allah, da alkawari daga mutãne. Kuma sun kõma da fushi daga Allah, kuma aka dõka talauci a kansu. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe annabãwa, bã da wani haƙƙi ba. Wannan kuwa dõmin sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta'adi."
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 64,
            "translated_text": "Ba su zama daidai ba; daga Mutãnen Littafi akwai wata al'umma wadda take tsaye, suna karãtun ayõyin Allah a cikin sã'õ'in dare, alhãli kuwa sunã yin sujada."
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 64,
            "translated_text": "Suna ĩmãni da Allah da Yinin Lãhira, kuma suna umurui da abin da aka sani kuma suna hani daga abin da ba a sani ba, kuma sunã gaugãwa a cikin alhẽrai. Kuma waɗannan suna cikin sãlihai."
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 64,
            "translated_text": "Kuma abin da suka aikata daga alhẽri, to, bã zã a yi musu musunsa ba. Kuma Allah Masani ne ga mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 65,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ ɗiyansu bã zã su wadatar musu da kõme ba daga Allah kuma waɗannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne."
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 65,
            "translated_text": "Misãlin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rãyuwar dũniya, kamar misãlin iska ce (wadda) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sãmi shukar wasu mutãne waɗanda suka zãlunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zãlunce su ba, amma kansu suka kasance sunã zãlunta."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 65,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi abõkan asĩri daga waninku, ba su taƙaita muku ɓarna. Kuma sun yi gũrin abin da zã ku cũtu da shi. Haƙĩka, ƙiyayya tã bayyana daga bãkunansu, kuma abin da zukãtansu ke ɓõyẽwane mafi girma. Kuma lalle ne, Mun bayyana muku ãyõyi, idan kun kasance kunã hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 65,
            "translated_text": "Gã ku yã waɗannan! Kunã son su bã su son ku, kuma kuna ĩmãni da Littãfi dukansa. Kuma idan sun haɗu da ku sukan ce \"Mun yi ĩmani\". Kuma idan sun kaɗaita sai su ciji yãtsu a kanku don takaici. Ka ce \"Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.\""
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 65,
            "translated_text": "Idan wani alhẽri ya shãfe ku sai ya baƙanta musu rai, kuma idan wata cũtar ta shãfe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu bã ya cũtar ku da kõme. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 65,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin* da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãƙi, kuma Allah Mai ji ne, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Misãli ne ga cewa idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, to, ƙullinsu bã ya cũtar da ku da kõme, dõmin abin da ya auku a Yãƙin Uhdu ya isa misãli ga cewa, sai kun karkace daga hanya sa'an nan wani abu zai sãme ku. Asalin maganar shĩ ne, Annabi yã fita Uhdu da mutum ɗari tara da hamsin kuma kãfirai sunã dubũ uku. Annabi ya sauka a Uhdu rãnar Asabat, bakwai ga Shawwal, shekara ta uku ga Hijira, ya sanya bayansa wajen dũtsen Uhdu, ya gyãra safũfuwan mayãƙa, kuma ya zaunar da wata runduna ta maharba a gefen dũtsen da shugabancin Abdullahi ɗan Jubair. Sa'an nan ya ce musu: \"Ku kãre mu da harbi, kada su zo mana daga bãya, kada ku ɗaga daga nan, mun rinjãya kõ an rinjãye mu.\" Sai suka sãɓãwa umurnin, don haka masĩfar Uhdu ta auku."
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "A lõkacin da ƙungiyõyi* biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majiɓincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Banũ salimah da Banũ Hãrisa sun tãshi kõmãwa gida su bar yãƙi, a lõkacin da Abdullahi bn Ubayyi bn Salũl ya kõma da jama'arsa, Allah Ya tsare musu ĩmãninsu, ba su kõma ba. Watau yana cewa idan wani abu na masĩfa ya sãme ku, to, kun sãɓãwa Allah ne kamar yadda ya auku a Uhdu, suka sanya Annabi ya fito daga Madĩna kuma maharba suka bar wurin da aka ayyana musu. Amma kuma ai Allah Ya Taimake ku, a Badar a lõkacin da ƙarfinku bai kai haka ba, sabõda rashin saɓawarku ga umurninSa."
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a Badar, alhãli kuwa kunã mafiya rauni, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, kuna gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "A lõkacin da kake cẽwa ga mũminai, \"Shin bai ishe ku ba, Ubangijinku Ya taimake ku da dubu uku daga malã'iku saukakku?\""
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "\"Na'am! Idan kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙãre ku da dubu biyar daga malãiku mãsu alãma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "Kuma Allah bai sanya shi* ba, fãce dõmin bushãra a gare ku, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Taimako da mala'iku."
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "Dõmin Ya katse wani gẽfe daga waɗanda suka kãfirta ko kuma Ya ƙasƙantã su, har su jũya, suna mãsu ruɓushi."
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "Bãbu kõme a gare ka game da al'amarin (shiryar da su banda iyar da manzanci). Ko Allah Ya karɓi tũbarsu, kõ kuwa Ya yimusu azãba, to lalle ne sũ, mãsu zãlunci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 129,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gãfarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 130,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci riba ninkininki, riɓanye, kuma ku bi Allah da taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 131,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "Kuma ku ji tsõron wutã wadda aka yi tattali dõmin kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 132,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 66,
            "translated_text": "Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, tsammaninku a yi muku rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 133,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 67,
            "translated_text": "Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nẽman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 134,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 67,
            "translated_text": "Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke mãsu haɗiyẽwar fushi, kuma mãsu yãfe wa mutãne laifi. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 135,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 67,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane."
        },
        {
            "ayah_number": 136,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 67,
            "translated_text": "Waɗannan sakamakonsu gãfara ce daga Ubangijinsu, daga Gidajen Aljanna (waɗanda) ƙõramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. Kuma mãdalla da ijãrar mãsu aiki."
        },
        {
            "ayah_number": 137,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 67,
            "translated_text": "Lalle ne misãlai sun shũɗe a gabãninku, sai ku yi tafiya a cikin ƙasa sa'an nan ku dũba, yãyã ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance."
        },
        {
            "ayah_number": 138,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 67,
            "translated_text": "Wannan bayãni ne ga mutãne, kuma shiryuwa ce da wa'azi ga mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 139,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 67,
            "translated_text": "Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baƙin ciki, alhãli kuwa kũ ne mafiya ɗaukaka, idan kun kasance mãsu ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 140,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 67,
            "translated_text": "Idan wani mĩki ya shãfe ku, to, lalle ne, wani mĩki kamarsa ya shãfi mutãnen, kuma waɗancan kwãnaki Muna sarrafa su a tsakãnin mutãne dõmin Allah Ya san waɗanda suka yi ĩmãni kuma Ya sãmi mãsu shahãda daga gare ku. Kuma Allah ba Ya son azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 141,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 68,
            "translated_text": "Kuma dõmin Allah Ya ɗauraye waɗanda suka yi ĩmãni, kuma Ya ƙõƙe kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 142,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 68,
            "translated_text": "Ko kun yi zaton ku shiga Aljanna alhãli kuwa Allah bai bãda sanin waɗanda suka yĩ jihãdi daga gare ku ba, kuma Ya san mãsu haƙuri?"
        },
        {
            "ayah_number": 143,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 68,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa kun kasance kuna gũrin mutuwa tun a gabãnin ku haɗu da ita, to lalle ne kun gan ta,* alhãli kuwa kuna kallo.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mutuwa watau, kunã gũrin wani yãƙi a bãyan na Badar yã zo."
        },
        {
            "ayah_number": 144,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 68,
            "translated_text": "Kuma Muhammadu bai zama ba face manzo lalle ne manzanni sun shũɗe a gabãninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, zã kujũya a kan dugaduganku? To, wanda ya jũya a kan dugadugansa, bã zai cũci Allah da kõme ba. Kuma Allah zai sãka wa mãsu gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 145,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 68,
            "translated_text": "Kuma bã ya yiwuwa ga wani rai ya mutu fãce da iznin Allah, wa'adi ne mai ƙayyadadden ajali. Kuma wanda yake nufin sakamakon dũniya Muna bã shi daga gare ta. Kuma wanda ke nufin samakon Lãhira Muna bã shi daga gare ta. Kuma zã Mu sãka wa mãsu godiya."
        },
        {
            "ayah_number": 146,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 68,
            "translated_text": "Kuma da yawa wani Annabi wanda ya yi yãƙi, akwai jama'a mãsu yawa tãre da shi, sa'an nan ba su yi laushi ba ga abin da ya same su a cikin hanyar Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su sad da kai ba. Kuma Allah yana son mãsu haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 147,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 68,
            "translated_text": "Kuma bãbu abin da ya kasance maganarsu fãce faɗarsu cẽwa: \"Ya Ubangijinmu! Ka gãfarta mana zunubanmu da ɓarnarmu a cikin al'amarinmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 148,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 68,
            "translated_text": "Allah Yã sãka musu da sakamakon dũniya da kuma kyakkyawan sakamakon Lãhira. Kuma Allah yana son mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 149,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 69,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗa'aga waɗanda suka kãfirta zã su mayar da ku a kan dugãduganku, har ku jũya kunã mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 150,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 69,
            "translated_text": "Ã'a, Allah ne Majiɓincinku kuma ShĨ ne Mafi alhẽrin matai maka."
        },
        {
            "ayah_number": 151,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 69,
            "translated_text": "Zã Mu jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta sabõda shirkin da suka yi da Allah gãme da abin da bai saukar da wani dalili ba game da shi. Kuma makõmarsu wuta ce, kuma tir da mazaunin azzãlumai!"
        },
        {
            "ayah_number": 152,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 69,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lõkacin da kuka kãsa,* kuma kuka yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma kuka sãɓã a bãyan (Allah) Ya nũna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lãhĩra. Sa'an nan kuma Ya jũyar da ku daga gare su, dõmin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Ya yãfe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga mũminai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A lõkacin da aka fãra Yãƙin Uhdu Musulmi suka fãra kõra sunã kisa sunã kãmu. Sai wasu maharba suka ce: \"Kada a kãme ganĩma a bar mu,\" Shugabansu Abdullahi bn Jubair ya ce musu, \"Ku tuna da maganar Manzon Allah da ya ce kada mu bar wurinmu sai idan shi ne ya kirãye mu.\" Sai suka ƙi saurãran maganarsa suka tafi kãmun ganima. Sai Allah Ya biyõ musu da Khãlid bn walĩd ta bãya, ya kashe Abdullahi da sauran waɗanda suka rage. Sa'an nan kuma sai yãƙĩn Musulmi ya karye, suka gudu suka hau dũtse, sai mutum gõma sha ɗaya ko shã biyu kawai aka bari tãre da Annabi, yana kiran su sunã gudu."
        },
        {
            "ayah_number": 153,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 69,
            "translated_text": "A lõkacin da kuke hawan dũtse, gudãne. Kuma ba ku karkata a kan kõwa ba, alhãli kuwa Manzon Allah nã kiran ku a cikin na ƙarshenku.* Sa'an nan (Allah) Ya sãkã muku da baƙin ciki a tãre da wani baƙin ciki. Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi baƙin cikin a kan abin da ya sãme ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyan da hankalinsu ya kõma gare su sai suka ga sakamakon sãɓãwa umurnin Allah, ya zama karyewar yãƙi da rashin ganĩma."
        },
        {
            "ayah_number": 154,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 70,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bãyan baƙin cikin; gyangyaɗi yanã rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rãyukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da bã shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cẽwa: \"Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?\" Ka ce, \"Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne.\" Suna ɓõyẽwa a cikin zukatansu, abin da bã su bayyana shi a gare ka. Suna cẽwa: \"Da munã da wani abu daga al'amarin dã ba a kashe mu ba a nan.\"Ka ce: \"Kõ dã kun kasance a cikin gidãjenku, dã waɗanda aka rubũta musu kisa sun fita zuwa ga wurãren kwanciyarsu;\" kuma (wannan abu yã auku ne) dõmin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirãzanku. Kuma dõmin Ya tsarkake abin da ke cikin zukãtanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza."
        },
        {
            "ayah_number": 155,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 70,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka jũya daga gare ku a ranar haɗuwar jama'a biyu, shaiɗan kawai ne ya talãlãɓantar da su, sabõda sãshen abin da suka tsirfanta. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yãfe laifidaga gare su. Lalle Allah ne Mai gãfara Mai haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 156,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 70,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku kasance kamar waɗanda suka kãfirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan, sun yi tafiya a cikin ƙasa kõ kuwa suka kasance a wurin yãƙi: \"Dã sun kasance a wurinmu dã ba su mutun ba, kuma dã ba a, kashe su ba.\" (Wannan kuwa) Dõmin Allah Ya sanya waccan magana ta zama nadãma a cikin zukãtansu. Kuma Allah ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 157,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 70,
            "translated_text": "Kuma lalle ne idan aka kashe, ku a cikin hanyar Allah, ko kuwa kuka mutu, haƙĩƙa, gãfara daga Allah da rahama ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 158,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 71,
            "translated_text": "Kuma lalle ne idan kun mutu ko kuwa aka kashe ku, haƙĩƙa, zuwa ga Allah ake tãra ku."
        },
        {
            "ayah_number": 159,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 71,
            "translated_text": "Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara* da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Annabi shi ne makomar al'amurra ga dukkan kome, amma Allah Ya lizimta masa sauƙin hali zuwa ga sahabbansa, da yin ma'ãmala da su, ma'ãmala mai kyau, da yi musu addu'a a kõwane hãli, kuma a wurin yãƙi kõ abin da ya shãfi yãƙi, Yã lizimta masa ya yi shãwara da su, kuma Ya bã shi damar yin ijtihãdi a nan, sa'an nan Ya umurce shi daya dõgara ga Allah wajen zartaswa, a kan ra'ayin da ya gani daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 160,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 71,
            "translated_text": "Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wãnẽ ne wanda yake taimakon ku bãyanSa? Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara."
        },
        {
            "ayah_number": 161,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 71,
            "translated_text": "Kuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu.* Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar ¡iyama. Sa'an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Gulũlu shĩ ne satar wani abu daga ganimar yãƙi a gabãnin raba ta a tsakãnin mayãka. Allah Yã ce, \"Yin gulũlu haram ne a kan kõwane annabi ko da waɗanda ba a halatta wa cin ganima ba, balle ga wanda aka halatta wa. Kamar yadda gulũlu yake haram a kan annabãwa haka yake haram a kan mabiyansu.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 162,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 71,
            "translated_text": "Shin fa, wanda ya bĩbiyi yardar Allah, yana zama kamar wanda ya kõma da fushi daga Allah kuma makomarsa Jahannama ce? Kuma tir da makõma ita!"
        },
        {
            "ayah_number": 163,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 71,
            "translated_text": "Sũ, darajõji* ne a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mũminai mãsu darajõji ne a wurin Allah gwargwadon ĩmãninsu da taƙawarsu da kuma falalar da Allah Ya yi musu. Haka sũ kuma kãfirai sunã da magangara zuwa ƙasa gwargwadon mugun aikinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 164,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 71,
            "translated_text": "Lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi babbar falala* a kan mũminai, dõmin Yã aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ãyõyinSa a gare su, kuma yana tsar kake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima kuma lalle, sun kasance daga gabãni, haƙĩƙa suna cikin ɓata bayyananniya.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Yã nũna falalar da Ya bai wa Annabi Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da yake har yanã yi wa mũminai gõri da kyautar da Ya yi musu ta hanyar aiko musu shi."
        },
        {
            "ayah_number": 165,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 71,
            "translated_text": "Shin kuma a lõkacin(5) da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: \"Daga ina wannan yake?\" Ka ce: \"Daga wurin rãyukanku(6) yake.\" Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n(5) Duk masĩfar da ta sãme ku, tõ, ku ne kuka jãwo wa kanku ita da wani laifi na sãɓãwa umurnin Allah. Kuma kãmin masĩfa guda ta sãme ku, to, alheri biyu sun sãme ku. (6) Kowace irin masĩfa ta sãmi mutum, to, shĩ ne ya yi sababinta a kansa. Kuma yã kamata ya yi bincike ya gãne sababin, a inda ya jãhilce shi. Kuma duk da haka kãmin masĩfa guda ta sãme shi, ya sãmi ni'ima biyu kõ fiye da haka."
        },
        {
            "ayah_number": 166,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 72,
            "translated_text": "Kuma abin da ya sãme ku a rãnar haɗuwar jama'a biyu, to, da izinin Allah ne, kuma dõmin (Allah) Ya san mũminai (na gaskiya)."
        },
        {
            "ayah_number": 167,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 72,
            "translated_text": "Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: \"Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe.*\" Suka ce: \"Dã mun san (yadda ake) yãƙi dã mun bĩ ku.\" Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ku tunkuɗe mana maƙiyã da duhunku, kõ dã ba ku yi yãƙi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 168,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 72,
            "translated_text": "Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: \"Dã sun yi mana ɗã'a, dã ba a kashe su ba.\" Ka ce: \"To, ku tunkuɗe mutuwa daga rãyukanku, idan kun kasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 169,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 72,
            "translated_text": "Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu*. Ana ciyar da su.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A cikin Hadisi an ruwaito cewa, Annabi yã ce Allah Yanã sanya rũhinsu a cikin cikkunan tsuntsãye mãsu kõren launi, sunã tafiya da su a cikin Aljanna sunã ci daga 'ya'yan itãcenta da rãna, sa'an nan su kõma zuwa ga wasu fitillu waɗanda aka rãtaye a cikin inuwar Al'arshi."
        },
        {
            "ayah_number": 170,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 72,
            "translated_text": "Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; \"Bãbu tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 171,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 72,
            "translated_text": "Suna yin bushãra sabõda wata ni'ima daga Allah da wata falala. Kuma lalle ne, Allah bã Ya tozartar da ijãrar mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 172,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 72,
            "translated_text": "Waɗanda suka karɓa* kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki ya sãme su. Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata** yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayan kõmawar Musulmi daga Uhdu da miyãkun da suka sãme su, sai Annabi ya umurce su da fita a bãyan kãfirai, dõmin kada su yi tunãnin kõmãwa. Sai suka fita bãyansu, aka dãce kuwa Abu Sufyãna ya umurci mutãnensa da kõmawa Madĩna dõmin su tumɓuke Musulmi. An yi Uhdu ta farko ran Asabat, sa'an nan suka fita a bãyansu a rãnar Lahadi, suka riske su a Hamra'al Asad. Sai aka yi tawãfuƙi (yarjejeniya) tsakanin Annabi da Abu Sufyãna a kan a bar yãƙi a lõkacin, sai shekara mai zuwa, a haɗu a Badar. Allah Ya yabi Musulmi, da suka karɓa wannan kira, a cikin miyãkũ. Haka duka mai karɓawa irinsu, yã shiga a cikin irin wannan yabo har ya zuwa tãshin Ƙiyãma. ** Kyautata yi shi ne tsarkake aiki dõmin Allah watau ihsani kõ ihlasi."
        },
        {
            "ayah_number": 173,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 72,
            "translated_text": "Waɗanda mutãne(5) suka ce musu: \"Lalle ne, mutãne sun tãra (rundunõni) sabõda ku, don haka ku ji tsõrnsu. Sai (wannan magana) ta ƙara musu ĩmãni, kuma suka ce: \"Mai isarmu Allah ne kuma mãdalla da wakili Shĩ.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n(5) Yãƙin Badar na Uku, a cikin shekara ta huɗu yake, a watan Sha'aban. Badar kãsuwa ce babba ga ƙabĩlun Lãrabãwa a kõwace shekara. A bãyan Uhdu an yi alkawari da Abu Sufyãna, a kan a haɗu a Badr shekara mai zuwa. Sabõda haka sai Abu Sufyãna ya fita daga Makka har ya sauka Marriz zahrãn, sai Allah Ya sanya masa tsõro a cikin zũciyarsa sai ya gamu da Nu'aima bn Mas'ũd el Ashja'iy, ya ce masa: \"Ni nã yi alkawari da Muhammadu a kan mu haɗu a Kãsuwar Badar. Wannan kuwa shekar fari ce. Inã son sãɓãwar alkawarin ta zama daga gare shi, bã daga gare ni ba. Ka tafi Madĩna ka yi ƙõƙarin hana su fitõwa, zan bã ka rãƙuma gõma.\" Sai Nu'aimu ya tafi Madĩna ya iske Annabi da Sahabbansa suna shirin fita. Sai ya ce musu: \"Me kuke nufi?\" Suka ce; \" Alkawarin Abu Sufyãna.\" Sai ya ce: \"Bã zã ku iya ba, dõmin kuwa sun tãra rundunõni sabõda ku.\" Sai Annabi ya ce: \"Zan fita kõ da nĩ kaɗai ne.\" Sai Annabi ya fita da mutum dubu da ɗari biyar, suka tafi Badar bãbu Abu Sufyãna. Suka ci kãsuwa suka kõmo."
        },
        {
            "ayah_number": 174,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 73,
            "translated_text": "Sa'an nan sukajũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 175,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 73,
            "translated_text": "Wancan, Shaiɗan ne kawai yake tsõratar da, ku masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu ku ji tsõro Na idãn kun kasance mãsu ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 176,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 73,
            "translated_text": "Kuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cẽwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 177,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 73,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda suka sayi kãfirci da ĩmani, ba zã su cũci Allah da kõme ba. Koma sunã da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 178,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 73,
            "translated_text": "Kuma kada waɗanda suka kãfirta su yi zaton cẽwa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alhẽri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su ƙãra laifi kawai kuma suna da azãba mai wulãƙantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 179,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 73,
            "translated_text": "Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai* Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba.** Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa.*** Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Watau Allah bã zai bar mutãne su ce: 'Mun yi ĩmãni, da bãki kawai ba,' sai Yã jarraba su Ya fitar da mũminan ƙwarai daga munãfukai. Sabõda haka Ya sanya rãnaiku kamar rãnar Uhdu wadda Allah Ya jarrabi mũminai da ĩta har haƙurinsu da ɗã'arsu suka bayyana, kuma munãfukai suka bayyana. ** Allah bai sanar da gaibi ga mutãne waɗanda ba Annabãwa ba, sabõda haka bã ku iya sanin ĩmãnin mutum ko rashin ĩmãninsa, sai da alãma ta wani aikĩ ko magana wadda take da ita za a iya yin hukunci da kãfirci ko ĩmãnĩ ga mutum. *** Allah Yã zãɓi wanda Ya so daga manzanninSa, watau Yã zaɓi Annabi Muhammadu da ƙãrin daraja a kan sauran Annabãwa da falalarsa. Wannan ne mafificin yabo a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 180,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 73,
            "translated_text": "Kuma kada waɗannan da suke yin rõwa da abin da Allah Ya bã su daga falalarSa su yi zaton shĩ ne mafi alhẽri a gare su A'a, shĩ mafi sharri ne a gare su. Zã a yi musu saƙandami da abin da suka yi rõwa da Shi a Rãnar ¡iyãma Kuma ga Allah gãdon sammai da ƙasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 181,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 74,
            "translated_text": "Lalle ne, haƙĩƙa Allah Yã ji maganar waɗanda suka ce: \"Lalle ne, Allah faƙĩri ne, mũ ne wadãtattu.\" za mu rubũta abin da suka faɗa, da kisan da suka yi wa Annabãwa bã da wani haƙƙi ba kuma Mu ce: \"Ku ɗanɗani azãbar gõbara!"
        },
        {
            "ayah_number": 182,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 74,
            "translated_text": "\"Wannan (azãbar) kuwa sabõda abin da hannuwanku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne Allah bai zama mai zãlunci ga bãyinsa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 183,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 74,
            "translated_text": "Waɗanda suka ce: \"Lalle ne Allah Yã yi alkawari zuwa gare mu, kada mu yi ĩmãni sabõda wani Manzo sai yã zo mana da Baiko wadda wuta za ta ci.\" Ka ce: \"Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabãnĩna, da hujjõji bayyanannu, kuma da abin da kuka faɗa, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance mãsu gaskiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 184,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 74,
            "translated_text": "To, idan sun ƙaryata ka, to lalle ne, an ƙaryata wasu manzanni a gabãninka, sun je musu da hujjõji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske."
        },
        {
            "ayah_number": 185,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 74,
            "translated_text": "Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar ¡iyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin rũɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 186,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 74,
            "translated_text": "Lalle ne zã a jarraba* ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Duk wanda ya tsayu da gaskiya ko umurni da alheri, ko hani daga abin da ba a so, to lalle ne sai an cũtar dashi, kuma ba shi da mãgani sai haƙuri, dõmin Allah, da neman taimako daga Allah, da kõmãwa zuwa ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 187,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 75,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa* Littãfi, \"Lalle ne kuna bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku ɓõye shi ba.\" Sai suka jẽfarda shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye!<br \/>\n____________________<br \/>\n* A cikin wannan akwai gargaɗi ga mãlaman Musulmi, kada su shiga hanyar Yahũdu ta ɓõye ilmin gaskiya, ko kuwa abin da ya sãme su, sũ ma ya sãme su, kuma ya shiga da su mashigarsu. Wãjibi ne akan mãlamai su bãyar da abin da ke hannuwansu na ilmi mai amfãni, mai nũni a kan aikin ƙwarai, kada su ɓõye kõme daga gare shi. Idan sun ɓõye, to, la'anar Allah da malã'iku da ta mutãne zã ta tabbata a kansu, kamar yadda ta tabbata a kan mãlaman Yahũdu."
        },
        {
            "ayah_number": 188,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 75,
            "translated_text": "Kada lalle ka yi zaton waɗanda suke yin farin ciki da abin da suka bãyar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikatã ba. To, kada lalle ka yi zaton su da tsĩra daga azãba. Kuma suna da azãba mai raɗadi."
        },
        {
            "ayah_number": 189,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 75,
            "translated_text": "Kuma ga Allah mulkin sammai da ƙasa yake. Kuma Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 190,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 75,
            "translated_text": "Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 191,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 75,
            "translated_text": "Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: \"Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta."
        },
        {
            "ayah_number": 192,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 75,
            "translated_text": "\"Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai, wanda Ka shigar a cikin wuta to, haƙĩƙa, Ka tozarta shi kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 193,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 75,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki."
        },
        {
            "ayah_number": 194,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 75,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar alkawari.\""
        },
        {
            "ayah_number": 195,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 76,
            "translated_text": "Sabõda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cẽwa, \"Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yãƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudãna daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako."
        },
        {
            "ayah_number": 196,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 76,
            "translated_text": "Kada jujjuyawar waɗanda suka kãfirta a cikin garũruwa ta rũɗe ka."
        },
        {
            "ayah_number": 197,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 76,
            "translated_text": "Jin dãɗi ne kaɗan sa'an nan makõmarsu Jahannama ce, kuma tir da shimfiɗa ita!"
        },
        {
            "ayah_number": 198,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 76,
            "translated_text": "Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa sunã da Gidãjen Aljanna (waɗabda) ƙoramu ke gudãna a ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu, a kan, liyãfa daga wurin Allah, kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alhẽri ga barrantattu."
        },
        {
            "ayah_number": 199,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 76,
            "translated_text": "Kuma lalle ne daga Mutãnen Littãfi* haƙĩƙa akwai wanda yake yin ĩmãnĩ da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, sunã mãsu tawãlu'i ga Allah, bã su sayen tamani kaɗan da ãyõyin Allah. Waɗannan suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako da yawa ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A cikin Mutãnen Littãfi akwai mutãnen ƙwarai na kirki waɗanda hãsada ba ta hana su bin gaskiya ba. Sun sifantu da sifõfin kamãla; watau ba dukkansu ne miyagu ba. Akwai na ƙwarai a cikinsu kamar yadda hãli yake a kõwane tãron mutãne."
        },
        {
            "ayah_number": 200,
            "surah_number": 3,
            "page_number": 76,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku yi haƙuri kuma ku yi dauriya, kuma ku yi zaman dãko, kuma ku yi taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Haƙuri a kan ibãda da ɗaukar wahalõlin sharĩ'a gabãɗaya gwargwadon ĩkon yi. Dauriya a kan abokan gaba; watau kada maƙiya su fi mũminai haƙuri wajen yãƙi daɗaukar wahalõlinsa. Zaman dãko ga taushewar hanyõyin abõkan gaba daga barin shiga ƙasar Musulmi. Bãbu bambanci ga maƙiyi bayyananne da maƙiyi ɓõyayye. Maƙiyi ɓõyayye ya fi aibi dõmin kasancewarsa, zai shiga wuta, amma kasancewarsa maƙiyi bayyananne, zai shiga Aljanna. Taƙawa ita ce bin umuruin Allah da kangewa daga barin haninSa kamar yadda Ya faɗa. Wannan shĩ ne kan ibãda duka bãyan ĩmãni, dõmin haka ya ce kõ zã ku ci nasara, idan kun riƙe waɗannan abũbuwa da kyãwo."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 77,
            "translated_text": "Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta.* Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bin Allah Wanda Ya halitta ku, kira ga tabbatar da tauhidin Ulũhiyya ne da Rubũbiyya. Fitar mutãne daga asali guda, wanda bãbu wani surki a cikinsa yana wajabtar da girman jinsin mutum, kõwane iri ne, kowane launi, kuma kõwace halitta yake ɗauke da ita.Tsõron Allah da tsaronSa a kan mutãne yana wajabtar da tsayãwa a cikin haddõdin sharĩ'arSa. Tsõron zumunta ko rantsuwa da ita yana wajabtar da tausayi da rahama a kan halittar Allah na kusa da na nesa. Hadĩsi ya nũna ba a yin rantsuwa da wanin Allah sabõda haka ma'anar aya itace, 'Ku ji tsõron Allah ku tsare mahaifa da zumunta!'."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 77,
            "translated_text": "Kuma ku bai wa marãyu dũkiyõyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau. Kuma kada ku ci dũkiyõyinsu zuwa ga dũkiyõyinku. Lalle shi, yã kasance zunubi ne mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 77,
            "translated_text": "Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu,* to, (akwai yadda zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Asalin marãya shĩ ne yãron da bai balaga ba, kuma ubansa ya mutu. Amma a cikin ãya-Allah Yã sani-anã nufin dukkan mai rauni a cikin al'umma, wanda yake neman a tsare haƙƙin sa da Allah Ya ɗõra wa Musulmi su tsare. Sabõda haka Ya shãfe jawãbin sharaɗin kuma Ya fãra da hukunce-hukunce, a kan tafsĩlin yadda zã a tsare mãsu rauni a cikin al'umma. Ya fãra da mãta a wajen aure, adadinsu daga ɗaya zuwa huɗu, gwargwadon ƙarfin mutum da iyãwarsa ga tsaida ãdalci a gare su, kõ a tsakãninsu. Ãdalci na kwãna da ciyarwa da tufãtarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 77,
            "translated_text": "Kuma ku bai wa mãtã sadãkõkĩnsu da sauƙin bãyarwa. Sa'an nan idan suka yãfe muku wani abu daga gare shi, da dãɗin rai, to, ku ci shi da jin dãɗi da sauƙin haɗiya."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 77,
            "translated_text": "Kada ku bai wa wãwãye* dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kunã mãsu tsayuwa (ga gyãranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufãtar da su, kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sa'an nan yadda ake riƙon dũkiyar wãwã wanda bai san yadda ake riƙon dũkiya ba, ko dã shĩ bãligi ne, yã yi aure, kuma ko da shĩ ne yake neman dũkiyarsa da kansa; kamar da ijãra. Wannan wata hanyace ta tsaron haƙƙin mãsu rauni."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 77,
            "translated_text": "Kuma ku jarraba marãyu, har a lõkacin da suka isa aure. To, idan kun lura da shiriya daga gare su, to, ku mĩƙa musu dũkiyõyinsu. Kada ku cĩ ta da ɓarna, kuma da gaggawa kãfin su girma. Kuma wanda yake wadãtacce, to, ya kãma kãnsa, kuma wanda yake faƙĩri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun mĩƙa musu dũkiyõyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 78,
            "translated_text": "Maza suna da rabo* daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hukunce-hukuncen rabon gãdo, hanya ce ta tsaron haƙƙin mãsu rauni."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 78,
            "translated_text": "Kuma idan ma'abũta zumunta da marãyu da matalauta suka halarci rabon, to, ku azurta su daga gare shi, kuma ku faɗa musu magana sananniya ta alhẽri."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 78,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke dã sun bar* zuriyya mãsu rauni a bãyansu, zã su ji tsõro a kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana madaidaiciya.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Watau yadda mutum mai ƙanãnan 'ya'ya yake tsõron ya mutu ya bar su bãbu wata dũkiya da zã ta taimake su, haka kuma su Musulmi waɗanda aka sanya aikin rabon gãdo a hannunsu, su yi tunani, dã su ne suka mutu suka bar 'ya'yansu haka. Sabõda haka wannan zai karya zũciyar mai son ya yi zãlunci daga dũkiyar marãyu."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 78,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda suke cĩn dũkiyar marãyu da zãlunci, to, wuta kawai suke ci a cikin cikkunansu, kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 78,
            "translated_text": "Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da rabon mãtã biyu. Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi ba, kuma iyãyensa ne (kawai) suka gãje shi, to, uwa tanã da sulusi (ɗaya daga cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa bãshi. Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 79,
            "translated_text": "Kuma kunã da rabin abin da mãtanku na aure suka bari idan rẽshe bai kasance gare su ba. Sa'an nan idan rẽshe ya kasance gare su, to, kunã da rubu'i (ɗaya daga cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga bãyan wasiyya wadda suka yi kõ kuma bãshi. (Sũ) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan rẽshe bai kasance ba gare ku, idan kuwa rẽshe ya kasance gare ku, to, sunã da sumuni (ɗaya daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga bãyan wasiyya wadda kuka yi kõ kuwa bãshi. Idan wani namiji ya kasance ana gãdon sa bisa kalãla, ko kuwa wata mace alhãli kuwa yana da ɗan'uwa kõ 'yar'uwa* to, kõwane ɗaya daga cikinsu yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa daga wannan, to, sũ abõkan tãrayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga bãyan wasiyya wadda aka yi kõ kuma bãshi. Bã da yana mai cũtarwa ba, ga wasiyya, daga Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ɗan'uwa kõ 'yar'uwa, a nan,ana nufin li'ummi kõ li'ummiya, kõwane ɗayansu yana da sudusi; idan sunã da yawa, watau sun kai biyu kõ abin da ya fi biyu, to, suna da sulusi. Babu bambanci tsakanin namiji da mace gare su, dõmin jihar gadonsu mace ce,watau uwar mamacin."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 79,
            "translated_text": "Waɗancan iyãkõkin Allah ne. Wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi gidãjen Aljanna (waɗanda) ɗõramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 79,
            "translated_text": "Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãkantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 80,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka je wa alfãsha daga mãtanku, to, ku nẽmi Shaidar mutãne huɗu daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje har mutuwa ta karɓi rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ãyõyi na 15 da l6 an shãfe hukuncinsu wajen haddi da ãyar sũratun Nũr ta biya da Hadisin Rajami ga zawari da zawara waɗanda suka yi zina, kuma da bũlãla ɗari dakõrar babane namiji, da kuma bũlãla ɗari ga budurwa. Kuma ana jefe mai liwãɗi da wanda ake yi a kansa idan sun balaga, ko dã su banãwa ne. Ana ladabi ga mailiwãɗi da matãrsa, amma ba a kashe shi. Liwãɗi da wata mace kamar zina yake ga namijin."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 80,
            "translated_text": "Kuma waɗanda (mazã biyu) suka je mata* daga ku, to, ku cũtar da su, sa'an nan idan sun tũba kuma suka kyautata hãlãyensu, sai ku kau da kai da ga barinsu. Lalle ne Allah Yã kasance Mai kaɓar tũba ne, Mai jin ƙai<br \/>\n____________________<br \/>\n* Maza biyu mãsu je wa alfasha su ne mãsu yin liwãɗi da jũnansu."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 80,
            "translated_text": "Abar da take tũba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatãwar mugun aiki da jãhilci sa'an nan su tũba nan kusa* to, waɗannan Allah Yanã karɓar tũ barsu kuma Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Nan kusa, watau a gabãnin mutuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 80,
            "translated_text": "Bã tũba ba ce ga waɗanda suke aikatãwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci ɗayansu ya ce: \"Lalle ne ni, na tũba yanzu,\" kuma bã tũba ba ce ga waɗanda suke mutuwa alhãli kuwa sunã kãfi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 80,
            "translated_text": "Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka zo da wata alfãsha* bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawaa cikinsa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mugun halin da sharĩ'a ba ta yarda da shi ba kamar ƙiyokõ yãwon banza, a nan bãbu laifi ku hana su aure sai sun yi muku hul'i, kuma Allah Yã hana gãdon mãta kamar dũkiya. Sun kasance sunã yin haka, ba da sãke bayar da sadaki ba, domin dogara da wanda ubansa ya bãyar, sai su aurar da ita a kan haka ga wani ɗan'uwan mamacin, kõ kuma wanda suke so ya aure ta."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 81,
            "translated_text": "Kuma idan kun yi nufin musanya mãta a matsayin wata mãta, alhãli kuwa kun bai wa ɗayarsu ƙinɗari* to kada ku karɓi kõme daga gare, shi, shin, zã ku karɓe shi da ƙarya da zunubi bãyyananne?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ƙinɗãri, shi ne dũkiya mai yawa; ũƙiyya dubu gõma sha biyu, na azurfa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 81,
            "translated_text": "Kuma yãyã zã ku karɓe shi alhãli kuwa, haƙĩƙa, sãshenkuyã sãdu zuwa ga sãshe, kuma sun riƙi alkawari* mai kauri daga gare ku?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Alkawarin riƙonsu da alheri ko kuma sallamarsu da kyautatãwa. Baƙara Ãya ta 231."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 81,
            "translated_text": "Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne shi, ya kasance alfãsha da abin ƙyãma. Kuma ya mũnana ya zama hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 81,
            "translated_text": "An haramta muku uwãyenku, da 'yã'yanku, da 'yan'uwanku mãtã, da goggonninku, da innoninku, da 'yã'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku mãma, da 'yan'uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi* a kanku, da mãtan 'yã'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ɗaurin aure a kan ɗiya yana haramta uwarta, amma ɗaurin aure a kan uwa,bã ya haramta ɗiyar sai in an yi duhũli da ita, kõ kuma an yi tamattu'i da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 82,
            "translated_text": "Da tsararrun auren* wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya** da shi a bãyan farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* An haramta muku matan auren wasu maza, matuƙar mazansu ba su sake su ba, Musulmi ne kõ kuwa Kitãbãwa, sai fa idan kun kãmo su ne daga ƙasar da take ta abõkan gaba, a nan kunã iya tãkinsu haka, dõmin kãmu yã warware aurensu. Idan kun yi tamattu'ida wasu mãtã a kan kuskure, ba da aure ba, sai ku biya su sadãki a kan haka. An hana auren tamattu'i, watau yin aure zuwa ga ajali. Abdullahi bn Abbas ya ce yin sa yã fi zina. ** Bãyan sadãkin da aka yanka bãbu laifi ĩdan kun yi yardatayya da ƙãra wani abu a kan farilla, kuma bãbu laifi idan ita matar tã yarda da kãyar da ƙarin kõ kuwa shĩ mijin ya yarda da biyan ƙãrin."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 82,
            "translated_text": "Kuma wanda* bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, (ya aura) daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma Allah ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga** sãshe. Sai ku aurẽ su da izinin mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu kamun kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azãba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hukunce-hukuncen auren kuyanga ga wanda bai sãmi ĩkon auren'ya ba. Aibin auren kuyangi shi ne bautar da zuriya, domin bauta daga uwa take. Saboda haka bã ya halatta ga Musulmi ya auri baiwar kafiri, kome larurar da take ciki,sai dai ya saye ta daga gare shi.. **Ku duka daidai kukewajen ĩmãni da Musulunci. Dubi kuma Ãli'Imrãna 195."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 82,
            "translated_text": "Allah Yanã nufin Ya bayyana muku, kuma Ya shiryar da ku hanyõyin waɗanda suke a gabãninku kuma Ya karɓi tũbarku. Kuma Allah Masani ne Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 83,
            "translated_text": "Kuma Allah Yanã nufin Ya karɓi tũbarku. Kuma waɗanda suke bin sha'awõyi suna nufin ku karkata, karkata mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 83,
            "translated_text": "Allah Yana nufin Ya yi muku sauƙi, kuma an halitta mutum yana mai rauni."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 83,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci dũkiyõyinku a tsakãninku da yaudara*, fãce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hukuncin cin dukiyar mutane da ƙarya ko yaudara, haramun ne, domin yana kai ga mutane su kashe kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 83,
            "translated_text": "Wanda ya aikata wancan bisa ta'adi da zãlunci, to, zã Mu ƙõne shi da Wuta. Kuma wannan yã kasance ga Allah (abu ne) mai sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 83,
            "translated_text": "Idan kuka nĩsanci manyan abubuwan da ake hana ku aikatãwa, to, zã Mu kankare mũnanan ayyukanku daga gare ku, kuma Mu shigar da ku mashiga ta karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 83,
            "translated_text": "Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita sãshenku da shi a kan sãshe; maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mãtã suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku rõƙi Allah daga falalarSa. Lalle ne Allah Yã kasance ga dukkan kõme, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 83,
            "translated_text": "Kuma ga kõwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta suka bari. Kuma waɗanda rantsuwõyinku suka ƙulla* ku bã su rabonsu. Lalle ne, Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mahalarci.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A zãmanin Jahiliyya ana ƙullin amana a tsakanin ƙabilu ko a tsakanin mutum da wani mutum. Wannan ƙullin amãnar yakan haɗa har da sudusin dukiyar wanda ya mutu daga cikinsu. Wasu Musulmi sun shiga Musulunci a bãyan sun ƙulla irin wannan amãnar sabõda haka Allah Ya yi umurni da cika wannan alkawarin, kuma Ya kashe al'adar, Ya musanya ta da hukunce-hukuncen Musulunci. Kuma ana fassara masu ƙullin rantsuwa da masu gudãnar da aikin rabon dũkiyar gãdo. Ana biyan su ijãrar wahalarsu daga kãwunan magãda kamar yadda ya kamata."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 84,
            "translated_text": "Maza mãsu tsayuwa ne* a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihanmãtã mãsu ɗã'a ne, mãsu tsarẽwa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to, kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Ya sanya shugabancin gida da gudanar da tasarrufinsa a hannuwan maza domin ginar jikinsu, da hankalinsu da kuma dukiyarsu da suke ciyarwa ga sadãki da kuma nafaƙar (ciyarwar) gidan. Kuma Allah Ya aza wa mãta ɗa'a ga maza da kuma tsare farjojinsu domin kada su kawo wani baƙon da ba ɗan gida ba, a cikin gidan."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 84,
            "translated_text": "Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta*. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hakamãni, ko masu sulhu biyu, su tafi su yi binciken abin da ya hana auren kyau, su tsawaci maras gaskiya daga cikin ma'auran, ko kuma su hukunta rabuwa da hul'i, ko ba da hul'i ba. Abin da suka hukunta alƙãlĩ ya zartar da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 84,
            "translated_text": "Kuma ku bauta wa *Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatãwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marãyu da matalauta, da maƙwabci ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci, da abõki a gẽfe da ɗan hanya, da abin da hannuwanku na dãma suka mallaka. Lalle ne Allah bã Ya son wanda ya kasance mai tãƙama, mai yawan alfahari.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bauta wa Allah shi ne a bi umurninsa, a bar haninsa a kome. Sa'an nan ya biyar da nau'ukan mutane waɗanda mutum zai yi ihsani zuwa gare su gwargwadon darajarsu kuma da halinsa. Sa'an nan zargi a kan marowaci da sakamakonsa, da mai ciyarwa amma ba a bisa hanyar bauta wa Allah ba."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 84,
            "translated_text": "Waɗanda suke yin rõwa, kuma sunã umurnin mutãne da yin rõwa, kuma suna ɓõyewar abin da Allah Ya bã su na falalarSa. Kuma Mun yi tattali, sabõda kãfirai, azãba mai walãkantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 85,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu dõmin nũna wa mutãne, kuma bã su yin ĩmãni da Allah, kuma bã su yin ĩmãnida Rãnar Lãhira kuma wanda Shaiɗan ya kasance abõkin haɗi a gare shi, to, yã mũnana ga abõkinhaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 85,
            "translated_text": "Kuma mẽne ne a kansu, idan sun yi ĩmãni da Allah, kumada Rãnar Lãhira, kuma sun ciyar da abin da Allah Yã azurtã su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani?"
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 85,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah bã Ya zãluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alhẽri ce, zai riɓanya ta, kuma Ya kãwo daga gunsa ijãra mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 85,
            "translated_text": "To, yãyã, idan Mun zo da shaidu daga dukkan al'umma, kuma Muka zo da kai a kan waɗannan, kana mai shaida!"
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 85,
            "translated_text": "A rãnar nan, waɗanda suka kãfirta kuma suka sãɓã wa Manzo, sunã gũrin dã an baje ƙasa dasu, kuma bã su ɓõye wa Allah wani labãri."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 85,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye*, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da hannuwanku.** Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A lokacin ba a hana shan giya ba. Sa'an nan aka hana ta da ayar Suratul Ma'idah ta 90. Mai janaba kuma ba ya yin salla kuma ba ya shiga masallaci sai ya yi wanka ko taimama, sai dai yana iya shiga da niyyar wucewa daga ƙõfa zuwa ga wata, ko kuwa ya shiga ya ɗebo ruwa ya fita. Ana yin taimama saboda rashin ruwa haƙiƙatan, ko ma'anan, kamar mai rashin lafiya. Shafar mace na karya alwala, amma ba ya sabbaba wanka idan an yi shafar da niyyar jin dãɗi ko kuma an sami jin dãɗin ba da nufi ba. Mai shafar da wanda aka shafa duka ɗaya suke.** Wãtau ku yi taimama sabõda rashin ruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 85,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda aka bai wa rabo daga Littafi, suna sayen ɓata, kuma suna nẽman ku ɓace daga hanya?"
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 86,
            "translated_text": "Kuma Allah ne Mafi sani ga maƙiyanku, kuma Allah Yã isa Ya zama Majibinci, kuma Yã isa Ya zama Mataimaki."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 86,
            "translated_text": "Daga waɗanda suka tũba (Yahũdu), akwai wasu sunã karkatar da magana daga wurãrenta suna cẽwa: \"Munjiya* kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyãwa, kuma rã'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu,\" dõmin karkatarwa da harsunansu, kuma dõmin sũkã a cikin addini. Kuma dã lalle sũ, sun ce: \"Mun jiya kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurãra kuma ka dãkata mana,\" haƙĩƙa, dã ya kasance mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yã la'anẽ su, sabõda kãfircinsu don haka bã zã su yi ĩmãni ba, sai kaɗan.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yahudu, ana kiran su da maganar Mũsa da ya ce wa Ubangiji, ‘Mun tuba zuwa<br \/>\ngare Ka, yã Allah,’ (A’ãrãf, ãyã ta 155) dõmin izgili da suke yi na ƙin bin haddõdin Allah.<br \/>\nSunã karkatar da magana da asalin ma’anarta zuwa ga wata ma’ana ta izgili, sunã céwa<br \/>\n‘Mun ji’ amma aikinsu yanã nuna céwa, ‘Sun ƙi’ suke nufi. Kuma ‘Ka jiya a wanin wurin<br \/>\njiyãwa’ addu’a ce mai ɗaukar ma’anar alhẽri da ma’anar sharri, su kuwa sunã nufin ta<br \/>\nsharrin. Haka kalmar ‘rã‘ina’ tanã da ma’anar ‘tsãre mu’ ko ‘saurãra mana’, kuma tanã da<br \/>\nma’anar ‘Yã ruɓaɓɓe'. Sunã nufin ma’anar ƙarshen.<br \/>\nWannan bayãni’ shi ma taimako ne ga Musulmi mãsu raunin hankali dõmin a tsare<br \/>\nmusu addininsu kamar yadda ake tsaron dũkiyarsu. An cũsa irin wannan mãkirci a wata<br \/>\naddu’a da suke cewa ‘Jauharatul Kamãli’ inda suka sifanta wanda suke yi wa salãti da<br \/>\n“asƙam” mafi cũta. Wannan tã yi daidai da kalmar rã’ina, ko ma ta fi mũni, dõmin rã’ina<br \/>\ntanã da wata ma’ana ta yabo, amma asƙam bã ta da wata ma'ana sai ta zãgi kawai. Allah<br \/>\nYa tsare mu daga sharrin maƙiyan addini."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 86,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda aka bai wa Littãfi! Ku yi ĩmãni da abinda Muka saukar, yana mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, tun gabanin Mu shãfe wasu fuskõki, sa'an nan Mu mayar da su a kan bãyayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 86,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 86,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? Ã'a, Allah ne Yake tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabĩno ba."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 86,
            "translated_text": "Ka dũba yadda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah! Kuma shi ya isa ga zama zunubi bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 86,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabõ da ga Littafi suna ĩmãni da gunki da Shaiɗan* kuma suna cẽwa ga waɗanda suka kãfirta: \"Waɗannan ne mafiya shiriya daga waɗanda suka yi ĩmãni ga hanya\"?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Jibti sunan kowane gunki ne.Ɗãgũtu sunan Shaiɗan ne mai ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, sheɗãnin da yake zama tare da gumãka ko waninsu, mutum ne ko aljani, dõmin ya ɓatar da mãsu raunin hankali, a cikin Yahũdu ko a cikin Musulmi."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 87,
            "translated_text": "Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la'ane su, kuma wanda Allah Ya la'ana to bã zã ka sãmi mataimaki a gare shi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 87,
            "translated_text": "Ko suna da rabõ ne daga mulki? To, a sa'an nan bã zã su iya bai wa mutãne hancin gurtsun dabino ba."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 87,
            "translated_text": "Ko suna hãsadar mutãne* ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah sun tabbata agare shi. An ce masa ɗan gidan Ibrahim domin Yahũdu su san shi ba kasasshe ba ne ga dangantaka, daga gare su. Kuma bai fita ba daga tsãrin cewa Annabãwa mãsu Littãfi a bãyan Ibrãhĩm, daga zuriyarsa za su fito. Kuma sun san wannan a cikin littãfinsu, watau Attaura."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 87,
            "translated_text": "To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kange daga gare shi. Kuma yã isa Jahannama ta hũru da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 87,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 87,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yiĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su gidãjen Aljanna, (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 87,
            "translated_text": "Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ.* Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji ne, Mai gani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Talakãwa mutãne ne mãsu rauni a cikin hannuwan shugabanninsu. Su da dukiyarsu amãnõni ne na Allah a cikin hannuwan shugabanni, saboda haka tsaronsu da dukiyarsu, gwargwadon shari'a, da yin hukunci a tsakaninsu da ãdalci, bãyar da amãna ne ga mãsu ita.Wanda ya bi son zuciyarsa duka ga ɗayan waɗannan abũbuwa, to, yã yi yaudara ga Allah ke nan. Allah kuma zai kama shi da hukuncin mayaudari."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 87,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku.* Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Haka su kuma mutãne talakãwa, amãna ce a kansu su yarda da hukuncin Allah da Manzonsa, a kome na al'amurransu da mu'ãmalõlinsu. Kuma wãjibi ne a kansu su yarda da abin da aka hukunta a kansu daidai da sharĩ'ar Allah. Su kuma idan sun sãɓa, to, sun yaudari amãnar Allah ke nan."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 88,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cẽwa sunã ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra zuwa ga ¦ãgũtu* alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma Shaiɗan yanã nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ɗãgũtu shi ne dukan mai yin dõkõki waɗanda ba dõkõkin Allah ba. Dukan wanda ya bi dõka wadda ba ta Allah ba a cikin ibãda, ko wadda ta saɓa wa haddin Allah a cikin mu'ãmalõli na haƙƙõƙi ko na laifuka, to, ya shiga cikin wannan tarkon."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 88,
            "translated_text": "Kuma idan aka ce musu: \"Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo\" zã ka ga munãfukai* sunã kange mutãne daga gare ka, kangẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Miyãgun shugabanni mãsu karkatar da mũminai daga hukuncin Allah da hujjar wai suna nufin su daidaita domin a haɗa Musulmi da kãfirai ga hukunci; ta haka har kãfiri ya kasance mai yin hukunci a kan Musulmi. Su waɗannan masu yin haka ba Musulmi ba ne, munãfukan Musulmi ne. Musuluncinsu na bãki ne kawai, dã yã kai ga zũciya dã ba su yi ko tunãnin yarda da haka ba. Allah Ya tsare mu daga sharrin Shaiɗan,."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 88,
            "translated_text": "To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar sa'an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cẽwa, \"Ba mu yi nufin kõme ba sai kyautatawa da daidaitãwa.\"?"
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 88,
            "translated_text": "Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasãha."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 88,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu,* sun zo maka sa'an nan suka nẽmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wanda ya ƙi hukuncin Allah, ya yi laifi biyu, domin sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wannan ya nũna rashin ĩmãninsa da Allah da ManzonSa. Saboda haka ne ãyã mai bin wannan ta ce Musulmi bã su da ĩmãni sai sun yarda da Hukuncin Allah ga kome daga al'amurransu, kuma su yarda da hukuncinsa, bã da jin wani ƙunci a cikin zukatansu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 88,
            "translated_text": "To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 89,
            "translated_text": "Kuma dã dai lalle Mũ, Mun wajabta musu cẽwa, \"Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita daga gidãjenku,\" dã ba su aikata shi ba, fãce kaɗan daga gare su. Kuma dã dai lalle sũ sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 89,
            "translated_text": "Kuma a sa'an nan, haƙĩƙa, dã Mun bã su, lãda mai girma, daga gunMu."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 89,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, dã Mun shiryar da su hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 89,
            "translated_text": "Kuma waɗannan da suka yi ɗã'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunã tãre da waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabãwa da mãsu yawan gaskatãwa, da masu shahãda* da sãlihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abõkan tafiya.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Darajar ɗaukaka ga addini shi ne zama Annabi sa'an nan siddĩƙ, watau manyan sahabban kowane Annabi. Waɗannan darajõji biyu yanzu an rufe su daga kõwa, dõmin bãbu sauran Annabci wanda yake tãre da siddĩƙanci. Ta uku ita ce shahãda watau a kashe mutum a wurin yãƙi dõmin ɗaukaka kalmar Allah da tsare haƙƙõƙin Musulmi. Wannan ita ce maƙasudin abin faɗa a nan, dõmin abin da sũrar ke karantarwa, kuma dõmin ya zama shimfiɗar magana a kan darajar jihãdi da amfanõninsa. Ta huɗu zama sãlihi mai son abin da Allah Yake so kuma mai ƙin abin da Allah Yake ƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 89,
            "translated_text": "Waccan falalar daga Allah take, kuma Allah Yã isa zama Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 89,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku riƙi shirinku* sa'an nan ku fitar da hari jama'a, jama'a ko ku fitar da yaƙi gaba ɗaya.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bã ya halatta Musulmi su zauna bãbu tattalin yãƙi da fitar da yãki ko hari a kan maƙiyansu, saboda abin da ke cikin wannan ãyar ta 71."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 89,
            "translated_text": "Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai fãsarwa*. To idan wata masĩfa ta sãme ku, sai ya ce: \"Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima dõmin ban kasance mahalarci tãre da su ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Siffar munãfuki ita ce ya ƙi fita zuwa yãƙi, kuma ya fãsar da waninsa, ya yi murnar hasãrar Musulmi, kuma ya yi baƙin cikin nasararsu, ya so a raba ganĩma da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 89,
            "translated_text": "Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta sãme ku haƙĩƙa, tabbas, yanã cẽwa, kamar wata sõyayya ba ta kasance a tsakãninku da shi ba: \"Yã kaitona! Dã na zama tãre da su dai, dõmin in rabonta da rabõ mai girma!\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 89,
            "translated_text": "Sai waɗanda suke sayar da rayuwar dũniya su karɓi ta Lãhira su yi yãƙi, a cikin hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yãki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa ya rinjãya, sa'an nan zã Mu ba shi ijãra mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 90,
            "translated_text": "Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã ku yin yãƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka raunanar daga maza da mata da yãra sunã cewa: \"Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga wannan alƙarya wadda mutãnenta suke da zãlunci, kuma Ka sanya mana majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa.\"?"
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 90,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi ĩmãni, sunã yãki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kãfirta sunã yãƙi a cikin hanyar ¦ãgũtu (Shaiɗan). To, ku yãƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle ne kaidin Shaiɗan yã kasance mai rauni."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 90,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: \"Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka.\"? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: \"Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?\"Ka ce: \"Jin dãɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!"
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 90,
            "translated_text": "\"Inda duk kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku, kuma kõ da kun kasance ne a cikin gãnuwõyi ingãtattu!\"Kuma idan wani alhẽri ya sãme su sai su ce: \"Wannan daga wurin Allah ne,\" kuma idan wata cũta ta sãme su, sai su ce: \"Wannan daga gare ka ne.\"Ka ce: \"Dukkansu daga Allah ne.\" To, me ya sãmi waɗannan mutãne, bã su kusantar fahimtar magana?"
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 90,
            "translated_text": "Abin da ya sãme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutãne, (kana) Manzo, kuma Allah Yã isa ga zama shaida."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 91,
            "translated_text": "Wanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah. Kuma wanda ya jũya bãya, to, ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 91,
            "translated_text": "Kuma sunã cẽwa, \"Dã'a\" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwãna da niyyar wanin abin da take faɗa, alhãli kuwa Allah na rubũta abin da suke kwãna da niyyarsa. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dõgara ga Allah, kuma Allah Yã isa ya zama wakĩli."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 91,
            "translated_text": "Shin, bã su kula da Alƙur'ãni, kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dã sun sãmu, a cikinsa, sãɓã wa jũnamai yawa?"
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 91,
            "translated_text": "Kuma idan wani al'amari* daga aminci ko tsõro ya je musu, sai su wãtsa shi. Dã sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abũta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, zã su san shi. Kuma bã dõmin falalar Allah bã a kanku da rahamarSa, haƙĩƙa, dã kun bi Shaiɗan fãce kaɗan.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Umurnin al'umma da cewa idan sun ga wani al'amari daba su san kansa ba kõ kuwa idan wani abu na ban tsõro ya auku, to, haram ne su yi ta bãrãrarsa domin su firgitar da mutãne. Abin da yake wãjibi a kansu sa'an nan, shi ne su kai rahõtonsa ga shugabanni mãsu sanyãwa a bincika asan yadda abin yake, da kuma yadda zã a yi mãganinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 91,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka* yi yãƙi a cikin hanyar Allah, ba a kallafa maka ba, face a kanka, kuma ka kwaɗaitar da mũminai. Akwai tsammãnin Allah Ya kange gãfin waɗanda suka kãfirta, kuma Allah ne Mafi tsananin gãfi, kuma Mafi tsananin azabtãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Umurni zuwa ga Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gareshi."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 91,
            "translated_text": "Wanda ya yi* cẽto, cẽto mai kyau, zai sãmi rabo daga gare shi, kuma wanda ya yi cẽto, cẽto mummũna, zai sãmi ma'aunidaga gare shi, Kuma Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mai ƙayyade lõkaci.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ma'anar ceto: watau wani ya yi wa wani hanya a kan biyan bukãtarsa ta kowace iri, saboda darajar mai yin ceton. Ya kamãta ya yi ceton domin Allah wanda Ya bã shi darajar, bã da ya bai wa Allah kome ba. Idan kuma sayar da ceton yake yi, Allah zai karɓe darajar daga gare shi. Ci da ceto harãmun ne. Sakamakonsa shi ne Allah Ya karɓe darajar ceton daga gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 91,
            "translated_text": "Kuma idan an gaishe* ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta, kõ kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Yã kasance a kan dukkan kõme Mai lissãfi.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A gaisuwa idan an ce muku: \"Assalãmu alaikum\" ku mayar da cewa, \"Wa'alaikumus Salãmu wa rahamatul Lãhi wa barakãtuH.\" Kõ ku mayar kamar yadda aka yi muku. Watau kada ku naƙasa 'yan'uwanku kõ da ga gaisuwa ne. Faɗakarwa: Fara sallama mustahabbi ne, mayarwa kuma farilla ne, amma wanda ya fãra, ya fi lãda. Haka yin tsarki a gabãnin lokaci mustahabbi ne, amma a bayãn shigar lokaci ya zama wajibi. Wanda ya yi mustahabbi a nan yã fi lãda. Haka jinkirtar da biyan bãshi ga matsattse wãjibine, amma barrantar da shi mustahabbi ne. Yin mustahabbi a nan yã fi lada."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 92,
            "translated_text": "Allah bãbu abin bautawa face Shi. Lalle ne haƙĩƙa Yana tãra* ku har zuwa ga Yinin ¡iyãma bãbu shakka a cikinsa. Kuma wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga ãbãri.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Idan kun tsare hukunce-hukuncen da Allah, Wanda babu abin bautawa sai Shi, Ya umurce ku da su, to zai haɗa kalmarku ta tabbata guda har ya zuwa Rãnar Ƙiyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 92,
            "translated_text": "To, mẽne ne ya sãme* ku a cikin munãfukai kun zama ƙungiya biyu, alhãli kuwa Allah ne Ya mayar da su sabõda abin da suka tsirfanta? Shin, kunã nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmi wata hanya ba zuwa gare shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hani ne kada mũminai su rarraba kansu domin jãyayya a cikin sha'anin kãfirai. Sai su bi abin da Allah Ya ce a yi da su, kamar yadda bayãninsa yake tafe a cikin wannan aya da ayoyin da suke a bãyanta. Yã yi bayãni da tafsĩli daki-daki."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 92,
            "translated_text": "Suna gũrin ku kãfirta kamar yadda suka kãfirta, dõmin ku kasance daidai. Sabõda haka kada ku riƙi wasu masõya daga cikinsu, sai sun yõ hijira a cikin hanyar Allah. Sa'an nan idan sun jũya, to, ku kãmã su kuma ku kashe su inda duk kuka sãme su. Kuma kada ku riƙi wani masõyi daga gare su ko wani mataimaki."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 92,
            "translated_text": "Fãce dai waɗanda suke sãduwa zuwa ga wasu mutãne waɗanda a tsakãninku da su akwai alkawari, kõ kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirãzansu sun yi ƙunci ga su yãke ku, kõ su yãƙi mutãnensu. Kuma dã Allah Yã so lalle ne, dã Yã bã su ĩko a kanku, sa'an nan, haƙĩka, su yãke ku. To, idan sun nĩsance ku sa'an nan ba su yãƙe ku ba, kuma suka jẽfa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 92,
            "translated_text": "Za ku sãmi wasu* sunã nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutãnensu, kõ da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyã su a cikinta. To, idan ba su nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kãmã su, kuma ku kashe su inda duk kuka kãmã su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalĩli bayyanannea kansu.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sun bayyana ĩmãninsu gare ku dõmin ku amince musu, kuma sun bayyana kãfirci a wurin mutãnensu kãfirai domin su amince musu watau suna ido ruwa ido tudu. Sũ kam kãfirai ne, ku yãƙe su, sai fa idan sun musulunta, ko kuma sun bayyana sulhunsu sosai a gare ku."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 93,
            "translated_text": "Kuma bã ya kasancẽwa* ga mũmini ya kashe wani mũmini, fãce bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mũmina tare da mĩƙa diyya ga mutãnensa, ãce idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan (wanda aka kashe) ya kasance daga wasu mutãne maƙiya a gare ku, kuma shi mũminine, sai ya 'yanta wuya mũmina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutãne ne (waɗanda) a tsakãninku da tsakãninsu akwai alkawari, sai ya bãyar da diyya ga mutãnensa, tare da 'yanta wuya mũmina. To, wanda bai sãmi (wuyan ba) sai azumin watanni biyu jẽre, dõmin tũba daga Allah. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kisan kuskure bãbu ƙisãsi a cikinsa, sai dai biyan diyya da kuma kaffãra. Amma biyan diyya yana kan dukkan dangin mai kisan, gwargwadon ƙarfin su, shi ɗaya ne daga cikin su. Idan danginsa ba su isa ba, ko kuwa bãbu su, to, sai baitulmãli na Musulmi ya biya. Ana biyan diyya a cikin shekaru huɗu. Ana bãyar da ita ga magãdan wanda aka kashe. Amma kaffãra ita kam a kan mai kisan kawai take a kan tartĩbinta. Wanda ya kashe bãwa bisa kuskure zai biya ƙĩmarsa ga mai shi, kuma ana son ya yi kaffãra."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 93,
            "translated_text": "Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci,* to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Yã yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azãba mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wanda ya kashe mũminai da ganganci, kuma yana ƙudurcin halaccin kashe shi ɗin, to, shi kãfiri ne. Amma idan yana ƙudurcin haramcin kisa, amma duk da haka ya kashe shi domin wata fã'ida ta dũniya, ko domin adãwa, to yana nan mũmini, hukuncinsa ƙisãsi. Surar Baƙara, ãya ta179."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 93,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi tafiya (a cikin ƙasa), dõmin jihãdi, to, ku nẽmi bãyani.* Kuma kada ku ce wa wanda ya jĩfa sallama zuwa gare ku: \"Bã Musulmi kake ba.\" Kunã nẽman hãjar rãyuwar dũniya, to, a wurin Allah akwai ganimõmi mãsu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabãnin ku musulunta, sa'an nan Allah Ya yi muku falala. Sabõda haka ku zan nẽman bayãni. Lalle ne Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin cewa ana ɗaukar wanda aka ji ya yi kalmar shahãda mumini, sai fa idan an ga ya yi wani aiki, ko aka ji ya yi wata magana wadda take warware ma'anar kalmar shahadar, bãbu kuma wani tãwĩli ko jãhilcin da yake iya zama uzuri ga mai shi."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 94,
            "translated_text": "Mãsu zama* daga barin yãƙi daga mũminai, wasun ma'abũta larũra da mãsu jihãdi a cikin hanyar Allah da dũkiyõyinsu da rãyukansu, bã su zama daidai. Allah Yã fĩfĩta mãsu jihãdi da dũkiyoyinsu da rãyukansu a kan mãsu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Yã yi musu alkawari da abu mai kyau.** Kuma Allah yã fĩfĩta mãsu jihãdi a kan mãsu zama da lãda mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Falalar mãsu jihãdi a kan waɗanda ba su jihãdi daga cikin muminai. Faɗar falalar tana ƙarfafa zukãta ga yin jihãdi domin tsaron addini da rãyukan mãsu rauni da dũkiyarsu. ** Aljanna."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 94,
            "translated_text": "Darajõji daga gare Shi da gãfara da rahama. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 94,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda malã'ĩku* suka karɓi rãyukansu, (alhãli) sunã mãsu zãluntar kansu, sun ce (musu): \"A cikin me kuka kasance?\" (Su kuma) suka ce: \"Mun kasance waɗanda aka raunana a cikin ƙasa.\" Suka ce: \"Ashe ƙasar Allah ba ta kasance mayalwaciya ba, dõmin ku yi hijira a cikinta?\" To, waɗannan makõmarsu Jahannama ce. Kuma tã mũnana ta zama makõma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hukuncin rashin hijira zuwa wurin yardar Allah dõmin tsayar da haƙƙõƙin Allah. Hukuncin mai dogewa ne, idan an sãmi dalĩlin yin hijirar, kuma bãbu abin da ya hana ta na uzurori."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 94,
            "translated_text": "Fãce waɗanda aka raunana daga maza da mãtã da yãra waɗanda bã su iya yin wata dabãra, kuma bã su shiryuwa ga hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 94,
            "translated_text": "To, waɗannan akwai tsammãnin Allah Ya yãfe laifi daga gare su, kuma Allah Yã kasance Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 94,
            "translated_text": "Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar* Allah, zai sãmu, a cikin ƙasa, wurãren jũyãwa mãsu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, lãdarsa tã auku ga Allah, Kuma Allah Yã kasance, a gare ku, Mai gãfara, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Yana kwaɗaitar da mũminai ga yin hijira zuwa wurin neman yardarsa. Hukuncin hijira yana nan a ko da yaushe hãli ya hukunta da a yi ta."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 94,
            "translated_text": "Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, bãbu laifi a kanku ku rage(5) daga salla idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku. Lalle ne kãfirai sun kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne.<br \/>\n____________________<br \/>\n(5) Rage salla a nan ba ana nufin sallar kasaru ta tafiya ba, wanda take ta tabbata da sunna. Wannan rage salla, shi ne sallar tsõro wadda ake yi gwargwadon hãlin da ake ciki na tsõro. Idan yana yiwuwa a yi ta da lĩmãmi, sai ya kasa jama'a kashi biyu, to, sai a yi kamar yadda ãya ta tafe zã ta yi bayãni, idan kuwa bã zai yiwu ba, sai a yi yadda hãli ya sauƙaƙa duka, kamar a ãyã ta 239 daga Suratul Baƙara."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 95,
            "translated_text": "Kuma idan kã kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su ta tsaya tãre da kai, kuma sai su riƙe makãmansu. Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga bãyanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tãre da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makãmansu. Waɗanda suka kãfirta sun yi gũrin dã dai kuna shagala daga makamanku da kãyanku dõmin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma bãbu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, kõ kuwa kun kasance mãsu jinya ga ku ajiye makãmanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Yã yi tattali, ga kãfirai, azãba mai walakantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 95,
            "translated_text": "Sa'an nan idan kun ƙãre salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan sãsanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla tã kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 95,
            "translated_text": "Kuma kada ku sassauta a cikin nẽman mutãnen idankun kasance kuna jin zõgi, to, lalle sũ ma, suna jin zõgi kamar yadda kuke jin zõgi. Kuma kuna tsammãni, daga Allah, abin da bã su tsammãni. Kuma Allah Yã kasance Masani Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 95,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ, Mun saukar,* zuwa gare ka, Littãfi da gaskiya, dõmin ka yi hukunci a tsakãnin mutãne da abin da Allah Ya nũna maka, kuma kada ka kasance mai husũma dõmin mãsu yaudara.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Gudãnar da hukunci a cikin mahakama, kada mai shari'a ya taimaki kowane sãshe, duk yadda suke a gare shi, sai ya ɗauke su daidai a gabansa, kamar yadda ya auku a gaban Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi. Wani mutum Musulmi ana ce masa Mat'ama bn Ubairak ya yi sãtar sulke ya ɓõye shi a wurin wani Bayahũde. A lõkacin da aka gãne sulken a wurin Bayahũden, sai Mat'ama ya yi masa ƙazafi da sãtarsa, shi kuma yayi rantsuwa cewa bã shi ne ya sãtã ba. Kuma mutãnensa suka rõƙi Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, dõmin ya yi musu jãyayya yakuɓutar da mat'ama, Annabi kuwa bai yarda ba. Kamar yadda ãyõyin nan suka bayyana, domin ya zama abin kõyi. Wannan kuma ya nũna cewa, ga gudanar da sharĩ'a Annabi yana yin ijtihãdi gwargwadon abin da ya bayyana daga hujjoji ya yi hukunci, kamar wajen shãwara a wurin yãki. Ya zama abin kõyi."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 96,
            "translated_text": "Kuma ka nẽmi Allah gãfara. Lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 96,
            "translated_text": "Kuma kada ka yi jãyayya dõmin tunkuɗe wa waɗanda suka yaudari kansu. Lalle ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai yawan hã'inci mai yawan zunubi."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 96,
            "translated_text": "Suna nẽman ɓõyewa daga mutãne kuma bã su nẽmanɓõyewa daga Allah, alhãli kuwa Shi Yana tãre da su a lõkacin da suke kwãna da niyyar yin abin da bã Ya yarda da shi daga maganar. Kuma Allah Yã kasance ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 96,
            "translated_text": "Gã ku, yã waɗannan*! Kun yi jidãli, dõmin tunkuɗe musu (kunya) a cikin rãyuwar dũniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Rãnar ¡iyãma? Ko kuwa wãne ne zai kasance wakĩli a kansu?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan yana nũna aikin lauya (Lawyer) dõmin ya taimaki marasa gaskiya sabõda ya kuɓuta harãmun ne, har dai idan zã a mayar da laifi ga wani barrantacce ko kuwa za a karɓe hakkin mai hakki a bai wa wanda bai cancanta da shi ba. Amma wakĩlin sharĩ'a yana halatta idan bai zama dõmin ɓõye gaskiya ba. Wakĩlai irin na zãmanin nan mãsu sanã'a da wannan, sũ ne karnukan dũniya na farautar haram dõmin su sha jini."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 96,
            "translated_text": "Kuma wanda ya aikata cũta kõ kuwa ya zãlunci kansa, sa'an nan kuma ya nẽmi Allah gãfara, zai sãmi Allah Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 96,
            "translated_text": "Kuma wanda ya yi tsirfanci zunubi, to yanã tsirfarsa ne a kan kansa kawai. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 96,
            "translated_text": "Kuma wanda ya yi tsiwirwirin kuskure ko kuwa zunubi sa'an nan kuma ya jẽfi wani barrantacce da shi, to, lalle ne yã tattali ƙirƙiren ƙarya da zunubi bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 96,
            "translated_text": "Kuma bã dõmin falalar Allah ba, a kanka, da rahamarSa, haƙĩƙa, dã wata ƙungiya daga gare su ta himmatu ga su ɓatar da kai. Kuma bã su ɓatarwa fãce kansu, kuma bã su cũtar ka daga kõme, Kuma Allah Yã saukar da Littãfi da hikima gare ka, kuma Ya sanar da kai abin da ba ka kasance kã sani ba. Kuma falalar Allah tã kasance mai girma a gare ka."
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 97,
            "translated_text": "Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu* fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hukuncin gãnawa da Annabi ko wani shũgaban jama'a mai tsayuwa matsayin Annabi ga gyãran sha'aninsu, bã ya halatta sai idan akwai wani alheri a ciki wanda amfaninsa zai shãfi jama'a duka."
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 97,
            "translated_text": "Kuma wanda ya sãɓã wa* Manzo daga bãyan shiriya tã bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar mũminai, zã Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙõne shi da Jahannama. Kuma tã mũnana ta zama makõma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Hana fassarar Alƙur'ãni ko sunnar Annabi, ba a kan hanyar da Annabi ko Sahabbansa da waɗanda suka bi hanyarsu suka fassara ba. Da mutum ya yi tãwilin Alƙur'ãni, gãra ya ce bai sani ba. Tãwĩlin Alƙur'ãni ko Hadĩsi da hankali yana kai ga bũɗe ƙõfar kãfirci ɓõyayye da yin hukunci da abin da Allah bai saukar ba. Na'am ba a hana ijtihãdi ga abin da ba a sãmi nassi a kansa ba, ko kuma aka sãmi nassi wanda bã bayyananne ba. Jingina ijtihãdi ga ra'ayi ya fi tãwĩlin abin da bai bayyana ba daga Alƙur'ãni ko Hadĩsi, domin ra'ayi ba ya ɓatar da wasu, amma tãwĩli yana ɓatarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 97,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace ɓata mai nĩsa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin shirki da hukunce-hukuncensa da abin da yake ratayuwa da shi. Sanin ma'anar shirki wajibi ne, dõmin a kan tauhĩdi ne aka gina shikãshikan Musulunci."
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 97,
            "translated_text": "Bã su kiran kõwa, baicin Shi, fãce mãtã kuma bã su kiran kõwa fãce Shaiɗan, mai tsaurin kai."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 97,
            "translated_text": "Allah Yã la'ane shi. Kuma ya ce: \"Lalle ne, zã ni riƙi rabõ yankakke,* daga bãyinKa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Rabon Shaiɗan daga kõwane dubu, shi ne ɗari tara da cas'in da tara kamar yadda aka ruwaito a cikin Hadĩsi."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 97,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne, inã ɓatar da su, kuma lalle ne inã sanya musu gũri, kuma lalle ne ina umurnin su dõmin su kãtse(5) kunnuwan dabbõbi, kuma lalle ne inã umurnin su dõmin su canza halittar Allah.\" Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙĩƙa yã yi hasara, hasara bayyananniya.<br \/>\n____________________<br \/>\n(5) Suna kãtse kunnuwan dabbõbi dõmin su nũna cewa na gumãkansu ne. Sunan mãtã shi ne ga duk abin da ba ya da rai, kamar watã itãtuwa duka mãtã ne. Canza halitta kamar tsãgen fuska da fãƙe haƙõra da karkarar gemu dõmin neman kyau, duka umurnin Shaiɗan ne."
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 97,
            "translated_text": "Yanã yi musu alkawari, kuma yanã sanya musu gũri, alhãli Shaiɗan bã ya yi musu wani wa'adĩn kõme face ruɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 97,
            "translated_text": "Waɗannan matattararsu Jahannama ce, kuma bã sãmun makarkata daga gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 98,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, zã mu shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada bisa ga wa'adin Allah tabbatacce. Wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga magana?"
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 98,
            "translated_text": "(Al'amari) bai zama gũrace- gũracenku ba, kuma* ba gũrace- gũracen Mutãnen Littãfi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki zã a sãka masa da shi kuma bã zai sãmi wani masõyi ba, baicin Allah, kuma bã zai sãmi mataimaki ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Addini bã tatsuniyar baki bane, aiki ne, ko mutum ya yi mugu ya shĩga Wuta, ko kuma ya yi na ƙwarai ya shiga Aljanna."
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 98,
            "translated_text": "Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhãli kuwa Yanã mũmini, to, waɗannan sunã shiga Aljanna kuma bã zã a zãlunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabĩ no ba."
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 98,
            "translated_text": "Kuma wãne ne ya fi kyau ga addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yanã mai kyautatawa kuma ya bi aƙidar Ibrãhĩm, Yanã mai karkata zuwa ga gaskiya? Allah Yã riƙi Ibrãhĩm badãɗayi.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Akwai kwaɗaitarwa ga cewa, wanda yake son Allah Ya so shi, to sai ya bi aƙĩda da aiki irin na Ibrãhĩma, sai Allah Ya so shi."
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 98,
            "translated_text": "Kuma Allah ke da* (mallakar) abin da ke cikin sammai da kuma abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã kasance, a dukkan, kõme, Mai kẽwayewa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ko da yake Allah Yã riƙi Ibrãhĩma \"Khalĩl\" watau masõyi, amma bai hana Ibrahĩma ya zama a cikin bãyin Allah kuma mulkinSa ba, domin yana daga cikin abin da sama da ƙasa suka ƙunsa a cikinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 98,
            "translated_text": "Sunã yi maka fatawa a cikin sha'anin mãtã. Ka ce: \"Allah Yanã bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantãwa a kanku a cikin Littãfi, a cikin sha'anin marãyun mãtã waɗanda ba ku bã su abin da aka rubũta musu* (na gãdo) ba, kuma kunã kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yãra, da sha'anin tsayuwarku ga marãyu da ãdalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yã kasance Masani a gare shi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* A cikin jahiliyya ba su bai wa yãra da mãtã gãdo. Musulunci ya sõke wannan al'ãda da ãyar gãdo, ãyã ta 11. Kuma idan akwai wata marainiya ga hannun wani tana da dũkiya, sai ya jefa mata mayafinsa domin ya hana ta auren wani namiji. Shi kuma ko ya aure ta ko kuma ya bar ta bãbu aure har ta mutu, su yi gãdonta."
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 99,
            "translated_text": "Kuma idan wata mace ta ji tsõron ƙiyo daga mijinta kõ kuwa bijirẽwa to, bãbu laifi a kansu su yi sulhu a tsakãninsu, sulhu (mai kyau) Kuma yin sulhu ne mafi alhẽri. Kuma an halartar wa rayũka yin rõwa. Kuma idan kun kyautata, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne, Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 129,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 99,
            "translated_text": "Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin* mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wajen so, bã zã a iya daidaita su ba, sai a daidaita ga kwãna da ciyarwa da wurin kwãna da tufãfi gwargwadon hãlin kõwace."
        },
        {
            "ayah_number": 130,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 99,
            "translated_text": "Kuma idan sun rabu, Allah zai wadãtar da kõwanne daga yalwarSa. Kuma Allah Yã kasance Mayalwaci, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 131,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 99,
            "translated_text": "Kuma Allah ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun yi wasiyya ga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku, da kũ, cẽwa ku bi Allah da taƙawa, kuma idan kun kãfirta, to, lalle ne, Allah Yanã da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa. Kuma Allah Yã kasance wadãtacce, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 132,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 99,
            "translated_text": "Kuma Allah ne da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa, kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli."
        },
        {
            "ayah_number": 133,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 99,
            "translated_text": "Idan Yã so, zã Ya tafi da ku, yã kũ mutãne! kuma Ya zo da wasu. Allah Yã kasance a kan haka, Mai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 134,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 99,
            "translated_text": "Wanda ya kasance* Yanã nufin sakamakon dũniya, to, a wurin Allah sakamakon dũniya da Lãhira yake. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Mai gani.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan shi ne ƙarshen wasiyya ga Yahũdu da Nasãra da kuma Musulmi kuma ma'anar wasiyya ĩta ce Allah Yã yi umurni da ku yi Masa ɗã'a amma bã domin Yana neman wani abu daga gare ku ba, domin bã zã ku ƙãra Masa mulki ba, dõmin shi ne da sammai da ƙasa da abin da ke tsakaninsu kũ kuma kuna cikinsu. Saboda haka neman ɗã'ar nan domin amfanin kanku ne."
        },
        {
            "ayah_number": 135,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 100,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida* sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyar da shaida da hukunce-hukuncen da suka rãtayu da shi. Bãyar da shaida amãna ce ta Allah daidai da tsaron dũkiyar amãna, ko mã ta fi tsanani, domin takan kai ga rai. Karkatar da magana, watau a faɗe ta bã yadda take ba. Bijirewa ita ce a ƙi bãyar da shaida."
        },
        {
            "ayah_number": 136,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 100,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni* da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni. To, wanda ya kãfirta da Allah da malã'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rãnar Lãhira, to, lalle ne yã ɓace, ɓata mai nĩsa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* ĩmãni da dukan rukunnan ĩmãni shida yana cikin tsaron amãna. Rukunnan ĩmãni su ne, ĩmãni da Allah da ManzanninSa, da malã'iku da LittattafanSa da Rãnar Lãhira da Ƙaddara."
        },
        {
            "ayah_number": 137,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 100,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sa'an nan kuma suka yi ĩmani, sa'an nan kuma suka kãfirta sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci, Allah bai kasance Yanã gãfarta musu ba, kuma bã zai shiryar da su ga hanya ba."
        },
        {
            "ayah_number": 138,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 100,
            "translated_text": "Ka yi wa munãfukai bushãra da cẽwa lalle ne sunã da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 139,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 100,
            "translated_text": "Waɗanda suke riƙon kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin sunã nẽman izza ne a wurinsu? To, lalle ne izza ga Allah take gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 140,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 100,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Yã sassaukar* muku a cikin Littãfi cẽwa idan kun ji ãyõyin Allah, anã kãfirta da su, kuma anã izgili da su, to, kada ku zauna tãre da sũ, sai sun shiga cikin wani lãbãri. Lalle ne kũ, a lõkacin nan misãlinsu kuke. Lalle ne, Allah Mai tãra munãfukai da kãfirai ne a cikin Jahannama gabã ɗaya.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A cikin Alƙur'ãni, sũratul An'ãm, ãyã ta 68."
        },
        {
            "ayah_number": 141,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 101,
            "translated_text": "Waɗanda suke jiran dãko game da ku; har idan wata nasara daga Allah ta kasance a gare ku, sai su ce: \"Ashe, ba mu kasance tãre da kũ ba?\" Kuma idan wani rabo ya sãmu ga kãfirai sai su ce: \"Ashe ba mu rinjãye ku ba, kuma muka tsare ku daga mũminai?\" To, Allah ne Yake yin hukunci tsakãninku a Rãnar ¡iyãma, kuma Allah bã zai sanya hanya ba ga kãfirai a kan mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 142,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 101,
            "translated_text": "Lalle ne munãfukai sunã yaudarẽwa da Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga salla, sai su tãshi sunã mãsu kasãla. Suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan."
        },
        {
            "ayah_number": 143,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 101,
            "translated_text": "Mãsu kai-kawo ne a tsakãnin wancan; bã zuwa ga waɗannan ba, kuma bã zuwa ga waɗannan ba. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã za ka sãmar masa wata hanya ba."
        },
        {
            "ayah_number": 144,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 101,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin, kanã nufin ku sanyã wa Allah dalĩli bayyananne a kanku?"
        },
        {
            "ayah_number": 145,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 101,
            "translated_text": "Lalle ne, manãfukai sunã a magangara mafi ƙasƙanci daga wuta. Kuma bã zã ka sãma musu mataimaki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 146,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 101,
            "translated_text": "Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka nẽmi fakuwa ga Allah, kuma suka tsarkake addininsu dõmin Allah, to, waɗannan sunã tãre da mũminai, kuma Allah zai bai wa mũminai lãda mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 147,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 101,
            "translated_text": "Mẽne ne Allah zai amfãna da yi maku azãba idan kun gõde, kuma kun yi ĩmãni? Allah Yã ksance Mai gõdiya Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 148,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 102,
            "translated_text": "Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana* fãce ga wanda aka zãlunta. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Magana mummũna. Allah bã Ya son bayyana mugunyar magana, sai dai wanda aka zãlunta, yana iya kai ƙãra, kuma yana iya yin addu'a a kan wanda ya zãlunce shi. Sa'an nan ya shiga bayyanãwar abin da ake nufi da miyagun maganganu a cikin ãyõyin da suke bin wannan."
        },
        {
            "ayah_number": 149,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 102,
            "translated_text": "Idan kun bayyana alhẽri, kõ kuwa kuka ɓõye shi, kõ kuwa kuka yãfe laifi daga cũta, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfewa, Mai ikon yi."
        },
        {
            "ayah_number": 150,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 102,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda uke kãfirta da Allah da ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe* a tsakãnin Allah da manzanninSa, kuma sunã cẽwa: \"Munã ĩmãni da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe.\" Kuma sunã nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Rarrabewa tsakãnin Allah da ManzanninSa, shi ne mutum ya ce ga misãli, \"Na yarda Allah gaskiya ne, zan yi duka abin da yake mai kyau saboda Shi, amma bãbu ruwãna da wani Annabi kõ wani manzõ,\" ko kuma ya ce ai duk addĩnai ɗaya ne, ana nufin Allah da su, sai mutum ya bi abin da ya ga dama. Duka irin waɗannan maganganu bã su da kyau, kãfirci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 151,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 102,
            "translated_text": "Waɗannan sũ ne kãfirai sõsai, kuma Mun yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai walãkantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 152,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 102,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma ba su rarrabe a tsakãnin kõwa ba daga gare su, waɗannan zã Mu bã su ijãrõrinsu, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 153,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 102,
            "translated_text": "Mutãnen Littãfi sunã tambayar ka ka saukar da wani littãfi daga sama, a kansu, to, lalle ne sun tambayi Mũsã mũfã girma daga wannan, suka ce: \"Ka nũna mana Allah bayyane.\" Sai tsãwa ta kãmã su sabõda zãluncinsu, sa'an nan kuma suka riƙi maraƙi (abin bautãwa) bãyan hujjoji bayyanannu sun je musu. Sa'an nan Muka yãfe laifi daga wancan. Kuma Mun bai wa Mũsã dalĩli bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 154,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 102,
            "translated_text": "Kuma Muka ɗaukaka dũtse sãma da su, sabõda alkawarinsu, kuma Muka ce musu: \"Ku shiga ƙõfar kunã mãsu tawãli'u,\" Kuma Muka ce musu: \"Kada ku ƙẽtare haddi a cikin Asabat,\" kuma Muka riƙi alkawari mai kauri daga gare su.\""
        },
        {
            "ayah_number": 155,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 103,
            "translated_text": "To, sabõda warwarẽwarsu ga alkawarinsu, da kãfirtarsu da ãyõyin Allah, da kisansu ga Annabãwa, bã da hakki ba, da maganarsu: \"Zukãtanmu sunã cikin rufi.\" Ã'a, Allah ne Ya yunƙe a kansu sabõda kãfircinsu, sabõda haka bã zã su yi ĩmãni ba fãce kaɗan."
        },
        {
            "ayah_number": 156,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 103,
            "translated_text": "Kuma sabõda kãfircinsu da faɗarsu, a kan Maryama, ƙiren ƙarya mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 157,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 103,
            "translated_text": "Da faɗarsu:* \"Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsã ɗan Maryama Manzon Allah,\" alhãli kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kẽre shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a garẽ su. Lalle ne waɗanda sauka sãɓã wa jũna a cikin sha'aninsa lalle ne, sunã shakka daga gare, shi, bã da wani ilmi fãce bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Faɗarsu ta izgili watau suna cewa: \"Mun kashe ĩsã ɗan Maryama wanda yake da'awar shi Manzon Allah ne.\" Asalin maganar Yahũdu suka karkatar da Dãwũda sarkin Dimashƙa, da cewa ga wani mutum nan yana ɓãta ƙasa da aƙĩdar mutãne a Baitil Maƙdis sabõda haka ya bãyar da õda ga hãkimansa a Baitil Maƙdis da a kashe ĩsã sai suka tafi suka tsare shi a cikin gida shi da sahabbansa, watau Hawãriyawa. ĩsã ya rõki waninsu da yarda da kisa a kan sakamakon Aljanna. Sai ƙaraminsu ya yarda, Allah Ya sanya masa sifar ĩsã, a bãyan haka Ya ɗauke ĩsã. Shi kuma aka kashe shi matsayin ĩsã. Daga nan,Yahũdu suna zaton sun kashe shi, kuma waɗanda suka halarci ƙissar, suka sãɓã wa jũna wajen sifar ĩsã da cewa Shi ne Allah, ko ɗan Allah, ko ɗayan uku, ko manzon Allah, kamar yadda ya gabãta a cikin Baƙara."
        },
        {
            "ayah_number": 158,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 103,
            "translated_text": "Ã'a, Allah Ya ɗauke shi zuwa garẽ Shi, kuma Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 159,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 103,
            "translated_text": "Kuma bãbu kõwa daga Mutãnen Littafi,* fãce lalle yanã ĩmãni da shi a gabãnin mutuwarsa, kuma a Rãnar ¡iyãma yana kasancẽwa mai shaida, a kansu.<br \/>\n____________________<br \/>\n* An ce Mutãnen Littafi na zamanin Annabi Isa lalle suna imani da shi gabanin mutuwarsa cewa shi ba Allah ne ba, kuma ba ɗan Allah ne ba; kowannensu kamin ya mutu yana imani da cewa Isa Manzon A1lah ne, a lokacin da imanin ba ya amfanin sa. Allah Ya fi sani."
        },
        {
            "ayah_number": 160,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 103,
            "translated_text": "To, sabõda zãlunci daga waɗanda suka tũba (Yahũdu) Muka haramta musu abũbuwa masu dãɗi waɗanda aka halatta su a gare su, kuma sabõda taushẽwarsu daga hanyar Allah da yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 161,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 103,
            "translated_text": "Da karɓarsu ga riba, alhãli kuwa an hana su daga gare ta, da cin su ga dũkiyar mutãne daƙarya. Kuma Muka yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 162,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 103,
            "translated_text": "Amma tabbatattu* a cikin ilmi daga gare su, da mũminai, suna ĩmani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, madalla da masu tsai da salla, da mãsu bãyar da zakka, da mãsu ĩmãni daAllah da Rãnar Lãhira. Waɗannan zã Mu bã su lãda mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kabĩla mai asali tana lãlãcewa sabõda rashin bin addini, har ta zama mafi sharrin halittar Allah, kamar Yahũdu. Kuma a cikin haka wanda ya komawa gaskiya sai ya koma ga tsohon asalin, ya ƙãra daukaka da shi, kamar waɗanda suka musulunta daga cikinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 163,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 104,
            "translated_text": "Lalle ne Mu, Mun* yi wahayi zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabãwa daga bãyansa. Kuma Mun yi wahayi zuwa ga Ibrãhĩma da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Yaƙũbu da jĩkõki da ĩsa da Ayũba da Yũnusa da Hãruna da Sulaimãn. Kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muhammadu bã shi ne farkon manzanni ba, kuma bã shi ne aka fãra yi wa wahayi ba, bã shi ne aka fãra bai wa Littãfi ba. Sai dai shi ne ƙarshensu ga dukkan waɗannan abũbuwa, kamar yadda bushãrarsu ta bayyana tun a gabãninsa. Kuma yawan Annabãwa da Manzanni bãbu wanda ya san shi sai Allah, wahayi shi ne ishãra ko yanda Allah ke aiko malã'iki da Manzanci zuwa ga wani Annabi ko Manzonsa."
        },
        {
            "ayah_number": 164,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 104,
            "translated_text": "Da wasu Manzanni, haƙĩ ƙa, Mun bã da lãbarinsu a gare ka daga gabãni, da wasu manzanni waɗanda ba Mu bã da lãbãrinsu ba a gare ka, kuma Allah Yã yi magana da Mũsã, magana sõsai."
        },
        {
            "ayah_number": 165,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 104,
            "translated_text": "Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin. Kuma Allah yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 166,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 104,
            "translated_text": "Amma Allah Yanã shaida da abin da Ya saukar zuwa gare ka. Yã saukar da shi da saninSa. Kuma malã'iku sunã shaida. Kuma Allah Yã isa Ya zama shaida."
        },
        {
            "ayah_number": 167,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 104,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka kange (wasu mutãne) daga hanyar Allah, haƙĩƙa, sun ɓace, ɓata mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 168,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 104,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta, kuma suka yi zãlunci, Allah bai kasance Yana yi musu gãfara ba, kuma bã Ya shiryar da su ga hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 169,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 104,
            "translated_text": "Fãce hanyar Jahannama, sunã mãsu dawwama a cikinta har abada, kuma wannan yã kasance, ga Allah, mai sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 170,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 104,
            "translated_text": "Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa, Manzo yã je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabõda haka ku yi ĩmãni yã fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kãfirta, to, Allah Yanã da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 171,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 105,
            "translated_text": "Yã Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafã a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, fãce gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yã jẽfa ta zuwa ga Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabõda haka, ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, \"Uku\". Ku hanu (daga faɗin haka) yã fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yã tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli."
        },
        {
            "ayah_number": 172,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 105,
            "translated_text": "Masĩhu bã ya ƙyãmar ya kasance bãwa ga Allah, kuma haka malã'ikun nan makusanta. Kuma wanda ya yi ƙyãmar bautarSa kuma yi yi girman kai, to, zai tãra su zuwa gare shi gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 173,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 105,
            "translated_text": "To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwaiai, to zã Ya cika musu ijãrõrinsu, kuma Yanã ƙãra musu daga falalarSa. Kuma amma waɗanda suka yi ƙyãma, kuma suka yi girman kai, to, zã Ya yi musu azãba, azãba mai raɗɗi kuma bã su samun wani masõyi dõmin kansu, baicin Allah, kuma bã su samun mataimaki."
        },
        {
            "ayah_number": 174,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 105,
            "translated_text": "Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa wani dalĩli daga Ubangijinku yã je muku kuma Mun saukar da wani haske, bayyananne zuwa gare ku."
        },
        {
            "ayah_number": 175,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 105,
            "translated_text": "To, amma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah kuma suka faku a gare Shi, to, zai shigar da su cikin wata rahama daga gare Shi da wata falala, kuma Ya shiryar da su zuwa gare Shi ga tafarki madaidaici."
        },
        {
            "ayah_number": 176,
            "surah_number": 4,
            "page_number": 106,
            "translated_text": "Sunã yi maka fatawa.* Ka ce: \"Allah Yanã bayyana muku fatawa a cikin 'Kalãla.\"' Idan mutum ya halaka, ba shi da, rẽshe kuma yana da 'yar'uwa, to, tana da rabin abin da ya bari, kuma shi yana gãdon ta, idan wani rẽshe bai kasance ba a gare ta. Sa'an nan idan ('yan'uwa mãtã) suka kasance biyu, to suna da kashi biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari. Kuma idan sun kasance, 'yan'uwa, maza da mãtã to namiji yana da misãlin rabon mãtã biyu. Allah Yana bayyanawa a gare ku, dõmin kada ku ɓace. Kuma Allah ne, Masani ga dukan kõme.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyan dõgon bayãni a kan tauhĩdin Allah, da kõrħwar shubhõhin yahũdu da nasãra a cikin addĩni, dõmin sai zũciya tã yarda da kaɗaitar Allah sa'annan zã ta ji ƙarfin riƙo da ƙarfin ɗauka ga hukunce-hukuncen da Allah Ya ke azã mata. To, yã kõma ne ga abin karantãwar sũrar na tsaron dũkiyã, ya rufe ta da shi. Ya yi magana akan mas'alar 'kalãla', watau, mutum ya mutu bai bar reshen sa ba, ko wani asali mai fukã-fukai kawai, watau 'yan uwa maza ko mãta waɗanda ba li'ummai ba. Maganã akan li'ummai kuwa tã gabãta a farkon sũra. Anã gabãtar da shaƙĩƙi a kan li'abi, kuma ana gabãtar da na kusa akan na nesa, mafi kusantar zumunta. Ana ƙiyasin baiwa 'yã'yã mãtã biyu, biyu daga uku na dũkiya akan 'yan uwa mãtã, dõmin su ba a ce fiye da biyu ba. Ɗiyar tsatso ta fi 'yar'uwa ƙarfin zumunta, kuma ta fi kusanci."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 106,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dãɗi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 106,
            "translated_text": "Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya, kuma da mãsu nufin ¦ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 107,
            "translated_text": "An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan fãsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 107,
            "translated_text": "Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: \"An halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi da abin da kuka sanar (farauta) daga mãsu yin mĩki, kunã mãsu sakinsu daga hannuwanku, kunã sanar da su daga abin da Allah Ya sanar da ku. To, ku ci daga abin da suka kama sabõda ku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawã ne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 107,
            "translated_text": "A yau an halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mãtã mãsu kãmun kai daga muminai da mãtã 'yã'ya daga waɗanda aka bai wa Littãfi* a gabãninku idan kun je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci, kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wãtau Yahudãwa da Kiristãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 108,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun tãshi* zuwa ga salla, to, ku wanke fuskõkinku da hannuwanku zuwa ga magincirõri, kuma ku yi shãfa ga kãnunku, kuma ku (wanke) ƙafãfunku zuwa idãnun sãwu biyu. Kuma idan kun kasance mãsu janaba, to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kõ kuwa a kan tafiya, kõ kuwa ɗaya daga gare ku ya zo daga kãshi, kõ kuka yi shãfayyar junã da mãtã, sa'an nan ba ku sãmi ruwa ba to ku yi nufin wuri** mai kyau, sa'an nan ku yi shãfa ga fuskõkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bã Ya nufi dõmin Ya sanya wani ƙunci a kanku, kuma amma Yanã nufi dõmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammãninku kunã gõdewa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Abin da ake halatta salla da shi ruwa mai tsarki domin ɗauke hadasi ƙarami da alwala, da hadasi babba da wanka. ldan bãbu ruwa a yi taimama da wuri na fuskar ƙasa wanda bai sãke ba da wata sana'ar mutum. Bauli da wadiyyi da kãshi da tusa da shãfar jin dãɗi na namiji ga mace ko mace ga namiji, da shafar zakarin kansa, duka suna wajabtar da alwalla. Fitar maniyyi da haila suna wajabtar da wanka. Maziyyi na wajabtar da wanke dukkan zakari sa'an nan a yi alwalla. Yankan hannun ɓarãwo yã nuna iyakar inda ake shãfar farilla na taimama, da sunna, kamar yadda ake yin sauran ayyuka duka a kan ƙiyãsinsu bisa ga wasu.** Wãtau ku yi taimama."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 108,
            "translated_text": "Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku da alkawarinku wanda Ya ɗaure ku da shi, a lõkacin da kuka ce: \"Mun ji kuma mun yi ɗã'a Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne ga abin da ke a cikin zukata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 108,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayin daka dõmin Allah mãsu shaida da ãdalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bã zã ku yi ãdalci ba. Ku yi ãdalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 108,
            "translated_text": "Allah Yã yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Sunã da wata gãfara da lãda mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 109,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryatã, game da ãyõyinMu, waɗannan su ne abõkan wuta."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 109,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku* sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan kiyãyewa ya auku a wurãre da yawa tun Musulmi suna da rauni kuma kãfirai suna da ƙarfi, kuma suna son su kashe Musulmi da Musulunci. Allah Ya tsare su. Saboda haka yanzu da Musulmi suka yi ƙarfi da ƙarfin Allah, yã wajaba a kansu su godewa Allah da taƙawa. Watau su riƙe alkawarin Allah, su yi abin da Ya aza musu gwargwadon hãli."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 109,
            "translated_text": "Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu* daga gare su kuma Allah Ya ce: \"Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * An ayyana wakilai goma shabiyu daga ƙabĩlun Bani Isrãĩla goma sha biyu domin su ɗaukar musu alkawari daga wurin, kuma su tsare mutãnensu ga ganin ba a sãɓa wa alkawarin ba. An gina addinin Bani Isrãĩla a kan ƙabĩlanci. Saboda haka addininsu bã ya fita daga dã'irarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 109,
            "translated_text": "To, sabõda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukãtansu ƙeƙasassu, sunã karkatar da magana daga wurãrenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, kuma bã zã ka gushe ba kana tsinkãyar yaudara daga gare su fãce kaɗan daga gare su. To, ka yãfe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 110,
            "translated_text": "Kuma daga waɗanda suka ce: \"Lalle ne mu Nasãra ne\" Mun riƙi alkawarinsu, sai suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka shushuta adãwa da ƙeta a tsakãninsu har ya zuwa ga Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah zai bã su lãbari da abin da suka kasance sunã sanã'antawa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 110,
            "translated_text": "Yã Mutãnen littãfi! Lalle ne, ManzonMu yã je muku, yanã bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kunã ɓõyewa daga Littãfi, kuma yanã rangwame daga abu mai yawa. Haƙĩƙa, wani haske da wani Littafi mai bayyanãwa yã je muku daga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 110,
            "translated_text": "Dashĩ, Allah Yanã shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyõyin aminci, kuma Yanã fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yanã shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 110,
            "translated_text": "Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: \"Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama,\" sun kãfirta. Ka ce: \"To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yã nufi Ya halakar da Masĩhu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabã ɗaya?\" Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, Yanã halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 111,
            "translated_text": "Kuma Yahudu da Nasãra sun ce: \"Mu ne ɗiyan Allah, kuma masõyansa.\" Ka ce: \"To, don me Yake yi muku azãba da zunubanku? Ã'a ku mutãne ne daga waɗanda Ya halitta, Yanã gãfartãwa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so. Kuma Allah ne da mulkin sammai da ƙasa da abin da ke tsakãninsu kuma zuwa gare shi makomã take.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 111,
            "translated_text": "Yã Mutãnen Littãfi! Lalle ManzonMu yã je muku yanã bayyana muku, a kan lõkacin fatara daga manzanni, dõmin kada ku ce: \"wani mai bayar da bushãra bai zo mana ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba.\" To, haƙĩƙa, mai bãyar da bushãra da mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 111,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Musa ya ce wa mutãnensa: \"Yã ku mutãnena! Ku tuna ni'imar Allah a kanku; dõmin Yã sanya annabãwa a cikinku, kuma Yã sanya ku sarãkuna, kuma Yã bã ku abin da bai bai wa kõwa ba daga tãlikai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 111,
            "translated_text": "\"Yã mutãnena! Ku shiga ƙasar nan, abar tsarkakewa, wadda Allah Ya rubuta sabõda ku, kuma kada ku kõma da bãya, har ku juya kunã mãsu hasara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 111,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ya Musã! Lalle ne, a cikinta akwai wasu mutãne mãsu ƙarfi kuma lalle ne bã zã mu shige ta ba sai sun fice daga gare ta, to, idan sun fice daga gare ta, to, lalle ne mu, masu shiga ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 111,
            "translated_text": "Wasu maza biyu* daga waɗanda suke tsõron Allah, Allah Yã yi ni'ima a kansu, suka ce: \"Ku shiga gare su, daga ƙõfar, dõmin idan kuka shige shi, to, lalle ne ku, mãsu rinjãya ne, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Maza biyu su ne Yusha'u da Kãlib daga Nuƙabã'u, watau wakilai goma sha biyu waɗanda Annabi Musã ya aike su domin su yiwo binciken hãlãyen mutanen da suke zaune a cikin Ƙudus. Yadda ya fãru shi ne, bãyan da Allah Ya halaka Fir'auna sai Bani Isrã'ĩla suka koma Masar, daga nan sai Allah Ya rubuta musu cewa su tashi su koma Ariha'a, a cikin ƙasar Sham alhãli mazaunanta kuwa Kan'aniyyawa ne. Sai Musã ya gaya musu cewa, ga ƙasar da Allah Ya bã su, su fitar da waɗanda ke a ciki su zauna. Musã ya aika da mutum goma sha biyu domin su yiwo leƙen asiri su zo masa da lãbãri, kada su gaya wa mutãne abin da suka gani domin kada su firgita. Bayan da suka kõmo, sai suka warware alkawarin; sai mutum biyu daga cikin su, Yusha'u da Kãlib."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 112,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ya Musa! Lalle ne mu, bã za mu shige ta ba har abada matuƙar sun dawwama a cikinta sai ka tafi kai da Ubangijinka dõmin ku yi yãƙi. Lalle ne mu, munã a nan zaune.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 112,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, bã ni mallakar kõwa fãce kaina da ɗan'uwãna, sai Ka rarrabe a tsakãninmu da tsakãnin mutãne fãsiƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 112,
            "translated_text": "(Allah) Ya ce: \"To, lalle ne ita abar haramtãwa ce a gare su, shekara arba'in, sunã yin ɗimuwa a cikin ƙasa*. Sabõda haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne fãsiƙai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan shi ne sakamakon sãɓawar alkawari, da aka ce wa magewaya kada su faɗi abin da suka gani, saboda aƙibar abin, kusan duka sai da suka mutu a cikin halin ɗimuwar."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 112,
            "translated_text": "Kuma karantã musu* lãbãrin ɗiya biyu** na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: \"Lalle ne zan kashe ka.\" (¦ayan kuma) ya ce: \"Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ƙuraishawa ko kuwa al'ummarka. ** Ɗiyan Ãdamu, biyu, Ƙãbĩla da Hãbĩla. Asalin maganar kamar yadda aka ruwaito, mãtar Ãdamu, Hauwa'u, tana haifuwar namiji da mace a kowane ciki, wajen aure sai a shirɓata dõmin bãbu wasu mutãne sai su. Sai Ƙabĩla ya ƙi yarda a bai wa Hãbĩla 'yar'uwarsa, har Ãdam ya sanya su yin baiko da abin sana'arsu. Ƙãbĩla manõmi ne, ya bãyar da munãna daga kãyan nõmansa, shi kuma Hãbĩla ya bãyar da rãgo mai kyau dõmin sana'arsa kiwo ne. Sai wuta ta sauko ta ɗauki rãgon Hãbĩla, alãmar karɓa. Wannan kuwa ya ɗauki Ƙãbĩla ga tunãnin kashe shi. Laifi guda yana sabbaba wasu laifuka mãsu yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 112,
            "translated_text": "\"Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dõmin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah Ubangijin tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 112,
            "translated_text": "\"Lalle ne nĩ inã nufin ka kõma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance daga abõkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 112,
            "translated_text": "Sai ransa ya ƙawãtar masa kashewar ɗan'uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa'an nan ya wayi gari daga mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 112,
            "translated_text": "Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gãwar ɗan'uwansa. Ya ce: \"Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan'uwana?\" Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 113,
            "translated_text": "Daga sababin wannan,* Muka rubuta a kan Banĩ lsrã'ĩla cewa, lalle ne wanda ya kashe rai bã da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yã kashe mutãne duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã ɗaya. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, ManzanninMu sun je musu da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, mãsu yawa daga gare su, a bãyan wannan, haƙĩƙa, mãsuɓarna ne a cikin ƙasa.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Aikata ƙaramin laifi yana sabbaba babban laifi har ɓarna mai yawa ta wãtsu a cikin ƙasa."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 113,
            "translated_text": "Abin sani kawai sakamakon* waɗanda suke Yãƙin Allah da Manzonsa, kuma sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna a kashe su ko kuwa a ƙere su, kõ kuwa a kakkãtse hannuwansu da ƙafãfunsu daga sãɓãni, ko kuwa a kõre su daga ƙasa. Sannan gare su wulakanci ne a cikin rãyuwar duniya, kuma a Lãhira sunã da wata azãba mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Muhãrib shi ne ɗan fashi mai tare hanya da makamai. Ana yi masa ɗayan abin da aka ga yã dãce da shi. Wanda aka yi wa \"Salbu\" sai kuma a kashe shi. Amfanin Salbu shi ne a gan shi, dõmin hankalin mutãne ya natsu. Korewa yanzu sai ta koma ga ɗauri har ya mutu ko ya tuba."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 113,
            "translated_text": "Fãce fa waɗanda suka tuba tun a gabãnin ku sãmi ĩko akansu, to, ku sani cewa lalle ne, Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 113,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihãdi* a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wasĩla ita ce dukkan aikin ibãda wanda zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangijinsa, amma da sharaɗin an gina shi a kan taƙawa. Kuma taƙawa ita ce bin Allah kamar yadda Ya yi umurni a bi Shi, ta hanyar manzonSa kawai. Jihãdi yana cikin taƙawa amma Yã kõma ambatonsa ne domin muhimmancinsa. Shi kuma iri biyu ne: ƙararmi, watau yãƙin abokan gãbã na bayyane, da babba, shi ne yãƙin abokan gãbã na ɓoye, watau rai da shaiɗan. Wanda maƙiyinsa na bayyane ya kashe shi yã mutu shahĩdi, wanda maƙiyinsa na ɓoye ya kashe shĩ ya mutu fãsiƙi ko kãfiri watau shaƙiyyi."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 113,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta, lalle dã sunã da abin da ke a cikin ƙasa gabã ɗaya da misãlinsa tãre da shi, dõmin su yi fansa da shi daga azãbar Rãnar ¡iyãma, bã a karɓarsa daga gare su, kuma sunã da azãba mai raɗadi."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 114,
            "translated_text": "Sunã nufin su fita ne daga wuta, kuma ba su zama mãsu fita daga gare ta ba, kuma sunã da azãba zaunanniya."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 114,
            "translated_text": "Kuma ɓarãwo da ɓarauniya sai ku yanke hannuwansu, bisa sakamako ga abin da suka tsirfanta, a kan azãba daga Allah. Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 114,
            "translated_text": "To, wanda ya tuba a bãyan zãluncinsa, kuma ya gyãra (halinsa), to, lalle ne Allah Yanã karɓar tubarsa. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 114,
            "translated_text": "Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin sammai da ƙasa, Yanã azãbtar da wanda Yake so, kuma Yanã yin gãfara ga wanda yake so, kuma Allah a dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 114,
            "translated_text": "Yã kai Manzo! Kada waɗanda suke tseren gaugawa a cikin kãfirci su ɓãta maka rai, daga waɗanda suka ce: \"Mun yi ĩmãni\" da bãkunansu, alhãli zukatansu ba su yi ĩmãnin ba, kuma daga waɗanda suka tuba (watau Yahudu) mãsu yawan saurare ga wasu mutane na dabam waɗanda ba su je maka ba, sunã karkatar da zance daga bãyan wurarensa, sunã cewa: \"Idan an bã ku wannan, to, ku karɓa, kuma idan ba a bã ku shĩ ba, to, ku yi sauna.\"Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bã zã ka mallaka masa kõme ba, daga Allah. Waɗannan ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukãtansu ba. Sunã da kunya a cikin duniya, kuma sunã da wata azãba mai girma a cikin ãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 115,
            "translated_text": "Mãsu yawan saurãre* ga ƙarya ne, mãsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka, sai ka yi hukunci a tsakãninsu kõ ka bijira daga gare su. Kuma idan ka bijira daga gare su, to, bã zã su cuce ka da kõme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai ka hukunta a tsakãninsu da ãdalci. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu ãdalci.<br \/>\n____________________<br \/>\n* An bai wa Annabi zaɓi da ya yi hukunci ko kada ya yi, a tsakãnin kafirai biyu idan sun yarda da hukuncinsa. Wannan dãmã tana aiki a kotunan Musulmi ga abin da ya shafi haƙƙoƙi kawai, amma ga 'jara'im a ƙasar Musulmi tilas sai a bi shari'ar Musulunci domin tsaron aminci, sai dai kafiri yana iya shan giyarsa, ga misãli a ɓoye banda a cikin jama'a. Haka kuma laifuka na al'adunsu kuma Musulmi bã za su taɓa masu su ba, sai su yi hukuncinsu a tsakãninsu."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 115,
            "translated_text": "Kuma yãya suke gabãtar da kai ga hukunci, alhãli a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sunã karkacewa a bãyan wannan? waɗannan bã muminai ba ne!"
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 115,
            "translated_text": "Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabãwa waɗanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da mãlaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littãfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, mãsu bã da shaida. To, kada ku ji tsõron mutãne kuma ku ji tsõroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyoyiNa. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 115,
            "translated_text": "Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (anã kashe) rai sabõda rai, kuma (anã ɗebe) idõ sabõda idõ, kuma (ana katse) hanci sabõda hanci, kuma kunne sabõda kunne kuma haƙori sabõda haƙõri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya yi sadaka da shi, to, shi kaffãra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 116,
            "translated_text": "Kuma Muka biyar a kan gurãbansu da Ĩsa ɗan Maryama, yãnã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma Muka bã shi Injĩla a cikinsa akwai shiriya da haske, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 116,
            "translated_text": "Kuma sai mutãnen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 116,
            "translated_text": "Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a kansa. sai ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyiniu daga abin da ya zo maka daga gaskiya.* Ga kõwanne daga gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta). Kuma dã Allah Yã so, dã Yã sanya ku al'umma guda, kuma amma dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku. Sai ku yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã sãɓãwa a cikinsa.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Allah. Kuma Mun bai wa kowa shari'õ'insa da dõkõkinsa sa'an nan kuma da hanyar da ake bi wajen zartar da shari'ar."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 116,
            "translated_text": "Kuma ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyinsu, kuma ka yi saunar su fitine ka daga sãshen abin da Allah Ya saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya bãya, to, ka sani cewa, kawai Allah yana nufin Ya sãme su da masĩfa ne sabõda sãshen zunubansu. Kuma lalle ne, mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, fãsiƙai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 116,
            "translated_text": "Shin, hukuncin Jãhiliyya* suke nema? Kuma wane ne mafi kyau ga hukunci daga Allah sabõda mutãne waɗanda suke yin yaƙĩni (tabbataccen ĩmãni)?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hukuncin Jahiliyya shi ne wanda ake ginawa a kan son rai da al'ãda da kuma ra'ayin azzalumai, ba ya da wani asali daga wani littafi na Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 117,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasãra majiɓinta. Sãshensu majiɓinci ne ga sãshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 117,
            "translated_text": "Sai ka ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta, sunã tseren gaugawa a cikinsu, sunã cewa: \"Munã tsõron kada wata masĩfa ta sãme mu.\" To, akwai tsammãnin Allah Ya zo da buɗi, kõ kuwa wani umurni daga wurinSa, har su wãyi gari a kan abin da suka ɓõye a cikin zukatansu, sunã mãsu nadãmã."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 117,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cewa: \"Shin, waɗannan ne waɗanda suka yi rantsuwa da Allah iyãkar rantsuwõyinsu, cewa su, lalle sunã tãre da ku?\" Ayyukansu sun ɓãci, sabõda haka suka wãyi gari sunã mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 117,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to, Allah zai zo da wasu mutãne, Yanã son su kuma sunã son Sa, mãsu tawãlu'i a kan muminai mãsu izza a kan kãfurai. Sunã yin, jihãdi a cikin hanyar Allah, kuma bã su tsõron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 117,
            "translated_text": "Abin sani kawai, majiɓincinku Allah ne da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmãni, waɗanda suke sunã tsayar da salla kuma sunã bãyar da zakka kuma sunã ruku'i,"
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 117,
            "translated_text": "Kuma wanda ya jiɓinci Allah da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmãni, to, ƙungiyar Allah sune mãsu rinjãya."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 117,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi waɗanda suka riƙi addininku bisa izgili da wãsa, daga waɗanda aka bai wa Littãfi daga gabãninku da kãfirai, masõya, Kuma ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 118,
            "translated_text": "Kuma idan kuka yi kira zuwa ga salla, sai su riƙe ta bisa izgili da wãsa. Wannan dõmin lalle ne su, mutãne ne (waɗanda) bã su hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 118,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ya Mutãnen Littãfi! Shin, kunã ganin wani laifi daga gare mu? Fãce dai dõmin mun yi ĩmãni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar daga gabãni, kuma dõmin mafi yawanku fãsiƙai ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 118,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dõmin sakamako* daga wurin Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ¦ãguta. Waɗannan ne mafiya sharrin wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kunã son in gaya muku ba dõmin ku bã ni wani sakamako ba, sai dõmin Allah Ya sãkã mini. Mutãnen da aka jũyar suka kõma birai da aladai kuma suka bauta wa wanin Allah, su ne mafi sharrin mutãne."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 118,
            "translated_text": "Kuma idan sun zo muku sai su ce: \"Mun yi ĩmãni.\" Alhãli kuwa haƙĩƙa, sun shigo da kãfirci, kuma su lalle ne, sun fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da suka kasance sunã ɓõyewa."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 118,
            "translated_text": "Kuma kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã tseren gaugawa a cikin zunubi da zãlunci da cinsu ga haram. Haƙĩƙa, tir da abin da suka kasance suna aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 118,
            "translated_text": "Don me Malaman Tarbiyya* da manyan malamai (na Yahudu) ba su hanã su daga faɗarsu ga zunubi da cinsu ga haram ba? Haƙiƙa, tir daga abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Don me malamansu bã su yin wa'azi ga jãhilansu? Tir da rashin wa'azi!."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 118,
            "translated_text": "Kuma Yahudu suka ce: \"Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne.* \" An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka faɗa. Ã'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yanã ƙãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma Mun jefa a tsakãninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rãnar ¡iyãma, kõ da yaushe suka hura wata wuta dõmin yãƙi, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Suna nufin wai Allah marowaci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 119,
            "translated_text": "Kuma dã dai lalle Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, kuma sun yi taƙawa, haƙĩƙa, dã Mun kankare miyãgun ayyukansu daga gare su, kuma dã Mun shigar da su gidãjen Aljannar Ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 119,
            "translated_text": "Kuma dã dai lalle su, sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, haƙĩƙa, dã sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin ƙafãfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaitãwa kuma mãsu yawa daga gare su, abin da suke aikatawa yã munana."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 119,
            "translated_text": "Yã kai Manzo! Ka iyar da* abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba ke nan. Kuma Allah Yanã tsare ka daga mutãne. Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ãya tã kãfirta dukan wanda ya ce kõ yã yarda da cewa Annabi yã ɓõye wani abu daga Allah, ko kuma yã keɓe wasu mutãne da wani abu daga manzancinsa daga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 119,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã ku Mutãnen Littãfi! Ba ku zama a kan kõme ba, sai kun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku.\"Kuma lalle ne, abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, yanã ƙara wa mãsu yawa daga gare su girman kai da kãfirci. To, kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 119,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda sukatuba (Yahũdu) da Karkatattu da Nasãra, wanda ya yi ĩmãni da Allahda Rãnar Lãhira, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su zamo sunã baƙin ciki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 119,
            "translated_text": "Lalle ne haƙĩƙa Mun riƙi alkawarin Bani Isrã'ĩla, kumaMun aiki manzanni zuwa gare su, ko da yaushe wani manzo ya je musu da abin da rãyukansu bã su so, wani ɓangare sun ƙaryata, kuma wani ɓangare sunã kashewa,"
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 120,
            "translated_text": "Kuma suka yi zaton cewa wata fitina bã zã ta kasance ba sai Suka makanta, kuma suka kurubta, sa'an nan Allah Ya karɓi tuba a gare su, sa'an nan suka makanta kuma suka kurunta mãsu yawa daga gare su, alhãli Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 120,
            "translated_text": "Lalle ne haƙĩƙa waɗanda* suka ce: \"Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama,\" sun kãfirta. Alhãli kuwa Masĩhu yã ce: \"Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku.\" Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Su ne Ya'aƙũbiyya, Bãyan bayãni a kan aibõbin Yahũdu sai Ya shiga bayãni a kan aibõbin Nasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 120,
            "translated_text": "Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: \"Allah na ukun uku ne,\" sun kãfirta, kuma babu wani abin bautãwa fãce Ubangji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke faɗa ba, haƙĩƙa, wata azãba mai raɗaɗi tãnã shãfar waɗanda suka kãfirta daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 120,
            "translated_text": "shin fã, bã su tuba zuwa ga Allah, kuma su neme Shi gãfara, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?"
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 120,
            "translated_text": "Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabãninsa, kuma uwarsa siddika* ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ãyõyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Siddĩƙ shi ne mai yawan gaskatãwar Annabãwa, shi ne mafi ɗaukakar daraja a waliyyan Allah, kamar Abubakar siddĩƙ Sahãbin Annabi."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 120,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ashe kunã bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta sabõda ku kuma haka wani amfani* alhãli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Idan bauta wa Ĩsã, Annabin Allah ya zama kãfirci bauta wa waliy yã zama shirka kenen. Kuma idan Ĩsã bai mallaki kõme ba, to, waliyyi mene ne matsayinsa?."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 120,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã ku Mutanen Littãfi! Kada ku zurfafa a cikin addininku, abin da bã gaskiya ba, kuma kada ku bĩbiyi son zuciyõyin waɗansu mutãne waɗanda suka riga suka ɓace a gabãni, kuma suka ɓatar da wasu mãsu yawa, kuma suka ɓace daga tsakar hanya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 121,
            "translated_text": "An la'ani waɗanda suka kãfirta daga Banĩ Isrã'ĩla a kan harshen Dãwuda da Ĩsa ɗan Maryama. wannan kuwa sabõda sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'addi.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ta'addi shĩ ne ƙetare iyãka da nufin zãlunci."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 121,
            "translated_text": "Sun kasance bã su hana juna daga abin ƙi, wanda suka aikata. Haƙĩƙa abin da suka kasancesunã aikatãwa yã munana."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 121,
            "translated_text": "Kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã jiɓintar waɗanda suka kãfirta. Haƙĩƙa tir da abin da rãyukansu suka gabãtar sabõda su, watau Allah Yã yi fushi da su, kuma a cikin azãba su mãsu dawwama ne"
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 121,
            "translated_text": "Kuma dã sun kasance sunã ĩmãni da Allah da Annabi da abin da aka saukar zuwa gare shi, dã ba su riƙe su masõya ba. Kuma amma mãsu yawa daga gare su, fãsiƙai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 121,
            "translated_text": "Lalle ne kana sãmun mafiya tsananin mutãne a adãwa ga waɗanda suka yi ĩmãni, Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kanã sãmun mafiya kusantarsu a sõyayya ga waɗanda suka yi ĩmãni su ne waɗanda suka ce: \"Lalle mu ne Nasãra.\" Wancan kuwa sabõda akwai ¡issawa da ruhubãnãwa* daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bã su yin girman kai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ƙissĩsi shĩ ne lĩmãnin kiristãwa, ruhubãnanci shĩ ne mutum ya tsabbace daga mutãne dõmin ibãda, kuma ba ya yin aure. Baruhubãne guda, ruhubãnãwa jam'i."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 121,
            "translated_text": "Kuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kanã ganin idanunsu sunã zubar da hawãye, sabõda abin da suka sani daga gaskiya, sunã cewa: \"Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai ka rubuta mu tãre da mãsu shaida."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 122,
            "translated_text": "\"Kuma mene ne yake gare mu, bã zã mu yi ĩmãni daAllah ba, da kuma abin da ya zo mana daga gaskiya, kuma munã gurin Ubangijinmu Ya shigar da mu tãre da mutãne sãlihai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 122,
            "translated_text": "Sabõda haka, Allah Yã sãkã musu, dõmin abin da suka faɗa da gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu, kuma wannan ne sakamakon mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 122,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗancan ne abõkan Wuta."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 122,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku haramta abubuwa mãsu dãɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bã Ya son mãsu ƙetare haddi.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Haramta abin da Allah Ya halatta kõ kuwa halatta abin da Allah Ya haramta kãfirci ne, dõmin wanda ya ƙetare haddi da kansa, yã yi da'awar Ilãhiyya kõ Annabci, haka wanda ya bi shi a kan wannan abin, ya yi shirki da Allah, dõmin yã sãmi wani mai waɗansu dõkõki wanda bã Allah ba, kuma ya bi shi a kansu, ko kuwa ya bi wani mai da'awar annabci, bãyan Alƙur'ãni yã ce an rufe annabci daga Annabi Muhammadu, tsĩra da amincĩ su tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 122,
            "translated_text": "Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake ku, mãsu ĩmãni ne da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 122,
            "translated_text": "Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa* a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa 'yantãwar wuya. Sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Rantsuwa alkawari ce da sunãn Allah, cewa mai rantsuwar zai aikata ko kuwa bã zai aikata ba, kõ kuwa a kan tabbatar wani abu a kan sifar da ya ambata, kõ kuwa kõruwarsa daga wannan sifar. Wanda ya yi rantsuwa sa'an nan ya yi hinsi, to, sai ya yi kaffãra, kamar yadda aka ambata a cikin ãyar. Sai fa idan ta zama yãsassar rantsuwa ce, wadda mutum ya yi a kan saninsa, sa'an nan sanin nan ya warware, sabõda bayyanar wani abu. Wasu sun ce ita ce rantsuwar da ake yi a cikin magana bã da nufi ba, kamar ã'a wallãhi, ko ĩ, wallãhi. Kuma akwai rantsuwar gamusa a kan ƙarya. Ita ma bãbu kaffãra sabõda ita, sai tuba zuwa ga Allah da istigfãri, kuma tanã sanya tsiya."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 122,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a*, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yin cãca da shan giya da refu da kiban ƙuri'a, aikatar da su warware alkawari ne na hana cin dukiyar mutãne da bãɗi1i (ƙarya), da tsaron salla da Allah Ya yi umurni a tsare; watau rashin taƙawa ke nan."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 123,
            "translated_text": "Abin sani kawaĩ Shaiɗan yanã nufin ya aukar da adãwa da ƙeta a tsakãninku, a cikin giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 123,
            "translated_text": "Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo, kuma ku kiyãye. To, idan kun jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, iyarwa bayyananniya."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 123,
            "translated_text": "Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata*. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yã maimaita faɗin taƙawa sau uku ga wanda ya tuba da shan giya da cãca dõmin ya nuna nauyinsu. Wanda ya shã giya kõ ya yi cãca, yã keta haddin Allah da alfarmar mutãne da darajar kansa. Sai yã yi taƙawa daga waɗannan zai iya rabuwa da su. Tsare su yanã cikin cika alkawari a tsakãnin mutum da Allah da kuma mutãne da ransa."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 123,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 123,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama*. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Barin farauta a cikin Harami yanã a cikin cikãwa da alkawari. Wanda ya sãɓa, sai ya yi fansa da biyan misãlin abin da ya kashe daga dabbõbin gida na jin dãɗi; watau a biya barewa da akuya kõ tunkiya. Amma kuma sai an sãmi mutum biyu ãdalai sun hukunta abin da mutum zai bayar ɗin. Idan bã Ya da dabbar, sai ya biya ƙĩmarta da abinci, ya bai wa kõwane miskĩni ɗaya mudu guda. Idan bã ya iyãwa kuwa sai ya yi azumi, kõwane mudu guda kwãna ɗaya, guntun mudu a biya shi da cikakken kwãna."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 124,
            "translated_text": "An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dõmin jin dãɗi a gare ku, kuma dõmin matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama mãsu harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tãra ku."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 124,
            "translated_text": "Allah Ya sanya Ka'aba ¦aki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane, kuma Yã sanya watã Mai alfarma da hadaya da rãtayõyin Allah Yã san abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma cewa lalle Allah, ga dukkan, kõme, Masani* ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Dõmin ku san haka kuma ku himmatu ga tsare alkawurranSa."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 124,
            "translated_text": "Ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne, kuma lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 124,
            "translated_text": "Bãbu abin da yake a kan Manzo, sai iyarwa, kuma Allah Yanã sanin abin da kuke bayyanãwa da abin da kuke ɓõyewa."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 124,
            "translated_text": "Ka ce: \"Mummuna da mai kyau bã su daidaita, kuma kõ dã yawan mummuan yã bã ka sha'awa. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abuta hankula ko la'alla zã ku ci nasara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 124,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku (hukuncinsu) su ɓãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lõkacin* da ake saukar da Alƙur'ãni, zã a bayyana maku. Allah Yã yãfe laifi daga gare su, Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan lõkacin yã nuna shiɗai ne lõkacin saukar hukunci kõwane iri ne daga Allah. Wanda ya ce Annabi yã faɗa masa wani hukunci a kan wata matsala, bãyan rasuwarsa, tsĩra da aminci su tabbata gare shi, to, bã zã a karɓar masa ba, dõmin yã sãɓã wa nassin Alƙur'ãni. Kuma mafarki bã ya zama hujja, balle a ɗauke shi hukunci wanda ake yin aiki da shi. Mafarkin Annabãwa ko mafarkin da Annabãwa suka tabbatar shi ne gaskiya, saura kuma sai abin da ya bayyana, kuma bai sãɓã wa sharĩa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 124,
            "translated_text": "Lalle ne wasu mutãne sun tambaye su daga gabãninku, sa'an nan kuma suka wãyi gari da su sanã kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 124,
            "translated_text": "Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka sã'iba, kuma haka wasĩla, kuma haka hãmi*, amma waɗanda suka kãfirta, su suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma mafi yawansu bã su hankalta.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bahĩra da sã'iba da hãmi sunãyen dabbõbi ne waɗanda ake bari dõmin tsãfi Bukhãri yã ruwaito daga Sa'ĩd ɗan Musayyab Ya ce: \"Bahĩra ita ce rãƙumar da ake hana nõnõnta dõmin aljannu, bãbu mai tãtsar ta daga mutãne. Sã'iba kuma sunã 'yanta ta dõmin gumãka, ba a ɗaukar kõme a kanta. Kuma wasĩla ita ce rãƙuma budurwa wadda ta fãra haifuwar mace, a ciki na farko, sa'an nan kuma na biyu haka mace. Suna barin ta ga gumãka idan ta sãdar da rãƙuma mata biyu bãbu namiji a tsakãninsu. Hãmi kuwa shĩ ne ƙaton rãƙumi wanda ya yi barbara shekaru sanannu a wurinsu. Idan ya ƙãre sai su bar shi ga gumãka, bã a aza kõme a kansa. Kuma waɗannan dabbõbin duka, mãsu hidimar gumãkan, su ne suke cin su.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 125,
            "translated_text": "Kuma idan aka ce musu: \"Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo,\" sai su ce: \"Mai isarmu shi ne abin da muka iske ubanninmu a kansa.\" Shin, kuma kõ dã ubanninsu sun kasance bã su sanin kõme kuma bã su shiryuwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 125,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku lazimci* rãyukanku, wanda ya ɓace bã zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wanda yake son Ya gyãra wani sai ya gyãra kansa daga farko. Wanda ya gyara kansa ɓatar wani bã ta cutarsa. Ba a nufin a bar wa'azi wãtau a ƙyãle mutane da jãhilcinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 125,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar* tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfarmutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: \"Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Idan husuma ta auku a tsakãnin Musulmi da tsakãnin kãfirai, kuma su kãfiran suka zama mudda'a alaihim (waɗanda ake tuhuma), kuma bãbu wata shaida sai su, to, sai su yi rantsuwa a wurin ibãdarsu, a kan su ne da gaskiya, a hukumta musu da hakkin. Bayan haka, idan an sãmi wata shaida a kan ƙaryarsu ana warware hukuncin a bãyan mudda'i (mãsu ƙãra) biyu Musulmi sun yi rantsuwa cewa abin da waɗancan suka faɗa ƙarya ne, abin da shaidunsu suka yi shaida da shi, shi ne gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 125,
            "translated_text": "To, idan aka gane cewa lalle sũ, sun cancanci zunubi to sai wasu biyu su tsayu matsayibsu daga waɗanda suka karɓa daga gare su, mutãne biyu mafiya cancanta, sa'an nan su yi rantsuwa da Allah: \"Lalle ne shaidarmu ce mafi gaskiya daga shaidarsu, kuma ba mu yi zãlunci ba. Lalle mu, a lõkacin haƙĩƙa, munã daga azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 125,
            "translated_text": "Wannan ne mafi kusantar su zo da shaida a kan fuskarta kõ kuwa su yi tsõron a tũre rantsuwõyi a bãyan rantsuwõyinsu. Kuma ku bi Allah da taƙawa kuma ku saurara, kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 126,
            "translated_text": "A ranar da Allah Yake tãra manzanni sa'an nan Ya ce: \"Mene ne aka karɓa muku?\" (zã) su ce: \"Bãbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * A nan hukunce-hukuncen alkawurra suka ƙãre a wannan sura daga ãyã ta sama da wannan. Kuma da wannan ãyã ta l09 Allah Yanã yi mana hikãyar abin da zai auku a Lãhira da bincinkenSa ga tsare alkawari, kõ rashin tsarewa. Ya fãra da AnnabãwanSa. Ya aiko, da ƙarin bãyani a kan irin muhãwarar da zã ta shiga a tsakãninSa da Annabãwa.Yã yi misãli da Ĩsã dõmin mutanensa nã nan a cikin wannan al'umma, anã kiran su zuwa ga musulunci, kuma domin shine Annabi na ƙarshen da ba a manta abubuwan da mutanensa suka yi ba a gabanin ɗauke shi ɗin."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 126,
            "translated_text": "A lõkacin da Allah Ya ce: \"Yã Ĩsã ɗan Maryama! Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ¡udusi, kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã'ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai waɗanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne.'"
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 126,
            "translated_text": "\"Kuma a lõkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawãriyãwa* cewa ku yi ĩmãni da Ni, kuma da ManzoNa. Suka ce: \"Mun yi ĩmãni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, mãsu sallamãwa ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hawãriyãwa su ne sahabban Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sunã sanyãwar farãren tufãfi, dõmin haka aka yi musu suna da haka."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 126,
            "translated_text": "A lõkacin da Hawarãyãwa suka ce: \"Ya Ĩsa ɗan Maryam! shin, Ubangijinka Yanã iyãwa Ya saukar da kaɓaki a kanmu daga samã?\" (Ĩsã) Ya ce: \"Ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 126,
            "translated_text": "Suka ce: \"Munã nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukãtanmu su natsu kuma mu san cewa lalle ne, kã yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga mãsu shaida a kansa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 127,
            "translated_text": "Ĩsã ɗan Maryam ya ce: \"Yã Allah. Ubangijinmu! Ka saukar da kaɓaki a kanmu daga sama dõmin ya zama ĩdi ga na farkonmu da na ƙarshenmu, kuma ya zama ãyã daga gare Ka. Ka azurta mu, kuma Kai ne Mafĩfĩcin mãsu azurtawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 127,
            "translated_text": "Allah Ya ce: \"Lalle ne Nĩ mai saukar da shi ne a kanku sa'an nan wanda ya kãfirta daga gare ku, to, lalle ne Nĩ, Inã azabta shi, da wata azãba wadda bã Ni azabta ta ga kõwa daga tãlikai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 127,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Allah Ya ce: \"Yã Ĩsã ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, 'Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?\" (Ĩsã) Ya ce: \"Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a gare ni, in faɗi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kanã sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 127,
            "translated_text": "\"Ban faɗa musu ba fãce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nã kasance mai shaida a kansu matuƙar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karɓi raina* Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kõme, Halartacce ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Karɓar ran Ĩsã biyu ne, na duniya da na mutuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 127,
            "translated_text": "\"Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bãyinKa ne, kuma idan Ka gãfarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima.\""
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 127,
            "translated_text": "Allah Ya ce: \"Wannan ce rãnar da mãsu gaskiya, gaskiyarsu take amfãninsu. Sunã da gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. wannan ne babban rabo mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 5,
            "page_number": 127,
            "translated_text": "Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a cikinsu kuma shi, a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 128,
            "translated_text": "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske*, sa'an nan kuma waɗanda suka kãfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Duffai na dare da zãlunci da bin hukunce-hukuncen al'ãdu, haske kuma shĩ ne na taurãri da wuta da shari'u na Littãfi da annabci."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 128,
            "translated_text": "Shi ne wanda Ya halitta ku daga lãkã, sa'an nan kuma Ya yanka ajali alhãli wani ajali ambatacce yanã wurinSa. Sa'an nan kuma ku kunã yin shakka."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 128,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin ƙasa Yanã sanin asĩrinku da bayyanenku, kuma Yanã sanin abin da kuke yi na tsirfa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 128,
            "translated_text": "Kuma wata ãyã daga Ubangijinsu ba zã ta jẽ musu ba, fãce su kasance, daga gare ta, mãsu bijirẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 128,
            "translated_text": "Sabõda haka, lalle sun ƙaryata (Manzo) game da gaskiya, a lõkacin da ta jẽ musu, to lãbãrun abin da suka kasance sunã izgili da shi, zã su jẽ musu."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 128,
            "translated_text": "Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabãninsu, Mun mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a kansu tanã ta zuba, kuma Muka sanya kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sa'an nan Muka halakã su sabõda zunubansu kuma Muka ƙãga halittar wani ƙarni na dabam daga bayansu?"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 128,
            "translated_text": "Kuma dã Mun sassaukar da wani littãfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dã waɗanda suka kãfirta sun ce: \"Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 128,
            "translated_text": "Suka ce: \"Don me ba a saukar da wani malã'ika ba a gare shi?\" to dã Mun saukar da malã'ika haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin* sa'an nan kuma ba zã a yi musu jinkiri ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Dã an hukunta al'amari da halakarsu, dõmin idan malã'ika ya sauka ga mutãnen da ake yi wa wa'azi bayyane, to, halakarsu tã je ke nan."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "Kuma dã Mun sanya malã'ika ya zama manzo lalle ne dã Mun mayar da shi mutum, kuma dã Mun rikita musu abin da suke rikitãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da manzanni daga gabaninka, sai waɗanda suka yi izgilin, abin da suka kasance sunã izgili da shi ya fãɗa musu."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "Ka ce: \"Na wãne ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa?\" Ka ce: \"Na Allah ne.\" Yã wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yanã tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, babu shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ ba zã su yi ĩmani ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "\"Kuma Shĩ ne da mallakar abin da ya yi kawaici a cikin dare da yini, kuma Shi ne Mai ji, Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, (alhãli Allah ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yanã ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi?\" Ka ce: \"Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga mãsu shirki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "Kace: \"Lalle ne nĩ inã tsõron azãbar Yini Mai girma, idan nã sãɓã wa Ubangijina.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "\"Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rãnar, to, lalle ne, (Allah) Yã yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "\"Idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, fãce Shĩ, kuma idanYa shãfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kõme, Mai ĩkon yi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 129,
            "translated_text": "\"Kuma Shĩ ne mai Tanƙwasa a kan bayinSa, kuma Shi ne Mai hikima, Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 130,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wane abu ne mafi girma ga shaida?\" Ka ce: \"Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa, kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?\" Ka ce: \"Bã zan yi shaidar (haka) ba.\" Ka ce: \"Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 130,
            "translated_text": "Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa* kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yahũdu da Nasãra sunã sanin Annabi Muhammadu tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da abin da ya zo da shi na Alƙur'ãni, kamar yadda suka san ɗiyan tsatsõnsu; kamar yadda Abdullahi ɗan Sallãmi ya ce wa Umar: \"Lalle ne na san shi a lõkacin da na gan shi, kamar yadda nake sanin ɗãna, kuma lalle ne, ni, mãfi tsananin sani ne ga Muhammadu fiye da ɗãna.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 130,
            "translated_text": "Wãne ne mafi zãlunci daga wanda yake ƙirƙira karya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinsa? Lalle ne shĩ, azzalumai bã zã su ci nasara ba."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 130,
            "translated_text": "Kuma rãnar da Muka tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Mu ce wa waɗanda suka yi shirki: \"Inã abõkan tãrayyarku waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 130,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma fitinarsu ba ta kasance ba, fãce dõmin sun ce: \"Munã rantsuwa da Allah Ubangijinmu, ba mu kasance mãsu yin shirki ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 130,
            "translated_text": "Ka dũba yadda suka ƙaryata kansu! Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙira ƙaryarsa, ya ɓace daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 130,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurãre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi. Kuma idan sun ga kõwace ãyã bã zã su yi ĩmãni da ita ba har idan sunjẽ maka sunã jãyayya da kai, waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: \"Wannan bai zama ba fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 130,
            "translated_text": "Kuma sunã hanãwa daga gare shi, kuma sunã nĩsanta daga gare shi, kuma bã su halakarwa, fãce kansu, kuma bã su sansancẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 130,
            "translated_text": "Kuma dã kanã gani, a lõkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: \"Yã kaitõnmu! Dã ana mayar da mu, kuma bã zã mu ƙaryata ba daga ãyõyin Ubangijinmu, kuma zã mu kasance Daga mũminai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 131,
            "translated_text": "Ã'aha, abin da suka kasance suna ɓõyẽwa, daga gabãni, ya bayyana a gare su. Kuma dã an mayar da su, lalle dã sun kõma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 131,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Ba ta zama ba, fãce rayuwarmu ta duniya, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 131,
            "translated_text": "Kuma dã kana gani, a lõkacin da aka tsayar da su ga UbangiJinsu, Ya ce: \"Ashe wannan bai zama gaskiya ba?\" Suka ce: \"Nã'am, muna rantsuwa da Ubangijinmu!\" Ya ce: \"To ku ɗanɗani azaba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 131,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasara, har idan Sa'a ta je musu kwatsam, sai su ce: \"Yã nadãmarmu a kan abin da muka yi sakaci a cikinta!\" Alhãli kuwa su suna ɗaukar kayansu masu nauyi a kan bayayyakinsu. To, abin da suke ɗauka yã mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 131,
            "translated_text": "Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba, fãce wãsa da shagala, kuma lalle ne, Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa. Shin, ba za ku yi hankali ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 131,
            "translated_text": "Lalle ne Muna sani cewa haƙĩƙa, abin da suke faɗa yana ɓãta maka rai. To, lalle ne su, bã su ƙaryata ka (a cikin zukatansu) kuma amma azzãlumai da ãyõyin Allah suke musu."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 131,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an ƙaryata manzanni daga gabãninka, sai suka yi haƙuri a kan abin da aka ƙaryata su, kuma aka cũtar da su, har taimakonMu ya je musu, kuma babu mai musanyãwa ga kalmõmin Allah. Kuma lalle ne (abin da yake natsar da kai) ya zo maka daga lãbãrin (annabãwan) farko."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 131,
            "translated_text": "Kuma idan yã kasance cewa finjirewarsu tã yi nauyi a gare ka, to, idan kana iyãwa, ka nemi wani ɓullõ a cikin ƙasa, kõ kuwa wani tsãni a cikin sama dõmin ka zo musu da wata ãyã, (sai ka yi). Kuma dã Allah Yã so haƙĩƙa dã Yãtãra su a kan shiriya. Sabõda haka, kada lalle ka kasance daga jãhilai."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 132,
            "translated_text": "Abin sani kawai, waɗanda suke saurare ne suke karɓãwa, kuma matattu Allah Yake tãyar da su, Sa'an nan kuma zuwa gare Shi ake mayar da su."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 132,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Don me ba a saukar da ãyã ba, a kansa, daga Ubangjinsa?\" Ka ce: \"Lalle ne Allah Mai ĩko ne a kan Yasaukar da ãyã, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 132,
            "translated_text": "Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa kuma bãbu wani tsuntsu wanda yake tashi da fukafukinsa fãce al'umma ne misãlanku. Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi, sa'an nan kuma zuwa ga Ubangjinsu ake tãra su."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 132,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka ƙaryata gameda ãyõyinMu, kurãme ne kuma bebãye, acikin duffai. Wanda Allah Ya so Yanã ɓatar da shi, kuma wanda Ya so zai sanya shi a kan hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 132,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shĩn, kun gan ku, idan azãbar Allah ta zo muku, kõ Sã'ar Tashin Kiyãma ta zo muku, shin wanin Allah kuke kira, idan dai kun kasance mãsu gaskiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 132,
            "translated_text": "\"Ã'a, Shĩ dai kuke kira sai Ya kuranye abin da kuke kira zuwa gare Shi, idan Ya so, kuma kunã mantãwar abin da kuke yin shirkin tãre da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 132,
            "translated_text": "Kuma lalle Mun aika zuwa ga al'ummai daga gabãninka, sai Muka kãmã su da tsanani da cũta, tsammãninsu zã su ƙanƙan da kai,"
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 132,
            "translated_text": "To, don me, a lõkacin da tsananinMu ya jẽ musu ba su yi tawãlu'i ba? Kuma amma zukatansu sun ƙẽƙashe kuma shaiɗan yã ƙawãta musu abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 132,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma alõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka bũɗe, a kansu, ƙõfõfin dukkan kõme, har a lõkacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, Muka kãmã su, kwatsam, sai gã su sun yi tsuru tsuru."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 133,
            "translated_text": "Sai aka katse ƙarshen mutãnen, waɗanda suka yi zãlunci. Kuma gõdiya tã tabbata ga Allah Ubangijin tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 133,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kun gani, idan Allah Ya riƙe jinku, da gannanku, kuma Ya sanya hãtimi a kan zukãtanku, wane abin bauttãwa ne, wanin Allah, zai jẽ muku da shi?\" Ka dũba yadda Muke sarrafaãyõyi, Sa'an nan kuma sũ, sunã finjirẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 133,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kun gan ku, idan azãbar Allah ta jẽ muku, kwatsam, kõ kuwa bayyane, shin, anã halakãwa, fãce dai mutãne azzãlumai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 133,
            "translated_text": "Kuma bã Mu aikãwa da manzãnni fãce mãsu bayar da bushãra, kuma mãsu gargaɗi. To, wanda ya yi ĩmãni kuma yagyãra aiki, to, babu tsõro a kansu, kuma ba su yin baƙin ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 133,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, azãba tanã shãfar su sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 133,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni malã'ika ne. Ba ni bi, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni.\" Ka ce: \"Shin, makãho da mai gani sunã daidaita? Shin fa, ba ku yin tunãni?\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 133,
            "translated_text": "Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsõron a tãra su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani masõyi baicinSa, kuma babu mai cẽto, tsammãninsu, sunã yin taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 133,
            "translated_text": "Kuma kada ka kõri waɗanda* suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Musulunci addinin Allah ne, wanda yake faƙĩrin dũkiya da mawãdãcinta, duka ɗaya suke a gare shi. Sabõda haka wanda duka ya rigayi wani a cikinsu, to, bã za a kõre shi ba dõmin ɗayan ya shiga. Allah ĩmãni Yake so, kõ daga wãne irin mutum yake, bã Ya bukãtar dũkiya."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 134,
            "translated_text": "Kuma kamar wannan ne, Muka fitini sãshensu da sãshe, dõmin su ce: \"Shin waɗannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakãninmu?\" Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga mãsu gõdiya?"
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 134,
            "translated_text": "Kuma idan waɗanda suke yin ĩmãni da ãyõyinMu suka jẽ maka, sai ka ce: \"Aminci ya tabbata a gareku; Ubangjinku Ya wajabta rahama ga kanSa, cẽwa lalle ne wanda ya aikata aibi da jãhilci daga cikinku, sa'an nan kuma ya tũba daga bãyansa, kuma ya gyãra, to, lalle Shi, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 134,
            "translated_text": "Kuma kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, kuma dõmin hanyar mãsu laifi ta bayyana."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 134,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle ne ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira daga baicin Allah.\" Ka cc: \"Ba ni bin son zũciyõyinku, (dõmin in nã yi haka) lalle ne, nã ɓace. A sa'an nan, kuma ban zama daga shiryayyu ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 134,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle ne inã kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da Shi; abin da kuke nẽman gaugãwarsa, bã ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba fãce, ga Allah, Yanã bãyar da lãbãrin gaskiya, kuma shĩ ne mafi alhẽrin mãsu rarrabẽwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 134,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle ne, dã a wurina akwai abin da kuke nẽman gaugãwa da shi, haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin, a tsakãnina da tsakãninku, kuma Allah Shĩ ne Mafi sani ga azzũlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 134,
            "translated_text": "Kuma a wurinSa mabũdan* gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Lõkacin aukuwar abũbuwa na alheri da na azãba da rãyuwa da mutuwa da sauransu, bãbu wanda ya san su sai Allah. Wanda ya ce ya san wani abu na gaibi alhãli kuwa shĩ ba wani manzon Allah ba, to, kãfiri ne. haka kuma wanda yake cewa, Annabãwã sun san dukkan gaibi, kamar yadda Allah Ya sani, shĩ mã kãfiri ne."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 135,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar* rãyukanku da dare, kuma Yanã sanin abin da kuka yãga da rãna, sa'an nan Yanã tãyar da ku a cikinsa, dõmin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makõmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku lãbari da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Karɓar rai da dare dõmin barci, tãyarwa a cikin ranã, watau yini daga barci. Akwai misalta dare da dũniya kuma rãna da Rãnar Ƙiyãma, kuma mutuwa da barci, da farkawa daga barci da Tãshin Ƙiyãma. Ãyar tã ƙunsa asĩrai mãsu yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 135,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne Mai rinjãya bisa ga bãyinSa, kuma Yanã aikan mãsu tsaro a kanku, har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayanku, sai manzanninMu su karɓi ransa alhãli su ba su yin sakaci."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 135,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma a mayar da su zuwa ga Allah Ubangjinsu na gaskiya. To! A gare shi hukunci yake, kuma Shi ne Mafi gaugãwar mãsu bincike."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 135,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wane ne Yake tsĩrar da ku daga duhũhuwan tududa ruwa, kunã kiran Sa bisa ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓõye: 'Lalle ne idan Ka tsĩrar da mu daga wannan (masĩfa), haƙĩƙa, muna kasancẽwa daga mãsu gõdiya?'\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 135,
            "translated_text": "Ka ce: \"Allah ne Yake tsĩrar da ku daga gare ta, kuma daga dukan baƙin ciki sa'an nan kuma ku, kunã yin shirki!\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 135,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shĩ ne Mai ĩko a kan Ya aika da wata azãba a kanku daga bisanku, kõ kuwa daga ƙarƙashin ƙafãfunku, kõ kuwa Ya gauraya ku ƙungiyõyi, kuma Ya ɗanɗanã wa sãshenku masĩfar sãshe.\" \"Ka dũba yadda Muke sarrafa ãyõyi, tsammãninsu sunã fahimta!\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 135,
            "translated_text": "Kuma mutãnenka sun ƙaryata (ka) game da Shi, alhãli kuwa Shi ne gaskiya. Ka ce: \"Nĩban zama wakĩli a kanku ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 135,
            "translated_text": "\"Akwai matabbata ga dukan lãbãri, kuma zã ku sani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 135,
            "translated_text": "Kuma idan kã ga waɗanda suke kũtsawa a cikin ãyõyinMu, to, ka bijire daga gare su, sai sun kũtsa a cikin wani lãbãri waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunãwa tãre da mutãne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 136,
            "translated_text": "Kuma babu wani abu daga hisãbinsu (mãsu kutsãwa a cikin ayõyin Allah (a kan mãsu taƙawa amma akwai tunãtarwa (a kansu), tsãmmãninsu (mãsu kutsawar) zã su yi taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 136,
            "translated_text": "Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addĩninsu abin wãsa* da wargi alhãli rãyuwar dũniya tã rũɗe su, kuma ka tunãtar game da shi (Alƙur'ãni): Kada a jẽfa raia cikin halaka sabõda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma babu wani mai cẽto; kuma, kõ ya daidaita dukan fansa, ba zã a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammãni sabõda abin da suka tsirfanta; sunã da wani abin shã daga ruwan zãfi, da wata azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Suka sanya sãbabbin abũbuwa a cikinsa, waɗanda suke bãbu su a cikinsa, kamar Khawãrijãwa da sãshen wanda ke da'awar danganuwa zuwa ga sãlihai inda suka sanya Ɗarĩka mai sãdarwa zuwa ga Allah, bandiri da algaita, kuma suka fãra abũbuwa waɗanda ba su halatta ba ga shari'a. Daga Sãwĩ. "
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 136,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'\"* Kace: \"Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Shi kuma bã ya karɓãwa balle ya nufi wurin shiriyar da suke kiran sa ya tafi, sabõda yã riga yã fãɗi daga sama zuwa ƙasa, kuma ɗimuwa tã kãmã shi."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 136,
            "translated_text": "\"Kuma (an ce mana): Ku tsai da salla kuma ku bĩ shi (Allah) da taƙawa kuma Shi ne wanda Yake zuwa gare Shi ake tãra ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 136,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da mulkinSa, kuma a Rãnar da Yake cẽwa: \"Ka kasance,\" sai abu ya yi ta kasancẽwa. MaganarSa ce gaskiya, kuma gare Shi mulki yake a Rãnar da ake bũsa a cikin ƙaho. Masanin fake da bayyane ne, Kuma Shi ne Mai hikima Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 137,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ibrãhĩma ya ce wa ubansa Ãzara: \"Shin, kanã riƙon gumãka abũbuwan bautãwa? Lalle nĩ, inã ganin ka kai damutã- nenka, a cikin ɓata bayyananniya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 137,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan ne, Muke nũna wa Ibrãhĩma mulkin sammai da ƙasa, kuma dõmin ya kasance daga mãsu yaƙĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 137,
            "translated_text": "To, a lõkacin da dare ya rufe a kansa, ya ga wani taurãro, ya ce: \"Wannan ne, ubangijina?\" Sa'an nan a lõkacin da ya faɗi, ya ce: \"Ba ni son mãsu fãɗuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 137,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da ya ga watã yanã mai bayyana, ya ce: \"Wannan ne Ubangijina?\" Sa'an nan a lõkacin da ya fãɗi, ya ce: \"Lalle ne idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa, inã kasancẽwa daga mutãne ɓatattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 137,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da ya ga rãnã tanã bayyana, ya ce: \"Wannan shĩ ne Ubangijina, wannan ne mafi girma?\" Sa'an nan a lõkacin da ta fãɗi, ya ce: \"Ya mutãnena! Lalle ne ni barrantacce nake daga abin da kuke yi na shirki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 137,
            "translated_text": "\"Lalle ne nĩ, na fuskantar da fuskata ga wanda, Ya ƙãga halittar sammai da ƙasa, inã mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bã ni cikin mãsu shirki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 137,
            "translated_text": "Kuma mutãnensa suka yi musu da shi. Ya ce: \"Shin kunã musu da ni a cikin sha'anin Allah, alhãli kuwa Yã shiryai da ni? Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, fãce idan Ubangijina Yã so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan kõme da ilmi. Shin, ba zã ku yi tunãni ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 137,
            "translated_text": "\"Kuma yãyã nake jin tsõron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba ku tsõron cẽwa lalle ne kũ, kun yi shirki da Allah, abin da (Allah) bai saukar da wata hujja ba game da shi? To, wane ɓangare daga sãshen biyu ne mafi cancanta da aminci, idan kun kasance kunã sani?\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 138,
            "translated_text": "\"Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma ba su gauraya ĩmãninsu da zãlunci ba, waɗannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 138,
            "translated_text": "Kuma waccan ita ce hujjarMu, Mun bayãr da ita ga Ibrãhĩma a kan mutãnensa. Munã ɗaukaka wanda Muka so da darajõji. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 138,
            "translated_text": "Kuma Muka bã shi Is'hãƙa da Yãƙubu, dukansu Mun shiryar, kuma Nũhu Mun shiryar da shi a gabãni, kuma daga zuriyarsa akwai Dãwũda da Sulaimãnu da Ayyũba, da Yũsufu da Mũsã da Hãrũna, kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 138,
            "translated_text": "Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Ilyasu dukansu daga sãlihai suke."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 138,
            "translated_text": "Da Ismã'la da Ilyasa, a da Yũnusa da Luɗu, kuma dukansu Mun fĩfĩtã su a kan tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 138,
            "translated_text": "Kuma daga ubanninsu, da zũriyarsu, da 'yan'uwansu, kuma Muka zãɓe su, kuma Muka shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 138,
            "translated_text": "Wancan ne shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Yake so daga bayinSa. Kuma dã sun yi shirki dã haƙĩƙa abin da suka kasance sunã, aikatãwa yã lãlãce."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 138,
            "translated_text": "Waɗancan ne waɗanda Muka bai wa Littãfi da hukunci da Annabci. To idan waɗannan (mutãne) sun kãfirta da ita, to, haƙĩƙa, Mun wakkala wasu mutãne gare ta, ba su zama game da ita kãfirai ba."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 138,
            "translated_text": "Waɗancan ne Allah Ya shiryar, sabõda haka ka yi kõyi da shiryarsu. Ka ce: \"Ba ni tambayar ku wata ijãra. Shĩ (Alƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ga tãlikai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 139,
            "translated_text": "Kuma ba su ƙaddara Allah a kan hakkin ƙaddara shi ba, a lõkacin da suka ce: \"Allah bai saukar da kõme ba ga wani mutum.\" Ka ce: \"Wãne ne ya saukar da Littãfi wanda Mũsã ya zo da shi, yanã haske da shiriya ga mutãne, kunã sanya shi takardu, kũna bayyana su, kuma kunã ɓõye mai yawa, kuma an sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ubanninku?\" Ka ce: \"Allah,\"* sa'an nan ka bar su a cikin sharhõliyarsu sunã wãsã.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah ne Ya saukar da shi, sabõda haka ba zai zama abin mãmãki ba ko abin musu ga Ya saukar da wani littãfi kamar Alƙur'ãni ga wani mutum a bãyan Taurãta ga Musã. Kuma a cikin Taurãtar ba a ce ita ce ƙarshen Littãfin Allah ba kuma Mũsã bã shi ne ƙarshen Annabawa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 139,
            "translated_text": "Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, mai gaskata wanda yake a gabansa ne, kuma dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda yake gefenta. Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da Lãhira sunã ĩmãni da shi (Alƙur'ãni), kuma sũ, a kan sallarsu, sunã tsarẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 139,
            "translated_text": "Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ce: \"An yi wahayi zuwa gare ni,\" alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: \"zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?\" Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) \"Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 139,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa, kun zo Mana ɗai ɗai, kamar yadda Muka halittã ku a farkon lõkaci. Kuma kun bar abin da Muka mallaka muku a bayan bayayyakinku, kuma ba Mu gani a tãre da kũ ba, macẽtanku waɗanda kuka riya cẽwa lalle ne sũ, a cikinku mãsu tãrayya ne. Lalle ne, hãƙĩƙa, kõme yã yanyanke a tsakãninku, kuma abin da kuka kasance kunã riyãwa ya ɓace daga gare ku."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 140,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai,* wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mai ĩmãni daga kãfiri kõ kãfiri daga mai ĩmãni, da mai arziki daga matalauci da matalauci daga mawadãci, sarki daga talaka da talaka daga sarki,da mai sanyi daga mai zãfi ko mai zãfi daga mai sanyi, haka dai ga kõme Allah Yanã fitar da kĩshiyarsa. "
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 140,
            "translated_text": "Mai tsãgẽwar sãfiya, kuma Ya sanya dare mai natsuwa, kuma da rãna da watã a bisa lissãfi. vwannan ne ƙaddarãwar Mabuwãyi Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 140,
            "translated_text": "Kuma Shi ne Ya sanya muku taurãri dõmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da ruwa. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 140,
            "translated_text": "Kuma Shi ne Ya ƙãga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda ake ajẽwa. Lalle ne Mun bayyanã ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke fahimta."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 140,
            "translated_text": "Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa'an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi (kõren),* kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah na halitta kõren ganye daga hasken rãnã, sa'an nan Ya halitta gãrin ƙwãyã daga kõren. "
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 140,
            "translated_text": "Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa (Shi) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 140,
            "translated_text": "Mafarin* halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Shi ne wanda Ya fãri halittarsu bã da Yã kõya daga wani ba. Sautin jan wasalin fa zaiyi sama dõmi bambanci daga mafãri watau sababin abu, ana mĩƙe sautin maddi a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 141,
            "translated_text": "Wancan ne Allah Ubangijinku. Bãbu wani abin bautãwa fãce Shĩ, Mahaliccin dukan kõme. Sabõda haka ku bauta Masa kuma Shi ne wakĩli a kan dukan, kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 141,
            "translated_text": "Gannai bã su iya riskuwarSa, kuma Shĩ Yanã riskuwar gannai, kuma Shĩ ne Mai tausasãwa, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 141,
            "translated_text": "Lalle ne abũbuwan lũra sun je muku daga Ubangijinku, to, wanda ya kula, to, dõmin kansa, kuma wanda ya makanta, to, laifi yanã a kansa, kuma nĩ, a kanku, bã mai tsaro ba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 141,
            "translated_text": "Kamar wannan ne Muke sarrafa ãyõyi, kuma dõmin su ce: \"Kã karanta!\" Kuma dõmin Mu bayyana shi ga mutãne waɗanda sunã sani."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 141,
            "translated_text": "Ka bi abin da aka yi wahayi zuwa gare ka daga Ubangijinka; babu wani abin bautãwa fãce Shi, kuma ka bijire daga mãsu shirki."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 141,
            "translated_text": "Kuma dã Allah Yã so, dã ba su yi shirki ba, kuma ba Mu, sanya ka mai tsaro a kansu ba, kuma ba kai ne wakĩli a kansu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 141,
            "translated_text": "Kuma kada ku zãgi waɗanda suke kira, baicin Allah, har su zãgi Allah bisa zãlunci, ba, da ilmi ba. Kamar wannan ne Muka ƙawãta ga kõwace al'umma aikinsu, sa'an nan zuwa ga Ubangijinsu makõmarsu take, sa'an nan Ya ba su lãbari da abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 141,
            "translated_text": "Kuma suka yi rantsuwa da Allah iyakar rantsuwõyinsu (cẽwa) lalle ne idan wata ãyã ta jẽmusu, haƙĩƙa, sunã yin ĩmãni da ita. Ka ce: \"Abin sani kawai, ãyõyi a wurin Allah suke. Kuma mẽne nezai sanya ku ku sansance cẽwa, lalle ne su, idan ãyõyin sun je, ba zã su yi ĩmãni ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 141,
            "translated_text": "Kuma Munã jujjũya zukãtansu da ganansu, kamar yadda ba su yi ĩmãni da shi ba a farkon lõkaci kuma Munã barin su a cikin kũtsãwarsu, sunã ɗĩmuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 142,
            "translated_text": "Kuma dã a ce, lalle Mũ Mun saukar da Malã'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tãra dukkan kõme a kansu, gungu-gungu, ba su kasance sunã iya yin ĩmãni ba, sai fa idan Allah Yã so, Kuma amma mafi yawansu sunã jãhiltar haka."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 142,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi maƙiyi; shaiɗãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra* zuwa sãshe da ƙawãtaccen zance bisa ga rũɗi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wahayin shaiɗãnu sãshensu zuwa ga sãshe da ƙãwata ƙarya ta zama kamar gaskiya. Kamar Shaiɗan ya sanya wasiwãsi: Dã da'awar Annabi gaskiya ce: Ai dã manyan mutãne ne zã su fãra bin ta, ba matalautã ba, kõ kuwa annabi mai sihiri ne dõmin yanã raba miji da mãta, da ɗa da uba. Watau su karkatar da magana, dõmin su karkatar da wãwãye daga bin gaskiya. "
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 142,
            "translated_text": "Kuma dõmin zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba su karkata saurãrẽ zuwa gareshi, kuma dõmin su yarda da shi, kuma dõmin su kamfaci abin da suke mãsu kamfata."
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 142,
            "translated_text": "Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhãli kuwa Shĩ ne wanda Ya saukar muku da Littãfi abin rabẽwadaki-daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littãfi sunã sanin cẽwa lalleshi (Alƙur'ãni) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Sabõda haka kada ku kasance daga mãsu shakka."
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 142,
            "translated_text": "Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya* da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Musulunci kõ Alƙur'ãni ne cikon addinin Allah, babu mai iya zõwa da wani abu sãbo kõ ya ƙãra wani abu a cikin sa ta kõwace hanya kuma bãbu mai iya musanya wani abu a cikinsa. Ya cika ya kammala, sai biya kawai. Annabi ya ce: \"Wanda ya yi wani aiki ba da umuruinsa a kan abin da ya aikata ɗin nan ba, to, an mayar masa; ba a karɓaba.\". "
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 142,
            "translated_text": "Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗã'a sunã ɓatar da kai daga hanyar Allah. Ba su bin kõme sai fãce ƙaddari-faɗi* suke yi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kamar maganarsu cewa mũshe wanda Allah da kansa Ya kashe, ya fi dã cewa da a ci shi, bisa ga abin da mutãne suka yanka. "
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 142,
            "translated_text": "Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda yake ɓacẽwa daga hanyarsa kuma Shi ne mafi sani ga masu shiryuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 142,
            "translated_text": "Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah* kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* An sani daga nan cewa ambaton sũnan Allah wajen yankan dabba wãjibi ne, idan an tuna. Wanda ya manta, anã cin yankansa, amma wanda ya bari da gangan, bã zã a ci yankansa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 143,
            "translated_text": "Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã zã ku ci ba daga abin da aka ambaci sũnan Allah a kansa, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Ya rarrabe, muku daki-daki, abin da Ya haramta a kanku, fãce fa abin da aka bukãtar da ku bisa lalũra zuwa gare shi? Kuma lalle ne mãsu yawa sunã ɓatarwa, da son zũciyõyinsu, ba da wani ilmi ba. Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga mãsu ta'addi."
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 143,
            "translated_text": "Kuma ku bar bayyanannen zunubi da ɓõyayyensa. Lalle ne waɗanda suke tsiwurwurin zunubi za a sãka musu da abin da suka kasance sunã kamfata."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 143,
            "translated_text": "Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa.* Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sabõda haka bã a cin yankan majũsu. Anã cin yankan bakitãbe, babu ruwanmu da abin da yake faɗa, tun da Allah Ya halatta mana cin abincinsu alhãli kuwa Ya san sun riga sun musanya addininsu. Idan Musulmi ya bar sũnan Allah da gangan, amma bai ambaci sũnan kõwa ba, to, akwai riwãya biyu game da haka, ci kõ rashin ci. Amma idan ya haɗa sũnan Allah da na wani, to, ba zã a ci ba, dõmin yã yi ridda. "
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 143,
            "translated_text": "Shin, kuma wanda ya kasance matacce sa'an nan Muka rãyar da shi, kuma Muka sanya wani haske dõminsa, yanã tafiya da shi, yanã zama kamar wanda misãlinsa yanã cikin duffai, shĩ kuma ba mai fita ba daga gare su? Kamar wancan ne aka ƙawãta wa kãfirai abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 143,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan ne Mun sanya a cikin kõwace alƙarya, shugabanni sũ ne mãsu laifinta dõmin su yi mãkirci a cikinta, alhãli kuwa ba su yin makirci fãce ga rayukansu, kuma ba su sansancẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 143,
            "translated_text": "Kuma idan wata ãyã ta je musu sai su ce: \"Ba zã mu yi ĩmãni ba, sai an kãwo mana kamar abin da aka kãwo wa manzannin Allah.\" Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa.* Wani wulaƙanci** a wurin Allah da wata azãba mai tsanani zã su sãmi waɗanda suka yi laifi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na mãkirci.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Manzanci da zãɓin Allah yake, bã da kuɗi kõ'ya'ya kõ kabĩla yake ba, sai a wurin da Allah Ya aza shi.  ** Mai girman kai ga bin umurnin Allah, sakamakonsa wulaƙanci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 144,
            "translated_text": "Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũɗa ƙirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa* ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar ƙazanta a kan waɗanda bã su yin ĩmãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mai tãkãwa zuwa sama ƙirjinsa ƙunci yake yi, sabõda iskar numfashi tanã raguwa gare shi. Kuma shi yanã shasshekar gajiya da rashin iska. Wannan ilmi yanã a cikin mu'ujizar Alƙur'ani. "
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 144,
            "translated_text": "Wannan ita ce hanya ta Ubangijinka madaidaiciya. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki ga mutãne mãsu karɓar tunãtarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 144,
            "translated_text": "Sunã da gidan aminci a wurin Ubangjinsu, kuma Shĩ ne Majiɓincinsu, sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 144,
            "translated_text": "Kuma rãnar da yake tãra su gaba ɗaya (Yanã cẽwa): \"Yã jama'ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutãne.\" Kuma majiɓantansu daga mutãne suka ce: \"Yã Ubangjinmu! Sãshenmu* ya ji dãɗi da sãshe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana!\" (Allah) Ya ce: \"Wuta ce mazaunarku, kunã madawwama acikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Haka dai mai laifi a bãyan azãbar laifinsa ta tabbata a kansa bã ya ɓõyewar abin da ya riga ya bayyanã, sai ya faɗa da kansa dõmin ya bayyanar da nadãmarsa a lõkacin da nadãma bã ta da amfãni"
        },
        {
            "ayah_number": 129,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 144,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan ne Muke jiɓintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 130,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 144,
            "translated_text": "Yã jama'ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jẽ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini nãku? Suka ce: \"Mun yi shaida a kan kãwunanmu.\" Kuma rãyuwar dũniya tã rũɗẽ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cẽwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 131,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 145,
            "translated_text": "Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah bã Ya halaka mutãne sabõda wani laifi, sai bãyan Ya aiki mai gargaɗi ya tafi ya yi musu gargaɗi, sun san laifinsu, sun ƙi bari, sa'an nan azãba ta je musu."
        },
        {
            "ayah_number": 132,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 145,
            "translated_text": "Kuma ga kõwanne,* akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kõwace jama'a, ta mãsu ɗã'a da ta mãsu sabõ, sunã da sakamakõ gwargwadon matsayin kõwanne, ga ĩmãninsa da aikinsa kõ kuwa kãfircin sãɓonsa."
        },
        {
            "ayah_number": 133,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 145,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinika Wadãtacce* ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Rashin gaugãwar yin sãkamako ga mãsu laifi sabõda wadãtar Allah ne. Bã shi yin uƙũba dõmin Ya yi fushin an rage masa mulki, haka kuma bã shi yin ni'ima domin an ƙãra masa mulki. Sai dai dõmin Ya nũna ãdalci da falala ne kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 134,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 145,
            "translated_text": "Lalle ne abin da ake yi muku wa'adi lalle mai zuwa ne kuma ba ku zama mãsu buwãya ba,"
        },
        {
            "ayah_number": 135,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 145,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã ku mutãnena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne nĩ mai aiki ne, sa'an nan da sannu zã ku san wanda ãƙibar gida zã ta kasance a gare shi. Lalle ne shi, azzãlumai bã zã su ci nasarã ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 136,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 145,
            "translated_text": "Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: \"Wannan* na Allah ne,\" da riyãwarsu \"Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne.\" Sa'an nan<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sun kasance a cikin  jahiliyya idan suka yi nõma kõ kuwa idan suka sami 'ya'yan itace, sai su sanya wani juz'i daga gare shi ga Allah, wani juz'i kuma ga gumãka. Abin da yake rabon gumaka, sai su tsare shi, kuma su lissafce shi. Idan wani abu ya fãɗi daga abin da aka ambace shi ga Samad, sai su mayar da shi zuwa ga rabõn gumãka, amma rabõn gumãkan, bã ya zuwa ga na Allah. Anã bayãr da rabon Allah ga miskĩnai, kuma rabõn gumaka ga matsaransu."
        },
        {
            "ayah_number": 137,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 145,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar* 'ya'yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sunã turbuɗe 'ya'ya mata, dõmin tsõron talauci kõ dõmin tsõron kunya. Sai mai haihuwa ta haihu a bãkin rãmi, idan mace ta haifa, sai ta tũra ta cĩkin rãmin ta rufe, idan kuma namiji ne sai ta bar shi. Haka kuma kashe 'ya'ya, a kan bãkance da alwãshi, sunã ganin sa ibada ne."
        },
        {
            "ayah_number": 138,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 146,
            "translated_text": "Kuma sukace: \"Waɗannan dabbõbi da shũka hanannu ne; bãbu mai ɗanɗanar su fãce wanda muke so,\" ga riyãwarsu. Da wasu dabbõbi an hana bãyayyakinsu, da wasu dabbõbi bã su ambatar sũnan Allah a kansu, bisa ƙirƙiren ƙarya gare Shi. Zai sãka musu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 139,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 146,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Abin da yake a cikin cikkunan waɗannan dabbõbi kẽɓantacce ne ga mazanmu, kuma hananne ne a kan mãtan aurenmu. Kuma idan ya kasance mũshe, to, a cikinsa sũ abõkan tãrayya ne, zai sãka musu sifantãwarsu. Lalle ne Shĩ, Mai hikima ne, Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 140,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 146,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kashe ɗiyansu sabõda wauta, ba da ilmi ba, sun yi hasãra! Kuma suka haramta abin da Allah Ya azurta su, bisa ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne sun ɓace, kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 141,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 146,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne Wanda Ya ƙãga halittar gõnaki mãsu rumfuna da wasun mãsu rumfuna da dabĩnai da shũka, mai sãɓãwa ga 'yã'yansa na ci, da zaituni da rummãni mai kama da jũna da wanin mai kama da jũna. Ku ci daga 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'yã'yan, kuma ku bãyar da hakkinSa a rãnar girbinsa, kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ, ba Ya son mafarauta."
        },
        {
            "ayah_number": 142,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 146,
            "translated_text": "Kuma daga dabbõbi (Ya ƙãga halittar) mai ɗaukar kãya da ƙanãna; Ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, kuma kada ku bi zambiyõyin shaiɗan: LalLe ne shi, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 143,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 147,
            "translated_text": "Nau'õ'i takwas daga tumãkai biyu, kuma daga awãkai biyu; ka ce: Shin mazan biyu ne Ya haramta ko mãtan biyu, ko abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Ku bã ni lãbãri da ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 144,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 147,
            "translated_text": "Kuma daga rãƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shãnu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko mãtan biyu Ya hana, kõ abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Kõ kun kasance halarce ne a lõkacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, dõmin ya ɓatar da mutãne bã da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 145,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 147,
            "translated_text": "Ka ce: \"Bã ni sãmu,* a cikin abin da aka yõ wahayi zuwa gare Ni, abin haramtãwa a kan wani mai ci wanda yake cin sa fãce idan ya kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, kõ kuwa fãsiƙanci wanda aka kurũrũta, dõmin wanin Allah da shi.\" Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a ba, kuma bã mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Bayãnin abũbuwan da aka haramta cinsu daga dabbõbi waɗanda Allah Ya hana, bã waɗanda al'ãda ta hana ba."
        },
        {
            "ayah_number": 146,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 147,
            "translated_text": "Kuma a kan waɗanda suka tũba (Yahũdu) Mun haramta *dukan mai akaifa, kuma daga shãnu da bisãshe Mun haramta musu kitsattsansu fãce abin da bãyukansu suka ɗauka, kõ kuwa kãyan ciki, kõ kuwa abin da ya garwaya da ƙashĩ wannan ne Muka sãka musu sabõda zãluncinsu, kuma Mu, haƙĩƙa, Mãsu gaskiya ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Bayãnin abũbuwan da Allah Ya hana a kan Yahũdu, shi ma hanin an yĩ shi sabõda wani laifinsu ne."
        },
        {
            "ayah_number": 147,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 148,
            "translated_text": "To, idan sun ƙaryatã ka, sai ka ce: \"Ubangijinku Ma'abũcin rahama ne Mai yalwa; kuma bã a mayar da azãbarSa daga mutãne mãsu laifi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 148,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 148,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi shirki* zã su ce: \"Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirki ba, kuma dã ubanninmu ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba.\" Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: \"Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wahayin shaiɗan zuwa ga mãsu shirki da hana dabbõbi da ƙãga wasu hukunce-hukunce. Kalmar gaskiya ce ake yin nufin ƙarya da ita, da bãyanin warware rikicin. Jũyar da maganar gaskiya dõmin a yi ƙarya da ita yanã sabbaba saukar azãba. Kuma dukan maganar da bã ta da asali ga Littãfi kõ sunna, to, bã gaskiya ba ce, bin ta nau'in shirki ne."
        },
        {
            "ayah_number": 149,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 148,
            "translated_text": "Ka ce: \"To Allah ne da hujja isasshiya, sabõda haka: Dã Yã so, dã Yã shiryar da ku gabã ɗaya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 150,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 148,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku kãwo shaidunku, waɗanda suke bãyar da shaidar cẽwa Allah ne Ya haramta wannan.\" To idan sun kãwo shaida kada ka yi shaida tãre da su. Kuma kada ka bi son zũciyõyin waɗanda suka ƙaryata, game da ãyõyinMu, da waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira, alhãli kuwa sũ daga Ubangijinsu suna karkacẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 151,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 148,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku zo, in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta.\" wãjibi ne a kanku kada ku yi shirkin kõme da Shi, kuma ga mahaifa biyu (ku kyautata) kyautatãwa, kuma kada ku kashe ɗiyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su, kuma kada ku kusanci abũbuwa alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓõyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, fãce da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da Shi: Tsammãninku, kunã hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 152,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 149,
            "translated_text": "Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 153,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 149,
            "translated_text": "Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 154,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 149,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Mun bai wa Mũsã Littãfi, yanã cikakke bisa ga wanda ya kyautata (hukuncin Allah) da rarrabẽwa, daki-daki, ga kõwane abu, da shiriya da rahama, tsammãninsu,* sunã yin ĩmãni da haɗuwa da Ubangijinsu.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mabiya Littãfin Mũsã watau Yahũdu, idan sun san cewa Alƙur'ãni kamar Attaura yake daga Allah aka saukar da shi, kuma Muhammadu Annabin Allah ne kamar Mũsã kuma sũ duka suna gaskata jũnã, sai su ji sauƙin ĩmãni da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 155,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 149,
            "translated_text": "Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku."
        },
        {
            "ayah_number": 156,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 149,
            "translated_text": "(Dõmin) kada ku ce: \"Abin sani kawai, an saukar da littãfi a kan ƙungiya* biyu daga gabãninmu, kuma lalle ne mũ, mun kasance, daga karatunsu, haƙĩƙa, gãfilai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ana magana da mãsu shirkin Larabawa, ƙungiyõyin biyu kuwa su ne Yahũdu da Nasãra, littãfin shĩ ne Attaura da Linjĩla."
        },
        {
            "ayah_number": 157,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 149,
            "translated_text": "Kõ kuwa ku ce: \"Dã dai lalle mũ an saukar da Littãfi a kanmu, haƙĩƙa, dã mun kasance mafiya, shiryuwa daga gare su.\" To, lalle ne wata hujja bayyananniya, daga Ubangijinku, tã zo muku, da shiriya da rahama. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma ya finjire daga barinsu? Zã Mu sãka wa waɗanda suke finjirẽwa daga barin ãyõyinMu da mugunyar azãba, sabõda abin da suka kasance sunã yi na hinjirẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 158,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 150,
            "translated_text": "Shin, sunã jiran (wani abu), fãce dai malã'iku* su je musu kõ kuwa Ubangijinka Ya je, kõ kuwa sãshen ãyõyin Ubangijinka ya je. A rãnar da sãshen ãyõyin Ubangijinka yake zuwa, ĩmãnin rai wanda bai kasance yã yi ĩmãnin ba a gabãni, kõ kuwa ya yi tsiwirwirin wani alhẽri, bã ya amfãninsa. Ka ce: \"Ku yi jira: Lalle ne mũ, mãsu jira ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Zuwan malã'iku dõmin karɓar rãyukansu, zuwan Allah dõmin yin hisãbin bãyi, zuwan sãshen ãyõyin Ubangiji shĩ ne fitõwar rãnã daga yamma da fitar Rãƙumar Sãlihu. Waɗannan abũbuwa duka idan sun auku a kan wanda bã shi da imani a gabãnin aukuwarsu, kuma ya zama yã aikata ayyukan alheri da shari'a ta umurce shi da yi, to, bã za a karɓi wani ĩmãninsa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 159,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 150,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda* suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bãyan bayãnin wanda bai yi ĩmani ba sai bayãnin sababin rashin karɓar ĩmãnin ya zo, sai kuma ya ci gaba da bayãnin cewa, kõ wanda ya yi ĩmãnin idan yã ƙãra wasa abũbuwa a cikin addĩni bisa ga abin da Allah Ya saukar, ta haka har mutane suka zama ƙungiya ƙungiya, kamar mãsu ɗarĩƙõƙi na tasawwufi, to, su ma Annabi bã ya tãre da su ga kõme dõmin sun kõma wa hanyar jahiliyya a lõkacin da wasu suke ƙãga hukunce-hukunce a kan mutãne, suka zama da yin haka nan abũbũwan bautãwa, kuma mãsu bin su suka zama mushirikai. Daga nan har zuwa ga ƙarshen sũrar duka ta'lĩƙi ne ga dukan abin da sũrar ta ƙunsa na tauhĩdin Rubũbiyya da taƙaitãwa ga bãyanin muhimman mas'alolin da ta ƙunsa. Saninta shi ne rũhin addini."
        },
        {
            "ayah_number": 160,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 150,
            "translated_text": "Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to, yanã da gõma ɗin misãlansa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, bã zã a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma sũ bã a zãluntar su."
        },
        {
            "ayah_number": 161,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 150,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle nĩ, Ubangijina Yã shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addĩni, ƙĩmantãwa (ga abũbuwa), mai aƙĩdar Ibrãhĩm, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 162,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 150,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle ne sallãta, da baikõna, da rãyuwãta, da mutuwãta, na Allah ne Ubangijin tãlikai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 163,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 150,
            "translated_text": "\"Bãbu abõkin tãrayya a gare Shi. Kuma da wancan aka umurce ni, kuma ni ne farkon mãsu sallamãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 164,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 150,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin wanin Allah nake nẽma ya zama Ubangiji, alhãli kuwa Shĩ ne Ubangijin dukan kõme? Kuma wani rai bã ya yin tsirfa fãce dõmin kansa, kuma mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani, sa'an nan kuma kõmawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Yã bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũnã?\""
        },
        {
            "ayah_number": 165,
            "surah_number": 6,
            "page_number": 150,
            "translated_text": "\"Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya ku mãsu maye wa jũnaga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sãshenku bisa ga sãshe da darajõji; dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku.\" Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggãwar uƙkũba ne, kuma lalle ne Shi, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "A. L̃. M̃. Ṣ̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jẽ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Sa'an nan bãbu abin da yake da'awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jẽ musu, fãce suka ce: \"Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci,\""
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Sa'an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Sa'an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakowa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 151,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa'an nan kuma Mun sũrantã ku, sa'an nan kumaMun ce wa malã'iku: \"Ku yi sujada ga Ãdam.\" Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah Yã ƙidanya ni'imõmin da Ya yi wa mutãne daga halittarsu da sũrantã su da Ya yi kuma Ya girmama su da sanyãwar malã'iku su yi sujada ga ubansu Ãdam, sa'an nan kuma Ya nũna musu ceSwa shaiɗan yã ƙi bin umurninSa ga girmama ubansu Ãdam, sabõda haka sũ ma su yi tsõron maƙiyin kãkansu."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "Ya ce: \"Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alõkacin da Na umurce ka?\" Ya ce: \"Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã halitta shi daga lãka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "Ya ce: \"To, ka sauka daga gare ta; dõmin bã, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kanã daga mãsu ƙasƙanci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar* da su.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Yã rõƙi kada ya mutu, dõmin a Rãnar Rãyarwa bãbu sauran wata mutuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne, kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * wannan ya nũna cewa, kowa ya rõki Allah wani abu, to, zai bã shi gwargwadon yaddaYake so, Shi Ubangijin."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "Ya ce: \"To inã rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, inã zaune musu tafarkinKa madaidaici.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "\"Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Inã je musu daga gaba gare su, kuma daga bãya gare su, kuma daga jihõhin damansu da jihõhin hagunsu; Kuma bã zã ka sãmi mafi yawansu mãsu gõdiya ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ka fita daga gare ta kanã abin zargi kõrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, zã Ni cika jahannama daga gare ku, gabã ɗaya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "\"Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: \"Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 152,
            "translated_text": "Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: \"Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 153,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 153,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 153,
            "translated_text": "Ya ce: \"A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 153,
            "translated_text": "Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa* a kanku, tanã rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tufar da aka saukar, ita ce addinin Allah. Wanda ya riƙã shi da taƙawa, to, ya kyauta ƙawarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 153,
            "translated_text": "Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 153,
            "translated_text": "Kuma idan suka aikata alfãsha* su ce: \"Mun sãmi ubanninmu akanta.\" Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita.\"Ka ce: \"Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Alfãsha ita ce dukan mugun aiki, watau abin da sharĩ'a ba ta zõ da shi ba, kõ dã an jingina shi ga addini, kamar yin ɗawafi  tsirãra da bauta wa malã'iku da sãlihai, da yin kõwace ibãda ba bisa ga yadda Annabi ya kõyar da ita ba."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 153,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙẽ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 153,
            "translated_text": "Wata ƙungiya (Allah) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ, mãsu shiryuwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 154,
            "translated_text": "Yã ɗiyan Ãdam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kõwane masallãci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bã Ya son mãsu ɓarna."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 154,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wãne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu dãɗi daga abinci?\" Ka ce: \"Sũ, dõmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin rãyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rãnar Kiyãma. \"Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãnen da suke sani."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 154,
            "translated_text": "Ka ce: \"Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama'a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 154,
            "translated_text": "Kuma ga kõwace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, bã zã a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma bã zã su gabãce shi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 154,
            "translated_text": "Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku ayõyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 154,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 154,
            "translated_text": "To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littãfi yanã sãmunsu, har a lõkacin da ManzanninMu suka je musu, sunã karɓar rãyukansu, su ce: \"Ĩnã abin da kuka kasance kunã kira, baicin Allah?\" Su ce: \"Sun ɓace daga gare mu, \"Kuma su yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kãfirai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 155,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: \"Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta.\" Ya ce: \"Ga kõwane* akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Shũgabannin ɓata su ne ke fãra shiga wuta, sa'an nan mabiyansu, su shiga, dõmin shũgabanni sunã da laifi biyu; nãsu, na aikinsu, da kuma sababin da suka yi, na ɓatar da mabiyansu. Kuma an fahimta daga nan cewa, \"Inã bin wane a kan ɓata, shĩ ne ya ɓatar da ni, bã ya zama hujja mai hana shiga wuta, dõmin AllahYã aza wa kõwane bãligi mai hankali da yayi binciken gaskiya gwargwadon iyãwarsa. Allah ba Ya kãma mutum da abin da ba ya a cikin ĩkonsa."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 155,
            "translated_text": "Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: \"To, bã ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azãba sabõda abin da kuka kasance kunã tãrãwa!\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 155,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 155,
            "translated_text": "Sunã da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 155,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 155,
            "translated_text": "Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: \"Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya.\" Kuma aka kira su, cẽwa: \"Waccan Aljlnna an gãdar da ku ita, sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 156,
            "translated_text": "Kuma 'yan Aljanna suka kirãyi 'yan Wuta suka ce: \"Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?\" Suka ce: \"Na'am.\" Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: \"La'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 156,
            "translated_text": "\"Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 156,
            "translated_text": "Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki,* kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: \"Aminci ya tabbata a kanku: \"Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A tsakanin Aljanna da wuta akwai bango, anã ce masa A'araf, inda zã a ajiye mutãnen da ayyukansu na ƙwarai suka yi daidai da miyãgun ayyukansu. Sunã ganin mutãnen Aljanna sunã yi musu sallama sunã gurin shigarta, kuma sunã ganin mutãnen wuta sunã la'anar su, sunã neman nisanta daga gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 156,
            "translated_text": "Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abõkan wuta, su ce: \"Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu tãre da mutãne azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 156,
            "translated_text": "Kuma abõkan A'araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce: \"Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba daga barinku?\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 156,
            "translated_text": "\"Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bã zai sãme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, bãbu tsõro akanku, kuma ba ku zama kunã baƙin ciki ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 156,
            "translated_text": "Kuma 'yan wuta suka kirãyi 'yan Aljanna cẽwa: \"Ku zubo a kaumu daga ruwa kõ kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku.\" Su ce: \"Lalle ne Allah Ya haramtã su a kan kãfirai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 156,
            "translated_text": "\"Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe su.\" To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 157,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jẽ musu da Littãfi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yanã shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmani."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 157,
            "translated_text": "Shin, sunã jira, fãce fassararsa, a rãnar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabãni, sunã cẽwa: \"Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ da gaskiya. To, shin, munã da wasu mãsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kõ kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatãwa?\" Lalle ne sun yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙĩrƙirawa yã ɓace musu."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 157,
            "translated_text": "Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana!"
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 157,
            "translated_text": "Ku kirãyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓõye: lalle ne Shĩ, bã Yã son mãsuwuce iyãka."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 157,
            "translated_text": "Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Kuma ku kirãye shi sabõda tsõro da tsammãni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 157,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskõki, sunã bishãra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizãgizai mãsu nauyi,* sai Mu kõra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammãninku, kunã tunãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ya kamanta hadari da ruwa da Alƙur'ãni da abin da ya ƙunsa, da sifanta ƙasa busasshiya da jahilci, da zuciyar ĩmãni da gari mai kyau, da zũciyar kãfirci da mugun gari, kuma rãyuwa da ĩmãni da mutuwa da tãshi. Annabi ya ce: \"Misãlin abin da Allah Ya aiko ni da shi na ilmi da shiriya kamar ruwa ne mai yawa, ya sãmi wata ƙasa. To, ta zama daga cikinta akwai mai kyau, ta karɓi ruwa, sa'an nan ta tsirar da ciyãwa da tsãtse mai yawa. Kuma ta zama daga gare ta akwai rãfuka, suka riƙe ruwa Allah Ya amfãni mutãne da shi, suka sha, suka shãyar kuma suka yi shũka. Kuma daga cikinta akwai nau'i, faƙanƙani bã ya riƙon ruwa, kuma bã ya tsirar da ciyawa,wannan shi ne misalin wanda ya fahimci addinin Allah, kuma abin da Allah Ya aiko ni da shi, ya amfãne shi, ya sani kuma ya sanar, da wanda bai ɗauka kai ba gare shi, kuma bai karɓi shiriyar Allah ba wadda aka aiko ni da ita.\" Kuma anã fahimtar cewa kullum akwai faɗa mai dõgewa a tsakãninsu, dõmin sũ, kĩshiyõyin jũna ne."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "Kuma gari mai kyau, tsirinsa yanã fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya mũnana, (tsirinsa) bã ya fita, fãce da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ãyõyi dõmin mutãne waɗanda suke gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnẽnsa, sai ya ce: \"Yã mutãnẽna! Ku bauta waAllah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa. Lalle ne nĩ, inã yimuku tsõron azãbar wani Yini mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "Mashawarta* daga mutãnensa suka ce: \"Lalle ne mu, haƙĩƙa, Munã ganin ka a cikin ɓata bayyananniya.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kissar Nũhu da mutãnensa tanã nũna yanda Annabawa mãsu kãwo gaskiya ke yin faɗa da miyãgun mutãne mãsu ƙin gaskiya, sunã ƙõƙarin rufe ta haka kuma ƙissõshin da ke tafe a bãyanta sunã nũna yadda ƙarya ke faɗa da gaskiya, ta hanyõyi dabam-dabam."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã mutãnena! Bãbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu!\""
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "\"Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina; kuma inã yi muku nasĩha, kuma inã sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "\"Shin, kunã mãmãkin cẽwa ambato yã zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi, kuma dõmin ku yi taƙawa, kuma tsammãninku anã jin ƙanku?\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutãne ɗĩmautattu."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "Kuma zuwa ga Ãdãwa, ɗan'uwansu Hudu, ya ce: \"Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da wani abin bautã wa, waninSa. Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "Mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: \"Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Munã zaton ka daga maƙaryata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 158,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã mutãnena! Bãbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu!\""
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 159,
            "translated_text": "Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nĩ, gare ku, mai nasĩha ne amintacce."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 159,
            "translated_text": "\"Shin, kuma kun yi mãmãki cẽwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tunã a lõkacin da Ya sanyã ku mãsu mayẽwa daga bãyan mutãnen Nũhu, kuma Ya ƙãra muku zãti a cikin halitta. Sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah; tsammãninku kunã cin nasara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 159,
            "translated_text": "Suka ce: \"Shin, kã zo mana ne dõmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sunã bauta wa? To, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi idan kã kasance daga mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 159,
            "translated_text": "Ya ce: \"Haƙĩƙa azãba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kunã jãyayya da ni a cikin wasu sunãye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunãyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tãre da ku mai jira ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 159,
            "translated_text": "To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tãre da shi sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma ba su kasance mũminaiba."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 159,
            "translated_text": "Kuma zuwa ga Samũdãwa ɗan'uwansu, Sãlihu, ya ce: \"Yã mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tã zo muku daga Ubangijinku! wannan rãƙumar Allah ce, a gare ku, wata ãyã ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta har azãba mai raɗaɗi ta kãmã ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 160,
            "translated_text": "\"Kuma ku tuna a lõkacin da Ya sanyã ku mamaya daga bãyan Ãdãwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kunã riƙon manyan gidãje daga tuddanta, kuma kunã sassaƙar ɗãkuna daga duwãtsu; sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna mãsu fasãdi.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Fasãdi kalmar Lãrabci ce, ma'anarta ɓarna. Watau an ce musu kada su yi ɓarna cikin ɓarna dõmin haka nan zai sanya ɓarnar ta game ƙasa duka har bã zã a gane mũninta ba."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 160,
            "translated_text": "Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar*, ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare su: \"Shin, kunã sanin cẽwaSãlihu manzo ne daga Ubangijinsa?\" Suka ce: \"Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, mãsu ĩmãni ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Shugabanni suka cewa mabiyansu mãsu rauni, waɗanda suka yi ĩmãni da Manzon Allah Sãlihu. Amma ba su yi magana da mãsu ƙarfin ĩmãni ba, dõmin sun yanke ƙauna daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 160,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi girman kai suka ce: \"Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmãni da shi kãfirai ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 160,
            "translated_text": "Sai suka sõke rãƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: \"Yã Sãlihu! Ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan kã kasance daga manzanni!\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 160,
            "translated_text": "Sai tsãwa ta kãmã su, sabõda haka suka wãyi gari a cikin gidansu guggurfãne!"
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 160,
            "translated_text": "Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: \"Ya mutãnena! Lalle ne, haƙĩƙa, nã iyar muku damanzancin Ubangijina. Kuma nã yi muku nasĩha kuma amma bã ku son mãsu nasĩha!\""
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 160,
            "translated_text": "Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa: \"Shin, kunã jẽ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 160,
            "translated_text": "\"Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 161,
            "translated_text": "Kuma bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai suka ce: \"Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutãne ne mãsu da'awar tsarki!\""
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 161,
            "translated_text": "Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu wanzuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 161,
            "translated_text": "Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar mãsu laifi ta kasance!"
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 161,
            "translated_text": "Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: \"Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku tã zõ muku! Sai ku cika mũdu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Wannan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance mũminai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 161,
            "translated_text": "\"Kuma kada ku zauna ga kõwane tafarki kunã ƙyacẽwa, kuma kunã kangẽwa, daga hanyar Allah, ga wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma kunã nẽman ta ta zama karkatacciya, kuma ku tuna, a lõkacin da kuka kasance kaɗan, sai Ya yawaita ku, kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu fasãdi ta kasance:\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 161,
            "translated_text": "\"Kuma idan wata ƙungiya daga gare ku ta kasance ta yi ĩmãni da abin da aka aiko ni da shi, kuma wata ƙungiya ba ta yi ĩmãni ba, to, ku yi haƙuri, har Allah Ya yi hukunci a tsakãninmu; kuma Shi ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 162,
            "translated_text": "Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: \"Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu.\" Ya ce: \"Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ?\""
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 162,
            "translated_text": "\"Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Alah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 162,
            "translated_text": "Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: \"Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 162,
            "translated_text": "Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidansu, sunã guggurfãne."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 162,
            "translated_text": "Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemãsu hasãra!"
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 162,
            "translated_text": "Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: \"Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 162,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aika wani Annabi* a cikin wata alƙarya ba, fãce Mun kãma mutãnenta da azãba da cũta, tsammãninsu sunã yin ƙasƙantar da kai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Daga ãyã ta 94 zuwa ãyã ta l03 duka tãlĩƙi ne dõmin farkarwa ga muhimman manganganu waɗanda ƙissoshin Annabawan nan da mutãnensu suka ƙunsa, kuma aka ce haka dai sauran Annabawa da ba a faɗa ba suka zauna da mutãnensu a cikin faɗa a tsakanin gaskiya da ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 162,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: \"Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu.\" (sai su kõma wa kãfirci). Sai Mu kãmã su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancẽwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 163,
            "translated_text": "Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 163,
            "translated_text": "Shin, mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbar Mu ta jẽ musu da dare, alhãli kuwa sunã barci?"
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 163,
            "translated_text": "Kõ kuwa mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbarMu ta jẽ musu da hantsi, alhãli kuwa sunã wãsa?"
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 163,
            "translated_text": "Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra!"
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 163,
            "translated_text": "Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gãdon ƙasa ba daga bãyan mutãnenta cẽwa da Munã so, dã Mun sãme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukãtansu, sai su zama bã su ji?"
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 163,
            "translated_text": "Waɗancan alƙaryu Munã gaya maka daga lãbãransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa manzanninMu sun jẽ musu da hujjõji bayyanannnu; to, ba su kasance sunã yin ĩmãnida abin da suka ƙaryata daga gabãni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufẽwa a kan zukãtan kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 163,
            "translated_text": "Kuma ba Mu sãmi wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sãmi mafi yawansu, haƙĩƙa, fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 163,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Mun aika Musa,* daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãƙibar maɓarnata take.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * An fitar da ƙissar Bani Isrã'ila dabam, dõmin tã ƙunsa abũbuwa mãsu yawa na faɗa a tsakãnin ƙarya da gaskiya, ta hanyõyi mãsu yawa, a bayyane da ɓõye a cikin addini."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 163,
            "translated_text": "Kuma Musa ya ce: \"Ya Fir'auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "\"Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Ya ce: \"Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyananne!"
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi!"
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: \"Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "\" Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "\"Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: \"Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Ya ce: \"Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ku jẽfa.\" To a õkacin da suka jẽfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: \"Ka jẽfa sandarka.\" Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi!"
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu."
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 164,
            "translated_text": "Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "Suka ce: \"Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "\"Ubangijin Mũsã da Harũna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "Fir'auna ya ce: \"Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, mãkirci ne kuka mãkirta a cikin birni, dõmin ku fitar da mutãnensa daga gare shi; To, da sannu zã ku sani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "\"Lalle ne, inã karkãtse hannãyenku da ƙafãfunku daga sãɓãni, sa'an nan kuma, haƙĩƙa, inã tsĩre, ku gabã ɗaya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "\"Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai!* \"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Musulmi shi ne wanda ya sallama kansa ga hukunce-hukuncen Allah waɗanda wani Annabin Allah ya zõ da su, a cikin zãmaninsa. Sabõda haka ma'anar Musulmi shi ne mai sallamãwa ga hukuncin Allah, a kõwane zãmani, tun daga Ãdamu har zuwa Rãnar Ƙiyãma. Sai dai wannan al'umma ta Muhammadu tã keɓanta da sũnan Musulmi, addinin kuma da sũnan Musulunci."
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: \"Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?\" Ya ce: \"Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "Mũsã ya ce wa mutãnensa:* \"Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Maganar Mũsã ga Banĩ Isrã'ila tã nũna cewa sun ga azãbar ta yi musu yawa, har sun fãra zargin Mũsã da cewa ya sabbaba musu tsananin fitinar, da zõwarsa. Shi kuma ya lallãshe su da cewa, \"Kõme ya yi tsanani, to, sauƙinsa ya yi kusa.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 129,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "Suka ce: \"An cũtar da mu daga gabãnin ka zõ mana, kuma daga bãyan da kã zõ mana.\" Ya ce: \"Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 130,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 165,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun kãma mutãnen Fir'auna da tsananin shẽkaru (fari) da nakasa daga 'ya'yan itãce; Tsammãninsu sunã tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 131,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 166,
            "translated_text": "Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: \"Masĩfa ta sãme su, sai su yi shu'umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani!\""
        },
        {
            "ayah_number": 132,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 166,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabõda kai, mãsu ĩmãni ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 133,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 166,
            "translated_text": "Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa*; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ãyõyin da suka je musu a cikin lõkatai daban-daban dõmin a ja hankalinsu, kõ zã su yi ĩmãni. Kõwace ãyã tanã kwãna bakwai sunã wahala da ita, sa'an nan su rõƙi Mũsã ya yi addu'a a kuranye ta, sa'an nan a bãyan wani lõkaci sai su kõma wa kãfircinsu, kamar yadda ãyõyi mãsu biyar wannan suka bayyana."
        },
        {
            "ayah_number": 134,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 166,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: \"Yã Mũsã! Ka rõƙa mana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, haƙĩƙa Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã'ila tĩre da kai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 135,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 166,
            "translated_text": "To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarẽwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 136,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 166,
            "translated_text": "Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dõmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai."
        },
        {
            "ayah_number": 137,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 166,
            "translated_text": "Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan shi ne ƙarshen ƙissar faɗan gaskiya daga wajen Mũsã da ƙarya daga wajen Fir'auna da rundunarsa da dũkiyarsa. Haka dai ƙarya kõme duhunta, to, na banzane, a ƙarshe zã ta wãtsa."
        },
        {
            "ayah_number": 138,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 167,
            "translated_text": "Kuma Muka ƙẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutãne waɗanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: \"Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa \"* Ya ce: \"Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Farkon faɗan ƙarya da gaskiya a tsakãnin Banĩ Isra'ila da Mũsã wajen son kõmawa ga al'ãdu da ƙãri a cikin addini ta hanyar bidi'a."
        },
        {
            "ayah_number": 139,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 167,
            "translated_text": "\"Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sunã aikãtawa ƙarya ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 140,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 167,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 141,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 167,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe ɗiyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku,* Mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Lamĩrin Musulmi ne waɗanda ake yi wa magana yanzu a harshen Muhammadu, domin su wa'aztu da labarun mutanen farko."
        },
        {
            "ayah_number": 142,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 167,
            "translated_text": "Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin* kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan'uwansa, Hãrũna: \"Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ƙissõshin da ke tafe daga nan, suna nũna hani ga a ƙãra wani abu a cikin umarnin Allah. Kõwane irin ƙãri shi ne ake cewa bidi' a, kuma kõ dã an yi shi ne da nufin ƙwarai. Bidi'a tanã kãwo fitina ga mãsu ita. "
        },
        {
            "ayah_number": 143,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 167,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Mũsã ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: \"Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!\" Ya ce: \"Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni.\" Sa'an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: \"TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 144,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 168,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 145,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 168,
            "translated_text": "Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: \"Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu;* zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Mafi kyau daga Attaura shi ne wanda yake bayyananne; watau kada a yi aiki da abin da yake bai bayyana ba, sai da abin da ya bayyana, bayan an yarda cewa dukansu daga Allah suke."
        },
        {
            "ayah_number": 146,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 168,
            "translated_text": "Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai."
        },
        {
            "ayah_number": 147,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 168,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 148,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 168,
            "translated_text": "Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi*, jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Riƙon maraƙi shi ne bauta masa. Shĩ maraƙin an yĩ shi ne da mundãyen ƙawarsu, yanã da jiki irin na mutãne, kuma yanã rũri kamar na shãnu. Bã shi yin magana. Sun bauta masa a bãyan tafiyar Mũsã, a cikin kwana gõma na ƙãrin mĩƙãtin."
        },
        {
            "ayah_number": 149,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 168,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: \"Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 150,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 169,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa, yanã mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: \"Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a bãyanã! Shin, kun nẽmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?\" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: \"Yã ɗan'uwata! Lalle ne mutãnen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabõda haka kada ka dãrantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tãre da mutãne azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 151,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 169,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijina! Ka gãfarta mini, nĩ da ɗan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama!\""
        },
        {
            "ayah_number": 152,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 169,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walãkanci a cikin rãyuwar dũniya, zã su sãme su: Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu ƙirƙira ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 153,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 169,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka, sa'an nan suka tũba daga bãyansu kuma sukayi ĩmãni, lalle ne Ubangijinka daga bãyansu, haƙĩƙa, Mai gãfarane, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 154,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 169,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da fushin ya kwanta daga barin Mũsã, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke sũ, ga Ubangijinsu, mãsu jin tsõro ne."
        },
        {
            "ayah_number": 155,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 169,
            "translated_text": "Kuma Mũsã ya zãɓi mutãnensa, namiji saba'in dõmin miƙãtinMu. To, a lõkacin da tsãwa ta kãma su, ya ce: \"Yã Ubangijina! Dã Kã so, dã Kã halakar da su daga gabãni, sũ da ni. Shin zã Kahalaka mu, sabõda abin da wãwãyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba fãce fitinarKa Kanã ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kanã shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka gãfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãfara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 156,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 170,
            "translated_text": "\"Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ, mun tũba zuwa gare Ka.\" Ya ce: \"AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyinMu mũminai ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 157,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 170,
            "translated_text": "\"Waɗanda suke sunã bin Manzo*, Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla.yanã umurnin su da alhẽri, kuma yana hana su daga barin abin da bã a so; kuma yana halatta musu abũ- buwa masu dadi, kuma yana haramtarwar mũnana a kansu. Kuma yanã kãyar da nauyinsu daga barinsu, da ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, wa- ɗanda suka yi ĩmãni da shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka tai- make shi, kuma suka bi haske wan- da aka saukar tãre da shi, waɗan- nan ne mãsu cin nasara.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bayãnin bisharar Attaura da Linjĩla game da Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi. Kuma bishãrar da Allah ya gaya wa Annabi Mũsã wurin Miƙatinsa tãre da mutãne saba'in, dõmin maganar ɗinke take."
        },
        {
            "ayah_number": 158,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 170,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã kũ mutãne!* Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mutãne a nan, anã nufin Yahũdu da wasunsu. Anã kiran su zuwa ga abin da Attaura ta yi musu bishãra da zuwansa,a cikin sifõfin da ta sifantã Shi da su."
        },
        {
            "ayah_number": 159,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 170,
            "translated_text": "Kuma daga mutãnen* Mũsã akwai al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Anã nũna cewa duka yadda mutãne suka ɓãci, bã zã a rasa na kirki a cikinsu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 160,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 171,
            "translated_text": "Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: \"Ka dõki dũtsen* da sandarka.\"Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu.\"Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku.\"Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau dũtsen da ya gudu da tufafinsa ne a lõkacin da yake yin wanka dõmin a nũna wa Banĩ Isra'ila, waɗanda suka sõke shi da gwaiwa, cewa lãfiya lau yake. Kuma aka umurce shi da ɗaukar dũtsen, kuma yanzu aka umurce shi da ya dõke shi dõmin ruwa ya fito sabõda shansu."
        },
        {
            "ayah_number": 161,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 171,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da aka ce masu: \"Ku zauna ga wannan alƙarya*, kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Alƙaryar ita ce Baitil Maƙdis, bisa shugabancin Yũsha'u. 'Saryarwa,' watau a saryar mana da zunubinmu, yã Allah!, 'Shiga ƙõfa da sujada,' watau da tawãli'u."
        },
        {
            "ayah_number": 162,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 171,
            "translated_text": "Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana* watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Suka musanya hiɗɗa da hinɗa: watau alkama. (Aya ta 161) Sai aka saukar da azãba a kansu, sabõda haka wannan yã nũna cewa Allah ba ya son a musanya addininSa da kõme, sai dai mutum ya yi shi kamar yadda ya zo masa. Musanyawar umarnin, yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya. Ma'anar hiɗɗa ita ce kãyar da zunubi."
        },
        {
            "ayah_number": 163,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 171,
            "translated_text": "Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar* ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wata alƙarya anã ce da ita Ailata a bãkin gãɓar Bahr Al Kulzum a zãmanin Dãwũda, Allah ya umurce su a kan harshen Dãwũda su riƙi Jumma'a rãnar ĩdi, su yanke aiki a ciki, dõmin ibãda, sai suka ƙi Jumma'a suka zãɓi Asabar, ma'anarsa yankewa. To, sai Allah ya tsananta musu, Ya hana su farautar kĩfi a rãnar Asabar, Ya halatta musu shi, a sauran kwãnukan mãko. Sai a rãnar Asabar, su sãmi kĩfi wani kan wani, amma sauran kwanuka bã su sãmunsa haka. Sai Iblis ya sanar da su ga su aikata matarar ruwa a gefen tekun, a rãnar Asabar, su bũde kifi ya shiga su rufe, har rãnar Lahadi su kãma. Sai garin ya kasu uku: kashi ɗaya suka yi farauta, wasu suka hana, sũ kuma suka yi gãru a tsakãninsu da mãsu yi, na uku ba su yi farautar ba kuma ba su hana ba. A bãyan 'yan kwãnaki sai aka mayar da mãsu farautar birai, sa'an nan suka mutu."
        },
        {
            "ayah_number": 164,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 172,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: \"Don me kuke yin wa'azi ga mutãne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani?\" Suka ce: \"Dõmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin taƙawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 165,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 172,
            "translated_text": "To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma waɗanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasiƙanci."
        },
        {
            "ayah_number": 166,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 172,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: \"Ku kasance birai ƙasƙantattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 167,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 172,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, zã Ya aika a kansu (Yahũd), zuwa, Rãnar¡iyãma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 168,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 172,
            "translated_text": "Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 169,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 172,
            "translated_text": "Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar* wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: \"Zã a gãfarta mana. \"Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sifar ƙasƙantacciya ita ce kãyan dũniya na haram, kamar rashawa. An kira ta sifa dõmin bã aba ce mai tsayuwa da kanta ba, kuma bã sifar abin kirki ba, sai dai abin da yake halaka ne nan da nan. Tãke gaskiya faɗa ne da addini, watau yaƙi a tsakãnin gaskiya da ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 170,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 172,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke riƙẽwa da laittãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 171,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 173,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse* sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): \"Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * A lõkacin da Mũsã ya karanta wa Banĩ Isra'ila Attaura da hukunce-hukuncen da suke a cikinta, mãsu wuya gare su, sai suka ƙi yarda da ita. Allah Ya yanka dũtse daidai da garinsu, Ya ɗaukaka shi a kansu, ko su yi aiki da ita kõ ya fãɗa a kansu. Daga nan idan suna salla, sai su yi sujada da rabin gõshi a kan tsãgin hagu, sunã kallon dũtsen. Kuma yin sujada a haka ya zama sunnarsu har yanzu. Watau bã a iya tsare gaskiya daga yãƙin ƙarya sai an yi amfãni da wani ƙarfi."
        },
        {
            "ayah_number": 172,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 173,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): \"Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?\" Suka ce: \"Na'am! Mun yi shaida!\" (ya ce): \"Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau kada ku ce ba ku san wannan alkawari ba."
        },
        {
            "ayah_number": 173,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 173,
            "translated_text": "Kõ kuwa ku ce: \"Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa, Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu ɓãtãwa suka aikata?\""
        },
        {
            "ayah_number": 174,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 173,
            "translated_text": "Kuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 175,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 173,
            "translated_text": "Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa* ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Asalin ƙissar anã cewa daga Bil'amu ɗan Bã'ura ne; Allah ya bã shi ilmi, sai ya bar ilmin. Yanã daga cikin mãlaman Banĩ Isrã' ĩla, yã kasance wanda ake karɓar addu'arsa, sunã gabatar da shi a cikin tsanance-tsanance, sai Mũsã ya aike shi zuwa ga sarkin Madyana ya kirãye shi zuwa ga Allah. Sai sarkin ya yanka masa ƙasa, ya bã shi, sai ya bi addinin sarkin, ya bar addinin Mũsã. Ya zama misãli ga duk mãlamin da bai yi aiki da ilminsa ba. Idan mãlami ya halaka, to, yã fi Shaiɗan sharri dõmin haka shaiɗan yake binsa wajen taimakon ƙarya a kan gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 176,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 173,
            "translated_text": "Kuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 177,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 173,
            "translated_text": "Tir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta."
        },
        {
            "ayah_number": 178,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 173,
            "translated_text": "Wanda* Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.<br \/>\n____________________<br \/>\n* An sifanta Musulmi da abin da aka sifanta Yahũdu da shi cewa a cikinsu akwai na kirki, kuma akwai miyãgu, dõmin yãƙi a tsakãnin gaskiya da ƙarya ya dõge."
        },
        {
            "ayah_number": 179,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 174,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu."
        },
        {
            "ayah_number": 180,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 174,
            "translated_text": "Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau.* Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Waɗanda suke rõƙon Allah bã da sũnãyenSa mãsu kyau ba, sũ ne aka sifanta da dabbõbi, har dabbõbi sun fi su, dõmin dabba tanã gudun abinda yake cũtar ta, amma sũ ba su san abin da yake cũtar su ba, balle su guje shi. Kuma anã fahimtar cewa bã a rõƙon Allah da wani sũna Nãsa, idan bai kasance a cikin sanayenSa mãsu kyau ba, sai fa idan ya zama a dunƙule ne, kamar a ce, \"Ya Allah inã rõƙonKa da sũnayenKa waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba,\" dõmin Hadĩsi ya nũna a yi haka. Kiran Allah bã da sunãyenSa mãsu kyau ba yana cikin yãƙi a tsakãnin ƙarya da gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 181,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 174,
            "translated_text": "Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma, da ita suke yin ãdalci."
        },
        {
            "ayah_number": 182,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 174,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 183,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 174,
            "translated_text": "Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 184,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 174,
            "translated_text": "Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu?* shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Watau, Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bã ya da hauka sai hankali, sabõda haka mãsu yin addini da hauka, kamar mãsu da'awar tasawwufi, ƙarya suke yi, sunã faɗa ne da gaskiya. Kuma sũkar mai wa'azi da sũnãye faɗa da gaskiya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 185,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 174,
            "translated_text": "Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To, da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 186,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 174,
            "translated_text": "Wanda Allah Ya ɓatar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin ɓatarsu sunã ɗimuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 187,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 174,
            "translated_text": "Sunã tambayar ka* daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: \"Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam.\" sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: \"Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Tambayar abin da Allah bai bayyana shi ba, kamar Rãnar Tãshin Kiyãma, yãƙi ne a tsakanin ƙarya da gaskiya. cewa wani mutum yã san gaibi ko yanã iya kãwo alheri kõ ya tunkuɗe wani sharri, ƙarya ne, kuma faɗã da gaskiya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 188,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 175,
            "translated_text": "Ka ce: \"Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 189,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 175,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare* ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: \"Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance dagamãsu gõdiya.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Asalin halitta, rai guda ce, watau Ãdam, Allah ya fitar da Hauwã'u daga Ãdamu, ya mayar da ita mãtarsa, daga gare su zũriya ta yaɗu, kuma ya zama sunnar rai, namijin ya natsu zuwa ga macen. Kuma daga nan zama ya ci gaba har idan mace ta yi ciki, bã ta damuwa da shi sai yã yi nauyi, ita da miji su dinga addu'a, sunã rõƙon Allah. A bãyan bukãtarsu tã biya sai su manta da Allah, su ɗõra jingina abũbuwa zuwa ga sabubbansu, su bar tunãnin Mai sabbabawa. Daga nan abu ya yi zurfi har ya kasance shirki; bauta wa wani tãre da Allah, yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 190,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 175,
            "translated_text": "To, a lõkacin da Ya bã su abin ƙwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki."
        },
        {
            "ayah_number": 191,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 175,
            "translated_text": "Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 192,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 175,
            "translated_text": "Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka!"
        },
        {
            "ayah_number": 193,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 175,
            "translated_text": "Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne!"
        },
        {
            "ayah_number": 194,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 175,
            "translated_text": "Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya!"
        },
        {
            "ayah_number": 195,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 175,
            "translated_text": "Shin sunã da ƙafãfu da suke yin tafia da su? Kõ sunã da hannãye da suke damƙa da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: \"Ku kirãwo abũbuwan* shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurãra mini.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyar da tsoro da wani abin bautãwa ko jingina wata bukãta a gare shi, duka yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 196,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "\"Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai,\""
        },
        {
            "ayah_number": 197,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "\"Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 198,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani."
        },
        {
            "ayah_number": 199,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Bayãnin sifõfin mai wa'azi, watau mataimakin gaskiya a kan ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 200,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 201,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra."
        },
        {
            "ayah_number": 202,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bã su taƙaitãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 203,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: \"Don me ba ka ƙãga ta ba?\" Ka ce: \"Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 204,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "Kuma idan an karanta* Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bãyãn an sifanta Alƙur'ãni da cewa abin kula ne ga mãsu ĩmãni, sai kuma ya yi umurni da saurãre, a lõkacin da ake karatunsa. Sauraren yana wajabta a cikin salla, idan lĩman ya bayyana karãtu kuma da a cikin huɗubar Jumma'a. Yanã zama mustahabbi ga sauran lõkatai. Kur'ãni shi ne abin da ake wa'azi da shi kuma shi ne ãyã da kansa. Hana saurãrensa yãƙi ne da gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 205,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci* Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sa'an nan kuma ya yi umurni da ambaton Allah da addu'a a farko da ƙarshen rãna kamar yadda ya yi umurni da yin salla a waɗannan lõkatai, watau wannan shine makãmin gaskiya a kan ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 206,
            "surah_number": 7,
            "page_number": 176,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 177,
            "translated_text": "Suna tambayar ka* ga ganĩma. ka ce: \"Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Yã fãra Sũrar da tambayar Sahabbai ga Annabi cewa. wãne ne ya fi cancanta da dũkiyar ganĩmar da aka sãmu a yãƙin Badar Babba, samãri mayãƙa kõ tsõfaffi mãsu bãyar da shãwara da ra'ayõyinsu, mãsu kyau. Sa'annan ya yi jawãbi da cewa: \"Ka ce ganimar ta Allah ce da ManzonSa,\" sabõda dalĩlan da suke tafe ga ayõyin da suke biye. Ana nufi wanke sõja daga jãyayya a kan dũkiya. AllahYa fi sani."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 177,
            "translated_text": "Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 177,
            "translated_text": "Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau sunã yin ibãda ta jiki da ta dũkiya wãjiba da nãfila."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 177,
            "translated_text": "Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 177,
            "translated_text": "Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 177,
            "translated_text": "Sunã jãyayya da kai a cikin (sha'anin) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 177,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin* da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai;<br \/>\n____________________<br \/>\n * Asalin fitar Musulmi zuwa Badar shi ne Annabi ya ji lãbãrin Abu Sufyãna yã fito daga Makka da ãyari zuwa Shãm, watau \"Syria\" , sai ya fita dõmin a kãma shi, suka sãmi Abu Sufyãna yã shige da dũkiya, sabõda haka Annabi daga Badar ya kõma Madĩna. Wannan fita, anã kiran ta Badar karama. Da Abu Sufyãna ya sãmi lãbãri, sai ya aika wa Kuraishãwa, dõmin su fito, su tsare dũkiyarsu daga Musulmi. Annabi, da ya ji lãbãrin kõmõwar Abu Sufyãna, sai ya fita tãre da jama'arsa, wanda ya ji Yanã son fita, kuma yanã da abin hawa. Abu Sufyãna tãre da ãyari sũ ne wajen da bãbu ƙaya. Yaƙin Kuraishãwa shĩ ne wajen da yake da ƙaya. Musulmi a tsakiya. Abu Sufyãna ya saki hanya ya tsĩra.Ya nemi Kuraishãwa da su kõma, Abu Jahal ya ce sai Allah Yã yi hukunci a tsakãninsu da Muhammadu wanda ya kãtse zumuntã, ya bar addinin iyãye."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 177,
            "translated_text": "Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 178,
            "translated_text": "A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku tairnako, sai Ya karɓa muku cẽwa: \"Lalle ne Nĩ, Mai taimakon ku ne da dubu daga malã'iku, jẽre.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 178,
            "translated_text": "Kuma Allah bai sanya shi ba fãce Dõmin bishãra, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi, kuma taimakon, bai zama ba fãce daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 178,
            "translated_text": "A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma Yanã saukar da ruwa* daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku, kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * A lõkacin zãfi ne na bazara, kuma aka faralta azumi, sai Allah Ya saukar da ruwa daidai da sansanin Musulmi, suka shã, suka yi wanka sa'an nan kuma aka daddale musu rairayi dõmin sauƙin tafiya."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 178,
            "translated_text": "A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: \"Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Sa'an nan kuma Annabi da umurnin Allah ya ɗebi tsakuwa da hannunsa mai daraja ya jefa a jihar kãfirai. Bãbu wanda ya rage a cikinsu, fãce tsakuwar nan tã shiga a cikin idãnunsa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 178,
            "translated_text": "Wancan ne, dõmin lalle ne sũ, sunã sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 178,
            "translated_text": "Wancan ne: \"Ku ɗanɗane shi, kuma lalle ne akwai azãbar wuta ga kãfirai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 178,
            "translated_text": "Yã kũ wacɗanda suka yiĩmãni! Idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta ga yãƙi, to, kada ku jũya musu bãyayyakinku."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 178,
            "translated_text": "Kuma duka wanda* ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita!<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Gudu a wurin yãƙin Jihãdi shĩ ne mafi girman haram duka, matuƙar kãfirai ba su fi ninki biyu na adadin Musulmi ba, kamar yadda zai zo. Wanda ya yi gudu a wurin jihãdi kamar yã nemi kãfirci ya rinjãyi Musulunci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 179,
            "translated_text": "To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa;* kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kisan da aka yi musu, Allah ne Ya kashe su, haka Annabi ya ɗebi tsakuwa da hannunsa mai daraja ya jefa wa kãfirai, tsakuwar ta shiga cikin idãnun kõwane ɗaya daga cikinsu. To, wannan jĩfar daga Allah take. Sabõda haka duk ganĩmar dai ta Allah ce da ManzonSa, sai yadda Ya so, zã a raba ta."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 179,
            "translated_text": "Wancan ne, kuma lalle ne, Allah Mai raunana kaidin kãfirai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 179,
            "translated_text": "Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu, to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama'arku bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah Yanã tãre da mũminai!"
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 179,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku jũya daga barinSa, alhãli kunã ji."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 179,
            "translated_text": "Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka ce: \"Mun ji, alhãli kuwa sũ bã su ji.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 179,
            "translated_text": "Lalle ne, mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne kurãme, bẽbãye, waɗanda bã, su yin hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 179,
            "translated_text": "Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da su, haƙĩƙa, dã sun jũya, alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 179,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 179,
            "translated_text": "Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 180,
            "translated_text": "Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 180,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 180,
            "translated_text": "Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da 'ya'yanku, wata fitina ce, kuma lalle ne Allah, a wurinSa, akwai ijãra mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 180,
            "translated_text": "Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma'abũcin falalã Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 180,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da waɗanda* suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ƙuraishãwa suka tãru sunã shãwarar yadda zã su yi da Muhammadu; kõ su ɗaure shi a cikin gida, kõ su kashe shi, kõ su kõre shi. Ra'ayinsu ya tsaya ga su kashe shi da zãɓaɓɓun mutãne daga kõwace ƙabĩla yadda danginsa, Banĩ Hãshim, bã su iya faɗa da dukkan Lãrabãwa, har su kõma ga diyya. A rãnar da suka shirya kashe shi, Allah Ya umurce shi da hijira zuwa Madĩna. A lõkacin da ya fita daga gidansa ya iske su tsaitsaye, sunã barci, ya zuba turɓãya a kunnuwansu, sa'annan ya shige suka tafi tãre da Abũbakar, suka sauka a cikin kõgon dũtsen Thaur. Bãyan kwãnaki uku, suka fita zuwa Madina."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 180,
            "translated_text": "Kuma idan aka karanta, ãyõyinMu a kansu, sukan ce: \"Lalle ne mun ji dã muna so, haƙĩƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba fãce tãtsunãyõyin mutãnen farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 180,
            "translated_text": "A lõkacin da suka ce: \"Yã Allah! Idan wannan ya kasancc shĩ ne gaskiya daga wurinKa, sai Ka yi ruwan duwãtsu, a kanmu, daga sama, kõ kuwa Kazõ mana da wata azãba, mai raɗaɗi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 180,
            "translated_text": "Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu,* kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Rãyuwar Annabi a cikin mutãne aminci ne daga azãba, haka kuma yin istigfãri aminci ne. Wanda ke son wadãta da aminci daga Allah, sai ya lazimci istigfãri da bin sunnar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 181,
            "translated_text": "Kuma mẽne ne a gare su da Allah ba zai yi musu azãba ba, alhãli kuwa sũ, sunã kangẽwa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Bãbu majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 181,
            "translated_text": "Kuma sallarsu a wurin ¦ãkin ba ta kasance ba fãce shẽwa da yãyã; sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 181,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadãma a kansu, sa'an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama ake tãra su;"
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 181,
            "translated_text": "Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a kan sãshe, sa'an nan Ya shirga shi gabã daya, sa'an nan Ya sanyã shi a cikin Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 181,
            "translated_text": "Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 181,
            "translated_text": "Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa Mai gani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 181,
            "translated_text": "Kuma idan sun jũya, to, ku sani cẽwa lalle Allah ne Majiɓincinku: Mãdalla da Majiɓinci, kuma mãdalla da Mai taimako, Shĩ."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 182,
            "translated_text": "Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi* ganĩma daga wani abu, to, lalle ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Daga farkon sũrar har zuwa a nan, anã bayãnin cewa ganĩmar Badar bã ta kõwa ba ce fãce Allah da ManzonSa; to, a nan Yanã bayãyin yadda zã a raba dũkiyar, kuma wannan rabon, ya zama sunna ga dukkan dũkiyar ganĩma da Musulmi suka sãmu da yãƙi kõ hari."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 182,
            "translated_text": "A lõkacin da kuke a gãɓa ta kusa sũ kuma sunã a gãɓa tanẽsa, kuma ãyarin yana a wuri mafi gangarãwa daga gare ku, kuma dã kun yi wa jũna wa'adi, dã kun sãɓa ga wa'adin; kuma amma dõmin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatãwa. Dõmin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rãyuwa ya rãyu daga shaida, kuma lalle Allah ne, haƙĩƙa, Mai ji Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 182,
            "translated_text": "A lõkacin da Allah Yake nũna maka sũ sunã kaɗan, a cikin barcinka, kuma dã Ya nũna maka su sunã da, yawa, lalle ne dã kun ji tsõro, kuma lalle ne dã kun yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma amma Allah Yã tsare ku: Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake a cikin ƙirãza."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 182,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Yake nũna muku su, a lõkacin da kuka haɗu, a cikin idanunku sunã kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu dõmin Allah Ya hukunta wani al'amari wanda ya kasance abin aikatãwa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'umurra."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 182,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci* Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ambaton Allah bayyane yã fi kyau a wurin yãƙi da wurin harama da hajji kõ umra, kuma da lõkacin da ake fitã zuwa ga masallacin ĩdi. Wurin da bã waɗannan wurãre uku ba, ambaton Allah, ya zama asirce yã fi kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 183,
            "translated_text": "Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jãyayya har ku raunana kuma iskarku ta tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 183,
            "translated_text": "Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu,* sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kada Musulmi su fita zuwa yãƙi da nũna alfahari da kiɗe-kiɗe da giya da mãtã da maganganun alfãsha, kamar yadda Kuraishãwa suka fita zuwa Badar; ku fita da tawãlu'i da zikirin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 183,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Shaiɗan* ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: \"Bãbu marinjayi a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku.\" To, a lõkacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: \"Lalle ne nĩ barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Shaiɗan ya fita zuwa ga Ƙuraishãwa a cikin sũrar surãƙ atu bn Mãlik, ya ce musu Yanã tãre da su, kuma shi ne maƙwabcinsu; watau danginsa, Kan'ãnãwa, bã zã su taɓã su ba da yãƙi, a lõkacin da suke yãƙi da Muhammadu. Bãyan haka da ya tafi Badar yã ga Malã'iku, shĩ ne ya kõma bãya, yanã c ewa wai shi yanã tsõron Allah; watau yanã yi wa Ƙuraishãwa izgili; sũ ne bã su tsõron Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 183,
            "translated_text": "A lõkacin da munãfukai da waɗanda suke akwai cũtã a cikin zukãtansu, suke cẽwa: \"Addĩnin waɗannan yã rũɗe su\" Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 183,
            "translated_text": "Kuma dã kã gani, a lõkacin da Malã'iku suke karɓar rãyukan waɗanda suka kãfirta, sunã dukar fuskõkinsu da ɗuwãwunsu, kuma suna cẽwa: \"Ku ɗanɗani azãbar Gõbara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 183,
            "translated_text": "\"Wancan sabõda abin da hannãyenku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne, Allah bai zama Mai zãlunci ba ga, bãyinSa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 183,
            "translated_text": "\"Kamar al'ãdar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke gabãninsu, sun kãfirta da ãyõyin Allah, sai Allah Ya kãma su da zunubansu. Lalle Allah ne Mai ƙarfi, Mai tsananin uƙũba."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 184,
            "translated_text": "\"Wancan ne, dõmin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda ya ni'imtar da ita a kan wasu mutãne ba fãce sun sãke abin da yake ga rãyukansu, kuma dõmin lalle Allah ne Mai jĩ, Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 184,
            "translated_text": "Kamar al'adar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata game da ãyõyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, sabõda zunubansu, kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna. Kuma dukansu sun kasance ne mãsu zãlunci."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 184,
            "translated_text": "Lalle mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne waɗanda suka kãfirta, sa'an nan bã zã su yi ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 184,
            "translated_text": "Waɗanda ka yi ƙullin alkawari da su, daga gare su, sa'an nan kuma sunã warwarewar alkawarinsu a kõwane lõkaci kuma sũ, bã su yin taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 184,
            "translated_text": "To, in dai ka kãma su a cikin yãƙi, sai ka kõre* waɗanda suke a bãyansu, game da su, tsammãninsu, zã su dinga tunãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wãtau a kashe waɗanda aka kãma dõmin saura su gani su ji tsõro."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 184,
            "translated_text": "Kuma in ka ji tsõron wata yaudara daga wasu mutãne, to, ka jẽfar da alkawarin, zuwa gare su, a kan daidaita: Lalle ne Allah, bã Ya son mayaudara."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 184,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta kada su yi zaton sun tsẽre: Lalle ne sũ, bã zã su gãgara ba."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 184,
            "translated_text": "Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi,* kuma da ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, zã a cika muku sakamakonsa, kuma kũ ba a zãluntar ku.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Tattali daga wani ƙarfi, ya haɗa dukkan abin da zai yiwu a yi yãƙin abõkin gãba da shi. A yanzu daga bindiga da abin da yake sama da ita, shi ne zã a yi tattali."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 184,
            "translated_text": "Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma ka dõgara ga Allah: Lalle ne Shĩ, Mai ji ne Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 185,
            "translated_text": "Kuma idan sun yi nufin su yaudare ka, to, lalle ma'ishinka Allah ne, Shĩ ne wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa, kuma da mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 185,
            "translated_text": "Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yake cikin ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba, kuma amma Allah Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 185,
            "translated_text": "Ya kai Annabi! Ma'ishinka Allah ne, kai da wanda ya biye maka daga mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 185,
            "translated_text": "Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da mũminai a kan yãƙi. Idan mutum ashirin mãsu haƙuri sun kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan kuma idan ɗari suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu daga waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ, mutãne ne bã su fahimta."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 185,
            "translated_text": "A yanzu Allah Yã sauƙaƙe daga gare ku, kuma Yã sani cẽwa lalle ne akwai mãsu rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, mãsu haƙuri, suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 185,
            "translated_text": "Bã ya kasancewa* ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayan da Musulmi suka ci nasara a Badar, suka kama Kuraishãwa a cikinsu har da Abbas baffan Annabi. Sai Annabi ya shãwarci Sahabbansa ga abin da zã su yi da kãmammu. Abubakar ya ce wa Annabi, \"Mutãnenka ne, ka sake su.\" Sa'an nan ya nemi Umar shãwara, ya ce masa: \"Ka kashe su.\" Sai ya karɓi fansa daga gare su. Bãyan haka Alƙur'ãni ya sauka da ƙarfafa ra'ayin Umar na a kashe su, ya fi. Amma tun da an riga an zartar da fansar, shĩ ke nan."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 185,
            "translated_text": "Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta,* dã azãba mai girma daga Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Abin da ya gabãta na Littãfi shi ne, amma Allah ne Masanin haƙĩƙa, abin da yake a cikin sũrar Ãl Imrãna, ãyã ta l59, inda aka bai wa Annabi umurnin ya yi shãwara da Sahabbansa ga abin da ya shãfi yãƙi, sa'an nan kuma ya dõgara ga Allah wajen zartar da abin da ya zãɓã daga shãwarar da suka bã shi."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 185,
            "translated_text": "Sabõda haka, ku ci daga abin da kuka sãmu ganĩma, Yanã halal mai kyau. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 186,
            "translated_text": "Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: \"Idan Allah Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 186,
            "translated_text": "Kuma idan sun yi nufin yaudararka, to, haƙĩƙa, sun yaudari Allahdaga gabãni sai Ya bãyar da dãmã daga gare su: Kuma Allah ne Masani, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 186,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma ba su yi hijira* ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A farkon Musulunci hijira sharaɗi ce ga shiga cikin waliccin Musulmi, amma bãyan da Musulunci ya yi ƙarfi, hijira ba ta zama sharaɗi ba, sai dai tanã wajaba ga Musulmi ya tashi daga inda bã ya iya tsare addininsa zuwa ga inda yake iya tsare shi, matuƙar bãbu wata wahala mai tsanani. Ana taimakon Musulmin da bai yi hijira ba ga abin da bai shãfi warware alkawarin Musulmi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 186,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta sãshensu ne waliyyan sãshe, idan ba ku aikata shi ba, wata fitina zã ta kasance a cikin ƙasa, da fasãdi babba."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 186,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako, waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani abinci na karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 8,
            "page_number": 186,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni daga bãya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihãdi tãre da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma'abũta zumunta, sãshensu ne waliyyan* sãshe a cikin Littãfin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kõme Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Walicci shi ne kusanta da lizimtar wajabcin taimakon jũna.A farkon Musulunci, Musulmi bã su da walicci a kan wani Musulmi, sai idan yã yi hijira zuwa Madĩna. Bãyan cin Makka da wãtsuwar Musulunci sai waliccin Musulmi ya wajaba a kan kõwane Musulmi a inda duk yake, a cikin dũniya, gwargwadon hãli, amma kuma a cikin haka mafi kusantar zumuntã shi ne mafi cancanta da waliccin kõwane Musulmi, har dai ga abin da ya shãfi hãlãye na zaman mutum kamar aure da gãdo, da sauransu, kamar yadda littattafan sunna suka bayyana, a can cikin bãbin walicci."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 187,
            "translated_text": "Barranta daga Allah da ManzonSa zuwa ga waɗanda kuka yi wa alkawari daga mãsu shirki*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kãfirai iri uku ne: mãsu addinin al'ãda kamar Lãrabãwa sũ ne mãsu shirki, sa'an nan mãsu bin Littãfi shãfaffe watau Yahudu da Nasãra sa'an nan da munãfukan wannan al'umma. Ya fãra da mãsu shirki da bayãnin irin ayubansu, sa'an nan ya yi bayãnin sauran kamar haka."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 187,
            "translated_text": "Sabõda haka ku yi tafiya a cikin ƙasa watã huɗu,* kuma ku sani lalle kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne, kuma lalle Allah ne Mai kunyatar da kãfirai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyan yanke sulhu, Allah Yabai wa kãfirai watã huɗu na amãna, dõmin su ƙãre harkõkinsu da wasu ma'amalõli da suka ƙulla tãre da Musulmi, sa'an nan yãƙi ya tãshi. Anã nufin mãsu addinin al'ãda na shirki a nan."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 187,
            "translated_text": "Kuma da yẽkuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutãne, a Rãnar Haji Babba cẽwa lallene Allah Barrantacce ne daga mãsu shirki, kuma ManzonSa (haka). To, idan kun tũba to shi ne mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun jũya, to, ku sani lalle ne kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka kãfirta, da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 187,
            "translated_text": "Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga mãsu shirki, sa'an nan kuma ba su rage ku da kõme ba, kuma ba su taimaki kõwa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare su, har ga iyakar yarjẽjẽyarsu. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 187,
            "translated_text": "Kuma idan watanni, mãsu alfarma suka shige, to, ku yãki mushirikai inda kuka sãmẽ su, kuma ku kãmã su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madãkata. To, idan sun tũba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka to ku sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 187,
            "translated_text": "Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa. Wancan fa domin lalle ne su, mutãne ne waɗanda ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 188,
            "translated_text": "Yãya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasancẽwa ga mushirikai, fãce ga waɗanda kuka yi wa alkawari wurin Masallaci Mai alfarma? To matuƙar sun tsaya sõsai gare ku, sai ku tsayu sõsai gare su. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 188,
            "translated_text": "Yãya, alhãli idan sun ci nasara a kanku, bã zã su tsare wata zumun ta ba a cikinku, kuma haka wata amãna, sunã yardar da ku da bãkunansu kuma zukãtansu sunã ƙi? Kuma mafi yawansu fãsiƙai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 188,
            "translated_text": "Sun saya da ãyõyin Allah, 'yan kuɗi kaɗan, sa'an nan suka kange daga hanyar Allah. Lalle ne sũ, abin da suka kasance sunã aikatãwa yã mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 188,
            "translated_text": "Bã su tsaron wata zumunta a cikin mũminai, kuma haka bãsu tsaron wata amãna. Kuma waɗannan ne mãsu ta'adi."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 188,
            "translated_text": "Sa'an nan idan sun tũba* kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to, 'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Rukunõnin Musulunci biyar ne: Kalmar shahãda da salla da azumi da zakka da hajji ga Ɗãkin Allah. Ana yãƙar mutum sabõda barin uku daga cikinsu, watau kalmar shahãda da salla da zakka kawai. Kuma uku sunã lazimtar mawãdaci da matalauci. Su ne kalmar shahãda da salla da azumi kawai. Amma zakka da hajji sai ga mai hãlin yi da wadãta."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 188,
            "translated_text": "Kuma idan suka warware rantsuwõyin amãna daga bãyan alkawarinsu, kuma suka yi sũka a cikin addininku, to, ku yaki shũgabannin kãfirci. Lalle ne sũ, bãbu rantsuwõyin amãna a gare su. Tsammãninsu sunã hanuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 188,
            "translated_text": "Shin, bã ku yaƙin mutãne, waɗanda suka warware rantsuwõyinsu, kuma suka yi niyya ga fitar da Manzo, kuma sũ ne suka fãra muku, tun a farkon lõkaci? Shin kunã tsõron su ne? To, Allah ne marfi cancantar ku ji tsõronSa, idan kun kasance mũminai!"
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 189,
            "translated_text": "Ku yãƙe su, Allah Ya yi musu azabã da hannãyenku, kuma Ya kunyatar da su, kuma Ya taimake ku, kuma Ya warkar da ƙirãzan mutãne mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 189,
            "translated_text": "Kuma Ya tafĩ da fushin zukãtansu, kuma Ya karɓi tũba a kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 189,
            "translated_text": "Kõ kunã zaton* a bar ku, tun Allah bai bayyana waɗanda suka yi jihãdi ba daga gare ku, kuma sũ ba su riƙi wani shigeba, baicin Allah da ManzonSa da mũminai? Kuma Allah ne Mai jarrabãwa ga abin da kuke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau kunã zaton ku shiga Aljanna sabõda cewarku, \"Mun yi ĩmãni,\" kawai? Ã'aha! Sai Allah Yã bayyanar da mai gaskiyar ĩmãni game da jihãdi, kuma gaskiyar ĩmãni itace ce rashin sõyayya da wanin Allah da ManzonSa da mũminai, duka wanda ya so wani abu baicinsu, to, bã mũmini ba ne, bã zai shiga Aljanna ba dõmin wai yã yi ĩmãni kawai. Ma'anar son Allah da son Annabi shi ne rashin sãɓa wa umurninSa. Ma'anar son wanin Allah da wanin Annabi, shi ne ka yi abin da wanin nan yake so, alhãli kuwa a wajen yinsa akwai sãɓa wa Allah da ManzonSa."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 189,
            "translated_text": "Bã ya kasancewa ga mãsu shirki su rãya masallatan Allah, alhãli kuwa sunã mãsu bãyar da shaida a kan rãyukansu da kafirci, waɗannan ayyukansu sun ɓãci, kuma a cikin wutã sũ madawwama"
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 189,
            "translated_text": "Abin sani kawai, mai rãya masallãtan Allah, shĩ ne wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya tsayar da salla kuma ya bãyar da zakka, kuma bai ji tsõron kõwa ba fãce Allah. To, akwai tsammãnin waɗannan su kasance daga shiryayyu."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 189,
            "translated_text": "Shin, kun sanya shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 189,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi, a cikin hanyar Allah, da dũkiyõyinsu, da rãyukansu, sũ ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah, kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 190,
            "translated_text": "Ubangijinsu Yanã yi musu bishãra da wata rahama daga gare shi, da yarda, da gidãjen Aljanna. sunã da, a cikinsu, ni'ima zaunanniya."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 190,
            "translated_text": "Sunã madawwamã a cikinsu, har abada. Lalle ne Allah a wurinSa akwai lãda mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 190,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi ubanninku da 'yan'uwanku masõya, idan sun nũna son kãfirci a kan ĩmãni*. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, waɗannan sũ ne azzãlumai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Idan an umurci mutum ya rabu da ubansa da 'yan'uwansa kãfirai, sabõda shĩ yanã Musulmi, to, ga waninsu abin yã fi ƙarfi."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 190,
            "translated_text": "Ka ce: \"Idan ubanninku da ɗiyanku da 'yan'uwanku da mãtanku da danginku da dũkiyõyi, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsõron tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya sõyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihãdi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah Ya zo da umurninSa! Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 190,
            "translated_text": "Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a cikin wurãre mãsu yawa, da Rãnar Hunainu,* a lõkacin da yawanku ya bã ku sha'awa, sai bai amfãnar da ku da kõme ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka jũya kunã mãsu bãyar da bãya.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Hunainu wani wãdi ne a tsakãnin Makka da Ɗã'ifa inda Musulmi suka yi yãƙi da Hawãzinãwa, a cikin Shawwal shekara ta takwas. Yawan Musulmi ya rũɗe su har suka ce: \"Yau bã zã a rinjãye mu ba, sabõda ƙaranci.\" Yawansu yã kasance dubũ gõma sha biyu, kuma kãfirai dubũ huɗu, sai suka ji tsõro, suka gudu, suka bar Annabi a kan alfadararsa Baidã'a, bãbu kõwa tãre da shĩ fãce Abbas da Abu Sufyãna wanda yake riƙe da likkãfar Annabi. Annabi ya sanya Abbas ya yi ta kiran su,\"Yã Ansãr! Ya Mũhajirũn!\" Har suka kõmo aka ci nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 190,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa kuma a kan mũminai, kuma Ya saukar da rundunõni waɗanda ba ku gan su ba, kuma Ya azabtar da waɗanda suka kãfirta: Wancan ne sakamakon kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 191,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Allah Ya karɓi tũba daga bãyan wancana kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 191,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bãyan shẽkararsu wannan. Kuma idan kun ji tsõron talauci* to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalarSa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Idan kun ji tsõron talauci sabõda hanã mushirikai zuwa hajji sabõda fataucinku da su zai rage, to, bãbu kõme, arziki ga Allah yake, Yanã bãyar da shi ga wanda Yake so."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 191,
            "translated_text": "Ku yãƙi waɗanda* bã su yin ĩmãni da Allah kuma bã su ĩmãni da Rãnar Lãhira kumabã su haramta abin da Allah da ManzonSa suka haramta, kuma bã su yin addini, addinin gaskiya, daga waɗanda aka bai wa Littãfi, har sai sun bãyar da jizya daga, hannu, kuma sunã ƙasƙantattu.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bãyan gama hukuncin alãƙar Musulmi da kãfiran farko, watau mãsu shirkin, Lãrabãwa, sai kuma ya fãra bayãnin alãƙar Musulmi kãfirai na biyu; watau Yahũdu da Nasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 191,
            "translated_text": "Kuma Yahũdãwa suka ce: \"Uzairu ɗan Allah ne.\"Kuma Nasãra suka ce: \"Masĩhu ɗan Allah ne.\" Wancan zancensu ne da bãkunansu. Sunã kamã da maganar waɗanda suka kãfirta daga gabãni. Allah Yã la'ance su! Yãya aka karkatar da su?"
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 191,
            "translated_text": "Sun riƙi mãlamansu* (Yahũdu) da ruhubãnãwansu (Nasãra) Ubannangiji, baicin Allah, kuma sun riƙi Masĩhu ɗan Maryama (haka). Kuma ba a umurce su ba fãce da su bautã wa Ubangiji Guda. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. TsarkinSa ya tabbata daga barin abin da suke yin shirki da shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Hibru shi ne mãlamin Yahũdãwa, Ruhubãni mai ibãda wanda ya yanke jin dãɗin dũniya daga kansa sabõda ibãda, daga cikin Nasãra, mabiyan,gefen biyu sun riƙi shũgabanninsu ubanningiji sunã bauta musu, watau sunã yanka musu dõkoki waɗanda ba na Allah ba, sũ kuma sunã bin su a kan haka. Bautar da suke yi wa Uzairu kõ Masĩhu, Ĩsaɗan Maryama dõmin sun ce sũ ɗiyan Allah ne, watau sun zama juz'inSa ke nan. Tsarki ya tabbata ga Allah daga waɗannan siffõfi duka."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 192,
            "translated_text": "Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunãnsu. Kuma Allah Yanã ki, fãce dai Ya cika haskenSa, kuma kõ da kãfirai sun ƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 192,
            "translated_text": "Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, dõmin ya bayyanl shi a kan addini dukansa, kuma kõ dã mushirikai sun ƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 192,
            "translated_text": "Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr* da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Jam'in Hibru watan malamin Yahũdãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 192,
            "translated_text": "A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): \"Wannan ne abin da kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a taska.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 192,
            "translated_text": "Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin* Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kõ dã, a cikin waɗannan watanni akwai mãsu alfarma, kõ da yake sũ kãfirai ba sa kiyaye alfarmarsu ba, sun shigar da wani wãyonsu a ciki wanda suke cewa Nasĩ'u (watau jinkiri); Idan sunã son su yi yãƙi a cikin ɗayan watannin, sai su halattar da shi, sa'an nan su haramta wani watã a matsayinsa, su ƙãra kãfirci a kan kafircinsu, da yin haka. Sabõda haka Allah Ya halattar da yãƙi a cikin kõwanne watã dõmin kada a mãmayi Musulmi. Kuma yin jihãdi Yanã cikin ayyukan ibãda wadda Allah Yake riɓanya lãdarta a cikin watannin, mãsu alfarma."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 193,
            "translated_text": "Abin sani kawai, \"Jinkirtãwa\" ƙãri ne a cikin kãfirci, anã ɓatar da waɗanda suka kãfirta game da shi. Sunã halattar da watã a wata shẽkara kuma su haramtar da shi a wata shẽkara dõmin su dãce da adadin abin da Allah Ya haramta. Sabõda haka sunã halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawãce musu mũnanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 193,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, \"Ku fita da yãƙi a cikin hanyar Allah,\" sai ku yi nauyi* zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin Lãhira, fãce kaɗan.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Nauyi zuwa ga ƙasa, watau ku ƙãsa tãshi tsaye balle mã ku fita zuwa yãƙin da aka neme ku da shi (sabõda shi). fita da yãƙi a nan, anã nufin yãƙin Tabũka a cikin lõkacin bazara, kuma bãbu abinci dõmin Allah Ya jarrabi Musulmi, Ya fitar da mũminai da kuma munãfukai, dõmin a san yadda zã a yi ma'ãmala da su. Haka kuma a kõwane lõkaci Allah Yakan sanya wani abin jarraba na wahala a cikin Musulmi dõmin Ya bambanta mũminai daga munãfukai."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 193,
            "translated_text": "Idan ba ku fita da yãƙi ba, Allah zai azabta ku da azãba mai raɗaɗi, kuma Ya musanya wasu mutãne, wasunku (a maimakonku). Kuma bã zã ku cũtar da Shida kõme ba. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 193,
            "translated_text": "Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: \"Kada ka yi baƙin ciki, lalle ne Allah Yanã tãre da mu.\" Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar waɗanda suka kãfirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 194,
            "translated_text": "Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 194,
            "translated_text": "Dã yã kasance* wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa. Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah, \"Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku.\" Sunã halakar da kansu (da rantsuwar ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.'<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ya Shiga bayãnin siffõfin munãfukai waɗanda suka ƙi fita da waɗanda suka fita zuwa Tabũka, da waɗanda suka nemi wani uzuri, a cikin siffõfi dabam-dabam da zã a iya gane munãfukai da su acikin kõwane zãmani na rãyuwar Musulmi a dũniya."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 194,
            "translated_text": "Allah Ya yãfe maka laifi. Dõmin me ka yi musu izinin zama? Sai waɗanda suka yi gaskiya ssun bayyana a gare ka, kuma ka san maƙaryata."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 194,
            "translated_text": "Waɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin, jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 194,
            "translated_text": "Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin kai kãwo."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 194,
            "translated_text": "Kuma dã sun yi nufin fita, dã sun yi wani tattali sabõda shi, kuma amma Allah Ya ƙi zãburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tãre da mãsu* zama.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Watau mãtã da yãra da gajiyayyu."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 194,
            "translated_text": "Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a cikinku akwai 'yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai,"
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 195,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka al'amari, har gaskiya ta zo,* kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu ƙyãma,<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tun farkon zuwan Annabi a Madĩna mũnafukai sun yi ta yin kaidi dõmin su ɓãta al'amarin Annabi da Musulunci, suka kãsa, har gaskiya ta bayyana, suka kãma bakinsu dõmin rashin abin da zã su iya faɗã a yarda da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 195,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu* akwai mai cẽwa, \"Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine ni.\" To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kuma a yanzu ga yãƙin Tabũka (munafukai) sun bayyana da irin uzurran da suke kãwowa dõmin kada su fita kamar mai cewa\" To, Allah Ya hana zina, idan na fita nã gã mãtan Rũmãwa, bã zan iya yin haƙuri daga barinsu ba' sabõdahaka inã son a karbi uzurina kada a jefa ni a cikin fitina.\" Bai sani ba. da wannan rashin fitar ya jefa kansa a cikin fitinar. Dõmin zã a bar shi tãre da mãtã, sũ da shi kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 195,
            "translated_text": "Idan wani alhẽri ya sãme ka, zai ɓãta musu rai, kuma idan wata masifa ta sãme ka sai su ce: \"Haƙĩƙa, mun riƙe al'amarinmu daga gabãni.\"Kuma sujũya, alhãli kuwa sunã mãsu farin ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 195,
            "translated_text": "Ka ce: \"Bãbu abin da yake sãmun mu fãce abin da Allah Ya rubũta sahõda mu. Shĩ ne Majiɓincinmu. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 195,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu* mãsu kyau, alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ɗayan abũbuwa biyu mãsu kyau, sũ ne mutuwa a kan shahãda kõ rinjaya da sãmun ganĩma da izza."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 195,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku ciyar a kan yarda kõ kuwa a kan tĩlas. Bã zã a karɓa daga gare ku ba. Lalle ne kũ, kun kasance mutãne fãsiƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 195,
            "translated_text": "Kuma bãbu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su fãce dõmin sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma bã su zuwa ga salla fãce Luma sunã mãsu kasãla, kuma bã su ciyarwa fãce sunã mãsu ƙyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 196,
            "translated_text": "Sabõda haka, kada dũkiyõyinsu su bã ka sha'awa, kuma haka 'ya'yansu. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba, da su a cikin rãyuwar dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 196,
            "translated_text": "Kuma sunã rantsuwa da Allah cẽwa, lalle ne sũ, haƙĩƙa, daga gare ku suke, alhãli kuwa ba su zamo daga gare ku ba. Kuma amma sũ mutãne ne mãsu tsõro."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 196,
            "translated_text": "Dã sunã sãmun mafaka kõ kuwa waɗansu ɓulõli, kõ kuwa wani mashigi, da sun, jũya zuwa gare shi, kuma suna gaggawar shiga."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 196,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha'anin dũkiyõyin sadaka, sai idan an bã su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a bã su ba daga cikinta sai su zamo sunã mãsu fushi."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 196,
            "translated_text": "Kuma dã dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya bã su, da ManzonSa kuma suka ce: \"Ma'ishinmu Allah ne, zai kãwo mana daga falalarSa kuma ManzõnSa (zai bã mu). Lalle ne mũ, zuwa ga Allah mãsu kwaɗayi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 196,
            "translated_text": "Abin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 196,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cũtar Annabi, kuma sunã cẽwa \"Shi kunne* ne.\" Ka ce: \"Kunnen alhẽri gare ku, Yanã ĩmãni da Allah, kuma Yanã yarda da mũminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare ku.\"Kuma waɗanda suke cũtar Manzon Allah sunã da azãba mai raɗaɗi.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Shi kunne ne, ma'anarsa, kome ka gaya masa Yanã gaskatawa, watau wai ba shi da wãyon gãne gaskiyã da ƙaryã. Sabõda haka Allah Ya ce: Kunnen alheri, watau ya san gaskiya kuma yana gaskata ta, kuma ya san ƙarya, ba ya aiki da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 197,
            "translated_text": "Sunã rantsuwa da Allah sabõda ku, dõmin su yardar da ku. Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancantar su yardar da Shi, idan sun kasance mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 197,
            "translated_text": "Shin, ba su sani ba cẽwa \"Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa babba!\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 197,
            "translated_text": "Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu, wadda take bã su lãbãri ga abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: \"Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsõro.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 197,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, idan ka tambaye,* su haƙĩƙa, sunã cẽwa, \"Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: \"Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ana a cikin tafiya zuwa Tabũka sai wasu mutãne daga cikin munãfukai suka ce wa junansu, \"Wannan Yana zaton ya ci gidajen Rumawa da Biranensu? faufau.\" Sai Allah Ya sanar da AnnabinSa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) abin da suka faɗa. Sai ya ce: \"Ku zo mani da waɗannan mutãne.\" Da suka je masa ya ce musu 'Kun ce kaza da kaza.' Sai suka yi rantsuwa da cewa: ba mu kasance ba sai muna hĩra muna wãsã."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 197,
            "translated_text": "\"Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun kasance mãsu laifi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 197,
            "translated_text": "Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu* daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi kuma sunã hani daga alhẽri. Kuma sunã damƙẽwar hannayensu. Sun mance Allah, sai Ya mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * sũ duka daidai suke ga hãlinsu na sharri. Damƙe hannu shi ne rõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 197,
            "translated_text": "Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance su, kuma sunã da azãba zaunanniya."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 198,
            "translated_text": "Kamar waɗanda suke a gabãninku, sun kasance mafi tsananin ƙarfi daga gare ku, kuma mafi yawan dũkiyõyi da ɗiya. Sai suka ji daɗi da rabonsu, sai kuka ji daɗi da rabonku kamar yadda waɗanda suke a gabãninku suka ji dãɗi, da rabonsu, kuma kuka kũtsa kamar kũtsãwarsu. Waɗancan ayyukansu sun ɓãci a dũniya da Lãhira, kuma waɗannan sũ ne mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 198,
            "translated_text": "Shin lãbarin waɗanda suke a gabãninsu bai je musu ba, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Ibrãhĩm da Ma'abũta Madyana da waɗanda aka birkice? Manzanninsu sun jẽ musu da ãyõyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yanã zãluntar su ba, amma sun kasance rãyukansu suke zãlunta."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 198,
            "translated_text": "Kuma mummunai maza da mummunai mãtã sãshensu majiɓincin sãshe ne, sunã umurni da alhẽri* kuma sunã hani daga abin da bã a so, kuma sunã tsayar da salla, kuma sunã bãyar da zakka, kuma sunãɗã'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Abin da aka sani ga sharĩ'a shĩ ne alheri, kuma abin da da ba a sani ba ga sharĩ'a shĩ ne abin ƙi wanda bã a so."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 198,
            "translated_text": "Kuma Allah Yã yi wa'adi ga mummunai maza da mummunai mãtã da gidãjen Aljanna ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu, da wurãren zama mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar. Kuma yarda daga Allah ce mafi girma. Wancan shi ne babban rabo, mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 199,
            "translated_text": "Ya kai Annabi! Ka yãƙi kãfirai da munãfukai kuma ka tsaurara a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce. Tir da ta zama makõmar!"
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 199,
            "translated_text": "Sunã rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhãli kuwa lalle ne, haƙĩƙa, sun faɗi kalmar kãfirci, kuma; sun kãfirta a bãyan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga abin da ba su sãmu ba. Kuma ba su zargi kõme ba fãce dõmin Allah da ManzonSa Ya wadãtar da su daga falalarSa. To, idan sun tũba zai kasance mafi alhẽri gare su, kuma idan sun jũya bãya, Allah zaiazabtã su da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wani masõyi kõ wani mataimaki a cikin kasa."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 199,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, \"Lalle ne idan ya kãwo mana daga falalarSa, haƙĩƙa, munãbãyar da sadaka, kuma lalle ne munã kasancẽwa, daga sãlihai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 199,
            "translated_text": "To, a lõkacin da Ya bã su daga falalarSa, sai suka yi rõwa da shi, kuma suka jũya bãya sunã mãsu bijirẽwa,"
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 199,
            "translated_text": "Sai Ya biyar musu da munãfunci a cikin zukatansu har zuwa ga Rãnar da suke haɗuwa da Shi sabõda sãɓã wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma sabõda abin da suka kasance sunã yi na ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 199,
            "translated_text": "Shin, ba su sani ba cẽwa lalle ne Allah Yanã sanin asĩrinsuda gãnawarsu, kuma lalle Allah ne Masanin abũbuwan fake?"
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 199,
            "translated_text": "Waɗanda suke aibanta mãsu yin alhẽri daga mummunaia cikin dũkiyõyin sadaka, da waɗanda ba su sãmu fãce iyãkar ƙõƙarinsu, sai sanã yi musu izgili. Allah Yanã yin izgili gare su. Kuma sunã da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 200,
            "translated_text": "Kõ kã nẽma musu gãfara ko ba ka nẽma musu ba, idan ka nẽma musu gãfara sau saba'in, to, Allah bã zai gãfarta musu ba. Sabõda sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 200,
            "translated_text": "Waɗanda aka bari sun yi farin ciki da zamansu a bãyan Manzon Allah, kuma suka ƙi su yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu a cikin hanyar Allah, kuma suka ce: \"Kada ku fita zuwa yãƙi a cikin zãfi.\"Ka ce: \"Wutar Jahannama ce mafi tsanlnin zãfi.\" Dã sun kasance sunã fahimta!"
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 200,
            "translated_text": "Sabõda haka su yi dãriya kaɗan, kuma su yi kũkada yawa a kan sãkamako ga abin da suka kasance sunã tsirfatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 200,
            "translated_text": "To, idan Allah Ya mayar da kai zuwa ga wata ƙungiyã daga gare su sa'an nan suka nẽme ka izni dõmin su fita, to, ka ce: \"Bã zã ku fita tãre da nĩ ba har abada, kuma bã zã ku yi yãƙi tãre da nĩ ba a kan wani maƙiyi. Lalle ne kũ, kun yarda da zama a farkon lõkaci, sai ku zauna tãre da mãtã mãsu zaman gida.\""
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 200,
            "translated_text": "Kuma kada ka yi salla a kan kõwa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lalle ne sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma sun mutu alhãli kuwa sunã fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 200,
            "translated_text": "Kuma kada dũkiyõyinsu da ɗiyansu su bã ka sha'awa. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba da su a cikin dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 200,
            "translated_text": "Kuma idan aka saukar da wata sũra cẽwa; Ku yi ĩmãni da Allah kuma ku yi jihãdi tãre da ManzionSa. Sai mawadãta daga gare su su nẽmi izninka, kuma su ce: Ka bar mu mu kasance tãre da mazauna."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 201,
            "translated_text": "Sun yarda da su kasance tãre da mãtã mãsu zama (a cikin gidãje). Kuma aka rufe a kan zukãtansu, sabõda haka, sũ, bã su fahimta."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 201,
            "translated_text": "Amma Manzon Allah da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sun yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu. Kuma waɗannan sunã da ayyukan alhẽri, kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 201,
            "translated_text": "Allah yã yi musu tattalin gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu. Wancan ne babban rabo mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 201,
            "translated_text": "Kuma mãsu uzuri daga ƙauyãwa zuka zo dõmin a yi musu izini, kuma waɗanda suka yi wa Allah da ManzonSa ƙarya, suka yi zamansu. wata azãba mai raɗaɗi zã ta sãmi waɗanda suka kãfirta daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 201,
            "translated_text": "Bãbu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma bãbu laifi a kan waɗanda bã su sãmun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasĩha* ga Allah da ManzonSa. Kuma bãbu wani laifi a kan mãsu kyautatãwa. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai tausayi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Nasĩha ita ce su faɗi maganar ƙwarai; kyautatãwa itace a yi aiki dõmin Allah, ba dõmin neman dũniya ba."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 201,
            "translated_text": "Kuma bãbu (laifi) a kan waɗanda idan sun je maka dõmin ka ɗauke su ka ce: \"Bã ni da abin da nake ɗaukar ku a kansa,\" suka jũya alhãli kuwa idãnunsu sunã zubar da hawãye dõmin baƙin ciki cẽwa ba su sãmi abin da suke ciyarwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 201,
            "translated_text": "Abin sani kawai, laifi Yanã a kan waɗanda suke nẽman izininka alhãli kuwa sũ mawadãta ne. Sun yarda su kasance tãre da mãtã mamaya (gidãje), kuma Allah Yã danne a kan zukãtansu, dõmin haka sũ, bã su gãnẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 202,
            "translated_text": "Sunã kãwo uzurinsu zuwa gare ku idan kun kõma zuwa gare su Ka ce: \"Kada ku kãwo wani uzuri, bã zã mu amince muku ba. Haƙĩƙa, Allah Yã bã mu lãbãri daga lãbãrunku, Allah zai ga aikinku kuma ManzonSa (zai gani). Sa'an nan kuma a mayar da ku zuwa ga Masanin gaibi da bayyane, sai Ya bã ku lãbarin abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 202,
            "translated_text": "Zã su yi rantsuwa da Allah a gare ku idan kun jũya zuwa gare su, dõmin ku kau da kai daga gare su. To, ku kau da kai daga gare su don kõ sũ ƙarantã ne, kuma Jahannama ce matattararsu bisa ga sãkamakon abin da suka kasance sunã tsirfatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 202,
            "translated_text": "Sunã rantsuwã gare ku dõmin ku yarda da su. To, idan kun yarda da su, to, lalle ne Allah bã shi yarda da mutãne fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 202,
            "translated_text": "¡auyãwã ne mafi tsananin* kãfirci da munãfinci, kuma sũne mafi kamanta ga, rashin sanin haddõjin abin da Allah Ya saukar a kan ManzonSa. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ƙauyãwã ne mafi tsananin kãfirci dõmin nĩsansu daga sanin hãlãyen girmamãwã da na zamantakewa, sa'an nan da nĩsansu daga Annabi har su saurari abin da ya zo da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 202,
            "translated_text": "Kuma daga ƙauyãwã akwai waɗanda* suke riƙon abin da suke ciyarwa a kan tãra ce, kuma sunã saurãron aukuwar masĩfa a gare ku, aukuwar mummunar masĩfa ta tabbata a kansu. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ƙauyãwã kashi biyu ne: Akwai wãwãye munãfukai mãsu ganin addĩni yã ɗõra musu nauyin biyan zakkã da sauran ayyukan alheri, sunã ɗaukar sa kamar tãra da biyan kakkarai. Kuma akwai ƙauyãwa mãsu hankali sun sani Annabi manzo ne daga Allah, sunã ɗaukar abin da addĩni ya azã musu duka ibãda ne, sunã fãtar kusanta da shi zuwa ga Allah, Ubangjinsu. To su mutãnen ƙwarai ne, zã su shigã Aljanna."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 202,
            "translated_text": "Kuma daga ƙauyãwã akawi waɗanda suke yin ĩmanida Allah da Rãnar Lãhira, kuma sunã riƙon abin da suke ciyarwa (tamkar) waɗansu ibãdõdin nẽman kusanta ne a wurin Allah da addu'õ'in ManzonSa. To, lalle ne ita (ciyarwar nan) ibãdar nẽman kusanta ce a gare su. Allah zai shigar da su a cikin RahamarSa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 203,
            "translated_text": "Kuma mãsu tsẽrẽwa* na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; ¡õramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Yãƙin Tabũka ya kasa jama'ar Musulmi gwargwadon ĩmãninsu da ayyukansu da gabãtarsu a cikin addĩni, cikin darajõji da ɗabaƙõƙi. Darajar farko ita ce, Sahabban farko waɗanda suka tsere wa sauran mutãne ga shigã Musulunci da ƙarfin ĩmãni da yawan aiki da tsarkake zũciya ga aikin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 203,
            "translated_text": "Kuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai,* haka kuma daga mutãnen Madnĩa. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su. zã Mu yi musu azãba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azãba mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kungiya ta biyu munãfukai mãsu zurfin wayo, sun san yadda suke ɓõye munãfuncinsu sabõda gõgewa da iya munãfunci har mutãne bã zã su iya gãne su ba, sai Allah Ya tõna su."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 203,
            "translated_text": "Kuma da waɗansu, sun yi furuci* da laifinsu, sun haɗa aiki na ƙwarai da wani mummuna. Akwai tsammãnin Allah Ya karɓi tũba a kansu. Lallai Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wata ƙungiya wadda ta yi munãfunci, tã ƙi fitã zuwa yãƙi amma kuma suka ga sun yi laifi suka yi iƙirãri da cewa, \"Sun yi laifi,\" sa'an nan suka tũba, Allah Ya karɓi tũbarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 203,
            "translated_text": "Ka karɓi sadaka daga dũkiyõyinsu kana tsarkake su, kuma kana tabbatar da kirkinsu da ita. Kuma ka yi musu addu'a. Lallai addu'õ'inKa natsuwã ne a gare su. Kuma Allah ne Mai ji, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 203,
            "translated_text": "Shin, ba su sani ba cẽwa lallai Allah, ne Yake karɓar tũbã daga bãyinSa, kuma Yanã karɓar sadakõkinsu, kuma lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai?"
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 203,
            "translated_text": "Kuma ka ce: \"Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku, da ManzonSa da Muminai kuma zã a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 203,
            "translated_text": "Kuma da waɗansu waɗanda* aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wata ƙungiya wadda ita ba munãfuka ba ce, amma kuma ba su fita zuwa yãƙin ba, kuma bã su da wani dalĩli sai kasãla kawai da taushewar Shaiɗan. Waɗannan an jinkirtar da al'amarinsu har Allah Ya yi hukunci a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 204,
            "translated_text": "Kuma waɗanda* suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, \"Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri\", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa, su, haƙĩƙa, maƙaryata ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wata ƙungiyã ta munãfukai mãsu aiki dõmin tumɓuke ƙarfin Musulmi ta hanyar da bã a iya gãnewa da sauri. Kamarsu gina masallaci kusa da wani tsõhon masallãci da sũnan taimakon addĩni amma da nufin su raba jama'ar Musulmi,kuma sun sãmi wurin da zã su riƙa tãro da ɓõye kãyan yãƙi da shirin sharri ga Musulmi. Kamar ma'abũta Masjidil Darãr, wanda aka yi kusa da masallacin Kuba a Madĩna. Aikinsu bai tsaya ga lõkacin yãƙin Tabũka ba, sabõda haka aka ce: da bagewa ga wanda ya yãƙi Allah a gabãni, watau a gabãnin bayyanar fallasar munãfukai da yãƙin Tabũka."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 204,
            "translated_text": "Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsãshinsa a kan taƙawa tun farkon yini, shĩ ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai waɗansu maza sunã son su tsarkaka*. Kuma Allah Yanã son mãsu nẽman tsarkakuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sunã son tsarkaka ta ɓõye da ta bayyane. Ta ɓõye sananniya ce: ita ce rashin munãfunci, kuma ta bayyane ita ce sunã kãma rũwa a bãyan sun karce kãshinsu da dũtse, kamar yadda ya zo a cikin Hadĩsi. Allah ne Mafi sani."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 204,
            "translated_text": "Shin, wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan taƙawa daga Allah da yarda, shi ne mafi alhẽri kõ kuwa wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan gãɓar rãmi mai tusgãwa? Sai ya rũsa da shi a cikin wutar Jahannama. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 204,
            "translated_text": "Gininsu, wanda suka gina, bã zai gushe ba Yanã abin shakka a cikin zukãtansu fãce idan zukãtansu sun yanyanke. Kuma Allah ne Masani, Mai Hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 204,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah Ya saya* daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cẽwa sunã da Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashẽwa anã kashẽ su. (Allah Yã yi) wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyan bayãnin nau'ukan kãfirai da alãmõminsu da yadda zã a bi wajen yankewa da su, da barin fage ga muminai na ƙwarai, sai kuma Yã kirãyi muminai zuwa ga mubãya'a ga Allah, watau ciniki, sa'an nan Ya bayyana musu kuɗin saye da abin sayarwa, ya ce: \"Allah Yã saya daga muminai.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 205,
            "translated_text": "Mãsu* tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdẽwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu umurni da alhẽri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarẽwaã ga iyãkõkin Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sa'an nan kuma ya bayyanã a cikin wannan ãyã ta 112 siffõfin muminai waɗanda aka fuskantar da kiran neman ciniki da su."
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 205,
            "translated_text": "Bã ya kasancẽw*a ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bayãnin umurni da yanke wa kãfirai, kõ da sun mutu, da barin yi musu addu'ar alheri."
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 205,
            "translated_text": "Kuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi (Ibrãhĩm) cẽwa lalle ne shĩ (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 205,
            "translated_text": "Kuma Allah bai kasance mai ɓatar da mutãne a bãyan Yã shiryar da su ba, sai Ya bayyanã musu abin da zã su yi taƙawa da shi. Lalle ne Alllh, ga kõme, Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 205,
            "translated_text": "Lalle ne Allah Yanã* da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa. Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ãyã tanã nũna cewa taklĩfin da Allah Yake azã wa bãyinSa na yãƙi da waninSa, bã dõmin ya wahalar da su ba ne. Yanã yi ne dõmin alheri a gare su, Shĩ Allah Mawãdaci ne, Yanã da ƙasa da sammai, kuma shĩ ne Mai yin halittar kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 205,
            "translated_text": "Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Ya karɓi tũbar Anbabi da* Muhãjirĩna da Ansãr waɗanda suka bĩ shi, a cikin sã'ar tsanani, daga bãya zukãtan wani ɓangare daga gare su sun yi kusa su karkata, sa'an nan (Allah) Ya karɓi tũbarsu. Lalle, Shĩ ne Mai tausayi, Mai jin ƙai gare su.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Yã fãra gabãtar da cewa, \"Allah Yã karɓi tũbar Annabi da waɗanda Ya ambata tãre da shi,\" dõmin ya biyar ãyar da ke zuwa ta tũbar waɗanda suka yi zamansu, bã da wani uzuri ba, kuma sũ bã munãfuƙai ba, aka jinkirtar da maganar tũbarsu har a bãyan hõron kwãna hamsin bãbu mai yi musu magana, bisa hanin Allah. Kuma dã an ambaci karɓar tũbarsu kawai bã da an gabãtar da tũbar waɗanda suka fita ba, dã sai a ce sun fi waɗanda suka fita, dõmin an yi nassi a kan tũbarsu. Wanda aka yi nassi akan tũbarsa, yã fi wanda. aka bari a cikin duhu."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 206,
            "translated_text": "Kuma (Allah) Yã karɓi tũba a kan ukun* nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce (kõmãwa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sũ mutãne uku waɗanda aka jinkintar da al'amarinsu, a ãyã ta l06, sũ ne Ka'abu bn Mãliki da Marãratu bn Rabĩ'a el Umary, da Hilãlu bn Umaiya el Wãƙify. Sun ƙi fita, bã da wani uzuri ba, kuma a lõkacin da Annabi ya kõmo daga Tabũka, waɗanda ba su fita ba suka tafi suka faɗi uzurõrinsu na rashin fitã. Annabi ya karɓa musu Kuma ya nema musu gãfara. Amma su ukun, suka faɗi gaskiya cewa sun zauna ne bã dõmin munãfunci ba, sai dai abin yã kasance haka kawai bã da wani uzuri ba. To, Annabi ya ce su dãkata, sai abin da Allah Ya ce a kansu. Aka hana kõwa ya yi musu magana a cikin Madĩna, har mãtansu na aure. Suka yi kwãna hamsin a cikin matsuwa, sa'an nan Allah Ya sauko da tũbarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 206,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku kasance tãre da mãsu gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 206,
            "translated_text": "Bã ya kasancẽwa* ga mutãnen Madĩna da wanda yake a gẽfensu, daga ƙauyãwã, su sãba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rãyukansu daga ransa. Wancan, sabõda ƙishirwa bã ta sãmun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma bã su tãkin wani matãki wanda yake takaitar da kãfirai kuma bã su sãmun wani sãmu daga maƙiyi fãce an rubuta musu da shi, lãdar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bayãnin falalar mutãne da ke zaune a Madĩna tãre da Annabi, a lokacinsa kõ bãyansa."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 206,
            "translated_text": "Kuma bã su ciyar da wata ciyarwa, ƙarama kõ babba, kuma bã su kẽta wani rafi sai an rubutã musu, dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyãwon abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 206,
            "translated_text": "Kuma bã ya kasancẽwã ga muminai su fita zuwa yãƙi gabã ɗaya.* Sabõda haka, don me ne wata jama'a daga kowane ɓangare daga gare su ba ta fita (zuwa nẽman ilimi ba) dõmin su nẽmi ilimi ga fahimtar addĩni kuma dõmin su yi gargaɗi ga mutãnensu idan sun kõma zuwa gare su, tsammãninsu, sunã yin sauna?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bãyan yã ƙãre bayãni a kan falalar da Allah Ya fĩfĩta mazauna Madĩna da ita, sabõda haka bã ya halatta a gare su su sãɓa wa Annabi da zama a bãyan yã fita zuwa yãƙi. Sa'annan kuma ya yi idiraki da ishãrar cewa fitã zuwa yãƙi farillar kifãya ce; wasu sunã ɗauke wa wasu. Kuma bã ya kyautuwã a ce kõwa ya zama sojan yãƙi, a bar sauran ayyuka na lalũrar rãyuwa kamar fita neman ilmi, shi ma farillar kifãya ne tĩlas wasu su fita zuwa nemansa dõmin idan sun kõma ga mutãnensu sai su karantar da su. Hikimar ãyar tã fãra da maganar fita zuwa yãƙi kuma ta ƙãre da sakamakon kõmõwa daga makaranta dõmin nunawar fita zuwa gare su duka wajibi ne: wanda wani ke iya ɗauke wa wani. Allah ne Mafi sani."
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 207,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yãƙi waɗanda suke kusantar* ku daga kãfirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bayãnin yadda ake yin yãƙi ne; bã a fãɗa wa dukkan maƙiyã gabã ɗaya, na kusa da na nesa. Sai an fara da na kusa tukuna sa' nan nan a dinga fãɗaɗãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 207,
            "translated_text": "Kuma idan aka saukar* da wata sũra, to, daga gare su akwai waɗanda suke cẽwa: \"Wãne a cikinku wannan sũra ta ƙãra masa ĩmãni?\" To amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sũ, sunã yin bushãra (da ita).<br \/>\n____________________<br \/>\n * Taƙaitãwa da ƙãrin tanbĩhi ga abin da sũrar ta ƙunsa."
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 207,
            "translated_text": "Amma kuma waɗanda suke a cikin zukãtansu akwai cũta, to, tã ƙãra musu ƙazanta zuwa ga ƙazantarsu, kuma su mutu alhãlin kuwa sunã kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 207,
            "translated_text": "Shin, bã su ganin cẽwa anã fitinar su a cikin kõwace shẽkara: Sau ɗaya kõ kuwa sau biyu, sa'an nan kuma bã su tũba, kuma ba su zama sunã tunãni ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 207,
            "translated_text": "\"Kuma idan haƙĩƙa, aka saukar da wata sũra, sai sãshensu ya yi dũbi zuwa ga wani sãshe, (su ce): \"Shin, wani mutum yanã ganin ku?\" Sa'an nan kuma sai su jũya. Allah Ya jũyar da zukãtansu, dõmin, haƙĩƙa sũ mutãne ne, bã su fahimta."
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 207,
            "translated_text": "Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo* daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bayãnin rahamar Allah game da aiko Manzõ daga cikin mutãne, cewa wata falala ce a gare su. Kuma shi Manzon nan ɗan'uwansu ne wanda bã ya son su da wani abu sai alheri, idan sun gãne dã sun bĩ shi, kuma idan ba su gãne bã, to, Allah Yã tsare shi daga sharrinsu, kuma Yã isar masa."
        },
        {
            "ayah_number": 129,
            "surah_number": 9,
            "page_number": 207,
            "translated_text": "To, idan sun jũya, sai ka ce: Ma'ishĩna Allah ne. Bãbu abin bautãwa fãce shi. A gare Shi nake dõgara. Kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 208,
            "translated_text": "A. L̃.R. Waɗancan ãyõyin littãfi ne kyautatacce."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 208,
            "translated_text": "Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cẽwa, \"Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cẽwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu.\"Kãfirai suka ce: \"Lalle ne wannan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 208,
            "translated_text": "Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãna shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yanã gudãnar da al'amari. Bãbu wani macẽci fãce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 208,
            "translated_text": "zuwa gare Shi makõmarku take gabã ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita dõmin Ya sãka wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ãdalci, kuma waɗanda suka kãfirta sunã da abin sha daga ruwan zãfi, da azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 208,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, babban haske, da watã mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manzilõli, dõmin ku san ƙidãyar shẽkaru da lissãfi. Allah bai halitta wannan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki-daki dõmin mutãne waɗanda suke sani."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 208,
            "translated_text": "Lalle ne a cikin sãɓãwar dare da yini, da abin da Allah Ya halitta a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙaakwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 209,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mũ, kuma suka yarda da rãyuwar dũniya kuma suka natsu da ita, da waɗanda suke gafalallu ne daga ãyõyinMu,"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 209,
            "translated_text": "Waɗannan matattãrarsu Jahannama ce sabõda abin da suka kasance sunã tsirfãtawa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 209,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, Ubangijinsu Yanã shiryar da su sabõda ĩmãninsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, a cikin gidãjen Aljannar ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 209,
            "translated_text": "Kiransu a cikinta, \"TsarkinKa yã Allah!\" Kuma gaisuwarsu a cikinta,\"Salãmun\", kuma ƙarshen kiransu, cẽwa, \"Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 209,
            "translated_text": "Kuma dã Allah Yana gaggãwa ga mutãne da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da alhẽri, haƙĩƙa dã an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Sabõda haka Munã barin waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu sunã ta ɗimuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 209,
            "translated_text": "Kuma idan cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, yanã (kwance) ga sãshensa kõ kuwa zaune, kõ kuwa a tsaye. To, a lõkacin, da Muka kuranye cũtar daga gare shi, sai ya shũɗe kamar ɗai bai kirãye Mu ba zuwa ga wata cũta wadda ta shãfe shi. Kamar wannan ne aka ƙawãta ga maɓannata, abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 209,
            "translated_text": "Kuma, haƙĩƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabãninku, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, amma ba su kasance sunã ĩmãni ba. Kamar wannan ne, Muke sãkãwa ga mutãne mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 209,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka sanya ku mãsu mayẽwa a cikin ƙasa daga bãyansu, dõmin Mu ga yãya kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 210,
            "translated_text": "Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: \"Ka zo da wani Alƙur'ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã shi.*\" Ka ce: \"Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sunã nufin idan ya musanya shi, su ce: \" To, gã shi ka bayyana cewa kai ne mai ƙirƙira shi, kanã jinginã shi ga Allah.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 210,
            "translated_text": "Ka ce: \"Dã Allah Ya so dã ban karanta shi ba a kanku, kuma dã ban sanar da kũ ba gameda shi, dõmin lalle ne nã zauna a cikinku a zãmani mai tsawo daga gabãnin (fãra saukar) sa. Shin fa, bã ku hankalta?\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 210,
            "translated_text": "\"Sabõda haka wãne ne mafi Zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata ãyõyinSa? Haƙĩƙa, mãsu laifibã su cin nasara!\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 210,
            "translated_text": "Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: \"Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah.\"Ka ce: \"Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Yã ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 210,
            "translated_text": "Kuma mutãne ba su kasance ba fãce al'umma guda, sa'an nan kuma suka sãɓã wa jũna, kuma ba dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, dã an yi hukunci a tsakãninsu a kan abin da yake a cikinsa suke sãɓã wa jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 210,
            "translated_text": "Kuma sunã cẽwa: \"Don me ba a saukar da wata ãyã ba a gare shi, daga Ubangijinsa?\" To, ka ce: \"Abin sani kawai, gaibi ga Allah yake. Sai ku yi jira. Lalle ne nĩ, tãre da ku, inã daga mãsu jira.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 211,
            "translated_text": "Kuma idan Muka ɗanɗanã wa mutãne wata rahama, a bãyan wata cũta tã shãfe su, sai gã su da mãkirci a cikin ãyõyinMu. Ka ce: \"Allah ne mafi gaggãwar (sakamakon) mãkirci.\" Lalle ne ManzanninMu sunã rubũta abin da kuke yi na mãkirci."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 211,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun kasance a cikin jirãge, su gudãna tãre da su da iska mai dãɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirãgen, kuma tãguwar ruwa ta jẽ musu daga kõwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirãyi Allah, sunã mãsu tsarkake addini gare Shi, (sunã cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙĩƙa munã kasancẽwa daga mãsu gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 211,
            "translated_text": "To, a lõkacin da Ya kuɓutar da su, sai, gã su sunã zãlunci a cikin ƙasa, bã da wanĩ hakki ba. Yã ku mutãne! Abin sani kawai, zãluncinku a kanku yake, a bisa rãyuwar dũniya. Sa'an nan kuma zuwa gare Mu makõmarku take, sa'an nan Mu bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa,"
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 211,
            "translated_text": "Abin sani kawai, misãlin rãyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutãne da dabbõbi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinãriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutãnenta suka zaci cẽwa sũ ne mãsu ĩkon yi a kanta, sai umurninMu ya je mata da dare kõ kuma da rãna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadãta ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki, ga mutãne waɗanda suke tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 211,
            "translated_text": "Kuma Allah Yanã kira zuwa ga gidan aminci, kuma, Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga tafarki madaidaici."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 212,
            "translated_text": "Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari)1), wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mãsu aikin ƙwarai waɗanda suka karɓa kiran Allah sunã da sakamakon abu mai kyau, wãtau Aljanna, kuma da ƙãri, watau ganin Ubangijinsu a cikin Aljanna. Haka Hadisi ya yi fassara."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 212,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi tsirfar mũnanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake, kuma ƙasƙanci yanã rufe su. Bã su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe fuskokinsu da guntãyen ƙirãruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abõkan wuta, sunã madawwama a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 212,
            "translated_text": "Kuma a rãnar da Muke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, \"Ku kãma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku.\" Sa'an nan Mu rarrabe a tsakãninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: \"Bã mũ kuka kasance kunã bauta wa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 212,
            "translated_text": "\"To, kuma Allah Yã isa zama shaida a tsakãninmu da tsakãninku. Haƙĩƙa mun kasance ba mu san kõme ba na bautãwarku a gare mu!\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 212,
            "translated_text": "A can ne kõwane rai yake jarraba abin da ya bãyar bãshi, kuma aka mayar da su zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace musu."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 212,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?\" To, zã su ce: \"Allah ne.\" To, ka ce: \"Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 212,
            "translated_text": "To, Wancan ne Allah, Ubangijinku Tobbatacce. To, mẽne ne a bãyan gaskiya fãce ɓãta? To, yãya ake karkatar da ku?"
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 212,
            "translated_text": "Kamar wancan ne kalmar Ubangijinka, ta tabbata a kan waɗanda suka yi fãsiƙanci, cẽwa haƙĩƙa sũ, bã zã su yi ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 213,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake fãra halitta, sa'an nan kuma ya mayar da ita?\" Ka ce: \"Allah ne Yake fãra halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita. To, yãyã akejũyar da ku?\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 213,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?\" Ka ce: \"Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda bã ya shiryarwa fãce dai a shiryar da shi? To, mẽne ne a gare ku? Yãya kuke yin hukunci?\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 213,
            "translated_text": "Kuma mafi yawansu bã su biyar kõme fãce zato. Lalle ne zato bã ya wadãtar da kõme daga gaskiya. Lalle Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 213,
            "translated_text": "Kuma wannan Alƙur'ãni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabãninsa da bayãnin hukuncin littãffan Allah, Bãbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 213,
            "translated_text": "Kõ sunã cẽwa, \"Yã ƙirƙira shi?\" Ka ce: \"Ku zo da sũra guda misãlinsa, kuma ku kirãyi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 213,
            "translated_text": "Ã'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassararsa ba ta riga ta jẽ musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabãninsu. Sai ka dũba, yãya ãƙibar azzãlumai ta kasance?"
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 213,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu akwai wanda yake yin ĩmãni da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda bã ya yin ĩmãni da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga maɓarnata."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 213,
            "translated_text": "Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: \"Inã da aikĩna kuma kunã da aikinku, kũ kuɓutattu ne daga abin da nake aikatãwa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 213,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke saurare zuwa gare ka. Shin fa, kai kana jiyar da kurma, kuma kõ dã sun kasance bã su hankalta?"
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu akwai wanda yake tsõkaci zuwa gare ka. Shin fa, kai kana shiryar da makãfi, kuma kõ dã sun kasance bã su gani?"
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Lalle ne Allah ba Ya zãluntar mutãne da kõme, amma mutãnen ne ke zãluntar kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Kuma rãnar da Yake tãra su, kamar ba su zauna ba fãce sa'a guda daga yini. Sunã gãne jũna a tsakãninsu. Haƙĩƙa, waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasãra. Kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Kuma imma dai, haƙĩƙa, Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu alkawari, kõ kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makõmarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne shaida a kan abin da suke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Kuma ga kõwace al'umma akwai Manzo*. Sa'an nan idan Manzonsu ya je, sai a yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma sũ, bã a zãluntar su.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Manzo na farko shĩ ne mai shiryar da su, Manzo na biyu shi ne ajalinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Kuma sunã cẽwa, \"A yaushe wannan wa'adi zai auku, idan kun kasance mãsu gaskiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ba na mallaka wa kaina wata cũta, haka kuma wani amfãni, sai abin da Allah Ya so. Ga kõwace al'umma akwai ajali, idan ajalinsu ya zo, to, bã zã su yi jinkiri daga gare shi ba, kõ dã sã'ã guda, kuma bã zã su gabãta ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kun gani, idan azãbarSa ta zo muku da dare ko da rãna? Mẽne ne daga gare shimãsu laifi suke nẽman gaggãwarsa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Shin sa'an nan kuma idan har ya auku, kun yi ĩmãni da shi? Ashe? Yanzu kuwa, alhãli kun kasance game da shi kunã nẽman gaggãwar aukuwarsa?"
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma aka ce ga waɗanda suka yi zãlunci, \"Ku ɗanɗani azãbar dawwama! Shin, anã sãka muku fãce da abin da kuka kasance kuna aikatãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 214,
            "translated_text": "Kuma sunã tambayar ka: Shin gaskiya ne? Ka ce: \"Ĩ, ina rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle gaskiya ne, kuma ba ku zama mãsu buwãya ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 215,
            "translated_text": "Kuma dã kõwane rai wanda ya yi zãlunci yã mallaki duka abin da yake a cikin ƙasa, to, dã yã yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma bã zã a zãlunce su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 215,
            "translated_text": "To! Haƙĩƙa Allah Ya mallaki abin da yake a cikin sammai da ƙasa. To! Haƙĩƙa wa'adin Allah gaskiya ne. Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 215,
            "translated_text": "Shi ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma zuwa gare Shi ne ake mayar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 215,
            "translated_text": "Ya ku mutãne! Lalle wa'azi yã jẽ muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙirãza, da shiriya da rahama ga muminai."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 215,
            "translated_text": "Ka ce: \"Da falalar Allah da rahamarSa. Sai su yi farin ciki da wannan.\" Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 215,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar sabõda ku na arziki, sai kuka sanya hukuncin haramci da halacci a gare shi?\" Ka ce: \"Shin, Allah ne Ya yi muku izni, ko ga Allah kuke ƙirƙirãwar ƙarya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 215,
            "translated_text": "Kuma mẽne ne zaton waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, a Rãnar ¡iyãma? Lalle haƙĩƙa, Allah Ma, abũcin falala ne a kan mutãne, amma kuma mafi yawansu bã su gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 215,
            "translated_text": "Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, fãce Mun kasance Halarce a lõkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bã zai yi nĩsa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma bãbu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma bãbu mafi girma, fãce yana a cikin littãfi bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 216,
            "translated_text": "To, Lalle ne masõyan* Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Waliyyin Allah, shi ne masõyin Allah da sharaɗin ya zama mumini mai taƙawa watau yanã aiki da abin da Allah Ya umurce shi, kuma yanã barin abin da Allah Ya hana shi, bisa harshen Annabinsa wanda yake biya. Bãbu ƙarin kõme bãbu ragi. Bushãrarsu, ita ce yabon mutãne a gare su, kõ kuma a lõkacin mutuwarsu malã'iku su riƙa yi musu bushãra da gamuwa da Ubangijinsu, kõ kuma a cikin kabari wajen tambaya. Allah ne Mafi sani. "
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 216,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 216,
            "translated_text": "Sunã da bushãra a cikin rãyuwar dũniya da ta Lãhira. Bãbu musanyãwa ga kalmõmin Allah. Wancan shi ne babban rabo mai girma,"
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 216,
            "translated_text": "Kada maganarsu* ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai jĩ, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Maganarsu ta izgili a gare ka. Idan Allah Ya ɗaukakã ka, bãbu mai iya hanãwa dõmin Shi kaɗai ne Mai izza kuma sai inda Ya sanya ta ga wanda Ya so."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 216,
            "translated_text": "To! Haƙĩƙa Allah Yanã da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bã su biyar waɗansu abõkan tarẽwa (ga Allah a MulkinSa). Bã su biyar kõme fãce zato. Kuma ba su zama ba fãce sunã ƙiri faɗi kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 216,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Ya sanya muku dare, dõmin ku natsu a cikinsa, da yini mai sanya a yi gani. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda sukẽ ji."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 216,
            "translated_text": "Suka ce: \"Allah Ya riƙi ɗa.\" Tsarkinsa yã tabbata! Shi ne wadãtacce Yanã da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku bãbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kunã faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah?"
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 216,
            "translated_text": "Ka ce: \"Haƙĩƙa waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, bã zã su ci nasara ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 216,
            "translated_text": "Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 217,
            "translated_text": "Kuma ka karanta musu lãbãrin Nũhu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, \"Ya mutãnẽna! Idan matsayĩna da tunãtarwata ameda ãyõyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dõgara. Sai ku tãra al'amarinku, kũ da abũbuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri.\""
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 217,
            "translated_text": "\"Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Watau dukan abin da na zo muku da shi na umurni kõ hani, to, ni ma an umurce ni da yinsa kõ barinsa. Kuma bã ni neman wata ijãrar karantarwa daga gare ku dõmin Allah Ya umarce ni da iyar da manzancinsa zuwa gare ku, sabõda haka Shi ne zai biyã ni tsãdar aikĩna."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 217,
            "translated_text": "Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tãre da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su mãsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ãyõyinMu. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 217,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga bãyansa zuwa ga mutãnensu, suka jẽmusu da hujjõji bayyanannu, to, ba su kasance zã su yi ĩmãni ba sabõda sun ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufẽwa a kan zukãtan mãsu ta'addi."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 217,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma a bãyansu Muka aika Mũsa da Hãrũna zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, tãre da ãyõyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutãne mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 217,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga gare Mu, suka ce: \"Wannan haƙĩƙa sihiri ne bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 217,
            "translated_text": "Mũsã ya ce: \" Shin, kunã cẽwa ga gaskiya a lõkacin data zo muku? Shin, sihiri ne wannan? Lalle masihirci, bã ya cin nasara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 217,
            "translated_text": "Suka ce: \"Shin, ka zo mana ne dõmin ka jũyar da mu daga abin da muka iske ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Bã zã mu zama mãsu ĩmãni ba sabõda ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "Kuma Fir'auna ya ce: \"Ku zo mini da dukan masihirci, masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,\"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: \"Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "\"Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "Sa'an nan bãbu wanda ya yi ĩmãni da Mũsa fãce zuriya daga mutãnensa, a kan tsõron kada Fir'auna da shũgabanninsu su fitinẽ su. Lalle, haƙĩƙa, Fir'auna marinjãyi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga mãsu ɓarna."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "Kuma Mũsã ya ce: \"Yã kũ mutãnena! Idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah, to, a gare Shi sai ku dõgara, idan kun kasance Musulmi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "Sai suka ce: \"Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu fitina ga mutãne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "\"Kuma Ka kuɓutar da mu dõmin RahamarKa, daga mutãne kãfirai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutãnenku a Masar a cikin wasu gidãje. Kuma ku sanya gidãjenku su fuskanci Alƙibla*, kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bãyar da bushãra ga mãsu ĩmãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Su sanya gidãjensu sunã fuskantar Alƙibla ta Ka'aba dõmin su riƙa yin salla a cikin gidãjen, sabõda tsõron in sun tafi masallaci zã a fãɗa su da dũka sunã a cikin salla. Wannan kuma yã nũna yadda ake son gidajen Musulmi su kasance a kõ da yaushe. "
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 218,
            "translated_text": "Sai MũSã ya ce: \"Yã Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyõyi a cikin rãyuwar dũniya, yã Ubangijinmu, dõmin su ɓatar (damutãne) daga hanyarKa. Yã Ubangijinmu! Ka shãfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri* a kan zukãtansu yadda bã zã su yi ĩmãni ba har su ga azãba mai raɗaɗi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mũsã ya yi addu'a a kansu, har da rashin ĩmãni sabõda yã sãmi lãbãrin bã zã su yi imãni ba, kamar mutãnen Nũhu."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 219,
            "translated_text": "(Allah) Yã ce: \"Lalle ne an karɓi addu'arku. Sai ku daidaitu kuma kada ku bi hanyar waɗanda ba su sani ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 219,
            "translated_text": "Kuma Muka ƙẽtãrar da Banĩ Isrã'ila tẽku sai Fir'auna da rundunarsa suka bĩ su bisa ga zãlunci da ƙẽtare haddi, har a lõkacin da nutsẽwa ta riske shi ya ce: \"Nã yi* ĩmãni cẽwa, haƙĩƙa, bãbu abin bautawa fãce wannan da Banũ Isrã'il suka yi ĩmãni da Shi, kumanĩ, ina daga Musulmi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ĩmãni a bãyan Manzon mutuwa ya isa ga kãfiri bã zai yi masa amfãni ba. "
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 219,
            "translated_text": "Ashe! A yanzu! Alhãli kuwa, haƙĩƙa ka sãɓa a gabãni, kuma ka kasance daga mãsu ɓarna?"
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 219,
            "translated_text": "To, a yau Munã kuɓutar* da kai game da jikinka, dõmin ka kasance ãyã ga waɗanda suke a bãyanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kuɓutar da jikin Fir'auna: Banda rũhinsa dõmin a tabbatar da yã mutu. "
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 219,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun zaunar* da Banĩ Isrã'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzũta su daga abũbuwa mãsu dãɗi. Sa'an nan ba su sãɓa ba har ilmi ya jẽ musu. Lalle ne Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar Kiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Allah Yã bai wa Banĩ Isrã'ila mulkin Masar da falasɗĩnu gabã ɗaya a bãyan halaka Fir'auna da mutãnensa."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 219,
            "translated_text": "To, idan ka kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littãfi daga gabaninka. Lalle ne, haƙĩƙa, gaskiya tã jẽ maka daga Ubangijinka dõmin haka kada ka kasance daga mãsu kõkanto."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 219,
            "translated_text": "Kuma kada ka kasance daga waɗanda suke ƙaryatãwa game da ãyõyin Allah, har ka kasance daga mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 219,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda kalmar Ubangijinka ta wajaba a kansu, bã zã su yi ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 219,
            "translated_text": "Kuma kõ dã kõwace ãyã ta jẽ musu, sai sun ga azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 220,
            "translated_text": "To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi* ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Alƙaryun da aka aika da Manzanni cikinsu, ba su yi ĩmãni duka ba fãce mutum ɗaya, kõ biyu a gabãnin halaka ta sãmi mutãnensu. Sai dai alƙaryar Yũnusa, ita kam tã ji tsõro, ta yi ĩmãni a gabãnin saukar azãba, sabõda haka suka tshĩra, ba a halaka garin bawatau Nĩnawa. Watau bãbu mai iya sãmun ĩmãni sai Allah Ya nufe shi da haka. Kõ da mai yin gargaɗin ya kan yiwu ya karkace, sai da tsarin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 220,
            "translated_text": "Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã waɗanda suke a cikin ƙasa sun yi ĩmãni dukansu gabã ɗaya. Shin, kai kanã tĩlasta mutãnene har su kasance mãsu ĩmãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 220,
            "translated_text": "Kuma ba ya kasancẽwa ga wani rai ya yi ĩmãni fãce da iznin Allah, kuma (Allah) Yanã sanya ƙazanta a kan waɗanda bã su yin hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 220,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku dũbi abin da yake cikin sammai da ƙasa.\"Kuma ãyõyi da gargaɗi bã su wadãtarwa ga mutãne waɗanda bã su yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 220,
            "translated_text": "To, Shin sunã jiran wani abu fãce kamar misãlin kwãnukan waɗanda suka shũɗe daga gabãninsu? Ka ce: \"Ku yi jira! Lalle nĩ tãre da ku, inã daga mãsu jira.\""
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 220,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Munã kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da mãsu ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 220,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã kũ mutãne! Idan kun kasance a cikin kõkanto daga addinĩna, to bã ni bauta wa, waɗanda kuke, bautã wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rãyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu ĩmãni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 220,
            "translated_text": "\"Kuma (an ce mini): Ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga mãsu shirka."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 220,
            "translated_text": "\"Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 221,
            "translated_text": "Kuma idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, bãbu mai yãyẽ ta fãce shi, kuma idan Yanã nufin ka da wani alhẽri, to, bãbumai mayar da falalarSa. Yanã sãmun wanda Yake so daga cikin bãyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 221,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã ku mutãne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 10,
            "page_number": 221,
            "translated_text": "Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 221,
            "translated_text": "A. L̃.R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa'an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 221,
            "translated_text": "Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 221,
            "translated_text": "Kuma ku nẽmi gãfara gun Ubangijinku. Sa'an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar da ku dãɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan ma'abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, inã tsõron azãbar yini mai girma a kanku."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 221,
            "translated_text": "Zuwa ga Allah makõmarku take, kuma Shĩ a kan kõmeMai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 221,
            "translated_text": "To, lalle sũ sunã karkatar* da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bã su son su ga mai yi musu wa'azi, sabõda haka idan sun tsinkãyi Annabi daga nesa, sai su ɓũya, dõmin kada ya gan su, balle ma har ya yi musu wa'azi. Kuma har idan ya sãme su da wa'azinsa, sai su sanya tufãfinsu su rufe idanunsu da kunnuwansu kamar yadda mutãnen Nũhu suka yi masa a lõkacin da yake yi musu wa'azi. Ka dũba sũratu Nũh' sũra ta 71."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 222,
            "translated_text": "Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa fãce ga Allah arzikinta yake, kuma Yanã sanin matabbatarta* da ma'azarta, duka sunã cikin littãfi bayyananne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Matabbatã shĩ ne uba, kuma ma'aza ita ce uwa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 222,
            "translated_text": "Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma Al'arshinSa ya kasance akan ruwa, dõmin Ya jarrabã ku, wannan ne daga cikinku mafi kyãwon aiki. Kuma haƙĩƙa idan ka ce: \"Lalle kũ waɗanda ake tãyarwa ne a bãyan mutuwa,\" haƙĩƙa waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: \"Wannan bai zama ba fãce sihiri bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 222,
            "translated_text": "Kuma lalle ne idan Mun jinkirta da azãba gare su zuwa ga wani lõkaci ƙidãyayye, haƙĩƙa sunãcẽwa me yake tsare* ta? To, a rãnar da zã ta je musu, ba ta zama abin karkatarwa ba daga gare su. Kuma abin da suka kasance suna yin izgili da shi, yã wajaba a kansu.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Me ke tsare ta, watau azãbar me ke hana ta ta zo yanzu?. "
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 222,
            "translated_text": "Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sa'an nan kuma Muka zãre ta daga gare shi, lalle ne shĩ, hakĩka, mai yanke tsammãnine, mai yawan kãfrci."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 222,
            "translated_text": "Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana masa ni'ima a bãyan cũta ta shãfe shi, Yana cẽwa mũnanan halaye sun tafi daga wurina. Lalle shi mai farin ciki ne, mai alfahari."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 222,
            "translated_text": "Sai waɗanda suka yi haƙuri kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai. Waɗannan sunã da gãfara da lãda mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 222,
            "translated_text": "Sabõda haka tsammãninka kai mai barin sãshen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka ne, kuma mai ƙuntata ƙirjinka da shi ne dõmin sun ce: \"Dõmin me ba a saukar masa da wata taska ba, kõ kuma Malã'ika ya zo tãre de shi?*\" Kai mai gargaɗi ne kawai. Kuma Allah ne wakili a kan kõme.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sabõda zaman mutãne bã su girmama mutum sai idan Yanã da wata dũkiya kõ kuma akwai wani ƙarfi bayyananne tãre da shi, to, kai kuma ga zãhiri, bã ka da dukiya kõ wani ƙarfin da zã ka iya tĩlasta su da shi a kan wani abu. Sabõda haka kanã tsõron iyar da duka abin da aka umurce ka, dõmin kada a ƙaryata ka. To, kada ka ji tsõron iyarwã, Allah ne wakili a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 223,
            "translated_text": "Kõ sunã cewa: \"Yã ƙirƙira *shi ne.\"Ka ce: \"Sai ku zo da sũrõri gõma misãlinsa ƙirƙirarru, kuma ku kirãyi wanda kuke iyãwa, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kõ kuwa bã zã ka iyar da abin da aka aike ka ba dõmin tsõron su ce: \"Kai ne ka ƙirƙira Alƙur'ãni, sa'an nan ka jinginã shi ga Allah.\" To, sai ka ce: \"Ni mutum ne kamarku, idan nĩ na ƙirƙira Alƙur'ãni, to, bã zai gãgare ku ku ƙirƙira irinsa ba, sai ku zo da surõri gõma irinsa.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 223,
            "translated_text": "To, idan ba su amsa muku ba, to, ku sani cẽwa an saukar da shi kawai ne da sanin Allah, kuma cẽwa bãbu abin bauta wa fãce Shi. To, shin, kũ mãsu sallamãwa ne?,"
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 223,
            "translated_text": "Wanda ya kasance yã yi nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, Munã cika musu ayyukansu zuwa gare su a cikinta, kuma a cikinta bã zã a rage su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 223,
            "translated_text": "Waɗannan ne waɗanda bã su da kõme a cikin Lãhira fãce wuta, kuma abin da suka sanã'anta a cikinta (dũniya) yã ɓãci, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa ɓãtacce ne."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 223,
            "translated_text": "Shin, wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma wata shaida tanã biyar sa daga gare Shi, kuma a gabãninsa akwai littãfin Mũsãabin kõyi da rahama? Waɗannan sunã yin ĩmãni da shi, kuma wanda ya kãfirta da shi daga ƙungiyõyi, to, wutã ce makõmarsa. Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga gare shi. Lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka, amma kuma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 223,
            "translated_text": "Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah? Waɗannan anã gitta su ga Ubangijinsu, kuma mãsu shaida su ce: \"Waɗannan ne suka yi ƙarya ga Ubangijinsu. To, la'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 223,
            "translated_text": "Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah kuma sunã nẽman ta karkace, kuma sũ ga Lãhira sunã kãfirta."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 224,
            "translated_text": "Waɗannan ne ba su kasance mabuwãya ba a cikin ƙasa, kuma waɗansu masõya ba su kasance ba a gare su, baicin Allah. Anã ninka musu azãba, ba su kasance sunã iya ji ba, kuma ba su kasance sunã gani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 224,
            "translated_text": "Waɗannan ne wɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirawa ya ɓace musu."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 224,
            "translated_text": "Bãbu makawã cẽwa, haƙĩƙa, sũ a lãhira, sũ ne mafi hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 224,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi tawãlu'i zuwa ga Ubangijinsu, waɗannan ne abõkan Aljanna, sunã madawwama a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 224,
            "translated_text": "Misãlin ɓangaren biyu kamar makãho ne da kurmã, da mai gani da mai ji. Shin, sunã daidaita ga misãli? Ashe, bã ku yin tunãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 224,
            "translated_text": "Kuma haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutanensa, (ya ce): \"Lalle ne ni, a gare ku mai gargaɗi bayyananne ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 224,
            "translated_text": "\"Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ, inã jin tsõron azãbar yini mai raɗaɗi a kanku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 224,
            "translated_text": "Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta, daga mutãnensa, suka ce: \"Bã mu ganin ka fãce mutum kake kamarmu, kuma ba mu ganin wani ya bĩ ka fãce waɗanda suke sũ ƙasƙantattunmu ne marasa tunani. Kuma bã mu ganin wata falalã agare ka a kanmu. Ã'a, Munã zaton ku maƙaryata ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 224,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya mutãnena! Shin, kun gani idan na kasance a kan wata hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Yã bã ni wata Rahama daga wurinSa, Sa'an nan aka rufe ta (ita Rahamar) daga gare ku, shin, zã mu tĩlasta mukuita, alhãli kuwa kũ mãsu ƙi gare ta ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 225,
            "translated_text": "\"Kuma yã mutãnena! Bã zan tambaye ku wata dũkiya ba akansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce daga Allah, kuma ban zama mai kõrar waɗanda suka yĩ ĩmãni ba. Haƙĩƙa sũ, mãsu haɗuwa da Ubangijinsu ne, kuma amma ni, inã ganin ku mutãne ne jãhilai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 225,
            "translated_text": "\"Kuma ya mutãnena! Wãne ne yake taimakõna daga Allah idan na kõre su? Ashe, bã ku tunãni?\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 225,
            "translated_text": "\"Kuma bã ni ce muku a wurĩna taskõkin Allah suke kuma bã inã sanin gaibi ba ne. Kuma ba inã cẽwa ni Malã'ika ba ne. Kuma ba ni cẽwa ga waɗanda idãnunku suke wulãkantãwa, Allah bã zai bã su alhẽri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (nã yi haka) dã ina daga cikin azzalumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 225,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã Nũhu, lalle ne kã yi jayayya da mu, sa'an nan kã yawaita yi mana jidãli, to, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi idan kã kasance daga mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 225,
            "translated_text": "Ya ce: \"Allah kawai ne Yake zo muku da shi idan Ya so. Kuma ba ku zama mabuwãya ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 225,
            "translated_text": "\"Kuma nasĩhãta bã zã ta amfãne ku ba, idan nã yi nufin in yi muku nasĩha, idan Allah Yakasance Yanã nufin Ya halaka ku. Shĩ ne Ubangijinku, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 225,
            "translated_text": "Ko sunã cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: \"Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to, laifĩnã a kaina yake, kuma nĩ mai barrantã ne daga abin da kuke yi na laifi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 225,
            "translated_text": "Kuma aka yi wahayi zuwa ga Nũhu cẽwa: Lalle ne bãbu mai yin ĩmãni daga mutãnenka fãce wanda ya riga ya yi ĩmãnin, sabõdahaka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 225,
            "translated_text": "Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau a kan idanunMu da wahayinMu, kuma kada ka yi Mini magana a cikin sha'anin waɗanda suka kãfirta, lalle ne sũ, waɗanda akenutsarwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 226,
            "translated_text": "Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga mutãnensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: \"Idan kun yi izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin izgili."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 226,
            "translated_text": "\"Sa'an nan da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira).\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 226,
            "translated_text": "Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: \"Ka ɗauka, a cikinta, daga kõme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta a kansa*, da wanda ya yi ĩmãni.\" Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi fãce kaɗan.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Iyalan Nũhu sun yi ĩmãni banda ɗansa Yãmu, da matarsa guda kãfira. Waɗanda suka yi ĩmãni daga sauran mutãnensa tamãnin ne maza da mãtã. Amma kuma an ce mutãne saba'in da biyu ne, kuma an ce gõma ne. Allah ne Mafi sani."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 226,
            "translated_text": "Kuma ya ce: \"Ku hau a cikinta, da sũnan Allah magudãnarta da matabbatarta. Lalle ne Ubangijĩna, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 226,
            "translated_text": "Kuma ita tanã gudãna da su a cikin tãguwar ruwa kamai duwãtsu, sai Nũhu ya kirãyi ɗansa alhãli, kuwa ya kasance can wuri mai nĩsa. \"Yã ƙaramin ɗãnã! zo ka hau tãre da mu, kuma kada ka kasance tãre da kãfirai!\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 226,
            "translated_text": "Ya ce: \"Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan.\" (Nũhu) ya ce: \"Bãbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah fãce wanda Ya yi wa rahama.\" Sai taguwar ruwa ta shãmakace a tsakãninsu, sai ya kasance daga waɗanda aka nutsar."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 226,
            "translated_text": "Kuma aka ce: \"Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme.\"Kuma aka faƙar da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi*, kuma aka ce: \"Nĩsa ya tabbata ga mutãne azzãlumai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Judiyyu sũnan wani dũtse ne a cikin Jazĩra. Jirgin Nũhu ya zauna a kansa, har mutãnen farko na wannan al'umma sun gan shi. Sa'an nan ya halaka."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 226,
            "translated_text": "Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa'an nan ya ce: \"Yã Ubangijina! Lalle ne ɗãna na daga iyãlĩna! Kuma haƙĩƙa wa'adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin mãsu yin hukunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 227,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Nũhu! Lalle ne shi bã ya a ciki iyãlanka, lalle ne shĩ, aiki ne wanda ba na ƙwarai ba, sabõda haka kada ka tambaye Ni abin da bã ka da ilmi a kansa. Haƙĩƙa, Nĩ Inã yi maka gargaɗi kada ka kasance daga jãhilai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 227,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini rahama, zan kasance daga mãsu hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 227,
            "translated_text": "Aka ce: \"Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma rahama ta tabbata a kan waɗansu al'ummõmi daga waɗanda suke tãre da kai. Da waɗansu al'ummõmi da zã Mu jiyar da su dãɗi, sa'an nan kuma azãba mai raɗaɗi ta shafe su daga gare Mu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 227,
            "translated_text": "Waccan ƙissa tanã daga lãbãran gaibi, Munã yin wahayinsu zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance kanã sanin su ba, haka kuma mutãnenka ba su sani ba daga gabãnin wannan. Sai ka yi haƙuri. Lalle ne ãƙiba tanã ga mãsu taƙawa,"
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 227,
            "translated_text": "Kuma zuwa ga Ãdãwa, (Mun aika) ɗan'uwansu Hũdu. Ya ce: \"Yã kũ mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Ba ku kasance ba fãce kunã mãsu ƙirƙirãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 227,
            "translated_text": "\"Yã ku mutãnena! Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce ga wanda Ya ƙãga halittata. Shin fa, bã ku hankalta?\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 227,
            "translated_text": "\"Kuma, ya mutãnena! Ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi, zai saki sama a kanku, tanã mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kunã mãsu laifi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 227,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã Hũdu! Ba ka zo mana da wata hujja bayyananna ba, kuma ba mu zama mãsu barin abũbuwan bautawarmu ba dõmin maganarka, kuma ba mu zama mãsu yin ĩmãni da kai ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 228,
            "translated_text": "\"Bã mu cẽwa, sai dai kurum sashen abũbuwan bautawarmu ya sãme ka da cũtar hauka.\" Yace: \"Lalle ne nĩ, inã shaida waAllah, kuma ku yi shaidar cẽwa\" lalle ne nĩ mai barranta ne dagb abin da kuke yin shirki da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 228,
            "translated_text": "\"Baicin Allah: Sai ku yi mini kaidi gabã ɗaya, sa'an nan kuma kada ku yi mini jinkiri.\""
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 228,
            "translated_text": "\"Haƙĩƙa, ni na dõgara ga Allah, Ubangijĩna kuma Ubangijinku. Bãbu wata dabba fãce Shi ne Mai riko ga kwarkwaɗarta*. Haƙĩƙa, Ubangijĩna Yanã (kan) tafarki madaidaici.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Gãshin gõshin dabba."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 228,
            "translated_text": "\"To! Idan kun jũya, haƙĩƙa, nã iyar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare ku. Kuma Ubangijĩna Yanã musanya waɗansu mutãne, waɗansunku su maye muku. Kuma bã ku cũtar Sa da kõme. Lalle Ubangijina a kan dukkan kõme, Matsari ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 228,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da umurninmu ya je, Muka kuɓutar da Hũdu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõdawata rahama daga gare Mu. Kuma Muka kuɓutr da su daga azãba mai kauri."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 228,
            "translated_text": "Haka Ãdãwa suka kasance, sun yi musun ãyõyin Ubangijinsu, kuma sun sãɓa wa ManzanninSa, kuma sun bi umurnin dukan mai girman kai, makangari."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 228,
            "translated_text": "Kuma an biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. To! Lalle ne Ãdãwa sun kãfirta da Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Ãdãwa, mutãnen Hũdu!"
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 228,
            "translated_text": "Kuma zuwa ga Samũdãwa (an aika) ɗan'uwansu Sãlihu. Ya ce: \"Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Shĩ ne Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma Ya sanya ku mãsu yin kyarkyara a cikinta. Sai ku nẽme Shi gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai karɓãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 228,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ya Sãlihu! Haƙĩƙa, kã kasance a cikinmu, wanda ake fatan wani alhẽri da shi a gabãnin wannan. Shin kana hana mu bauta wa abin da ubanninmu suke bauta wa? Kuma haƙĩƙa mũ, munã cikin shakka daga abin da kake kiran mu gare shi, mai sanya kõkanto.\""
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 229,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya mutãnẽna! Kun gani? Idan na kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Ya bã ni rahama daga gare Shi, to, wane ne zai taimake ni daga Allah idan nã sãɓa Masa? Sa'an nan bã zã ku ƙãre ni da kõme ba fãce hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 229,
            "translated_text": "\"Kuma ya mutãnena! wannan rãƙumar Allah ce, tanã ãyã a gare ku. Sai ku bar ta ta ci a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta kar azãba makusanciya ta kãma ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 229,
            "translated_text": "Sai suka sõke ta. Sai ya ce: \"Kuji dãɗi a cikin gidãjenku kwãna uku. Wannan wa'adi ne bã abin ƙaryatãwa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 229,
            "translated_text": "To, a lõkacin da umurninMu ya je, muka kuɓutar da Sãlihu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma daga wulãkancin rãnar nan. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMai ƙarfi, Mabuwãyi."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 229,
            "translated_text": "Sai tsãwa ta kãma waɗanda suka yi zãlunci, sai suka wãyi gari sunã guggurfãne a cikin gidãjensu."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 229,
            "translated_text": "Kamar dai ba su zauna a cikinta ba. To! Lalle ne samũdãwa sun kãfirce wa Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Samũdãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 229,
            "translated_text": "Kuma haƙĩƙa, manzanninMu sun je wa Ibrãhim da bushãra suka ce: \"Aminci.\" Ya ce: \"Aminci (ya tabbata a gare ku).\" Sa'an nan bai yi jinkiri ba ya je da maraƙi ƙawãtacce."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 229,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da ya ga hannayensu bã su sãduwa zuwa gare shi (maraƙin), sai ya yi ƙyãmarsu, kuma ya ji tsõronsu. Suka ce, \"Kada kaji tsõro lalle ne mũ, an aiko mu ne zuwa ga mutãnen Lũɗu\""
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 229,
            "translated_text": "Kuma mãtarsa tanã tsaye.* Ta yi dãriya. Sai Muka yi mata bushãra (da haihuwar) Is'hãƙa, kuma a bayan Is'hãƙa, Yãƙũbu.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Matar Ibrãhĩm Sãrah tanã tsaye ga yi musu hidima, sai ta yi dãriyar mamãki, dõmin bãƙin sun ƙi cin abinci. Waɗansu na fassarãwa ta yi haila. Wannan bai dãce ba."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "Sai ta ce: \"Yã kaitõna! Shin, zan haihu ne alhãli kuwa inã tsõhuwa, kuma ga mijĩna tsõho ne? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmãki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "Suka ce: \"Shin kinã mãmaki ne daga al'amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarSa su tabbata a kanku, ya mutãnen babban gida! Lalle ne Shĩ abin gõdewa ne, Mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "To, a lõkacin da firgita ta tafi daga Ibrãhĩm, kuma bushãra tã je masa, Yanã mai jayayya a gare Mu, sabõda mutãnen Lũɗu!"
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "Lalle Ibrãhĩm, haƙĩƙa mai haƙuri ne, mai yawan addu'a, mai tawakkali."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "Ya Ibrãhĩm! Ka bijira daga wannan. Lalle shi, haƙĩƙa, umurnin Ubangijinka ne ya zo, kuma lalle ne sũ, abin da yake mai je musu azãba ce wadda bã a iya hanãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da manzanninMu suka je wa Lũɗu aka ɓãta masa rai game da su, ya, ƙuntata rai sabõda su. Ya ce: \"Wannan yini ne mai tsananin masĩfa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "Kuma mutãnensa suka je masa sunã gaggãwa zuwa gare shi, kuma a gabãni, sun kasance sunã aikatãwar mũnãnan ayyuka. Ya ce: \"Yã mutãnẽna! waɗannan, 'yã'yã na* sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulãkantã ni a cikin bãƙĩna. Shin, bãbu wani namiji shiryayye daga gare ku?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * 'Ya'yansa-Yanã nufin mãtan aurensu, dõmin kõwane Annabi uban al'ummarsa ne.Bã ya kamãta a ce wai yanã kiran mazan gari zuwa ga 'ya'yansa uku, dõmin bãbu wata shari'a ta Allah, ga saninmu, wadda ta halattã haɗuwar mazã biyu ko fiye da biyu a kan auren mace guda."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle, haƙĩƙa kã sani, bã mu da wani hakki a cikin 'ya'yanka, kuma lalle kai haƙĩƙa, kanã sane da abin da muke nufi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "Ya ce: \"Dã dai inã da wani ƙarfi game da ku, kõ kuwa inã da gõyon bãya daga wani rukuni* mai ƙarfi?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ya faɗi haka dõmin bã shi da dangi a cikinsu. Daga gare shi ba a kuma aiko wani Annabi ba sai a cikin wadãtar danginsa."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 230,
            "translated_text": "(Manzannin) Suka ce: \"Yã Lũɗu! Lalle mũ, manzannin Ubangijinka ne. Bã zã su iya sãduwa zuwa gare ka ba. Sai ka yi tafiyarka a wani yankin dare da iyãlinka, kuma kada wani daga gare ku ya waiwaya fãce mãtarka. Lalle ne abin da ya same su mai sãmunta ne. Lalle wa'adinsu lõkacin sãfiya ne. Shin lõkacin sãfiya bã kusa ba ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 231,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu a kanta (ƙasar Lũɗu) daga taɓocũrarre."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 231,
            "translated_text": "Alamtacce a wurin Ubangijinka. Kuma ita (ƙasar Lũɗu) ba ta zama mai nĩsa ba daga azzãlumai (kuraishãwa)."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 231,
            "translated_text": "Kuma zuwa ga Madyana (Mun aika) ɗan'uwansu* Shu'aibu. Ya ce: \"Ya Mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce shi kuma kada ku rage mũdu da sikẽli. Lalle nĩ, inã ganin ku da wadãta**. Kuma lalle inã ji muku tsõron azãbar yini mai kẽwayẽwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Lãrabãwa ne, sunã zaune a tsakãnin Hijaz da Shãm. ** Inã ganin ku a cikin wadãta; bã ku da bukãtar rage wa mutãne kãyansu. Sabõda haka ku yi adalci ga mutãne wajen ciniki ya fi muku alheri daga dũkiyar haram mai ƙãrewa kõme yawanta."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 231,
            "translated_text": "\"Ya mutãnẽna! Ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, kuma kada ku naƙasta wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi ɓarnã a cikin ƙasa kunã mãsu fasãdi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 231,
            "translated_text": "\"Falalar Allah mai wanzuwa ita ce mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni bã mai tsaro ne a kanku ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 231,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã Shu'aibu! Shin sallarka ce take umurtar ka ga mu bar abin da ubanninmu suke bautãwa, kõ kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin dũkiyõyinmu? Lalle, haƙĩƙa kai ne mai haƙuri shiryayye!\""
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 231,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya mutãnena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyãwo daga gare Shi? Kuma bã ni nufin in sãɓa muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bã ni nufin kõme fãce gyãrã, gwargwadon da na sãmi dãma. Kuma muwãfaƙãta ba ta zama ba fãce daga Allah. A gare shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala.\""
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 232,
            "translated_text": "\"Kuma ya mutãnena! Kada sãɓa mini ya ɗauke ku ga misãlin abin da ya sãmi mutãnen Nũhu kõ kuwa mutãnen Hũdu kõ kuwa mutãnen Sãlihu ya sãme ku. Mutãnen Lũɗu ba su zama a wuri mai nĩsa ba daga gare ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 232,
            "translated_text": "\"Kuma ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare shi. Lalle Ubangijĩna Mai Jin ƙai ne, Mai nũna sõyayya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 232,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã Shu'aibu! Bã mu fahimta da yawa daga abin da kake faɗi, kuma munã ganin ka mai rauni a cikinmu. Kuma bã dõmin jama'arka ba dã mun jẽfe ka, sabõda ba ka zama mai daraja a gunmu ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 232,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya mutãnena! Ashe, jama'ãta ce mafi daraja a gare ku daga Allah, kuma kun riƙẽ Shi a bãyanku abin jẽfarwa? Lallene Ubangijĩna Mai kẽwayẽwa nega abin da kuke aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 232,
            "translated_text": "\"Kuma ya mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku. Lalle nĩmai aiki ne. Da sannu zã ku san wãne ne azãba zã ta zo masa, ta wulakanta shi, kuma wãne ne maƙaryaci. Kuma ku yi jiran dãko, lalle ni mai dãko ne tãre da ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 232,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da umurninMu yã je, Muka kuɓutar da Shu'aibu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare, Mu. Kuma tsãwa ta kama waɗanda suka yi zãlunci. Sai suka wãyi gari guggurfãne a cikin gidãjensu."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 232,
            "translated_text": "Kamar ba su zaunã ba a cikinsu. To, halaka ta tabbata ga Madyana kamar yadda Samũdãwa suka halaka."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 232,
            "translated_text": "Kuma haƙĩƙa Mun aiki Mũsã da ãyõyinMu, da dalĩli bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 232,
            "translated_text": "Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa. Sai suka bi umurnin Fir'auna, amma al'amarin Fir'auna bai zama shiryayye ba."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Yanã shũgabantar mutãnensa a Rãnar Kiyãma, har ya tuzgar da su a wuta. Kuma tir da irin tuzgãwarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. Tir da kyautar* da ake yi musu.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Kyautar la'ana ita ce wadda ake la'antar su da ita a dũniya da Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Wancan Yanã daga lãbãran alƙaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Daga nan zuwa ƙarshen sũra ta'alĩƙi ne dõmin farkarwa. Mai tsayi, watau tana nan tsaye, alãmõminta ba su ɓãce ba, kuma akwai waɗanda suka halaka kamar karan da aka girbe."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun zãlunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawarsu waɗanda suke kiran su, baicin Allah, ba su wadãtar musu kõme ba a lõkacin da umurnin Ubangijinka ya je, kuma (gumãkan) ba su ƙãra musu wani abu ba fãce hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan ne kãmun Ubangijinka, idan Ya kãma alƙaryõyi alhãli kuwa sunã mãsu zãlunci. Lalle kamũnSa mai raɗaɗi ne, mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga wanda ya ji tsõron azãbar Lãhira. Wancan yini ne wanda ake tãra mutãne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Ba Mu jinkirtã shi ba fãce dõmin ajali ƙidãyayye."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Rãnar da za ta zo wani rai ba ya iya magana fãce da izninSa. Sa'an nan daga cikinsu akwai shaƙiyyi da mai arziki."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "To, amma waɗanda suka yi shaƙãwa, to, sunã a cikin wuta. Sunã mãsu ƙãra da shẽka acikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatãwa ne ga abin da Yake nufi."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 233,
            "translated_text": "Amma waɗanda suka yi arziki to, sunã a cikin Aljanna sunã madawwama, a cikinta, matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda bã ta yankẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 234,
            "translated_text": "Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma haƙĩƙa Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 234,
            "translated_text": "Kuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãɓã* wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma haƙĩƙa, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Yahũdãwa sun sãɓa wa jũna a cikin littattafan da aka bai wa Mũsã. To, ku Musulmi kada ku bi hanyarsu, har ku sãɓawa Allah, har abin da ya sãme su ya sãme ku."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 234,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa, Ubangijinka Mai cika wa kõwa (sakamakon) ayyukansa ne. Lalle Shĩ, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 234,
            "translated_text": "Sai ka daidaitu* kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan ãyã tanã hana dukan bidi'a a cikin addini. Tun da ba a yarda Annabi ya ƙara ra'ayinsa ba sai dai ya bi umurnin Allah kamar yadda Ya yi umurnin, kuma haka ne Ya umurci wanda ya bi Annabi. Sabõda haka mai sãɓa wa umurnin Allah da ƙãri ko ragi, bã ya cikin mabiyan Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 234,
            "translated_text": "Kada ku karkata* zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ba ya halatta ga Musulmi ya karkata zuwa ga kãfirai kamar yadda bã ya halatta ya karkata a cikin addininsa. Wannan shĩ ne babban makãmi a kan mãƙĩya."
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 234,
            "translated_text": "Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. Wancan* ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tsayar da sallõli farillai tãre da Lĩman a cikin masallatai shĩ ne zikiri ga mai son zikirin gaskiya. Ayyukan ƙwarai sunã shãfe miyãgu."
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 234,
            "translated_text": "Kuma ka yi haƙuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa.(5)<br \/>\n____________________<br \/>\n(5) Haƙuri a kan ibãda wãjibi ne, haka kuma kyautatãwa, wãtau shĩ ne yin kõwãne aiki na ibãda tsantsa kamar salla kõ na ma'amala kamar ciniki da aure, dõmĩn Allah kawai. An yi wa wannan fanni na biyu sũna da \"Tasawwuf\", bidi'a ne dõmin bai taho daga sunna ba. Asalinsa \"theosophy\" daga lugar Ajam, ma'anarsa neman hikima ta Allah a hãlin keɓance kai a cikin kaɗaita da wasu aikace-aikace na ibada, kamar girka ga 'yanbõri."
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 234,
            "translated_text": "To, don me mãsu hankali ba su kasance daga mutãnen ƙarnõnin da suke a gabãninku ba, sunã hani daga ɓarna a cikin ƙasa? fãce kaɗan daga wanda Muka kuɓutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma waɗanda suka yi zãlunci suka bin abin da aka ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 234,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinka bai kasance Yanã halakar da alƙaryu sabõda wani zãlunci ba, alhãli mutãnensu sunã mãsu gyãrãwa.(6)<br \/>\n____________________<br \/>\n   (6) Wannan ãyã da ta sama da ita sunã nũna muhimmancin wa'azi a cikin kõwane hãli na al'umma, dõmin tsarewar zamanta al'umma."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã Yã sanya mutãne al'umma guda. Kuma bã zã su gushe ba sunã mãsu sãɓã wa jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama, kuma dõmin wannan* ne Ya halicce su. Kuma kalmar \"Ubangijinka\" Lalle ne zã Ni cika Jahannama da aljannu da mutãne gaba ɗaya\" ta cika.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Allah ya halicci mutãne da hãlãye dabam-dabam dõmin su sãɓa wa jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "Kuma dũbi dai Munã bã da lãbãri a gare ka daga lãbarun Manzanni, abin da Muke tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan da wa'azi da tunãtarwã ga mãsu ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "kuma kace wa waɗanda bã su yin ĩmãni, \"Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle mũ mãsu aiki ne."
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "\"Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko* ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ku yi jira ku gani wãne ne zai ci nasara; mũ da muka bi umurnin Allah, kõ kuwa ku da kuke bin zuciyõyinku. Ãƙiba dai tanã ga mãsu taƙawa. Allah ya tabbatar da mu a kan binsa a kan taƙawa. Amin."
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 11,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake. Kuma zuwa gare Shi ake mayar da dukan al'amari. Sabõda haka ku bauta Masa kuma ku dõgara a kanSa. Kuma Ubangijinka bai zama Mai gafala daga abin da kuke aikatãwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga gafalallu."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 235,
            "translated_text": "A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, \"Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tarbiyyar uba ga ɗansa.Yaro ƙarami anã renon sa da jawãbi mai laushi a fahimtar matsayin yãron."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "\"Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima.\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi* sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa** dõmin mãsu tambaya.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ãyõyi a nan, anã nufin hãlãye waɗanda suka zama darussa na kõyarwa ga mutãne dõmin tarbiyya ga yãra da manya na kõwane matsayi ga rãyuwar ɗan Ãdam. ** Yũsufu da ɗan'uwansa shaƙĩƙi, Binyãmĩnu, da sauran gõma. Babbansu ga shekaru, shi ne Raubĩlu, kuma sai Lãwiya. A cikin gidansa aka yi Annabãwa, sai Yahũza kuma shĩ ne shũgabansu a ra'ayi, shĩ ne uban sarãkunansu, sabõda haka sũnansa ya rinjãya a kan ƙabĩlar, aka ce musu Yahũdu."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "A lõkacin da suka ce:* lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hĩrar yãra a tsakãninsu. Sunã tunãnin sõyayyar ubansu ga ɗayansu wanda bã ya cikinsu yanzu. Sunã tunãnin yadda zã su sãmi ãdalcin daidaitãwar so daga ubansu bãki ɗayansu. Ɗan'uwansu wanda ubansu yake so, watau Yũsufu, ya sãmi baƙin jini daga gare su dõmin ubansu yana sonsa. Sabõda haka shaiɗan yanã sanya musu tunãnin su yi zunubin rabuwa da shi, sa'an nan su tũba ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "Wani mai magana daga cikinsu ya ce: \"Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã bãbanmu(5)! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Sun fara zartar da abin da suka shirya, watau ɗauke Yusufu daga gaban ubansa. Sun fãra da maganar da ubansu yake so game da su tattara da ɗan'uwansu ƙarami. Sunã muhãwara da ubansu sunã neman yardarsa don ya bar su su tafi da Yusufu."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "\"Ka bar shi tãre da mu a gõbe, ya ji dãɗi, kuma ya yi wãsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, mãsu tsaro ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne ni, haƙãƙa yanã ɓãta mini rai ku tafii da shi, Kuma inã tsõron kerkẽci ya cinye shi, alhãli ku kuwa kunã mãsu shagala daga gare shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 236,
            "translated_text": "Suka ce: \"Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhãli kuwa munã dangin jũna, lalle ne mũ, a sa'an nan, hakĩka, mun zama mãsu hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 237,
            "translated_text": "To, a lõkacin* da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, \"Lalle ne, kanã bã su lãbari game da wannan al'amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Suka cire rĩgarsa, suka jefa shi da gũga a cikin rĩjiya. Sa'an nan suka sanya wa rigarsa jinin wata dabba da suka yanka, dõmin ya zama alãmar cewa kerkeci ya cinye Yũsufu. Gã rĩgarsa ta ɓãci da jinin jikinsa, watau jinin shĩ ne alãmar yã mutu. Sai suka manta cewa kãfin kerkeci ya cinye yãro a cikin rĩgarsa, sai yã kekketa rĩgar tukun."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 237,
            "translated_text": "Kuma suka je wa ubansu da dare sunã kũka."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 237,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã bãbanmu!* Lalle ne, mun tafi munã tsẽre, kuma muka bar Yusufu a wurin kãyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bã mai amincẽwa da mu ba ne, kuma kõ dã mun kasance mãsu gaskiya!\"_<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muhãwararsu tãre da ubansu.Yã nũna baƙin ciki, amma kuma ya mayar da al'amari ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 237,
            "translated_text": "Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: \"Ã'a, zukatanku suka ƙawãta muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake nẽman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 237,
            "translated_text": "Kuma wani ãyari* ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: \"Yã bushãrata! Wannan yãro ne.\" Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ãyari ya je kusa da rĩjiyar Yũsufu, har suka kãma shi ya zama bãwa abin sayarwa a hannunsu."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 237,
            "translated_text": "Kuma suka sayar* da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ãyarin, sun tafi da shi, sun sayar da shi a kan kuɗi kaɗan, dõmin sun sani, shĩ bã bãwansu ba ne, tsintõ shi suka yi. Sabõda haka kõme suka sãmu game da shi, rĩba ce a gare su. Kuma gudun kada iyãyensa su gãne shi, su rasa kõme daga gare shi gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 237,
            "translated_text": "Kuma wanda ya saye shi daga Masar(5) ya ce wa mãtarsa, \"Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã.\"Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu, a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Yũsufu a gidan sarauta, kuma a cikin hãlin girma da ɗaukaka. Gidan Azĩzĩ Masar, watau firãyim Minista, babban wazĩrin Masar."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 237,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka bã shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 238,
            "translated_text": "Kuma wadda yake *a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, \"Yã rage a gare ka!\" ya ce: \"Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Yũsufu yã shiga cikin fitinar uwar ɗãkinsa, Zalĩha. Yã mai da al'amarinsa ga Ubangijinsa wanda ya fitar da shi daga rĩjiya zuwa gidan sarautar Masar kuma Ya bã shi hukunci, watau Annabci da ilmi da Ya saukar masa na ibãda da mu'amãla. Ya sanar da shi halal da haram kuma ya sanya masa tsaro daga zunubi."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 238,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 238,
            "translated_text": "Kuma suka yi tsẽre* zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: \"Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Idan namiji da mace sun haɗu, to, bã ya halatta ga namijin ya dõgara ga ilminsa na amanarsa, ya zauna tãre da fitinar Shaiɗan. Sabõda haka Yũsufu ya gudu, ta bĩ Shi da hãlin kãsãwar mutum ga hãlin so har bãkin kõfa. Suka haɗu da mijinta. Ta mayar da maganar rawãtsa (ƙarya) a kan Yũsufu. Shi kuma ya kãre kansa da maganar gaskiya. Sai shaida zã a nema.Tã himmantu da dũkarsa dõmin yã ƙi ya yi mata ɗã'a ga abin da take so daga gare shi alhãli yanã bãwanta, shĩ kuma yã himmantu da dũkarta dõmin ya tunkuɗe macũci. Alfãshar ita ce zina, cũtar kuwa ita ce dũka, dalĩlin Ubangijinsa shĩ ne bin sharĩ'ar Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 238,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ita ce ta nẽme ni a kaina.\"Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: *\"Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bãyar da shaida a kan al'ãda, mai bãyar da shaidar yanã gabãtar da ita da magana a kan Yusufu, dõmin a ganinsa tuhuma a kanta, tã fi karfi, kuma zumuntarsa da ita ba ta ɗauke shi ba ga karkatar da magana dõmin ya taimake ta."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 238,
            "translated_text": "\"Kuma idan rigarsa ta kasance an tsãge ta daga bãya, to, tã yi ƙarya, kuma shĩ ne daga mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 238,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da ya ga rĩgarsa an tsãge ta daga bãya, ya ce: \"Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne!\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 238,
            "translated_text": "\"Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi gãfara* dõmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga mãsu kuskure.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mai gida ya yi hukunci da yabon girman hãlin Yũsufu da kuma neman ya kashe maganar a nan."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 238,
            "translated_text": "Kuma waɗansu mãtã(5) a cikin Birnin suka ce: \"Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  (5) Tsegumin mãtã a cikin gari da yadda mãtar Azĩz ta yi maganin tsegumin, ta hanyar yiwa mãtan liyafa. Mace bã ta kunyar mãtã 'yan'uwanta ga irin wannan fitina idan ta sãme ta, ita kaɗai, balle mãtã ga sũ duka sun kãmu a cikin tarkon da ya kãma ta. Sai ta gaya musu gaskiyar abin da ya auku a tsakãninta da Yũsufu, a bãyan ta rãma zargin da suka yi mata."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 239,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: \"Ka fito a kansu.\" To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: \"Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja!\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 239,
            "translated_text": "Ta ce: \"To wannan ne fa wanda kuka, zarge* ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* A cikin maganar mãtar Azĩz a tsakãnin mãtã bãbu wata kunya, dõmin tã nũna kãsãwarsu. Kuma akwai tsõratarwa ga Yũsufu idan bai yi mata ɗã'a ba ga bukãtarta gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 239,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 239,
            "translated_text": "Sai Ubangijinsa Ya karɓa masa sabõda haka Ya karkatar da kaidinsu daga gare shi. Lalle Shĩ ne Mai jĩ, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 239,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma ya bayyana a gare su a bãyan sun ga alãmõmin, lalle ne dai su ɗaure shi har zuwa wani lõkaci."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 239,
            "translated_text": "Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi.* ¦ayansu ya ce: \"Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya.\" Kuma ɗayan ya ce: \"Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Yũsufu a cikin kurkuku tare da abõkan shigarsa kurkukun. Kuma yanã fassara mafarki a bãyan kiransa zuwa ga addini."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 239,
            "translated_text": "Ya ce: \"Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku lãbãrin fassararsa,* kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kõwane irin abin ne kãfin in gan shi da idõna, zan iya gaya muku nau'insa, kamar yadda Ĩsa ya ce: \" Inã bã ku lãbãrin abin da kuke ci a gidãjenku.\" A Sũrar Ãl Imrãna ãyã ta 49."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 240,
            "translated_text": "\"Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 240,
            "translated_text": "\"Yã abõkaina biyu na kurkuku! Shin iyãyen giji dabam-dabam ne mafiya alhẽri kõ kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 240,
            "translated_text": "\"Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku. Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 240,
            "translated_text": "\"Yã abõkaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shãyar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, zã a tsĩrẽ shi, sa'an nan tsuntsãye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 240,
            "translated_text": "Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kuɓuta ne daga gare su, \"Ka ambacẽ ni a wurin uban gidanka.\" Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunãwar Ubangijinsa, sabõda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 240,
            "translated_text": "Kuma sarki ya ce: \"Lalle ne, nã yi mafarki*; nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da waɗansu ƙeƙasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mafarkin sarki wanda zai zama sanadin fitar Yũsufu daga kurkuku. Wannan yanã nũna ba akeɓance yin mafarki ga Musulmi kawai, kãfiri ma yanã yin mafarki. Bã a iya fassara mafarki sai da ilmin Alƙur'ãni da Hadisi da kuma sanin al'ãdun mutãne. Mafarki bã ya zama hujja sai idan wani annabi yã fassara shi."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 241,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yãye-yãyen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yãye-yãyen mafarki ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 241,
            "translated_text": "Kuma wannan da ya kuɓuta daga cikinsu ya ce: a bãyan yã yi tunãni a lõkaci mai tsawo, \"Nĩ, inã bã ku lãbãri game da fassararsa. Sai ku aike ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 241,
            "translated_text": "\"Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 241,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa,* sai kaɗan daga abin da kuke ci.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Barin hatsi a cikin zangarniyarsa shĩ ne mãganin ruɓewarsa, kõ waɗansu tsũtsõtsi da suke cin sa."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 241,
            "translated_text": "\"Sa'an nan kuma waɗansu bakwai mãsu tsanani su zo daga hãyan wancan, su cinye abin da kuka gabãtar dõminsu, fãce kaɗan daga abin da kuke ãdanãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 241,
            "translated_text": "\"Sa'an nan kuma wata shẽkara ta zo daga bãyan wancan, a cikinta ake yi wa mutãne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mãtsar abin sha.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 241,
            "translated_text": "Kuma sarkin ya ce: \"Ku zo mini da shi.\" To, a lõkacin da manzo ya je masa (Yũsufu), ya ce: \"Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Mẽnene hãlin mãtãyen nan waɗanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidinsu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 241,
            "translated_text": "Ya ce: \"Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?\" Suka ce: \"Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba.\" Mãtar Azĩz ta ce: \"Yanzu fagaskiya* ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Da wannan magana ta mãtarAzĩz Zalĩha anã fahimtar ita tã musulunta ta hannun Yũsufu kãfin a ɗaure shi."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 241,
            "translated_text": "\"Wancan ne, dõmin ya san cẽwa lalle ne ni ban yaudareshi ba a ɓõye, kuma lalle Allah bã Ya shiryar da kaidin mayaudara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "\"Kuma bã ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙĩƙa, mai yawan umurni ne da mummũnan aiki, fãce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "Kuma sarkin ya ce: \"Ku zo mini da shi in kẽɓe shi ga kaina.\" To, a lõkacin da Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: \"Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Maganar da Yusuf ya gayã wa sarki lõkacin da ya je masa ba a faɗe ta ba, sai dai an nuna ta ƙãyatar da shi har ya yabe shi da cewa shi mai daraja ne amintacce."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ka sanya ni a kan taskõkin ƙasa. Lalle ne nĩ, mai tsarẽwa ne, kuma masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa* yanã sauka a inda duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Lõkacin da Yũsufu yanã aikin tattalin arzikin ƙasa a cikin shekarar wadãta, ya Mallakeƙasar Masar duka a lõkacin da wahala da yunwa suka auku."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "Kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗandasuka yi ĩmãni, kuma suka kasance mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "Kuma 'yan'uwan* Yũsufu suka jẽ, sa'an nan suka shiga a gare shi, sai ya gãne su, alhãli kuwa su, sunã mãsu musunsa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * 'Yan'uwan Yũsufu sun zo sunã neman awo a gunsa, ya gãne su dõmin baƙauye kõ matalauci bai faye canja kamanninsa ba, amma sũ, ba su gane shi ba, sabõda haibar mulki da kwarjinin halittarsa a bayan ya zama babban mutum ga idonsu a inda bã su zaton sa."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: \"Ku zo mini da wani ɗan'uwa nãku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, inã cika ma'auni, kuma nĩ ne mafi alhẽrin mãsu saukarwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "\"Sa'an nan idan ba ku zo mini da shĩ ba, to, bãbu awoa gare ku a wurĩna, kuma kada ku, kasance ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "Suka ce: \"Zã mu nẽme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu aikatãwa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "Kuma ya ce wa yaransa, \"Ku sanya hajjarsu a cikin kãyansu, tsammãninsu sunã gãne ta idan sun jũya zuwa ga mutãnensu, tsammã ninsu, zã su kõmo.\""
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 242,
            "translated_text": "To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce: \"Yã bãbanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan'uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, mãsu lũra da Shi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 243,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan'uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 243,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da suka bũɗe kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: \"Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye ɗan'uwanmu, kuma mu ƙãra awon kãyan rãƙumi guda, wancan awo ne mai sauki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 243,
            "translated_text": "Ya ce: \"Bã zan sake shi tãre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙĩƙa, kunã dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku.\" To, a, lõkacinda suka yi mãsa alkawari, ya ce: \"Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 243,
            "translated_text": "Kuma ya ce: \"Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam,* kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yãƙũbu ya umurci ɗiyansa su shiga garin, ta ƙõfõfi dabam- dabam, yanã nũna cewa yanã gudun kyawunsu da yawansu zai ja hankalin mutãne zuwa gare su. A cikin mutãne akwai mãsu kambun baka da mugun nufi kõ da yake Yãƙũba a cikin hãlin haka ya aza tawakkalinsa ga Allah. Ya yi abin da yake zaton alhħri ne, wanda bai saɓa wa sharĩ'a ba. Amma kuma yã yi haka ne a kan wani ilmi da Allah Ya sanar da shi cewa a wannan fitar tãsu ce Allah zai yi sanadin sãke sãduwarsu da Yũsufu, sabõda haka ya umurce su da su shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam, dõmin mutum shi kaɗai yã fi sãmun dãmar ta'ammalin ganin mutãne da abũbuwa. Kuma ta yin haka, yanã tsammãnin waninsu zai ga Yũsufu."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 243,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu, ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma'abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 243,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: \"Lalle nĩ ne ɗan'uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 244,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kãyan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa,\" Yã kũ ãyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 244,
            "translated_text": "Suka ce: kuma suka fuskanta zuwa gare su: \"Mẽne ne kuke nẽma?\""
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 244,
            "translated_text": "Suka ce: \"Munã nẽman ma'aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yanã da kãyan rãkumi ɗaya, kuma ni ne lãmuni game da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 244,
            "translated_text": "Suka ce: \"Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarãyi ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 244,
            "translated_text": "Suka ce: \"To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata?\""
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 244,
            "translated_text": "Suka ce: \"Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa,* kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Shari'ar Banĩ yã'aƙũbu ita ce anã bautar da ɓarãwõ shekara guda. Wannan shĩ ne shari'ar da Tũrãwa suka ɗauka suka mayar da ita ɗaurin kurkuku da bautar da ɓarãwo a cikin mudda ayyananna."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 244,
            "translated_text": "To, sai ya fãra (bincike) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kãma ɗan'uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba, fãce idan Allah Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma'abũcin ilmi akwai wani masani."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 244,
            "translated_text": "Suka ce: \"Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa.\" Sai Yũsufu ya bõye* ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: \"Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * 'Yan'uwan Yũsfu sun faɗi cewa ɗan'uwan Binyaminu ya taɓa yin sãta, dõminsu nũna cewa a wajen ubansu tsarkakakku ne daga yin sãta. Shi kuma wanda ya yi sãtan ya gade ta ne daga wajen uwarsa, dõmin wani shaƙĩƙinsa(Yũsufu) ya taɓa yin sãta. To, sai Yũsufu ya ce a ransa: \"Kũ ne dai mafi sharrin mutãne, Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffintãwa.\" Asalin wannan magana wata goggonsa ce (Shi Yũsufu) ɗiyar Is'hãƙa, ta riƙe shi, yanã yaro, har a lõkacin da ubansa (Yãƙũbu) ya so ya karɓe shi daga gare ta, sai ta yi kaidin sanya kãyan sãta a cikin rigarsa (Yũsufu) dõmin ta hana uban ɗaukarsa. A wata ruwaya kuma an ce shi (Yũsufu) ya ɗauke wani mutum mutumi ne na zĩnãri (gunki) ya karairaya shi. Don haka 'yan'uwansa suke jingina sãta a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 244,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka ka kãma ɗayanmu amatsayinsa. Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 245,
            "translated_text": "Ya ce: \"Allah Ya tsare mu daga mu kãma wani fãce wanda muka sãmi kãyanmu a wurinsa. Lalle ne mũ, a lõkacin nan, haƙĩƙa, azzãlumai ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 245,
            "translated_text": "Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa.* Babbansu ya ce: \"Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * 'Yan'uwan Yũsufu sun yanke tsammãnin sãmun Binyãminu daga sharĩ'a, sun kõma sunã gãnãwa a tsakãninsu. Sai dai waɗannan ɗiyansu ne domin su, suna Masar."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 245,
            "translated_text": "\"Ku kõma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yã bãbanmu, lalle ne ɗanka yã yi sãta, kuma ba mu yi shaida ba fãce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 245,
            "translated_text": "\"Kuma ka tambayi alƙarya wadda muka kasance a cikinta da ãyari wanda muka gabãto acikinsa, kuma lalle ne haƙĩƙa, mũ mãsu gaskiya ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 245,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ã'a, zukatanku sun ƙawãta wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyãwo, akwai tsammãnin Allah Ya zo mini da su gabã ɗaya (Yũsufu da 'yan'uwansa). Lalle ne Shĩ ne Masani, Mai hikima.\""
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 245,
            "translated_text": "Kuma ya jũya daga gare su, kuma ya ce: \"Yã baƙin cikina a kan Yũsufu!\" Kuma idãnunsa suka yi fari sabõda huznu sa'an nan yanã ta haɗẽwar haushi."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 245,
            "translated_text": "Suka ce: \"Tallahi! Bã zã ka gushe ba, kanã ambaton Yũsufu,* har ka kasance Mai rauni ƙwarai, kõ kuwa ka kasance daga mãsu halaka.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mai tsõhon laifi bã ya son ya ji anã ambatonsa, sabõda haka ('yan'uwan Yũsufu) suke zargin bãbansu da ambaton (tuna) Yũsufu."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 245,
            "translated_text": "Ya ce: \"Abin sani kawai, inã kai ƙarar baƙin cikĩna da sunõna zuwa ga Allah, kuma na san abin da ba ku sani ba daga Allah.\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 246,
            "translated_text": "\"Yã ɗiyãna! Sai ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu* da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammãni daga rahamar Allah. Lalle ne, bãbu Mai yanke tsammãni daga rahamar Allah fãce mutãne kãfirai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Anan Yãƙũbu yã bayyana irin ilmin da Allah Ya sanar da shi, cewa Yũsufu yanã nan da ransa, kuma sun yi kusa su sãdu da jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 246,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: \"Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin sadaka. \"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ya nũna ba a haramta sadaka ba ga Annabãwan da suka gabãta, sai ga Annabinmu Mahammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, shĩ da danginsa na kusa aka hana wa cin sadaka."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 246,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin, kan* san abin da kuka aikata ga Yũsufu da ɗan'uwansa a lõkacin da kuke jãhilai?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Yũsufu ya bayyana ga 'yan'uwansa, kuma sun yãfe wa jũna laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 246,
            "translated_text": "Saka ce: \"Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?\" Ya ce: \"Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 246,
            "translated_text": "Suka ce: \"Tallahi! Lalle ne haƙĩƙa, Allah Yã zãɓe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, mãsu kuskure.\""
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 246,
            "translated_text": "Ya ce: \"Bãbu zargi akanku a yau, Allah Yanã gãfartã muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 246,
            "translated_text": "\"Ku tafi da rĩgãta wannan, sa'an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kõma mai gani. Kuma ku zo mini da iyãlinku bãki ɗaya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 246,
            "translated_text": "Kuma, a lõkacin da ãyari* ya bar (Masar) ubansa ya ce: \"Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yãƙũba da jĩkõkinsa. Yanã gaya musu, cewa yanã shãƙar ƙanshin Yũsufu, su kuma suna jingina shi ga ruɗewar tsũfa dõmin rabonsa da Yũsufu shħkara talãtin da biyar zuwa arba'in."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 246,
            "translated_text": "Suka ce: \"Tallahi lalle ne, kai, haƙĩƙa, kanã a cikin ɓatarka daɗaɗɗa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 247,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: \"Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?\""
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 247,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã ubanmu!* ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ɗiyan Yãƙũbu sunã iƙrãri da laifinsu, sunã neman Allah Ya gãfarta musu gaba ɗaya. Ubansu yanã jinkirta nema musu gãfara gun Allah har a lõkacin asuba kõ kuwa daren Jumma'a dõmin ya yi rõƙo a lõkacin karɓar addu'a. Wannan yã nũna anã iya neman mai albarka kõ wani mutum yayi wa wani mutum addu'a."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 247,
            "translated_text": "Ya ce: \"Da sannu zã ni nẽma muku gãfara daga Ubangijina. Shi ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 247,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin* da suka shiga gun Yũsufu, yã tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: \"Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Yũsufu ya sãdu da ubansa da uwarsa. A Larabci anã rinjãyar da uba a kan uwa, a ce ubanni biyu, kuma ga Hausa anã rinjayar da wa a kan uba, a ce uwãye biyu."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 247,
            "translated_text": "Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãɗi a gare shi, suna mãsu sujada.* Kuma ya ce: \"Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, Shĩ ne Masani, Mai hikima.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sujada idan ta zama da umurnin Allah ne ga kõwa, to, ba ta da laifi duk yadda take, amma idan an yi ta bã inda Allah Ya ajiye ta ba, to, tã zama kãfirci. A Musulunci gaisuwa da dũƙãwar kai haram ce, waɗansu Malamai sun ce idan ba ta kai ga rukũ'i ba, makarũhi ce, amma idan ta kai ga rukũ'i tã zama harãmun ga duka mãlamai, wãtau ijmã'in Malamai sun haramta dũƙãwar da ta kai ga rukũ'i."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 247,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijina* lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Yũsufu yanã addu'a a ƙarshen rãyuwarsa, yanã neman Allah Ya cika masa da imãni."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 247,
            "translated_text": "Wannan daga(5) lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci.<br \/>\n____________________<br \/>\n   (5) Ƙarfafãwa da ƙãrin tambĩhi daga abin da sũrar ta ƙunsa, daga nan har zuwa karshenta."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 247,
            "translated_text": "Kuma mafi yawan mutãne ba su zama mãsu ĩmãni ba, kõ da kã yi kwaɗayin haka."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 248,
            "translated_text": "Kuma bã ka tambayar su wata lãdã a kansa. Shĩ bai zama ba fãce ambato dõmin halittu."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 248,
            "translated_text": "Kuma da yawa, wata ãyã a cikin sammai da ƙasa sunã shũɗẽwa a kanta kuma sũ, sunã bijirẽwa daga gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 248,
            "translated_text": "Kuma mafi yawansu ba su yin ĩmãni da Allah fãce kuma sunã mãsu shirki."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 248,
            "translated_text": "Shin fa, sun amince cẽwa wata masĩfa daga azãbar Allah ta zo musu ko kuwa Tãshin ¡iyãma ta zo musu kwatsam, alhãli sũ ba su sani ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 248,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wannan ce hanyãta;* inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bin hukuncin Allah kamar yadda ƙissar Yũsufu ta nũna cewa, a ƙõwane hãli mutum ya kasance akwai yadda Allah Ya yi umurni a wannan hãlin da a bĩ Shi, wanda ya bi umurnin Allah, to, zai ɗaukaka a dũniya kuma Allah bã zai tõzartar da lãdarsa a Lãhira ba."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 248,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su, daga mutãnen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dõmin su dũbayadda ãƙibar waɗanda suka kasance daga gabãninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lãhira shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bã ku hankalta?"
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 248,
            "translated_text": "Har a lõkacin da Manzanni suka yanke tsammãni, kuma suka yi zaton cẽwa an jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tsẽrar da wanda Muke so, kuma bã a mayar da azãbarMu daga mutãne mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 12,
            "page_number": 248,
            "translated_text": "Lalle ne haƙĩƙa abin kula yã kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 249,
            "translated_text": "A. L̃. M̃.R. Waɗancan ayõyin littãfi ne kuma abin da aka saukar gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 249,
            "translated_text": "Allah Shi ne wanda Ya ɗaukaka sammai, bã da ginshiƙai ba waɗanda kuke ganin su. Sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, kuma Ya hõre rãnã da watã, kõwane yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. Yanã shirya al'amari, Yanã rarrabe ãyõyi daki-daki, mai yiwuwa ne ku yi yaƙĩni da haɗuwa da Ubangijinku."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 249,
            "translated_text": "Kuma shĩ, ne wanda Ya shimfiɗa kasa, kuma Ya sanya duwãtsu da kõguna a cikinta, kuma daga dukan 'ya'yan itãce Ya sanya ma'aura biyu cikinsu. Yanã sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 249,
            "translated_text": "Kuma a cikin ƙasa akwai yankuna mãsu maƙwabtaka, da gõnaki na inabõbi da shũka da dabĩnai iri guda, da waɗanda bã iri guda ba, anã shayar da su da ruwa guda. Kuma Munã fĩfĩta sãshensa a kan sãshe a wajen ci. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga muiãne waɗanda suke hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 249,
            "translated_text": "Kuma idan ka yi mãmãki, to, mãmãkin kam shi ne maganarsu, \"Shin, idan muka kasance turɓãya, zã mu zama a cikin wata halitta sãbuwa?\" Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, kuma waɗanda akwai ƙuƙumai a cikin wuyõyinsu, kuma waɗancan ne abõkan wuta. Sũ, a cikinta, mãsu dawwama ne."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 250,
            "translated_text": "Kuma sunã nẽman ka da gaggãwa da azãba a gabãnin rahama, alhãli kuwa abũbuwan misãli sun gabãta a gabãninsu. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne ga mutãne a kan zãluncinsu, kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai tsananin uƙũba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 250,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa don me ba a saukar da wata ãyã a gare shi ba daga Ubangijinsa? Abin sani kawai, kai dai mai gargaɗi ne kuma a cikin kõwaɗanne mutãne akwai mai shiryarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 250,
            "translated_text": "Allah Yanã sanin abin da kõwace mace take ɗauke da shi a cikinta da abin da mahaifu suke ragẽwa* da abin da suke ƙãrãwa. Kuma dukkan kõme, a wurinSa, da gwargwado yake.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ragõwar lõkacin cikin ko ƙãruwarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 250,
            "translated_text": "Shi ne Masanin fake da bayyane, Mai girma, Maɗaukaki."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 250,
            "translated_text": "Daidai ne daga gare ku, wanda ya asirta magana da wanda ya bayyana game da ita, da wanda yake shi mai nẽman ɓõyewa ne da dare, da mai bayyana a cikin tafiyarsa a hanya da rãna*.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hasken rãnã mai kama da ruwa ga idon mai dũbi daga nesa."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 250,
            "translated_text": "(Kowannenku) Yanã da waɗansu malã'iku mãsu maye wa jũna a gaba gare shi da bãya gare shi, sunã tsare shi daga umurnin Allah. Lalle ne Allah bã Ya canja abin da yake ga, mutãne sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azãba game da mutãne, to, bãbu mai mayar da ita, kuma bã su da wani majiɓinci* baicin Shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãbu wani majiɓinci baicin Allah, wanda zai iya tsĩrar da su daga azãbarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 250,
            "translated_text": "Shĩ ne Wanda Yake nũna muku walƙiya dõmin tsõro da tsammãni, kuma Ya ƙãga halittar girãgizai mãsu nauyi."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 250,
            "translated_text": "Kuma arãdu tanã tasbĩhi game da gõde Masa, da malã'iku dõmin tsoronsa. Kuma Yanã aiko tsãwawwaki, sa'an nan Ya sãmi wanda Yake so da su alhãli kuwa sũ, sunã jãyayya a cikin (al'amarin) Allah kuma shĩ ne mai tsananin hĩla.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Hĩla, ita ce mãkirci, Allah Yanã azabta mãsu yin hĩla ga addininsa, da azãba mai tsanani, kuma Ya kãmã su da hĩlarsu ta hanyar da ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 251,
            "translated_text": "Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kãfirai) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) dõmin (ruwan) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai (ga wanin Allah) bai zama* ba fãce yanã a cikin ɓata.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Allah Mamallakin ruwa, Yanã kiran mutãne dõmin Ya bã su ruwan su shã. Su kuma kãfirai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam waɗanda kõ karɓa musu kiran bã zã su iya yi ba, kuma sunã neman ruwa daga gare su, alhãli kuma ba su mallaki kõme ba. Watau Mai abu Yanã kiran su dõmin Ya bã su, sun ƙi karɓa Masa sai sunã kiran wani wanda bai mallaki kõme ba, sunã rõƙon Sa ruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 251,
            "translated_text": "Kuma sabõda Allah wanda yake a cikin sammai da ƙasa suke yin sujada, so da ƙi, kuma da inuwõyinsu, a sãfe da maraice."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 251,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wãne ne Ubangijin sammai da ƙasa?\" Ka ce: \"Allah\". Ka ce: \"Ashe fa, kun riƙi waɗansu masõya baicin Shi, waɗanda ba su mallaka wa kansu wani amfãni ba kuma haka bã su tũre wata cũta?\" Ka ce: \"Shin makãho da mai gani sunã daidaita? Kõ shin duhu da haske sunã daidaita? ko sun sanya ga Allah waɗansu abõkan tãrayya waɗanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da jũna a gare su?\" Ka ce: \"Allah ne Mai halitta kõme kuma Shĩ ne Maɗaukaki, Marinjãyi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 251,
            "translated_text": "Ya saukar da ruwa daga sama*, sai magudanai suka gudãna da gwargwadonsu, Sa'an nan kõgi ya ɗauki kumfa mai ƙãruwa, kuma daga abin da suke zuga a kansa (azurfa ko zinari kõ ƙarfe) a cikin wuta dõmin nẽman ado kõ kuwa kãyan ɗãki akwai kumfa misãlinsa (kumfar ruwa). Kamar wancan ne Allah Yake bayyana gaskiya da ƙarya. To, amma kumfa, sai ya tafi ƙẽƙasasshe, kumaamma abin da yake amfãnin mutãne sai ya zauna a cikin ƙasa. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana misãlai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Idan ruwa ya sauka daga sama sa'an nan ya gudãna a cikin rãfuna zai yi kumfa. Sai ruwa mai amfãnin mutãne ya nutse a ƙasa ya zauna, sa'an nan kumfan kuma ya ƙeƙashe ya lãlãce. Haka kuma idan an sanya ƙarfe na zinãri kõ na azurfa kõ baƙin ƙarfe a cikin wuta, aka zuga ta a kansa, zai fitar da kumfa, wãtau tsakin tama wanda zã a fitar dõmin rashin amfãninsa, dõmin zĩnariyar ƙwarai mai amfãni ta wanzu. To haka ga kõme akwai kumfa marashin amfãni da mai kyãwo mai amfani."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 251,
            "translated_text": "Ga waɗanda* suka karɓa wa Ubangijinsu akwai abu mafi kyau a gare su, kuma waɗanda suke ba su karɓa Masa ba, to, lalle dã sunã da abin da yake a cikin ƙasa gaba ɗaya da misãlinsa tãre da shi, haƙĩƙa, dã sun yi fansa da shi. Waɗancan sunã da mummunan bincike kuma matabbatarsu Jahannama ce, kuma tir da ita ta zama shimfida.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bãyan da ya faɗi cewa Allah Yanã kira, kiran gaskiya a cikin ãyã ta l4, kuma waɗansu mutãne sun ƙi karɓar kiran Allah, sai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam, sai ya bayyana, a nan, sakamakon wanda ya karɓi kiran Allah sãmun ruwan sha, sabõda Mai abu ne Ya kirãwo shi, Ya kuma bã shi, ya sha a hankali kwance, sa'an nan kuma Allah zai bã shi abin da ya fi ruwan kyau, watau Aljanna. Amma wanda ya ƙi karɓãwa, to, yã yi hasãra biyu, bai sãmi ruwan da ya yi kiran wani ya bã shi ba, sa'an nan kuma ya haɗu da azãbar da take zai iya bãyar da dukan abin da ya mallaka dõmin ya yi fansar kansa da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "Shin, fa, wanda yake sanin cẽwa lalle abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya yanã zama kamar wanda yake makãho? Abin sani kawai masu hankali sũ ke yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "Sũ ne waɗanda suke cikãwa da alkawarin Allah, kuma bã su warware alkawari."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "Kuma sũ ne waɗanda suke sãdar da abin da Allah Ya yi umurni da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã tsõron Ubangijinsu, kuma sunã tsõron mummũnan bincike."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi haƙuri dõmin nẽman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, kuma sunã tunkuɗe mummunan aiki da mai kyau. Waɗancan sunã da ãƙibar gida mai kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, sũ da waɗandasuka kyautatu daga iyãyensu, da mãtansu da zũriyarsu. Kuma malã'iku sunã shiga zuwa gunsu ta kõwace kõfa."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "\"Aminci* ya tabbata a kanku sabõda abin da kuka yi wa haƙuri. Sãbõda haka madalla da ni'imar ãƙibar gida.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sallamar malã'iku a kansu idan sun shiga a gare su, ita ce su ce musu: \"Aminci ya tabbata a gare ku.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "Kuma waɗanda* suka warware alkawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma sunã yanke abin da Allah Ya yi umurui da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã ɓarna a cikin ƙasar. Waɗancan sunã da wata la'ana, kuma sunã da mũnin gida.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bayãnin siffõfin waɗanda suka ƙi karɓar kiran Allah. Watau akasin waɗanda aka yi bayaninsu a bãyã."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "Allah ne Yake* shimfiɗa arziki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuntatãwa. Kuma sun yi farin ciki da rãyuwar dũniya, alhalikuwa rãyuwar dũniya ba ta zama ba dangane ga ta Lãhira fãce jin dãɗi kaɗan.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ta'aƙĩbi da tambĩhi ne da ƙãrin bayãni ga mai hankali dõmin ya zãbura ga karɓar kiran Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "Kuma wanɗanda suka kãfirta, sunã cẽwa, \"Don me ba a saukar da wata ãyã ba a kansa daga Ubangijinsa?\" Ka ce: \"Lalle ne Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so kuma Yanã shiryar da wanda ya tũba zuwa gare shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 252,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah* zukãta suke natsuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ambaton Allah, shĩ ne bin hukunce-hukuncensa ga kõme. Umar ɗan Khattãb ya ce: \"Mafificin ambaton Allah, shi ne wanda aka yi a wurin umurninsa ko haninsa. Wanda yake yin zikirin bãki ba da yanã aiki da hukunce-hukuncen Allah ba a cikin ibãdarsa da mu'amalarsa, to, shi mai izgili kawai ne da sũnan Ubangijinsa, ba mai yin zikiri ba ne.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 253,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata aiki nagari, farin ciki yã tabbata a gare su, da kyakkyawar makõma."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 253,
            "translated_text": "Kamar wancan ne Muka aika ka a cikin al'umma wanda take waɗansu al'ummai sun shũɗe daga gabaninta, dõmin ka karanta musu abin da Muka yi wahayi zuwa a gare ka, alhãli kuwa sũ, sunãkãfirta da Rahaman.* Ka ce: \"Shi ne Ubangijĩna, bãbu abin, bautãwa fãce Shi, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi tũbãta take.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Sũnan Allah Rahmãn, daga rahama, watau Mai Rahama wadda yake dukan alheri yanã shiga a cikin ma'anarta a wajen halitta da rãyuwa da bãyar da lãfiya da shiryarwa. Mafi girman nĩ'imarsa shĩ ne aikõwar Manzon Allah daga gare mu zuwa gare mu. Kãfirai ba su yi tunãni ba a kan waɗannan rahamõmi, balle su yi gõdiya, sabõda haka sai kãfirci suke yi."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 253,
            "translated_text": "Kuma dã lalle an saukar da wani littafi abin karatu wanda ake tafiyar da duwãtsu game da shi, kõ kuma aka yanyanke ƙasa da shi, ko kuwa aka yi magana da matattu da shi (dã ba su yi ĩmãni ba). Ã'a ga Allah al'amari yake gabã ɗaya! Shin fa, waɗanda suka yi ĩmãni ba su yanke tsammãni ba da cẽwa da Allah Yã so, dã Yã shiryar da mutãne gabã ɗaya? Kuma waɗanda suka yi kãfirci ba zã su gushe ba wata masĩfa tanã samun su sabõda abin da suka aikata, kõ kuwa ka saukã* kusa da gidãjẽnsu, har wa'adin Allah ya zo. Kuma lalle ne Allah bã ya sãɓã wa lõkacin alkawari.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Annabi ya sauka kusa da gidãjen Ƙuraishãwa a rãnar bũɗe Makka. Kuma wannan hukunci yanã nan yanã aiki ga mãsu ƙiyayya da addini, kullum masĩfu sunã aukuwa a kansu har rãnar da Musulunci ya rinjãye su."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 253,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da Manzanni kãfinka, sai Na yi jinkiri ga waɗanda suka kãfirta, sa'an nan Na kãma su. To, yãya uƙũbãta take?"
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 253,
            "translated_text": "Shin fa, wanda shĩ Yake tsaye a kan kõwane rai game da abin da ya tanada (zai zama kamar wanda ba haka ba)? Kuma suka sanya abõkan tãrayya ga Allah! Ka ce: \"Ku ambaci sũnãyensu.\"Ko kunã bai wa Allah lãbãri ne game da abin da bai sani ba a cikin ƙasa? Kõ da bayyananniyar magana kuke yin shirka, (banda a cikin zũciya)? Ã'a, an dai ƙawãta wa waɗanda suka kafirta mãkircinsu kuma an kange su daga hanya. Kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bãbu wani mai shiryarwa a gare shi!\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 253,
            "translated_text": "Sunã da wata azãba a cikin rãyuwar dũniya, kuma haƙĩƙa azãbar Lãhira ce mafi tsanani kuma bãbu wani mai tsare su daga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 254,
            "translated_text": "Misãlin Aljanna wadda aka yi alkawarinta ga mãsu taƙawa, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinta. Abincinta yana madawwami da inuwarta. Waccan ce ãƙibar waɗanda suka yi taƙawa, kuma ãƙibar kãfirai, ita ce wuta,"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 254,
            "translated_text": "Kuma waɗanda Muka bã su Littãfi sunã farin ciki da abin da aka saukar zuwa gare ka, kuma daga ƙungiyõyi akwai mai musun sãshensa. Ka ce: \"Abin sani kawai, an umurce ni da in bauta wa Allah kuma kada in yi shirka da Shi, zuwa gare Shi nake kira, kuma zuwa gare Shi makõmata take.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 254,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan ne Muka saukar da shi*, Hukunci a cikin Lãrabci. Kuma lalle ne idan kã bi son zuciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bãbu wani masõyi a gare ka mai kãre ka daga Allah, kuma bãbu matsari.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kamar yadda littattafan farko suke, haka Alƙur'ãni yake daga Allah, sai dai shi Alƙur'ãni an saukar da shi a cikin Lãrabci."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 254,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabãninka, kuma Muka sanya mãtan aure a gare su da zũriyya, kuma ba ya kasancẽwa ga wani Manzo ya zo da wata ãyã, sai da iznin Allah. Ga kõwane ajali* akwai littãfi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Aikõwar Manzanni da littattafai ba ya hana Allah Ya aiko wani Manzo daga bãya da wani littãfi wanda ya shãfe abin da yake cikin littattafan farko. Allah Yã tabbatar da abin da yake so na hukunce-hukuncen da suka gabãta dõmin dõgewar aikinsu ga mutãne har yanzu, kuma Ya shãfe abin da yake so sabõda amfãninsu da hukuncinsu yã shige, sabõda wata hikima da Allah Ya sani amma asalin littattãfan duka wanda bã zai canja ba a cikin sanin Allah, yanã wurinsa.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 254,
            "translated_text": "Allah Yanã shafe abin da Yake so, kuma Yanã tabbatarwa kuma a wurinsa asalin Littãfin yake."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 254,
            "translated_text": "Kuma imma lalle Mu nũna* maka sãshen abin da Muke yi musu wa'adi, kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka to abin sani kawai iyarwa ce a kanka, kuma hisãbi yana gare Mu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Idan Mun so Mu yi musu azãba a gaban idonka zã Mu yi musu, kuma idan Mun so Mu jinkirta musu har a bãyan ka mutu, wannan bã aikinka ba ne, Nãmu ne. Abin da yake aikinka shĩ ne iyar da manzanci kawai. Yin hisãbi a kansu alhakin Allah ɗai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 254,
            "translated_text": "Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne, Muna jẽ wa ƙasar (su), Munã rage ta daga gẽfunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shĩ ne Mai gaggãwar sakamako.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Gaggãwar sakamako ga wanda ya ƙi bin umurnin Allah wanda Annabinsa ya iyar zuwa gare shi. Asalin hisãbi, shine bincike dõmin a sãmi abin da aka yi na alhħri kõ na sharri amma abin da ake nufi a nan maƙasũdin bincike shĩ ne sakamako da alhħri kõ da azãba, gwargwadon nufinSa."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 254,
            "translated_text": "Kuma lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci. To, ga Allah mãkircin yake gabã ɗaya. Ya san abin da kõwane rai yake tãnada. Kuma kãfirai zã su sani, ga wane ãƙibar gida take."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 13,
            "page_number": 255,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: \"Ba a aiko ka ba.\" Ka ce, \"Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da tsakãninku da wanda yake a wurinsa akwai ilmin* Littãfi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Allah Yã isa zama shaida, haka wanda yake a kan wani ilmi daga Allah kamar Yahudu da Nasãra sunã isa zama shaida a tsakãnĩna da ku a kan gaskiyar da'awã ta cewa nĩ abin aikõwa ne daga Allah zuwa gare ku dõmin akwai wannan magana a cikin littattafanku."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 255,
            "translated_text": "A. L̃.R. Littãfi ne mun saukar da shi zuwa gare ka dõmin ka fitar da mutãne daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin Mabuwãyi, Abin gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 255,
            "translated_text": "Allah wanda Yake Yanã da abin da ke cikin sammai da cikin ƙasa. Kuma bone yã tabbata ga kãfirai daga azãba mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 255,
            "translated_text": "Waɗanda suka fi son rãyuwar dũniya fiye da ta Lãhira, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta karkace. Waɗancan na a cikin ɓata mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 255,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aika wani Manzo ba fãce da harshen mutãnensa dõmin ya bayyanã musu. Sa'an nan Allah Ya ɓatar da wanda Yake so kuma Ya shiryar da wanda Yake so, Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 255,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Mũsã game, da ãyõin Mu cẽwa, \"Ka fitar da mutãnenkadaga duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunar musu da kwãnukan (masĩfun) Allah.\" Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi dõmin dukan mai yawan haƙuri, mai gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 256,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Mũsã yace wa mutãnensa, \"Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da Ya tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã yi muku mummunar azãba, kuma sunã yanyanka ɗiyanku, kuma sunã rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa mai girmã daga Ubangijinku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 256,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, \"Lalle ne idan kun gõde, haƙĩƙa, Inã ƙãramuku, kuma lalle ne idan kun kãfirta haƙĩƙa azãbãta, tabbas, mai tsanani ce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 256,
            "translated_text": "Kuma Mũsã ya ce: \"Idan kun kãfirta kũ da waɗanda suke a cikin ƙasa, gabã ɗaya, to, lalle ne Allah haƙĩƙa Mawadãci ne, Mai yawan gõdiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 256,
            "translated_text": "Shin lãbãrin waɗanda suke a gabãninku, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa bai zomuku ba? Kuma da waɗanda suke daga bãyansu bãbu wanda yake sanin su fãce Allah? Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji mabayyana, sai suka mayar da hannayensu a cikin bãkunansu, kuma suka ce: \"Lalle ne mũ, mun kãfirta da abinda aka aiko ku da shi. Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa munã a cikin shakkada abin do kuke kiran mu zuwa gare shi, mai sanya kõkanto.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 256,
            "translated_text": "Manzanninsu suka ce \"Ashe, akwai shakka a cikin (sha'anin) Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa Yanã kiran ku dõmin Ya gãfarta muku zunubanku, kuma Ya jinkirtã muku zuwa ga ajali ambatacce?\" Suka ce: \"Ba ku zama ba fãce mutãne misãlinmu kuma nufinku ku kange mu daga abin da iyãyenmu suka kasance sunã bautãwa sai ku zo mana da dalĩli mabayyani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 257,
            "translated_text": "Manzanninsu suka ce musu, \"Bã mu zama ba fãce mutãne misã, linku, kuma amma Allah Yanã yin falala a kan wanda Yake so daga bãyinsa, kuma bã ya kasancẽwa a gare mu, mu zo muku da wani dalĩli fãce da iznin Allah. Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 257,
            "translated_text": "\"Kuma mẽne ne a gare mu, bã zã mu dõgara ga Allah ba, alhãli kuwa haƙĩƙa Yã shiryar da mu ga hanyõyinmu? Kuma lalle ne munã yin haƙuri a kan abin da kuka cũtar da mu, kuma ga Allah sai mãsu dõgaro su dõgara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 257,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa Manzanninsu, \"Lalle ne munã fitar da ku daga ƙasarmu, kõ kuwa haƙĩƙa, kunã kõmowã acikin addininmu.\" Sai Ubangijinsu Ya yi wahayi zuwa gare su, \"Lalle ne, Munã halakar da azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 257,
            "translated_text": "Kuma haƙĩƙa, Munã zaunar da ku ga ƙasa a bãyansu. Wancan ne abin gargaɗi ga wanda ya ji tsõron matsayiNa, kuma ya ji tsõron ƙyacẽwãTa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 257,
            "translated_text": "Kuma suka yi addu'ar alfãnu*. Kuma kõwane kangararre mai tsaurin kai ya tãɓe.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kõwane ɓangare ya yi addu'ar alfãnu ga abin da yake ganin gaskiyarsa. Annabãwa suka yi alfãnu da Allah, kuma mutãnensu suka yi da abin da suke zato alheri a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 257,
            "translated_text": "Daga bãyansa akwai Jahannama, kuma anã shãyar da shi daga wani ruwa, surkin jini."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 257,
            "translated_text": "Yanã kwankwaɗarsa, kuma bã ya jin sauƙin haɗiyarsa, kuma mutuwa ta jẽ masa daga kõwane wuri kuma bai zama mai mutuwa ba, kuma daga bãyansa akwai azãba mai kauri."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 257,
            "translated_text": "Misãlin waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, ayyukansu sun yi kama da tõka wadda iska ta yi tsananin bugãwa da ita a cikin yini mai gũguwa. Ba su iya amfãni daga abin da suka yi tsirfa a kan kõme. Wancan ita ce ɓata mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 258,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle ne Allah Yã halicci sammai bakwai da ƙasa da mallakarSa.* Idan Yã so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Dalĩli ne a kan kãfircin kãfirai ba ya rage mulkin Allah da kõme, domin bã su iya fita daga halittar sammai da ƙasa, waɗanda Allah Ya halitta da abin da yake mallakarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 258,
            "translated_text": "Kuma wancan bai zama mabuwãyi ba ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 258,
            "translated_text": "Kuma suka bayyana ga Allah gabã daya, sai mãsu rauni suka ce wa waɗanda suka kangara, \"Lalle ne mũ, mun kasance mãsu bi a gare ku, to, shin, kũ mãsu kãrewa ga barinmu ne daga azãbar Allah daga wani abu?*\" Suka ce: \"Dã Allah Ya shiryar da mu, dã mun shiryar da ku, daidai ne a kanmu, mun yi rãki ko mun yi haƙuri ba mu da wata mafaka.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muhãwarar 'yan wuta a tsakãnin mabiya da shũgabannin kafirci."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 258,
            "translated_text": "Kuma Shaiɗan ya ce a lõkacin da aka ƙãre al'amarin, \"Lalle ne Allah Ya yi muku wa'adi, wa'adin gaskiyã, kuma na yi muku wa'adi, sa'an nan na sãɓã muku. Kuma bãbu wani dalĩli a gare ni a kanku fãce na kirã ku, sa'an nan kun karɓã mini. Sabõda haka kada ku zarge ni, kuma ku zargi kanku. Ban zama mai amfaninku ba, kuma ba ku zama mãsu amfãnĩna ba. Lalle na barranta da abin da kuka haɗã ni da shi gabanin wannan (matsayi). Lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Huɗubar Shaiɗan ga mabiyansa, a cikin wuta, a bãyan an yi muhãwara a tsakãnin mabiya da shugabannin kãfirci, sãshe yanã la'antar sãshe har abu ya kai ga Shaiɗan, watau Iblis. Shi kuma ya tãshi ya yi wannan huɗuba dõmin ya ƙãra musu baƙin ciki a kan wani."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 258,
            "translated_text": "Kuma aka shigar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, a gidãjen Aljanna, kõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwamã a cikinsu da iznin Ubangijinsu, gaisuwarsu a cikinta \"Salãm\", (wãtau Aminci)."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 258,
            "translated_text": "Shin, ba ka ganĩ ba, yadda Allah Ya buga wani mĩsali, kalma mai kyau* kamar itãciya ce mai kyau, asalinta yanã tabbatacce, kuma rẽshenta yanã cikin sama?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kalma mai kyau ta addini tanã da asali, kamar itãciyar dabĩno ce."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 259,
            "translated_text": "Tanã bãyar da abincinta a kõwane lõkaci da iznin Ubangijinta! Kuma Allah Yanã buga misãli ga mutãne, mai yiwuwã ne, sunã tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 259,
            "translated_text": "Kuma misalin kalma mummũnã* kamar itãciya mummũnã ce, an tumɓuke ta daga bisa ga ƙasa, bã ta da wata tabbata.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kalma ta kãfirci, bã ta da asali, kamar gunar shãnu ce."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 259,
            "translated_text": "Allah Yanã tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni da magana tabbatacciya a cikin rãyuwar dũniya, da cikin Lãhira, Kuma Allah Yanã ɓatar da azzãlumai, kuma Allah Yanã aikata abin da Yake so."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 259,
            "translated_text": "Shin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya* ni'imar Allah da kãfirci kuma suka saukar da mutãnensu a gidan halakã?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kuraishãwa wadanda Allah Ya yi musu ni'imar zama a cikin hurumin Allah da aminci da Ya zuba a kansu da albarku, sun musanya gõdiya da kãfirci a lõkacin da suka ƙaryata Manzon Allah. Sun saukar da mutãnensu a gidan halaka a Badar."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 259,
            "translated_text": "Sunã ƙõnuwa a wutar jahannama, kuma tir da matabbatarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 259,
            "translated_text": "Kuma suka sanya wa Allah kĩshiyõyi, dõmin ɓatarwa daga hanyarSa, Ka ce: \"Ku ji dãɗi, sa'an nan, lalle ne, makõmarku Wutar ce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 259,
            "translated_text": "Ka ce wa bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka azurtã su, a asirce da bayyane, daga gabãnin wani wuni ya zo, bãbu ciniki a ciki, kuma bãbu abõtaka."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 259,
            "translated_text": "Allah ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar game da shi, daga 'ya'yan itãce arziki dõminku kuma Ya hõrẽ jirgin ruwa dõmin ya yi gudu a cikin tẽku da umurninSa, kuma Ya hõrẽ muku kõguna."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 259,
            "translated_text": "Kuma Ya hõrẽ muku rãnã da watã sunã madawwama biyu, kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 260,
            "translated_text": "Kuma Ya bã ku dukkan abin da kuka rõƙe Shi kuma idan kun ƙidaya, ni'imar Allah bã zã ku lissafe ta ba. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan zãlunci ne, mai yawan kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 260,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: \"Yã Ubangijina! Ka sanyã wannan gari* amintacce kuma Ka nĩsanta ni, nĩ da ɗiyãna daga bauta wa gumãka.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan gari watau Makka. Anã tunãtar da Lãrabãwa ga kãkansu Ibrãhĩm da addu'ar da ya yi sabõda garin Makka da mutãnen garin da ɗiyan Ismã'ila dõmin su wa'aztu."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 260,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijina! Lalle ne sũ, sun ɓatar da mãsu yawa daga mutãne sa'an nan wanda ya bĩ ni, to, lalle shi, yanã daga gare ni, kuma wanda ya sãɓa mini, to, lalle ne Kai Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 260,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijinmu! Lalle ne ni, na zaunar da zuriyata ga rãfi wanda ba ma'abũcin shũka ba, a wurin ¦ãkinka mai alfarma. Yã Ubangijinmu! Dõmin su tsayar da salla. Sai Ka sanya zukãta daga mutãne sunã gaggãwar bẽgenzuwa gare su, kuma ka azurtã su daga 'ya'yan itãce, mai yiwuwã ne sunã gõdẽwã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 260,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijinmu! Lalle ne Kai Kanã sanin abin da muke ɓõyẽwa, da abin da muke bayyanãwa. Kuma bãbu abin da yake ɓõyẽwa ga Alah, daga wani abu a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 260,
            "translated_text": "\"Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda Yake Ya bã ni inã a cikin tsufa Ismã'ila da Is'hãƙa. Lalle ne Ubangijina, haƙĩƙa, Mai jin addu'a ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 260,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijina! Ka sanyã ni mai tsayar da salla. Kuma daga zũriyyata. Yã Ubangijinmu! Kuma Ka karɓi addu'ata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 260,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara gare ni, kuma ga mahaifãna, kuma da mũminai, a rãnar da hisãbi yake tsayãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 260,
            "translated_text": "\"Kuma kada ka yi zaton Allah Mai shagalã ne daga abin da azzalumai suke aikatãwã. Abin sani kawai, Yanã jinkirta musu ne zuwa ga wani wuni, wanda idãnuwa suke fita turu- turu a cikinsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "\"Sunã mãsu gaggãwa, mãsu ɗaukaka kãwunansu zuwa sama ƙiftawar ganinsu ba ta kõmãwa gare su. Kuma zukãtansu wõfintattu.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * A nan ne iyakar maganar shugabanmu Ibrahĩm da addu'arsa."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "Kuma ka yi gargaɗi ga mutãne ga rãnar da azãba take jẽ musu, sai waɗanda suka yi zãlunci su ce: \"Yã Ubangijinmu! Ka yi mana jinkiri zuwa ga wani ajali makusanci, mu karɓa wa kiranKa, kuma mu bi Manzanni.\"(Allah Ya ce musu) \"Ashe, ba ku kasance kun yi rantsuwã ba daga gabãni, cẽwa bã ku da wata gushẽwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "\"Kuma kuka zaunã a cikin gidãjen waɗanda suka zãlunci kansu, kuma ya bayyana a gare ku yadda Muka aikatã game da su, kuma Muka buga muku misãlai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "Kuma lalle sun yi mãkirci irin makircinSu kuma a wurin Allah makircinsu, yake, kuma lalle ne makircinsu yã kasance, haƙĩƙa, duwãtsu sunã gushẽwã sabõda shi."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "Sabõda haka, kada ka ƙarfafa zaton Allah Mai sãɓa wa'adinSa ne ga ManzanninSa. Lalle ne Allah ne Mabuwãyi, Ma'abũcin azãbar rãmuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "A rãnar da ake musanya ƙasa* bã ƙasar nan ba, da sammai kuma su bayyana ga Allah Makaɗaici, Mai tanƙwasãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * A Rãnar Ƙiyãma Allah zai musanyã ƙasa da sama a kãwo waɗansu a lõkacin da mutãne suke a kan Sirãɗi kamar yadda ya zo a Hadisi."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "Kuma kana ganin mãsu laifi, a rãnar nan, sunã waɗanda aka yi wa ciri daidai a cikin marũruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "Rigunansu daga farar wutã ne, kuma wuta ta rufe fuskõkinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "Dõmin Allah Ya sãkã wa kõwane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah Mai gaggãwar hisãbi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 14,
            "page_number": 261,
            "translated_text": "Wannan iyarwa ce ga mutãne, kuma dõmin a yi musu gargaɗi da shi, kuma dõmin su sani cẽwa, abin sani kawai, shĩ ne abin bautawa guda. Kuma dõmin masu hankali su riƙa tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kõwane kãfiri yanã gũrin yã zama Musulmi dõmin abin da yake gani na shiriya da ladubban Musulunci, waɗanda ya tabbata bãbu zama lãfiya ga mutum fãce idan yã sãme su, amma shaiɗan yanã hana shi musulunta sabõda waɗansu dalĩlai da yake sanyãwa a ganinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "\"Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,* bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Gaskiya a nan anã nufin azãba dõmin zuwanta tabbatacce ne. Dukan abin da yake tabbatacce shĩ ne haƙƙun, watau gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Kamar wancan ne Muke shigar da shi* a cikin zukãtan mãsu laifi.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Shirki da kãfirci da ƙaryatãwa, su duka izgili ne da addini."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanyar mutãnen farko ta ƙaryata Manzanni har a lõkacin da Allah zai halaka su da azãbarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 262,
            "translated_text": "Lalle ne dã sun ce: \"Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã* da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Muka sanya muku abũbuwan rãyuwa a cikinta, kuma Muka mallaka muku bãyi waɗanda suke bã kũ ne kuke ciyar da su ba, Mũ ne ke ciyar da su game da ku duka. Wãtau aza abũbuwa a kan ma'auni shĩ ne maslaha rashin yarda da tsaron ma'aunin nan shĩ ne izgili."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar* iskar zafi.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Halittar Ãdamu daga yumbu kekasasshe, ya fi daraja bisa halittar Shaiɗan daga harshen wuta, dõmin wuta tanã nũni ga sassabcin hankali da rashin natsuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: \"Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "\"To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa* a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ya nũnã Ãdamu an yi halittarsa ne da lãka da Rũhi daga Allah kamar yadda aka halitta Isã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sabõda haka halittar Ãdamu ta fi zama abin mãmãki daga halittar Ĩsã, dõmin Ĩsã asali guda kawai ya rasa daga halittar ɗiyan Adam ta al'ãda, amma halittar Ãdamu tã rasa dukan asalan biyu na uwa da na uba. Haka kuma halittar Hawwã'u, matar Ãdamu tã fi ta Ĩsã ban mãmãki dõmin rashin asalin uwa da ta yi inda ɗã yake ɗaukar lõkacin sũrantãwa, ya fi ban mãmãki daga rashin asalin uba."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 263,
            "translated_text": "Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Ya ce: \"To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Ya ce: \"To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "\"Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "\"Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Ya ce: \"Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "\"Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Tanã da ƙõfõfi bakwai,* ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ƙõfofin Jahannama bakwai ne, watau ɗabaƙõƙinta ta farko ita ce Jahannama, sa'an nan Lazza, sa'an nan Alhuɗama sa'an nan Assa'ĩra, sa'an nan saƙar, sa'an nan Aljahĩm, sa'an nan Alhãwiya. Kõwace ɗabaƙa tanã da juz'i sananne, watau ƙõfa ga Yahudu, wata ga Nasãra, wata Saba'ãwa, wata ga Majũsãwa, wata ga Mushirikai, wata ga munãfukai, wata ga Musulmi waɗanda aka yi musu hushi (mummunan aiki). Anã fatan fita ga mãsu tauhĩdi daga gare ta. Ba a fatan kõme ga sauran, sunã dawwama a cikinta har abada."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "\"Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 264,
            "translated_text": "Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: \"Sallama.\" Ya ce: \"Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Suka ce: \"Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin kun bã ni bushãra* ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ibrahĩm yanã yi musu tambayã ne dõmin yanã ganin kamar sunã yi masa magana ta izgili ne a kan sãmun ɗã a bãyan tsũfansa da na mãtarsa. Sabõda haka suka gaya masa cewa sũ masu gaskiya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Suka ce: \"Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Ya ce: \"To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!\""
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "\"Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "\"Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,"
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "\"Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "\"Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "\"Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 265,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ga waɗannan, 'ya'yãna* idan kun kasance mãsu aikatãwa ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yanã nufin mãtan garin, dõmin Annabin mutãne shĩ ne ubansu."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Rantsuwa da* rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Yã yi rantsuwã da rãyuwar Annabi Muhammadu, tsĩrã da amincin Allah su tabbata a gare shi. Wannan shĩ ne matuƙar girmamãwar wadda Allah Yake yi wa mutum. Kuma yanã nũna cewa rãyuwar Annabi tanã da muhimmanci ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Hanya tabbatacciya ta mutãnen Makka zuwa Syria (Sham)."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika* sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ma'abũta Al'aika, sũ ne mutãnen shu'aibu."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri(5) sun ƙaryata Manzanni.<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Ma'abũta Hijiri, sũ ne samũdãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu(6) da Alƙur'ãni mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n (6) Bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu su ne Fãtiha mai ãyõyi bakwai. Anã karanta su a cikin kõwace raka'a ta salla."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kuma ka ce: \"Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 266,
            "translated_text": "Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,(7)<br \/>\n____________________<br \/>\n  (7) Mãsu rantsuwa a kan sãɓa wa Annabãwa, watau kamar sun yi rantsuwa wa bã zã su bi abin da Annabãwa suka zoda shi ba. Wãtau su ne mãsu tsananin izgili da addini."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "To, rantsuwa da Ubangijinka!* Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Ya yi rantsuwa da ZãtinSa a kan Shĩ ne Ubangijin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi, dõmin Ya natsar da ransa daga tsõron mãsu yi masa izgili, kuma dõmin Ya ƙarfafa shi ga zartar da aikin da Ya sanya shi na iyar da Manzanci bã da wata fargaba ba."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu* izgili.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Mãsu tsananin izgili ga Annabi waɗanda Allah Ya isar masa daga gare su su biyar ne, daga Bani Asad bn Abdul'uzza bn Kusayyi akwai Aswadu bn el Muttalib, Abu zam'ah, kuma daga Bani Zuhrah akwai el Aswad bn Abdu Yagũth. Daga Bani Makhzumi akwai el walid bn Mugira. Daga Bani Sahmi akwai el Ãs bn wã'il. Daga Banĩ Khuzã'a akwai el Harith bn el-Tulãtilah. Su ne mãsu darajar mutãnensu. A lõkacin da suka dõge da sharri, Allah Ya hũtar da Annabi daga sharrinsu da nau'i-nau'i na masĩfu suka halaka. Dubi ƙarin bayãni daga tafsĩrin bn Kathĩr. tsare Annabi daga gare su, tun yanã shi kaɗaia Makka yã isa ya sanya shi ya dõgara ga Allah bãyan abubuwa sun ƙãra yawa da sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili)."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 15,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi* daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Saukar da malãiku da Rũhi watau Alƙur'ãni a zãmanin Annabci kõ kuma fahimta da ƙarfin zũciya waɗanda Allah ke sanyãwa ga wanda Ya nufa da jaddada addĩni a kan kõwane ƙarni. Aiko mãsu gargaɗi shĩ ne mafi girman ni'imar Allah a kan mutãne."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 267,
            "translated_text": "Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 268,
            "translated_text": "Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 268,
            "translated_text": "Kuma da dawãki* da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Haɗa dawãki da alfadarai zuwa ga jãkuna kuma aka ce dõmin \"hawansu da yin ƙawã\" yana nũna cewa ba a cin dawãki da alfadarai dõmin an san cewa an hana cin jãkuna a lõkacin yãƙin Khaibara, kuma ãyõyin da ke gaba da wannan ãya sun nũna anã cin dabbõbin ni'ima kuma anã hawansu, kuma cin nãma yã fi hawa zama ni'ima, sabõda haka, shĩ ne ya kamãta a ambata inda ya halatta. Wannan ne mazhabar Mãliki da Ahu Hanĩfa, kuma shĩ ne maganar Abdullah bn Abbãs Allah Ya yarda da su. Wasu sun ce ana cin dawãki da alfadarai dõmin cewa, \"Anã hawansu dõmin ƙawa,\" bã ya hana a yi wani abu da su, wato cin nãmansu, dõmin a cikin Bukhãri daMuslim an ruwaito halaccin cin dawãki. Wannan shĩ ne maganar Al-Hasan da Shuraih da 'Aɗa' a da Sa'ĩd bn Jubair. Kuma Shi ne mazhabar shãfi'i da Is'hãƙ. Sun yi hujja da halaccin nãman dawãki da abin da Asmã'u bint Abĩ Bakar Assiddiƙ ta ce, \"Mun sõke wata gõɗiya' muka ci a zamanin Manzon Allah,a Madina.\" Kuma a cikin Bukhãri da Muslim daga jãbir, Allah Ya yarda da shi, \"Mun ci dawãki da jãkunan jeji a Khaibara, kuma Annabi tsira da aminci sun tabbata a gare shi, ya hana jãkunan gida\" Acikin Abĩ Dãwud, \"Mun yanke dawãki da alfadarai da jakuna alhãli yunwa ta kãmã mu, amma sai Annabi ya hana mu cin jãkuna da alfadarai, bai hana mu cin dawãki ba\" Nĩ, a ganina, ra'ayin cin dawãki ya fi ƙarfi dõmin sũrar ta sauka a Makka, amma hadisin yankan gõɗiyar, a Madĩna aka yi shi. Saboda haka surar ba ta shãfe shi ba. Dũbi Radd Al-Azhãn."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 268,
            "translated_text": "Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacẽwa. Kuma da Yã so, dã Ya shiryar da ku gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 268,
            "translated_text": "Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dõminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itãce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 268,
            "translated_text": "Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 268,
            "translated_text": "Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 268,
            "translated_text": "Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai sãɓãnin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 268,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Kuma Ya jẽfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dõmin kada ta karkata da ku, da kõguna da hanyõyi, ɗammãninku kunã shiryuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci)."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Shin, wanda Yake yin halitta yanã yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bã ku tunãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Kuma idan kun ƙidãya ni'imar Allah, bã ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke asirtãwa da abin da kuke bayyanãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kõme ba, kuma sũ ne ake halittawa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Matattũ ne, bã su da rai, kuma ba su san a wane lõkaci ake tãyar da su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Abin bautawarku, abin bautãwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, zukãtansu mãsu musu ne, kuma su makangara ne."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yanã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. Lalle ne Shi, bã Ya Son mãsu girman kai."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Idan aka ce musu: \"Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?\" Sai su ce: \"Tãtsũniyõyin mutãnen farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar ¡iyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 269,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa,* sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kamar yadda Allah Ya halaka Bukht Nasar. Aka halaka shi da ginin gidansa. Allah Yanã halaka kãfirai da abin da suke tãnadã wa kansu dõmin nħman rãyuwarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 270,
            "translated_text": "Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: \"Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?\" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: \"Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kãfirai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 270,
            "translated_text": "Waɗanda malãiku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu zãluntar kansu. Sai suka jẽfa nẽman sulhu (suka ce) \"Ba mu kasance muna aikata wani mummũnan aiki ba.\" Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 270,
            "translated_text": "Sai ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kunã madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin mãsu girman kai."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 270,
            "translated_text": "Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, \"Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?\" Suka ce, \"Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri.\" Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 270,
            "translated_text": "Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke sãkã wa mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 270,
            "translated_text": "Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã cẽwa. \"Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 270,
            "translated_text": "Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 270,
            "translated_text": "Sai mũnãnan abũbuwan da suka aikata ya sãme su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 271,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: \"Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya haramta.\" Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã?"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 271,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): \"Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu.\" To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 271,
            "translated_text": "Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah bã Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma bã su da waɗansu mataimaka."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 271,
            "translated_text": "Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bã ya tãyar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 271,
            "translated_text": "Dõmin Ya bayyana musu abin da suke sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin waɗanda suka kãfirta su sani cẽwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryatã."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 271,
            "translated_text": "Abin sani kawai, MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, \"Ka kasance; sai yanã kasancẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 271,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su, haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi girmã, dã sun kasance sunã sani."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 271,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, fãce waɗansu mazãje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutãnen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãninsu su yi tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Ko kuwa Ya kama su a cikin jujjuyawarsu? Sabõda haka ba su zama masu buwãya ba."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Ko kuwa Ya kama su a kan naƙasa? To, lalle ne Ubangijinka haƙĩƙa Mai tausayi ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu ƙasƙantar da kai?"
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma bã su kangara."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Suna tsõron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umuruin su."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Kuma Allah Ya ce: \"Kada ku riƙi abũbuwan bautãwa biyu. Abin sani kawai, wanda ake bautãwa guda ne, sa'an nan sai kuji tsõroNa, Ni kawai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Kuma Yana da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, kuma Yana da addini wanda yake dawwamamme. Shin fa, wanin Allah kuke bĩ da taƙãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "Kuma abin da yake a gare ku na ni'ima, to, daga Allah ne. Sa'an nan kuma idan cũta ta shãfeku, to, zuwa gare Shi kuke hargõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 272,
            "translated_text": "sa'an nan idan Ya kuranye cũtar daga gare ku, sai gã wani ɓangare daga gare ku game da Ubangijinsu sunã shirki."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Dõmin su kãfirta da abin da Muka bã su. To, ku ji dãɗi, sa'an nan da sannu zã ku sani."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Kuma sunã sanya rabõ *ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sunã sanyãwar rabõ daga dabbõbi da hatsi ga gumãka kõ aljannu, alhãli ba su san amfãnin da gumãkan kõ aljannun suke iya jãwo musu ba kõ suke tunkuɗewa daga gare su. Akwai daga cikin ni'imõmin Allah, Ya shiryar da mutãne ga gãne cewa waɗannan gumãka da aljannu kõ wani mahalũƙi bã ya iya cũta kõ jãwo wani amfãni fãce da iznin Allah. Sabõda haka bãbu wanda ya cancanci a bauta masa fãce Allah, Mai tumɓuke cũta kuma Mai jãwo amfãni. Watau wannan bãyar da ni'imar 'yancin ɗan Adam kãmilan, su duka bãyi ne, bãbu daraja ga kõwa sai da taƙawa.Sanin haka wata ni'ima ce daga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Kuma sunã danganta 'ya'ya mãta ga Allah. Tsarkinsa yã tabbata! Kuma sũ ne da abin da suke sha'awa."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace* sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Fahintar cewa ɗã namiji da'ya mace duka ɗaya suke, da hana kashe su kõ turbuɗe su, wata ni'ima ce babba da 'yancin mãtã babba, a cikin rãyuwar ɗan Ãdam."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Ga waɗanda ba su yi ĩmãni* da Lãhira ba akwai sifar cũta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ƙãrin bãyani ne ga abin da ya gabãta kuma na bãya da shi ya rãtayu da shi, shiryarwa zuwa ga halãye maɗaukaka ni'ima ce babba."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu,* dã bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Rashin halaka dũniya sabõda laifin mutãne da rashin kãmasu da dukan laifinsu, ni'ima ce babba."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlẽwa ne (a cikinta)."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabãninka, sai Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 273,
            "translated_text": "Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 274,
            "translated_text": "Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 274,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima; Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 274,
            "translated_text": "Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye* da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yã ambaci abin mãye a cikin abũbuwan ni'ima a gabãnin aharamta giya. Kuma haramtã ta bã ya hanã ta zuma a cikin ni'imõmin Allah ga mutãne dõmin an haramtã ne sabõda tsaron hankalinmu a kan neman waɗansu ni'imõmin da suka fĩ ta a Aljanna a inda bã zã a hana ta ba sabõda ƙarewar taklĩfi a can. Sabõda haka ne ya ƙãre ãyar da cewa: \"Akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 274,
            "translated_text": "Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi* zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: \"Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wahayi na ilhama, watau Allah Ya cũsa wa ƙudan zama ilmin yin sã ƙar gidan zuma da gãne hanyõyin tafiya ta kõma gidanta, da cin kõwane irin furen itãce dõmin a fitar dani'imar abin sha mai dãdi ga mutãne, kuma wanda ya ƙunsa dukkan mãgani ga ciwarwatansu. Wannan ni'ima ce babba."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 274,
            "translated_text": "\"Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru.\" Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 274,
            "translated_text": "Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 274,
            "translated_text": "Kuma Allah Ya fifita sãshenku* a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Arziki daga Allah yake, yanã fĩfĩta waɗansu bãyinsa da arziki a kan waɗansu, sa'an nan wanda aka bai wa arziki daga ckinsu bã ya iya mayar da arzikin a tsakãninsa da wani bãwa nasa har su zama daidai a kan arzikin. to, idan haka ne, yaya kuke sanya waɗansu bãyin Allah daidai da Allah wajen bautarku gare su?."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 274,
            "translated_text": "Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta?"
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 275,
            "translated_text": "Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa (ga aikata kõme)."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 275,
            "translated_text": "Sa'an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 275,
            "translated_text": "Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme, da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 275,
            "translated_text": "Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici?"
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 275,
            "translated_text": "Kuma ga Allah gaibin* sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ɓõye lõkacin Ƙiyãma a bãyan bayãnin tabbatar aukuwarta yanã daga cikin ni'imõmin Allah, dõmin mai hankali ya yi tattãli sabõda ita."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 275,
            "translated_text": "Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 275,
            "translated_text": "Shin ba su ga tsuntsãye* ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tsuntsãye hõrarru a cikin sararin sama, ana nufi da su, a ganĩna, Allah ne Ya san haƙĩƙa, su ne jirãgen sama, sabõda ambaton hõrewa tãre da sũ a cikin sararin samãniya, dõmin abin da aka hõre, ana hõronsa ne dõmin a ci amfãninsa a lõkaci da wurin hõron. Tsuntsãyen al'ãda bã su da wani amfãni a gare mu a lõkacin da suke a cikin sãrãrin sama. Sabõda haka bãbu wani abu, sai jirgin sama. Bã zã a ce anã nufin shãho ba a lõkacin farauta, dõmin wannan amfãni yã yi kaɗan bisa ga abin da sũrar take ƙidãyãwa na ni'imõmin Allah a kan mutãne gabã ɗaya. Farauta keɓãɓɓiya ce ga mutãnen ƙauye kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 276,
            "translated_text": "Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu* da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Sũfi, shi ne gãshin tumãki mai kama da audugã, wabar shi ne gãshin rãƙumi mai laushi, sha'ar, shi ne gãshin awaki da gezar dawãki. Bai ambaci audugã da kattãni ba, dõmin a wajen shũka suke."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 276,
            "translated_text": "Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna *sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Rĩgã dõmin zãfi da sanyi daga sũfi da wabar da gãshi da audugã da kattãni da rĩga dõmin makãmi shi ne sulke, dõmin makãmi daga baƙin ƙarfe yake kamar takõbi, mãshi da kibiya."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 276,
            "translated_text": "To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 276,
            "translated_text": "Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 276,
            "translated_text": "Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 276,
            "translated_text": "Kuma idan waɗanda suka yi zãlunci suka ga azãba, sa'an nan bã za a saukake ta daga gare su ba, kuma bã su zama anã yi musu jinkiri ba."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 276,
            "translated_text": "Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: \"Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa\". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, \"Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 276,
            "translated_text": "Kuma su shiga nẽman sulhu zuwa ga Allah a rãnar nan, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 277,
            "translated_text": "Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange daga hanyar, Allah, Mun ƙãra musu wata azãba bisa ga azãbar, sabõda abin da suka kasance sunã yi na fasãdi."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 277,
            "translated_text": "Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al'umma a kansu daga kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littãli a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi)."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 277,
            "translated_text": "Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 277,
            "translated_text": "Kuma ku cika da alkãwarin* Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wanda yake rantsuwar alkawari da wani, sa'an nan ya warware rantsuwar dõmin neman ya ƙulla wata rantsuwa da wani mutum sabõda wani amfãninsa kõ jama'arsa a cikin wata kabĩla wadda ta fi ta mutãnen farko ƙarfi to, siffarsa kamar mace ce mahaukaciya, mai yin zare, a bayan ta tukka shi, ya yi ƙarfi, sa'an nan ta warware shi. Sabõda haka idan ta so mayar da shi wani zare, to, bã zai yi kyau ba kamar zaren farko da ta yi kuma mutãne sun gãne haukarta, bã zã su yi wata ma'ãmala da ita ba. Wanda ya yi rantsuwa da Allah a kan abu, to, yã sanya Allah lãmuni ke nan. Bã ya halatta ga wanda ya shugabantar da Allah ga wani abu, sa'an nan ya kõma bãya ya ƙi cika wannan alkawarin dõmin bai kiyãye girman Allah ba, wanda ya sanya a tsakaninsa da abõkin ma'ãmalarsa. Tsaron alkawari ni'ima ne."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 277,
            "translated_text": "Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bãyan tukka, ya zama warwararku, kunã riƙon rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, dõmin kasancẽwar wata al'umma tãfi rĩba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yanã jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yanã bayyana muku a Rãnar ¡iyãma, abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wajũna."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 277,
            "translated_text": "Kuma dã Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dã Ya sanya ku al'umma gudã, kuma Yanã ɓatar da wanda Ya so. kuma Yanã shiryar da wanda Ya so. Lalle ne anã tambayarku abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 278,
            "translated_text": "Kada ku riƙi rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wanda yake yin rantsuwa da Allah dõmin ya yaudari wani, to, yanã rũsa kansa ne da kansa, kuma Allah Yanã ħbe jãrumci da natsuwa daga zũciyarsa, sa'an nan kuma yanã da wata azãba mai girma a Lãhira idan Allah bai gãfarta masa ba, da tũba kõ da wani sababi. Sanin haka ni'ima ne."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 278,
            "translated_text": "Kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 278,
            "translated_text": "Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 278,
            "translated_text": "Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 278,
            "translated_text": "Sa'an nan idan ka karantã *Alƙur'ãni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * An yi saɓãni ga zaman Isti'ãza gabãnin karãtu kõ a bãyansa. Mãlik ya zãɓi a yi 'Isti'ãza' bãyan karãtu, kõ a bãyan an ƙãre yin salla, dõmin kada shaiɗan ya rinjãyi mutum a bãyan ĩmãninsa da salla. Sabõda haka ya karhanta shi a cikin salla. Wasu kuma sunã isti'ãzã a gabãnin karãtu kõ a gabãnin salla."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 278,
            "translated_text": "Lalle ne shi, bã shi da wani ƙarfi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 278,
            "translated_text": "Abin sani kawai ƙarfinsa yanã a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, mãsu shirki ne."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 278,
            "translated_text": "Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: \"Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne.\" Ã'a, mafi yawansu bã swa sani."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 278,
            "translated_text": "Ka ce: \"Rũhul ¡udusi* ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma (dõmin) shiriya da bushãra ga Musulmi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Rũhul Ƙudusi, watau rai mai tsarki, anã nufin Jibrilu, amincin Allah ya tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 279,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin (cẽwa) lalle ne sũ, sunã cẽwa, \"Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi.\" Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan (Alƙur'ãni) harshe ne Balãrabe bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 279,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, Allahbã zai shiryar da su ba, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 279,
            "translated_text": "Abin sani kawai waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 279,
            "translated_text": "Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 279,
            "translated_text": "Waɗancan ne kãfirai dõmin sun fĩfĩta son dũniya a kan Lãhira, kuma lalle ne Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 279,
            "translated_text": "Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukãtansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗancan sũ ne gafalallu."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 279,
            "translated_text": "Bãbu shakka lalle ne a Lãhira sũ ne mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 279,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 280,
            "translated_text": "A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 280,
            "translated_text": "Kuma Allah Ya buga misãli,* wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kamar Makka. Annabi Muhammadu ya je musu sun ƙaryata shi, sai Allah Yã musanya amincinsu da tsõro, kuma wadãtarsu da yunwa. Wannan shĩ ne sakamakon ridda a kõwane lõkaci."
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 280,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci."
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 280,
            "translated_text": "Sa'an nan ku ci daga* abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyan bayãni a kan hukuncin ridda sabõda sanyãwar sãshen ni'imõmin Allah ga wasu gumãka kõ aljannu kõ waɗansu mutãne sãlihai, sa'an nan Ya yi umurni da cin abin da Allah Ya azurta mutum duka amma da sharuɗɗa uku, watau ya zama halas ga shari'a kuma mai dãɗin ci, wani haƙƙi na wani mutum bai rãtaya ba a kansa ga shari'a, kuma a bi shari'a wajen aikatar da shi kamar yadda Allah Ya ce wajen yanka da mai kama da shi, shi ne gõde wa Allah. Sabõda haka banda kamar giya da kãyan wani mutum sai fa a bisa yardarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 280,
            "translated_text": "Abin sani kawai (Allah) Ya haramta* muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bayãnin abũbuwan da aka haramta, idan bãbu larũra. Anã cin abin da shari'a ta hana a ci a kan larũra sai idan larũrar ta sãmi mutum ne a cikin hãlin sãɓon Allah, kamar mai fita daga ɗã'ar sarkin Musulunci ya yi tãsa ƙungiya dabam, kõ wanda ya fita dõmin wani zãlunci kamar sãta ga misãli, to, ba su cin haram dõmin su ci gaba da aikinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 280,
            "translated_text": "Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, \"Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne.\" Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba."
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 280,
            "translated_text": "Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 280,
            "translated_text": "Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni,* kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Gabãnin wancan sũra, kamar a cikin sũratul An'ãm ãyã ta l46. Sabõda haka bã a biyar da Yahũdu a wajen haramcin abin da Allah Ya haramta musu, su kaɗai sabõda zãluncinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki* da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wanda ya yi wani abu da Allah Ya hana wajen ni'imõmi ko wajen wani abu dabam na sãɓon Allah, to, idan ya tũbã A gabãnin ya kai ga gargara, Allah zai gãfartã masa. Wannan ni'ima ce."
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Lalle ne Ibrãhĩm* ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Akwai daga ni'imõmin Allah,Ya sanya mutum maɗaukaki sabõda addininsa da ĩmãninsa ga Ubangijinsa, kuma Yã bã shi ĩkon binsa da taƙawa kamar yadda Ya yi wa Ibrahĩm. Kuma akwai daga ni'imõmin Allah Ya sanya mutum a cikin zuriyyar mutumin kirki kamar yadda Ya yi wa Annabi Muhammadu Ya sanya shi a cikin zuriyyar Ibrãhĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Mai gõdiya* ga ni'imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici.<br \/>\n____________________<br \/>\n * An ambaci Ibrãhĩm sabõda ya gõde wa ni'imõnin Allah dõmin Musulmi su yi kõyi da shi wajen gõde wa Allah ga ni'imõmin da Ya yi ishãra zuwa gare su a cikin wannan Sũra da watanta. Gõde wa ni'ima wata ni'ima ce."
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai."
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cẽwa), \"Ka* bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.'<br \/>\n____________________<br \/>\n * Yanã cikin ni'ima ga Ibrãhĩm da kammalarta a gare shi a umurci mafĩfĩcin tãlikai Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, da bin aƙĩdar Ibrãhĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa.(5) Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã.<br \/>\n____________________<br \/>\n  (5) Waɗanda suka sãɓa wa jũna a cikin sha'anin Ibrahĩm wanda yake ya kasance yanã girmama Juma'a dõmin ita ce rãnar cikon ni'imõmin Allah a kan bãyinsa. Yahudu suka sãɓã wa Ibrãhĩm suka girmama Asabar dõmin a rãnar nan ne bãbu wani aiki. Wannan ya dõge har a bãyan ɗauke Ĩsa. Nasãra suka jũya dõmin ƙin Yahũdu zuwa ga Lahadi, dõmin su yi daidai da Kaisara, Ƙustantin, mai girmama Lahadi, rãnar bautã wa rãnã. Kafirce wa ni'ima azaba ce."
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima(6) da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n (6) Kira zuwa ga hanyar Ubangiji, Allah, yanã daga cikin abũbuwan kõyo daga Ibrãhĩm kuma kira zuwa ga Allah na daga cikin ni'imõmin Allah ga mai kiran da wanda ake kiran sa'an nan zaman kiran da hikima da wa'azi mai kyau, ni'ima ce ga mai yi da waɗanda ake kira zuwa ga shiriyar duka. Abin da ake cħwa Hikima shĩ ne a yi magana a kan hujja wadda abõkin husũma bã zai iya kauce mata ba."
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Kuma idan kuka sãka(7) wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri.<br \/>\n____________________<br \/>\n (7) Kuma mai kiran mutãne zuwa ga Allah lalle ne sai ya haɗu da cũtarwa daga mutãnen da bã su son gaskiyã. To, Allah bã Ya son zãlunci ko dã a kan maƙiyansa, sabõda haka Ya yi umurni da yin ƙisãsi da misãlin uƙũba, kõ a yi haƙuri, amma yin haƙuri yã fi rãmãwa dõmin nħman ni'imar Allah ta ƙãra kammala."
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci."
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 16,
            "page_number": 281,
            "translated_text": "Lalle Allah Yanã tãre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ mãsu kyautatãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 282,
            "translated_text": "Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare* da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa** wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Isrã'i, shi ne tafiyar dare da Allah Ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitil Maƙadis. Sa'an nan Mi'iraji zuwa sama inda aka ba shi sallõli. ** Muƙarana a tsakãnin Masjidil Harãm watau tsararre daga a yãki mutãnensa da Masjidil Aƙsã wanda ba tsararre ba. Isrã'i da Mi'irãji sun fi Miƙãtin Mũsã da gãnãwarsa da Ubangiji a Ɗũr-Sĩna'a."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 282,
            "translated_text": "Kuma Mun bai wa Mũsã* littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isrã'ila, cẽwa kada ku riƙi wani wakĩli baiciNa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Tsakãnin Bãwan Allah Muhammadu da Mũsã, kuma an aiko Mũsã ga Banĩ Isrã'ila kawai, kuma Nũhu an ce masa bãwa amma ba a jingina shi kamar yadda aka jingina bawanSa ba. Sa'an nan kuma Jingina Yahũdu ga Nũhu ya daidaita su da sauran mutãne wajen da'awar ɗaukaka da nasaba."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 282,
            "translated_text": "Zuriyar waɗanda Muka ɗauka tãre da Nũhu. Lalle ne shi ya kasance wani bãwa mai gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 282,
            "translated_text": "Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isrã'ĩla a cikin Littãfi, cewa lalle ne, kunã yin ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kunã zãlunci, zãlunci mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 282,
            "translated_text": "To idan wa'adin na farkonsu yajẽ, za Mu aika, a kanku waɗansu bãyi* Nãmu, ma'abũta yãƙi mafĩ tsanani, har su yi yãwo a tsakãnin gidãjenku, kuma yã zama wa'adi abin aikatawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sun yi fasãdi da barin aiki da Taurãti, sabõda haka aka aika Jãlũta a kansu. Ya kashe su kuma ya kãma zuriyarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 282,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Mu nwayar da ɗauki a gare ku a kansu, kuma Mu taimake ku da dũkiyõyi da ɗiya kuma Mu sanya ku mafiya yawan mãsu fita yãƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 282,
            "translated_text": "Idan kun kyautata, kun kyautata dõmin kanku, kuma idan kun mũnana to dõmĩnsu. Sa'an nan idan wa'adin na ƙarshe(5) ya jẽ, (za su je) dõmin su baƙanta fuskokinku, kuma su shiga masallaci kamar yadda suka shige shi a farkon lõkaci, kuma dõmin su halakar da abin da suka rinjaya a kansa, halakarwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  (5) Suka yi fasãdi marra ta biyu da kashe Zakariyya da Yahaya, sai aka aika musu da Bukht Nasar daga Bãbila ya karkashe su, kuma ya kãma zuriyarsu, kuma ya rũshe Baitil Maƙadis. Waɗannan lãbaru biyu na ɓarnar Banĩ Isrã'ila sunã cikin bãyar da lãbaru ga gaibi. Idan an daidaita su da lãbarun gaibi waɗanda Alƙur'ãni ya faɗã, waɗansu suka auku kuma waɗansu sunã ta aukuwa zã a san falalar Alƙur'ãni a kan Taurãti kamar yadda ya bayyana cewa Attaura ta yi kira zuwa ga tauhidi da shiriya, sa'an nan ya bayyana abũbuwan da Alƙur'ãnĩ yake karantarwa daga ãyã ta 9 zuwa ga ãyã ta 38 inda ya tãra hãlãyen ƙwarai kuma ya kõre mũnãna."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "Akwai tsammãnin Ubangijinku Ya yi muku rahama. Kuma idan kun sãke Mu sãke. Kuma Mun sanya Jahannama matsara ga kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita* kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) \"Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Bãyan ya faɗi abũbuwan da Attaura ta karantar, ya ce: \"Alƙur'ãni yanã shiryarwa zuwa ga hãlãyen da suka fi daidaita daga abin da Attaura ta karantar.\" Sa'an nan ya ci gaba da bayãnin abũbuwan da Alƙur'ãni yake karantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, Mun yimusu tattalin wata azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "Kuma mutum yanã* yin addu'a da sharri kamar addu'arsa da alhẽri, kuma mutum ya kasance mai gaggãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Alƙur'ani yanã shiryar da mutum har ga yadda yake yin addu'a dõmin kada ya yi wa kansa addu'a ta sharri alhãli kuwa yanã nufin ya yi alhħri dõmin an halicci mutum da son gaggãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "Kuma Mun sanya dare da rãna, ãyõyi biyu, sa'an nan Muka shãfe ãyar dare, kuma Muka sanya ãyar rãna mai sanyãwa a yi gani, dõmin ku nẽmi falala daga Ubangijinku, kuma dõmin ku san ƙidãyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kõme Mun bayyana shi daki-dakin bayyanãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "Kuma kõwane mutum Mun lazimta masa abin rekõdinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Rãnar ¡iyãma da littãfi wanda zai haɗu da shi buɗaɗɗe."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "\"Karanta Littãfinka. Ranka ya isa ya zama mai hisãbi a kanka a yau.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dõminkansa kawai kuma wanda ya ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bã ya ɗaukar nauyin wani ran, kuma ba Mu zama mãsu yin azãba ba, sai Mun aika wani Manzo."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta, har su yi fãsicci a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 283,
            "translated_text": "Kuma da yawa Muka halakar da al'ummomi a bãyan Nũhu. Kuma Ubangijinka Ya isa ya zama Mai ƙididdigewa ga zunubban bãyinSa, Mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Wanda ya kasance yanã nufin mai gaggãwa, sai Mu gaggauta masa a cikinta, abin da Muke so ga wanda Muke nufi, sa'an nan kuma Mu sanya masa Jahannama, ya ƙõnu da ita, yanã abin zargi kuma abin tunkuɗewa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Kuma wanda ya nufi Lãhira, kuma ya yi aiki sabõda ita irin aikinta alhãli kuwa yanã mũmĩni, to, waɗannan aikinsu ya kasance gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Dukkansu Munã taimakon waɗannan da waɗancan daga kyautar Ubangijinka, kuma kyautar Ubangijinka ba ta kasance hananna ba."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Ka duba yadda Muka fĩfĩtar da sãshensu a kan sãshe! Kuma lalle ne Lãhira ce mafi girman darajõji, kuma mafi girman fĩfĩtãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Kada ka sanya wani abin bautawa na daban tãre da Allah har ka zauna kana abin zargi, yarɓaɓɓe."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: \"Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da yake a cikin rãyukanku. Idan kun kasance sãlihai to lalle ne shĩ Ya kasance ga mãsu kõmawa gare Shi, Mai gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Kuma ka bai wa ma'abũcin zumunta hakkinsa* da miskĩna da ɗan hanya. Kuma kada ka bazzara dũkiyarka, bazzarãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Hakkin zumunta shi ne alheri da sãdar da zumunta. Hakkin miskini da ɗan hanya zakka da sadakar taɗawwa'i da liyãfar kwana uku ga bãƙo bisa al'ada da alheri, bã bisa ɓarna da kallafãwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 284,
            "translated_text": "Lalle ne mubazzarai sun kasance 'yan'uwan shaiɗanu. Kuma Shaiɗan ya kasance ga Ubangijinsa, mai yawan kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Ko dai ka kau da kai daga gare su dõmin nẽman rahama daga Ubangijinka, wadda kake fãtanta, to sai ka gaya musu magana mai laushi."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Kuma kada ka sanya hannunka ƙuƙuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfiɗa shi dukan shimfiɗãwa har ka zama abin zargi, wanda ake yanke wa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kada ka zama marõwaci a zarge ka, kuma kada ka zama almubazzari ka rasa mutãne, su yanke daga gare ka."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Lalle ne Ubangijinka Yanã shimfiɗa arzĩki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntãwa. Lalle Shi, Yã kasance Mai sani ga bãyinSa, Mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Kuma kada ku kashe 'yã'yanku dõmin tsõron talauci. Mu ne ke arzũta su, su da ku. Lalle ne kashe su yã kasance kuskure babba."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kuma wanda aka kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Kuma kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce dai da sifa wadda take ita ce mafi kyau, har ya isa ga mafi ƙarfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari yã kasance abin tambayãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Kuma ku cika mũdu idan kun yi awo, kuma ku auna nauyi da sikẽli madaidaici. Wancan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Kuma kada ka yi tafiya a cikin ƙasa da alfahari. Lalle kai bã zã ka hũda ƙasa ba kuma bã zã ka kai a duwãtsu ba ga tsawo."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 285,
            "translated_text": "Dukan wancan mli mũninsa yã kasance abin ƙyãma a wurin Ubangijinka."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Wancan yãnã daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikima. Kuma kada ka sanya wani abin bautãwa na daban tãre da Allah har a jẽfa ka a cikin Jahannama kanã wanda ake zargi, wanda ake tunkuɗẽwa*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan shĩ ne ƙarshen muƙãrana tsakãnin shiryarwar da Alƙur'ãni ya kãwo wa dũniya da abin da Attaura ta kãwo wa Banĩ Isrã'ĩla. Kuma akwai daidatãwa a cikinsu a tsakãnin hãlãye mãsu kyau da kĩshiyõyinsu, watau hãlãye mãsu mũni."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Shin fa, Ubangijinku Ya zãɓe ku da ɗiya maza ne, kuma Ya riƙi 'ya'ya mãta daga malã'iku?* Lalle ne kũ, haƙĩƙa, kunã faɗar magana mai girma!<br \/>\n____________________<br \/>\n * Farkon muƙãrana a tsakãnin al'ãdun mushirikai da shiryarwar Alƙur'ãni dõmin gyãra tunãninsu ga karɓar ĩmãnin tauhĩdi."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarrafa bayãni a cikin wannan Alƙur'ãni dõmin su yi tunãni, kuma bã ya ƙãra musu kõme fãce gudu."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Ka ce: \"Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lõkacin, dã (abũbuwan bautãwar) sun nẽmi wata hanya* zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Dã su abõkan tãrayyar sun nemi hanya zuwa ga Allah dõmin su yãƙe shi sabõda Ya ce Al'arshi Tãsa ce, Shi kaɗai, dõmin su sãmi nãsu rabon, sabõda Al'arshi tã haɗiye kõme, har da su."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "TsarkinSa yã tabbata kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke faɗã, ɗaukaka mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sunã yi Masa tasbĩhi. Kuma bãbu wani abu fãce yanã tasbĩhi game da gõde Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Kuma idan ka karanta Alƙur'ani,* sai Mu sanya a tsakãninka da tsakanin waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira wani shãmaki mai suturcẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mushirikai jahilai ne, ba su iya ɗaukar jãyayyar magana, sabõda sun fi kusanta zuwa ga dabbõbi ga tunãninsu, bisa gare su zuwa ga mutãne, kõ da yake sauran jikinsu na mutãne ne. Sabõda haka a kõ yaushe sunã kusa ga faɗan tãyar da hankali da dõke-dõke. Sabõda haka Allah Ya sanya tsari ga AnnabinSa da wanda ya bi hanyar Annabin, wajen shiryar da mutãne game da karanta Alƙur'ãni. Bã zã su iya fãɗa mai karanta Alƙur'ãni da dũka ba, kuma tsõronsa suke ji dõmin kwarjinin Alƙur'ãni."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Kuma Mu sanya marufai a kan zukãtansu dõmin kada su fahimce shi, da, wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma idan ka ambaci Ubangijinka, a cikin Alƙur'ãni shĩ kaɗai, sai su jũya a kan bayayyakinsu dõmin gudu."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Mũ ne Mafi sani game da abin da suke saurãre da shi a lõkacin da suke yin saurãren zuwa gare ka, kuma a lõkacin da suke mãsu gãnãwa a tsakãninsu a lõkacin da azzãlumai suke cẽwa, \"Bã ku biyar kõwa fãce wani namiji sihirtacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Ka dũba yadda suka buga maka misãlai, sai suka ɓace bã su iya sãmun hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 286,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Shin, idan mun kasance ƙasũsuwa da, niƙaƙƙun gaɓãɓuwa ashe, lalle ne mũ haƙĩƙa, waɗanda ake tãyarwa ne a wata halitta sãbuwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 287,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku kasance duwãtsu ko kuwa baƙin ƙarfe.\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 287,
            "translated_text": "\"Kõ kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku.\" To zã su ce \"Wãne ne zai mayar da mu?\" Ka ce: \"Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lõkaci.\" To, zã su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sunã cẽwa, \"A yaushene shi?\" Ka ce: \"Akwai tsammãninsa ya kasance kusa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 287,
            "translated_text": "\"A rãnar da Yake kiran ku, sa'an nan ku riƙa karɓãwa game dã gõde Masa, kuma kunã zaton ba ku zauna ba fãce kaɗan.\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 287,
            "translated_text": "Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma* wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyananne.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ka ce wa bãyĩNa, mutãne, idan sunã magana su auna kalmõmin da suke zance da su, sa'an nan su riƙa amfãni da kalma mafi kyãwo dõmin kada shaiɗan ya sãmi mashiga daga maganarsu zuwa ga zukãtansu, ya sanya ɓarna a tsakãninsu."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 287,
            "translated_text": "Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so, zai yi muku rahama, kõ kuwa idan Yã so zai azabtãku. Kuma ba Mu aika ka kanã wakĩli a kansu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 287,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muƙãrana a tsakãnin Annabãwa. Allah Yã fĩfĩta waɗansu a kan waɗansu. Falalar Dãwũda a kan waɗansu Annabãwa da Zabũra ne to inã fĩfĩkon wanda aka bai wa Alƙur'ãni mafĩfĩcin littafi da sauran Annabãwa?."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 287,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku kirãyi waɗanda kuka riya, baicinSa.\" To, ba su mallakar kuranyẽwar cũta daga gare ku, kuma haka jũyarwa.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bã zã su iya jũyar da cũta daga gare ku zuwa ga wani ko kuwa daga wani zuwa gare ku ba."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 287,
            "translated_text": "Waɗancan, waɗanda suke kiran*, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sunã fãtan sãmun rahamarSa, kuma sunã tsõron azãbarSa. Lalle ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Waɗanda kãfirai ke neman tawassuli da su zuwa ga Allah, sũ ma sunã neman abin da zai sãdar da su zuwa ga Allah, sabõda haka bãbu bambanci a tsakãnin mai tawassuli da wanda ake tawassulin da shi ga kusanta zuwa ga Allah. Bãbu mai kusanta zuwa ga Allah sai da taƙawa ga ibãdarSa kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 287,
            "translated_text": "Kuma bãbu wata alƙarya fãce, Mu ne mãsu halaka ta a gabãnin Rãnar ¡iyãma kõ kuwa Mũ mãsu azãbta ta ne da azãba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littãfi rubũtacce."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 288,
            "translated_text": "Kuma bãbu abin da ya hana Mu, Mu aika da ãyõyi fãce sabõda mutãnen farko sun ƙaryata game da su. Kuma Mun bai wa Samũdãwa tãguwa, ãyã bayyananna, sai suka yi zãlunci game da ita. Kuma bã Mu aikãwa da ãyõyi fãce dõmin tsõratarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 288,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka ce maka, \"Lalle ne Ubangijinka Yã kẽwaye mutãne.\" Kuma ba Mu sanya abin da ya gani wanda* Muka nũna maka ba, fãce dõmin fitina ga mutãne, da itãciya wadda aka la'anta a cikin Alƙur'ani. Kuma Munã tsõratar da su, sa'an nan (tsõratarwar) bã ta ƙãra su fãce da kangara mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Abũbuwan da Annabi ya gani a daren Isrã'i da Mi'irãji, watau tafiyarsa zuwa sama wadda aka yi ishãrã da ita a farkon sũrar. Itãciyar da aka la'anta ita ce Zaƙƙũm abincin mutãnen Wuta. Akwai muƙãrana, a cikin wannan,cħwa ãyõyin da aka bai wa wani Annabi sun fi waɗanda aka bai wa wasu Annabãwa girma."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 288,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin* da Muka cẽ wa malã'iku, \"Ku yi sujada ga Ãdamu,\" sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa, ya ce: \"shin, zan yi sujada ga wanda ka** halitta shi yanã lãka?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da malã'iku da aljannu. An fĩfĩtar da jinsin mutum da sanya wa sauran jinsõshi biyu su yi masa sujada, sa'an nan aka ɗaukaka jinsin malã'ika sabõda ɗã'a, kuma aka la'anci jinsin Iblĩsa da sãɓo.  ** Rubũta \"ka\" da ƙaramin \"ka\" ne kõ da yake lamĩrin Allah ne, dõmin ya nuna hãlin maganar Shaiɗan zuwa ga Allah Mai girma. Yanã yin maganar da hushi, ba da girmamawa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 288,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin, kã gan ka*! Wannan wanda ka girmama a kaina, lalle ne idan ka jinkirtã mini zuwa ga Rãnar ¡iyãma lalle ne, zan tumɓuke zuriyarsa, fãce kaɗan.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mai sãɓõ sabõda hassada bã ya ganin girman Ubangijinsa. A cikin maganar Iblĩs akwai rashin ladabi da nũna ƙiyayya ga Ãdamu, har zuwa ga zuriyarsa, wadda ba a haifã ba tukuna."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 288,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ka tafi. Sa'an nan wanda ya bĩ ka daga gare su, to, Jahannama ce sakamakonku, (Mu ba ku shi) sakamako cikakke.\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 288,
            "translated_text": "\"Kuma ka rikitar da wanda ka sãmi ĩko a kansa, daga gare su, da sautinka, kuma ka yi hari a kansu da dawãkinka da dãkãrunka kuma ka yi tãrẽwa da su a cikin dũkiyõyi da ɗiyã, kumaka yi musu wa'adi. Alhãli kuwa Shaiɗan bã ya yi musu wa'adin kõme fãce da ruɗi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 288,
            "translated_text": "\"Lalle ne bãyiNa, bã ka da wani ƙarfi a kansu. Kuma Ubangijinka Ya isa Ya zama wakĩli.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 288,
            "translated_text": "Ubangijinku ne Yake gudãnar da jirgi a cikin tẽku, dõmin ku nema daga falalarSa. Lalle ne Shĩ, Yã kasance a gare ku Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 289,
            "translated_text": "Kuma idan cũta ta shãfe ku, a cikin tẽku, sai wanda kuke kira ya ɓace fãce Shi. To, a lõkacin da Ya tsira da ku zuwa, ga tudu sai kuka bijire. Kuma mutum ya kasance mai yawan butulci."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 289,
            "translated_text": "Shin fa kun amince cẽwa (Allah) bã Ya shãfe gẽfen ƙasa game da ku kõ kuwa Ya aika da iska mai tsakuwa a kanku, sa'an nan kuma bã zã ku sãmi wani wakĩli ba dõminku?"
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 289,
            "translated_text": "Ko kun amince ga Ya mayar da ku a cikin tẽkun a wani lõkaci na dabam, sa'an na Ya aika wata gũguwa mai karya abũbuwa daga iska, har ya nutsar da ku sabõda abin da kuka yi na kãfirci? Sa'an nan kuma bã ku sãmun mai bin hakki sabõda ku, a kanMu, game da Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 289,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Mun girmama 'yan Adam*, kuma Muka ɗauke su a cikin ƙasa da tẽku kuma Muka azurta su daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma Muka fĩfĩta su a kan mãsu yawa daga waɗanda Muka halitta, fĩfĩtãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da sauran halittar Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 289,
            "translated_text": "A rãnar da Muke kiran* kõwane mutãne da lĩmãminsu to, wanda aka bai wa littafinsa a dã, mansa, to, waɗannan sunã karãtun littãfinsu, kuma bã a zãluntar su da zaren bãkin gurtsin dabĩno.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Muƙãrana a Lãhira a tsakãnin al'ummõmi kuma da tsakãnin mũminai da kãfirai,."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 289,
            "translated_text": "Kuma wanda ya kasance makãho* a cikin wannan sabõda haka shi a Lãhira makãho ne kuma mafi ɓata ga hanya.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Muƙarana a tsakãnin makantar basĩra da makantar ganin ido."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 289,
            "translated_text": "Kuma lalle ne sun yi kusa haƙĩƙa, su fitinẽ ka daga abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, dõmin ka ƙirƙira waninsa a gare Mu, a lõkacin, haƙĩƙa, dã sun riƙe ka masoyi."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 289,
            "translated_text": "Kuma bã dõmin* Mun tabbatar da kai ba, lalle ne, haƙĩƙa, dã kã yi kusa ka karkata zuwa gare su ta wani abu kaɗan.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muƙãrana a tsakãnin sarauta da Manzancin Allah. Sarkin dũniya yanã canja manufarsa dõmin neman yardar mutãnensa. Amman Manzon Allah bã ya sãke abin da Allah Ya umurce shi da shi dõmin neman yardar mutãne."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 289,
            "translated_text": "A lõkacin, lalle ne, dã Mun ɗanɗana maka ninkin azãbar rãyuwa da ninkin azãbar mutuwa, sa'an nan kuma bã zã ka sãmi mataimaki ba a kanMu."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, sun* yi kusa, haƙĩƙa, su tãyar da hankalinka daga ƙasar, dõmin su fitar da kai daga gare ta. Kuma a lõkacin, bã zã su zauna ba a kan sãɓãninka fãce kaɗan.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Muƙãrana a tsakãnin mai aiki dõmin Allah, bã a iya jũyar da shi daga aikinsa dõmin neman wata kamãla, amma mai aikin dũniya anã iya canja shi dõmin haka. Kuma bambancin hijira da kõra waɗanda suka kõri Annabinsu sai a halaka su, amma waɗanda Annabinsu ya yi hijira gabãnin azãba, to, bã zã a halaka su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Hanyar waɗanda, haƙĩƙa, Muka aika a gabãninka, daga ManzanninMu, kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyarMu."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Ka tsayar da salla* a karkatar rãnã zuwa ga duhun dare da lõkacin fitar alfijir** lalle ne karãtun fitar alfijir ya kasance wanda ake halarta.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tsayar da salla a cikin lõkutanta, shi ne yake hana a yaudari mutum da magana har a sanya shi ya yi abin da bai kamãta ba, ko kuma ya yi abin da sharĩ'a ta hana. ** Karãtun fitar alfijir, ana nufin sallar asuba. Sabõda haka anã son dõgon karãtu a cikinta, gwargwadon fãrã ta a duhun dare a bayan fitar alfijir."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Kuma da dare, sai ka yi hĩra* da shi (Alƙur'ãni) akan ƙãri gare ka. Akwai tsammãnin Ubangijinka Ya tãyar da kai a wani matsayi gõdadde.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Hĩra da Alƙur'ãni, watau a yi sallõlin nãfila na dare, shafa'i bibbiyu, a ƙãre da wutri. Ga Annabi tahajjudi da wutrin wãjibi ne ƙãri a kan abin da aka ɗõra wa sauran mutãne, a lõkacin da yake zaune a gida. Ga sauran mutãne wutri sunna ce, kamar sallõlin ĩdi da rõkon ruwa da husũfin rãnã da na wata. A nan akwai bambanci a tsakãnin Annabi da jama'arsa a wajen wutri."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Kuma ka ce: \"Yã Ubangijĩna(5)! Ka shigar, da ni shigar gaskiya, kuma Ka fitar da ni fitar gaskiya. Kuma Ka sanya mini, daga gunKa, wani ƙarfi mai taimako.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Kuma ka yi addu'a a cikin sallarka da bãyanta da wannan addu'a dõmin ta nũna sallamãwarka ga Ubangijinka Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Kuma ka ce: \"Gaskiya tã zo, kuma ƙarya ta lãlãce. Lalle ne ƙarya ta kasance lãlãtacciya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Kuma Munã sassaukarwa daga Alƙur'ãni, abin da yake waraka ne da rahama ga mũminai. Kuma bã ya ƙãra wa azzãlumai (kõme) fãce hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Kuma idan Muka yi ni'ima a kan mutum,(6) sai ya hinjire, kuma ya nĩsanta da gefensa, kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya kasance mai yanke ƙauna.<br \/>\n____________________<br \/>\n(6) Muƙãrana a tsakãnin hãlãye biyu na mutum, hãlin tsanani da hãlin cũta."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Ka ce: \"Kõwa ya yi aiki a kan hanyarsa. Sa'an nan Ubangijinka ne Mafi sani ga wanda yake mafi shiryuwa ga hanya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Sunã tambayar ka ga rũhi. Ka ce: \"Rũhi daga al'amarin Ubangijina ne, kuma ba a bã ku (kõme) ba daga ilmi fãce kaɗan.\""
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 290,
            "translated_text": "Kuma lalle ne idan Mun so, haƙĩƙa, Munã tafiya da abinda Muka yi wahayi zuwa gare ka. Sa'an nan kuma bã za ka sãmi wani wakĩli ba dõminka game da shi a kanMu."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "Fãce da rahama daga Ubangijinka. Lalle ne falalarSa ta kasance mai girma a kanka."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance, mataimaki ga sãshi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun caccanza dõmin mutãne, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli sai mafi yawan mutãne suka ƙi (kõme) fãce kãfirci,"
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka sai kã ɓuɓɓugar* da idan ruwa daga ƙasa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kãfiri bã ya iya hangen abinda bã a iya taɓa shi da gaɓoɓin ji na jiki, dõmin haka suka nemi ɗayan waɗannan abũbuwa ya auku kãmin su yi ĩmãni. Mũmini yanã kange da ganin basĩra, dõmin haka ya wadãtu da zaman Alƙur'ani ãyã mai isa ga ya yi ĩmãni da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "\"Kõ kuma wata gõna daga dabĩnai da inabi ta kasance a gare ka. Sa'an nan ka ɓuɓɓugar da ƙõramu a tsakãninta ɓuɓɓugarwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "\"Kõ kuwa ka kãyar da sama a kanmu kaɓukka kõ kuwa ka zo da Allah, da malã'iku banga-banga.\""
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "\"Kõ kuwa wani gida na zĩnãriya ya kasance a gare ka, kõ kuwa ka tãka a cikin sama. Kuma bã zã mu yi ĩmãni ba ga tãkawarka, sai ka sassaukõ da wani littãfi a kanmu, munã karantã shi.\" Ka ce: \"Tsarki ya tabbata ga Ubangijĩna! Ban kasance ba fãce mutum, Manzo.\""
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni, a lõkacin da shiriya ta jẽ musu, fãce sunce, \"Shin, Allah zai aiko mutum ya zamo yana Manzo.\""
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "Ka ce: \"Dã malã'iku sun kasance a cikin ƙasa, kuma sunã tafiya, sunã masu natsuwa, lalle ne dã mun saukar da malã'ika daga sama ya zama manzo a kansu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 291,
            "translated_text": "Ka ce: \"Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da ku. Lalle Shi Ya kasance ga bãyinsa, mai ƙididdigewa ne Mai gani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 292,
            "translated_text": "Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne shiryayye, kuma wanda Ya ɓatar to bã zã ka sãmi waɗansu masõya gare su ba baicinSa. Kuma Munã tãra su a Rãnar ¡iyãma a kan fuskõkinsu, sunã makãfi, kuma bẽbãye da kurãme. Matattararsu Jahannama ce, kõ da yaushe ta bice, sai Mu ƙãra musu wata wuta mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 292,
            "translated_text": "Wancan ne sãkamakonsu sabõda lalle sũ, sun kãfirta da ãyõ yinMu, kuma suka ce: \"Shin idan muka kasance ƙasũsuwa da nĩƙaƙƙun gaɓũɓuwa, shin lalle mũ, haƙĩ ka, waɗanda ake tãyarwa ne a cikin wata halitta sãbuwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 292,
            "translated_text": "Shin, kuma ba su ganĩ* ba (cẽwa) lalle ne Allah, wandaYa halicci sammai da ƙasa, Mai ikon yi ne a kan Ya halicci misãlinsu? Kuma Ya sanya wani ajali wanda bãbu kõkwanto a cikinsa? Sai azzãlumai suka ƙi fãce kãfirci.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muƙãrana a tsakãnin farkon halitta da mayarwa da ita, idan fãrãwa ba ta buwãya ba, mayarwa bã zã ta buwãya ba."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 292,
            "translated_text": "Ka ce: \"Dã dai kũ, kunã mallakar* taskõkin rahamar Ubangijĩna, a lõkacin, haƙĩƙa dã kun kãme dõmin tsõron ƙãrẽwar taskõkin. Kuma mutum yã kasance mai ƙwauro ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muƙãrana a tsakãnin kyautar mutum da rõwarsa ga dũkiyar da ya mallaka."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 292,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun bai wa Mũsã ãyõyi* guda tara bayyanannu, sai ka tambayi Banĩ Isrã'ila, a lõkacin da ya jẽ musu, sai Fir'auna ya ce masa, \"Lalle nĩ, inã zaton ka, ya Mũsã, sihirtacce.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muƙãrana a tsakãnin maganar makangari Fir'auna da Manzon Allah, Mũsã dõmin nũna ãyar Annabãwa ba su tsõron kõwa wajen iyar da Manzancin Allah, kuma bã su ganin wani ƙarfi a gabansu fãce na Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 292,
            "translated_text": "Ya ce: \"lalle ne haƙĩƙa ka sani bãbu wanda ya saukar da waɗannan, fãce Ubangijin sammai da ƙasa dõmĩn su zama abũbuwan lũra. Kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, ina zaton ka, yã Fir'auna, halakakke.\""
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 292,
            "translated_text": "Sai ya yi nufin fitar da su daga ƙasar, sai Muka nutsar da shi, shi da wanda yake tãre da shi gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 292,
            "translated_text": "Kuma Muka ce: daga bãyansa ga Banĩ Isrã'ĩla, \"Ku zauni ƙasar. Sa'an nan idan wa'adin ƙarshe ya zo, zã Mu jẽ da ku jama'a-jama'a.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan magana tanã kamã da da'awar Yahũdu cewa yanã rubuce a cikin littãfinsu za su kõma haɗuwa bãyan rarraba a nan dũniya kuma Hadĩsin kõmawar Yahũdu a Falasɗĩnu, har Musulmi su yi yãƙi da su, sunã a kan gãɓar gabas kuma su Yahũdãwa suna a kan gãɓar yamma daga Kõgin Urdun yanã ƙarfafa wannan ra'ayi. Kuma an ruwaito cewa daga cikin alãmõmin Tãshin Ƙiyãma akwai kõmãwar Yahũdu a Falasɗinu. Allah ne Mafi sani."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Kuma da gaskiya Muka saukar da shi, kuma da gaskiya ya sauka. Kuma ba Mu aike ka ba fãce kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Kuma yanã abin karãtu Mun rarraba shi dõmin ka karanta shi ga mutane a kan jinkiri kuma Mun sassaukar da shi sassaukarwa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Saukar da Alƙur'ãni a cikin shekaru ashirin ko ashirin da uku ya yi kama da saukar ãyõyin Mũsã tãre a lõkacin da yake kiran Fir'auna zuwa ga addini."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku yi ĩmãni* da Shi, ko kuwa kada ku yi ĩmãni, lalle ne waɗanda aka bai wa ilmi daga gabãninsa, idan anã karãtunsa a kansu, sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu, sunã mãsu sujada.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Muƙãranar yin ĩmãni da rashin ĩmãnin mutãne ga Alƙur'ãni ba zai rage gaskiyarsa da kõme ba, sai dai waɗanda suka ƙi ĩmãnin ne zã su cũtu, sa'an nan da bambanci a tsakãnin mai ilmi da jãhili. Mai ilmi yanã da sauƙin jãwuwa zuwa ga gaskiya har ya rasa abin da zai aikata fãce ya fãɗi rikice, a kan haɓarsa, yanã mayar da al'amari ga Allah kuma yanã tawali'u."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "\"Kuma sunã cẽwa: Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle ne wa'adin Ubangijinmu ya kasance, haƙĩƙa, abin aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Kuma sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu sunã kũka, kuma yanã ƙara musu tsõro."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku kirayi Allah* kõ kuwa ku kirãyi Mai rahama. Kõwane kuka kira to Yanã da sũnãye mafi kyau. Kuma, kada ka bayyana** ga sallarka, kuma kada ka ɓõye ta. Ka nẽmi hanya a tsakãnin wancan.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Muƙarana a tsakãnin sũnayen Allah waɗanda ake kiran sa da su wajen rõƙo da waɗanda bã a yin roko da su. Sũnãyen mafiya kyau da ake kiran Allah da su Hadĩsi ya kãwo su sai a nħma daga Jalãlaini.** Kuma tsakaitãwa wajen karãtun salla ko addu'a kamar yadda aikin Annabi ya nũna yadda ake yi, kada a bayyana kada a ɓõye. Sai dai tsaka."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 17,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Kuma ka ce: \"Gõdiyã(5) ta tabbata ga Allah wanda bai riƙi ɗã ba kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa, kuma wani masõyi sabõda wulãkancin bai kasance a gare Shi ba.\" Kuma ka girmama Shi, girmamãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  (5) Ka ce: \"Allah ba Shi da abõkin muƙãrana a kõwace jiha. Shi kaɗai Ya cancanci girmamãwa.\" Sabõda haka ka girmama Shi, girmãmãwar da ta dãce da Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bãwansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata lãdã mai kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Sunã mãsu zama a cikinta har abada."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 293,
            "translated_text": "Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda(6) suka ce: \"Allah yanã da ɗa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n (6) Lãrabawa sun ce malã'iku 'ya'yan Allah ne. Yahũdawa sunce Uzairu ɗan Allah ne, Nasãra sun ce Ĩsã ɗan Allah ne. Bãbu ladabi ga faɗin wannan magana. Sabõda haka Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya gaya musu, cewa wannan magana ƙarya ce kuma rashin ladabi ne ga Allah, da ba su yi ĩmãni ba, ya ji tsõro kada ya zama shĩ ne ya yi ƙwauron bãki ga faɗã musu gaskiya. Sai Allah Ya gaya masa, cewa kada ya halakar da ransa dõmin baƙin cikin haka."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "To, kã yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai dõmin ba su yi ĩmãni da wannan lãbãri ba sabõda baƙin ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa* ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sabõda haka ƙawar ƙasa, kamar furen itãcenta ne, bã su ruɗin mai hankali ga tsarewar ladabi tãre da Ubangijinsa, da bin sharĩ'ar Littafin da aka saukar wa Annabi kuma ba a sanya masa karkata ba."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "Kuma lalle Mũ, Mãsu sanya abin da ke a kanta (ya zama) turɓãya ƙeƙasasshiya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo* da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Lõkacin da Allah Ya ce: \"kada Annabi ya wahalar da kansa dõmin baƙin cikin ba a karɓi maganarsa ba, sai Ya ba shi lãbãrin ma'abũta kõgo, yadda suka yi gudun hijira da addininsu, Allah Ya tsare su daga wahala, a cikin halin abin al'ajabi. Sa'an nan ƙissar ta tattara a kan ladubba waɗanda ake nħman Mutum ya tsare su tãre da Ubangijinsa a cikin dukan mõtsinsa, kamar yadda bayãni zai nũna."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: \"Ya Ubangijinmu*! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sun fara da addu'a ta nħman shiriya daga Allah, Ubangijinsu. Addu'a tun farko ga kõme ladabi ne. Kuma fãrãwa da nũna bautarsu ga Ubangiji, ladabi ne. Hijira da addini 1adabi ne, kuma amincewa da sãmun rahamar Allah, ladabi ne ga Allah, sabõda haka Allah ya jiɓinci tsaron kõgon ya zame musu mafi kyawun wurin zama."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "Sai Muka yi dũka a kan kunnunwansu,* a cikin kõgon, shẽkaru mãsu yawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Dũka a cikin kunnuwa, shĩ ne sanya musu barci."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "Sa'an nan Muka tãyar da su, dõmin Mu san wane ɗayan ƙungiyõyin biyu suka fi lissãfi ga abin da suka zauna na lõkacin."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "Mu ne ke jẽranta maka lãbãrinsu da gaskiya. Lalle ne sũ, waɗansu samãri ne. Sun yi ĩmãni da Ubangijinsu, kuma Muka ƙãra musu wata shiriya."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: \"Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi waninSa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare haddi a sa'an nan.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 294,
            "translated_text": "\"Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar)? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah?\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 295,
            "translated_text": "\"Kuma idan kun nĩsance su sũ da abin da suke bautãwa, fãce Allah, to, ku tattara zuwa ga kõgon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamarSa kuma Ya sauƙaƙe muku madõgara daga al'amarinku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 295,
            "translated_text": "Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare shi. Wannan abu yanã daga ãyõyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shĩ ne mai shiryuwa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmar masa wani majiɓinci mai shiryarwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 295,
            "translated_text": "Kuma kanã zaton su farkakku ne, alhãli kuwa sũ mãsu barci ne. Munã jũya su wajen dãma da wajen hagu, kuma karensu yanã shimfiɗe da zirã'õ'in ƙafãfuwansa ga farfãjiya (ta kõgon). Dã ka lẽka (a kan) su (dã) lalle ne, ka jũya daga gare su a guje kuma (dã) lalle ne ka cika da tsõro daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 295,
            "translated_text": "Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin* su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: \"Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?\" suka ce: \"Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini.\" Suka ce: \"Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin**. Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mahãwarar muminai a bãyan barcin shekara ɗari uku, amma duk da haka sunã cikin hankalinsu sunã mayar da al'amari ga Allah. ** Birnin shi ne Tarasus. Sunan sarƙinsu Daƙayãnus."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 295,
            "translated_text": "\"Lalle ne sũ idan sun kãmã ku, zã su jẽfẽ ku, kõ kuwa su mayar da ku a cikin addininsu kuma bã zã ku sãmi babban rabo, ba, a sa'an nan har abada.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 296,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su (gare su) dõmin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar al'amarinsu a tsakãninsu* sai suka ce: \"Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su.\" Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: \"Lalle mu riƙi masãllãci a kansu.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Muhãwarar mũminai da kãfirai, da yadda kãfirai ke zartar da al'amari bã da ambaton yardar Allah Ubangijinsu ba. Da yadda suke yin sãri-faɗi ga matsalõlin ilmi da ya kamãta a mayar da saninsu ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 296,
            "translated_text": "Zã su ce: \"Uku ne da na huɗunsu karensu.\"Kuma sunã cẽwa, \"Biyar ne da na shidansu karensu,\" a kan jĩfa a cikin duhu. Kuma sunã cẽwa, \"Bakwaine da na takwas ɗinsu karensu.\"Ka ce: \"Ubangijĩna* ne Mafi saniga ƙidãyarsu, bãbu wanda ya san su fãce kaɗan.\"Kada ka yi jãyayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa** ga kõwa daga gare su a cikin al'amarinsu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bayãnin ladubban magana ga matsalõlin ilmi da na aiki. Bãbu wanda ya san gaibu sai Allah. Bã a tambayar mãlaman ɓata da son zũciya, dõmin sãri-faɗi suke yi ga jawãbin mai tambaya.** Dõmin haka ba a yin fatawa a wurin mãlamin bidi'a kõ jãhili dõmin zai faɗi abin da yake so, kõ kuma ya yi ƙaddari faɗi, jĩfa a cikin duhu."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 296,
            "translated_text": "Kuma kada lalle ka ce ga wani abu, \"Lalle ni, mai aikatãwa ne ga wancan a gõbe.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 296,
            "translated_text": "Fãce idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: \"¦ammãni ga Ubangijĩna, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga wannan na shiriya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 296,
            "translated_text": "Kuma suka zauna a cikin kõgonsu shẽkaru ɗarĩ uku kuma suka daɗa tara."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 296,
            "translated_text": "Ka ce: \"Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shĩ ne da (sanin) gaibin sammai da ƙasa. Mũne ne ya yi ganinSa da jinSa! Bã su da wani majiɓinci baicinSa kuma bã Ya tãrayya da kõwa a cikin hukuncinsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 296,
            "translated_text": "Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littãfin Ubangijinka. Bãbu mai musanyãwa ga kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata madõgara ba daga waninsa."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 297,
            "translated_text": "Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa. Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar rãyuwar dũniya.* Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga hukuncinMu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ãyõyi na ashirin da bakwai da ashirin da takwas sunã umurni da bin shari'a ta Alƙur'ãni, kuma sunã hani daga bin son zũciya dõmin nħman ƙawar rãyuwar dũniya wadda aka yi dõmin a jarrabi wãwã da ita, sa'an nan ta kõma turɓãya ƙeƙasasshiya. Dũbi ãya kuma, ta takwas da ta tara. Mun dai sani, cewa umurni da bin sharĩ'a bayyananna shĩ ne kan labarin sũrar."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 297,
            "translated_text": "Kuma ka ce: \"Gaskiya daga Ubangijinku take.\" Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 297,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai lalle ne Mũ bã Mu tõzartar da lãdar wanda ya kyautata aiki."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 297,
            "translated_text": "Waɗannan sunã da gidãjen Aljannar zama, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, anã sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar waɗansu tũfãfi kõre, na alharĩni raƙĩƙi da alharini mai kauri sunã kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 297,
            "translated_text": "Kuma ka buga musu misãli* da waɗansu maza biyu. Mun sanya wa ɗayansu gõnaki biyu na inabõbi, kuma Muka kẽwayesu da itãcen dabĩnai, kuma Muka sanya shũka a tsakãninsu (sũ gõnakin).<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Misãli ga mai shagala da dũniya da ƙawarta, mai saurin kõmãwa turɓaya ƙeƙasasshiya, da maĩ bin umurnin Allah, mai ladabi da bin sharĩ'a. Yadda aƙibar kõwanensu zã ta kasance."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 297,
            "translated_text": "Kõwace gõna daga biyun, tã bãyar da amfãninta, kuma ba ta yi zãluncin kõme ba daga gare shi. Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙoramu a tsakãninsu."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 297,
            "translated_text": "Kuma ɗan ĩtãce ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abõkinsa, alhali kuwa yanã muhãwara da shi, \"Nĩ ne mafĩfĩci daga gare ka a wajen dũkiya, kuma mafi izza a wajen jama'a.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "Kuma ya shiga gõnarsa, alhãli yanã mai zãlunci ga kansa, ya ce: \"Bã ni zaton wannan zã ta halaka har abada.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "\"Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "Abõkinsa ya ce masa, alhãli kuwa yanã muhãwara da shi, \"Ashe kã kãfirta da wanda Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum?\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "\"Amma ni, shĩ ne Allah Ubangijina, kuma bã zan tãra kõwa da Ubangijina ba\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "\"Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "\"To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turɓãya mai santsi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "\"Kõ kuma ruwanta ya wãyi gari faƙaƙƙe, sabõda haka, bã zã ka iya nẽmo shi ba dõminta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, \"Kaitõna, dã dai ban tãra* wani da Ubangijina ba!\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ya yi nadãmar halakar gõnar kawai, amma bai yi nadãmar kãfircin shirkin da ya yi ba, sabõda haka Allah bai mayar masa da badalinta ba. Daga nan kuma anã fahimtar cewa rashin mai da al'amari ga Allah shirku ne, kuma girman kai sabõda dũkiya, shirku ne wanda ƙawar dũniya ke sanya wãwãye a ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "Kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, waɗanda ke taimakon sa, baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "A can taimako da jiɓinta ga Allah yake. Shĩ ne kawai Gaskiya, shĩ ne Mafĩfĩci ga lãda kumaMafĩ fĩci ga ãƙiba."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 298,
            "translated_text": "Ka buga musu misãlin rãyuwar dũniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirin ƙasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wãyi gari dudduga, iska tanã shiƙar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ĩkon yi ne a kan dukan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 299,
            "translated_text": "Dũkiya da ɗiya,* sũ ne ƙawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Dũkiya da ɗiya, ƙawar dũniya ne, idan suka zama abin alfahari ga mai su, amma idan an ciyar da dũkiya ga tafarkin Allah, kuma aka karantar da ɗiya ga bisa tafarkin hanyar sharĩ'a suka tãshi Musulmin ƙwarai, to, sun zama aikin sharĩ'a na Lãhira kħ nan."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 299,
            "translated_text": "Kuma a rãnar da Muke tafiyar da duwãtsu, kuma ka ga ƙasa bayyane, kuma Mu tãra su har ba Mu bar kõwa ba daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 299,
            "translated_text": "Kuma a gittã* su ga Ubangijinka sunã sahu guda, (Mu ce musu), \"Lalle ne haƙĩƙa kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lõkaci. Ã'a, kun riya cẽwa bã zã Mu sanya mukuwani lõkacin haɗuwa ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bayãnin abũbuwan da ke aukuwa a wurin hisãbi ke nan ga mãsu bin son zũciya, su bar sharĩ'a."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 299,
            "translated_text": "Kuma aka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa \"Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta?\" Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 299,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, \"Ku yi sujada ga Ãdamu.\" Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa, su zama majiɓinta baicin Ni, alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzãlumai.**<br \/>\n____________________<br \/>\n  ** Allah Shĩ ne Ya halitta mutãne, kuma Ya ɗaukaka darajarsu, dõmin Yã sanya malã'iku su yi sujada ga ubansu Ãdamu. Sabõda wannan sõyayyar kuma Ya bã su sharĩ'ar da zã su bi su shiryu har su shiga Aljanna, amma sai suka ƙi, suka kõma wa Shaiɗan wanda yake shi ne farkon maƙiyin ubansu, Ãdamu, wanda ya ƙi yi wa sujada, har aka la'ane shi, sunã bin sa, shi da ɗiyansa, alhãli kuwa bãbu wani abin da zã su iya yi musu na alheri ko na sharri, dõmin sũ ma halitta ne kamarsu. Bã su san kõme ba a sama kõ a ƙasa, kuma Allah bã Ya yin ma'amalar kõme da su. Wanda ya bi Shaiɗan ya bar Allah, to, yã yi mugunyar musanya, kuma yã zãlunci kansa ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 299,
            "translated_text": "Ban shaida musu halittar sammai da ƙasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar rãyukansu ba kuma ban kasance mai riƙon mãsu ɓatarwa (da wani) su zama mataimaka ba."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 299,
            "translated_text": "Kuma da rãnar da Allah Yake cẽwa, \"Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, waɗanda kuka riya.\" Sai su kirãye su, sai bã zã su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa* (Mahalaka) a tsakãninsu,<br \/>\n____________________<br \/>\n* Maubiƙã sũnan wani rãfi ne na wuta, asalinsa daga 'Wabiƙa,' wãtau yã halaka. Za a sanya wannan rãfi a tsakãnin mãsu bin Shaiɗan da sũrõrin gumãka, da wanda ya shirya musu gumãkan, sunã bauta musu."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 299,
            "translated_text": "Kuma mãsu laifi suka ga wutã suka tabbata lalle ne, sũ mãsu, auka mata ne, kuma ba su sãmi majũya ba daga gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 300,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin misãli ga mutãne (dõmin su gãne, su bi sharĩ'a), kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Jidãli, shĩ ne jãyayya, alhãli kuwa mutum yã san yanã kanƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 300,
            "translated_text": "Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko* ta je musu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i-nau'i.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hanyar farko ita ce Allah Ya halaka su sabõda laifinsu kõ kuma azãba ta je musu nau'i-nau'i, dõmin su musulunta sai ƙarshe idan sun ƙi a halaka su. Waɗansu sun fassara 'ƙubala' ko 'ƙibala' da ta fuskance su bayyane, bisa ga karãtun kalmar 'ƙibala' da wasalin ƙasa, da ma'anar azaba."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 300,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jidãli da ƙarya dõmin su ɓãta gaskiya da ita, kuma suka riƙi ãyõyiNa da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 300,
            "translated_text": "Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar game da ãyõyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar? Lalle ne Mũ, Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya, to, bã zã su shiryu ba, a sa'an nan, har abada."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 300,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau ba su da wata makõma su bar wannan lõkacin alkawarin saukar azãbar."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 300,
            "translated_text": "Kuma waɗancan alƙaryu* Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka(5) su.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Alƙaryun Ãdãwa da samũdãwa da waɗansunsu. (5) Kõme Allah Zai yi, sai Yã sanya masa lõkacin aukuwarsa, kuma bã zai aukun ba sai ajalin nan da Ya ambata masa ya zo."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 300,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Mũsã(6) ya ce wa yãronsa, \"Bã zan gushe ba sai na isa mahaɗar tẽku biyu, kõ in shũɗe da tafiya shekara da shẽkaru.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   (6) Shĩ ne MũSã bn Imrãn Manzon Banĩ Isrã'ĩla. Sababin wannan ƙissa, an tambaye shi ne, \"Wãne ne ya fi ilmi a saninsa?\" Sai ya ce: \"Shĩ ne ya fi. Wannan jawãbi nãsa gaskiya ne, dõmin shĩ ne Manzon zãmaninsa, shĩ ne aka bai wa Attaura, kuma Allah Ya yi magana da shi, sai dai ya mance bai ce Allah Ya fi sani ba, dõmin haka aka ce masa ya tafi neman ilmi ga wani mutum a magamar teku biyu. Wannan bãwan Allah Haliru ne. Yãron Mũsã kuwa, shĩ ne Yũsha'u bn Nũn, Manzon Allah a bãyan Mũsã. Kĩfin kuma na guzurinsu ne wanda Allah Ya umurce shi ya ɗauka, sõyayye, kuma aka ce musu duka inda yai rai, to, a nan ne Bãwan Allah yake, mai shirin ƙãra wa Mũsã ilmi. Mayar da ilmi ga Allah, shĩ ne ladabin shari'a."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 300,
            "translated_text": "To, a lõkacin da suka isa mahaɗar tsakãninsu sai suka manta kĩfinsu, sai ya kãma tafarkinsa a cikin tẽku kamar bĩga."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "To, a lõkacin da suka wuce ya ce wa yãronsa, \"Ka kãwo mana kãlãcinmu. Lalle ne haƙĩƙa mun haɗu da wahala daga tafiyarmu wannan.\""
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "(Yãron) ya ce: \"Kã gani! A lõkacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle nĩ, na manta kĩfin, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaiɗan, dõmin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin tẽku, da mãmãki!\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Ya ce: \"Wancan ne abin da muka kasance munã biɗã.\" Sai suka kõma a kan gurãbunsu, sunã bĩbiya."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyinMu, Mun bã shi wata rahama* daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gunMu.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Rahama a nan ita ce Annabci sabõda cħwa kuma an bã shi ilmi daga gun Allah, kuma ya yi hukunci da shi. Ilmin ilhãma bã a yin hukunci da shi dõmin Annabãwa kawai Allah Ya tsare daga kuskure game da wahayi. Wannan ne bambanci bayyananne a tsakanin wahayin Annabci da wahayin walicci. Haka mu'ijiza da karãma, su duka sãɓãwar al'ada ne, amma mu'ujizar Annabi an san zã ta zo daga bãkin wanda aka yi dõminsa, amma karãma bãbu mai saninta, sai tã auku. Sabõda waliyyi bã ya iya yin tãkara, amma annabi yana iya yin tãkara a kan maƙiyansa."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Mũsã ya ce masa, \"Ko in bĩ ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ, ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "\"Kuma yãya zã ka yi haƙuri a kan abin da ba ka kẽwayeda shi ba ga jarrabãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Ya ce: \"Za ka sãme ni, in Allah Yã so mai haƙuri kuma bã zan sãɓa maka ba ga wani umurni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Ya ce: \"To idan ka bĩ ni to kada ka tambaye ni daga kõme sai na lãbarta maka ambato* daga gare shi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau sai na gaya maka hukuncinsa da kaina, kuma na ambace shi da kaina."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Sai suka tafi har a lõkacin da suka hau a cikin jirgi, ya hũje shi, ya ce, \"Kã hũje shi dõmin ya nutsar da mutãnensa? Lalle ne, haƙĩƙa, kã zo da wani babban abu!\""
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ashe ban ce, lalle kai, bã za ka iya yin haƙuri tãre da ni ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kada ka kãma ni da abin da na manta kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al'amarĩna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 301,
            "translated_text": "Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: \"Ashe kã kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne haƙĩƙa ka zo da wani abu na ƙyãma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 302,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin, ban ce maka ba, lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 302,
            "translated_text": "Ya ce: \"Idan na tambaye* ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mũsã ya kãsa yin haƙuri a bãyan ya yi alkawura cewa zai yi haƙuri, sabõda ba yã halatta ga mutum ya ga abin da ya sãɓa wa shari'a, sa'an nan ya yi shiru. Dã zai halatta a yi shiru, dã Mũsã bai yi magana ba ga aikin mãlamin da Allah Ya umurce shi da ya tafi ya karɓo ilmi daga gare shi, a bãyan Yã gaya masa cewa,Yã bã shi wani ilmi daga gare shi. Dõmin sharaɗin da ya sãɓa wa shari'a warwararre ne. Sabõda haka Allah bai zargi Mũsa ba a bayan sun rabu. Sake al-munkar wãjibi ne a cikin ladubban shari'a gwargwadon hãli, kamar yadda yake a cikin Hadĩsi. Ana gabãtar da hukuncin da ya fi tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 302,
            "translated_text": "Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alƙarya, suka nẽmi mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai (Halliru) ya tãyar da shi mĩƙe. (Mũsã) ya ce: \"Dã kã so, lalle ne dã kã karɓi ijãra a kansa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 302,
            "translated_text": "Ya ce: \"Wannan shi ne rabuwar tsakanina da tsakaninka. Zã ni gaya maka fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 302,
            "translated_text": "\"Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne sunã aiki* a cikin tẽku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã karɓẽwar kõwane jirgi (lãfiyayye) da ƙwãce.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau wani kamfani ne na matalauta, sunã sana'ar ɗaukar kãya a cikin teku, sharika watau kamfani ciniki ya halatta da sharuɗɗansa."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 302,
            "translated_text": "\"Kuma amma yaron, to, uwãyensa sun kasance mũminai, to, sai muka ji tsõron ya kallafa musu kangara da kãfirci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 302,
            "translated_text": "\"Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu mafi alhẽri daga gare shi ga tsarkakuwa, kuma mafi kusantar tausayi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 302,
            "translated_text": "\"Kuma amma bangon, to, yã kasance na waɗansu yãra biyu ne, marãyu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tãsu a ƙarƙashinsa, kuma ubansu ya kasance sahĩhin mutum* ne, dõmin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyãkar ƙarfinsu, kuma sũ, su fitar da taskarsu, sabõda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnĩna. Wancan shĩ ne fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ya nũna cewa kirkin uba yanã amfãnin ɗiyansa, haka gari na daraja sabõda sãmun mutãnen kirki a cikinsa, kamar yadda yake ƙasƙanta da ƙasƙancin mazaunansa bisa dalĩlin da farko an kira garin 'alƙarya' sabõda rõwar mazauna, kuma aka kira shi Madĩna sabõda darajar yãran nan biyu da ubansu da taskarsu. Alƙarya ita ce ƙaramin gari watau ƙauye, kuma Madĩna ita ce babban gari."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 302,
            "translated_text": "Kuma suna tambayar ka daga zulƙarnaini*, ka ce: \"Zan karanta muku ambato daga gare shi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Zulƙarnaini an ce sarki ne yanã bin shari'ar lbrãhĩm, ga hannunsa ya musulunta sunansa Askandar. Haliru wazirin sane yanã tafiya a gaban yãƙinsa, kuma ɗan innarsa, watau ɗan khãlarsa ne. Shi ne ya gĩna Askandariyya. Sai dai ga maganar akwai warware jũna. Allah Ya sani. Abin da ke a gabãninmu a nan shĩ ne sanin cħwa Allah Yã bã shi mulki, ya kõ yi shĩ bisa sharĩ'a, ya yi ƙarfi, da ƙarfin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Lalle ne Mũ Mun bã shi mulki a cikin ƙasa kuma Muka bã shi daga kõwane abu, hanya (zuwa ga murãdinsa)."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Sai ya bi hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Har a lõkacin da ya isa ga mafãɗar rãnã, kuma ya sãme ta tanã ɓacẽwa a cikin wani ruwa mai baƙar lãkã, kuma ya sãmi waɗansu mutãne a wurinta. Muka ce: \"Yã Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatãwa a cikinsu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Ya ce: \"Amma wanda ya yi zãlunci, to zã mu azabta shi, sa'an nan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa, sai kuma Ya yi masa azãba, azãba abar ƙyãma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "\"Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau*, kuma zã mu gaya masa sauƙi daga umurninmu.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kyauta mai kyau a nan ba Aljanna ba ce, dõmin maganar ta Zulƙarnaini ce idan ya ci ƙasa, yanã iya sanya mãsu ĩmãninta a cikin hãli mai kyau. Amma idan an ɗauki maganar, ta Allah ce, a cikin maganar Zulƙarnaini ga kãfiri, to, a nan 'mai kyau' sai ta zama Aljanna ke nan."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma ya bi hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Har a lõkacin da ya isa ga mafitar rãnã, ya sãme ta tanã fita a kan waɗansu mutãne (waɗanda) ba Mu sanya musu wata kãriya ba daga barinta."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Kamar wancan alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun kẽwaye da jarrabãwa ga abin da ke gunsa."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma ya bi hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi waɗansu mutãne daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Ya ce: \"Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhẽri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "\"Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe\". (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen) ya ce: \"Ku hũra (da zugãzugai).\" Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: \"Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 303,
            "translated_text": "Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya hujẽwa gare shi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Ya ce: \"Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin* Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wa'adin Ubangiji da fitõwar Yãjũj da Mãjũj. A yanzu bãbu wanda ya san inda suke zaune, sai Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan, yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin ƙaho sai muka tãra su, tãrãwa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Ya nũna yadda hãlin da Zulƙarnaini ya bar Yãjũj da Mãjũj, watau sun garwaya a cikin jũnansu, sa'an nan kuma wannan ma'anar aka bãyar da ita ga mutãne waɗanda ke bin son ransu, bã su bin shari'ar Allah, sunã hargitse a tsakãninsu, har a yi bũsar farko, su mutu, kuma a yi bũsa ta biyu su tãshi a cikin hargitsinsu, sai kuma a gitta Jahannama gaba gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Kuma Muka gitta Jahannama, a rãnar nan ga kãfirai gittãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Waɗanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunã* Ni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Zikr- tunãwa- shi ne Alƙur'ãni da abin da ya tãra na ibãda da sauran ma'ãmalõli, dukansu ibãda ne, matuƙar an bi abin da Allah Ya ajiye a cikinsu na hukunce-hukunce."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bãyĩNa*, majiɓinta baiciNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Waɗanda suka riƙi wasu bãyin Allah, sunã bauta musu, kamar Yahũdu mãsu bauta wa Uzairu da Nasãra mãsu bautawa Ĩsã da wasu Musulmi mãsu bauta wa wasu sãlihai sun zama kãfirai. Ma'anar bautawar shi ne su ƙirƙira wasu hukunce-hakunce kõ wasu sifõfi waɗanda suka sãɓa wa maganar Alƙur'ãni da Hadĩsi, sa'an nan su jingina su zuwa ga waɗannan bãyin Allah, su bi su da su."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Ka ce: \"Kõ mu gaya muku game da mafĩfita hasãra ga ayyuka?\""
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "\"Waɗanda aikinsu ya ɓace a cikin rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sunã zaton lalle ne sũ, sunã kyautata, (abin da suke gani) aikin ƙwarai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓãci. Sabõda haka bã zã Mu tsayar musu da awo(5) ba a Rãnar ¡iyãma.<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Watau ko aunawa bã zã a yi ba balle a daidaita ma'auni."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Wancan ne sakamakonsu shĩ ne Jahannama, sabõda kãfircinsu, kuma suka riƙi ãyõyiNa da ManzanniNa abin izgili."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyãfa a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Suna madawwama a cikinta, bã su nẽman makarkata daga barinta."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Ka ce: \"Dã tẽku(6) ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   (6) Ma'anar ãyar nan ita ce Allah ne Mafi sani. llmin Allah bã shi da iyãka, kõ kalmõmin da suka ɗauki ma'anõninsa, bã zã a iya rubuta su ba, balle ma'anõnin da ke cikinsu. Sabõda haka abin da ke hankali a mutum, shĩ ne ya yi aiki da ɗan ilmin da Allah Ya umurce shi da aiki dashi. Idan ya nemi ya wuce nan, to, ya halakar da kansa dõmin bai san inda zai fãɗa ba. Wannan ilmin shi ne sharĩ'a da aiki da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 18,
            "page_number": 304,
            "translated_text": "Ka ce: \"Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa.\"(7)<br \/>\n____________________<br \/>\n (7) Wannan ãya, a dunƙule, ta tãra dukan abin da ke cikin sũrar. Allah Ya shiryar da mu, ga kaɗaita shi ga ibãda, da yin ibadar, kuma yadda Allah Ya ce a yĩ ta, ga mai tsammãnin rabo a Lãhira. Wanda ba ya tsammãnin rabon Lãhira, ya tsaya ga dũniya mai gushħwa da sauri, to, shĩ bã a shiga batunsa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "K̃.H. Y.I. Ṣ̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "\"Kuma lalle nĩ, na ji tsõron* dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Amfãnin sãmu ɗã ga mutumin kirki shi ne dõmin ya gãji kirkin kuma ya taimaki sauran danginsa, ya rãyar da gida. Kuma wanda ba mutumin kirki ba yana yiwuwa ya sãmi ɗan kirki mai shiryar da shi zuwa ga hanyar ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "\"Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "(Allah Ya karɓa) \"Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma.\" Ya ce: \"Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 305,
            "translated_text": "Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, \"Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Yã Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Yahaya an zakariyya, shi neAnnabi da aka bai wa hukunci tun yanã yãro. Kuma Shĩ ne mai bãyar da bushãra da Ĩsa, amincin Allah ya tabbata agare su."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci Maryamu* a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * An fãra da ƙissar Maryamu dõmin a nũna sakamakon da aka yi mata da sãmun ɗan kirki sabõda kasancewarta mutumiyar kirki, kuma da nũna cewa Annabi Ĩsa bã ɗan Allah ba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Ta ce: \"Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Ya ce: \"Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Ta ce: \"A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi* ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Malã'ikin da ya je ga Maryama a cikin sũrar mutum jibrĩlu ne Yã hũra a cikin wuyan rĩgarta, sai ta yi ciki da Ĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce \"Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "Sai (yãron da ta haifa) ya* kira ta daga ƙarƙashinta, \"Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Annabi Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya fãra magana ga uwarsa tun a lõkacin da aka haife shi yanã a ƙarƙashin uwarsa. Gudãnar ruwan marmaro a ƙarƙashinta da fitar da 'ya'yan dabĩno dagakututturen dabĩno, alãmu ne mãsu nũna cħwa Allah nã iya halitta jãrĩri bã da uba ba, kuma Yanã tãyar da matattu daga kabarinsu bã da wata wahala ba."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 306,
            "translated_text": "\"Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "\"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki*. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Jin sanyi ga idãnu shĩ ne farin cikin sabõda sãmun haihuwa. Ga ibãdar Banĩ lsrã'ĩla, mai azumi bã ya yin magana, amma ga Musulunci Allah Ya shãfe wannan hukunci. Mai azumi yanã magana sai dai anã son ya kãma bãkinsa daga maganar da bã ta ibãda ba."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: \"Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!"
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "\"Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: \"Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ita ce maganar da Ĩsa ya yi wa mutãnen uwarsa dõmin ya barrantar da ita daga tuhuma, kuma ya nũna matsayinsa ga Allah da muƙãminsa na Annabci."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "\"Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "\"Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "\"Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã*. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, \"Kasance.\" Sai ya dinga kasan cẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ba ya kasancewa ga Allah Ya riƙi ɗã, dõmin bã Ya mutuwa balle Ya yi bukãtar mai gãdo ga tsaron dũkiya. Shi kaɗai ne, bã Ya bukãtar wani ɗã mai tsaron dangi dõmin kada su bar hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "\"Kuma lalle Allah ne Ubangijina* kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tana a cikin maganar Ĩsã a lõkacin da ya girma yana wa'azi ga mutãnensa, sabõda haka aka raba ta da maganar farko a lõkacin da yake jãrĩri."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "Sai ƙungiyõyin(5) suka sãɓã wa jũna a tsakãninsu. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Bãyan ɗauke Annabin Allah Ĩsã ɗan Maryama ƙungiyõyin mutãne sun sãɓa wa jũnansu a cikin sha'aninsa. Yahũdu suna sũkar sa, Nasãra suka kasu uku: Nasũriyya suka ce: \"Shi ɗan Allah ne\" Malakaniyya suka ce: \"Shi ne na uku ɗin uku,\" Ya'aƙũbiyya suka ce: \"Shi ne Allah.\" Sabõda haka Nasara sukahaihaye kuma suka zurfafa, sa'an nan Yahũdu suka taƙaita kuma suka yi sũka gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 307,
            "translated_text": "Mẽne ne ya yi jinsu(6), kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna.<br \/>\n____________________<br \/>\n (6) A rãnar Lãhira a lõkacin da ake yi musu hisãbi a gaban Allah ganinsu da jinsu sunã da kyau ƙwarai, amma a nan dũniya sunã a cikin makanta da kurumci sabõda ɓatar da suka yi, suka ƙaryata Ĩsã, aminci ya tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa* da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su.<br \/>\n____________________<br \/>\n *Tun da yake Mũ ke gãdon ƙasa da wanda yake a cikinta,bã zã Mu yi bukãtar sãmun wani magãji ba."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "Kuma ambaci Ibrãhĩm* a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ibrãhĩm ya yi ƙõƙarin shiryar da ubansa, sai dai Allah bainufi shiryuwarsa ba. Daga cikin amfãnin haihuwa akwai abin haihuwa ya shiryar da mahaifinsa, ya yi masa nasĩha gwargwadon hãli."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "A lõkacin da ya ce wa ubansa, \"Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka?\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "\"Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici.\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "\"Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓãwa ga Mai rahama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "\"Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan.\""
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "Ya ce: \"Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka.* Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ibrãhĩm yã mayar da magana mai kyau da laushi da aminci ga maganar ubansa mai mũni da gautsi da tsõratarwa. Wannan yanã kõyar da yadda ake kira zuwa ga Allah da kuma yadda ya kamãta a tausasa wa uba kõ dã shi kãfiri ne."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "\"Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "Kuma Muka yi musu kyauta daga RahamarMu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya* maɗaukaki.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Harshen gaskiya, shi ne yabo mai kyau daga Allah da mutãne. Wanda ya yankewa mutãnenSa dõmin Allah, to, zai sãka masa da waɗansu mutãnen kirki dõmin su ɗebe masa kewa."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 308,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Kuma Muka yi masa kyauta daga RahamarMu da ɗan'uwansa Hãrũna, ya zama Annabi."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens *da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Mãtarsa da 'ya'yansa da Jurhum, yanã umurninsu da salla da zakka. Yanã wajaba ga mutum ya umurci iyalinsa da tsare haƙƙõƙin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Sai waɗansu 'yan bãya* suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * An ruwaito cewa wannan zai auku a lõkacin Tãshin Ƙiyãma ne a bãyan tafiyar sãlihan wannan al'umma ta Muhammadu. Zã su dinga barbarar jũnansu a cikin hanyõyi. Su tõzarta salla, su gina manyan gidãje su hau dukan abin da aka hana su, su tufanci abin da aka hana su, Ƙurɗabi."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "Wancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 309,
            "translated_text": "(Sunã mãsu cẽwa) \"Kuma bã mu sauka* Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan.\" Kuma** (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * 'Yan Aljanna sunã cewa ba mu sauka a waɗannan gidãje ba sai da umurnin Ubangijinka, kai mai karatu, A1lahne Mai mallakar kõme, kuma kõme ãyã ne mai nũni zuwa gare shi, sabõda haka bã a mantãwa da shi. ** Maganar Allah ce a bãyan maganar 'yan Aljanna dõmin ta'aƙĩbi da ƙãrin bayãni ga maganarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautarsa. Shin kã san wani takwara a gare shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Kuma mutum yana cẽwa, \"Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "To, Munã rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗanda suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata.* Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Idan an tãra mutãne dõmin hisabi, anã ajiye wuta a tsakãnin mutãne da Aljanna, Sa'annan a gitta sirãɗi a cikan wutar dõmin mutãne su bi akansa su ƙetare wutar zuwa Aljanna kuma waɗansu su fãɗa a cikin wutar dõmin azãba dawwamamma kõ kuma ta ɗan lõkaci gwargwadon laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, \"Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kãyan ɗãki na jin dãɗi kamar gadãje da kujeri da kãyan cin abinci. Magãnã kuwa ita ce wurin da ake ganĩ ga mutum kamar tufãfinsa da sũrar jikinsa da dukan abin gani daga gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna!\""
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 310,
            "translated_text": "Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: \"Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Kuma suka riƙi gumãka,* baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Gunki, shi ne dukan abin bautawa wanda bã Allah ba. Wanda ya riƙi wani sãlihi ko malã'iki ko aljani, yanã bauta masa, to, yã riƙe shi gunki ke nan. Bauta ita ce bin umurni da barin hani. Wanda ya bi umurnin da bã na Allah ba, kõ ya bar abin banin da ba na Allah ba, to, ya bauta wa mai umurnin ko mai hanin, yã riƙe shi gunki baicin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu* a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Idan shaiɗanu sun ga mai wa'azin gaskiya, sai su dinga shũshũta mabiyansu dõmin su yi faɗa da mai wa'azin, dõmin kada su saurare shi har su gãne ɓatarsu. Shaidan shi ne mai ɓatar da wani, mutum ne kõ aljani."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar ajali ne kawai, ƙidãyãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Ba su malakar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Mai rahama Yã riƙi ã!\""
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 311,
            "translated_text": "Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wanda ya bi Allah da gaskiya, Allah zai sanya zukãtan mutãne su sõ shi kamar yadda yake a cikin Hadisi wanda Imãm Tirmizi ya ruwaito daga sa'ad da Abu Huraira."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 19,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu?"
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "¦.H."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Mai rahama, Ya daidaita* a kan Al'arshi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Allah Ya daidaitu a kan Al'arshi daidaita wadda ta dãce da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka?"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, \"Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, \"Ya Mũsã!\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 312,
            "translated_text": "\"Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka* Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * An ce wa Mũsã ya ɗebe takalmansa dõmin sunã da najasa kõ kuwa sũ kansu najasa ne dõmin ya shiga wuri mai tsarki wanda ake kira Ɗuwa a cikin sahãrar Sina'i a tsakãnin Masar da Madyana.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci* na dabam a gare ta.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Amfãnõnin sanda: Anã riƙon alkĩbla a cikin daji ta zama sitra, anã dõgara a kanta sabõda gajiya kõ rauni. Lĩmãmin Juma'a na dõgara a kanta a lõkacin huɗuba anã fita da ita a cikin ruwan sama anã dõgara a kanta, anã dũkan iyãli da ita dõmin ladabtarwa. A cikin wani Hadĩsi Annabi ya ce: \"Ka rãtaye sandarka inda iyãlinka suke ganin ta.\" Riƙon sanda na sanya farkawa gabarin dũniya, watau mai ita ya zama a cikin hãlin tafiya."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyinMu manya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai).\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya Ubangiji! Ka buɗa* mini, ƙirjĩna.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ma'anar buɗa ƙirji, shine a sanya masa haƙuri.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "kuma ka sawwake mun Al'amari na"
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Su fahimci maganãta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Hãrũna ɗan'uwana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Ka ƙarfafa halittata da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Dõmin mu tsarkake Ka da yawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Kuma mu tuna Ka da yawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã!\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 313,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "\"A lõkacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "\"Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a kan ganiNa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "\"A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi* kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã Mũsã!<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Idon ta ya yi sanyi, watau ta ji dãɗi sabõda ganin ɗanta.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "\"Kuma Na zãɓe ka dõmin Kaina.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "\"Ka tafi kai da ɗan'uwanka game da ãyõyiNa, kuma kada ku yi rauni ga ambatõNa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "\"Ku tafi kũ biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (ga girman kai).\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "\"Sai ku gaya masa magana mai laushi,* tsammãninsa yanã tunãwa kõ kuwa ya ji tsõro.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan shĩ ne dalilin umurni da alheri da hani daga sharri, kuma a yi haka da maganamai laushi ga wanda yake da iko da ƙarfi. Kõ dã ga wanda Allah Ya tsare da tsarinsa ne, balle ga wanda bai tãki kõme ba. Ta haka ne mai wa'azi ke cin nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "Su biyu suka ce: \"Ya Ubangijinmu! Lalle ne munã tsõron ya yi gaggawa a kanmu, kõ ya ƙẽtare haddi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kada ku ji tsõro. Lalle Nĩ, Inã tãre da ku, Inaji, kuma Inã gani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "\"Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "\"Lalle mũ, haƙĩƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cẽwaazãba tanã a kan wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "Ya ce: \"To, wãne ne Ubangijinku? Ya Mũsã!\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ubangijinmu Shi ne wanda Ya bai wa dukan kõme halittarsa, sa'an nan Ya shiryar.\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 314,
            "translated_text": "Ya ce: \"To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko?\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Ya ce: \"Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "\"Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama.\" Sa'an nan game da shi* Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ruwan."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Daga gare ta* Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ƙasa."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyinMu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya!"
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã?\""
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "\"To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Ya ce: \"Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Mũsã ya ce musu, \"Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe.\""
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãninsu kuma suka asirta gãnawa."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku* game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ya fara da siyãsa dõmin ya karkatar da hankalin mutãne daga ãyõyin Allah. Cewarsa yãyi nufin ya fitar da ku daga ƙasarku, shĩ ne siyãsa dõmin idan mutãne suka ji maganar fitarwa daga ƙasa, sai su manta da kõwace irin magana tawani alheri."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 315,
            "translated_text": "\"Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ã'a, ku jẽfa.\" Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Muka ce: \"Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "\"Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Sai aka jẽfar da masihirtan sunã mãsu sujada, suka ce: \"Mun yi ĩmãni da Ubangijin Hãrũna da Mũsã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa, babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno, kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar (azãba).\""
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Suka ce: \"Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa, ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "\"Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kumaMafi wanzuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Lalle* shĩ wanda ya je wa Ubangijinsa yanã mai laifi, to lalle ne yanã da Jahannama, bã ya mutuwa a cikinta kuma bã ya rãyuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Ãyã ta 74 da ta 75 maganar Allah ce dõmin ƙarin bayãni a kan maganar masihirta a bãyan sun musulunta."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Kuma wanda ya je Masa yanã mai ĩmãni, alhãli kuwaya aikata aikin ƙwarai to waɗannan sunã da darajõji maɗaukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 316,
            "translated_text": "Gidãjen Aljannar zama kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, \"Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riskuwa, kuma bã ka fargabar nutsẽwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya rufe su."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar (dasu) ba."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har hushĩNa ya sauka a kanku. Kuma wanda hushĩNa ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "\"Kuma mẽne ne ya gaggautar* da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã!\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Mũsã ya zãɓi mutun sabã'in daga Banĩ Isrã'ĩla, dõmin su tafi wurin Mĩƙãti tãre, su ji maganar Ubangiji. A lõkacin da ya yi kusa, sai ya yi gaggãwa dõmin bege. Kõ kuwa a bãyan azumin kwãna arba'in ya tafi a wurin Mĩƙãtin, Allah Ya fãra yi masa magana game da mutãnensa dõmin ɗebe masa kewa. Sai ya karɓa da cewa, \"Sunã nan a kan sãwũna.\" Wãtau sunã nan a kan abin da na ɗõra su a kansa na addini da aƙĩda ta tauhĩdi. Sai Allah Ya ce masa \"A'aha! sun musanya addininka da bautar maraƙi.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Ya ce: \"Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda.\""
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Ya ce: \"To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su.\""
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: \"Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna?\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 317,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ba mu sãɓa wa alkawarinka* ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Alõkacin da Banĩ Isrã'ĩla zãsu fita daga Masar sun yi aron mundãyen mutãnen Masar dõmin su nũna cewa biki suke yi, bã gudu zã su yi ba, dõmin kada a bĩ su da wuri waɗannan mundãyen ne sãmiri ya tãra a bãyan tafiyar Mũsã zuwa ga Mĩƙãtin Ubangijinsa ya ƙera musu maraƙi mai jiki irin na mutãne da sauti irin na shãnu dõmin yã yi masa magudãnar iska a cikin cikinsa idan iskar ta fito, sai a jĩ ta da sauti kamar sautin kũkan shãnu. Kuma shi maraƙin bã ya dã wani rai, bã ya mõtsi, sai dai ƙũgin kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "\"Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, \"Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umurnĩna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "Suka ce ba zamu gushe ba muna bauta a gareshi ba har sai Musa dawo<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Lazimta a kan bautawa maraƙin akwai wahala a cikinta dõmin haka aka kãwo wannan ƙissa sabõda a nũna cewa bautar Allah bãbu lazimta da wahala a cikinta duk abin da yake da wahala a cikinsa, bã addinin Allah ba ne. Akwai ĩ'itikãfi a cikin Musulunci wanda mafi yawansa kwãna gõma ne a cikin masallaci. Mutãnen Sãmiri ne suka fãra ibãda da kiɗa da rawa da wãƙã a cikin wurin ibãdarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "(Mũsã) ya ce: \"Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace.\""
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "\"Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umurnina ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "(Hãrũna) ya ce: \"Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "(Mũsã) ya ce: \"Mẽne ne babban al'amarinka? Ya Sãmiri!\""
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "(Sãmiri) ya ce: \"Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini.\""
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "(Mũsã) ya ce: \"To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi,* sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mũsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya ƙõne maraƙin ya sheke shi a cikin ruwan teku ya nũna ĩkon maraƙin ga kãre kansa daga wata cũta kuma da ƙarancinsa a cikin teku wadda take ɗaya ce daga cikin abũbuwan ĩkon Allah da suke iya gani, da lãlãcewar ibãdar mãsu bauta wa wanin Allah, a bãyan wahalarsu mai yawa ta lazimta a kansa."
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 318,
            "translated_text": "Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci* dukkan kõme da ilmi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Allah Ya yalwaci dukan kõme da sani, watau Yanã aikata kõme da ilminsa kuma Yanã umurni da bauta Masa da ilmi, wanda Ya aiki Manzanninsa da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Kamar wancan ne Muke lãbartãwa* a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gunMu.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Yã kãwo ƙãrin bayãni game da wannan ƙissa a cikin ãyõyin da ke tafe daga nan yadda bin addinin Allah yake da sauƙi a cikin lõkaci gajere na dũniya kawai a cikin taƙaitaccen lõkaci, da kuma wuyar bautawa wani ga ɗaukar kãya mãsu nauyi a dũniya da Lãhira, a cikin dõgon lõkaci."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanãɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) \"Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, \"Ba ku zauna ba fãce a yini guda.\""
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu* sai ka ce: \"Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa,<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Ana siffanta duwãtsu maɗaukaka da ayyukan dũniya waɗanda bã ibãdar Allah ba, watau al'adu da ibãdõjin da ba ibãdar Allah ba, dukansu kõme yawansu zã su lãlãce a rãnar da Mai kira, wãtau lsrãfĩl, zai bũsa ƙaho na kiran mutãne zuwa ga Tãshin Ƙiyãma, kira wanda bãbu makarkata daga gare shi, watau bã kamar kiran da Annabãwa suka yi ba, wanda waɗansu mutãne suka karkace daga gare shi a nan dũniya."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "\"Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da magan*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Bãbu ceto ga kõwa sai wanda Allah Mai rahama Ya yi masa iznin da yin ceton, ga wanda aka yi iznin sabõda shi, kuma izni anã yin sa ne da maganar Allah, ba da wata ishãra ba."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Yanã sanin* abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Ya san kõme ga halittunsa, su kuwa bã su iya kewayewa da sanin kõme game da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye, Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa."
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 319,
            "translated_text": "Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa* da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: \"Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Allah Ya umurci Annabi da ya bar gaggãwar karatun Alƙur'ãni a lõkacin da ake yin wahayinsa zuwa gare shi, dõmin kada ya wahala dõmin sũrar tanã karantar da cewa addinin Musulunci sauƙi ne, bai zo dõmin ya wahalar ba. Kuma tsõron yin kuskure yanã sanya yin kuskure mai jãwo wahala kamar yadda Ãdamu ya yi gaggãwar ga tsoron umurnin Allah, sai ya yi mantuwa, ya yi abin da aka hana shi har masifa ta sãmu aka fitar da shi daga Aljanna."
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shiba."
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, \"Ku yi sujada ga Ãdamu.\" Sai suka yi sujada, fãce Iblĩsa, yã ƙiya."
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Sai Muka ce: \"Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi* ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Anã farkar da ɗiyan Ãdamu ga maƙiyin ubansu wanda ya sabbaba musu wahalar zuwa dũniya da haɗuwa da taklĩfi a cikinta. Kuma bin wannan taklĩfi yanã zame masa sauƙi idan sun bĩ shi yadda Allah Ya ce: amma idan sun bi hanyar Shaiɗan, maƙiyinsu, to, bãbu abin da zai sãmu a gare su fãce ƙãrin wahala daga dũniya har Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Lalle ne kã sãmu bã zã ka ji yunwa ba a cikinta, kuma bã zã ka yi tsiraici ba."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "\"Lalle kai, bã zã ka ji ƙishirwa ba, kuma bã zã ka shiga hantsi ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: \"Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace."
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi)."
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala.\""
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "\"Kuma wanda ya bijire* daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wanda ya bijire daga ãyõyin Allah, shĩ ne kãfirin da bai yarda da shiga Musulunci ba."
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 320,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya Ubangiji! Don me Ka tãyar da ni makãho alhãli kuwa nã kasance mai gani?\""
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kamar wancan ne ãyõyinMu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita,* kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wanda ya yawaita, shi ne Musulmi fãsiƙi kõ mai bidi'a yanã ƙara abin da ba a sani ba a cikin addini, ya yawaita shi. Shi ma ya shiga a cikin wahalar dũniya. Kuma ta Lãhira ta fi tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda (kãfirai) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula."
        },
        {
            "ayah_number": 129,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta."
        },
        {
            "ayah_number": 130,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Sai ka yi haƙuri* a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Haƙuri da riƙe ibãda ta sallõli da tasibĩhi a lõkutanta farilla da na nafila shi ne maganin izgilin mãsu izgili. Tasbĩhi da gõde wa Allah a gabanin fitõwar rãnã ga sallar Asuba, a gabanin ɓacewarta ga La'asar, a sã'õ'in dare ga Lisha, da gefukan rãna ga Azahar."
        },
        {
            "ayah_number": 131,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikinsa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 132,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 133,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa?\" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 134,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: \"Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu!\""
        },
        {
            "ayah_number": 135,
            "surah_number": 20,
            "page_number": 321,
            "translated_text": "Ka ce: \"Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Hisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) \"Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Ã'a, suka ce: \"Yãye-yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato* idan kun kasance ba ku sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ma'abũta ambato, watau mutãnen da aka bai wa littattafan sama: Yahũdu da Nasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mãsu yawaitãwa, sũ ne mãsu wuce haddõdin Allah ga Kõme, fãsiƙai da mãsu bidi'õ'i."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 322,
            "translated_text": "Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku,* a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Al'ummar Muhammad, tsirar Allah da amincinsa su tabbata a gare shi. An saukar musu da Alƙur'ãni, a cikinsa akwai ɗaukakarsu da darajarsu, dõmin wanda aka ambata, to, an ɗaukaka shi."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Sai a lõkacin da suka hangi azãbarMu, sai gã su sunã gudu daga gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "\"Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Suka ce: \"Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun* riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Abin wãsã, shi ne mãtã, kõɗã, kõ wani abin da ake shagaltuwa da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurinSa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdarSa. kuma bã su gajiya."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Sunã tasbĩhi dare da rãnã, bã su yin rauni."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Kõ (kãfirai) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa ne ga ƙasã, su ne mãsu tãyarwa (gare su)?"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Bã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 323,
            "translated_text": "Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: \"Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa \"Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Mai rahama ya riƙi ɗã.\" Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, (malã'iku) bãyi ne mãsu daraja."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõronSa."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Kuma wanda ya ce daga gare su, \"Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa,\" to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke,* sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Abin wãsã, shi ne mãtã, kõɗã, Kõ wani abin da ake shagaltuwa da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhãli kuwa su daga ãyõyinta mãsu bijirẽwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu* a cikin wani sarari suKe iyo.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan yã nũna cewa rãnã da watã a cikin sarari guda suke, Kõ da yake akwai nĩsan gaske a tsakãninsu."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama?"
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 324,
            "translated_text": "Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 325,
            "translated_text": "Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cẽwa), \"Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?\" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta* ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sun kasance sunã aibanta wanda yake musun gumãkansu alhãli kuwa sũ, sunã musun zaman Allah Mai rahama ya kasance abin bautãwa guda. Wannan shi ne gãyar jãhilci."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 325,
            "translated_text": "An halitta mutum daga gaggãwa, zan nũna muku ãyõyiNa. Sabõda haka kada ku nẽmiyin gaggãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 325,
            "translated_text": "Kuma sunã cẽwa, \"A yaushe wannan wa'adi zai tabbata, idan kun kasance mãsu gaskiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 325,
            "translated_text": "Dã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu, kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 325,
            "translated_text": "Ã'a, tanã jẽ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa'an nan bã su iya mayar da ita, kuma ba su zama anã yi musu jinkiri ba."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 325,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 325,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wãne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?\" Ã'a, sũ mãsu bijirẽwa ne daga ambaton Ubangijinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 325,
            "translated_text": "Ko kuwa sunã da waɗansu abũbuwan bautãwa waɗanda ke tsare su, daga gare Mu? Bã su iya taimakon kansu kuma ba su kasance anã abũtar su* ba daga gareMu.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Bã su iya sãmun wani abõki wanda zai tsare su daga azãbarMu. Kuma wanda bai tsarekansa ba yãya zaĩ iya tsare wani?."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 325,
            "translated_text": "Ã'a, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni'imarMu, har rãyuwa ta yi tsawo a kansu. Shin, to, bã su ganin cẽwa lalle Mũ, Munã je wa ƙasarsu, Munã rage* ta daga sãsanninta? Shin, to, su ne marinjaya?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Munã rage ƙasarsu daga sãsanninta, watau mutãnen da ke bin su ga ɓatarsu kullum sunã raguwa, sunã shiga Musulunci, Musulunci na ƙãruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Ka ce: \"Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi,\" kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cẽwa, \"Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Waɗanda suke tsãron Ubangijinsu a fake, alhãli kuwa sũ, mãsu sauna ne daga Sa'a."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Ya ce wa ubansa da mutanensa, \"Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Suka ce: \"Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Suka ce: \"Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãSu wãsã ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 326,
            "translated_text": "\"Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Sai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Suka ce: \"Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Suka ce: \"Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm.\""
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Suka ce: \"To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida.\""
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Suka ce: \"Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!\""
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: \"Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) \"Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah?\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "\"Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta?\""
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Muka ce: \"Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 327,
            "translated_text": "Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 328,
            "translated_text": "Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 328,
            "translated_text": "Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 328,
            "translated_text": "Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 328,
            "translated_text": "Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 328,
            "translated_text": "Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 328,
            "translated_text": "Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 328,
            "translated_text": "Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar)* ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Asalin mats'alar, tumãkin wani mutum suka yi kĩwon ɓarna a gõnar wani a cikin dare alhãli kuwa anã kallafa wa mai dabbõbi ya kange dabbõbinsa da dare kamar yadda ake kallafa wa mai shũka da tsare shũkarsa a cikin yini. Sai Dãwũdu ya yi hukunci da cewa mai shũkar ya mallaki tumakin, shi kuma mai tumãki ya mallaki shũkar ɓãtacciya. Sai Sulaimãn ya gyãra hukuncin da cħwa mai gõna ya riƙi tumãkin ya rãyu a kansu har a lõkacin da mai dabbõbin ya gyãra masa gonarsa har ta Koma yadda take a farKon lõkacin,sa'an nan ya mayar da tumãkin ya karɓi gõnarsa. A cikin ƙissar akwai nũnin cewa Annabãwa bã su saunar faɗin gaskiya, sabõda wani mutum duk yadda yake, kuma anã warware hukunci idan kuskure ya auku a ciki, kuma Annabãwa sunã yin kuskure ga abin da bai shãfi wahayiba. Kuma kõmãwa ga askiya idan tã bayyana wajibi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 328,
            "translated_text": "Kuma Muka sanar da shi sana'ar* wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan yanã nũna wajabcin yin sana'a wadda mutum ke rãyuwa a kanta. Kuma yanã nũna wajabcin aiki da sabubba dõmin neman tsaron kai. Bã ya halatta ga mutum ya yi kwance bãbu sanã'ar da zai tsayu a kanta Kõ kuma ya gĩtta kansa ga halaka da tãwilin tawakkali. Tawakkali shĩ ne mayar da ãƙibar al'amura ga Allah a bãyan mutum ya yi abinda yake iya yi."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 328,
            "translated_text": "Kuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 329,
            "translated_text": "Kuma daga Shaiɗannu (Mun hõre) wanda ke nutso sabõda shi. Kuma sunã yin wani aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Mãsu tsaro a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 329,
            "translated_text": "Kuma da Ayyũba a sã'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) \"Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 329,
            "translated_text": "Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurinMu da tunãtarwa* ga mãsu ibãda.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ayyuba Manzon Allah, an jarrabe shi da wahalõlĩ ga jikinsa da halakar ɗiyansa ya yi haƙuri da hukuncin Allah, sai Allah Ya mayar masa da abin da ya halaka, sa'an nankuma ya ƙãrã masa wani kamarsa, dõmin rahamarSa ga mãsu mayar da al'amari a gare shi, da kuma wa'azi ga mãsuibãda dõmin kada aukuwar wata masĩfa ta sanya su kãtsewa da rashin ɗaukar haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 329,
            "translated_text": "Kuma da Ismãĩla da Idrĩsa da Zulkifli, dukansu sunã daga mãsu haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 329,
            "translated_text": "Kuma Muka shigar da su a cikin rahamarMu. Lalle ne, sunã daga sãlihai."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 329,
            "translated_text": "Kuma mai kifi* a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, \"Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Shĩ ne Yũnus bn Matta. Yãyi hushi da mutãnensa dõmin ba su karɓi addini ba, sai ya bar su tun a gabãnin a yi masa iznin barinsu. Sai Allah Ya jarrabe shi da fãɗãwã cikin ruwa har wani kĩfi ya haɗiye Shi, sa'an nan kuma ya amãyo Shi a bãyan wahala, ya kõma wa mutãnensa. Suka yĩ ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 329,
            "translated_text": "Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 329,
            "translated_text": "Kuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirãyi Ubangijinsa cẽwa, \"Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãdo.\""
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 329,
            "translated_text": "Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata* masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar (aikata sãɓo) gare Mu.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãyan mãtarsa ta tsũfa ba ta haihu ba Allah Ya kyautata mahaifarta, ta sãmi cikin Yahaya daga gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu.* Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Rũhin Allah a nan, shi ne Malã'ika jibrĩla. Shĩ ne ya hũra a cikin wuyan rĩgarta, sai ta yi cikĩ da Ĩsã. Maryamu bã Annabiya ba ce, an ambace ta ne dõmin shimfiɗa ga maganar Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare Shi. Zamanta ãyã shi ne ta sãmi ɗã bãda namiji ba, kuma wanda ya yi haƙuri ga tsaron haddojin Allah, Allah zai ɗaukaka shi da ni'imar dũniya da ta Lãhira. Ɗanta ya zama ãyã sabõda magana yana yãro, da Annabci da ɗaukar haƙuri ga zartar da umurnin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Lalle ne wannan* ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Al'ummar Musulmi duka guda ce kõ da yake Annabãwansu sun zo dabam-dabam, a cikin lõkuta mãsu nĩSa tsakãninsu da harsuna dabam-dabam dõmin duk aƙĩdarsu guda ce a kan Ubangiji guda ne. Sa'an nan daga bãya waɗanda suka fita daga wannan aƙĩdar suka rarrabu ƙungiya-ƙungiya."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Kuma suka kakkãtse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni"
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), \"Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!\""
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "(A ce musu) \"Lalle ne, kũ da abin* da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bãyin Allah sãlihai da malãiku waɗanda waɗansu mutãne suka bauta musu da tsammãnin cewa zã su cecesu daga Allah, bã zai sanya su Wuta ba sabõda ibãdar da aka yi musu, dõmin yabon Allah yã rigãyi hushinsa zuwa gare su. Bãyansu da mai bautar da wanda ake bautawar kamar gumãka da waɗansunsu, Wuta za su shiga."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne."
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 330,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã'iku na yi musu marãba (sunã cẽwa) \"Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa'adi da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon* halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Tun da fãrãwa bai buwãye Mu ba mayarwa ba za ta buwãye Mu ba. A Rãnar Ƙiyãma ake naɗe sama kan abin da yake a cikinta kamar yadda ake naɗe takarda a kan abin da ta ƙunsa na rubutun malã'iku a kan bãyin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato* (Lauhul Mahfũz) cẽwa ƙasã, bayĩNa sãlihai, sunã gãdonta.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Allah Yanã mallakar da ƙasa bãyinsa sãlihai, bã zã ta fita daga gare su ba sai idan sun musanya addininsu na ƙwarai da wani mugu."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "Lalle ne a cikin wannan (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta gabãta* ga waɗansu mutãne mãsu ibãda.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Ita ce cewar, Allah sãlihai sunã gadon ƙasa."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "Ka ce: \"Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: \"Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci?\""
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "\"Lalle ne Shĩ (Allah) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "\"Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 21,
            "page_number": 331,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 332,
            "translated_text": "Yã ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar* ƙasa ta tsayuwar Sa'a wata aba ce mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Addĩni tsantsa shĩ ne ke sanya ƙafa ta tsaya da kyau. Idan an cũɗanya addĩni da wasu abũbuwa na bidi'a kõ al'ãdu, to, ƙafa bã ta iya tsayi balle ma a lõkacin girgizar ƙasã ta tsayin Sa'a."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 332,
            "translated_text": "A rãnar da kuke ganin ta dukan mai shãyar da mãma tanã shagala daga abin da ta shãyar, kuma dukan mai ciki tanã haihuwar cikinta, kuma kanã ganin mutãne sunã mãsu mãyẽ alhãli kuwa su bã mãsu mãye ba, amma azãbar Allah ce mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 332,
            "translated_text": "Akwai daga mutãne* wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bã da wani ilmi ba, kuma yanã biyar kõwane Shaiɗan mai taurin kai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * An raba mutãne a game da addĩni kashi huɗu, sa'annan ya fãra da kashi na farko mafi yawa daga cikin sauran kasũsuwan, watau kashin wãwãye mãsu biyar Shaiɗan ga al'ãdu da son zũciyõyi su bar hukunce-hakuncen Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 332,
            "translated_text": "An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azãbar sa'ĩr."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 332,
            "translated_text": "Ya ku mutãne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tãshin ¡iyãma, to, lalle ne Mũ, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudãjin jini, sa'an nan kuma daga taõka wadda ake halittãwa da wadda ba a halittawa dõmin, Mu bayyana muku. Kuma Munã tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Munã fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan kuma dõmin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rãyuwa dõmin kada ya san kõme a bãyan ya sani. Kuma kanã ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kõwane nau'i mai ban sha'awa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "Wancan ne dõmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake rãyar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Sa'ar Tãshin ¡iyãma mai zuwa ce, bãbu shakka a cikinta kuma lalle ne Allah Yanã tãyar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "Kuma daga mutãne akwai mai yin musu* ga Allah bã da wani ilmi ba kuma bã da wata shiriya ba, kuma bã da wani littãfi mai haskakãwa ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kashi na biyu shi ne mũgun malami ko Shaiɗan mai ƙõƙarin ɓatar da mabiyansa wãwãye."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "Yanã mai karkatar da sãshensa dõmin ya ɓatar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yanã da wani wulãkanci a dũniya, kuma Munã ɗanɗana masa azãbar gõbara a Rãnar ¡iyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "(A ce masa): \"Wancan azaba sabõda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah bai zama Mai zãlunci ga bãyinSa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "Kuma daga mutãne akwai mai bauta* wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani alhẽri ya sãme shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta sãme shi, sai ya jũya bãya a kan fuskarsa. Yã yi hasãrar dũniya da Lãhira. Waccan ita ce hasãra bayyananna.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kashi na uku shi ne munãfuki mai shiga addĩni da biyu."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "Yanã kiran baicin Allah, abin da bã ya cũtarsa da abin da bã ya amfãninsa! waccan ita ce ɓata mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "Yanã kiran wanda yake lalle cũtarwarsa ce mafi kusa daga amfãninsa! Lalle ne, tir da shi ya zama majiɓinci, kuma tir da ya zama abõkin zama!"
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "Lalle ne Allah Yanã shigar da waɗanda suka yi ĩmãni* kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake nufi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kashi na huɗu sũ ne mũminai waɗanda suke tsõron Allah, su tsaya a inda Yatsayar da su. Su ne mafi ƙarancin kashi ga uku na farko."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 333,
            "translated_text": "Wanda ya kasance yanã zaton cẽwa Allah bã zai taimake shi* ba a cikin dũniya da Lãhira to sai ya mĩƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an nan ya dũba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wanda yake zaton Allah bã zai taimaki Annabinsa ba kuma yanã jin hushin Allah Ya zãɓi Muhammadu da Annabci, to, sai ya mutu da hushinsa,kuma ya yi dukan kaidin da yake so ya yi, Allah bã zai fãsa abin da Ya yi nufi ba a game da Annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 334,
            "translated_text": "Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur'ãni) yanã ãyõyi bayyanannu. Kuma lalle ne Allah Yanã shiryar da wanda Yake nufi."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 334,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda suka tũba* (Yahũdu) da waɗanda suka karkace (Saba'ãwa) da Nasãra da Majũsãwa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Ranãr ¡iyãma. Lalle ne Allah Mahalarci ne a kan dukkan kõme.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Anã ce wa Yahũdãwa 'waɗanda suka tũba,' dõmin sun sãɓã wa maganar Annabinsu,Mũsã, wanda ya ce wa Allah,\"Mun tũba zuwa gare Ka.\" Saba'ãwa su ne mãsu bauta wa malã'iku daga cikin Lãrabãwa ko Yahũdãwa. Nasãra sũ ne waɗanda suka bi Annabi Ĩsa Ɗan Maryamu, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Majũsãwa sũ ne mãsu bautã wa wuta da irin addinin Fãrisa. Mãsu shirki, su ne mãsu bauta wa, gumãka kõ aljannu kõ waɗansu mutãne, wãtau irin addinin Lãrabãwa na lõkacin Jãhiliyya da irin bautar da waɗansu Musulmi ke yi wa waliyyai a yanzu."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 334,
            "translated_text": "Ashe, ba ka gani ba, lalle Allah, wanda yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasa yanã yin sujada a gare shi, da kuma rãna da watã da taurãri da duwãtsu da itãce da dabbõbi, da kuma mãsu yawa daga mutãne? Kuma waɗansu mãsu yawa azãba tã tabbata a kansu. Kuma wanda Allah Ya wulãkantar, to, bã ya da wani mai girmamãwa. Kuma Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake so."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 334,
            "translated_text": "waɗannan ƙungiyõyi biyu* ne mãsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kãfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, anã zuba tafasasshen ruwa daga bisa kãwunansu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kuma ya kasa mutãne ƙungiya biyu, ƙungiyar farko sũne mãsu bin addinin gaskiya, ƙungiya ta biyu sũ ne mãsu karkace wa addinin gaskiya, kamar kasũsuwa uku na farko. A kõ da yaushe akwai husũma a tsakãnin ƙungiyoyin biyu. Sa'an nan ya ambaci sakamakon ƙungiyar ƙarya ta farkon,."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 334,
            "translated_text": "Da shĩ ake narkar da abin da yake a cikin cikunansu da fãtun jikinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 334,
            "translated_text": "Kuma sunã da waɗansu gwalmõmin dũka na baƙin ƙarfe."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 334,
            "translated_text": "A kõyaushe suka yi nufin fita daga gare ta, daga baƙin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu) \"Ku ɗanɗani azãbar gõbara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 334,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah Yana shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, anã ƙawãta su, a cikinsu, da waɗansu mundãye na zĩnãri da lu'u-lu'u. Kuma tufãfinsu a cikinsu alharĩni ne.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sakamakon ƙungiya ta gaskiya, wãtau muminai."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 335,
            "translated_text": "Kuma an shiryar da su zuwa ga mai kyau na zance kuma an shiryar da su zuwa ga, hanyar wanda ake gode wa."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 335,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta kuma suka taushe (mutãne) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutãne alhãli kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar* da gaskiya a cikinsa da zãlunci zã Mu ɗanɗana masa daga wata azãba mai raɗadi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ilhãdi, shĩ ne yin ibãda bã yadda Allah Ya yi umurni da a yi ta ba. Wanda ya yi nufin karkatar da gaskiyar ibãda a cikin hurumin Makka, Allah zai yi masa azãba mai tsanani,balle fa a ce mutum ya aikata. Sabõda haka yanã wajaba ga mai nufin zuwa Hajji ya kõyi yadda ake yin ibãda kãfinya tafi Makka dõmin kada ya jãwo wa kansa halaka."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 335,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka iyãkance* wa Ibrãhim wurin ¦akin (Muka ce masa), \"Kada ka haɗa kõme da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake ¦ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu tsayuwa da mãsu ruku'u da mãsu sujada.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah Ya nũna wa Ibrahĩm iyãkar Ɗãkin Ka'aba da iska, sa'an nan ya fãra ginashi, kuma Ya nuna masa iyãkõkin Hurumin Makka, ya sanya alãmõmi."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 335,
            "translated_text": "\"Kuma ka yi yẽkuwa ga mutãne da wajabcin Hajji su je maka suna mãsu tafiya da ƙafãfu da kuma a kan kõwane maɗankwarin rãƙumi mãsu zuwa daga kõwane rango mai zurfi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 335,
            "translated_text": "\"Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu sabõda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbõbin jin dãɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 335,
            "translated_text": "\"Sa'an nan kuma sai su ƙãre ibãdarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawãfi (sunã gẽwaya) ga ¦ãkin nin 'yantacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 335,
            "translated_text": "Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbõbin ni'ima* fãce abin da ake karantãwa a kanku. Sabõda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumãka kuma ku nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Dabbõbin ni'ima, sũ ne raƙumai da shãnu da tumãki da awãki. An halatta cinsu sai waɗanda suka mutu a gabãnin a yanka. Kuma shaidar zur kamar bauta wa gumãka take wajen sabbaba azãba, dõmin anã halattar da haram kõ aharamtar da halat game da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 336,
            "translated_text": "Kuna mãsu tsayuwa ga gaskiya dõmin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yanã kamar abin da ya fãɗo daga sama, sa'an nan tsuntsãye su cafe shi, ko iska ta fãɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 336,
            "translated_text": "Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita (girmamãwar) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 336,
            "translated_text": "Kuna da waɗansu abũbuwan amfãni* a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattãta zuwa ga ¦ãkin 'yantacce ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Anã amfãni da dabbar hadaya wajen hawa sabõda larũra da shan nõno har a kai ga wurin sõke ta. Anã sõke hadaya a cikin hurumin Makka."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 336,
            "translated_text": "Kuma ga kõwace al'umma Mun sanya ibãdar yanka, dõmin su ambaci sũnan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbõbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushãra ga mãsu ƙanƙantar da kai."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 336,
            "translated_text": "Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukãtansu su firgita, da mãsu haƙuri a kan abin da ya sãme su, da mãsu tsayar da salla, kuma sunã ciyarwa daga abin da Muka azurta su.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Waɗannan sũ ne siffõfin mãsu ƙasƙantar da kai watau mãsu tawãli'u. Zukãtansa na firgita idan an ambaci Allah, su ga kamar sunã ganin sa, a gaba gare su, sabõda haka sai su ji sauƙin haƙuri ga ɗaukar masifa, kuma su tsayar da salla da sauran ibãdõdi na jiki kuma su bãyar da zakka da sauran ibãdõdin dũkiya. "
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 336,
            "translated_text": "Kuma rãƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibãdõjin Allah. Kunã da wani alhẽri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sunã tsaye* a kan ƙafãfu uku. Sa'an nan idan sãsanninsu suka fãɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hõre muku su, tsammãninku kunã gõdẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan yanã nũna yadda ake sũkar rãƙuma sunã tsaye a kan ƙafãfu uku a ɗaure guda bãyan an lanƙwasa guiwarta an ɗaure sama. Anã ambatar sũnan Allah kuma a yi kabbara a lõkacin sũkar a masõkar zũciyarta. Anã sukar shãnu kuma anã yankansu. Anã yankan tumãki da awaki kawai. Anã yanka sauran dabbõbi da tsuntsaye kawai. "
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 336,
            "translated_text": "Nãmõminsu bã za su sãmi Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tanã, sãmun Sa. Kamar haka Ya hõre su sabõda ku dõmin ku girmama Allah sabõda shiriyar da Ya yi muku. Kuma ka yi bushãra ga mãsu kyautata yi."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 336,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah Yanã yin faɗa* sabõda waɗanda suka yi ĩmãni. Lalle ne Allah bã Ya son dukkan mayaudari, mai yawan kãfirci.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah Yã yi alkawarin kãre wanda yake aiki da taƙawa dõminsa. Yanã tunkuɗe masa maƙiyansa, Ya yi masa faɗa."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 337,
            "translated_text": "An yi izni ga waɗanda ake yãƙar su da cẽwa lalle an zãlunce su, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ĩkon yi ne a kan taimakonsu."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 337,
            "translated_text": "Waɗanda aka fitina daga gidajensu bã da wani hakki ba fãce sunã cẽwa, Ubangijinmu Allah ne.\"Kuma ba dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne ba, sãshensu da sãshe, haƙĩƙa, da an rũsa sauma'õ'in (Ruhbãnãwa) dã majãmi'õ'in Nasãra da gidãjen ibãdar Yahudu da masallatai waɗanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa. Kuma lalle, haƙĩƙa, Allah Yanã taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle Allah ne haƙĩƙa Mai ƙarfi Mabuwãyi."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 337,
            "translated_text": "Waɗanda suke idan Muka bã su ĩko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani,* kuma su hana daga abin da ba a sani ba. Kuma ãƙibar al'amura ga Allah take.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Abin da aka sani daga shar'ia watau shĩ ne alheri, kuma abin da ba a sani ba ga shari'a, watau sharri wanda Allah bã Ya so, akasin alheri. Tsayar da ayyukan alheri ba zai isa ba sai anã yin wa'azi ga mutãne a umarce su da yin alhħri kuma a hana su daga aikata sharri."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 337,
            "translated_text": "Kuma idan sun ƙaryata ka, to lalle haƙĩƙa, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa, sun ƙaryata a gabaninsu."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 337,
            "translated_text": "Da mutãnen Ibrahim da mutãnen Lũɗu."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 337,
            "translated_text": "Da mãsu Madyana, kuma an ƙaryata Mũsã. Sai Na jinkirtawa kãfiran, sa'an nan kuma Na kãma su. To, yãya musũNa (gare su) ya kasance?"
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 337,
            "translated_text": "Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhãli kuwa tanã mai zalũnci sai ta zama fãɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wõfintar, da kuma gidãjen sarauta maɗaukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 337,
            "translated_text": "Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dõmin zukãta waɗanda zã su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurãre da su su kasance a gare su? Dõmin lalle ne idãnun ba su makanta, amma zukãta waɗanda ke a cikin ƙirãza sũ ke makanta."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 338,
            "translated_text": "Kuma sunã nẽman ka yi gaggãwa da azãba, alhãli kuwa Allah bã zai sãɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini* ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidãyãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah bã Ya sãɓa wa'adinSa.Daɗewar rashin saukar azãba bã sãɓãwar wa'adi ba ne, ajalin azãbar ne bai zo ba.Dõmin yini guda a wurin Allah daidai yake da shekara dubu na shekarun dũniya. Sabõda haka kwana guda daidai yake da shekara dubu biyu. Sabõda haka sa'a guda ta Allahna daidai da shekara tamãnin da uku da wata huɗu."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 338,
            "translated_text": "Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azãba gare ta (da laifinta) sa'an nan Na kãma ta, kuma zuwa gare Ni makõma take."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 338,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ya ku mutãne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 338,
            "translated_text": "To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sunã da gãfara da arziki na karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 338,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi aikin ɓãtãwa a cikin ayõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗancan 'yan Jahĩm ne."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 338,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri,* sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyinSa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Annabãwa sukan yi wahami ga tunãninsu, su yi zaton wani abu daidai ne alhãli kuwa a wurin Allah bã haka Yake nufi ba. A kan wannan, sai shakka ta shiga wãwã a kansu, amma wanda ke da ĩmãni to bã zai rikice ba sabõda wannan kuskure dõmin Allah bã Ya barin su a kansa, sai Ya gyãra abin da ke ciki na wahami. Misãli ƙissar Yũnusu, da ƙissar Annabi a cikin suratu Abasa, da ƙissar Ibrãhim wajen jãyayya da malã'ikun da aka aika zuwa alƙaryõyin mutãnen Lũɗu."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 338,
            "translated_text": "Dõmin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jẽfãwa ya zama fitina ga waɗanda a cikin zukãtansu akwai cũta, da mãsu ƙẽƙasassun zukãtansu. Kuma lalle ne azzãlumai haƙĩƙa, sunã a cikin sãɓãnimai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 338,
            "translated_text": "Kuma dõmin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka dõmin su yi ĩmãni da shi sabõda zukãtansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi ĩmãni ne zuwa ga hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 338,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta bã zã su gushe ba sunã a cikin shakka daga gare shi, har Sa'a ta jẽ musu bisa ga abke, kõ kuwa azãbar wani yini bakarãre ta jẽ musu."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 339,
            "translated_text": "Mulki a rãnar nan ga Allah yake, Yanã hukunci a tsakãninsu. To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã a cikin gidãjen Aljannar ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 339,
            "translated_text": "Kuma waɗandra suka kãfirta kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu, to, waɗannan sunã da azãba mai wulãkantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 339,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su, kõ suka mutu, lalle ne Allah Yanã azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu azurtãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 339,
            "translated_text": "Lalle ne, Yanã shigar da su a wata mashiga wadda zã su yarda da ita. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa Masani ne, Mai haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 339,
            "translated_text": "Wancan! Kuma wanda ya rãma azãba da misãlin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma aka zãlunce shi, lalle ne Allah Yanã taimakon sa. Lalle ne Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 339,
            "translated_text": "Wancan! sabõda Allah Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 339,
            "translated_text": "Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 339,
            "translated_text": "Ashe, ba ka gani ba, lalle ne, Allah Yã saukar da ruwa* daga sama, sai ƙasa ta wãyi gari kõriya? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Mai ƙididdigewa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ya misalta Alƙur'ãni da ruwan girgije. Kamar yadda ruwa ke sauka daga sama ya rãya ƙasã haka Alƙur'ãni yake sauka ya rãya zukãta."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 339,
            "translated_text": "Abin da ke a cikin sammai, da abin da ke a cikin ƙasa, Nasa ne, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shi ne wadatacce, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 340,
            "translated_text": "Shin ba ka gani ba, lalle ne Allah Ya hõre muku abin da yake a cikin ƙasa, kuma jirãge sunã gudãna a cikin tẽku, da umurninSa kuma Yanã riƙe sama dõmin kada ta fãɗi a kan ƙasa fãce da izninsa? Lalle ne Allah ga mutãne haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 340,
            "translated_text": "Kuma shĩ ne wanda Ya rãya ku, sa'an nan kuma Yanã matar da ku, sa'an nan kuma Yanã rãyar da ku. Lalle mutum, haƙĩƙa, mai kãfirci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 340,
            "translated_text": "Ga kõwace al'umma Mun sanya wurin yanka, su ne masu yin baiko gare Shi, sabõda haka, kada su yi maka jãyayya a cikin al'amarin (hadaya). Kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka lalle kai kana a kan shiriya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 340,
            "translated_text": "Kuma idan sun yi maka jidãli, sai ka ce: \"Allah ne Mafi sani game da abin da kuke aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 340,
            "translated_text": "\"Allah ne zai yi hukunci a tsakãninku, a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da kuka kasance a cikinsa kunã sãɓawa jũna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 340,
            "translated_text": "Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 340,
            "translated_text": "Kuma sunã bautãwa baicin Allah, abin da (Allah) bai saukar da wani dalili ba game da shi, kuma abin da bã su da wani ilmi game da shi, kuma bãbu wani mai taimako ga azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 340,
            "translated_text": "Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu kanã sanin abin ƙyãma a cikin fuskõkin waɗanda suka kãfirta sunã kusa su yi danƙa ga waɗanda ke karãtun ayõyinMu a kansu. Ka ce: \"Shin to in gaya muku abin da yake mafi sharri daga wannan? (Ita ce) Wuta.\" Allah Yã yi alkawarinta ga waɗanda suka kãfirta. Kuma makõmarsu ta mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 341,
            "translated_text": "\"Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi, kuma idan ƙudãn ya ƙwãce musu wani abu, bã zã su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nẽma da wanda ake nẽman gare shi sun raunana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 341,
            "translated_text": "Ba su ƙaddara wa Allah hakkin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 341,
            "translated_text": "Allah nã zãɓen Manzanni daga malã'iku kuma daga mutãne.* Lalle Allah, Mai ji ne, Mai gani.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Allah nã zaɓen Manzanni daga mutãne da malã'iku kawai. Sabõ da haka bãbu wani manzo da jinsin aljannu kõ wani jinsi, kuma ãyar Sũratul Ahzãb ta 40 tã nũna zãɓen nan ya ƙãre daga Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Duk wanda ya yi da'awar Allah Ya bã shi wani hukumci a bãyan Annabi Muhammadu, kõ dã bai yi da'awar annabci ba, to, shĩ Dajjal ne, bã a bin sa."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 341,
            "translated_text": "Yanã sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 341,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi rukũ'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alhẽri, tsammãninku, ku sami babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 22,
            "page_number": 341,
            "translated_text": "Kuma ku yi jihãdi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihãdinSa. shĩ ne Ya zãɓe ku alhãli kuwa bai sanya wani ƙunci* ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar ubanku Ibrãhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi** daga gabãnin haka. Kuma a cikin wannan (Littãfi ya yi muku sũna Musulmi), dõmin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, kũ kuma ku kasancemãsu shaida a kan mutãne. Sabõda haka ku tsayar da salla kuma ku bãyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Sãbõda haka mãdalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mãdalla da Shi ya zama Mai taimako.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bãbu ƙunci a cikin Musulunci, duk inda aka faɗi tsanani kuma an faɗi yadda sauƙi zai sãmu a kõwane hãli. ** Sharaɗin Musulunci ya zama a kan aƙĩdar Ibrãhĩm wanda ya yi wa wannan al'umma sũna da Musulmi tun a zãmaninsa, kuma an ambaci wannan magana a cikin wannan Littafi, wãtau Alƙur'ãni, a cikin sũrar Baƙara ãyã ta 128."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũminai* sun sãmi babban rabõ.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mũminai su ne waɗanda suke da siffõfin da aka jeranta a cikin ãyõyĩn da ke biye daga ta 2 zuwa ga ta 9."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Waɗannan, sũ ne magãda."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi,* su a cikinta madawwama ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Asalin firdausi fadama mai ruwa da itãce da ni'ima. Aljannar firdausi ita ce mafi ɗaukakar Aljanna."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar ¡iyãma, za a iãyar da ku,"
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 342,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "Da wata itãciya,* tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Itãciyar Zaitũni. Ita ce itãciyar farko da ta tsira a kan ƙasa a bãyan Ɗũfãna tanã rãyuwa mai dõgon lõkaci; an ce tanã rãyuwa kamar shekara dubũ huɗu. Anã cin 'ya'yanta, anã man shãfãwa da su, kuma anã yin miya dasu. Asalin sibg, rini dõmin tanã rina lõmar tuwo. Dũtsen Sĩnã'a mai albarka, ɗũr, shĩ ne dũtSe mai itãce a kansa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni* mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sũfi da gashi dõmin tufãfi da kãyan ɗãki, kãsũsuwa da fãtu da kõfatai dõmin yin abũbuwan amfãni."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: \"Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: \"Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "\"Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijĩna! Ka taimakeni Saboda mutãnena sun ƙaryatã ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 343,
            "translated_text": "Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. \"Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "\"Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: \"Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "\"Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.'\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙẽƙa' Mãsu jarrabãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. \"Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: \"Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "\"Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "\"Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "\"Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa,* kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Munã mutuwa kuma munã rãyuwa da haihuwar ɗiya da 'yã'ya. A bãyan wannan bãbu wata rãyuwa ta wata Lãhira,."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "\"Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "Ya ce: \"Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai!"
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 344,
            "translated_text": "Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni!"
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyinMu da, dalĩli bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Sai suka ce: \"Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu* zã su shiryu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Banĩ Isrã'ĩla na yanzu idan sun tuna cewa Alƙur'ãni bã shĩ ne farkon littafin sama ba, an bai wa Mũsã wani littafi, su kuma sunã alfahari da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã* Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ãyar Ĩsã da uwarsa ita ce an haife shi bãbu uba. Kuma a lõkacin nan Yahũdu suka so sarkin zãmanin nan ya kashe shi, sai uwarsa ta gudu da shi zuwa Baitil Maƙaddas, kõ Dimashƙa, kõ Falasɗĩnu, inda suka zauna shekara gõma sha biyar har sarkin nan ya mutu."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi* kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah Ya umurci ManzanninSa da cin halat sa'an nan su aikata aikin ƙwarai. Haka kuma Ya umurci Mũminai. Sabõda haka karɓar aiki na ƙwarai an tsayar da shi ne a kan cin halat."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Taƙawa, ita ce bautawa Allah da abin da Ya yi umurni a bauta Masa, a kan harshenAnnabinsa na zamaninsa. Yanzu bãbu taƙawa sai a cikin Musulunci kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu,(5) kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Kõwa ya kãma hanyarsa, al'ummar Musulmi ta zama ƙungiyõyi dabam-dabam, kõwanensu yanã farin ciki da abin da ke gare shi, yanã ganin shi ne mafifici"
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya,"
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri?"
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu,"
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni,"
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 345,
            "translated_text": "Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki,"
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu,"
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri)."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su, mãsu aikatãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Har idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Kunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu?"
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Kõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Kõ sunã cẽwa, \"Akwai hauka gare shi?\" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton* (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Zikiri a nan, shi ne Alƙur'ãni wanda ya zo wa Lãrabãwa kõ Ƙuraishawa da abũbuwa na ɗaukakarsu, da ambatonsũnansu, da shiryar da su, da gabãtar da su a kan sauran kabĩlu. Amma duk da haka sunã bijirewa daga gare Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 346,
            "translated_text": "Kuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba* sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Azãbar dũniya kamar yunwa da ciwo da talauci da rashin kwanciyar hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mugi, shi ne kãsa yin magana sabõda ɗebe tsammãni daga sãmun kõwane alheri. Asalin kalmar daga Fulãtanci take."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Suka ce: \"Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lale ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "\"Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani?\""
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Zã su ce: \"Ta Allah ne.\" Ka ce, \"Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma?\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Zã su ce: \"Na Allah ne.\" Ka ce, \"Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani?\""
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 347,
            "translated_text": "Zã su ce: \"Ga Allah yake.\" Ka ce: \"To, yãya ake sihirce ku?\""
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka."
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ neMafi sani game da abin da suke siffantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "\"Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni,* \"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Inã neman tsari da Kai, yã Ubangijina! Kada Shaiɗãnu su halarto ni a cikin al'amurana duka, dõmin ba su halarta, fãce da sharri."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: \"Yã Ubangijina, Ku mayar da ni (dũniya).\""
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "\"Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari.\" Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su."
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 348,
            "translated_text": "Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "\"Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã Ubangijinmu, shaƙãwamiu ce ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "\"Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, \"Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõNa kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Ya ce: \"Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru?\""
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Suka ce: \"Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "\"Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja."
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 23,
            "page_number": 349,
            "translated_text": "Kuma ka ce: \"Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "(Wannan) sũra ce. Mun saukar da ita, kuma Mun wajabta ta, kuma Mun saukar da ãyõyi bayyanannu a cikinta, dõmin ku riƙa tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "Mazinãciya da mazinãci,* to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Hukuncin waɗanda ba su yi aure ba ne, amma waɗanda suka yi aure hukuncinsu a jefe su har su mutu, bãyan sharuɗɗa sun cika, kamar yadda yake ga sunna. Kuma wannan ga hakkin 'ya'ya ne, amma bãyi, hukuncinsu bũlãla hamsin kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "Mazinãci bã ya aure* fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Auren mazinãci kõ mazinãciya makarũhi ne ga wanda bahakanan yake ba, dõmin tsaron mutunci da kõre tuhuma."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "Kuma waɗanda ke jĩfar* mãtã masu kãmun kai, sa'an nan kuma ba su jẽ da shaidu huɗu ba to, ku yi musu bũlãla, bũlãla tamãnin, kuma kada ku karɓi wata shaida tãsu, har abada. Waɗancan su ne fãsiƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Haddin ƙazafi bũlãla tamãnin ga ɗã, kõ arba'in ga bãwa idan ya yi ƙazafi ga ɗã,."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "Fãce waɗanda suka tũbadaga bãyan wannan, kuma suka gyãru, to lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "Kuma waɗanda ke jĩfar mãtan* aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su ba, fãce dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah, 'Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga magasganta.'<br \/>\n____________________<br \/>\n * Hukuncin ranstuwar li'ani da yadda ake yin ta."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "Kuma ta biyar cẽwa 'La'anar Allah ta tabbata a kansa, idan ya kasance daga maƙaryata.'"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "Kuma yanã tunkuɗe mata azãba ta yi shaida, shaida huɗu da Allah, 'Lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga maƙaryata.'"
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "Kuma tã biyar cẽwa 'Hushin Allah ya tabbata a kanta idan ya kasance daga magasganta.'"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 350,
            "translated_text": "Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku, da rahamarSa, kuma cẽwa Allah Mai karɓar tũba ne, Mai hikima!"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda* suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã'a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sanã'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Farko Hadĩsil Ifk ne wanda waɗansu suka jefi Ã'isha, Ummul Mũminĩna da zina a cikinsa Allah Ya barrantar da ita. Bai zama sharri ba ga Musulmi, sai dai ya zama alheri dõmin ya zama sanadi ga sanin hukunce-hukunce mãsu yawa, na zaman jama'a da kuma darajar mutãnen da abin ya shãfa. Yadda ƙissar take shi ne yadda Ã'ishatu, Uwar Mũminai ta faɗa, ta ce: \"Na kasance tãre da Annabi tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, a cikin wani yãƙi, a bãyan an saukar da Hijãbi, watau kulle. Sai ya ƙãre daga yãƙin ya kõma, ya yi kusa da Madĩna, sai ya yi umurni da tãshi ga tafiya a wani dare, sai ni kuma na tafi na ƙãre sha'anĩna, na fuskanta zuwa ga wurin rãƙumãta, sai na ga abin wuyana ya yanke, saina kõma, na neme shi, kuma su mãsu kula da ni suka ɗauki darbũka suka aza a kan rãkuma sunã zaton inã ciki alhãli mãtã sun kasance sauƙãƙa dõmin ba su cin kõme sai kaɗan na abinci.\" Na sãmi abin wuyãna na kõmo a bãyan sun tafi. Sai na zaunaa masaukĩna wanda na kasance a ciki. Kuma na yi zaton mutãnen zã su rasa ni su kõmo zuwa gare ni. Sai na ji barci na yi barcin. Shi kuma Safwãnu ya yi rurumi daga bãyan ãyarin yãƙi, ya fita da sauran dare sai ya wãyi gari a inda nake. Sai ya ga duhun mutum mai barci, sai ya gãne ni a lõkacin da ya gan ni, dãmã ya kasance yanã ganĩ na a gabãnin kulle, sai na farka da jin sautinsa na istirjã'i. \"A lõkacin da ya gãne ni, sai na rufe fuskãta da mayãfina. Wallãhi bai yi mini magana ba da kalma, ni kuma ban ji kõ kalma ba daga gare shi, sai dai istirjã'insa a lõkacin da ya gurfanar da rãƙumarsa, ya take ƙafarta ta gaba, ni kuma nã hau, ya shiga yanã jan rãƙumar da ni har muka isa ga uwar yãƙin, a bãyan sun sauka, a cikin zãfin rãna. Daga nan wanda ya halaka ya halaka, wanda ya jiɓinci girman abin, shi ne Abdullahi bn Ubayyi bn salũl. \"Buhãri da Muslimu sun ruwaito shi."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "Don me a lõkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai mãta ba su yi zaton alhẽri game da kansu ba kuma su ce: \"Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kãwo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira. Lalle ne, dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a cikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "A lõkacin da kuke marãbarsa da harsunanku kuma kunã cẽwa da bakunanku abin da bã ku da wani ilmi game da shi, kuma kunã zaton sa mai sauƙi alhãli kuwa, shi a wurin Allah, babba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "Kuma don me a lõkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, \"Bã ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne mai girma\"?"
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "Allah Yanã yi muku wa'azi, kada ku kõma ga irinsa, har abada, idan kun kasance mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "Kuma Allah Yanã bayyana muku ãyõyinSa, kuma Allah Masani ne, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhãli kuwa, kũ ba ku sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 351,
            "translated_text": "Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa. Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne, Mai jin ƙai!"
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 352,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni, kada ku bi hanyõyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin hanyõyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yanã umurni da yin alfãsha da abin da ba a sani ba, kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, bãbu wani mutum daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yanã tsarkake wanda Yake so kuma Allah Mai ji ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 352,
            "translated_text": "Kuma kada* ma'abũta falala daga gare ku da mawadãta su rantse ga rashin su bãyar da alhẽri ga ma'abũta zumunta da miskĩnai da muhãjirai, a cikin hanyar Allah. Kuma su yãfe, kuma su kau da kai. shin, bã ku son Allah Ya gãfarta muku, alhãli Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mai yin alheri dõmin Allah kada ya yanke shi daga wanda yake yi wa alherin nan, sabõda yã yi masa wani laifi, da ya shãfe shi ga mutuncinsa kõ dũkiyarsa. Sai ya yãfe, ya kau da kai, ya ci gaba da alherinsa dõmin Allah, kamar yadda Mistahu, wanda yake a cikin dangin Abũbakar As-siddiƙ ya shiga a cikin Hadĩsil Ifk alhãli kuwa Abũbakar ke ciyar da shi sabõda shi misĩkini ne da zumuntã kuma a tsakãninsu, sai Abũbakar ya gãfarta masa, kuma ya ci gaba da bã shi abin da yake bã shi. Haka sauran wuɗanda suka fãda a cikin wannan masifa, an yãfe musu a bãyan an yi musu haddin ƙazafi, sai dai wanda ya ɗauki mai girmansa, wãtau Ibn Ubayyu, shi kam ba a yi masa haddi ba dõmin Allah Ya yi masa alkawarin azãba mai tsanani a Lãhira. Watau Musulmi ake yi wa haddi dõmin ya tsarkaka."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 352,
            "translated_text": "Lalle ne waɗannan da suke jĩfar mãtã mãsu kãmun kai gãfilai* mũminai, an la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma sunãda azãba mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Gãfila, ita ce wadda ba ta jarrabi kõme ba sabõda ƙurucciya."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 352,
            "translated_text": "A rãnar da harsunansu da hannãyensu, da ƙafãfunsu suke bãyar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 352,
            "translated_text": "a rãnar dl Allah Yake cika musu sakamakonsu tabbatacce kuma sunã sanin (cẽwa) lalle Allah, Shi ne Gaskiya bayyananna."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 352,
            "translated_text": "Miyãgun mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun* maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan mãtã suke. waɗancan sũ ne waɗanda ake barrantãwa daga abin da (mãsu ƙazafi) suke faɗa kuma sunã da gãfara da arziki na karimci.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Haka miyãgun kalmõmi bã su dãcewa sai daga mũgun mutum. Kuma kalmõmin ƙwaraiba su fitõwa sai daga mutãnen ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 352,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai kun sãmi izni, kuma kun yi sallama* a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare ku, tsammaninku, zã ku tuna.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hukuncin shiga gidãje da neman izni da sallama."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 353,
            "translated_text": "To, idan ba ku sãmi kõwa a cikinsu ba, to, kada ku shige su, sai an yi muku izni. Kuma idan an ce muku, \"Ku kõma.\" Sai ku kõma, shi ne mafi tsarkaka a gare ku. Kuma Allah game da abin da kuke aikatãwa, Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 353,
            "translated_text": "Bãbu laifi a kanku, ga ku shiga gidãje waɗanda bã zaunannu ba, a cikinsu akwai waɗansu kãya nãku. Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke nũnãwa, da abin dakuke ɓãyẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 353,
            "translated_text": "Ka ce wa mũminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjõjinsu.* wannan shĩ ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sanã'antãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Hukuncin tsare idãnu da rũfe al'aura ga maza da mãtã."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 353,
            "translated_text": "Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan* ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mãtansu, watau mãtã Musulmi banda mãtã kãfirai, bã ya halatta ga mace kãfira ta ga al'aurar mace Musulma. Mabiya sũ ne mãsu nħman bukãta ga mãtã wãtau miskĩnai, tsõfaffi daga maza. Al'aurar mace, ɗiya a cikin salla kõ a tãre da wani namiji ajnabi, to, dukan jikinta ne sai fuska da tãfuna, haka kuma a cikin salla. Amma a tãre da mace Musulma tsakãnin cĩbiya da guiwõyi, shi ne al'aura, kuma tãre da muharraminta, dukan abin da bã sasanni ba. Baiwa kamar namiji take, al'aurarsu abin da ke tsakãnin cĩbĩya da guiwa."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 354,
            "translated_text": "Kuma ku aurar da gwaurãye daga gare ku, da sãlihai daga bãyinku, da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadãtar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 354,
            "translated_text": "Kuma waɗannan da ba su sãmi aure ba su kãme kansu har Allah Ya wadãtar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansã idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu kuma ku bã su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bã ku. Kuma kada ku tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu,* dõmin ku nẽmi rãyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a bãyan tĩlasta su, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Tsaron kai, shi ne su yi aure; tĩlastãwa a nan, shi ne a hana su aure dõmin su yi wa ubangijinsu aiki."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 354,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Mun saukar zuwa gare ku, ãyõyi mãsu bayyanãwa, da misãli daga waɗanda suka shige daga gabãninku, da wa'azi ga mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 354,
            "translated_text": "Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misãlin HaskenSa, kamar tãgã, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi taurãro ne mai tsananin haske, anã kunna shi daga wata itãciya mai albarka, ta zaitũni, bã bagabashiya ba kuma bã bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma kõ wuta ba ta shãfe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misãlai ga mutãne, kuma Allah game da dukan kõme, Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 354,
            "translated_text": "A cikin waɗansu gidãje waɗanda Allah Yã yi umurnin a ɗaukaka kuma a ambaci sũnansa a cikinsu, sunã yin tasbĩhi a gare Shi a cikinsu, sãfe da maraice."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 355,
            "translated_text": "Waɗansu maza, waɗanda wani fatauci bã ya shagaltar da su, kuma sayarwa bã ta shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsai da salla da bãyar da zakka, sunã tsõron wani yini wanda zukãta sunã bibbirkita a cikinsa, da gannai."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 355,
            "translated_text": "Dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Ya ƙãra musu daga falalarsa. Kuma Allah Yanã azurta wanda Yake so, bã da lissafi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 355,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka ƙãfirta ayyukansu sunã kamar ƙawalwalniyã ga faƙo, mai ƙishirwa yanã zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kõme ba, kuma ya sãmi* Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisãbinsa. Kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ya sãmi Allah a wurin da ƙawalwalniyar take, alhãli Allah Ya gaya masa cħwa bãbu ruwa a nan, kuma Ya nũna masa hanyar da zai sãmi ruwa, idan zai bĩ ta. Sai Allah Ya cika masa hisãbinsa da cħwa, \"Allah Mai saurin sakamako ne ga wanda ya sãɓa wa umurninSa,\" Dõmin nan da nan mai sãɓawar zai ga kuren kansa, tun daga dũniya. HisãbinAllah yanã aukuwa da sauri a kan mai sãɓã wa umurninsada gangan."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 355,
            "translated_text": "Kõ kuwa kamar* duffai a cikin tẽku mai zurfi, tãguwar ruwa tanã rufe da shi, daga bisansa akwai wata tãguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai sãshensu a bisa sãshe, idan ya fitar da tãfinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai sanya masa haske ba, to, bã ya da wani haske.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ayyukan kafiri, wanda bã ya bin Hasken Allah ga aikinsa kamar mai ƙishirwa da wanda ya siffanta a sama yake, kõ kuwa kamar mai tafiya a cikin duffan da aka siffanta a wannan ãya."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 355,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba (cẽwa) lalle ne Allah, Wanda yake a cikin sammai da ƙasa sunã yi Masa tasbĩhi, kuma tsuntsaye sunã mãsu sanwa, kõwane lalle ya san sallarsa da tasbĩhinsa kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 355,
            "translated_text": "Mulkin sammai da ƙasa ga Allah kawai yake, kuma zuwa ga Allah makõma take."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 355,
            "translated_text": "Ashe, ba ka ganĩ ba, lalle ne Allah Yanã kõra girgije, sa'an nan kuma Ya haɗa a tsakãninsa sa'an nan kuma Ya sanya shi mai hauhawar jũna? Sai ka ga ruwa yanã fita daga tsattsakinsa, kuma Ya saukar daga waɗansu duwãtsu a cikinsa na ƙanƙarã daga sama, sai ya sãmu wanda Yake so da shi, kuma Ya karkatar da shi daga barin wanda Yake so. Hasken walƙiyarsa Yanã kusa ya tafi da gannai."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Allah Yanã jũyar da dare da yini. Lalle ne a cikin wannan akwai abin kula ga ma'abũta gannai."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Kuma Allah ne Ya halitta kõwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan cikinsu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan ƙafãfu biyu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya akan huɗu. Allah Yãna halitta abin da Yake so, lalle Allah, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Lalle ne haƙĩƙa Mun saukar da ãyõyi, mãsu bayyanãwa. Kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Kuma sunã cẽwa, \"Mun yi ĩmãni da Allah da kuma Manzo, kuma mun yi ɗã'ã.\" Sa'an nan kuma wata ƙungiya daga gare su, su jũya daga bãyan wancan. Kuma waɗancan ba mũminai ba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Kuma idan aka kirã su zuwa ga Allah da ManzonSa, dõmin Ya yi hukunci* a tsakãninsu, sai gã wata ƙnngiya daga gare su sunã mãsu bijirewa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan yanã nũna cewa rashin yardã da hukuncin Allah kãfirci ne. Wanda ya kai ƙãra ga kõtun al'ada alhãli kuwa yanã Musulmi kuma ya halatta haka, bã da wata lalũra ba, ya zama kãfiri sai idan ya tũba. Bã ya halatta ga Musulmi su yarda da yin kõtunanal'ãda a ƙasarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Kuma idan hakki ya kasance a gare su, zã su jẽ zuwa gare shi, snnã mãsu mĩƙa wuya."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Shin, a cikin zukãtansu akwai cũta ne, ko kuwa sunã tsõron Allah Ya yi zãlunci a kansu da ManzonSa? Ã'a, waɗancan sũ ne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Maganar mũminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa dõmin Ya yi hukunci a tsakãninsu takan kasance kawai su ce \"Mun ji, kuma mun yi ɗã'ã, Kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Kuma wanda ya yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsõron Allah, ya kuma bĩ Shi da taƙawa to waɗannan sũ ne mãsu babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 356,
            "translated_text": "Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu, 'Lalle ne idan ka umurce su haƙĩƙa sunã fita.' Ka ce, \"Kada ku rantse, ɗã'ã sananna ce! Lalle ne, Allah Mai ƙididdigewã ne ga abin da kuke aikatãwã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 357,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu. Kuma bãbu abin da yake a kan Manzo fãce iyarwa bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 357,
            "translated_text": "Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya musu daga bãyan tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini bã su haɗa kõme da Nĩ. Kuma wanda ya kãfirta a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 357,
            "translated_text": "Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo, tsammãninku a yi muku rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 357,
            "translated_text": "Kada lalle ka yi zaton waɗanda suka kãfirta zã su buwãya a cikin ƙasa, kuma makõmarsu wuta ce, kuma lalle ne makomar tã mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 357,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni* sau uku; daga gabãnin sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ladabin shiga gida shĩ ne dukan yãron da ya balaga, ɗa ne kõ bãwa, kada ya shiga gida kõ a ɗãki a bãyan sallama sai ya nemi izni da cewa \"In shiga?\" Idan an karɓa masa da izni, ya shiga, idan kuma yanã zaton ba a ji shi ba, sai ya sãke neman izni har sau uku. neman izni yanã wajaba kõ ga yãran gidan a cikin lõkuta uku, wãtau a gabãnin sallar asuba da lõkacin tsakar rãnar na ƙailũla da bãyan sallar ishã'i."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 358,
            "translated_text": "Kuma idan yãra daga cikinku suka isa mafarki to su nẽmi izni, kamar yadda waɗanda suke a gabãninsu suka nẽmi iznin. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku, kuma Allah Masani ne, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 358,
            "translated_text": "Kuma tsõfaffi daga mãtã, waɗanda bã su fatan wani aure to, bãbu laifi a kansu su ajiye tufãfinsu, bã sunã mãsu fitar da ƙawa ba, kuma su tsare mutuncinsu shĩ ne mafi alhẽri a gare su. Kuma Allah Mai jĩ ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 358,
            "translated_text": "Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku,* gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Akwai daga ladubban zamantakewa har dai a tsakãnin dangi a ci abincin jũna, kõ aci tãre a waje guda, kõ kuwa kõwa ya ci dabam. Kuma idan an haɗu a yi gaisuwã a tsakãnin jũna, gaisuwa irin wadda Allah Ya ce Musulmi su yi wa jũnansu da cewa \"Assalãmu alaikum\". Ita ce gaisuwa mai kyau. Anã ƙãra \"Wa rahmatul Lãhi wa barakãtuh,\" dõmin ta ƙãra dãɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 359,
            "translated_text": "Waɗanda ke mũminai sõsai, su ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tãre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bã su tafiya sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke yin ĩmãni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabõda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmã musu gãfara daga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai*.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Babban ladabin haɗuwar jama'a shĩ ne ĩmãni da Allah kuma da ManzonSa. Sa'an nan kuma biyayya ga shũgaba wajen ayyukan gayya na rãyuwa haɗe, kamar ginin masallaci da hanya da kãsuwa da maƙabarta. Shũgaba yanã da ĩkon bãyar da iznin fakuwar mai uzuri, kuma yanã da ĩkon hanãwa gwargwadon hãli. Wannan kuma ya nũna muhimmancin aikin gayya da tsayuwar shũgaba a kansa, da wajabcin karɓa kira zuwa gare shi. Kuma wannan yanã nũna halaccin karɓar harãji daga mutãne dõmin a tsayu da bukãtocin haɗuwar jama'a gwargwadon hãli."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 359,
            "translated_text": "Kada ku sanya kiran Manzo* a tsakãninku kamar kiran sãshenku ga sãshe. Lalle ne Allah Yanã sanin waɗanda ke sancẽwa daga cikinku da saɗãɗe. To, waɗanda suke sãɓãwa daga umurninSa, su yi saunar wata fitina ta sãme su, kõ kuwa wata azãba mai raɗãɗi ta sãme su.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan yanã nũna ladabin yadda ake kiran Manzon Allah tã hanya mai ladabi. Kada a kira shi da sũnansa kamar yadda ake kiran sauran mutãne da 'Yã Ali', 'Ya zaid,' sai dai a ce Yã Manzon Allah! a cikin sauti mai laushi mai dãɗi. Kuma wannan ladabi yanã shãfar dukan Musulmi na kõwane zãmani game da shũgabansu wanda yake shũgabantar su ga al'amurransu na zamantakewa. Kuma wannan yanã nũna rashin kyãwon mãsu cewa sunã zikiri da kiran sũnan Allah kamar haka \"Allah! Allah! Allah!\" Sabõda rashin ladabin da ke cikin yin haka ga Manzon Allah balle ga Allah.Ba a yin addini sai yadda Allah Yake son a yi Masa, wãtau yadda AnnabinSa ya shiryar da mutãne dõmin su bi Shi, su yi aiki da shi, Kuma sãɓã wa umurnin Annabi yanã sabbaba fitina ga mutãne kõ kuma ga ƙasa gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 24,
            "page_number": 359,
            "translated_text": "To! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa, Yanã sanin abin da kuke a kansa kuma a rãnar da ake mayar da su zuwa gare shi, sai Yanã bã su lãbãri game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kõme, Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 359,
            "translated_text": "Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 359,
            "translated_text": "wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 360,
            "translated_text": "Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 360,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: \"Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa.\" To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 360,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Tatsũniyõyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare shi sãfe da yamma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 360,
            "translated_text": "Ka ce: \"wanda Yake sanin asĩri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle ne shĩ Ya kasance Mai gãfara, Mai, jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 360,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya kasance mai gargaɗi tãre da shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 360,
            "translated_text": "\"Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare shi, yanã ci daga gare ta?\" Kuma azzãlumai suka ce: \"Bã ku bin kõwa, fãce mutum sihirtacce:\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 360,
            "translated_text": "Ka dũba yadda suka buga maka misãlai sai suka ɓace, dõmin haka bã su iya bin tafarki."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 360,
            "translated_text": "Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan (abu): gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidãje."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 360,
            "translated_text": "Ã'a, sun ƙaryata game da Sã'a, alhãli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 361,
            "translated_text": "Idan ta gan su daga wani wuri mai nĩsa, sai su ji sautin fushi da wani rũri nãta."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 361,
            "translated_text": "Kuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sunã waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirãyi halaka a can."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 361,
            "translated_text": "Kada ku kirãyi halaka guda, kuma ku kirãyi halaka mai yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 361,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, wancan ne mafi alhẽri, kõ kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa'adi ga mãsu taƙawa? Tã zama, a gare su, sakamako da makõma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 361,
            "translated_text": "\"Sunã da abin da suke so, a cikinta sunã madawwama. Wannan ya kasance wa'adi abin tambaya a kan Ubangijinka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 361,
            "translated_text": "Kuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: \"Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 361,
            "translated_text": "suka ce: \"Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 361,
            "translated_text": "To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa, sabõda haka bã ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 361,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "Kuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: \"Don me ba a saukar da malã'ĩku ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?\" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "A rãnar da suke ganin malã'iku bãbu bushãra a yinin nan ga mãsu laifi kuma sunã cẽwa,\"Allah Ya kiyãshe* mu!\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Asalin maganar shĩ ne \"Tsari tsararre,\" wãtau muna neman tsari daga Allah, tsari tabbatacce."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "Kuma Muka gabãta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra wãtsattsiya."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "Ma'abũta Aljanna a rãnar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailũla."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "Kuma a rãnar da sama take tsattsãgewa tãre da gizãgizai, kuma a saukar da malã'iku, saukarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "Mulki a rãnar nan, na gaskiya, yanã ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kãfirai, mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "Kuma rãnar da azzãlumi yake cĩzo a kan hannayensa, yanã cẽwa \"Ya kaitõna! (A ce dai) na riƙi hanya tãre da Manzo!"
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "\"Ya kaitõna! (A ce dai) ban riƙi wãne masõyi ba!"
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "\"Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunãwa a bãyan (Tunãwar) ta je mini.\"Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "Kuma Manzo ya ce: \"Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur'ãni abin ƙauracẽwa!\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga mãsu laifi ga kõwane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 362,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: \"Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba, jimla guda?\" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Waɗanda ake tãyarwa a kan fuskõkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, Mun bai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hãrũna, mataimaki tãre da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Sai Muka ce: \"Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da ãyõ yinMu.\" sai Muka darkãke su, darkãkewa."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Da Ãdãwa da Samũdãwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakãnin wannan, mãsu yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Kuma kõwannensu Mun buga masa misãlai, kuma kõwanne Mun halakar da (shi), halakarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma)."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Kuma idan sun gan ka, bã su rikon ka fãce da izgili, (sunã cẽwa) \"Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo?"
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "\"Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi haƙuri a kansu ba.\"Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi ɓacẽwa ga hanya!"
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 363,
            "translated_text": "Shin, kã ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancẽwa mai tsaro a kansa?"
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida* suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Dabbõbin gida sun fi rashin hankali bisa ga na dãji, dõmin na dãji na gudun abin da zai cũce sũ su kuma dabbõbin gida sunã zamã tãre da mãsu cin su, su shã nõnonsu kuma su kashe 'ya'yansu."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã Yã bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Sa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã yini ya zama lokacin tãshi (kamar Tashin ¡iyãma)."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Kuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamarSa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Dõmin Mu rãyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbõbi da mutãne mãsu yawa daga abin da Muka halitta."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa* shi (Alƙur'ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sarrafa Alƙur'ãni watau Munsanya shi a cikin misãlai dabam-dabam dõmin su gani kõ su ji, su yi tunãni, amma sai suka ƙi saurãren, sai dai kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi* a ciƙin kõwace alƙarya.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Dã Muna so dã Mun aika wa kõwane gari da Annabinsa mai yi musu gargaɗi, amma ba Mu so haka ba, sai Muka aika ka kai ɗaya zuwa ga dukan dũniya dõmin Mu ɗaukaka darajarka."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Sabõda haka kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai, ka yãke su, da shi, yãƙi mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Kuma shĩ ne Ya gauwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurbatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 364,
            "translated_text": "Kuma sunã bauta wa, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin su, kuma bã ya cũtar su, kuma kãfiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Ba Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Ka ce: \"Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya* zuwa ga Ubangijinsa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bã na neman wata ijãra sabõda inã karanta muku Alƙur'ãni, ko, sabõda inã shiryar da ku, amma wanda ya so ya ciyar da dũkiyarsa dõmin Allah, to, shĩ kam bã ni hana shi, sai ya ciyar. Kuma mun sani Annabi ba ya cin sadaka. A kan haka ne waɗansu Malamai suka hana karɓar ijãraa kan karantar da Alƙur'ãni. Abin da yake Mu'utamadi ya halatta sabõda Hadĩsi, kumada sauƙaƙewa ga aikin yãɗa addĩnin Musulunci. Hukumci yanã canzawa da canzãwar hãli."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "kuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da* Shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Idan kanã son sanin siffofin Allah, sai ka tambayi Allah, dõmin bãbu wanda ya san shi, sani na gani balle ya iya gaya maka yadda Yake, sabõda haka siffõfin Allah da sũnãyenSa duka bã a yin shisshigi a gare su, sai yadda aka ji su daga Manzon Allah.Tauƙifiyyai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Idan aka ce musu, \"Ku yi sujada ga Mai rahama.\" Sai su ce: \"Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?\"Kuma wannan (magana* ta ƙãra musu gudu.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kõ sun san gaskiyar abin daaka kira su zuwa gare shi, bã zã su yi ɗã'ã ba, dõmin wai sunã jin nauyi su karɓi umurni daga wani mutum."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai* (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Taurãri bakwai waɗandaake cewa matafa su ne Mirrikh da Zahra da Uɗãrid da Ƙamar, wãtau Watã, da Rãnã, da Mushtari, da Zuhal; Kuma burjõji sũ gõma sha biyu ne, su ne Himlu, da Saur, da jauzã'a, da Sirtãn, da Asad, da Sunbula da Mĩzãn da Aƙrab, da Ƙausu, da Jadyu,da Dalwu da Hũt."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa, ga wanda yake son ya yi tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Kuma bãyin Mai rahama(5) su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: \"Salãma\" (a zama lafiya).<br \/>\n____________________<br \/>\n   (5) Bãyan da ya ambaci masu ƙin su yi sujada ga Mai rahama sabõda kangararsu sai kumaya fãra ambaton siffofin mãsu son yin sujada gare shi, Yãyi musu sunã Bãyin Mai rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke cẽwa \"Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra(6)<br \/>\n____________________<br \/>\n  (6) Garama, ita ce uƙũba da dũkiya mai lazimtar wanda aka aza wa ita. Da Hausa anã cewa tãra. Watau azãba da zã tafi ƙarfin jiki har tanã neman wani abu wanda ya danganci jiki. Kõ mene ne, kamar dũkiya."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "\"Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 365,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka,"
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "A riɓanya masa azãba a Rãnar ¡iyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "Kuma wanda ya tũba,* kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wanda ya tũba daga kõwane irin zunubi, waɗanda aka ambata da waɗanda ba a ambata ba, kõ dã laifinsa kãfirci ne, to, sai ya tũba zuwa ga Allah kawai, tũba ta gaskiya, lalle ne Allah zai karɓi tũbarsa matuƙar ajalin mutuwa bai sauka a kansa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame* da makãfi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Idan an yi musu wa'azi zã su saurãre shi, kuma su yi aiki da shi. Bã zã su zama kurãme ba ga karɓar gaskiya, kuma bã zã su zama makãfi ba gaganin hanyar shiryawa."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke cẽwa \"Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya* mu shũgabanni ga mãsu taƙawa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Anã son mutum ya rõƙi Allah Ya ɗaukaka shi, shi da zuriyarsa, ɗaukakar addini, kamar yadda Annabi Ibrãhĩm ya yi rõƙon haka. Kuma wannan yanã cikin sifõfin Bãyin Mai rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "Waɗannan anã sãka musu da bẽne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 25,
            "page_number": 366,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bã dõmin addu'arku* ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, sabõda haka al'amarin zã ya zama malizimci.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan yanã nũna cewa Allah Yanã son bãyinSa mãsu rõƙonsa. Kuma Yanã son a rõkeShi ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "¦. S̃. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba!<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan yã nũna cewa Annabi Muhammadu yanã jin tsõron rashin ĩmãnin mutãnensa, kada ya zama shĩ ne ya gajarta daga abin da Allah Ya ɗõra a kansa, na iyar da manzanci. Haka mũmini yake, kullum girman Ubangijinsa yake dũbi, sabõda haka kõme ya yi na ɗã'a, sai ya ga kãsãwar kansa ga tsayuwa da hakkin Ubangijinsa, a kansa, ya ƙãra jin tsõro da tawãli'u."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, \"Ka je wa mutãnen nan azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "\"Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "\"Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci* kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mũsa yanã nũna cewa, shi yanã jin tsõro kada ya zama ya gajarta wajen iyar da manzanci, dõmin shi mai saurin fushine, yanã neman a taimake shi ɗan'uwansa Hãrũna.Wannan ya yi kama da farkon sũrar inda Annabi, tshĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya nũna tsõron taƙaitãwa ga iyar da manzancin Allah zuwa ga mutãnensa dõmin haka ba su yi ĩmãni ba. Hãlin Annabawa duka ɗaya ne ga tsõron taƙaita aikin Ubangijinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "\"Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "\"Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "\"Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 367,
            "translated_text": "\"Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Ya ce: \"Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "\"Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "\"Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Fir'auna ya ce: \"Kuma mene ne Ubangijin halittu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, \"Bã za ku saurãra ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Ya ce: \"To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, \"Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi!"
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "\"Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "\"Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 368,
            "translated_text": "Kuma aka ce wa mutãne \"Kõ kũ mãsu tãruwã ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "\"Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,\"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Ya ce: \"Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Mũsã ya ce musu, \"Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: \"Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Suka ce: \"Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "\"Ubangijin Mũsa da Hãrũna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Suka ce: \"Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "\"Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã* ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mũsa yanã nũna cewa, shi yanã jin tsõro kada ya zama ya gajarta wajen iyar da manzanci, dõmin shi mai saurin fushine, yanã neman a taimake shi ɗan'uwansa Hãrũna.Wannan ya yi kama da farkon sũrar inda Annabi, tshĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya nũna tsõron taƙaitãwa ga iyar da manzancin Allah zuwa ga mutãnensa dõmin haka ba su yi ĩmãni ba. Hãlin Annabawa duka ɗaya ne ga tsõron taƙaita aikin Ubangijinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "\"Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan.\""
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Da taskõki da mazauni mai kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 369,
            "translated_text": "Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: \"Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa \"Ka dõki tẽku da sandarka.\" Sai tẽku ta tsãge,* kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Teku ta tsãge hanya gõma sha biyu a kan adadin danginBanĩ Isrãĩla. Suka bi suka wuce, sa'ilin nan aka nutsar daFir'auna, shi da jama'arsa, a cikin hanyõyin ruwan,."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, \"Mẽne ne kuke bauta wa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Suka ce: \"Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su.\""
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "\"Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "Ya ce: \"Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "\"Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "\"To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "\"Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "\"Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "\"Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "\"Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "\"Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako.\""
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 370,
            "translated_text": "\"Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya* a cikin mutãnen ƙarshe.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Harshen gaskiya shĩ ne yabõ mai kyau. Mutãnen ƙarshe sũ ne Musulmi al'ummar Annabi Muhammadu, mãsu shaida ga annabawa da iyar da manzanci"
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima.\""
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su.\""
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Kuma aka ce musu, \"Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Sai aka kikkife su* a cikinta, su da halakakkun.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Gumãkan, sũ da halakakku mabiyansu. Dukkan mai ɓatarda wani shĩ ne gunki ga mai bin sa halakakke."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,"
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Kuma bã mu da abõki, masõyi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!\""
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba."
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, \"Bã zã ku ji tsoron Allah ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "\"Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 371,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?\""
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Ban zama mai kõre mũminai ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa\""
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi."
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, \"Bã zã ku yi taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Shin, kunã yin ginin sitadiyo* a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sitãdiyo shi ne gidan wasanni da Turanci, alãmã da Lãrabci."
        },
        {
            "ayah_number": 129,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?*\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kõ kuma wurãren sanã'õ'i kamar masãƙoƙi irin na zãmanin nan."
        },
        {
            "ayah_number": 130,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 131,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 132,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 133,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 134,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Da gõnaki da marẽmari.\""
        },
        {
            "ayah_number": 135,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "\"Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 136,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 372,
            "translated_text": "Suka ce: \"Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 137,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen* mutãnen farko.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wãtau lãbarun mutãne waɗanda ba su ci gaba ba bã su son a yi rawa da nishãɗi. Anã karantawar ma'anar ƙaryar ta farko, watau wai tãtsũniya ce: a ce wai a hana ãyã akan tsaunuka dõmin wasanni. Suna nufi da ãya ko alãma gidãjen rawa da na nashãdi watau stadiyam da kasĩno. "
        },
        {
            "ayah_number": 138,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 139,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 140,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 141,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 142,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: \"Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 143,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 144,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
        },
        {
            "ayah_number": 145,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 146,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Shin, anã barin ku* a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kuna zaton zã a bar ku a irin wannan ni'ima' Allah bã zai karɓi rãyukanku ba kuma Ya yi muku hisãbi a kanta? Kayya! Zã a yi muku hisãbi a bãyan kun mutu an tsayar da ku, dõmin hisãbin ayyukan da kuka yi."
        },
        {
            "ayah_number": 147,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"A cikin gõnaki da marẽmari.\""
        },
        {
            "ayah_number": 148,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi* mãsu narkẽwa a ciki?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Hirtsi shi ne 'ya'yan itãce sãbabbi tun ba su nuna ba. Wãtau hirtsin gonakinsu idan an ci shi narkewã ya ke yi a cikin ciki, balle kuma 'ya'yan itãce nunannu."
        },
        {
            "ayah_number": 149,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?\""
        },
        {
            "ayah_number": 150,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 151,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 152,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 153,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "Suka ce: \"Kai daga mãsu sihiri kurum kake.\""
        },
        {
            "ayah_number": 154,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 155,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "Ya ce: \"Wannan rãkuma ce tanã da shan* yini, kuma kunã da shan yini sasanne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kuna zaton zã a bar ku a irin wannan ni'ima' Allah bã zai karɓi rãyukanku ba kuma Ya yi muku hisãbi a kanta? Kayya! Zã a yi muku hisãbi a bãyan kun mutu an tsayar da ku, dõmin hisãbin ayyukan da kuka yi."
        },
        {
            "ayah_number": 156,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "\"Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 157,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma."
        },
        {
            "ayah_number": 158,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 159,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 373,
            "translated_text": "Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 160,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 161,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "A lõkacin da ɗan'uwansu,* Lũɗu ya ce musu, \"Bã zã ku yi taƙawa ba?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Lũɗu ɗan'uwansu ne na zaman gari da aure kawai. Asalinsa ɗan baffan Ibrãhĩm ne, sun tãso daga gabas, ƙasar Bãbila suka yi hijira, har ibrahĩm ya sauka Habrũna a ƙasar Shãm, Lũɗu kuwa ya sauka a sadũm da alƙaryunta."
        },
        {
            "ayah_number": 162,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 163,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 164,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 165,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 166,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!\""
        },
        {
            "ayah_number": 167,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari).\""
        },
        {
            "ayah_number": 168,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 169,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 170,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 171,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 172,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu."
        },
        {
            "ayah_number": 173,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 174,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 175,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 176,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 177,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, \"Bã zã ku yi taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 178,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 179,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 180,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 181,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne).\""
        },
        {
            "ayah_number": 182,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 183,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 374,
            "translated_text": "\"Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 184,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "\"Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 185,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Suka ce: \"Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 186,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "\"Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 187,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "\"To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 188,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 189,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije* ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * An ruwaito cewa Allah Ya bũɗe musu ƙõfar Jahannama, zãfi ya hana su zama akõ'ina cikin gidãjensu, sa'an nan aka sanya girgije ya yi musu inuwa mai sanyi-sanyi har suka tãru a ciki, sa'an nan aka sanya girgijen ya kãma da wuta a kansu suka ƙõne kurmus kamar an gasa fãra. Suka kõma tõka kamar yadda suka nema daga Shu'aibu da a jefa musu ɓaɓɓake daga sama idan ya zama daga mãsu gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 190,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 191,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 192,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne."
        },
        {
            "ayah_number": 193,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Rũhi* amintacce ne ya sauka da shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Rũhul Ƙudus, shi ne Jibirĩl, amincin Allah ya tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 194,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 195,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Da harshe na Larabci mai bayãni."
        },
        {
            "ayah_number": 196,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko."
        },
        {
            "ayah_number": 197,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 198,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa,"
        },
        {
            "ayah_number": 199,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 200,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 201,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi."
        },
        {
            "ayah_number": 202,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba."
        },
        {
            "ayah_number": 203,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Sai su ce: \"Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 204,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Ashe, to, da azãbarMu suke nẽman gaggãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 205,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru,"
        },
        {
            "ayah_number": 206,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 375,
            "translated_text": "Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu,"
        },
        {
            "ayah_number": 207,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare* su.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Dã an bã su lõkaci mai tsawo sunã jin dãɗi da rãyuwar dũniya a cikinsa, to, rãnar da mutuwa kõ azãbar Allah ta je gare su, wannan lõkacin bã zai tunkuɗe mutuwar kõ azabar ba daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 208,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 209,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba."
        },
        {
            "ayah_number": 210,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba."
        },
        {
            "ayah_number": 211,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 212,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne."
        },
        {
            "ayah_number": 213,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba."
        },
        {
            "ayah_number": 214,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci."
        },
        {
            "ayah_number": 215,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Kuma ka sassauta fikãfikanka* ga wanda ya bĩ ka daga mũminai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ka zama mai tausayi ga mũminai waɗanda suka bĩ ka, ka yi musu kamar yadda kãzã take yi wa 'ya'yanta ƙanana a lõkacin sanyi, kõ kuwa idan zã su yi barci dõmin ta kãre su daga cũta."
        },
        {
            "ayah_number": 216,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: \"Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 217,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 218,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye."
        },
        {
            "ayah_number": 219,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada."
        },
        {
            "ayah_number": 220,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Lalle Shi, Shi* ne Mai ji, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah Shi ne Mai ji, ji na gaskiya, kuma Masani, sani na gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 221,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Shin, (kunã so) in gaya* muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan dõmin raddi ne gamãsu cewa aljannu ke gayawa Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Alƙur'ãni. Aljannu bã su saukã sai ga maƙaryaci, mai zunubi' Muhammadu kuwa bã haka yake ba. Sabõda haka shi bã mahaukaci ba, kuma ba wanda aljannu suke gaya wa ba. Dukan abin da ya faɗa, to, wahayi ne daga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 222,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi."
        },
        {
            "ayah_number": 223,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne."
        },
        {
            "ayah_number": 224,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Kuma mawãƙa(5) halakakku ne ke bin su.<br \/>\n____________________<br \/>\n   (5) Siffõfin mawãƙa sun nũna cewa Annabi Muhammadu bã mawãƙi ba ne, dõmin bã shi da ɗaya daga cikin siffõfin mawãƙa. Kuma mabiyansa ba halakakku ba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 225,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 226,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 227,
            "surah_number": 26,
            "page_number": 376,
            "translated_text": "Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "¦. S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "Shiriya ce da bushãra ga mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ, sunã yin yaƙĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa* ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Lãhira da ĩmãni da ita sunã a cikin ashĩran Allah. Haka karɓar Alƙur'ãni daga Allah yanã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana a Littafi. Ganin Mũsa ga wutã da abubuwan da suka auku a wurin game da maganar Allah a gare shi da jũyãwar sanda macijiya da kõmawarta sanda da jũyãwar hannunsa fari ƙal da jũyãwarsa zuwa ga asalinsa, duka sunã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana su ga wani mutum."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa \"Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, \"An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "\"Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "\"Kuma ka jẽfa sandarka.\" To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, \"Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "\"Sai wanda ya yi zãlunci, sa'an nan ya musanya kyau a bãyan cũta, to, lalle Nĩ, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "\"Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta, a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance mutãne ne fãsiƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 377,
            "translated_text": "To, a lõkacin da ãyõyinMu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan sihiri ne bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 378,
            "translated_text": "Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai. To, ka dũbi yadda ãƙibar maɓarnata ta kasance."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 378,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: \"Gõdiya* ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Abin da ke hakkin ni'imar Allah a kan mutum, ya gõde Masa. Dãwũda da Sulaiman Allah Yã bã su ilmi na Annabci sun tsayu da gõdiyarsa a kan aiki da shi, da kuma iƙrãri da cewa nĩ'ima ce daga Allah, bã da wani aiki nãsu ba. Annabci da ilmi da sanin maganar tsuntsu da ta aljannu da taturũruwa duka sunã cikin ashĩrin Allah da Yake nũnãwa ta hanyar waɗansu bãyinsa Annabãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 378,
            "translated_text": "Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: \"Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar (Allah) bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 378,
            "translated_text": "Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, to, sũ anã kange su (ga tafiya)."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 378,
            "translated_text": "Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, \"Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 378,
            "translated_text": "Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, \"Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 378,
            "translated_text": "Kuma ya binciki* tsuntsãye, sai ya ce: \"Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ya nũna tsayuwar sulaimãn da binciken kõme da kõwa a cikin daularsa. Kuma da yadda yake yin tsanani a cikin sauƙi. Wannan ita ce hanyar mulki mai kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 378,
            "translated_text": "\"Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 378,
            "translated_text": "Sai ya zauna bã nẽsa ba, sa'an nan ya ce: \"Nã san abin da ba ka sani ba, kuma na zo maka daga Saba da wani lãbari tabbatacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "\"Lalle ni nã sãmi wata mace wadda tanã mulkinsu kuma an bã ta daga dukkan kõme, kuma tanã da gadon sarauta mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "\"Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya, sa'an nan sũ, ba su shiryuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "\"Ga* su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwada abin da kuke bayyanãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * An kãyar da harafin kõrewa dõmin barinsa, da Hausa, yanã ɓãta ma'ana, dõmin shaiɗan bai kange su daga rashin yin sujada ba."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "\"Allah bãbu abin bautãwa fãce shĩ Ubangijin* Al'arshi, mai girma.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ya siffanta Allah da cewa bãbu abin bautãwa fãce Shi, dõmin ya kõre cancantar rãnã ga ibãda, da Ubangijin Al'arshi dõmin ya ɗebe girman gadon Bilkisu daga zukãta."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "Ya ce: \"Za mu dũba shin kã yi gaskiya ne, kõ kuwa kã kasance daga maƙaryata?\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "\"Ka tafi da takardata wannan, sa'an nan ka jẽfa ta zuwa gare su, sa'an nan kuma ka jũya daga barinsu, sa'an nan ka ga mẽne ne suke mayarwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "Ta ce: \"Yã kũ mashawarta! Lalle ne, an jẽfo, zuwa gareni, wata takarda mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "\"Lalle ita daga Sulaiman take, kuma lalle ita da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "\"Kada ku yi girman kai a gare ni, kuma ku zo mini kunã mãsu sallamãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "Ta ce: \"Yã ku mashawarta*! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai yanke wani al'amari ba, sai kun halarta.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah bai keɓance hikima ga maza kawai ba har mãtã akwai mãsu hikima a cikinsu. Sai dai Musulunci yã hana shugabancin mãtã, sabõda galibinsu ãdifarsu tã rinjãyi hankalinsu, sabõda kyautata tarbiyyar yãra. Anã fahimtar cewa iya mulki shi ne rashin fallewa da ra'ayi ga shũgaba, sai a bãyan ya shãwarci mutãnensa, kamar yadda sarauniyar Saba' ta yi da Majalisarta."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "Suka ce: \"Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umurui (da shi)?\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "Ta ce: \"Lalle sarakuna idan sun shiga wata alƙarya, sai su ɓãta ta, kuma su sanya mãsu darajar mutãnenta ƙasƙantattu. Kuma kamar wancan ne suke likatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 379,
            "translated_text": "\"Kuma lalle nĩ mai aikãwa ce zuwa gare su da kyauta, sa'an nan mai dũbawa ce: Da me manzannin zã su kõmo.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 380,
            "translated_text": "To, a lõkacin da ya jẽ wa Sulaiman ya ce: \"Shin, za ku ƙãra ni da dũkiya ne? To, abin daAllah Ya bã ni, shi ne mafi alhẽridaga abin da Ya bã ku. A'a, kũ nekuke yin farin ciki da kyautarku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 380,
            "translated_text": "\"Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 380,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã ku mashãwarta! Wannenku zai zo mini da gadonta a gabãnin su zo, sunã mãsu sallamãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 380,
            "translated_text": "Wani mai ƙarfi daga aljannu ya ce: \"Nĩ inã zo maka da shi a gabãnin ka tãshi daga matsayinka. Kuma llale nĩ a gare shi, haƙĩƙa, mai ƙarfi ne amintacce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 380,
            "translated_text": "Wanda yake a wurinsa akwai* wani ilmi daga Littafin ya ce: \"Ni inã zo maka da shi a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka.\" To, a lõkacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: \"Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne, Karĩmi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah na bãyar da asirai daga littattafai, kõ da wahayi zuwa ga Annabãwa, kõ da ilhãma daga abin da aka bai wa Annabãwa. Waɗansu sun ce ilmin nan sũnan Allah ne Mafi girma. Allah ne Mafi sani. Sai dai sharaɗin aiki da ilmi ga ĩbãda, ya kasance daga Annabãwa kawai, a cikin lõkacin aiwatar da shari'arsu.Bã a iya amfãni da wani sũnan Allah wanda wani Annabi bai zo da shi ba a gabãnin Musulunci, kuma a bãyan Musulunci."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 380,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ku canza kamar gadonta gare ta, mu gani, shin zã ta shiryu, kõ kuwa tanã kasancẽwa daga waɗanda bã su shiryuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 380,
            "translated_text": "To a lõkacin da ta jẽ aka ce \"Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?\" Ta ce: \"Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu sallamãwar (al'amari ga Allah).\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 380,
            "translated_text": "Kuma abin da ta kasance tanã bautãwa, baicin Allah, ya kange ta. Lalle ita, tã kasance daga mutãne kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 380,
            "translated_text": "Aka ce mata, \"Ki shiga a gidan sarauta.\" To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye* daga ƙwaurinta. Ya ce: \"Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai.\" Ta ce: \"Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, \"Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba.\" Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Idan ĩmãni ya shiga a cikin zũciya, sai girman kai ya fita daga gare ta sarauniya Bilkisu tanã kuranye ƙafãfunta da niyyarta ta shiga a cikin ruwa dõmin ta nũna ɗã'arta ga umurnin Annabin Allah Sulaimãn kuma ta yarda da shiga gulbin da ba ta san tsawon zurfinsa ba, kõ da za ta mutu awurin ɗã'ã da taƙawa. Mace da sarauta iyakar girman kai ke nan, bãbu abin da zai gusar da shi sai ĩmãnin gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, mun aika zuwa Samũdãwa da ɗan'uwansu, Salihu (ya ce), \"Ku bauta wa Allah.\" Sai gã su ƙungiyõyi biyu sunã ta husũma."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama?\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Suka ce: \"Munã shu'umci da kai, kuma da wanda ke tãre da kai.\" Ya ce: \"Shu'umcinku a wurin Allah yake. Ã'a, kũ mutãne ne, anã fitinar ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Kuma waɗansu jama'a tara* sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su kyautatãwa. Suka ce: \"Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa,** shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Yawan mãsu ɓarnã bã ya hana gaskiya bayyana. Kuma mai mãkirci dõmin ya halakar da mai gargaɗin addinin Allah, yanã yi wa kansa sanadin halaka kawai ne. Waɗannan mutãne tara sun yi niyyar kashe Sãlihu ne, bã da sanin danginsa ba, a wurin dayake kwãna yanã salla a masallacinsa, a bãyan gari. A can Allah ya halakar da su. Wannan shĩ ne sakamakon mãkircin da suka ƙulla.  ** Zã mu kwãnan masa, ai zãmu kwãna da niyyar kashe shi a cikin dare, a ɓõye."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Kuma suka ƙulla mãkirci, kuma Muka ƙulla sakamakon mãkirci, alhãli sũ ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Ka dũba yadda ãƙibar mãkircinsu ta kasance lalle Mũ Mun darkãke su da mutãnensu, gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Waɗancan, gidãjensu ne, wõfintattu sabõda zãluncin da suka yi, lalle ne a wancan akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke sani."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sun kasance sunã taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Da Lũdu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, \"Shin kunã jẽ wa alfasha* ne, alhãli, kuwa kunã gani?\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "\"Shin lalle kũ haƙĩƙa kunã je wa maza da sha'awa baicin mãtã? Ã'a, kũ wasu irin mutãne ne kuna aikin jãhilci.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Alfãshar mutãnen Lũɗu, ita ce luwãɗi, namji yabi namiji a duburarsa wannan alfãsha, kõ dabbõbi bã su yin ta. Ga mutãnen Lũɗuta fãra bayyana. Allah Ya halakar da su kamar yadda Ya ambata. Sa'an nan kuma ba a ƙãra ganinta ba, sai ga wannan al'umma asĩirin da ke ciki, shĩ ne yadda Allah Yake jũyar da ɗabĩ'ar mutum ta zama bã ta mãsu hankali ba, tãre da dõgewar halittar jikinsa kamar yadda take ga zãhiri."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 381,
            "translated_text": "Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 382,
            "translated_text": "Bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa fãce suka ce \"Ku fitar da mutãnen Lũɗu daga alƙaryarku, lalle sũ, wasu irin mutãne ne mãsu da'awar sunã da tsarki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 382,
            "translated_text": "Sai Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa,* fãce mãtarsa, Mun ƙaddara ta a cikin mãsu wanzuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mutãnensa mũminai. Ĩmãni da gaskiya idan gaskiya ta bayyana asĩri ne daga asĩran Allah sai wanda Ya bai wa. Kusanci ga wani Annabi da aure kõ zumunta, bã ya bãyar da shi. Ruwan azãba, shĩ ma asĩri ne na Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 382,
            "translated_text": "Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa. To, ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 382,
            "translated_text": "Ka ce: \"Godiya ta tabbata ga Alah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa, waɗanda Ya zãɓa.\" Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi?*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Daga wannan ãyã ta 59 zuwa ƙarshen Sũra, duka tambĩhi ne ga abũbuwan fake na ilmin Allah, wanda ya shãfi jikunanmu, amma ba mu san yadda suke aukuwa a gare mu ba. Sa'an nan kuma da tambĩhi ga abũbuwan gaibi da suke zuwa dõmin mu yi ĩmãni da su."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 382,
            "translated_text": "Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa (Allah da wani)."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 382,
            "translated_text": "Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 382,
            "translated_text": "Kõ wãne ne yake karɓã, kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 382,
            "translated_text": "Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku, kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita, kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: \"Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Ka ce: \"Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: \"Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "\"Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi take?\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Kuma sunã cẽwa, \"A yaushe wannan wa'adi (zai auku), idan kun kasance mãsu gaskiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Ka ce: \"Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta* a gare ku.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Kuturi, shi ne a bãyan wani ya hau dabba ya kuma aza wani a kanta daga bãya gare shi. Kinaya ce na cewa abin yanã kusa gare su ƙwarai, kamar tsakãnin ɗan kuturi da mahayin dabba."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kanmutãne kuma amma mafi yawansu, bã su gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Kuma bãbu wata (mas'ala) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 383,
            "translated_text": "Lalle ne wannan Alƙur'ãni* yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Idan wannan Alƙur'ani ya ƙunsã ilmin asĩrai da yake iya gaya wa Banĩ Israĩla mafi yawan abin da sũ da kansu, suke sãɓã wa jũna a kansu, tãre da shahararsu da ilmi, da yawan Annabãwan da suka wuce a cikinsu, to, ga Lãrabãwa jãhilai hiyãka ke nan. Bãbu abin da ya wajaba a gare su, sai sallamawa ga abin da yake kiran zuwa gare shi. In abin da yake faɗa ba gaskiya ba ne, dã Banĩ Isrãĩla ne farkon mãsu nũna ƙaryarsa. Ammã ba su yi ba. Sabõda haka duka gaskiya ne. Sai kõwa ya bĩ shi ya tsĩra."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "\"Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne Mabuwãyi, Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa (al'amari zuwa ga Allah)."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba* daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa \"Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wata dabba ce anã kiranta Jassãsa an ce 'yar rãƙumar Sãlihu ce a lõkacin da aka kashe uwarta, ta gudu, ta shiga cikin dũtse' dũtsen ya rufe da ita. Tanã fitõwa daga dũtsen Safa a Makka da hantsi. Bãyan fitõwarta, bãbu sauran wa'azi. Mũmini ya tabbata mũmini kãfiri kuma ya tabbata haka. Tanã riƙe da sandar Mũsã da Hãtimin Sulaimãn. Tana fitõwa a bãyan fitõwar rãnã daga yamma. Allah ɗai Ya san gaskiyar yadda take."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. (ga kõra)"
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Har idan sun zo, (Allah) zai ce, \"Ashe kun ƙaryata ãyõyinNa, kuma ba ku kẽwaye su da sani ba? To, mẽne ne kuka kasance kunã aikatãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Kuma magana ta auku a kansu, sabõda zãluncin da suka yi. To, sũ bã su da ta cẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa, kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne waɗanda suka yi ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Kuma da rãnar* da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bãyan fitõwar dabba, kuma sai bũsar ƙahõ na farkõ, sa'an nan na biyu sa'an nan Ƙiyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 384,
            "translated_text": "Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi, Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita,* a yinin nan, amintattu ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Firgita daga azãbar Lãhira, wannan firgita ba irin ta farko ba ce wadda aka ambata a cikin ãyã ta 87, dõmin wancan firgitar kwarjini ce a bãyan tãshi daga kaburbura."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "(Ka ce): \"An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari,* Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan Gari shĩ ne Makka. Sanya Makka hurumi ba a iya shiga cikinsa da yãki yanã a cikin ashĩrai na Allah. Shiryuwa da ɓata duka asĩrai ne na Allah. Tsãrin Alƙur'ani da abubuwan da ya ƙunsa duka asĩran Allah ne."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "\"Kuma inã karanta Alƙur'ãni.\" To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: \"Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake.\""
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 27,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "Kuma ka ce: \"Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu.\" Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "¦. S̃. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 385,
            "translated_text": "Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 386,
            "translated_text": "Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 386,
            "translated_text": "Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi, kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 386,
            "translated_text": "Sai mutãnen Fir'auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 386,
            "translated_text": "Kuma matar* Fir'auna ta ce (\"Ka bar shi yanã) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, kõ mu riƙe Shi ɗã,\" alhãli kuwa sũ ba su sansance ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sunan mãtar Fir'auna Ãsiya, tanã da zumunta da Mũsã. Tace ka yi masa sũna 'Mũshã,' ma'anarsa an same shi tsakãnin \"mũ,\" wãtau ruwa da \"shã\" watau itãce, sa'an nan ya zama Mũsã. Allah Yanã tsare mutum gaba ga maƙiyinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 386,
            "translated_text": "Kuma zuciyar uwar Mũsã ta wãyi gari yõfintatta.* Lalle ne, haƙĩƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, bã dõmin Mun ɗaure zũciyarta ba, dõmin ta kasance daga mũminai.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Zũciya yõfintatta, ita ce wadda bã ta da wani tunãni sabõda abin da ya shagaltar da ita na tunãnin ɗanta a hannun maƙiyinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 386,
            "translated_text": "Kuma ta ce wa 'yar'uwarsa,* \"Ki bĩ shi.\" Sabõda haka sai ta lẽƙe shi daga gẽfe, alhãli sũ ba Su sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sũnan 'yar'uwar Mũsã Maryamu ko Kalsuma ko Kalsumu. Sũnan uwarsu Yũhãniz ɗiyar Hãmid ɗan Lãwaya ɗan Yãƙũbu."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 386,
            "translated_text": "Kuma Muka hana masa mãsu shãyai da mãma, a gabãnin haka sai ta ce: \"Kõ in nũnamuku mutãnen wani gida, su yi muku renonsa alhãli kuwa su mãsu nasĩha ne a, gare shi?\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 386,
            "translated_text": "Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa dõmin idanunta su yi sanyi, kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba, kuma dõmin ta san cẽwa lalle wa'adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 387,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci* da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan ya nũna, cewa Mũsã an bã shi Annabci a gabãnin ya yi hijira zuwa Madyana. Kuma yanã ƙãra ƙarfafa wannan magana abin da ke cikin ãyã ta 16 inda ya rõƙi Allah gãfara, Ya gãfarta masa, da ãyã ta l7 wadda ta nũna ya san an yi masa gãfarar har yanã neman tsari dõmin kada ya kõma yin haka a gaba. Annabãwa sunã wahami ga abin da bã wahayi ba, sa'an nan Allah Ya gyãra kuskuren, Ya tabbatar da gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 387,
            "translated_text": "Kuma sai ya shiga garin a lõkacin da mutãnen garin suka shagala, sai ya sãmu, a cikin garin, waɗansu maza biyu sunã faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa, sai Mũsã ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: \"Wannan aikin Shaiɗan ne, dõmin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne!\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 387,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya Uhangijĩna! Lalle na zãlunci kaina, sai Ka yi mini gãfara.\" Sai Ya gãfarta masa, dõmin Shĩ ne Mai yawan gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 387,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijĩna! Dõmin abin da Ka ni'imta shi a kaina, sahõda haka bã zan kasance mai taimako ga mãsu laifi ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 387,
            "translated_text": "Sai ya wãyi gari a cikin birnin yanã mai tsõro, yanã sauna. Sai ga wanda ya nẽmi taimako daga gare shi a jiya, yanã nẽman ãgajinsa. Mũsã ya ce masa, \"Lalle kai ɓatacce ne, bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 387,
            "translated_text": "To, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce,* \"Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa** a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ya faɗi haka zaton Mũsã zai kashe shi ne sabõda gargaɗin da ya gabãtar a gareshi, Maganar ta nũna Mũsã ya shahara da son gyãran abũbuwa dõmin islãhi, haka ne ga al'adar mutãne wanda ya tãshi yanã gyãra sai sun tuhumce shi da neman girma. ** Tanƙwasa ce sanya mutãne su yi abin da bã Su son yi. Kyautatãwar islãhi bã ta sãmuwa sai da tanƙwasãwa dõmin gãlibi mutãne sun fi son ɓarna a kan kyautatãwa tãre da saninsu ga cewar kyautatãwar ita ce daidai."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 387,
            "translated_text": "Kuma wani mutum ya zo daga mafi nĩsan birnin yanã taliya da gaggãwa, ya ce: \"Ya Mũsã! Lalle mashãwarta sunã shãwara game da kai dõmin su kashe ka sabõda haka ka fita. Lalle nĩ, mai nasĩha ne a gare ka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 387,
            "translated_text": "Sai ya fita daga gare ta,* yanã mai jin tsõro yanã sauna. Ya ce: \"Ya Ubangijĩna! Kã tsẽrar da ni daga mutãne azzãlumai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ya fita daga alƙaryar."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 388,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da ya fuskanci wajen Madyana, ya ce: \"Inã fatan Ubangijĩna Ya shiryar da ni a kan madaidaiciyar hanya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 388,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: \"Mẽne ne shã'aninku?\" Suka ce, \"Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho* ne mai daraja.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sabõda girma bã ya zuwa ya shãyar da tumakinsa, sai ya sanya mu, mu 'ya'yansa, kõ da muke mãtã. Wannan ya nũna mace tanã yin aikin maza sabõda larũra. Kuma sabõda darajar ubansu ba su shiga a cikin makiyãya ba dõmin tsaron mutuncinsu don haka ake son asali mai kyau. NĩSantarsu daga maza nau'in ƙauracewa ne na sharĩ'a."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 388,
            "translated_text": "Sai ya shãyar musu, sa'an nan kuma ya jũya zuwa ga inuwa, sa'an nan ya ce: \"Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 388,
            "translated_text": "Sai ɗayansu ta je masa, tanã tafiya a kan jin kunya, ta ce, \"Ubãna yanã kiran ka, dõmin ya sãka maka ijãrar abin da ka shãyar sabõda mu.\" To, a lõkacin da ya je masa, ya gaya masa lãbãrinsa, ya ce: \"Kada ka ji tsõro, kã tsĩra daga mutãne azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 388,
            "translated_text": "¦ayarsu ta ce, \"Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi* amintacce.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau tanã iShãra ga ubantada cewa Mũsa ya tãra siffõfin nan biyu na ƙarfi da amãna dõmin abin da ta jarraba daga gare shi kafin ya iso ga ubanta."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 388,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle ne inã nufin in aurar da kai ɗayan 'yã'yãna biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijãra shẽkara takwas to, idan ka cika gõma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsanantã maka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga sãlihai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 388,
            "translated_text": "Ya ce: \"Wannan yanã a tsakanina da tsakãninka kõwane ɗayan adadin biyun na ƙãre, to, bãbu wani zãlunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 389,
            "translated_text": "To, a lokacin da Mũsã ya ƙãre adadin kuma yanã tafiya da iyãlinsa, sai ya tsinkãyi wata Wutã daga gẽfen dũtse (¦ũr). Ya cewa iyãlinsa, \"Ku dãkata, lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wutã, tsammãnĩna ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani lãbãrĩ, kõ kuwa da guntun makãmashi daga Wutar don kõ ku ji ɗimi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 389,
            "translated_text": "To, a lõkacin da ya jẽ wurinta (Wutar) aka kirã shi, daga gẽfen rãfin na dãma, a cikin wurin nan mai albarka, daga itãciyar (cẽwa) \"Ya Mũsã! Lalle Nĩ ne Allah Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 389,
            "translated_text": "\"Kuma ka jẽfa sandarka.\" To, a lõkacin da ya gan ta, tanã girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya jũya yanã mai bãyar da bãya, bai kõma ba. \"Ya Mũsã! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsõro lalle ne kanã daga waɗanda ke amintattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 389,
            "translated_text": "\"Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, ba da wata cũta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kãfaɗunka, dõmin tsõro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abũbuwa dalĩlai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da 'yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutãne ne fãsiƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 389,
            "translated_text": "Ya ce: \"Yã Ubangijĩna! Lalle nã kashe wani rai daga gare su, dõmin haka inã tsõron kada su kashe ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 389,
            "translated_text": "\"Kuma ɗan'uwana Hãrũna shĩ ne mafi fasãha daga gareni, ga harshe, sabõda haka Ka aika shi tãre da ni, yanã mai taimako, yanã gaskata ni, lalle ne inã tsõron su ƙaryata ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 389,
            "translated_text": "Ya ce: \"Zã Mu ƙarfafa damtsenka game da ɗan'uwanka kuma Mu sanya muku wani dalĩli, sabõda haka bã zã su sãdu zuwa gareku ba, tãre da ãyõyinMu, kũ da waɗanda suka bĩ ku ne marinjãya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 390,
            "translated_text": "To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: \"Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 390,
            "translated_text": "Kuma Mũsã ya ce: \"Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 390,
            "translated_text": "Kuma Fir'auna ya ce: \"Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka* (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Fir'auna ya fãra yin gasasshen tũbali da ake cewa ajurru, aka gina masa dõgon bene, ya hau samansa, ya harba kibiya ta tafi ama, ta kõmo da jini. Saĩ ya ce: \"yã kashe Ubangijin Mũsa.\" Bayan haka sai benen ya karye guntu uku' guntu ɗaya ya fãɗa wa sõjansa, da yawa daga cikinsu suka mutu, guntu ɗaya kuma ya fãɗa a cikin ruwa, sauran guntu ɗaya ya fãɗa wa magina, suka mutu. Kuma cewar Fir'auna, \"Lalle ne nĩ, inã zuton Mũsã daga maƙaryata,\" ya nũna girman kansa kawai ne ya hana shi ĩmãni, ba rashin gãnewa ba, sai dai kuma sun ga kamar bãbu Tãshin Ƙiyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 390,
            "translated_text": "Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 390,
            "translated_text": "Sai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 390,
            "translated_text": "Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta, kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 390,
            "translated_text": "Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 390,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 391,
            "translated_text": "Kuma ba ka kasance ba ga gẽfen rãfi na yamma a lõkacin da Muka hukunta al'amaru zuwa ga Mũsã, kuma ba ka kasance daga halartattu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 391,
            "translated_text": "Kuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa (da kai game* da waɗancan lãbarai).<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sanin waɗannan abũbuwa duka ga Ummiyyi a wuri mai nĩsa daga wurin da abin ya auku a ciki, da kuma nĩsa daga waɗanda abin ya fi shãfuwa, ya nũna gaskiyar abin da kake da'awa. Kuma yanã natsar da zũciyarka da zũciyar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira tãre da ku, cewa sunã cikin tsaron Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 391,
            "translated_text": "Kuma ba ka kasance ga gẽfen dũtse ba a lõkacin da Muka yi kira, kuma amma dõmin rahama daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabãninka bai je musu ba, tsammãninsu sunã tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 391,
            "translated_text": "Kuma bã dõmin wata masĩfa ta sãme su ba sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, su ce: \"Yã Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bĩn ãyõyinKa, kuma mu kasance daga mũminai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 391,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga wurinMu, suka ce: \"Don me ba a bã shi kamar abin da aka bai wa Mũsã ba?\" Shin kuma ba su kãfirta ba da abin da aka bai wa Mũsã a gabãnin (wannan)? suka ce: \"Sihirõri biyu ne suka taimaki jũna,\" kuma suka ce: \"Lalle ne mũ, mãsu kãfirta ne ga dukansu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 391,
            "translated_text": "Ka ce: \"To ku zo da wani littãfi daga, wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bĩ shi, idan kunkasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 391,
            "translated_text": "To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 392,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sãdar* da magana sabõda su, tsammãninsu, suna tunãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Attaura da Alƙur'ãni. Ayyukan Annabawa sãshenSu sun sãdu da sãshe."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 392,
            "translated_text": "Waɗanda Muka bã su littãfi daga gabãninsa (Alƙur'ãni), su mãsu ĩmãni ne da shi.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mun sãdar da ilmin Taurãta da ilmin Alƙur'ãni, kowãne ya gaskata wani, ko kuwa Mun sãdar da maganar Alƙur'ani, wata ta bi wata, babu bambanci ga fasãha da abũbuwan ban mãmaki a cikinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 392,
            "translated_text": "Kuma idan anã karanta shi a kansu, sai su ce: \"Mun yi ĩmãni da shi, lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinmu. Lalle mũ, mun kasance a gabãninsa masu sallamãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 392,
            "translated_text": "Waɗancan anã ba su lãdarsu sau biyu, sabõda haƙurin da suka yi, kuma da kyautatãwa suna tunkuɗewar mũnanãwa kuma daga abin da Muka azũrtã susunã ciyarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 392,
            "translated_text": "Kuma idan sun ji yãsassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, \"Ayyukanmu sunã a gare mu, kuma ayyukanku sunã a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu bã mu nẽman jãhilai (da husũma).\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Waɗanda aka bai wa littafi a gabãnĩn Alƙur'ãni, sũ ne Yahũdu da Nasãra,waɗansu daga cikin Malamansu sun musulunta, kamar Abdullahi bn salãmi daga Yahũdu, da Nasãran Najrãna daga Nasãra, sun musulunta. Idan ba'ali ya musulunta sai a ce dukansu ke nan sun musulunta, sai wanda ya yi girman kai ya ƙigaskiya. Bã zã a kula da shi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 392,
            "translated_text": "Lalle ne kai bã ka shiryar* da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, ya kasance yanã son mutãnensa Ƙuraishãwa su shiryu har dai Amminsa Abu Talib, sai Allah Ya gaya masa cewa shiriya ga hannunsa take, shi kaɗai, kuma sai wanda Ya so, shi ne zai shiryu, amma kuma akwai daga cikin dalĩlai bayyanannu maganar hijira kamar yadda ãyar da ke tafe ta bayyana."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 392,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Idan mun bi shiriya tãre da kai anã fizge mu(5) daga ƙasamiu.\" Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, anã jãwõwa zuwa gare shi, 'ya'yan itãcen kõwane iri, bisa ga azurtãwa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Wanda ya makkana musu Hurumi ya zama amintacce, yanã iya tsare bãwanSa kuma Yabã shi arziki a kõ'ina yake a cikin ƙasa, sabõda haka tsõron fita daga Hurumi da tsõron wuyar abinci a wurin baƙunci, bã zai hana mũmini ya yi hijira da addininsa ba zuwa wurin yardar Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 392,
            "translated_text": "Kuma da yawa Muka halakar da wata alƙarya wadda ta yi butulci ga rãyuwarta. To, waɗancan gidãjensu ne, ba a zaune su ba, a bãyansu, fãce kaɗan. Kuma mun kasance Mũ ne Magãda."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 392,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryu ba, sai Ya aika a cikin hedkwatarsu da wani Manzo yanã karanta ãyõyinMu a kansu. Kuma ba Mu kasance Mãsu halaka alƙaryu ba, fãce mutanensu sun kasance mãsu zãlunci."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Kuma abin da aka bã su daga kõme, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne da ƙawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shĩ ne mafi alhẽri, knma mafi wanzuwa. Shin bã ku hankalta?"
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Shin fa, wanda Muka yi wa wa'adi, wa'adi mai kyau, sa'an nan shĩ mai haɗuwa da shi ne, yanã zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan dãɗi, dãɗin rãyuwar dũniya, sa'an nan shi a Rãnar ¡iyãma yanã daga mãsu shiga wuta?"
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Kuma rãnar da (Allah) Yake kiran su sa'an nan Ya ce: \"Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Waɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: \"Yã Ubangijinmu! Waɗannan sũ ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mũ suke bautã wa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Kuma a ce ku kirãwo abõkan tãrayyar ɗinku, sai su kira su, sai ba su amsa ba, kuma su ga azãbar. Dã dai lalle su sun kasance snnã shiryuwa*!<br \/>\n____________________<br \/>\n   * An shãfe jawãbi. ƘaddarawarSa ita ce: \"Dã Sun kaSance sunã shiryuwa a dũniya, dã ba su gan ta ba a Lãhira.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Kuma rãnar da Yake kiran su, sa'an nan Ya ce: \"Mẽne nekuka karɓa wa Mananni?\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Sai lãbãru su ɓace musu a rãnar nan sa'an nan bã zã su tambayi jũnaosu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "To, amma wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni' ya aikata aiki na ƙwarai, to, akwai fãtan su kasance daga mãsu cin nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinka Yanã halitta abin da Yake so kuma Yake zãɓi. Zãɓi bai kasance a gare su ba. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinka Yanã sanin abin da zukãtansu ke ɓõyẽwa, da abin da suke bayyanãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 393,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne Allah, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kuma Shi ne abin gõdiya a cikin ta farko (dũniya), da ta ƙarshe (Lãhira). Kuma Shi ne da hukunci, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 394,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, bã ku ji?\""
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 394,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kunã natsuwa a cikinsa? Shin fa, bã ku gani?\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 394,
            "translated_text": "\"Kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini dõmin ku natsu a cikinsa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde.\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 394,
            "translated_text": "Kuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: \"Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bãyan Allah Ya tunãtar da Musulmi rahamarSa da kaɗaita ga bãyar da ni'ima kõ hana ta da siffõfi mãsu kwaɗaitar da mũmini ga ɗã'a ga Allah da ManzonSa, daga cikin ɗã'ã akwai yin hijira wanda yake shĩ ne kan lãbãrin sũrar, sai kuma Ya tsõratar da mai bin wanin Allah ga rashin yin hijira. Duka abin da ya hana mũminai hijira idan shi abin nan ba uzuri ne na shari'a ba, to, ya zama gunki, abin bautãwa, wanin Allah. Umurnin da ya sãɓa wa umurnin Allah duka, umurnin abõkin tãrayya ne ga Allah ga wanda ya bĩ shi."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 394,
            "translated_text": "Kuma Muka zãre mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan Muka ce: \"Ku kãwo dalilinku.\" Sai suka san cẽwa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya ɓace daga barinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 394,
            "translated_text": "Lalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita* daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a** ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, \"Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Asalin baghy zãlunci, amma ga izɗilãhi, shi ne fita daga ɗã'ar shugaban Musulmi. ** Yawan su saba'in, an ce arba'in, kuma an ce gõma."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 394,
            "translated_text": "\"Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa,* lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ɓarna a cikin ƙasa, shi ne fita daga tsarin jama'a, da rabasu ƙungiya-ƙungiya, ko barin hijira a bãyan an yi umurni da yin ta."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 395,
            "translated_text": "Ya ce: \"An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai.\" Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba?*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Yanã ganin dũkiyar da ya samu, ya sãme ta ne sabõda ya san ilmin fatauci da sana'a kuma yanã da ƙarfin neman dũkiyar, sabõda raddin irin tunãninsa Allah Ya ce Ya halaka wanda ya fi shi tsananin ƙarfi da ƙõƙarin tãra dũkiya, kuma idan Ya tãshi halaka mai laifi bã Ya tsayãwa tambayarsa dalĩlin da ya sa ya yi laifin kãfin Ya halakar da shi. Waɗannan abũbuwa uku sun isa ga mai dũkiya ya yi tunãni, dõmin kada annashuwa ta shige shi ya ƙi gõde waAllah."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 395,
            "translated_text": "Sai (¡ãrũna) ya fita a kan mutãnensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rãyuwar dũniya suka ce: \"Inã dai munã da kwatancin abin da aka bai wa ¡ãrũna! Lalle shĩ haƙĩƙa ma'abũcin rabo babba ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 395,
            "translated_text": "Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: \"Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai,* kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai ha ƙuri.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * ĩmãni da aikin ƙwarai wanda Allah Ya yi umurni da a yi shi, kuma yinsa kamar yadda ManzonSa ya nũna. Akwai daga cikin aikin ƙwarai yin hijira da barin kula da dũkiya. Bã a sãmun sakamakon Allah sai da haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 395,
            "translated_text": "Sai Muka shãfe ƙasa* da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* An ce a bãyan Ƙãrũna ya yanke kansa da nasa mutãne daga Mũsã, sai ya shirya da wata kãruwa dõmin ta yi wa Mũsã ƙazafin cewa ya yi zina da ita, a kan ya aure ta. Sai Mũsãya tãshi yanã wa'azi a cikin Banĩ Isrã'ĩla ya ce: \"Yã Banĩ Isrã'ĩla wanda ya yi sãta zã mu yanke hannunsa, wanda yayi ƙazafi mu yi masa bũlãla tamãnin, wanda ya yi zina, bã ya da mãtã, mu yi masa bũlãla ɗãri, wanda ya yi zina yanã da mãtã, mu jefe Shi sai yã mutu.\" Sai Ƙãruna ya ce: \"Kõ dã kai ne?\" Ya ce: \"Kõ da ni ne.\" Sai Kãrũna ya ce: \"An ce kã yi fãjirci tãre da wance, kãruwa.\" Sai Mũsã ya ce: \"A kirã ta\" Da ta zo, ya gama ta da Allah, ta faɗi gaskiya, sai ta ce Ƙãrũna ne ya yi tsãda da ita, ta faɗi hakanan. Sai Mũsã ya yi addu'a a kansa, ƙasa ta haɗiye shi, shi da gidansa duka."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 395,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi bũrin matsayinsa a jiya suka wãyi gari sunã cẽwa, \"Wai! Allah Yanã shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bãyinsa, kuma Yanã ƙuntatãwa. Bã dõmin Allah Ya yi mana falala ba dã Yã shãfe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kãfirai bã su cin nasara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 395,
            "translated_text": "Wancan gidan Lãhira Munã sanya shi ga waɗanda suke bã su nufin ɗaukaka a cikin rãyuwar dũniya kuma bã su son ɓarna. Kuma ãkiba ga mãsu taƙawa take."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 395,
            "translated_text": "Wanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alhẽri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mũgun abu, to, bã zã a sãkawa waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka ba, fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma. ka ce: \"Ubangijĩna ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "Kuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako* ga kãfirai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Taimakon, shi ne ka yi bũrin musuluntarsu har ka wahala dõmin a sauƙaƙe ma hukuncin hijira wadda Allah Ya yi umurni da a yi ta a bãyan musulunta sai ka iyar da Manzanci, shiryarwa kuwa ga hannun Allah take. Wannan ãyã tanã nunãwa bayyana ƙaryar mãsu da'awar cewa wani mutum yanã bai wa wani ĩmãni ko ya karɓe shi daga gare shi. Kõwa a cikin tsõro yake, sai wanda Allah Ya sanya shi cikin aminci. Allah Ya sanya mu cikin amincinSa dõmin rahamarsa. "
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "Kuma kada lalle su karkatar da kai daga barin ãyõyin Allah, a bãyãn har an saukar da su uwa gare ka. Ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma kada lalle ka kasance daga mãsu shirka."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 28,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "Kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kõwane abu mai halaka ne fãce fuskarSa. Shi ne da hukunci kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ãyã ta ƙarshen sũrar, ta tãra ilmin da sũrar ta karantar a cikin abũbuwa biyar da ta zãna"
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "A. L̃. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "Ashe, mutãne sun yi zaton a bar su su ce: \"Mun yi ĩmãni,\" alhãli kuwa bã zã a Jarrabe su ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabãninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "Kõ waɗanda ke aikata miyãgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke hukuntãwa ya mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "Wanda ya kasance yanã fãtan gamuwa da Alah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne, kuma (Allah) Shĩ ne Mai ji, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 396,
            "translated_text": "Kuma wanda ya yi jihãdi, to, yanã yin jihãdin ne dõmin kansa. lalle Allah haƙĩƙa waɗatacce ne daga barin tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 397,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã kankare musu miyãgun ayyukansu, kuma lalle Munã sãka musu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 397,
            "translated_text": "Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatãwa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta maka dõmin ka yi shirki da Ni game da abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'ã. Zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 397,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã shigar da su a cikin mutãnen kirki."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 397,
            "translated_text": "Kuma daga cikin mutãne akwai mai cẽwa, 'Mun yi ĩmãni da Allah\" sa'an nan idan aka cũce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutãne kamar azãbar Allah kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙĩƙa, ya kan ce: \"Lalle mũ mun kasance tãre da ku.\" shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin ƙirãzan halittunSa?"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 397,
            "translated_text": "Kuma lalle Allah na sanin waɗanda suka yi ĩmãni kuma lalle Yanã sanin munfukai."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 397,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, \"Ku bi hanyarmu, kuma Mu ɗauki laifuffukanku,\" alhãli kõwa ba su zamo mãsu ɗauka da a kõme ba daga laifuffukansu. Lalle sũ maƙaryata ne."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 397,
            "translated_text": "Kuma lalle sunã ɗaukar kãyan nauyinsu da waɗansu nauyãyan kãya tãre da kãyan nauyinsu, kuma lalle zã a tambaye su a Rãnar ¡iyama game da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 397,
            "translated_text": "Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu fãce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfãna) ta kãmã su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 398,
            "translated_text": "Sa'an nan Muka tsĩrar da shi da mutãnen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama wata ãyã ga tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 398,
            "translated_text": "Da Ibrãhĩm a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, \"Ku bautã wa Allah ku bĩ Shi da taƙawa. Wannan Shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 398,
            "translated_text": "\"Abin da dai kuke bautãwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya. Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bã su mallakã muku arziki. Sabõda haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gõdiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 398,
            "translated_text": "\"Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummõmi a gabãninku sun ƙaryata, kuma bãbu abin da ke kan Manzo, fãce iyar da manzanci, iyarwa bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 398,
            "translated_text": "Shin, ba su* ga yadda Allah ke fãra yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ga wata ƙirã'a, ba ku ga da Iamĩrin abõkan magana waɗanda Ibrahĩm ke yi wa magana. A kan wannan ƙirã'a, maganar Ibrãhĩm ba ta yanke ba har ƙarshen ãya ta 23"
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 398,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin halitta, sa'an nan kuma Allah Yanã ƙãga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 398,
            "translated_text": "\"Yanã azabta wanda Ya so, kuma Yanã jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake jũyaku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 398,
            "translated_text": "\"Yanã azabta wanda Ya so, kuma Yanã jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake jũyaku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 398,
            "translated_text": "\"Kuma ba ku zamo mãsu buwãya ba a cikin ƙasã, kuma haka a cikin sama kuma bã ku da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 399,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan sunã da wata azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 399,
            "translated_text": "Sa'an nan bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa (Ibrãhĩm) fãce dai suka ce: \"Ku kashe shi kõ, ku ƙõnã shi,\" Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wutã. Lallea cikin wannan akwai ayõyi ga mutãnen da ke yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 399,
            "translated_text": "Kuma Ibrahĩm ya ce \"Bãbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumãka sabõda sõyayyar tsakãninku a cikin rãyuwar dũniya, a'an nan a Rãnar ¡iyãma sãshinku zai kãfirce wa sãshi, kuma makõmarku ita ce wutã kuma bã ku da waɗansu mataimaka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 399,
            "translated_text": "Sai Lũɗu ya yi ĩmãni da shi. Kuma Ibrãhĩm ya ce: \"Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 399,
            "translated_text": "Kuma Muka bã shi Ishãƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littãfi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun bã shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lãhira, tabbas, yanã a cikin sãlihai."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 399,
            "translated_text": "Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa, \"Lalle kũ, haƙĩƙa kunã jẽ wa alfãsha wadda wani mahalũƙi daga cikin dũniya bai riga ku gare ta ba."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 399,
            "translated_text": "\"Ashe, lalle kũ kunã je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin majalisarku da abin da bã shi da kyau? To, jawãbin mutãnensa bai kasance ba fãce dai sun ce: 'Ka zo mana da azãbar Allah, idan ka kasance daga mãsu gaskiya.'\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 400,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni a kan mutãnen nan maɓarnata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 400,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka jẽ wa Ibrãhĩm da bushãra suka ce: \"Lalle mu mãsu halaka mutãnen, wannan alƙarya ne. Lalle mutãnenta sun kasance mãsu zãlunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 400,
            "translated_text": "Ya ce: \"Lalle akwai Lũɗu a cikinta!\" Suka ce: \"Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke a cikinta, lalle munã tsĩrar da shi da mutãnensa, fãce fa mãtarsa ta kasance a cikin mãsu wanzuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 400,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka je wa Lũɗu ya ɓãta rai sabõda su, kuma yã ƙuntata ga kirji sabõda su. Kuma suka ce: \"Kada ka ji tsõro kuma kada ka yi baƙin ciki lalle mũ mãsu tsĩrar da kai ne da iyãlanka, fãce dai matarka ta kasance daga mãsu wanzuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 400,
            "translated_text": "\"Lalle mũ, mãsu saukar da azãba ne daga sama a kan mutãnen wannan alƙarya sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 400,
            "translated_text": "Kuma lalle Mun bar wata ãyã bayyananna daga gare ta ga mutãne mãsu hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 400,
            "translated_text": "Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: \"Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Rãnar Lãhira, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasã, alhãli kuwa kunã mãsu lãlãtarwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 400,
            "translated_text": "Sai suka ƙaryata shi, sabõda haka tsãwa ta kãmã su, dõmin haka suka wãyi gari sunã guggurfãne."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 401,
            "translated_text": "Da Ãdawa da Samũdãwa alhãli kuwa lalle alãmun azãba sun bayyana a gare su daga gidãjensu kuma Shaiɗan ya ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance mãsu basĩra!"
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 401,
            "translated_text": "Kuma ¡ãrũna da Fir'auna da Hãmãna, kuma lalle Mũsaya je musu da hujjõji, sai suka yi girman kai a cikin ƙasã kuma ba su kasance mãsu tsẽrẽwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 401,
            "translated_text": "Sabõda haka kõwanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsãwa ta kãmã, kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasã da shi kuma daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar. Bã ya yiwuwa ga Allah Ya zãlunce su, amma sun kasance kansu suke zãlunta."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 401,
            "translated_text": "Misãlin waɗanda suka riƙi waɗansu masõya waɗanda bã Allah ba, kamar misãlin gizõgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhãli kuwa lalle mafi raunin gidãje, shĩ ne gidan gizogizo, dã sun kasance sunã sane."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 401,
            "translated_text": "Lalle Allah Yanã sane da abin da suke kira wanda bã Shi ba na wani abu duka kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 401,
            "translated_text": "Kuma waɗancan misãlan Munã bayyana su ga mutãne kuma bãbu mai hankalta da su sai mãsu ilmi."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 401,
            "translated_text": "Allah Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle cikin wancan akwai ãyã ga mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 402,
            "translated_text": "Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littãfi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abni ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 402,
            "translated_text": "Kada ku yi jayayya da mazowa Littãfi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, kuma ku ce, \"Mun yi ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautãwarmu da Abin bautãwarku Guda ne, kama mũ mãsu sallamãwa ne a gare shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 402,
            "translated_text": "Kuma kamar haka Muka saukar da Littafi a gare ka, to, waɗannan da Muka bai wa Littãfi sanã ĩmãni da shi, daga cikin wãɗannan akwai mai ĩmãni da shi, kuma bãbu mai musun ãyõyinMu, fãce kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 402,
            "translated_text": "Kuma ba ka kasance kana karãtun wani littãfi ba a gabãninsa, kuma bã ka rubũtunsa da dãmanka dã haka yã auku, dã mãsu ɓarnã sun yi shakka."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 402,
            "translated_text": "Ã'a, shĩ ãyõyi ne bayyanannu a cikin ƙirãzan waɗanda aka bai wa ilmi. Kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 402,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Don me ba a saukar masa da ãyõi ba daga Ubangijinsa? \"Ka ce: \"Su ãyõyi a wurin Allah kawai suke, kuma lalle ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 402,
            "translated_text": "Shin bai ishe su ba cẽwa lalle Mũ, Mun saukar da Littãfin akanka, anã karanta shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙĩƙa akwai rahama da tunãtawa ga mutanen da ke yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Ka ce: \"Allah Yã isa shaida a tsakãnĩna da tsakãnĩnku Yanã sane da abin da ke a cikin sammai da ƙasã, kuma waɗanda suka yi ĩmãni da ɗarya kuma suka kãfirta da Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Kuma suna nẽman ka da gaggauta azãba, to, bã dõmin ajali ƙayyadadde ba, dã azãba ta jẽ musu kuma lalle dã tanã iske su bisa ia abke, alhãli kuwa sũ ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Sunã nẽman ka da gaggauta azãba, kuma lalle Jahannama, tabbas, mai kẽwayewa ce gakãfirai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ga wata ruwãyar \"Mu\" matsayin \"Ya\" watau Malã'ika waki1in azãbarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Rãnar da azãba ke rufe su daga samansu da kuma ƙasan ƙafafunsu kuma Ya* ce: \"Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Tun da ƙasa nã da yalwã, sai mutum ya yi hijira zuwa wurin da yake mai sauƙi a gareshi, ya bauta wa Allah da sauƙi, idan garinsu ya buwãye shi."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Yã bãyiNa, waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle fa ƙasãTa mai yalwã* ce, sabãda haka ku bauta Mini."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi haƙuri, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi haƙuri, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu kawai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sabõda haka tunãnin abinci kada ya hana ku yin hijira zuwa wurin yardar Allah, Mai ciyar da dabbõbin da bã su tattalin abincinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Kuma da yawa* dabba wadda bã ta ɗaukar abincinta Allah Yanã ciyar da ita tãre da ku, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai ilmi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Yãya ake karkatar da su daga hijira dõmin tsõron yankewar abinci, alhãli kuwa sun tafi wurin yardar wanda Ya halicci sammai da ƙasã? Yin hijira yanã a cikin jarrabãwar Allah ga Musulmi."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Lalle idan ka tambaye su: \"Wãne ne ya halitta sammai da ƙasã kuma ya hõre rãnã da watã?\" Lalle sunã cẽwa Allah ne. TO, yãya ake karkatar da su*?"
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 403,
            "translated_text": "Alah ne ke shimfiɗa arziki ga wanda Yake so daga cikin bãyinsa kuma Yanã ƙuntãtãwa ga (wanda, Yake so). Lalle Allah, Masani ne ga dukan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "Kuma lalle idan ka tambaye su. \"Wãne ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta?\" Lalle sunã cẽwa, \"Allah ne.\" Ka ce: \"Gõdiya tã tabbata ga Allah.\" Ã'a, mafi yawansu bã su hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "Dõmin su kãfirce wa abin da Muka bã su kuma dõmin su ji dãɗi sa'an nan kuma zã su sani."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhãli kuwa anã fisge mutãne a gẽfensu? Shin, da ɓãtaccen abu suke ĩmãni kuma da ni'imarAllah suka kãfirta?"
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 29,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, kõ kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama bãbu mazauna ga kãfirai?"
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa (ga addĩninsu)."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "A. L̃. M̃.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Rũmãwa Kiristoci ne mãsu aiki da littãfi, sunã faɗa da Fãrisãwa mãsu bautã wa wutã. Fãrisawa suka rinjãyi Rumãwa, sabõda haka Ƙuraishãwa suka ji dãɗi sabõda alfãnun cewa zã su rinjãyi Musulmi idan sun yi faɗa. A bãyan saukar surar, sai Musulmi suka yi farin ciki sabõda alfãnun cewa sũ kuma zã su rinjãyi Ƙuraishãwa. Wannan ya sanya Abũbakar ya yi ƙuri'a da Ubaiyu bn Halaf a kan rãƙuma gõma a cikin shekaru uku. Sai Annabi ya ce wa Abũbakar ya ƙãra rãkuma da ajãli zuwa shekaru tara. A bãyan shekaru bakwai sai Rũmawa suka ci nasara a kan Fãrisãwa, kuma wannan ya yi daidai da Badar,watau rãnar da Musulmi suka ci nasara a kan Ƙuraishãwa. Abũbakar ya ci rãƙumansa daga magãdan Ubaiyu. Amma sai ya yi sadaka da su da umurnin Annabi, dõmin Allah Yã hana Musulmi su yi cãca a lõkacin."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 404,
            "translated_text": "Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar Lãhira.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Dangantakar rashin sanin ĩkon Allah da sanin sha'anin dũniya da kuma jãhiltar al'amarin Lãhira,."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya* da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu?<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Gaskiya ita ce tsãri tabbatacce wanda bã ya canzãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu suka kasance sunã zãlunta."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "Sa'an nan ãƙibar waɗannan da suka aikata mũgun aiki ta kasance mafi muni, wãtau sun ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma suka kasance sunã izgili da su."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "Allah ne ke fãra yin halitta, sa'an nan Ya sãke ta sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "Kuma a rãnar da sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi zã su kãsa magana."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "Kuma bã su da mãsu cẽto daga abũbuwan shirkinsu, kuma snn kasance mãsu kãfircẽwadaga abũbuwan shirkinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "kuma a rãnar tashin Alkiyama ranar ne suke rarrabuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 405,
            "translated_text": "To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã faranta musu rãyuka, a cikin wani lambu."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 406,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 406,
            "translated_text": "Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da lõkacin da kuke shiga sãfiya.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Akwai dangantaka a tsakãnin tasbĩhi, watau ibãda da rãyuwa, da tsakãnin fitar hantsi da sãfiya kamar yadda yake akwai dangantaka a tsakãnin mutuwa da maraice, da yamma da kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 406,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin zawãli."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 406,
            "translated_text": "Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 406,
            "translated_text": "Kuma akwai daga ãyõyinSa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum, kunã wãtsuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 406,
            "translated_text": "Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku.* Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Akwai dangantaka a tsakãnin halittar namiji da mace daga yumɓu da kuma natsuwar da suke sãmu daga junã da sõyayya da rahamar da ke a ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 406,
            "translated_text": "Kuma akwai daga ãyõyinSa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 406,
            "translated_text": "Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 406,
            "translated_text": "Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 407,
            "translated_text": "Kuma akwai daga ãyõyinsa, tsayuwar sama da asƙã bisa umurninsa, sa'an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasã, sai gã ku kunã fita."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 407,
            "translated_text": "Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasã Nãsa ne shi kaɗai. Dukansu mãsu tawãli'u ne a gare Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 407,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 407,
            "translated_text": "Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltawa."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 407,
            "translated_text": "Ã'aha! waɗanda suka yi zãunci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba. To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka?"
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 407,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini,* kanã mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah, wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Yin addini ɗabĩ'a ce wadda Allah Ya halicci mutum akanta. Idan mutum ya bi abin da Allah Ya umurce shi da yi kõ bari, to yã yi addinin gaskiya, idan kuwa bai yi haka ba, ya zama mushiriki game da wanda yake karɓar umurni daga gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 407,
            "translated_text": "Kunã mãsu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bĩ Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ya fassara mushirikai da ãyã ta 32. Wannan ya nũna ta yi nũni ga hana dukkan ɗarĩƙun sũfãye dõmin sunã rarraba mutãne ƙungiya-ƙungiya, kuma kõwa nã ganin abin da yake yi ko kuma wanda yake bi yã fi na wani. Kumawanda ke cikin wata ƙungiya bã zai iya haɗuwa da wata ba a lõkacin wurudinsu, a bãyan abũbuwan da suke ƙunsãwa a cikin ayyukansu na bidi'õ'i da aƙĩdõdi da suka sãɓa wa Musulunci."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 407,
            "translated_text": "Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 408,
            "translated_text": "Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 408,
            "translated_text": "Dõmin su kãfirta dl abin da Muka bã su. To ku ji dãɗi kaɗan Sa'an nan zã ku, sani."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 408,
            "translated_text": "Kõ Mun saukar da wani dalĩ li a gare su? Shi kuwa yanã magana da abin da suka kasance sunã shirkin da shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 408,
            "translated_text": "Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã yanke ƙauna,"
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 408,
            "translated_text": "Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 408,
            "translated_text": "Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 408,
            "translated_text": "Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar Allah to (mãsu yin haka) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa (ga dũkiyarsu)."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 408,
            "translated_text": "Allah ne Wanda Ya halitta ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 408,
            "translated_text": "¥arnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su kõmo."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 409,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku tafi a cikin ƙasã sa'an nan ku dũbi yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninku ta kasance. Mafi yawansu sun kasance mãsu yin shirki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 409,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgẽwa (su rabu biyu)."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 409,
            "translated_text": "Wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, sabõda kansu suke yin shimfiɗa."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 409,
            "translated_text": "Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 409,
            "translated_text": "Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra kuma dõmin Ya ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma dõmin jirãgen ruwa su gudãna da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, fãtanku zã ku gode."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 409,
            "translated_text": "Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabãninka, zuwa ga mutãnensu sai suka je musu da hujjõji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi, kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 409,
            "translated_text": "Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 409,
            "translated_text": "Kuma kõ da sun kasance a gabãnin a saukar da shi a kansu, kusa-kusa, sunã baƙin ciki hai bã su iya magana."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 409,
            "translated_text": "Sai ka dũbi alãmõmin rahamar Allah yadda Yake rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas, Mai rãyar da halitta ne, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "Kuma lalle idan Mun aika wata iska, suka ganta fatsifatsi, lalle zã su yini a bãyansa sunã kãfirta."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "Sabõda haka, kai, bã ka jiyar da matattu kira, kuma bã ka jiyar da kurãme kira idan sun jũya bãya sunã gudu."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "Kuma ba ka zamo mai shiryar da makãfi ba daga ɓatarsu, bã ka jiyarwa fãce wanda ke yin ĩmãni da ãyõyinMu, watau sũ ne mãsu mĩƙa wuya, su sallama."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "Allah ne Ya halitta ku daga rauni,* sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Mai ilmi, Mai ĩkon yi,<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Raunin farko, shĩ ne maniyyi, na biyu jãruntaka da ƙarfin ƙurũciya, rauni na uku, shi ne tsũfa bãyan ƙarfin hankalin kamãla ta dattãko."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "Kuma a rãnar da Sa'a* ke tsayuwa, mãsu laifi na rantsuwã: Ba su zauna a cikin kabari ba fãce sã'a guda. Kamar haka suka kasance anã karkatar da su.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sa'a ta farko Rãnar Ƙiyãma,ta biyu ɗan lõkaci, watau ɗan lõkacin da suka sãmi hutun azãbar kabari a tsakãnin bũsar farko da ta biyu. Akwai munãsabar ƙaryarsu ta dũniya da ta Lãhira. Akwai munasabar dangantakar lafazin kalmomi."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da ĩmãni suka ce: \"Lalle, haƙĩƙa kun zauna a cikin Littãfin Allah, har zuwa rãnar tãyarwa, to, kuma wannan ita ce rãnar tãyarwar, kuma amma kũ, kun kasance* ba ku sani ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Rashin aiki da littãfin Allah a dũniya yakan sanya ɗĩmuwa a rãnar Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "To, a rãnar da uzurin waɗanda suka yi zãlunci bã ya amfaninsu, kuma bã a neman yardarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "Kuma lalle tabbas Mun buga kõwane irin misãli ga mutãne a cikin wannan Alƙur'ãni, kuma lalle idan kã je musu da kõwace ãyã, lalle, waɗanda suka kãfirta zã su ce \"Kũ, bã kõme kuke ba fãce mãsu barua.\""
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "Kamar haka Allah Yake shãfe haske a kan zukãtan waɗanda ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 30,
            "page_number": 410,
            "translated_text": "Sabõda haka ka yi haƙuri lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma kada waɗanda bã su da yaƙĩni su sassabce maka hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "A. L̃. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "Waɗancan ãyõyin Littãfin ne mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "Shiriya da rahama ne ga mãsu kyautatawa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "Waɗanda ke tsai da salla kuma sunã ɓãyar da zakka kuma sũ, sunã yin ĩmãnin yaƙĩni, ga lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "Waɗannan sunã a kan shiriya ta daga Ubangijinsu kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi* dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tatsũniyõyi sunã shagaltarwa daga ilmi mai sanya sanin Allah. Allah Ya hana a yi tarbiyyar yãra game da tãtsũniya mai ɗauke hankalinsu daga ibãda, Littattafan makaranta na zãmani da jarĩdu duka tãtsũniyõyi ne, sai abin da ya dãce da sunna."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "Kuma idan an karanta ãyõyinMu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai, kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "Lalle, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljannar ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "Sunã dawwama a cikinsu Allah Yã yi alkawarin, Ya tabbatar da shi. Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "(Allah) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 411,
            "translated_text": "Wannan shĩ ne halittar Allah. To ku nũna mini, \"Mẽne ne waɗanan da ba Shi ba suka halitta? Ã'a, azzalumai sunã a cikin ɓata bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 412,
            "translated_text": "Kuma lalle haƙĩƙa Mun bai wa Luƙmãn hikima. (Muka ce masa) Ka gõde wa Allah, kuma wanda ya gõde, to yanã gõdẽwa ne dõmin kansa kawai kuma wanda ya kãfirta, to, lalle, Allah Mawadãci ne, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 412,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Luƙmãn ya ce wa ɗansa, alhãli kuwa yanã yi masa wa'azi, \"Yã ƙaramin ɗãna! Kada ka yi shirki game da Allah. Lalle shirki wani zãlunci ne mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 412,
            "translated_text": "Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa) \"Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 412,
            "translated_text": "\"Kuma idan mahaifanka suka tsananta* maka ga ka yi shirki game da Ni, ga abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'a. Kuma ka abũce su a cikin dũniya gwargwadon sharĩ'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa gare Ni, sa'an nan zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * A bãyan haƙƙin Allah sai haƙƙin iyãye. Sabõda haka ba zã a yi ɗã'a ga iyãye ba ga abin da ya sãɓãwa Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 412,
            "translated_text": "\"Yã ƙaramin ɗãna! Lalle ita idan gwargwadon ƙwãyar kõmayya ce ta kasance, to, ta kasance a cikin wani falalen dũtse, kõ a cikin sammai, kõ a cikin ƙasã, Allah zai kãwo ta Lalle Allah Mai tausasãwa ne, Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 412,
            "translated_text": "\"Yã ƙaramin ɗãna! Ka tsai da salla, kuma ka yi umurni da abin da aka sani, kuma ka yi hani daga abin da ba a sani ba, kuma ka yi haƙuri a kan abin da ya sãme ka. Lalle, wancan yanã daga muhimman al'amura.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 412,
            "translated_text": "\"Kada ka karkatar da kundukukinka* ga mutãne, kada ka yi tafiya a cikin ƙasã kanã mai nũna fãɗin rai. Lalle, Allah bã Ya son dukan mai tãƙama, mai alfahari.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Karkata kundukuki ga mutãne, alamar wulãkanta su ne."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 412,
            "translated_text": "\"Kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka runtse ga sautinka. Lalle mafi mũnin sautuka haƙĩƙa shĩ ne sautin jãkuna.* \"<br \/>\n____________________<br \/>\n * A nan ne iyãkar wasiyyar Luƙmãn ga ɗansa. Sa'an nan kuma Allah Ya ci gaba da bayãnin yadda ake tarbiyyar mutãne."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 413,
            "translated_text": "Ashe, ba ku gani ba, cẽwa Allah Yã hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasã, kuma Ya zuba ni'imõminsa a kanku, bayyanannu da ɓõyayyu? Kuma akwai daga mutãne wanda ke yin jidãli ga al'amarin Allah, bã da wani ilmi ba, kuma bã da wata shiriya ba, kumã ba da wani littãfi mai haskakãwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 413,
            "translated_text": "Kuma idan aka ce musu, \"Ku bi abin da Allah ya saukar,\" sai su ce: \"Ã'a, munã bin abin da muka sãmi ubanninmu a kansa.\" shin kõ dã Shaiɗan nã kiran su ne zuwa ga azãbar sa'ir,"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 413,
            "translated_text": "kuma wanda ya mĩka fuskarsa zuwa ga Allah, alhãli kuma yanã mai kyautatãwa, to, lalle ya yi riƙo ga igiya amintacciya. Kuma zuwa ga Allah ãƙibar al'amura take."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 413,
            "translated_text": "Kuma wanda ya kãfirta, to, kada kãfircinsa ya baƙanta maka rai, zuwa gare Mu makõmarsu take, sa'an nan Mu bã su lãbari game da abin da suka aikata. Lalle Allah, Masani ne ga abin da ke a cikin ƙirãza."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 413,
            "translated_text": "Munã jĩshe su dãdi kaɗan sa'an nan Mu tĩlasta su ga shiga zuwa azãba kakkaura."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 413,
            "translated_text": "Kuma lalle, idan ka tambaye su, \"Wãne ne ya halĩtta sammai da kasa?\" Lalle zã su ce: \"Allah ne.\" Ka ce: \"Gõdiya ta tabbata ga Allah\" Ã'a, mafi yawansu ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 413,
            "translated_text": "Abin da yake a cikin sammai da ƙasa duka na Allah kawai ne. Lalle, Allah Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 413,
            "translated_text": "Kuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su ƙãre ba.* Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan bayãni ne ga yawan ilmin Allah, watau yanã nũnawa mutãne cewa su yi aiki da ilmin da Ya bã su, mai amfãni zuwa gare su, kada su wuce shi zuwa neman wani ilmi daga wani abu, su bar Allah, su halaka a kan wani ilmi da bai umurce su da su yi aiki da shi ba. Ilmin da Ya bã su a cikin Alƙur'ãni shi ne sharĩ'a wãtau hanya mai kai su ga Aljanna. Sauran hanyõyi ɓata ne."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 413,
            "translated_text": "Halittarku bã ta zama ba, kuma tãyar da ku bai zama ba, fãce kamar rai guda. Lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 414,
            "translated_text": "Ashe, ba ku ga, lalle, Allah Yanã shigar da dare a cikin rãna ba, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare kuma Yã hõre rãnã da watã kõwane yanã gudãna zuwa a ajali ambatacce kuma lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 414,
            "translated_text": "Wannan fa dõmin Allah Shĩ ne Gaskiya, kuma abin da suke kira wanda bã Shi ba, shi ne ƙaryã, kuma lalle, Alah shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 414,
            "translated_text": "Ashe, ba ka ga lalle jirgin ruwa nã gudãna ba a cikin tẽku da ni'imar Allah dõmin Ya nũna muku daga ãyõyinSa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, mai gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 414,
            "translated_text": "Kuma idan tãguwar ruwa, kamar duwatsu, ta rufe su, sai su kira Allah sunã tsarkakẽwar addini a gare shi. To, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudu, sai daga cikinsu akwai mai taƙaitãwa kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce dukkan mayaudari mai yawan kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 414,
            "translated_text": "Ya ku mutãne! Ku bauta wa Ubangijinku da taƙawa, kuma ku ji tsõron wani yini, rãnar da wani mahaifi bã ya sãka wa abin haifuwarsa da kõme kuma wani abin haifuwa bã ya sãka wa mahaifinsa da kõme. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Sabõda haka, kada wata rãyuwa ta kusa ta rũde ku, kuma kada marũɗin* nan ya rũɗẽ ku game da Allah.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Shaiɗan."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 31,
            "page_number": 414,
            "translated_text": "Lalle, Allah a wurinsa kawai sanin sa'a yake, kuma Yanã saukar da girgije, kuma Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "A. L̃. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Saukar da Littafin bãbu shakka a gare shi, daga Ubangijin tãlikai yake."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Kõ sunã cẽwa (Muhammadu ne) ya ƙirƙira shi? Ã'a, shĩ ne gaskiya daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda wani mai gargaɗi bai je musu ba a gabãninka, fãtan zã su shiryu."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Allah ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu a cikin kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Bã ku da, baicin Shi, wani majiɓinci kuma babu wani maceci. Shin, bã zã ku yi tunãni ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Yanã shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasã, sa'an nan ya tãka zuwa gare Shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shẽkaru dubu ne ga abin da kuke lissafãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Wannan shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwãyi, Mai jinƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Wanda Ya kyautata kõme, Wanda Ya halitta shi. Shi ne kuma Ya fãra halittar mutum daga lãka."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Sa'an nan Ya sanya ɗiyansa daga wani asali na wani ruwa wulãkantacce."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Sa'an nan Ya daidaita shi, kuma Ya hũra a cikinsa, daga ruhinSa kuma Ya sanya muku ji, da ganunuwa da zukãta. Gõdiyarku kaɗan ce ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Shin, idan mun ɓace a cikin ƙasã, shin, lalle mu, tabbas ne munã zama a cikin wata halitta sãbuwa?\" Ã'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kãfirai"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 415,
            "translated_text": "Ka ce: \"Mala, ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shĩ ne ke karɓar rãyukanku.* Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Watau bã ku ke mutuwa da kanku ba, sai an matar da ku, sabõda haka tãyarwar ma bãkũ zã ku yi ta da kanku ba,balle ku yi musu."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 416,
            "translated_text": "Kuma da kã gani a lõkacin da mãsu laifi suke mãsu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, \"Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu aikata aiki na ƙwarai. Lalle mũ mãsu yaƙĩni ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 416,
            "translated_text": "Kuma dã Mun so dã Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 416,
            "translated_text": "To, ku ɗanɗana sabõda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mũ mã Mun manta da ku, kuma ku dãnɗani azãbar dawwama sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 416,
            "translated_text": "Waɗanda ke ĩmãni da ãyõyinMu kawai, sũ ne waɗanda idan aka karanta musu ãyõyinMu sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma su yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, alhãli kuwa su bã su yin girman kai."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 416,
            "translated_text": "Sãsanninsu nã nĩsanta daga wurãren kwanciya, sunã kiran Ubangijinsu bisa ga tsõro da ɗammãni, kuma sunã ciryawa daga abin da Muka azurta su."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 416,
            "translated_text": "Sabõda haka wani rai bai san abin da aka ɓõye musu ba, na sanyin idãnu, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 416,
            "translated_text": "Shin, wanda ya zama mũmini yanã kamar wanda ya zama fãsiƙi? Bã zã su yi daidai ba."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 416,
            "translated_text": "Amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwafai, to, sunã da gidãjen Aljannar makõma, a kan liyãfa sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 416,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi fãsiƙanci to makõmarsu ita ce wuta, kõ da yaushe suka yi nufin su fita daga gare ta, sai a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu: \"Ku ɗanɗana azãbai wutã, wadda kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, mafi ƙasƙanci, kãfin a kai ga azãba mafi girma, dõmin fãtan za su kõmo."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littafi,* sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga haɗuwa da shi. Kuma Mun sanya shi ya zama shiriya ga Banĩ Isrã'ĩla.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Ba Alƙur'ãni ne farkon Littãfin sama ba kuma bã Muhammadu ne farkon Manzannin Allah ba, Mun bai wa Mũsã Attaura, mutãnensa sun yi aiki da ita, sun ɗaukaka kamar yadda ake neman Musulmi su yi aiki da Alƙur'ãni su ɗaukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Kuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, sunã shiryarwa da umurninMu, a lõkacin da suka yi haƙuri, kuma sun kasance sunã yin yaƙĩni da ãyõyinMu."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Lalle Ubangijinka shĩ ne zai rarrabe a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Shin, ba ya shiryar da su cẽwa da yawa Muka halakara gabãninsu, daga al'ummõmi sunã tafiya a cikin masaukansu?* Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi. Shin, ba su jĩ ne?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ƙuraishãwa sunã tafiya a cikin gidãjen al'ummõmin da suka halaka sunã ganin abin da ya auku gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle Mũ, Munã kõra ruwa zuwa ga ƙasã ƙeƙasasshiya, sa'an nan Mu fitar, game da shi, wata shũka wadda dabbõbinsu, da su kansu ke ci daga gare ta? Ashe fa ba su gani ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Kuma sunã cẽwa, \"Yaushe wannan hukunci yake, aukuwa idan kun kasance mãsu gaskiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ranar hukuncin nan, ĩmãnin waɗanda suka kãfirta bã zai amfãne su ba (a cikinta) kuma bã zã a yi musu jinkiri ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 32,
            "page_number": 417,
            "translated_text": "Sabõda haka ka kau da kai daga barinsu, kuma, ka yi jira lalle, sũ ma mãsu jira ne."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 418,
            "translated_text": "Yã kai Annabi! Ka bi Allah da taƙawa, kuma kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai da munãfukai. Lalle, Allah Ya kasance Mai ilmi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 418,
            "translated_text": "Kuma ka bi abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka daga Ubangijinka. Lalle, Allah Ya kasance Mai labartawa ga abin da kuke aikatawa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 418,
            "translated_text": "Ka dõgara ga Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama wakĩli."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 418,
            "translated_text": "Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mãtanku waɗanda kuke yin zihãri daga gare su, su zama uwãyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankãkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu nãku, maganarku ce da bãkunanku alhãli kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 418,
            "translated_text": "Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to, 'yan'uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma bãbu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukãtanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 418,
            "translated_text": "Annabi ne mafi cancanta* ga mũminai bisa ga su kansu, kuma mãtansa uwãyensu ne. Kuma ma'abuta zumunta waɗansunsu sun fi waɗansu a cikin Littãfin Allah bisa ga mũminai da Muhãjirai, fãce fa idan kun aikata wani alhẽri zuwa ga majiɓintanku. Wancan yã kasance a cikin Littafi, rubũtacce.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Idan son mũmini ya Sãɓãwa faɗar Annabi, sai ya bar son ransa ya kõma wa faɗar Annabi."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 419,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nũhu da Ibrãhĩm da Mũsa da kuma Ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka riƙi wani alkawari mai kauri daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 419,
            "translated_text": "Dõmin Ya tambayi mãsu gaskiya a kan gaskiyarsu, kuma Yã yi tattalin wata azãba mai raɗaɗi ga kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 419,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da waɗansu rundunõni suka zo muku, sai Muka aika wata iskã a kansu da waɗansu rundunõni waɗanda ba ku gani ba, Kuma Allah Yã kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 419,
            "translated_text": "A lõkacin da suka zo muku daga samanku da kuma ƙasa daga gare ku, kuma a lõkacin da gannai suka karkata kuma zukãta suka kai ga maƙõsai, kuma kuka yi zaton zace-zace, game da Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 419,
            "translated_text": "A can aka jarrabi mũminai, kuma aka yi girgiza da su, girgiza mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 419,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da munafukai da waɗanda akwai cũta a cikin zukãtansu ke cẽwa, Allah da ManzonSa, \"Ba su yi mana wa'adin kõme ba, fãce rũɗi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 419,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce, \"Ya mutãnen Yasriba!* Bã ku da wani matsayi, sabõda haka ku kõma.\" Kuma wata ƙungiya daga gare su na nẽman izni ga Annabi sunãcẽwa, \"Lalle gidãjenmu kuranye suke,\" alhãli kuwa bã kuranye suke ba, bã su da nufin kome fãce gudu.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Sun kõma ga sũnan Madĩnan a zãmanin Jãhiliyya sunã izgili da cewa ba su yarda da sãbon sũnan ba na Madĩna, fãce Yasriba, sũnanta da suka sani na asali."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 419,
            "translated_text": "Kuma dã an shige ta (Madĩna) a kansu, daga sasanninta, sa'an nan aka tambaye su fitina (kãfirci), lalle dã sun jẽ mata, kuma dã ba su zauna a cikinta (Madĩna) ba fãce kaɗan."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 419,
            "translated_text": "Kuma lalle haƙĩƙa, sun kasance sunã yi wa Allah alkawari, a gabãnin wannan; Bã zã su jũya dõmin gudu ba, kuma alkawarin Allah ya kasance abin tambaya."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 420,
            "translated_text": "Ka ce: \"Gudun nan bã zai amfãne ku ba daga mutuwa ko kisa. Kuma har in kun gudu, bã zã a jĩshe ku dãɗĩ ba fãce kaɗan.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 420,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wãne ne wanda yake tsare ku daga Allah, idan Yã yi nufin wata cũta game da ku?\" Kuma bã zã su sãmar wa kansu wani majiɓinci ba, banda Allah, kuma bã zã su sãmar wa kansu wani mataimaki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 420,
            "translated_text": "Lalle Allah Ya san mãsu hana mutãne fita daga cikinku, da mãsu cẽwa ga 'yan'uwansu,\"Ku zo nan a wurinmu.\" Kuma bã zã su shiga yãƙi ba fãce kaɗan."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 420,
            "translated_text": "Suna mãsu rõwa gare ku, sa'an nan idan tsõro ya zo, sai ka gan su sunã kallo zuwa gare ka, idãnunsu sunã kẽwaya, kamar wanda ake rufe hankalinsa sabõda mutuwa. Sa'an nan idan tsõron ya tafi, sai su yi muku miyãgun maganganu da harussa mãsu kaifi, sunã mãsu rõwa a kan dũkiya. Waɗannan, ba su yi ĩmani ba, sabõda hakaAllah Ya ɓãta ayyukansu. Kuma wannan ya kasance mai sauƙi ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 420,
            "translated_text": "Sunã zaton ƙungiyõyin kãfirai ba su tafi ba. Kuma idan ƙungiyõyin kãfirai sun zo, sunã gũrin da dai sun zama a karkara a cikin ƙauyãwa, sunã tambayar lãbãranku. Kuma kõ dã sun kasance a cikinku, bã zã su yi yãƙi ba, fãce kaɗan."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 420,
            "translated_text": "Lalle, abin kõyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã fãtan rahamar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 420,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da mũminai suka ga ƙungiyõyin kãfirai, sai suka ce, \"Wannan ne abin da Allah da ManzonSa suka yi mana wa'adi, Allah da ManzonSa sunyi gaskiya.\" Kuma wannan bai ƙãra musu kõme ba fãce ĩmãni da sallamãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 421,
            "translated_text": "Daga mũminai akwai waɗansu mazãje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkwari a kansa, sa'an nan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukãtarsa,* kuma daga cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Biyan bukãtarsa wãtau ya mutu, cikinsu akwai wanda yake jiran mutuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 421,
            "translated_text": "Dõmin Allah Ya sãka wa masu gaskiya da gakiyarsu, kuma Ya azabtar da munafukai idan Ya so, ko Ya karɓi tũba a kansu. Lalle, Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 421,
            "translated_text": "Kuma Allah Yã mayar *da waɗanda suka kãfirta da fushinsu, ba su sãmi wani alhẽri ba. Allah Ya isar wa mũminai daga barin yãƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwãyi.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah Yã kõre ƙungiyõyin kãfirai da iskarsa mai tsananin sanyi, watau iskar Saba."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 421,
            "translated_text": "Kuma Ya saukar *da waɗannan da suka taimake su daga mazõwa Littãfi, daga birãnensu, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kunã kashẽwa, kuma kunã kãma wata ƙungiyar.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Sa'an nan kuma Musulmi suka tsare Yahũdun Bani Ƙuraiza, a cikin birninsu har suka sallama kansu ga hukuncin sa'ad bn Mu'azu wanda ya hukunta a kashe wanda ya balaga daga cikinsu, kuma a bautar da mãtã da yãra. Aka yi musu hakanan, aka zartar da hukuncinsa a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 421,
            "translated_text": "Kuma Ya gãdar da ku gõnakinsu da gidãjensu da dũkiyõyinsu, da wata ƙasa wadda ba ku taɓa tãkarta bã. Kuma Allah ya kasance Mai ĩkon yi ne a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 421,
            "translated_text": "Yã kai Annabi! Ka ce wa matanka, \"Idan kun kasance kunã nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, to, ku zo in yi muku kyautar ban kwãna kuma in sake ku, saki mai kyau.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 421,
            "translated_text": "\"Kuma idan kun kasance kunã nufin Allah da Manzonsa da gidan Lãhria, to, lalle, Allah Yã yi tattalin wani sakamako mai girma ga mãsu kyautatãwa daga gare ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 421,
            "translated_text": "Yã mãtan Annabi! Wadda ta zo da alfãsha bayyananna daga cikinku zã a ninka mata azãba ninki biyu. Kuma wancan yã kasance mai sauƙi ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 422,
            "translated_text": "Kuma wadda ta yi tawãli'u daga cikinku ga Allah da ManzonSa, kuma ta aikata aiki na ƙwarai, zã Mu bã ta sakamakonta ninki biyu, kuma Mun yi mata tattalin arziki ma karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 422,
            "translated_text": "Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kun yi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 422,
            "translated_text": "Kuma ku tabbata a cikin gidãjenku,* kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar gãye-gãye ta jãhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩ da salla, kuma ku bãyar da zakka, ku yi ɗã, ã ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Umurni ga mãtan Annabi umurni ne ga matãn sauran Musulmi. Sabõda haka ba ya halatta mace ta fita daga gidanta fãce da larũra."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 422,
            "translated_text": "Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin ɗãkunanku daga ãyõyin Allah da hukunci. Lalle Allah Yã kasance Mai tausasãwa Mai labartawa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 422,
            "translated_text": "Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu tawãli'u maza da mãsu tawãlĩu mãtãda mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata gãfara da wani sakamako mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 423,
            "translated_text": "Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lõkacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zãɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, to, yã ɓace, ɓacẽwa bayyananna.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wannan ãyã hani ne ga kõwane Musulmi kõ Musulma ga sãɓawa umurnin Allah da Manzonsa, su bi son rãyukansu ga kõme. Kuma ba a lõkacin auren Zainab da Zaidu ne ta sauka ba kamar yadda waɗansu mãsu tafsiri ke rubũtãwa dõmĩn an yi wannan aure a gabãnin hijira da nĩsa, ita ãyãr kuwa tã sauka a Madĩna ne a bãyan yãƙinAhzab, kamar yadda tsarin maganarta ya nũna."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 423,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin* da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, \"Ka riƙe mãtarka, kuma ka bi Allah da taƙawa,\" kuma kana ɓõyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi,** kanã tsõron mutãne, alhãli kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsõronSa. to a lõkacin da zaidu ya ƙãre bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dõmin kada wani ƙunci ya kasance a kan mũminai a cikin (auren mãtan) ɗiyan hankãkarsu, idan sun ƙãre bukãta daga gare su. Kuma umurnin Allah yã kasance abin aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Idan Allah ya umurci mutãne da yin wani abu kõ da barinsa to, Annabi shĩ ne mai fãra bin umurnin kõ kange kansa daga abin da aka hana. Wannan ƙissa misãli ce ga ãyarda ke a gaba da ita, yadda Annabi ya bi umurni wajen auren mãtar Zaidu bn Hãrisa wanda Annabi ya yi tabanninsaa gabãnin a hana aiwatar da tabanni. Auren yã auku Annabi na da shekara 58 ita kuwa da shekara 43. Sũnanta Zainab bintu Jahash ɗiyar goggon Annabi. Allah Yã nũna cewa dai tabanni yã mutu sõsai.** Abin da Annabi ke ɓoyewa shĩ ne umurnin Allah da Ya gaya masa cħwa, zai auri Zainab mãtar Zaidu a bãyan Zaidun ya sake ta. Sabõda haka Annabi ke lallãshin Zaidu dõmin kada sakin ya auku har aurenta ya zama wãjibi akansa, a bãyan abin da aka sani na cħwa, Zaidu yã zama ɗansa da tabanni a gabãnin haka."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 423,
            "translated_text": "Wani ƙunci bai kasance a kan Annabi ba ga abin da Allah Ya faralta a kansa, a kan ƙã'idar, Allah a cikin (Annabãwa) waɗanda suka shige daga gabãninsa. Kuma umurnin Allah yã kasance abin ƙaddarãwa tabbatacce."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 423,
            "translated_text": "Waɗanda ke iyar da Manzancin Allah, kuma sunã tsõronSa, kuma bã su tsõron kõwa fãce Allah, Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisabi."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 423,
            "translated_text": "Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 423,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 423,
            "translated_text": "Kuma ku tsarkake shi, a sãfiya da maraice."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 423,
            "translated_text": "(Allah) Shĩ ne Wanda ke tsarkake ku, da mala'ikunSa (sunã yi muku addu'a), dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. Kuma (Allah) Yã kasance Mai Jĩn ƙai ga mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 424,
            "translated_text": "Gaisuwarsu a rãnar da suke haɗuwa da shi \"Salãm\", kuma Yã yi musu tattalin wani sakamako na karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 424,
            "translated_text": "Yã kai Annabi! Lalle Mũ Mun aike ka kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 424,
            "translated_text": "Kuma mai kira zuwa ga Allah da izninSa, kuma fitila mai haskakãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 424,
            "translated_text": "Kuma ka yi bushãra ga mũminai cẽwa, sũnã da falalamai girma daga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 424,
            "translated_text": "Kuma kada ka yi ɗã'a ga kãfirai da munãfukai, kuma ka ƙyãe cũtarsu (gare ka), kuma ka dõgara ga Allah. Allah Yã isa zama wakĩli."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 424,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun auri mũminai mãtã, sa'an nan kuka sake su a gabãnin ku shãfe su, to, bã ku da wata idda da zã ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin dãɗi* kuma ku sake su saki mai kyau.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kyautar jin daɗi ita ce kyautar ban kwana ga mãtar da aka saki."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 424,
            "translated_text": "Yã kai Annabi! Lalle Mũ, Mun halatta maka mãtanka waɗanda ka bai wa sadãkõkinsu da abin da hannun dãmanka ya mallaka daga abin da Allah Ya bã ka na ganĩma, da 'yã'yan baffanka, da 'ya'yan goggonninka da 'yã'yan kãwunka da 'yã'yan innõninka waɗanda suka yi hijira tãre da kai, da wata mace mũmina idan ta bãyar da kanta ga Annabi, idan shi Annabi yanã nufin ya aure ta (hãlin wannan hukunci) kẽɓe yake gare ka, banda gamũminai. Lalle Mun san abin da Muka faralta a kansu (smũminai) game da mãtansuda abin da hannayensu suka mallaka. Do min kada wani ƙunci ya kasance a kanka, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 425,
            "translated_text": "Kanã iya jinkirtar da* wadda ka ga dãmã daga gare su, kuma kanã tãro wadda kake so zuwa gare ka. Kuma wadda ka nẽma daga waɗanda ka nĩsantar, to, bãbu laifi agare ka. Wannan yã fi kusantar da sanyaya idãnunsu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba, kuma su yarda da abin da ka bã su, sũ duka. Kuma Allah Yanã sane da abin da yake a cikin zukãtanku. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai haƙuri.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Rabon kwãna ga mãtan Annabi, ba sharĩ'a ba ce a kan hususiyyarsa, sabõda yawan nauyin da yake ɗauke da Shi na isar da Manzancin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 425,
            "translated_text": "Waɗansu mãtã bã su halatta a gare ka a bãyan haka, kuma ba zã ka musanya su da mãtan aure ba, kuma kõ kyaunsu yã bã ka sha'awa, fãce dai abin da hannun dãmanka ya mallaka. Kuma Allah Yã kasance Mai tsaro ga dukan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 425,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada kũ shiga gidãjen Annabi, fãce fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga wani abinci, bã da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wãtse, kuma bã da kun tsaya kunã masu hĩra da wani Iãbãri ba. Lalle wannan yanã cũtar da Annabi, to, yanã jin kunyarku, alhãli kuwa Allah bã Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan shãmaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukãtanku da zukãtansu. Kuma bã ya halatta a gare ku, ku cũci Manzon Allah, kuma bã ya halatta ku auri mãtansa a bãyansa har abada. lalle wannan a gare ku yã kasance babban abu a wurin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 425,
            "translated_text": "Idan kun bayyana wani abu, kõ kuma kuka ɓõye shi, to, lalle Allah Ya kasance Masani ga kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 426,
            "translated_text": "Bãbu laifi a kansu game da ubanninsu, kuma bãbu game da ɗiyansu, kuma bãbu game da 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kuma bãbu game da mãtan mũminai, kuma bãbu game da abin da hannãyensu suka mallaka, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Yã kasance Mahalarci a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 426,
            "translated_text": "Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati* ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Salãtin Allah ga Annabi, shĩ ne ɗaukaka darajarsa a kõyaushe. Salãtin malã'iku, shĩne istigfãri da addu'a a gare shi. Salãtin mutãne, shĩ ne ibãda da istigfãri da addu'a a gare shi da tawassuli da shi dõmin neman Allah Ya karɓi ibãdarsu. Salãti sau ɗaya wãjibi ne a kan kõwane Musulmi a tsawon rayuwarsa, sa'an nan kuma sunna ce a cikin kõwace salla. Kuma mustahabbi ne a cikin kõwane mazauni da wurin ambatonsa."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 426,
            "translated_text": "Lalle waɗanda ke cũtar Allah da MauzonSa Allah Yã la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma Yã yi musu tattalin azãba mai wulãkantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 426,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke cũtar mũminai maza dã muminai mãtã, bã da wani abu da suka aikata ba to, lalle sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 426,
            "translated_text": "Yã kai Annabi! Ka* ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Anã fãra gyãra daga sama, sa'an nan gyãran ya sauko ƙasa, kamar ɓarnar da tã fãru daga sama, sai tã kai ƙasa. "
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 426,
            "translated_text": "Lalle, idan munãfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukãtansu, da mãsu tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba (daga hãlãyensu),* lalle, zã Mu shũshũta ka a gare su, sa'an nan bã zã su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, fãce kaɗan.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Munãfukai da Shaiɗãnu da mãsu tsegumi bãbu abin da ke hana su mugun hãlinsu sai tsanani da tsõrõ."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 426,
            "translated_text": "Tsinannu ne duk inda suka shi za'a kame su kuma akarkashe su kashe."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 426,
            "translated_text": "A kan hanyar Allah (ta gyaran jama'a) a cikin waɗanda suka shũɗe gabãninka, kuma bã zã ka sãmi musanyãwa ba ga hanyar Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Sunã tambayar ka* ga Sã'a. Ka ce: \"Saninta yanã wurin Allah kawai.\" Kuma me yã sanar da kai cẽwa anã tsammãnin sa'a ta kasance kusa?<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Shiryarwa ce ga Musulmi cewa idan zã su yi tambaya su tambayi addininsu da abũbuwa mãsu amfãni a gare su, kada su tambayi abinda ya fi hankalinsu kamar sa'a da abũbuwan gaibi da Allah Yã keɓãnta da saninsu. "
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Lalle Allah Yã la'ani kãfirai, kuma Yã yi musu tattalin wata wuta mai ƙũna."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Sunã madawwama a cikinta har abada, bã su sãmun majiɓinci, kuma bã su sãmun mataimaki."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Rãnar da ake jũya fuskõkinsu a cikin wuta sunã cẽwa, \"Kaitonmu, sabõda, rashin biyarmu ga Allah da rashin biyarmu ga Manzo!\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Yã Ubangijinmu! Lalle mũ mun* bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka ɓatar da mu daga hanya!<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan yã nũna bi da jãhilci ga addini bã uzuri bã ne.Anã azãbtar da mai bi, kamar yadda ake azabtar da shugaban ɓata. "
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azãba, kuma ka la'ane su, la'ana mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci* Mũsã sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kada ku cũci Muhammadu da ƙazafĩ kõ mũguwar magana kamar yadda Yahũdu suka yi ƙazafi ga Mũsã da neman wata kãruwa ta ce yã neme ta da zina kõ kuma da cewa shi mai gwaiwa ne, sai Allah Ya tsare Mũsã daga ƙazafin' kuma Ya sanya wani dũtse, ya gudu da tufãfinsa daga wurin wanka har suka gan Shi mai cikakkiyar halitta ne, bãbu naƙasa game da shi. Allah Yã barrantar da shi daga dukan aibi. Haka Yake barrantar da Muhammadu ga mai son ya sa masa aibi."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku faɗi magana madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gãfarta zunubanku. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, lalle, yã rabbanta, babban rabo mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun gitta amãna ga sammai da ƙasã da duwãtsu, sai suka ƙi ɗaukarta kuma sukaji tsõro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shĩ (mutum) ya kasance mai yawan zãlunci, mai yawan jãhilci."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 33,
            "page_number": 427,
            "translated_text": "Dõmin Allah Ya azabta munãfukai maza da munãfukai mãtã, da mushirikai maza da mushirikai mãtã, kuma Allah Yã karɓi tũba ga mũminai maza da mũminai mãtã. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 428,
            "translated_text": "Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Yake abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã Nãsa ne, kuma shĩ ne Mai hikima, Mai labartawa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 428,
            "translated_text": "Yã san abin da yake shiga a cikin ƙasã da abin da yake fita daga gare ta, da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shĩ ne Mai jin ƙai, Mai gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 428,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: \"Sã'a bã zã ta zo mana ba.\" Ka ce: \"Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku.\" Masanin gaibi, gwargwadon zarra bã ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma bã ta nĩsanta a cikin ƙasã, kuma bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin Littãfi bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 428,
            "translated_text": "Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Waɗancan suna da wata gãfara da wani arziki mai karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 428,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi mãkirci ga ãyõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗannan sunã da wata azãba daga azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 428,
            "translated_text": "Kuma waɗanda aka bai wa ilmi sunã ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yanã shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwãyi, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 428,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: \"Shin zã mu nũna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsãge ku, kõwace irin tsattsãgẽwa, lalle kũ, tabbas, kunã a cikin wata halitta sãbuwa.?\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 429,
            "translated_text": "\"Ya ƙãga ƙarya ga Allah ne kõ kuwa akwai wata hauka a gare shi?\" Ã'a, waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba, sunã a cikin azãba da ɓãta mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 429,
            "translated_text": "Ashe fa, ba su yi dũbi ba zuwa ga abin da ke a gaba gare su da abin da ke a bãyansu daga sama da ƙasã? idan Mun so, sai Mu shãfe ƙasã da su, kõ kuma Mu kãyar da wani ɓaɓɓake daga sama a kansu. Lalle, a cikin wancan akwai ãyã ga dukan bãwã mai maida al'amarinsa ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 429,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda wata falala dagagare Mu. Yã duwatsu, ku konkõma sautin tasbihi tãre da shi kuma da tsuntsãye. Kuma Muka tausasa masa baƙin ƙarfe."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 429,
            "translated_text": "Ka aikata sulkuna kuma ka ƙaddara lissãfi ga tsãrawa, kuma ka aikata aikin ƙwarai. Lalle NĩMai gani ne ga abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 429,
            "translated_text": "Kuma ga Sulaimãn, Mun hõre masa iska, tafiyarta ta safiya daidai da wata, kuma ta maraice daidai da wata. Kuma Muka gudãnar masa da marmaron gaci, kuma daga aljannu (Muka hõre masa) waɗanda ke aiki a gaba gare shi, da iznin Ubangijinsa. Wanda ya karkata daga cikinsu, daga umurninMu, sai Mu ɗanɗana masa daga azãbar sa'ĩr."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 429,
            "translated_text": "Sunã aikata masa abin da yake so, na masallatai da mutummutumai da akussa kamar kududdufai, da tukwãne kafaffu. Ku aikata gõdiya, yã ɗiyan Dãwũda, kuma kaɗan ne mai gõdiya daga bãyĩNa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 429,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da Muka hukunta mutuwa a kansa bãbu abin da ya ja hankalinsu, a kan mutuwarsa, fãce dabbar ƙasa (gara) wadda take cin sandarsa. To a lõkacin da ya fãɗi, sai aljannu suka bayyana (ga mutãne) cẽwa dã sun kasance sun san gaibi, dã ba su zauna ba a cikin azãba mai wulãkantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 430,
            "translated_text": "Lalle, haƙĩƙa, akwai ãyã ga saba'ãwa* a cikin mazauninsu: gõnakin lambu biyu, dama da hagu. \"Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gõdiya gare shi. Gari mai dãɗin zama, da Ubangiji Mai gãfara.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ƙissar Dãwũda da ta Sulaimãn sunã nũna yadda Allah ke sauƙaƙe wa bãyinsa hanyar ibãda da ta sãmun abinci da sauƙi idan sun mayar da al'amuransu gare shi. Ƙissar sabaãwa tanã nũna yadda Allah ke karɓe wadãta daga wanda ya kãfirce Masa"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 430,
            "translated_text": "Sai suka bijire sabõda haka Muka saki Mãlãlin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gõnakinsu biyu da waɗansu gõnaki biyu mãsu 'ya'yan itãce kaɗan: talãkiya da gõriba da wani abu na magarya kaɗan."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 430,
            "translated_text": "Wancan, da shi Muka yi musu sakamako sabõda kãfircinsu. Kuma lalle, bã Mu yi wa kõwa* irin wannan sakamako, fãce kafirai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah na saka wa kãfirai gwargwadon aikinsu, kuma Yanã yin falala ga mũmini da kyautar da ta fi aikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 430,
            "translated_text": "Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin* garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, \"Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Tafiya a tsakãnin Yemen, ƙasar Saba'awa da Syria, watau Sham, ƙasã mai albarka, ƙasarAnnabãwa kuma ƙasa mai yawan ruwa da itãce."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 430,
            "translated_text": "Sai suka ce: \"Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu,\" kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce* su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Muka sanya saba'ãwa suka wãtse a cikin waɗansu ƙasãshe sabõda ruwa ya halaka ƙasãrsu, sa'an nan kuma ta bũshe bãbu wadãta, har ana cewa 'Sun yi rarrabar Saba'ãwa' watau sun wãtse."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 430,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa, Iblĩs ya gaskata zatonsa a kansu, sai suka bi shi fãce wani ɓangare na mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 430,
            "translated_text": "Kuma bã ya da wani dalĩli a kansu fãce dai dõmin Mu san wanda yake yin ĩmãni da Lãhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kõme, Mai tsaro ne."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 430,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa), kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 431,
            "translated_text": "\"Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurinSa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye* tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma,\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Bãbu wanda ya san lõkacin bãyar da izni ga yin ceto kõ wanda zã a bai wa iznin ya yi, kõ a yi masa, Sabõda haka mutãne a Lãhira na cikin tsõro har a lõkacin da aka koranye tsõron ta hanyar bãyar da izni ga ceto babba ga Annabi Muhammadu, sai mũminai su yi farin ciki su dinga tambayar jũna da cewa, \"Menene Ubangijinku Ya ce?\" waɗansu su ce, \"Yã faɗi gaskiya' Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 431,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?\" Ka ce: \"Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 431,
            "translated_text": "Ka ce: \"Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 431,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ubangijinmu zai tãra tsakãninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 431,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 431,
            "translated_text": "Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 431,
            "translated_text": "Sunã cẽwa, \"Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance mãsu gaskiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 431,
            "translated_text": "Ka ce: \"Kunã da mi'ãdin wani yini wanda bã ku jinkirta daga gare shi kõ da sa'a ɗaya, kuma bã ku gabãta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 431,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: \"Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba, kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba (na waɗansu littattafan sama).\" Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa makangara (shũgabanni) \"Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 432,
            "translated_text": "Makangara suka ce wa maraunana, \"Ashe, mũ ne muka kange ku daga shiriya a bãyan ya zo muku? Ã, a' kun dai kasance mãsu laifi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 432,
            "translated_text": "Kuma maraunana suka ce wa makangara. \"Ã'a, (ku tuna) mãkircin dare da na rãna a lõkacin da kuke umurnin mu da mu kãfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abõkan tãrayya.\" Kuma suka assirtar da nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyin waɗanda suka kãfirta. Lalle, bã zã a yi musu sakamako ba fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 432,
            "translated_text": "Kuma ba mu aika wani mai gargaɗi ba a cikin wata alƙarya fãce mani'imtanta (shũgabanni) sunce, \"Lalle mũ, mãsu kãfirta ne da abin da aka aiko ku da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 432,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Mũ ne mafiya yawa ga dũkiya da ɗiya, kuma mu ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 432,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfiɗa arziki ga wanda Ya so, kuma Yanã ƙuntatãwa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 432,
            "translated_text": "Kuma dũkiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙãmi fãce wanda, ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai. To, waɗannan sunã da sakamakon ninkawa sabõda abin da suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin bẽnãye."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 432,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke mãkirci a cikin ãyõyinMu, sunã nẽman gajiyarwa, waɗannan abin halartãwa ne a cikin azãba."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 432,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfida arziki ga wanda Ya so daga bãyinSa, kuma Yanã ƙuntatãwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shĩ ne zai musanya shi, kuma Shĩ ne Mafi fĩcin mãsu azurtawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 433,
            "translated_text": "Kuma rãnar da Allah Ya ke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Ya ce wa Malã'iku, \"Shin, waɗannan kũ ne suka kasance sunã bauta wa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 433,
            "translated_text": "Sukace: \"Tsarki ya tabbata a gare Ka. Kai ne Majiɓincinmu, bã su ba. Ã'a, sun kasance sunã bauta wa aljannu. Mafi yawansu, da sũ suka yi ĩmani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 433,
            "translated_text": "Sabõda haka, a yau sãshenku bã ya mallakar wani amfãni ga wani sãshen, kuma bã ya mallakar wata cũta, kuma Munã cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wutã wadda \"kuka kasance game da ita, kunã ƙaryatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 433,
            "translated_text": "Kuma idan an karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, sai su ce: \"Wannan bai zama ba fãce namiji ne yanã son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance sunã bauta wa.\" Kuma su ce: \"Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya da aka ƙãga.\" Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: ga gaskiya a lõkacin da ta je musu: \"Wannan bã kõme ba fãce sihiri ne bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 433,
            "translated_text": "Kuma ba Mu bã su waɗansu littattafai ba waɗanda suke karãtun su, kuma ba Mu aika wani mai gargaɗi ba zuwa gare su a gabãninka!"
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 433,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata, alhãli kuwa ba su kai ushurin-ushurin abin da Muka bã su ba, sai suka ƙaryata ManzanniNa! To, yãya musũNa (ga maƙaryata) ya kasance?"
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 433,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu dõmin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunãni, bãbu wata hauka ga ma'abũcinku. Shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azãba mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 433,
            "translated_text": "Ka ce: \"Abin da na rõƙe ku na wani sakamako, to, amfãninsa nãku ne. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma shi Mahalarci ne a kan dukan kõme.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 433,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle Ubangijina Yanã jẽfa gaskiya. (Shi) Masanin abũbuwan fake ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 434,
            "translated_text": "Ka ce: \"Gaskiya ta zo, kuma ƙarya bã ta iya fara (kome) kuma bã ta iya mayarwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 434,
            "translated_text": "Ka ce: \"Idan na ɓace, to, inã ɓacẽwa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu, to, sabõda abin da Ubangijina Yake yõwar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shĩ Mai ji ne, Makusanci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 434,
            "translated_text": "Kuma dã kã gani, a lõkacin da suka firgita, to, bãbu kuɓuta, kuma aka kãma su daga wuri makusanci."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 434,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Mun yi ĩmãni da Shi.\" To inã zã su sãmu kãmãwa daga wuri mai nisa?"
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 434,
            "translated_text": "Kuma lalle sun kãfirta da Shi a gabãnin haka, kuma sunã jĩfa da jãhilci daga wuri mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 34,
            "page_number": 434,
            "translated_text": "Kuma an shãmakance a tsakãninsu da tsakãnin abin da suke marmari, kamar yadda aka aikata da irin ƙungiyõyinsu a gabãninsu. Lalle sũ sun kasance a cikin shakka mai sanya kõkanto."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 434,
            "translated_text": "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Mai fãra halittar sammai da ƙasã, Mai sanya malã'iku manzanni mãsu fukãfukai, bibbiyu, da uku-uku da hurhuɗu. Yanã ƙãrãwar abin da Ya ke so a cikin halittar. Lalle Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 434,
            "translated_text": "Abin da Allah Ya buɗa wa mutãne daga rahama, to, bãbu mai riƙewa a gare shi, kuma abin da Ya riƙe, to, bãbu mai saki a gare shi, waninSa, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 434,
            "translated_text": "Yã kũ mutãne! Ku tuna ni'imar Allah a kanku. Shin, akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da, ƙasã? Bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 435,
            "translated_text": "Kuma idan sun ƙaryata ka, to, lalle, an ƙaryata waɗansu Manzanni a gabãninka, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 435,
            "translated_text": "Yã kũ mutãne! Lalle wa'adin Allah gaskiya ne, sabõda haka kada rãyuwar dũniya ta rũɗar da ku, kuma kada marũɗi ya rũɗe ku game da Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 435,
            "translated_text": "Lalle Shaiɗan maƙiyi ne a gare ku, sai ku riƙe shi maƙiyi. Yanã kiran ƙungiyarsa kawai ne, dõmin su kasance 'yan sa'ir."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 435,
            "translated_text": "Waɗanda suka kãfirta suna da azãba mai tsanani kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wata gãfara da sakamako mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 435,
            "translated_text": "Shin to, wanda aka ƙawãta masa aikinsa, har ya gan shi mai kyau (yanã daidai da waninsa)? Sabõda haka, lalle, Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so, kuma Yanã shiryar da wanda Yake so, sabõda haka kada ranka ya halaka a kansu dômin baƙin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sanã'antawa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 435,
            "translated_text": "Kuma Allah ne Ya aika da iskõki har su mõtsar da girgije, sa'an nan Mu kõra shi zuwa ga gari matacce, sa'an nan Mu rãyar da ƙasã game da shi a bayan mutuwarta. Kamar wancan ne Tãshin ¡iyãma yake."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 435,
            "translated_text": "Wanda ya kasance yanã nẽman wata izza, to, Allah ne da izza gabã ɗaya. zuwa gare Shi magana mai dãɗi ke hawa, kuma aiki na ƙwarai Yanã ɗaukar ta Kuma waɗanda ke yin mãkircin mũnanan ayyuka, sunã da wata azãba mai tsanani, kuma mãkircin waɗannan yanã yin tasgaro."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 435,
            "translated_text": "Kuma Allah ne Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga ɗigon maniyyi, sa'an nan Ya sanya ku surkin maza da mãtã. Kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma bã zã a rãyar da wanda ake rãyarwa ba, kuma bã zã a rage tsawon ransa ba fãce yanã a cikin Littãfi. Lalle, wancan mai sauki ne ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 436,
            "translated_text": "Kuma kõguna biyu ba su daidaita: Wannan mai ruwan dãɗi, mai zãƙi, mai sauƙin haɗiya kuma wannan mai ruwan gishiri mai zartsi, kuma daga kõwane, kunã cin wani nama sãbo, kuma kunã fitar da kawa wadda kuke tufantarta, kuma kanã ganin jirãge a cikinsa sunã mãsu gudãna, dõmin ku nẽmo daga falalarSa, kuma ɗammãninku zã ku dinga gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 436,
            "translated_text": "Yanã shigar da dare a cikin rãna, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare. Kuma Ya hõre rãnã da watã kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce Wannan Shĩ ne Allah, Ubangijinku, gare Shi mulki yake, kuma waɗanda kuke kira waninSa bã su mallakar kõ fãtar gurtsun dabĩno."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 436,
            "translated_text": "Idan kun kira su, bã zã su ji kiranku ba, kuma kõ sun jiya, bã zã su karɓa muku ba, kuma a Rãnar ¡iyãma zã su kãfirce wa shirkinku, kuma bãbu mai bã ka lãbãri, kamar wanda ya sani."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 436,
            "translated_text": "Yã kũ mutãne! Kũ ne mãsu bukãta zuwa ga Allah, kuma Allah, Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 436,
            "translated_text": "Idan Ya so, zai tafi da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 436,
            "translated_text": "Kuma wancan bai zama mabuwãyi ba ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 436,
            "translated_text": "Kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bai ɗaukar nauyin wani rai. Kuma idan ran da aka nauyaya wa kãya ya yi kira (ga wani mataimaki) zuwa ga kãyansa, bã zã a dauki kõme ba daga gare shi, kuma kõ dã (wanda ake kiran) yã kasance makusancin zumunta ne. Kanã gargaɗi kawai ne ga waɗanda ke tsoron Ubangijinsu a fake, kuma suka tsayar da salla. Kuma wanda ya tsarkake, to, yanã tsarkaka ne dõmin kansa. Kuma zuwa ga Allah kawai makõma take."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Kuma makãho bã ya daidaita da mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Kuma duffai bã su daidaita, kuma haske bã ya daidaita."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Kuma inuwa bã ta daidaita, kuma iskar zãfi bã ta daidaita."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Kuma rãyayyu bã su daidaita kuma matattu ba su daidaita. Lalle Allah Yanã jiyar da wa'azi ga wanda Ya so, kuma ba ka jiyar da waɗanda suke a cikin kaburbura."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Ba ka zama ba fãce mai gargaɗi kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Lalle Mũ Mun aike ka da gaskiya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Kuma bãbu wata al'umma fãce wani mai gargaɗi yã shũɗe a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Kuma idan sunã ƙaryata ka, to, haƙĩƙa, waɗanda suke a gabãninsu sun ƙaryata. Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji, kuma da takardu, kuma da Littafi mai haske."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Sa'an nan Na kãma waɗanda suka kãfirta. To, yãya musũNa yake?"
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Ba ka gani ba, lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama? Sai Muka fitar, game da shi,'yã'yan itãce mãsu sãɓanin launuka kuma daga duwatsu akwai zane-zane, farfaru da jãjãye, mãsu sãɓanin launin, da mãsu launin baƙin ƙarfe, baƙãƙe."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Kuma daga mutãne da dabbõbi da bisãshen gida, mãsu sãɓãnin launinsu kamar wancan. Malamai kawai ke tsõron Allah daga cikin bãyinSa. Lalle, Allah, Mabuwãyi ne, Mai gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Lalle waɗanda ke karãtun Littãfin Allah* kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sunã fãtan (sãmun) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Littattafan sama a gabãnin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 437,
            "translated_text": "Dõmin (Allah) zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙarã musu daga falalarSa. Lalle Shi Mai gãfara ne, Mai gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 438,
            "translated_text": "Kuma abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, daga Littãfi,"
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 438,
            "translated_text": "Sa'an nan Mun gãdar da Littãfin, ga waɗanda Muka zãɓa daga bãyinMu, sa'an nan daga cikinsu, akwai mai zãlunci ga kansa, kuma daga cikinsu akwai mai tsakaitãwa, kuma daga cikinsu akwai mai tsẽrẽwa da ayyukan alhẽri da iznin Allah. Waccan ita ce falalar (Allah) mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 438,
            "translated_text": "Gidãjen Aljannar zamã sunã shigar su. Anã ƙawãce su a cikinsu, da ƙawã ta mundãye daga zĩnãriya da lu'ulu'u, kuma tufãfinsu, a cikinsu alharĩni ne."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 438,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tafiyar da baƙin ciki daga gare mu. Lalle Ubangijinmu, haƙĩƙa Mai gafarane, Mai godiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 438,
            "translated_text": "\"Wanda Ya saukar da mu a gidan zamã, daga falalarSa, wata wahala bã ta shãfar mu a cikinsa, kuma wata kãsãwa bã ta shãfar mu a cikinsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 438,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta sunã da wutar Jahannama, bã a yin hukunci a kansu balle su mutu kuma bã a sauƙaƙa musu daga azãbarta. Kamar haka Muke sãka wa kõwane mai yawan kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 438,
            "translated_text": "Kuma sũ, sunã hargõwar nẽman ãgaji a cikinta. (Sunã cẽwa) \"Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu, mu aikata aiki mai kyau, wanin wanda muka kasance munã aikatãwa.\" Ashe, kuma, ba Mu rãyar da ku ba, abin da mai tunãni zai iya yin tunãni a ciki, kuma mai gargaɗi yã jẽ muku? To, ku ɗanɗana, sabõda haka bãbu wani mataimaki, ga azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 438,
            "translated_text": "Lalle Allah ne Masanin gaibin sammai da ƙasã. Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake ainihin zukata."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 439,
            "translated_text": "Shĩ ne Wanda Ya sanya ku mãsu maye wa junã, a cikin ƙasã. To, wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa yanã a kansa. Kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme fãce baƙin jini, kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme face hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 439,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kun ga abũbuwan shirkinku, waɗanda kuke kira, wasun Allah? Ku nũna mini, mẽne ne suka halitta daga ƙasã? Kõ sunã da tãrayya ne a cikin sammai? Kõ kuma Mun bã su wani littãfi ne sabõda haka sunã a kan wata hujja ce daga gare shi? Ã'a, azzãlumai bã su yin wani wa'adi, sãshensu zuwa ga sãshe, fãce rũɗi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 439,
            "translated_text": "Lalle Allah Yanã riƙe sammai da ƙasã dõmin kada su gushe. Kuma haƙĩƙa, idan sun gushe, bãbu wani baicinSa da zai riƙe su. Lalle Shi Yã kasance Mai haƙuri, Mai gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 439,
            "translated_text": "Kuma suka* yi rantsuwa da Allah, mafi nauyin rantsuwarsu, \"Lalle, idan wani mai gargaɗi ya zo musu tabbas zã su kasance mafi shiryuwa, daga ɗayan al'ummõmi.\" To, a lõkacin da mai gargaɗi ya jẽ musu, bai ƙarã su da kõme ba fãce gudu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Lãrabãwa sun kasance sunã gũri su sãmi mai ja musu gõra kamar Yahũdu kõ Nasãra, sa'an nan Muhammadu ya je musu, sai suka kãfirce."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 439,
            "translated_text": "Dõmin nũna girman kai a cikin ƙasã da mãkircin cũta. Kuma mãkirci na cũta bã ya fãdãwa fãce a kan mutãnensa. To shin sunã jiran (wani abu ne) fãce dai hanyar (kãfiran) farko. To, bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah. Kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyar Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 439,
            "translated_text": "Ashe, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗannan da suke a gabãninsu ta kasance? Alhãli kuwa sun kasance mafĩfĩta ƙarfi daga gare su? Kuma Allah bai kasance wani abu nã iya rinjãyarSa ba, a cikin sammai, kuma haka a cikin kaƙã. Lalle Shi ne Ya kasance Masani, Mai ĩkon yi."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 35,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne sabõda abin da suka aikata, dã bai bar wata dabba ba a kanta (kasã). Amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambatã. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, to, lalle Allah yã kasance Mai gani ga bãyinSa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Y. S̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni* Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Al-ƙur'ãni ma'anarsa abin karãtu. "
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikinManzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "A kan hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "(Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Lalle, haƙĩƙa, kalma* tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kalma a nan ita ce faɗar Allah da take cewa zai yi azãba ga kãfirin da bai yi ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 440,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni* suka jẽ mata.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Su Manzannin Ĩsã ne zuwa Antãkiya, bãbban garin kasar Rũmu. Sũ ne Yõhana da Pulis. Na uku, shĩ ne sham'ũn. Mutumin da ya jħ yanã gaggawa, shi ne Habĩb Masassaki wanda ya fãra gamuwa da Manzannin farko, ya yi ĩmãni da su, sa'an ya jħ yanã wa'azi ga mutãnensa. "
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: \"Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "Suka ce: \"Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "\"Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "Suka ce: \"Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: \"Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "\"Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "\"Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku?\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "\"Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "\"Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "\"Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "Aka ce *(masa), \"Ka shiga Aljanna.\" Ya ce, \"Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * An ce masa haka a bayan mutãne sun kashe shi sabõda ĩmãninsa. Wannan shi ne sakamakon mai wa'azi idan ya yi shahada a kan aikinsa na wa'azi."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 441,
            "translated_text": "\"Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama* a kan (halaka) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wãtau halakar da su abu ne mai sauƙi a gare Mu, ba Mu yi bukãtar saukar da wasu sõjõjin malã'iku daga samã ba."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Yã nadãma a kan bãyĩNa! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurinMu."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Kuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 442,
            "translated_text": "Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Kuma ãyã ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lõdi."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Kuma idan Mun so, zã Mu nutsar da su, har bãbu kururuwar neman ãgaji, a gare su, kuma ba su zama anã tsirar da su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dãɗi zuwa ga wani ɗan lõkaci."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Kuma idan aka ce musu, \"Ku kãre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a bãyanku, dõmin tsammãninku a ji tausayinku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Kuma wata ãyã daga ãyõyin Ubangijinsu bã ta zuwa a gare su, sai sun kasance sunã mãsu bijirẽwa daga gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Kuma idan aka ce musu, \"Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku,\" sai waɗanda suka kãfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmãni, \"Ashe, zã mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yanã ciyar da shi? Ba ku zama ba fãce a cikin ɓata bayyananniya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Kuma sunã cẽwa, \"A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance mãsu gaskiya?\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Bã su jiran (kõme) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin husũma."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Bã zã su iya yin wasiyya* ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mãsu izgili ga addini idan ajali ya je musu bisa ga abke, bã zã a bã su dãmar wasiyya ba ga iyãlansu."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sunã ta gudu."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Suka ce: \"Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu?\" \"Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "Ba ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a gare Mu."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 443,
            "translated_text": "To, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "\"Aminci,\" da magana,* daga Ubangiji Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ana ce musu aminci ya tabbata a gare ku, da magana daga wajen Ubangijinsu Mai rahama, watau ana fada musu haka da magana bã da wata ishãra ba. "
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "\"Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "\"Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "\"Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "\"Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "\"Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita.\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "\"Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "Dã Mun so, dã Mun shãfe gani *daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Dã Mun so shãfe ganinsu na ido kamar yadda Muka shãfe basĩrarsu ta hankali, dã Mun shãfe shi, sai su zama makãfin idãnu kamar yadda suke makãfin zũci. Sabõda haka ko sun so gani, bã zã su yi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta?"
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "Ba Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 444,
            "translated_text": "Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Shin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su?"
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Kuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Kuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su gõdẽ ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake su."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Bã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wutã)."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Sabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Ashe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: \"Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Ka ce: \"Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "\"Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "\"Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne, Mai ilmi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, \"Ka kasance,\" sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi)."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 36,
            "page_number": 445,
            "translated_text": "Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi)."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Sa'an nan mãsu yin tsãwa* dõmin gargaɗi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mãsu tsãwa, sũ ne Malamai mãsu sãmun ilmin wa'azi daga Annabãwa waɗanda ke karãtun abin tunãwa daga Allah Ubangijin sammai da ƙasa, Mai bãyar da haske ga rãnã, Mai haskaka taurari mãsu ƙãwãtar da samã kuma su tsare ta daga shaiɗanu. An siffanta rãnã da Annabãwa, Malamai da taurãri, ilmi da haske da sababin ƙawa da shiryarwa da kõrar mãsu ɓarna."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Ka tambaye su: \"Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?\" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Kuma su ce, \"Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "\"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "\"Ashe kõ da ubanninmu na farko?\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Ka ce: \"Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Kuma su ce: \"Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 446,
            "translated_text": "Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?"
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince).\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ã'a, ba ku kasance mũminai ba."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "\"Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "\"Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "\"Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: \"Bãbu abin bautãwa, fãce Allah,\" sai su dõra girman kai."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Kuma sunã cẽwa, \"Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?"
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Waɗannan sunã da abinci sananne."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "A cikin gidãjen Aljannar ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Farã mai dãɗi ga mashãyan."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,"
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 447,
            "translated_text": "Wani mai magana daga cikinsu ya ce: \"Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya).\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Yanã cewa, \"Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "\"Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "(Mai maganar) ya ce: \"Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?\""
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Ya ce (masa), \"Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "\"Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã).\""
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "\"Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "\"Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?"
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 448,
            "translated_text": "Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, \"Mẽne ne kuke bautãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "\"Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "\"To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri."
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Sã'an nan ya ce: \"Nĩ mai rashin lãfiya ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya."
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: \"Ashe bã zã ku ci ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "\"Me ya sãme ku, bã ku magana?\""
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Ya ce, \"Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,"
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "\"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 97,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm.\""
        },
        {
            "ayah_number": 98,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci."
        },
        {
            "ayah_number": 99,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Kuma (Ibrahĩm] ya ce: \"Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 100,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "\"Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 101,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro *mai haƙuri.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Yãron da aka yi bushãra da shi a nan, shĩ ne Ismã'ĩla' sabõda abin da yake tafe a gaba wanda ya shãfi Is'hãƙa da sũnansa a bayyane yã nũna a nan bã shi ba ne. Watau Ismã'ĩla kawai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 102,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 449,
            "translated_text": "To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: \"Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?\" (Yãron) ya ce: \"Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri.\""
        },
        {
            "ayah_number": 103,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago"
        },
        {
            "ayah_number": 104,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka kira shi cẽwa \"Ya Ibrahĩm!\""
        },
        {
            "ayah_number": 105,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "\"Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin.\" Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 106,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna."
        },
        {
            "ayah_number": 107,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 108,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe."
        },
        {
            "ayah_number": 109,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 110,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 111,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 112,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka yi masa bushãra* Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wannan sãbuwar bushãra da Is'hãƙa tanã nũna cewa bã shĩ ne wanda kissar yankã ta shãfa ba sabõda haka Isma'ĩla dai ne tabbas, mai ƙissar yankã. Sabõda haka Allah Ya sanya shi wata al'umma dabam' dõmin a sãka masa, sa'an nan aka sãkawa Ibrãhĩm da Is'hãƙa dõmin ya zama wata al'umma ta dabam,."
        },
        {
            "ayah_number": 113,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin)."
        },
        {
            "ayah_number": 114,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna."
        },
        {
            "ayah_number": 115,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 116,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya."
        },
        {
            "ayah_number": 117,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni."
        },
        {
            "ayah_number": 118,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya."
        },
        {
            "ayah_number": 119,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe."
        },
        {
            "ayah_number": 120,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna."
        },
        {
            "ayah_number": 121,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 122,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 123,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 124,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, \"Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 125,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "\"Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?\""
        },
        {
            "ayah_number": 126,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 450,
            "translated_text": "\"Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?\""
        },
        {
            "ayah_number": 127,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã)."
        },
        {
            "ayah_number": 128,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
        },
        {
            "ayah_number": 129,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe."
        },
        {
            "ayah_number": 130,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Aminci ya tabbata ga Ilyãs."
        },
        {
            "ayah_number": 131,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 132,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 133,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 134,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 135,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba)."
        },
        {
            "ayah_number": 136,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen."
        },
        {
            "ayah_number": 137,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci."
        },
        {
            "ayah_number": 138,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 139,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 140,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi."
        },
        {
            "ayah_number": 141,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya."
        },
        {
            "ayah_number": 142,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi."
        },
        {
            "ayah_number": 143,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,"
        },
        {
            "ayah_number": 144,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su."
        },
        {
            "ayah_number": 145,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya."
        },
        {
            "ayah_number": 146,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 147,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka)."
        },
        {
            "ayah_number": 148,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci."
        },
        {
            "ayah_number": 149,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka tambaye su, \"Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?\""
        },
        {
            "ayah_number": 150,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?"
        },
        {
            "ayah_number": 151,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 152,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "\"Allah Yã haihu,\" alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne."
        },
        {
            "ayah_number": 153,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 451,
            "translated_text": "Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?"
        },
        {
            "ayah_number": 154,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?"
        },
        {
            "ayah_number": 155,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Shin, bã ku tunãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 156,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 157,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 158,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, \"Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)\""
        },
        {
            "ayah_number": 159,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 160,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
        },
        {
            "ayah_number": 161,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,"
        },
        {
            "ayah_number": 162,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 163,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 164,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "\"Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,* fãce yanã da matsayi sananne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Malã'iku da sauran halitta duka kõwa yã san matsayinsa na bauta ga Allah wanda ba Ya da dã ko diya, kuma ba Ya da dangantaka da kõwa. "
        },
        {
            "ayah_number": 165,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "\"Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda).\""
        },
        {
            "ayah_number": 166,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "\"Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 167,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,"
        },
        {
            "ayah_number": 168,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "\"Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 169,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "\"Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.\""
        },
        {
            "ayah_number": 170,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani."
        },
        {
            "ayah_number": 171,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 172,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako."
        },
        {
            "ayah_number": 173,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya."
        },
        {
            "ayah_number": 174,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci."
        },
        {
            "ayah_number": 175,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan ƙãrin bayãni ne ga abin da sũrar ke karantarwa na cewa Annabãwa sũ ne kamar rãna mai haske na asali. Mãlamai kamar taurãri suke mãsu sãmun haske daga rana su wãtsa ga dũniya kuma su kõre ɓarna. Aya ta l79 da ke tafe karfafawa ce ga ma'anar wannan."
        },
        {
            "ayah_number": 176,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 177,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 178,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci."
        },
        {
            "ayah_number": 179,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 180,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 181,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 182,
            "surah_number": 37,
            "page_number": 452,
            "translated_text": "Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu)."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, \"Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "\"Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!\""
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),\"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi!\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "\"Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "\"Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?\" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta?"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu)."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa)."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, *waɗancan ne ƙungiyõyin.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Mutãnen ƙunci, sũ ne mutãnen Annabi Shu'aibu. A cikin Sham suke."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Kuma waɗannan *bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Watau mutãnen Annabi Muhammadu: Ƙuraishãwa da waninsu har ya zuwa Tashin Ƙiyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 453,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ita ce maganar dukan kãfirai na kõwane zãmani mãsu nħman rabon dũniya kawai, ba su yarda da Tãshin Ƙiyãma ba, balle sãmun sakamako a cikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwanMu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima* da rarrabẽwar magana.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Hikima, ita ce Annabci, rarrabe magana, shĩ ne sanin hanyar yin sharĩ'a da rarrabe mai ƙãra daga wanda aka yi ƙãra, da neman shaidu daga mai ƙãra da neman rantsuwa ga mai musu."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci?"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: \"Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "\"Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "(Dãwũda) ya ce: \"Lalle, haƙiƙa ya zãlunce* ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai.\" Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara, kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Dãwũda ya yi hukunci da zãlunci ga wanda ya yi ƙãra, sabõda abin da ya rufe shi na ƙin zãluntar mai rauni wanda Allah Ya hana. Nauyin wani laifi ya rufe shi daga tunãwa da wani laifi, watau yin hukunci tun binciken shari'a bai cika ba, sabõda iya maganar wani abõkin ƙãra. Wannan shĩ ne fitinar da ta same shi kawai kuma a kanta ya yi nadãma, kuma a kanta ne Allah Ya yi masa gargaɗin kada ya bi son rai mai sanya Fushi kõ yarda ga abin da bai cancanci haka ba. Yarda da wata ƙissar mãtar Uriya wadda Yahũdãwa ke sanyãwa, a nan, kãfirci ne ga Musulmi, dõmin ta kõre ismar Annabãwa, kuma ba ta dãce da lafazin Alƙur'ãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "Sabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a wurinMu, da kyaun makõma."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 454,
            "translated_text": "Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi"
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata?"
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "(Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, *a lõkacin maraice.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Shĩ ne dõki mai tsayuwa a kan ƙafãfu uku. Wannan yanã nũna asalinsa mai kyau ne."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Sai ya ce: \"Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki!\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "\"Ku mayar da su a gare ni.\" Sai ya shiga yankansu* da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sulaimãna ya yanka dawãkin,dõmin kallonsu yã hana shi salla, wadda take farlu ainin ce a gare shi, amma tattalin kãyan yãƙi farlu kifãya ce. Anã gabãtar da farlu ainin a kan farlu kifãya. Wannan kuma ya nũna cewa anã cin dõki idan wani dalĩli bai hana ba. Dũbi Sũra ta 16, ãyã ta 8."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini* Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wata rãna Sulaiman ya yi tunãnin ya sãdu da mãtansa ɗari uku, dõmin su yi cikunna su haifi diya mãsu taimakonsa jihãdi fi sabilillahi, amma ya manta, bai ce in Allah Yã so ba. Sai ya sãdu da su, ba su yi cikin ba, sai guda ɗaya daga cikinsu, kuma ta haife shi bãbu rai. Ma'anar kissar, ita ce ko aikin Allah, sai mutum ya mayar da yinsa ga mashĩ'ar Allah, sa'an nan zai ci nasara a kansa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna.* Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Yã yi wannan addu'a dõmin kada wani ya yi alfahari da sarauta a bãyansa, ya halaka kuma ya halakar da wani. Sarauta ita ce asalin girman kai da alfahari. Bã ka ganin wanda ya shiga wajan sarki, dõmin ya gaishe shi, idan ya fito daga gare shi, sai ya ɗõra yin tãƙama dõmin abin da zuciyarsa ta ɗebo daga girman kan sarkin da alfaharinsa?."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Sabõda haka Muka hõre masa iska(5) tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  (5) An hore masa iska matsayin dawãkin da ya yanke dõmin Allah. An hõre masa aljannu dõmin niyyarsa ta sãmun diya mãsu jihãdi dõmin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.)"
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Wannan kyautarMu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurinMu da kyaun makõma."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba(6) a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: \"Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  (6) Wannan ƙissa tanã nũna haƙuri ga riƙon iyãli, mulkin ƙasã da mulkin gida duka daidai suke, sai yadda Allah Ya yi umurni a yĩ su. Haka mallakar rai idan mutum bai bi umurnin Allah ba a cikinsu, sai su buwãye shi tsarewa, kamar yadda mulkin ƙasa ke buwãya a riƙe shi tãre da kãfirci da zãlunci."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 455,
            "translated_text": "Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci bãyinMu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurninMu) da basĩra."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira)."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Kuma lalle sũ a wurinMu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Gidãjen Aljannar zama, alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwarMu ce, bã ta ƙãrẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu.\" To, matabbatar tã mũnana (ita wutar)."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 456,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "\"Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Ka ce: \"Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "\"Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma\"."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "\"Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!\""
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "\"Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "\"Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, \"Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "\"Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga RuhĩNa a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "(Allah) Ya ce, \"Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Ya ce, \"Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Ya ce, \"To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "\"Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako.\""
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Ya ce, \"Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su.\""
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Ya ce, \"To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri,"
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "\"Zuwa ga yinin lõkaci sananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "Ya ce, \"To, inã rantsuwa da buwãyarKa, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 457,
            "translated_text": "\"Fãce bãyinKa tsarkakakku daga gare su.\""
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "(Allah) Ya ce, \"To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "\"Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya\""
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "Ka ce: \"Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "\"Shĩ (Alkur'ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 38,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "\"Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa* a bayan ɗan lõkaci.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bauta wa gumãka da hidimar shehunai da suka mutu waɗanda suka shirya wani sãbon abu da bãbu ga sunnar Annabi duka ɗaya suke, dõmin kõwanensu kiran wanin Allah ne sabõda neman ãgaji."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "Saukar da Littãfin daga Allah ne, Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "Mun saukar da littafi a gareka da Gaskiya ka bautawa Allah kana mai tsarkake Addini a gare shi"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) \"Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja.\" Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 458,
            "translated_text": "Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 459,
            "translated_text": "Yã halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma ya saukar muku daga dabbõbin gida nau'i takwas Yanã halitta ku a cikin cikunnan uwayenku, halitta a bãyan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shĩ ne Allah Ubangijinku. Mulki a gare shi yake. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 459,
            "translated_text": "Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da kãfirci ga bãyinSa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar) a gare ku, kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma makõmarku zuwa ga Ubangijinku take, dõmin Ya bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. Lalle Shĩ, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 459,
            "translated_text": "Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), \"Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga 'yan wutã ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 459,
            "translated_text": "Shin, wanda yake mai tawãli'u sã'õ'in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai da waninsa?) Ka ce: \"Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba?\" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 459,
            "translated_text": "Ka ce: (Allah Ya ce): \"Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai fãɗi *ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani lissãfi ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bãbu dalĩli da zai sanya mutum ya zauna a inda bã ya iya bautawa Ubangijinsa da kyau. Watau hijira zuwa wurin yardar Allah, wãjibi ne, sai idan dũniya ta zama haka a kõ'ina bãbu wurin tafiya, kõ kuma tafiya can da wuya ƙwarai tanã kallafa nauyin da zai zama wani laifin da ke daidai da rashin hijirar, to, sai mutum ya zauna, ya tsare kansa gwargwadon hãli."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle nĩ, an umurce ni da in bauta wa Allah, inã tsarkake addini a gare Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "\"Kuma an umurce ni da in kasance farkon mãsu miƙa wuya (ga umurnin Allah).\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle nĩ inã tsõro, idan na sãɓã wa Ubangijĩna, ga azãbar yini mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "Ka ce: \"Allah nake bautã wa, inã mai tsarkake addinĩna a gare Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "\"To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa.\" Ka ce: \"Lalle mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa, ita ce hasãra bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka nĩsanci Shaiɗannu ga bauta musu, kuma suka mai da al'amari ga Allah, sunã da bushãra. To, ka bãyar da bushãra ga bãyiNa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "Waɗanda ke sauraren* magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali,<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bãyin Allah na ƙwarai sũ ne waɗanda suke saurãren maganar Allah, sa'an nan su yi aiki da abin da yake mai bayyanannar ma'ana daga gare ta, kuma su bar abin da ba su gãne ma'anarsa ba bãyan sun yi ĩmãni da shi cewa daga Allah yake, kuma su tsarkake Allah daga abin da ba ya sifantuwa da Shi na sũrõrin hãlittarSa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "Shin fa, wanda kalmar azãba ta wajaba a kansa? Shin fa, kanã iya tsãmar da wanda ke a cikin wutã?"
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah. Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 460,
            "translated_text": "Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna)."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa'an nan shi yanã a kan haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata bayyananna."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Allah Ya sassaukar da mafi kyaun lãbãri, Littãfi mai kama da jũna, wanda ake konkoma karãtunsa fãtun waɗanda ke tsõron Ubangijinsu, sunã tãƙura sabõda Shi, sa'an nan fãtunsu da zukãtansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Shin fa, wanda ke kãre mũguwar azãba da fuskarsa (yanã zama kamar waninsa) a Rãnar ƙiyãma? Kuma a ce wa azzãlumai, \"Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata, sai azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Sai Allah Ya ɗanɗana musu azãbar wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi girma, dã sun kasance sunã da sani."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun buga wa mutãne a, cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli, ɗammãninsu su yi tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Abin karantãwa ne na Lãrabci, ba mai wata karkata ba, ɗammãninsu, su yi taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Allah Yã buga misãli; wani mutum (bãwa) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun hãlin jãyayya, da wani mutum (bãwa) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah (a kan bayãni). Ã'a, mafi yawan mutãne ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Lalle kai mai mutuwa ne, kuma su mã lalle mãsu mutuwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 461,
            "translated_text": "Sa'an nan, lalle kũ, a Rãnar ¡iyãma, a wurin Ubangijinku, zã ku yi ta yin husũma."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 462,
            "translated_text": "To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta jẽ masa? Shin bãbu mazauni a cikin Jahannama ga kãfirai?"
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 462,
            "translated_text": "Kuma wanda ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata a game da ita, waɗancan sũ ne mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 462,
            "translated_text": "Sunã da abin da suke so wajen Ubangijinsu. Wancan shĩ ne sakamakon mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 462,
            "translated_text": "Dõmin Allah Ya kankare musu mafi mũnin abin da suka aikata, kuma Ya sãkã musu ijãrarsu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 462,
            "translated_text": "Ashe Allah bai zama Mai isa ga BãwanSa ba? Kuma sunã tsõratar da kai ga waɗanda suke waninSa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bã, shi da mai shiryarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 462,
            "translated_text": "Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, bã shi da mai ɓatarwa. Ashe, Allah bai zama Mabuwãyi ba, Mai azãbar rãmuwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 462,
            "translated_text": "Kuma lalle idan ka tambaye su: \"Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?\" Haƙĩƙa, zã su ce, \"Allah ne.\" Ka ce: \"Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan mãsu kãme rahamarSa ne?\" Ka ce: \"Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke dõgara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 462,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle nĩ, inã aiki a kan hãlĩna. Sa'an nan zã ku sani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 462,
            "translated_text": "\"Wanda azãba ta je masa, zã ta wulãkanta shi, kuma wata azãba mai dawwama za ta sauka a kansa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 463,
            "translated_text": "Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa'an nan wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 463,
            "translated_text": "Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 463,
            "translated_text": "Kõ kuma sun riƙi mãsu cẽto ne, waɗansun Allah? Ka ce: \"Shin, kuma kõ dã sun kasance bã su da mallakar kõme, kuma bã su hankalta?\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 463,
            "translated_text": "Ka ce: \"Cẽto gabã ɗaya ga Allah yake. Mulkin sammai da ƙasã Nãsa ne. Sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 463,
            "translated_text": "Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasunSa, sai gãsu sunã yin bushãrar farin ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 463,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane! Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 463,
            "translated_text": "Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a Rãnar ¡iyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 464,
            "translated_text": "Mũnãnan ayyuka da suka aikata, suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi, na izgili, ya wajaba a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 464,
            "translated_text": "To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa'an nan idan Muka canza masa ita, ya sãmi ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: \"An bã ni ita ne a kan wani ilmi nãwa kawai.\" Ã'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 464,
            "translated_text": "Lalle waɗanda ke a gabãninsu, sun faɗe ta, sabõda haka abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su da kõme ba."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 464,
            "translated_text": "Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma ba su zama mabuwãya ba."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 464,
            "translated_text": "Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 464,
            "translated_text": "Ka ce: (Allah Ya ce): \"Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 464,
            "translated_text": "\"Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin azãba ta zo muku, sa'an nan kuwa bã zã a taimake ku ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 464,
            "translated_text": "\"Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 464,
            "translated_text": "\"Kada wani rai ya ce: 'Yã nadãmãta a kan abin da na yi sakaci a cikin sãshen Allah' kuma lalle na kasance, haƙĩƙa, daga mãsu izgili!\"'"
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "\"Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa.'\""
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "\"Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba, 'Dã lalle a ce inã da wata kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa.'\""
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "\"Na'am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai?"
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "Kuma Allah na tsĩrar da waɗanda suka yi taƙawa a game da wurin sãmun babban rabonsu, cũta bã zã tashãfe su ba, kuma ba su zama sunã baƙin ciki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "Shĩ ke da mabũɗan sammai da ƙasã. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, wanin Allah kuke umurni na da in bauta wa? Yã ku jãhilai!\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, \"Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "Ã'aha! Ka bauta wa Allah kaɗai, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 465,
            "translated_text": "Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin* ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Yã yi bayãnin yadda zã a iya ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinSa da cewa, \"ƙasã duka damƙarSa ce har zuwa ƙarshen sũrar. Wãtau yã dunƙule sũrar abũbuwan da zã su auku a Rãnar Ƙiyãma dõmin su bai wa mai hankali yadda suranta ikon yi na Allah Mai girma zai yiwu."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 466,
            "translated_text": "Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 466,
            "translated_text": "Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 466,
            "translated_text": "Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani game da abin da suke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 466,
            "translated_text": "Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, \"Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?\" Suka ce, \"Na'am, \"kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!\""
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 466,
            "translated_text": "Aka ce, \"Ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kaunã madawwama a cikinta. Sa'an nan mazaunin makangara yã munana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 466,
            "translated_text": "Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, \"Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama (a cikinta).\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 466,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa, kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so.\" To, madalla da ijãrar ma'aikata."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 39,
            "page_number": 467,
            "translated_text": "Kuma kanã ganin malã'iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga kẽwayen Al'arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce, \"Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 467,
            "translated_text": "Ḥ. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 467,
            "translated_text": "Saukar da Littãfi daga Allah ne, Mabuwãyi, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 467,
            "translated_text": "Mai gãfarta zunubi kuma Mai karɓar tũba Mai tsananin azãba, Mai wadãtarwa bãbu abin bautawa fãce Shi, zuwa gare Shi makõma take."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 467,
            "translated_text": "Bãbu mai jãyayya a cikin ãyõyin Allah, fãce waɗanda suka kãfirta. Sabõda haka kada jũyãwarsu a cikin garũruwa ta rũɗe ka"
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 467,
            "translated_text": "Mutãnen Nũhu sun ƙaryata a gabãninsu, da ƙungiyõyin da suke a bãyansu, kuma kõwace al'umma tã yi nufi game da Manzonsu, dõmin su kãmã shi. Kuma suka yi jãyayya da ƙarya dõmin su gusar da gaskiya da ita. Sai Na kãmã su. To, yãya azãbãTa take?"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 467,
            "translated_text": "Kuma kamar haka kalmar Ubangijinka ta wajaba a kan waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ 'yan wutã ne."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 467,
            "translated_text": "Waɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kẽwayenta, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, kuma sunã yin ĩmãni da Shi, kuma sunã yin istigfãri dõmin waɗanda suka yi ĩmãni, (sunã cẽwa), \"Yã Ubangijinmu! Kã yalwaci dukan kõme da rahama da ilmi to Ka yi gãfara ga waɗanda suka tũba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare musu azãbar Jahĩm.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 468,
            "translated_text": "\"Ya Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su a gidãjen Aljannar zama, wannan da Ka yi musu wa'adi, sũ da wanda ya kyautatu daga ubanninsu da mãtan aurensu da zurriyarsu. Lalle Kai, Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima.\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 468,
            "translated_text": "\"Kuma Ka tsare su daga mũnãnan ayyuka, kuma wanda Ka tsare shi daga mũnãnan ayyuka a rãnarnan, to, lalle, Ka yi masa rahama kuma wancan shi ne babban rabo mai girma.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 468,
            "translated_text": "Lalle waɗanda suka kãfirta, anã kiran su, \"Haƙĩƙa, ƙin Allah (a gare ku) shĩ ne mafi girma daga ƙinku ga kanku a lõkacin da ake kiran ku zuwa ga ĩmãni, sai kunã ta kãfircẽwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 468,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ya Ubangijinmu! Kã matar da mu sau biyu, kuma Kã rãyar da mu sau biyu, sabõda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga fita?\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 468,
            "translated_text": "Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirãyi Allah Shi kaɗai, sai ku kãfirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi ĩmãni. To, hukuncin fa, na Allah Maɗaukaki, Mai girma ne."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 468,
            "translated_text": "Shĩ ne Wanda ke nũna muku ãyõyinSa, kuma Ya saukar da arziki daga sama sabõda ku, kuma bãbu mai yin tunãni fãce mai mayar da al'amari ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 468,
            "translated_text": "Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 468,
            "translated_text": "Mai ɗaukaka darajõji (dõmin mũminai), Mai Al'arshi, Yanã jẽfa rũhi *daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bãyinSa, dõmin ya yi gargaɗi kan rãnar gamuwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Rũhi a nan, ga fahimta ta, Allah ne Mafi sani, shĩ ne karfin rai da basĩrar fahimtar addĩni da aiki wajen rãyar da shi, wanda Allah Yake sakãwa ga mãlamin da Yake nufin jaddada addini da shi a kan kõwane karni kamar yadda Hadisi ya zo da shi, ya kõre jidãlin mãsu jidãli."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 468,
            "translated_text": "Rãnar da suke bayyanannu, bãbu wani abu daga gare su wanda yake iya bõyuwa ga Allah. \"Mulki ga wa ya ke a yau?\" Yana ga Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 469,
            "translated_text": "Yau anã sãka wa kõwane rai a game da abin da ya aikata, bãbu zãlunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisãbi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 469,
            "translated_text": "Kuma ka yi musu gargaɗi kan rãnar (Sã'a) makusanciya, a lõkacin da zukãta suke mãsu cika da bakin ciki, ga maƙõsansu. Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a (ga cẽtonsu)."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 469,
            "translated_text": "(Allah) Ya san yaudarar idãnu da abin da ƙirãza ke ɓõyẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 469,
            "translated_text": "Kuma Allah Shĩ ke yin hukunci da gaskiya, waɗannan da kuke kira, waninSa, bã su yin hukunci da kõme. Lalle Allah, Shĩ ne Mai ji, Mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 469,
            "translated_text": "Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba ga yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninsu ta zama? Sun kasance sũ ne mafi tsananin ƙarfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasã, sai Allah Ya kãmã su da laifuffukansu. Kuma bã su da wani mai tsarẽwa daga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 469,
            "translated_text": "Wancan sababinsa, dõmin sũ Manzanninsu sun kasance sunã zuwa gare su da hujjõji bayyanannu, sai suka kãfirta, sai Allah Ya kãmã su. Lalle Shĩ Mai ƙarfi ne, Mai tsananin azãba."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 469,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã a game da ãyõyinMu da wani dalĩli bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 469,
            "translated_text": "Zuwa ga Fir'auna da Hãmãna da Kãrũna, sai suka ce: \"Mai sihiri ne, maƙaryaci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 469,
            "translated_text": "Sa'an nan, a lõkacin da ya jẽ musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce: \"Ku kashe ɗiyan waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, kuma ku rãyar da mãtansu.\" Kuma mugun shirin kãfirai, bai zama ba fãce a cikin bata."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 470,
            "translated_text": "Kuma Fir'auna ya ce: \"Ku bar ni in kashe Mũsã, kuma shĩ, ya kirãyi Ubangijinsa. Lalle ne nĩ, inã tsõron ya musanya addininku, kõ kuwa ya bayyana ɓarna a cikin kasã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 470,
            "translated_text": "Kuma Mũsã ya ce: \"Lalle nĩ, nã nẽmi tsari da Ubangijĩna kuma Ubangijinku, daga dukan makangari, wanda bã ya ĩmani da rãnar Hisãbi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 470,
            "translated_text": "Kuma wani namiji mũmini daga dangin Fir'auna, yanã bõye ĩmãninsa, ya ce: \"Ashe, za ku kashe mutum dõmin ya ce Ubangijina Allah ne, alhãli kuwa haƙĩƙa ya zo muku da hujjõji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan yã kasance maƙaryaci ne, to, ƙaryarsa na kansa, kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, sãshen abin da yake yi muku wa'adi zai sãme ku. Lalle ne Allah bã Ya shiryar da wanda yake mai barna, mai yawan ƙarya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 470,
            "translated_text": "\"Yã kũ mutãnẽna! Kunã da mulki a yau, kuma kũ ne marinjãya a cikin kasã to wãne ne zai taimake mu daga azãbar Allah idan ta zo mana?\" Fir'auna ya ce: \"Bã ni nũnamuku kõme face abin da na gani, kuma ba ni shiryar da ku, sai ga hanyar shiryuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 470,
            "translated_text": "Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: \"Ya mutãnẽnã! Lallene, nĩ, inã yi muku tsõron kwatankwacin rãnar ƙungiyõyi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 470,
            "translated_text": "\"Kwatankwacin al'adar mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da waɗanda ke a bãyansu. Kuma Allah bã Ya nufin zãlunci ga bãyinSa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 470,
            "translated_text": "\"Kuma ya mutãnẽna! Lallenĩ, inã yi muku tsõron rãnar kiran jũna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 470,
            "translated_text": "\"A rãnar da zã ku jũya, kunã mãsu bãyar da bãya (gudãne) bã ku da wani mai tsaro daga Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 471,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Yusufu ya zo muku daga gabãni, da hujjõji bayyanannu, ba ku gushe ba kunã a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lõkacin da ya halaka kuka ce, 'Allah bã zai aiko wani Manzo ba, a bãyansa.' Kamar haka Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 471,
            "translated_text": "\"Waɗanda kejayayya a cikin ãyõyin Allah, bã da wani dalĩli da ya zo musu ba. Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi ĩmãni. Kamar haka Allah ke bicẽwar haske a kan zũciyar dukan makangari, mai tĩlastãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 471,
            "translated_text": "Kuma Fir'auna ye ce, \"Yã Hãmana! Ka gina mini bẽne, dammãnĩna zã ni isa ga ƙõfõfi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 471,
            "translated_text": "\"¡õfõfin sammai dõmin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautãwar Mũsã. Kuma lalle nĩ haƙĩƙa inã zaton sa maƙaryaci.\" Kuma haka dai aka ƙawãce wa Fir'auna mũnãnan aikinsakuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir'auna bai zama ba fãce yanã a cikin hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 471,
            "translated_text": "Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: \"Ya mutãnẽna! Ku bĩ ni, in shiryar da ku tafarkin shiryuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 471,
            "translated_text": "\"Kuma ya mutãnẽna! Wannan rãyuwa ta dũniya dan jin dãɗi ne kawai, kuma lalle Lãhira ita ce gidan tabbata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 471,
            "translated_text": "\"Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a sãka masa ba fãce da misãlinsa, kuma wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ mace alhãli kuwa shĩ mũmini ne, to, waɗannan sunã shiga Aljanna, anã ciyar da su a cikinta, bã da lissãfi ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 472,
            "translated_text": "\"Kuma ya mutãnẽna! Me ya sãme ni, inã kiran ku zuwa ga tsĩra, kuma kunã kira na zuwa ga wutã?\""
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 472,
            "translated_text": "\"Kuna kira na zuwa ga in kãfirta da Allah, kuma in yi shirki, game da Shi, da abin da bãbu wani ilmi game da shi gare ni, kuma ni inã kiran ku zuwa ga Mabuwãyi, Mai gãfara.\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 472,
            "translated_text": "\"Haƙƙan ne abin da kawai kuke kira na zuwa gare shi, bã ya da wani kira a cikin dũniya, kuma bã shi da shi a Lãhira kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah take, kuma lalle mabarnata sũ ne 'yan wutã.\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 472,
            "translated_text": "\"To zã ku ambaci abin da nake gaya muku, kuma inã fawwala al'amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai gani ne ga bãyinSa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 472,
            "translated_text": "Sai Allah Ya tsare shi daga mũnãnan abũbuwa da suka yi na mãkirci, kuma mummunar azãba ta wajaba ga mutãnen Fir'auna."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 472,
            "translated_text": "Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cẽwa, \"Ku shigar da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 472,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da suke husũma a cikin wutã, sai raunãna (mabiya) su ce wa waɗanda suka kangara (shugabanni), \"Lalle mũ, mun kasance mabiya gare ku, to, shin kũ mãsu wadãtar da mu ne daga barin wani rabo daga wutã?\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 472,
            "translated_text": "Waɗanda suka kangara suka ce: \"Lalle mũ duka munã a cikinta. Lalle ne, Allah Ya yi hukunci a tsakãnin bãyinSa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 472,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke a cikin wutã suka ce wa matsaran Jahannama, \"Ku rõki Ubangijinku Ya sauƙaƙa mana, a yini ɗaya, daga azãba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 473,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ashe, Manzanninku ba su jẽ muku da hujjõji bayyanannu ba?\" Suka ce: \"Na'am, sun jẽ!\" Suka ce: \"To, ku rõƙa.\" Kuma rõƙon kãfirai bai zamo ba fãce a cikin ɓata."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 473,
            "translated_text": "Lalle Mũ, hakĩka, Munã taimakon ManzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, a cikin rãyuwar dũniya da rãnar da shaidu ke tsayãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 473,
            "translated_text": "Rãnar da uzurin azzãlumai bã ya amfãninsu, kuma sunã da la'ana, kuma sunã da mũnin gida."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 473,
            "translated_text": "Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã shiriya, kuma Mun gãdar da Banĩ Isrã'ĩla Littãfi."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 473,
            "translated_text": "Shiryarwa da tunãwa ga ma'abũta hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 473,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka yi haƙuri, lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Kuma ka nẽmi gãfara ga zunubinka, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, maraice da kuma wãyẽwar sãfiya."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 473,
            "translated_text": "Lalle waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, bã game da wani dalĩli wanda ya jẽ musu ba, bãbu kõme a cikin kirãzansu, fãce girman kai, ba su zama mãsu isa ga gũrinsu ba, sabõda haka ka nẽmi tsari daga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 473,
            "translated_text": "Lalle halittar sammai da ƙasã, ita ce mafi girma daga halittar mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 473,
            "translated_text": "Kuma makãho da mai gani bã su daidaita kuma waɗanda suka yi ĩmãni suka, aikata ayyukan ƙwarai da mai mũnanãwa bã su daidaita. Kaɗan ƙwarai, kuke yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 474,
            "translated_text": "Lalle Sa'a, haƙĩƙa mai zuwa ce, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 474,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinku ya ce: \"Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 474,
            "translated_text": "Allah ne Wanda Ya sanya muku dare dõmin ku natsu a cikinsa, da rãna mai gãnarwa. Lalle Allah, haƙĩƙa, Ma'abũcin falala ne a kan mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 474,
            "translated_text": "Wancan shine Allah Ubangijinku, Mahaliccin dukan kõme, bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?"
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 474,
            "translated_text": "Kamar haka ake karkatar da waɗanda suka kasance sunã jãyayya game da ãyõyin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 474,
            "translated_text": "Allah ne Ya sanya muku kasã tabbatacciya, da sama ginanniya, kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku,, kuma Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 474,
            "translated_text": "Shĩ ne Mai rai, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Sabõda haka ku kira Shi, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi. Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 474,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle nĩ, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a lõkacin da hujjõji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in sallama ga Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "Shĩ ne Wanda Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga maniyyi, sa'an nan daga sãren jini, sa'an nan Ya fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan dõmin ku isa ga cikar ƙarfinku sa'an nan dõmin ku kasance tsõfaffi, kuma daga cikinku, akwai wanda ake karɓar ransa a gabãnin haka, kuma dõmin ku isa ga ajali ambatacce, kuma dammãninku ko zã ku hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "Shi ne Wanda ke rayarwa kuma Yana kashewa. To, idan Ya hukunta wani al'amari, to, Yana cewa kawai gare shi, ka kasance sai yana kasancewa (kamar yadda ake bukatar sa.)"
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "Ashe, ba ka gani ba ga waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, yadda ake karkatar da su?"
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "Waɗanda suka ƙaryata, game da Littãfin, kuma da abin da Muka aika Manzanninmu da shi. To, za su sani."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "A lõkacin da ƙuƙumma suke a cikin wuyõyinsu, da sarƙõƙi anã jan su."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "A cikin ruwan zãfi, sa'an nan a cikin wutã anã babbaka su."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "Sa'an nan a ce musu, \"Ina abin da kuka kasance kunã shirki da shi\""
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "\"Wanin Allah?\" Suka ce: \"Sun ɓace mana. Ã'a, ba mu kasance munã kiran kõme ba a gabani.\"Kamar wancan ne Allah Yake ɓatar da kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "Wancan dõmin abin da kuka kasance ne kunã farin ciki da shi, a cikin ƙasã, bã da hakki ba, kuma da abin da kuka kasance kunã yi na nishãɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "Ku shiga kofõfin Jahannama kunã madawwama a cikinta. To, mazaunin mãsu girman kai yã mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 475,
            "translated_text": "Sabõda haka ka yi haƙuri. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. To, kõ dai lalle Mu nũna maka sãshen abin da Muka yi musu wa'adi da shi kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu ake mayar da su."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 476,
            "translated_text": "Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta lãbãrinsa ba a gare ka. Bã ya yiwuwa ga wani Manzo ya jẽ da wata ãyar mu'ujiza fãce da iznin Allah. Sa'an nan idan umurnin Allah ya jẽ, sai a yi hukunci da gaskiya, mãsu ɓãtãwa sun yi hasara a can."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 476,
            "translated_text": "Allah ne Wanda Ya sanya muku dabbõbi dõmin ku hau daga gare su, kuma daga gare su kuke ci."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 476,
            "translated_text": "Kuma kunã da abũbuwan amfãni a cikinsu, kuma dõmin ku isar da wata buƙãta, a cikin ƙirãzanku a kansu kuma a kansu da a kan jirãge ake, ɗaukar ku."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 476,
            "translated_text": "Kuma Ya nũna muku ayõyinSa. To, wane ãyõyin Allah kuke musu?"
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 476,
            "translated_text": "Ashe fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasã ba, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafi yawa daga gare su. Kuma sun fi tsananin ƙarfi, da (yawan) gurãbun sanã'õ'i a cikin ƙasã. To, abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 476,
            "translated_text": "A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi* kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi ya wajaba a kansu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ilmin dũniya na sanã'õ'i ya zõ ne daga Annabãwa kamar na ibãdu. Nũhu ya fãra sassaƙar jirgin ruwa da wahayi daga Allah, Zulƙarnaini ya fãra haɗa baƙin ƙarfe da gaci dõmin hana tsãtsa, Yũsufu ya fãra barin hatsi a cikin sõshiya dõmin hana ƙwãri. Dãwũda ya fãra sanã'ar sulke. Ãdam ya fara rubũtu, Idirĩsu ya fara yin alƙalami. ĩsã ya fãra warkar da majinyata, Alƙur' ãni ya nũna anã iya tãshi sama da jirgin sama. Shu'aibu shi ya nũna kasuwanci, da sauransu."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 476,
            "translated_text": "Sa'an nan a lõkacin da suka ga azãbarMu, suka ce: \"Mun yi ĩmãni da Allah, Shi kaɗai, kuma mun kãfirta da abin da muka kasance munã shirki da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 40,
            "page_number": 476,
            "translated_text": "To ĩmaninsu bai kasance yanã amfaninsu ba a lõkacin da suka ga azãbarMu. Hanyar Allah wadda ta gabãta a cikin bãyinSa. Kuma kãfirai sun yi hasãra a can."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Ḥ. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Saukarwa (da Alƙur' ãni) dãga Mai rahama ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Littãfi ne, an bayyana ãyõyinsa daki-daki, yanã abin karantãwa na Lãrabci, dõmin mutãnen dake sani"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Yanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Sai mafi yawansu suka bijire. Sabõda haka sũ, bã su saurãrãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Zukatanmu nã a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da tsakaninka akwai wani shãmaki. sahõda haka ka yi aiki, lalle mũ mãsu aiki ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Ka ce: \"Nĩ mutum kawai ne kamarku, ãnã yin wahayi zuwa gare ni cẽwa abin bautãwarku, abin bautãwa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nẽmi gafararSa.\" Kuma bone ya tabbata ga mãsu yin shirki."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Waɗanda bã su bãyar da zakka, kuma sũ a game da Lãhira su kafirai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Lalle wɗdanda suka yi ĩmãni, Kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bai yankẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ashe lalle kũ, haƙĩƙa, kunã kafurta a game da wanda Ya halitta kasã a cikin kwanuka biyu, kuma kunã sanya Masa kĩshiyõyi? Wancan fa, shĩ ne Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Kuma Ya sanya, a cikinta, dũwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a cikinta, kuma Ya ƙaddara abũbuwan cinta a cikinta a cikin kwanuka huɗu mãsu daidaita, dõmin matambaya."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 477,
            "translated_text": "Sa'an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhãli kuwa ita (a lõkacin) hayãƙi ce, sai Ya ce mata, ita da ƙasã \"Ku zo, bisa ga yarda kõ a kan tĩlas.\" Suka ce: \"Mun zo, munã mãsu ɗã'ã. \""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 478,
            "translated_text": "Sai Ya hukunta su sammai bakwai a cikin kwãnuka biyu. Kuma Ya yi wahayi, a cikin kõwace sama da al'amarinta, kuma Muka kãwata sama ta kusa da fitilu kuma don tsari. Wancan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 478,
            "translated_text": "To, idan sun bijire sai ka ce: \"Nã yi muku gargaɗi ga wata tsãwa kamar irin tsãwar Ãdãwa da samũdãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 478,
            "translated_text": "A lõkacin da Manzanninsu suka je musu daga gaba gare su kuma daga bãyansu, \"Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah.\" suka ce: \"Dã UbangiJinmu Yã so, lalle dã Ya saukar da malã' iku, sabõda haka lalle mũ, mãsu kafirta ne a game da abin da aka aiko ku da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 478,
            "translated_text": "To, amma Ãdãwa, sai suka yi girman kai a cikin kasã, bã da wani hakki ba, suka ce: \"Wãne ne mafi tsananin ƙarfi daga gare mu?\" Ashe, kuma ba su gani ba cẽwa Allah, wanda Ya halitta su Shĩne Mafi ƙarfi daga gare su, kuma sun kasance a game da ãyõyinMu suna yin musu?"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 478,
            "translated_text": "Sai Muka aika, a kansu, da iska mai tsananin sauti da sanyi, a cikin kwãnuka na shu'umci, dõmin Mu ɗanɗana musu azãbar wulãƙanci, a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi wulãƙantarwa, kuma sũ bã zã a taimake su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 478,
            "translated_text": "Kuma amma Samũdãwa, sai Muka shiryar da su, sai suka fi son makanta a kan shiriya, dõmin haka tsawar azãbar wulãkanci, ta kamã su sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa (dõmin nẽman wata fã'ida)."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 478,
            "translated_text": "Kuma Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 478,
            "translated_text": "Kuma rãnar da ake tãra maƙiyan Allah zuwa wutã, to, sũ anã kakkange su."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 478,
            "translated_text": "Har idan sun jẽ mata, sai jinsu da ganinsu da fãtunsu, su yi shaida a kansu a game da abin da suka kasance sunã aikatawa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 479,
            "translated_text": "Kuma suka ce wa fãtunsu, \"Don me kuka yi shaida a kanmu?\" Suka ce: \"Allah, Wanda ke sanya kõwane abu ya yi furuci, Shĩ ne Ya sanya mu mu yi furuci, kuma Shĩ ne Ya halitta ku can da farko, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 479,
            "translated_text": "\"Ba ku kasance kunã sani ba a ɓõye, cẽwa jinku zai yi shaida a kanku kuma ganinku zai yi, kuma fãtunku za su yi. Kuma amma kun yi zaton cẽwã Allah bai san abũbuwa mãsu yawa daga abin da kuke aikatãwa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 479,
            "translated_text": "\"Kuma wancan zaton nãku wanda kuka yi zaton shi, game da Ubangijinku, ya halakar da ku, sai kuka wãyi gari a cikin mãsu hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 479,
            "translated_text": "Sabõda haka idan sun yi hakuri, to, wutar, ita ce mazauni a gare su, kuma idan sun nẽmi yarda, to, ba su zama daga waɗanda ake yardwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 479,
            "translated_text": "Kuma Muka sallaɗar da mabiya* a gare su, sai suka ƙawãta musu abin da ke a gabansu da abin da ke a bãyansu. Kuma kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin wasu al'ummõmi da suka shũɗe a gabãninsu daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mabiya, sũ ne aljannun kõ Shaiɗãnun da ke tãre da mutum."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 479,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kafirta suka cc, \"Kada ku saurãra ga wannan Alkur' ãni, kuma ku yi ta yin kuwwa a ckin (lõkacin karãtun) sa, ɗammãninku zã ku rinjaya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 479,
            "translated_text": "Sabõda haka, lalle zã Mu ɗanɗana wa waɗanda suka kafirta wata azãba mai tsanani, kuma lalle zã Mu sãka musu da mafi mũnin abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 479,
            "translated_text": "Wancan shĩ ne sakamakon makiyan Allah, watau wuta. Sunã a gidan dawwama a cikinta, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã yin musu game da ãyõyinMu."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 479,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: \"Yã Ubangijinmu! Ka nũnã mana wadannan biyun da suka batar da mu daga aljannu da mutãne, mu sanya su a karkashin, ƙafãfunmu, dõmin su kasance daga ƙaskantattu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 480,
            "translated_text": "Lalle waɗannan da suka ce: \"Ubangjinmu, shĩ ne Allah,\" sa'an nan suka daidaitu, malã'iku na sassauka a kansu (a lõkacin saukar ajalinsu sunã ce musu) \"Kada ku ji tsõro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushãra da Aljanna, wadda kun kasance anã yi muku wa'adi da ita.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 480,
            "translated_text": "\"Mũ ne majibintanku a cikin rãyuwar dũniya da kuma a cikin Lãhira, kuma a cikinta kunã da abin da rãyukanku ke sha'awa, kuma kunã da abin da kuke kira (akawo muku) a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 480,
            "translated_text": "\"A kan liyãfa daga Mai gafara, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 480,
            "translated_text": "Kuma wãne ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na ƙwarai kuma ya ce: \"Lalle nĩinã daga mãsu sallamãwar al'amari zuwa ga Allah?\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 480,
            "translated_text": "Kuma kyautatãwa bã ta daidaita kuma haka mũnanãwa. Ka tunkuɗe cũta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai ƙiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar dai shi majibinci ne, masoyi."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 480,
            "translated_text": "Kuma bã za a cũsa wa kõwa wannan hãli ba fãce waɗanda suka yi haƙuri, kuma bã zã a cũsa shi ba fãce ga mai rabo mai gima."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 480,
            "translated_text": "Kuma idan wata fizga ta fizge ka daga Shaiɗan, to ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 480,
            "translated_text": "Kuma akwai daga ãyõyinSa, dare da yini, da rãnã da watã. Kada ku yi sujada ga rãnã, kuma kada ku yi ga watã. Kuma ku yi sujada ga Allah wanda Ya halitta su, idan kun kasance Shĩ ne kuke bauta wa."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 480,
            "translated_text": "To, idan sun yi girman kai, to, waɗanda ke a wurin Ubangijinka, sunã tasbĩhi a gare Shi, a dare da rana, alhãli kuwa sũ, bã su ƙõsãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 481,
            "translated_text": "Kuma akwai daga ãyõyinSa cẽwa lalle kai kanã ganin ƙasã ƙẽƙasasshiya, to, idan Mun saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura. Lalle wannan da Ya rãya ta, haƙĩƙa, Mai rãyar da matattu ne. Lalle Shĩ Mai ĩkon yi ne a kan kõwane abu."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 481,
            "translated_text": "Lalle waɗannan da ke karkacẽwa a cikin ãyõyinMu, bã su fakuwa a gare Mu. Ashe fa, wanda ake jẽfãwa a cikin Wutã ne mafĩfĩci kõ kuwa wanda zai je amintacce a Rãnar ¡iyãma? Ku aikata abin da kuke so! Lalle Shĩ Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 481,
            "translated_text": "Waɗannan da suka kãfirta game da Alkur'ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 481,
            "translated_text": "¥arna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 481,
            "translated_text": "Bã zã a fada maka ba fãce abin da aka riga aka faɗa ga Manzannin da suke a gabãninka. Lalle Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne, kuma Ma'abũcin azãba mai raɗaɗi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 481,
            "translated_text": "Kuma da Mun sanya shi abin karãtu na ajamanci, lalle dã sun ce, \"Don me ba a bayyana ãyõyinsa ba? Ashe, zai yiwu a sãmi littãfi ba'ajame da Manzo Balãrabe?\" Ka ce: \"Shi, shiriya ne da warkewa ga waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma wadanda ba su yi ĩmãni ba akwai wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma shi wata makanta ne a kansu. Waɗannan anã kiran su daga wuri mai nĩsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 481,
            "translated_text": "Kuma lalle Mun bai wa Mũsã Littãfi, sai aka yi ɗãɓãni a cikinsa, Kuma ba dõmin wata kalma da tã gabata ba daga Ubangijinka, lalle dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle sũ, haƙĩƙa sunã a cikin shakka daga, gare shi, mai sanya kõkanto."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 481,
            "translated_text": "Wanda ya aikata aiki na ƙwarai to sabõda kansa ne, kuma wanda ya mũnanã, to, yanã akansa. Kuma Ubangiwinka, bã Mai zãlunci ga bãyinSa ne ba."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 482,
            "translated_text": "Zuwa gare Shi ake mayar da sanin Sa'a. Kuma waɗansu 'yã'yan itãce bã su fita daga kwasfõfinsu, kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma a rãnar da Yake kiran su (Ya ce): \"Inã abõkan tãrayyaTa?\" Sai su ce, \"Mun sanar da Kai bãbu mai bãyar da shaida da haka nan daga gare mu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 482,
            "translated_text": "Kuma abin da suka kasance sunã kira a gabãnin haka ya ɓace musu, kuma suka yi zaton cẽwa bã su da wata mafakã."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 482,
            "translated_text": "Mutum bã ya kõsãwa daga addu 'ar nẽman alhẽri kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya zama mai yanke kauna, Mai nũna kãsãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 482,
            "translated_text": "Kuma lalle idan Mun ɗanɗana masa wata rahama daga gareMu, daga bãyan wata cũta ta shãfe shi, lalle zai ce, \"Wannan (ni'ima) tãwa ce kuma bã ni zaton Sã'a mai tsayuwa ce, kuma lalle idan aka mayar da ni zuwa ga Ubangijĩna, haƙĩƙa, inã da makõma mafi kyau, a wurinSa.\" To, lalle zã Mu bã da lãbãri ga waɗanda suka kãfirta game da abin da suka aikata, kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, Mai kauri."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 482,
            "translated_text": "Kuma idan Muka yi ni'ima ga mutum, sai ya bijire, kuma ya nĩsantar da gẽfensa, kuma idan sharri ya sãme shi, sai ya zama ma'abũcin addu'a mai fãɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 482,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ashe, kun gani! Idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga Allah ne, sa'an nan kun kãfirta a game da Shi, wãne ne mafi ɓata daga wanda yake yanã a cikin sãɓani manisanci (daga gaskiya)?\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 482,
            "translated_text": "Zã Mu nũna musu ãyõyinMu a cikin sãsanni da kuma cikin rãyukansu, har ya bayyana a gare su cẽwã lalle (Alƙur'ãni), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cẽwa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 41,
            "page_number": 482,
            "translated_text": "To lalle sũ, sunã a cikin shakka daga gamuwa da Ubangijinsu. To, lalle Shĩ, Mai kẽwayẽwane ga dukan kõme ne."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "Ḥ. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "Ĩ. Ṣ̃."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "Kamar wancãn *(asĩrin) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabãninka.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Asirin haɗa jama'a bã zã su rarrabu ba. Watau su riƙi Allah Shi kaɗai ne Ubangiji Mai yin umurni ko hani, kuma su riƙi cewa Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gareshi, shĩ ne cikamakin Annabãwa, bãyansa bã a bai wa kõwa kõme fãce fahimta ga abin da ya zo da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "(Allah) Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "Sammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã'iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda bã Shĩ ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, bã wakili ne a kansu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa (Alƙur'ãni) na Lãrabci zuwa gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa'ĩr."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "Kuma dã Allah Ya so, da Ya haɗã su al'umma guda, kuma Amma Yanã shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhãli kuwa azzãluMai bã su da, wani majiɓinci, kuma bã su da wani mataimaki."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "Kõ kuma sun riƙi waninSa majiɓinta? To Allah Shĩ ne Majiɓinci, kuma Shĩ ne ke rãyar da matattu alhãli kuwa Shĩ, Maiĩkon yi ne a kan dukan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 483,
            "translated_text": "Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 484,
            "translated_text": "(Shĩ ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 484,
            "translated_text": "Shĩ ne da mabuɗan sammai da ƙasa Yanã shimfiɗa arziki ga wanda ya so kuma Yanã hukuntãwa. Lalle ne, Shĩ Masani ne ga dukan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 484,
            "translated_text": "Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. *Abin da kuke kira zuwa gare shi,** ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyarSa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ku bi umurnin Allah kamar yadda Ya aza muku hukunce-hukuncenSa, kada ku karkace da bin umurnin waɗansu na dabam waɗanda bã Allah ba, kõ kuma kada ku bi son zũciyarku. Bin umurnin wani zai sanya ku sãɓãwa jũnanku, ku rarrabu, ku rasa ƙarfi a kan maƙiyanku. Wanda ya bi umurnin waɗansu, waɗanda bã Allah ba, to ya yi shirka da Allah ke nan kuma haɗuwar mãsu bin umurnin waɗansu waɗanda bã Allah ba, to, tanã da wuya. Wannan ãya ta hana bin ɗarĩƙõƙin ƙungiyõyin sũfãye duka, dõmin bin su, bin umurnin waɗansu ne waɗanda bã Allah ba kuma yanã rarraba Musulmi, su zama ƙungiya-ƙungiya, da sãɓãni mai nĩsa. Bã zã a ce ba, \"Ã'aha! Wannan ãya ta sauka ga Yahũdu da Nasãra kawai\" dõmin ãyõyi biyu l4 da l5, mãsu bin wannan, sun gama harda Musulmi, dõmin umurni ga Annabi, umurni ne sabõda al'ummarsa. Kuma sãɓãnin mãsu ɗariƙõƙi sãɓãni ne a kan asali watau aƙida, bã sãɓãnine a kan rassuna na furũ'a ba. Sabõda haka bãbu ƙiyayya a tsakãnin mabiya mazhabõbi, dõmin sãɓãninsu, na fahimta ne kawai. Sãɓãni ga reshe, rahama ce, amma sãɓãni ga asali azãba ce. ** Watau haɗuwar jama'a ga bin addini guda, bã da sãɓawa ba ga asalinsa. Wanda ya ce: An saukar wa wani mutum, baicin Muhammadu, da wani abu daga Allah, to, shĩ ya sãɓãwa asali. Sãɓãwa ga asali kãfirci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 484,
            "translated_text": "Kuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu kuma bã dõmin wata kalma* tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kalmar da ta gabãta, ita ce \"Allah bã zai halaka mutane ba sabõda zunubi sai ajalinsu ya zo.\" Zãlunci da ke hana su haɗuwa a bãyan sanin gaskiya, shi ne hassadar jũna, sa kwaɗayi da son shugabanci a cikin mu'amala."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 484,
            "translated_text": "Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, \"Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 485,
            "translated_text": "Kuma waɗannan da ke jãyayya a cikin al'amarin Allah daga bãyan an karɓa masa, hujjarsu ɓãtãcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sunã da wata azãba mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 485,
            "translated_text": "Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi da gaskiya, da sikeli. Kuma me ya sanar da kai (cẽwa anã) tsammãnin Sa'ar kusa take?"
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 485,
            "translated_text": "Waɗanda ba su yi ĩmãnida ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautõwarta. Alhãli kuwa waɗanda suka yi ĩmãni, mãsu tsõro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙĩƙa, sunã a cikin ɓata Mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 485,
            "translated_text": "Allah Mai tausasãwa ne ga bãyinsa. Yanã azurta wanda yake so, alhãli kuma Shĩ ne Maiƙarfi, Mabuwãyi."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 485,
            "translated_text": "Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 485,
            "translated_text": "Kõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma bã dõmin kalmar hukunci ba, da lalle, an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 485,
            "translated_text": "Kanã ganin azzãlumai sunã mãsu tsõro daga abin da suka sanã'anta alhãli kuwa shi abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai sunã a cikin fadamun Aljanna sunã da abin da suke so a wurin Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 486,
            "translated_text": "Wancan shĩ ne Allah ke bãyar da bushãra da shi ga bãyinSa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: \"Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, fãce dai sõyayya ta cikin zumunta.\" Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 486,
            "translated_text": "Kõ zã su ce: \"Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne?\" To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a kan zũciyarka, kuma Allah Yana shãfe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da kalmõminSa. Lalle ne Shĩ Masani ne ga abin da ke cikin zukata."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 486,
            "translated_text": "Kuma Shi ne ke karɓar tũba daga bãyinSa, kuma Yanã Yafe ƙananan laifuffuka, alhãli kuwa Yanã sanin abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 486,
            "translated_text": "Kuma Yanã karɓa wa waɗannan da suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma Yanã ƙãra musu (sakamako) daga falalarSa. Kuma kãfirai sunã da wata azãba mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 486,
            "translated_text": "Kuma dã Allah Ya shimfiɗa arziki ga bãyinSa, dã sun yi zãluncin rarraba jama'a a cikin ƙasa, kuma amma Yanã sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, game da bãyinSa, Mai labartawa ne, Mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 486,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne ke sassaukar da girgije (ruwa) a bãyan sun yanke ƙauna kuma Yana wãtsa rahamarSa, alhãli kuwa Shĩ ne Majiɓinci, Mai gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 486,
            "translated_text": "Kuma akwai daga ãyõyinSa, halittar sammai da ƙasa da abin da Ya wãtsa a cikinsu na dabba alhãli kuwa Shĩ Mai ĩko ne ga tãra su, a lõkacin da Yake so."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 486,
            "translated_text": "Kuma abin da ya sãme ku na wata masifa, to, game da abin da hannãyenku suka sana' anta ne kuma (Alah) Yanã Yafẽwar (waɗansu laifuffuka) mãsu yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 486,
            "translated_text": "Kuma ba ku zama mãsu buwãya ba a cikin ƙasa kuma bã ku da wani majiɓinci, wanin Allah, kuma bã ku da wani mataimaki."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Kuma akwai daga ãyõyinsa, jirãge mãsu gudãna a cikin tẽku kamar duwãtsu."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirãgen su yini sunã mãsu kawaici a kan bãyan tẽkun, Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, Mai gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Kõ Ya halakã su (sũ jirãgen) sabõda abin da mãsu su suka sanã'anta, alhãli kuwa Yanã yãfe (laifuffuka) mãsu yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Kuma dõmin waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyinMu su sani (cẽwa) bã su da wata mafaka."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci, kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Kuma waɗanda *ke nisantar manyan zunubbai da ayyukan alfãsha, kuma idan sun yi fushi, sũ, sunã gãfartawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bayãnin siffõfin mũminai, waɗanda suke tsare su, Yana lãmunce zama haɗe, da gamuwar Musulmi, sũ ne siffõfi shida, nisantar manyan zunubbai da zina, da gãfarta fushi, da tsayar da salla, da shãwara ga al'amuran tsakãninsu, da ciyar da dũkiya da ta wajabci mutum ya ciyar da ita a cikin alheri ga inda Allah Ya ce a ciyar da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shãwara ne a tsakãninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sunã ciyarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Da waɗanda* idan zãlunci ya sãme su, sunã nẽman taimako (su rãma).<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wajen rãma zãlunci kõ yinsa, mutãne sun kasu kashi huɗu. Mãsu rãmãwa gwargwadon zãlunci, bã su da laifi; da mãsu rãmãwa da abin da ya fi laifin da aka yi musu, to, sunã da laifi kamar mãsu fãra zãlunci, da mãsu gãfartãwa, waɗannan sũ ne Allah ke so."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Kuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yãfe kuma ya kyautata, to lãdarsa nã ga Allah. Lalle ne, Shĩ (Allah) bã Ya son azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Kuma Lalle ne, wanda ya nẽmi taimakon rãmãwa a bãyan an zãlunce shi, to waɗannan bãbu wata hanyar zargi a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "lnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zãluntar mutãne kuma sunã ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bã tare da haƙƙi ba. Waɗannan sunã da azãba Mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Kuma Lalle ne, wanda ya yi haƙuri kuma ya gãfarta (wa wanda ya zãlunce shi), to shĩ wancan aiki haƙĩƙa, yanã daga manyan al'amura (da Allah ke so)."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 487,
            "translated_text": "Kuma wanda* (Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani majiɓinci bãyanSa, kuma zã ka ga azzãlumai, a lõkacin da suka ga azãba, sunã cẽwa, \"Shin, akwai hanya zuwa ga kõmãwa?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bayãnin mai zãlunci da sakamakonsa a Rãnar Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 488,
            "translated_text": "Kuma kanã ganin su anã gitta su a kanta, sunã ƙasƙantattu sabõda wulãkanci, sunã hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sai su ce, \"Lalle ne, mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu da iyãlansu a Rãnar ¡iyãma.\" To, lalle ne, azzãlumai sunã a cikin wata azãba zaunanniya."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 488,
            "translated_text": "Kuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu, baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani gõdabe na tsĩra."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 488,
            "translated_text": "Ku karɓã wa Ubangijinku tun gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare shi daga Allah, bã ku da wata mafaka a rãnar nan, kuma bã ku iya yin wani musu."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 488,
            "translated_text": "To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kanã mai tsaro a kansu ba, bãbu abin da ke a kanka fãce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, to, lalle ne mutum mai tsananin kãfirci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 488,
            "translated_text": "Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yanã halitta abin da Yake so. Yanã bãyar da 'ya'ya mãtã ga wanda yake so, kuma Yanã bãyar da ɗiya maza ga wanda Yake so."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 488,
            "translated_text": "Kõ kuma Ya haɗa su maza da mãtã, kuma Yanã sanya wanda Ya so bakarãre.* Lalle shi, Mai ilmi ne, Mai ĩkon yi.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Bakarãrre, shi ne wanda bã ya haihuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 488,
            "translated_text": "Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana* fãce da wahayi, kõ daga bãYan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Annabãwa a lõkacin da Allah Ya yi musu magana ba su gan shi ba, sai dai sun ji maganarsa kamar yadda Musã ya ji, kõ kuma da wãsiɗar malã'ika kamar sauran Annabãwa, kõ kuwa da ilhama watau ya san hukunci ba da magana kõ wani wãsiɗar malã'ika ba. Ilhãmar Annabãwa da mafarkinsu gaskiya ne. Ilhãma da mafarkin sauran mutãne bã ya zama hujja sai idan yã dãce da shari'a, sai a yi aiki da shi a kan shari'a bã a kan mafarkin ko ilhãmar ba."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni, kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ãni) wani haske ne, Munã shiryar da wanda Muke so daga cikin bãyĩnMu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 42,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Hanyar Allah wanda ke da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. To, zuwa ga Allah kawai al'amura ke kõmãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Ḥ. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Ina rantsuwa da Littãfi Mabayyani."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Kuma lalle, shĩ, a cikin uwar littãfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Shin, zã Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dõmin kun kasance mutane mãsu ɓarna?"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Alhãli kuwa sau nawa Muka *aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko!<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tun da ba Mu bar mutãnen farko mãsu ɓarna ba, sai da Muka aika musu Manzanni, kuma kõwace ƙungiya daga cikin waɗanda aka aikawa wani Manzo sai da ta yi izgili game da Manzonsu, har abin ya kai ga halakar shũgabanninsu. To, haka mutãnenka, bã zã Mu bar su ba, sabõda ɓarnarsu, sai Mun aike ka zuwa gare su, su yi izgili game da kai, har a halaka shũgabanninsu, sa'an nan sauransu, su bi abin da aka umurce su da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Kuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Sai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, \"Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?\" Lalle zã su ce, \"Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 489,
            "translated_text": "Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.'"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari)."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, \"Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "\"Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu* jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ku yi dalĩli da hõrewar abin hawa gare ku zuwa ga tabbatar tãshinku dõmin hisãbin Ƙiyãma, dõmin ku bi umurninsa a dũniya, kuma ku bar al'adunku."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Kuma suka sanya *Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * suka ce malã'iku 'ya'ya mãtane na Allah, sunã bauta musu ne dõmin su kusantar da su zuwa ga Allah, watau dõmin su cece su daga azãba. Sun yi wannan ƙarya ne dõmin su tabbatar da al'ãdarsu ta surkulle. Sabõda haka suka yi wa Allah ƙarya suka naƙasa shi da haka, kuma suka naƙasa malã'iku mãsu daraja a wurin Allah kuma suka kãfirce wa ni'imar da Allah Ya yi musu wajen aiko musu Manzo mai shiryar da su. Sa'an suka kafa hujja da ƙarya dõmin su danne gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza?"
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Ashe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba.\" Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Kõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe?"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 490,
            "translated_text": "Ã'a, sun ce dai, \"Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini (na al'ãda) kuma lalle mũ, a kan gurãbunsu muke mãsu nẽman shiryuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, \"Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbunsu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "(Sai mai gargaɗin) ya ce: \"Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?\" Suka ce, \"Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "Sabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "Kuma (ka ambaci) lõkacin da Ibrãhĩm ya ce wa ubansada mutãnensa, \"Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "\"Fãce wannan *da Ya ƙãga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bã ni bauta wa gumãka, amma inã bautawa Allah wanda Ya ƙãgi halittata."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "Kuma (Ibrãhĩm) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammãninsu su kõmo daga ɓata."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "Ã'a, Na jiyar da waɗannan mutãne dãɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: \"Wannan sihiri ne kuma mũ mãsu kãfirta da shi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun* nan biyu ba?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sunã nufin Makka da tã'ifa, kuma sunã nufi a saukar da Alƙur'ãni ga walĩdu ɗan Mugĩra na Makka kõ ga Urwatu ɗan Mas'ũdi As saƙafi a Ta'ifa. Watau sunã sũkar Muhammadu dõmin bã shi da dũkiya. A gare su mai dũkiya shĩ ne babban mutum, wanda ya cancanta Allah Ya aiko shi ga mutãne."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci*), ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Tun da ba Mu bar rabon abincin rãyuwarsu ta dũniya a hannunsu ba, to, ta yãya ne zã Mu bar babban abu kamar Annabci da shiryar da mutãne ga hannãyensu? Wãtau bã zai yiwu Mu yi ba sai yadda Muke so kawai, kõ su bi, kõ su kãfirta, duka daidai ne a gare Mu."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 491,
            "translated_text": "Kuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Kuma a gidãjensu, Mu sanya) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Da zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Kuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Har a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) \"Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum!\""
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Kuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Shin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna?"
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "To, kõ dai Mu tafi *da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mu tafi da kai, watau Mu karɓi ranka, ka mutu, to, dã Mun yi musu azãba ke nan, dõmin sun rasa mai shiryar da su."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Kõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciyl."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, \"Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: \"Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 492,
            "translated_text": "To, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyinMu, sai gã su sunã yi musu dãriya."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "To, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: \"Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "\"Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar?"
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "\"To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe?\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Sai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Sabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Sai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?\" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli.* Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wãtau da aka ce gumãka damãsu bauta musu duka abincin wutar Jahannama ne kamar yadda yake a cikin sura ta 21 ãyã ta 98 da 99, sai suka ce sun yarda gumakansu su zama tãre da ɗan Maryama."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Shi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 493,
            "translated_text": "Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Dã Mun so dã Mun sanya ɗiyansu su zama malã'iku, su fi Ĩsa ɗan Maryama zama abin mãmãki ga halitta, sa'an nan su maye muku a cikin ƙasã maimakon ɗiya masu siffõfi irin na jikunkunanku. Zai fi zama abin mãmãki mutum yahaifi malã'ika bisa mace ta haifi ɗã bã da wani namiji yã kusance ta ba."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Kuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabõda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Kuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanãwar ƙiyayya."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: \"Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a.\""
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "\"Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Sai ƙungiyõyi *suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi!<br \/>\n____________________<br \/>\n * Nasãra suka kasu a cikin ƙungiyõyi a bayan Ĩsã. Ya'akubiyya, mãsu cewa Ĩsã ɗan Allah ne, da Malakãniyya, mãsu cewa Ĩsa ɗayan uku ne. Waɗansu kuma suka ce bãwan Allah ne watau su ne Musulminsu, kuma waɗansu daga Musulmin suka kãfirta a bãyan zakuwar, Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sabõda sun ƙi yarda da Annabcinsa. Yahũdu suka ce: \"Ĩsã bã Annabi ba ne dan zina ne.\" Allah Ya la'ani kãfirai dukansu."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Shin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne)."
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Ya bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Waɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyinMu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah)."
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Ku shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne."
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 494,
            "translated_text": "Kunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Lalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Bã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ, a cikinta, mãsu kãsa magana ne."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Kuma suka yi kira, \"Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana* \" (Mãliku) ya ce: \"Lalle kũ mazauna ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Watau sunã neman su mutu su huta da ɗaukar aZãba."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Kõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Ka ce: \"Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan).\""
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurinSa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane* (da haka).<br \/>\n____________________<br \/>\n * Su waɗanda suka yi shaida da gaskiya sun san bãbu mai mallakar ceto ga wani fãce Allah. Sabõda haka Allah nã yi musu izni su ceci wanda Yake son su cece shi, ba wanda su suke so ba. Ma'anar iznin da ceto ga bãyin Allah sãlihai ita ce dõmin Allah Ya bayyana darajar mai ceton ne kawai, bã don yanã da wani hakki ba, ga Allah. Allah Ya tsarkaka daga wata halittarSa ta sãmi wani hakki a kanSa. Kõwa bãwanSa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Kuma lalle idan ka tambaye su: \"Wãne ne ya halitta su?\" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su?"
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "Kuma da (ilmin) maganarSa (Annabi) \"Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 43,
            "page_number": 495,
            "translated_text": "To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, \"salãmã.\" Sa'an nan kuma zã su sani."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Ḥ. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka)."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?"
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: \"Wanda ake gayãwa* ne, mahaukaci.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sunã nufin waɗansu mutãne ne ke gaya wa Annabi Alƙur'ãni, kõ kuma daga alãma watau wai Annabi taɓaɓɓe ne, mahaukaci. Taɓaɓɓe da mahaukaci duka ma'anarsu guda ce, watau marashin hankali,wanda aka yi wa alãma da rashin hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin)."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 496,
            "translated_text": "(Mazon ya ce): \"Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "\"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "\"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "\"Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "(Allah Ya ce): \"To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "\"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Da shuke-shuke da matsayi mai kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka *a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau sama da ƙasa ba su girgizu ba sabõda halaka su da aka yi kamar ba a yi, kõme ba."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna*<br \/>\n____________________<br \/>\n * An bai wa Banĩ lsrã'ĩla ni'imar ilmi na Taurãta, an ɗaukaka su, sabõda aiki da ilmin, a kan sauran mutãnen zãmaninsu, kuma aka bã su ãyõyin mu'ujiza kamar tsãge teku da mannu da salwa da sauransu, amma kuma dukkan waɗannan ni'imomĩn sai da suka gushe a lõkacin da suka sãɓawa umurnin Allah, sai kuma ƙasƙanci ya maye musu daga bãya. Wannan kuma wa'azi ne ga Musulmi waɗanda Allah Ya ɗaukaka su da Alƙur'ãni a kan sauran mutãne, idan sun kauce masa zã su wulãkantu."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Lalle waɗannan mutãne*, haƙĩka, sunã cẽwa,<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Anã nufin mutãnen zãmanin Annabi Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, waɗanda ake kiran su zuwa ga Musulunci."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "\"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "\"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 497,
            "translated_text": "Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),"
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Ita ce abincin mai laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Kamar tafasar ruwan zãfi."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "(A cẽ wa malã'ikun wutã), \"Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "\"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "(A ce masã), \"Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "\"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro)."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 44,
            "page_number": 498,
            "translated_text": "Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mãsu jira ne ga abin da zai sãme su idan ba su yi ĩmãni ba, watau ni'imar da aka ba su zã ta gushe ke nan dõmin ba su aiwatar da ita ba a kan umuruin Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Ḥ. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Saukar Littãfi daga Allah Mabuwãyi Mai hikima yake."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Lalle ne a cikin sammai da ƙasa akwai ãyõyi* ga mãsu ĩmãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Ãya, ita ce alãma mai jan hankalin mutum zuwa ga shiriya. Jam'inta, shi ne ãyõyi."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Kuma a cikin halittarku da abin da ke watsuwa na dabba akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yaƙĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki, akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Waɗancan ãyõyin Allah ne, Munã karanta su gare ka da gaskiya. To, da wane lãbãri bãyan Allah da ãyõyinSa suke yin ĩmãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Bone ya tabbata ga dukan mai yawan ƙiren ƙarya, mai laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Yanã jin ãyõyin Allah anã karanta su a kansa, sa'an nan ya dõge yanã makãngari, kamar bai jĩ su ba. To, ka yi masa bushara da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Kuma har idan ya san wani abu daga ãyõyinMu, sai ya rika su da izgili. Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa (a dũniya)."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Wannan (Alƙur'ãni) shi ne shiryuwa. Kuma waɗanda suka kãfirta game da ãyõyin Ubangijinsu, sunã da wata azãba ta wulãkanci mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Allah ne wanda Ya hõre muku tẽku dõmin jirgi ya gudãna a cikinta da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 499,
            "translated_text": "Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 500,
            "translated_text": "Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, *dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Kwanukan Allah, sũ ne masĩfu waɗanda ke sãmun kãfirai waɗanda bã su bin sharĩ'ar Allah. Wãtau Allah Ya umurci Annabi ya gaya wa Musulmi, cewa wanda bã ya tsõron masĩfu sabõda ya ki aiwatar da sharĩ'ar Allah a kansa to kada Musulmi su dãmu da shi, watau kãfiran amãna nã iya bin dõkõkinsu na al'ãda, bãbu ruwan Musulmi matuƙar dai ba su shũka wata fitina ba a gare su. A bãyan haka Allah zai sãka wa kõwa game da aikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 500,
            "translated_text": "Wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, dõmin kansã, kuma wanda ya mũnana aki, to, a kansa. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 500,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai* (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu).<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bã Musulmi kawai aka aikowa Manzo ba,ba su kawai aka bã su sharĩ'a ba, kuma aka umurce su da binta ba, Banĩ Isrã'ĩla ma an bã su haka kuma sunɗaukaka a kan mutãne a lõkacin da suka yi aiki da sharĩ'ar, kuma suka ƙasƙanta a lõkacin da suka bar aiki da ita. Musulmi ma haka suke idan sun bar sharĩ'ar da Allah Ya aza su a kanta, zã su ƙasƙanta yadda Yahũdawa suka ƙasƙanta."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 500,
            "translated_text": "Kuma Muka bã su hujjõji na umurni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu, sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu, a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna)."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 500,
            "translated_text": "Sa'an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ'a ta al'amarin. Sai ka bĩ ta, Kuma kada kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 500,
            "translated_text": "Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 500,
            "translated_text": "wannan (Alkur'ãni) hukunce-hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 500,
            "translated_text": "Kõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã!"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 500,
            "translated_text": "Alhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi,* Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ilmin Allah bã shi da iyãka, Yanã bũɗa shi ga wanda Ya ga dãma, a inda kõ a lõkacin da Ya ga dãma, amma dai duk ilmin da bai saukar da shi ga Annabi Muhammadu ba, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, to, bã a aiki da shi ga hukunci kõ sharĩ'a, wanda ya bi shi kuwa, to, ya ɓace ga aikinsa, bã ya cikin shiryayyu mãsu zaman lãfiya a dũniya kuma su shiga Aljanna a Lãhira, dõmin sharaɗin haka shĩne bin sunna. Wanda ya bar sunna kuwa, ya yi kuskuren hanya, bãbu mai shiryar da shi kuma sai Allah idan Yã so shi da rahama, watau Ya sanya shi ya tũba. Wannan ya nũna cewa ibãda da mu'ãmala duka ɗaya suke ga Musulunci, barin aiki da sharĩ'a a cikin kõwannensu duka, kãfirci ne ga wanda ya halatta yin haka nan. Mafi yawan kãfircin da ya sãmi Musulmi, ya zo musu ne ta hanyar barin mu'ãmalõli da sharĩ'ar Allah, suka &# 82auki yin salla da mai kama da ita, shi kaɗai ne Musulunci, suka kãfirta da haka."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa (da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani.\" Alhãli kuwa (ko da suke faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance hujjarsu fãce suka ce: \"Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "Ka ce: \"Allah ne ke rãyar* da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wãtau ba kũ ne ke rãyuwa da kanku ba, sai an rãyar da ku, haka ne ga mutuwa, bã ku ne ke mutuwa da kanku ba, sai an matar da ku, kuma Allah Shi Ɗaya ke iya rãyarwa ko matarwa. To, yãya ne zã ku ƙi bin sharĩ'ar da Ya umurce ku da binta?."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "\"Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa) zã su yi hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga littãfinta. (A ce musu) \"A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "\"Wannan littãfinMu ne yanã yin magana a kanku da gas, kiya. Lalle Mũ, Mun kasanceMuna sauya rubũtun tamkar abin dakuka kasance kunã aikãtãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "To, amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, to, Ubangijinsu zai sanya su a cikin rahamarsa. Wannan shĩ ne babban rabo bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): \"Shin, ãyõyĩNã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi?\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 501,
            "translated_text": "\"Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba.\"'"
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "Kuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "Kuma aka ce: \"A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "\"Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "Sabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã, Ubangijin halittu."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 45,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "Kuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "Ḥ. M̃."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "Saukar da littafi daga Allah, Mabuwãyi, Mai hikima yake."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi (da shi)."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nũna mini, menene suka halitta daga ƙasa? Kõ kuwa sunã da tãrayya a cikin sammai? Ku zo mini da wani littãfi na gabãnin wannan (Alƙur'ãni) kõ wata alãma daga wani ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 502,
            "translated_text": "Kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da bã zai karɓa masa ba, bar Rãnar Kyama, alhãli sũ (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiransu?"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 503,
            "translated_text": "Kuma idan aka tãra mutãne sai su kasance maƙiya a gare su, alhãli sun kasance mãsu ƙi ga ibãdarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 503,
            "translated_text": "Kuma idan anã karãtun ãyõòyinMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta ga gaskiya a lõkacin da ta jẽ musu, su ce, \"Wannan sihiri ne bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 503,
            "translated_text": "Kõkuwã sunã cẽwa: \"Yã ƙirƙira shi (Alƙur'ãni) ne?\" Ka ce: \"Idan na ƙirƙira shi ne, to bã ku mallaka mini kõme daga Allah. Shĩ ne Mafi sani ga abin da kuke kũtsãwa a cikinsa na magana. (Allah) Yã isa Ya zama shaida a tsakãnĩnada tsakãninku. Kuma shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 503,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ban kasance fãrau ba daga Manzanni, kuma ban san abin da zã a yi game da ni kõ game da ku (na gaibi) ba, bã ni bin kõme fãce abin da ake yin wahayi zuwa gare ni, kuma ban zama ba, fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 503,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shin, kun gani, idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma kuka kãfirta da shi, kuma wani mai shaida daga Banĩ Isrã'ĩla ya bãyar da shaida a kan kwatankwacinsa, sa'an nan ya yi ĩmãni, kuma kuka kangare? Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 503,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni: \"Da (Alƙur'ãni) ya kasance, wani alhẽri ne,\" dã ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su shiryu game da shĩ ba, to, zã su ce, \"Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe.\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 503,
            "translated_text": "Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma rahama. Kuma wannan (Alƙur'ãni) littafi ne mai gaskatãwa (ga littafin Mũsã), a harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra ga mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 503,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda* suka ce: \"Ubangijinmu Allah ne,\" sa'an nan suka daidaitu, to, bãbu wani tsõro a kansu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Yã fara da wanda ya yi wa kansa nasĩha, kuma ya yi aiki da ita, to, shĩ mai gargaɗi ne. Haka kuma mai yin nasĩha ga mutãne, shĩ mã mai gargaɗi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 503,
            "translated_text": "Waɗannan 'yan Aljanna ne, sunã madawwama a cikinta, a kan sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 504,
            "translated_text": "Kuma Mun yi wasiyya ga mutum* game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in, ya ce: \"Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa).\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mutum a cikin iyãlinsa, kõ ya zama mai gargaɗi ga kansa da nasĩha ga mahaifansa da zuriyarsa kamar yadda ya bayyana a cikin ãyõyi 13,l4 da l5, kõ kuma ya zama mai butulci ga kansa, ya tõzartar da iyãyensa da zuriyarsa, kamar yadda ya bayyanaa cikin ãyõyi 17 da 18."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 504,
            "translated_text": "Waɗancan ne waɗanda Muke karɓa, daga gare su, mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Muke gãfarta mafi mũnanan ayyukansum (sunã) a cikin 'yan Aljanna, a kan wa'adin gaskiya wanda suka kasance anã yi musu alkawari (da shi)."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 504,
            "translated_text": "Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: \"Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni cẽwa zã a fitar da ni daga (kabari) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa sun shũɗe a gabãnĩna (ba su kõmo ba)?\" Kuma sũ (mahaifan) sunã nẽman Allah taimako (sunãce masa) \"Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa'adin Allah gaskiya ne.\" Sai shi kuma ya ce. \"Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 504,
            "translated_text": "Waɗancan ne waɗanda kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin al'ummõmi waɗanda suka shũɗe, (bã da daɗẽwa ba), a gabãninsu, daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 504,
            "translated_text": "Kuma ga kõwane nau'i, yanã da darajõji daga abinda suka aikata. Kuma dõmin (Allah) Ya cika musu (sakamakon) ayyukansu, alhãli kuwa sũ, bã zã a zãlunce su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 504,
            "translated_text": "Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã (a ce musu): \"Kun tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 505,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci ɗan'uwan* Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare shi (da cẽwa) \"Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku azãbar yini mai girma.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ya ambaci hũdu da mutãnensa Ãdãwa da misãlin waɗansu mãsu garagaɗi daga Annabãwan da suka shũɗe da kuma mutãnensu da yadda aka halaka su daga inda suke zaton rahama ta Je musu. Haka ne hukuncin. Dukan wanda aka yi wa gargaɗi da bin umurnin Allah, idan ya ƙi bi, sa'an nan ya bi son zũciyarsa, Allah zai Kãwo masa azãba daga inda yake zaton alheri ga kansa."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 505,
            "translated_text": "Suka ce: \"Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 505,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma inã iyar maku abin da aka aiko ni da shi, kuma amma inã ganin, kũ, wasu mutãne ne, kunã jãhiltar gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 505,
            "translated_text": "To, a lõkacin da suka ga azãbar, kumar hadari mai fuskantar rãfukansu, suka ce: \"Wannan hadari ne mai yi mana ruwa. Ã'a, shĩ na abin da kuke nẽman gaggawar saukarsa; Iska ce, a cikinta akwai wata azaba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 505,
            "translated_text": "Tanã darkake kõwane abu da umurnin Ubangijinta. Sai suka wãyi gari, bã a ganin kõme fãce gidãjensu. Kamar wannan ne Muke sãka wa mutãne mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 505,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun ba su ĩko ga abin da ba Mubã ku ĩko gare shi ba, kuma Muka sanya musu wani irin jĩ da gani dazukãta. Sai dai jnsu bai amfãne su ba, kuma zukãtansu ba su amfãne su ba ga kõme, dõmin sun kasance sunã musu game da ãyõyin Allah, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa na izgili game da shi ya wajaba* a gare su.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ya wajaba a gare su, watau sakamakonsa ya tabbata a kansu da azãba."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 505,
            "translated_text": "Kuma ne, lalle haƙĩƙa, Mun halakar da abin da yake kẽwayenku na alƙaryu kuma Muka jujjũya ãyõyi, tsammãninsu zã su kõmo."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 505,
            "translated_text": "To, don mẽne ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abũbuwan yi. wa baiko, gumaka, ba su taimake su ba? Ã'a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 506,
            "translated_text": "Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu* zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: \"Ku yi shiru.\" Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wannan yã nũna cewa a cikin aljannu akwai Musulmi da masu gargaɗi, kuma idan mutum ya yi gargaɗi, dõmin Allah, Allah zai taimake shi da mãsu saurãra masa, kõ da daga waɗansu jinsin da ba nãsa ba. Kuma zama a cikin wani addinin Allah da ya shige, ba ya isa ga wanda bai shiga addinin Musulunci ba, a bãyan bayyanar Musulunci."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 506,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ya mutãnenmu! Lalle mũ, mun ji wani littãfi an saukar da shi a bãyãn Mũsã, mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 506,
            "translated_text": "\"Yã mutãnenmu! Ku karɓa wa mai kiran Allah, kuma ku yi ĩmãni da Shi, Ya gãfarta muku daga zunubanku, kuma ya tserar da ku daga azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 506,
            "translated_text": "\"Kuma wanda bai karɓa wa mai kiran Allah ba to bai zama mai buwãya a cikin ƙasa ba, kuma ba ya da waɗansu majiɓinta, baicin Shi. Waɗannnan sunã a cikin ɓata bayyananna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 506,
            "translated_text": "Shin, kuma ba su gani ba cẽwa: \"Lalle Allah, Wanda Yã halitta sammai da ƙasa kuma bai kãsa ga halittarsu ba, Mai ĩkon yi ne a kan rãyar da matattu?\" Na'am, lalle Shi, Mai ĩkon yi ne a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 506,
            "translated_text": "Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, (a ce musu) \"Ashe, wannan bã gaskiya ba ne?\" Su ce: \"Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!\" Sai Ya ce, \"To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 46,
            "page_number": 506,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka yi haƙuri kamar yadda mãsu ƙarfin niyya daga Manzanni suka yi haƙuri. Kuma kada ka yi musu gaggãwa. Kamar dai sũ, a rãnar da suke ganin (sakamako) abin da ake yi musu wa'adi ba su zauna ba, fãce sa'a guda daga yini. Iyarwa dai da Manzanci). Shin, akwai wanda za a halakar? (Bãbu), fãce mutãne fasiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange mutãne daga tafarkin Allah, (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Wannan kuwa sabõda lalle, waɗanda suka kãfirta sun bi ƙarya, kumar lalle waɗanda suka yi ĩmãni, sun bi gaskiya daga Ubangijinsu. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana wa mutãne misãlansu."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Sabõda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta, sai ku yi ta dũkan wuyõyinsu har a lõkacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma karimci a bãyan' haka kõ biyan fansa, har yãƙi ya saukar da kayansa mãsu nauyi. Wancan, dã Allah nã so da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaƙin ba) kuma amma (ya wajabta jihadi) dõmin Ya jarraba sãshenku da sãshe. Kuma waɗanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah,* to, bã ai ɓatar da ayyukansu ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Tafarkin Allah, (fi sabilillahi)a wannan sũra tanã nufin jihãdi na takõbi dõmin ɗaukaka kalmar Allah da tsare ta. Anã fassara tafarkin Allah a waɗansu wurãre da jihãdi na takõbi kõ na magana dõmin shiryar da mutãne kõ dõmin tsaron gaskiya, kõ kuma karantarwa, da kuma tsare rai daga sha'awarta da fushinta. A cikin Hadisi anã ruwaitõwa cewa tsaron rai daga sha'awarta da fushinta shĩ ne jihãdi wanda ya fi girma."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Zai shiryar da su, kuma Ya kyautata hãlãyensu."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Kuma Ya shigarda su Aljanna (wadda) Ya siffanta ta a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku..*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Tabbatar da dugadugan ƙafãfun, yanã nufin sanya musu jãrumta a cikin zukãtansu, dõmin ƙafãfunsu, su kafu a wurin yaƙi, dõmin kada su gudu."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta, to, ruɓushi ya tabbata a gare su, kuma (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Wannan, sabõda lalle sũ, sun ƙi abin da Allah Ya saukar dõmin haka Ya ɓata ayyukansu."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai (na kõwane zãmani)."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 507,
            "translated_text": "Wancan! Sabõda lalle Allah ne Majiɓincin waɗanda suka yi ĩmãni, kuma lalle, kafirai bãbu wani majiɓinci a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 508,
            "translated_text": "Lalle ne, Allah nã shigar da waɗanda suka yi ĩmani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jin ɗan daɗi (adũniya) kuma sunã ci, kamar yadda dabbõbi ke ci, kuma wutã ita ce mazauni a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 508,
            "translated_text": "Kuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa bãbu wani mai taimako a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 508,
            "translated_text": "Shin, wanda ya kasance a kan wata hujja daga Ubangijinsa, zai zama kamar wanda aka ƙawãce masa mugun aikinsa, kuma suka bibbiyi son zũciyõyinsu?"
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 508,
            "translated_text": "Misãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata gãfara daga Ubangijinsu. (Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya kakkãtse hanjinsu?"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 508,
            "translated_text": "Kuma daga cikinsu akwai wanda ke saurare* zuwa gare ka, har idan sun fita daga wurinka, su ce wa waɗanda aka bai wa ilmi \"Mẽne ne (Muhammadu) ya fãɗa ɗazu?\" Waɗannan ne waɗanda Allah Ya shãfe haske daga zukãtansu, kuma suka bi son zũciyõyinsu.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan shĩ ya nũna cewa wani ɗan rahõto ba zai iya fahimtar gaskiya ba, matuƙar anã aikin Allah da gaskiya. Allah na sanya tsõro a cikin zukãtan kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 508,
            "translated_text": "Kuma waɗannan da suka nẽmi shiryuwa (Allah) Ya ƙara musu shiryuwarsu, kuma Yã bã su (sakamakon) taƙawarsu.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Taƙawa, ita ce bin umurnin Allah da nĩsantar haninsa sabõda haka abin da Allah ke bai wa mai taƙawa, shi ne sakamkon aikinsa wanda ya yi daidai da sunnar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 508,
            "translated_text": "To shin sunã jiran (wani abu)? Fãce S'a ta jẽ musu bisa abke, dõmin lalle sharuɗɗanta sun zo. To, yãya tunãwarsu* take, idan har ta jẽ musu?<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Tunãwarsu da wa'aztuwarsu ga Sa'a bã zai yi musu amfãni ba, a bãyan tã je musu. Wa'azi bã ya amfãni, sai idan wanda aka yi wa shi, yã yi aiki da shi a gabãnin mutuwa ta je masa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 508,
            "translated_text": "Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka,* (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku.<br \/>\n____________________<br \/>\n * An umurci Annabi ya nemi gãfara dõmin mutãne su yi kõyi da shi, dõmin Allah Ya riga ya tsare shi daga zunubi a gabãni da bayan Manzanci."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: \"Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba? \"To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a gare su:"
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "Yin ɗã'a da magana mai kyau. Sa'an nan idan al'marin ya ƙullu,* to, dã sun yi wa Allah gaskiya, lalle dã ya kasance mafifi ci a gare su.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * kulluwar a'lamari, shĩ ne umurni da yin yãƙi, yi wa Allah gaskiya, shĩ ne zartar da umurninSa, bã tãre da tsõro ba. Tsõro mũnafunci ne."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "To, shin, kunã fãtan idan kun jũya (daga umurnin) zã ku yi ɓarna a cikin ƙasã, kuma ku yan yanke* zumuntarku?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Dõmin barin jihãdi yanã kai ga wãtsuwar ɓarna da fasãdi a cikin ƙasã. Wãtsuwar fasãdi,yanã kai ga yanke zumunta tsakãnin dangi, sabõda zãluntar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "Waɗannan sũ ne waɗanda Allah Ya la'anẽ su, sa'an nan Ya kurumtar da su, kuma Ya makantar da ganinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "Shin to, bã zã su, kula da Alƙur'ãni ba, kõ kuwa a bin zukã tansu akwai makullansu?"
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "lalle ne, waɗanda suka kõma bãya a kan dugãdugansu a bãyan shiryuwa tã bayyana a gare su, Shaiɗan ne ya ƙawãta *musu (haka), kuma ya yi musu shibta.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Barin jihãdi, ridda ne da kõmãwa zuwa ga kãfirci da ƙawãtãwar Shaiɗan cewa rashin zuwa yãƙi na sanya kwanciyar hankali da rashin mutuwa, kuma yanã sanya musu waswasi da haka."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "Wancan, dõmin lalle sũ sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: \"Za mu yi muku ɗã'ã ga sãshen al'amarin,\" alhãli kuwa Allah Yanã sane da gãnawarsu ta asĩri."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "To, yãya hãlinsu yake a lõkacin da malã'iku ke karɓar rãyukansu, sunã dũkan fuskõkinsu da ɗuwaiwansu?"
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "Wannan, dõmin lalle sũ sun bi abin da ya, fusãtar da Allah kuma sun ƙi yardarSa, sabõda haka Ya ɓãta ayyukansu."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 509,
            "translated_text": "Ko kuwa waɗanda ke da wata cũta a cikin zukatansu suna zaton cẽwa Allah ba zai fitar da mugun ƙulle-ƙullen su (ga Musulunci) ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 510,
            "translated_text": "Kuma dã Munã so, dã lalle Mun nũna maka su. To, lalle kanã sanin su game da alãmarsu. Kuma lalle kanã sanin su ga shaguɓen magana, alhali kuwa Allah Yanã sanin ayyukanku."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 510,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, Munã jarraba ku, har Mu san mãsu jihãdi daga cikinku da mãsu haƙuri kuma Muna jbrraba lãbãran ku."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 510,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda suka kãfirta, kuma suka kange daga tafarkin Allah, kuma suka saɓa wa Manzon sa a bãyan shiriyar ta bayyana a gare su, bã za su cũci Allah da kõme ba, kuma zã Ya ɓãta ayyukansu."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 510,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗa'a ga ManzonSa, kuma kada *ku ɓãta ayyukanku.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kada ku ɓata ayyukanku da ƙin ɗa'a ga Allah da ManzonSa ga fita zuwa yãƙi da waninsa. Ridda na ɓãta ayyuka, kuma riya da mãmãkin kai na ɓãta lãdar ayyuka, kuma ƙwãra da cũtarwa sunã ɓãta lãdar sadaka. Sauran manyan zunubbai, bã su ɓãta ayyuka sai ga ra'ayin Mu'utazilãwa mãsu cewa manyan zunubbai na ɓãta lãdar ayyuka kamar ridda. An ɓãta maganarsu da ãyar da ke cewa: \"Allah na gãfarta abin da ya kãsa hãka ga wanda Yã so.\" Sũratun Nisa'i ãyã ta48."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 510,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kãfirta sa'an nan kuma suka kange (mutãne) daga tafarkin Allah, sa'an nan suka mutu, alhãli kuwa sunã kãfirai, to, Allah bã zai yi gãfara ba a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 510,
            "translated_text": "Sabõda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zũwaga sulhi alhãli kuwa kũ ne mafiɗaukaka kuma Allah na tãre da ku, kuma bã, zai naƙasa muku ayyukanku ba."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 510,
            "translated_text": "Rãyuwar dũniya, wãsã da abin shagala kawai* ce, kuma idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, Allah zai kãwo muku ijarõrinku, kuma bã zai tambaye ku dũkiyarku ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wãsã, shi ne dukan aiki wanda aka yi bã da nufin wata fa'ida ta addini ba, watau anã yin sa ne dõmin a sãmi abin aikatãwa a ɓãta lõkaci. Dukan ayyukan da mutum ya yi da nufin rãyuwar dũniya kawai, to, ya zama wãsã kõ dã cin abinci ne da karãtu. Kuma duk abin da mutum ya yi da niyyar bin umurnin Allah, wãjibi to ya zama aikin Lãhira kõ da cin abinci ne da jima'insa da matarsa, kamar yadda yake a cikin Hadĩsin Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 510,
            "translated_text": "Dã Allah zai tambaye ku su (dũkiyõyin) har Ya wajabta muku bãyarwa, zã ku yi rõwa kuma Ya fitar da miyãgun ƙulle-ƙullenku."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 47,
            "page_number": 510,
            "translated_text": "Ga ku, ya ku waɗannan! Anã kiran ku dõmin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa'an nan daga cikinku akwai mai yin rõwa. Kuma wanda ke yin rõwa, to, yanã yin rõwar ne ga kansa. Kuma Allah ne wadãtacce alhãli kuwa kũ fãƙĩrai ne. Kuma idan kuka jũya (daga yi Masa ɗã'a), zai musanya waɗansu mutãne waɗansunku sa'an nan bã zã su kasance kwatankwacinku ba."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 511,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun yi maka rinjãye (a kan maƙiyanka), rinjaye bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 511,
            "translated_text": "Dõmin Allah Ya shãfe abin da ya gabãta na laifinka* da abin da ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imarSa a kanka, kuma Ya shiryar da kai ga hanya madaidaiciya.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Laifin Annabi wanda Allah Ya gãfarta, shĩ ne a lõkacin da ya fãra kiran mutãne zuwa ga bauta wa Allah, Shĩ kaɗai, mãsu bauta wa waɗansu abũbuwa sun ga laifinsa a wannan, sun yi ƙiyayya da shi sabõda haka, har suka yi yãƙi da shi, dõmin tsare ibãdarsu, da al'adunsu, har a lõkacin da Allah Ya bã shi rinjãye bayyananne a kansu, suka gãne amfãnin abin da yake kiran su zuwa gare shi na alheri, suka yãfe laifin da suke zato kuma suka so shi son da bã ya ƙãrewa har Tãshin Ƙiyãma. Wannan ni'imar Allah ce babba ga Annabinsa, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanya madaidaiciya, ita ce sharĩ'ar da Allah Ya bã shi, wadda ke jan jama'arsa a kan alheri har ya zuwa Tãshin ƙiyãma, kuma su tãshi a cikin alheri mafi girma, matuƙar dai sun bĩ ta, sun yi aiki da ita gwargwadon yadda ya nũna musu ita."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 511,
            "translated_text": "Kuma Allah Ya taimake ka, taimako mabuwãyi."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 511,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukãtan mũminai dõmin su ƙãra wani ĩmãni tãre da imãninsu, alhãli kuwa rundunõnin sammai da ƙasa, na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 511,
            "translated_text": "Dõmin Ya shigar da mũminai maza da mũminai mãtã gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen, sunã madawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu mũnãnan ayyukansu. wannan abu ya kasance a wurin Allah babban rabo, mai gimia."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 511,
            "translated_text": "Kuma Ya yi azãba ga munãfikai maza da munãfikai mãtã da mushirikai maza da musbirikai mãtã, mãsu zaton mugun zato game da Allah, mugunyar masĩfa mai kẽwayẽwa ta tabbata a kansu, kuma Allah Ya yi hushi da su, kuma Ya la'ane su, kuma Ya yi musu tattlain Jahannama kuma ta mũnana ta zama makõma (gare su)."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 511,
            "translated_text": "Rundunõnin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 511,
            "translated_text": "Lalle Mũ Mun aike ka, kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 511,
            "translated_text": "Dõmin ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku ƙarfafa shi, kuma ku girmama Shi, kuma ku tsarkake Shi (Allah) sãfiya da maraice."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 512,
            "translated_text": "Lalle waɗanda ke yi maka mubãya'a,* Allah kawai ne suke yi wa mubãya'a, Hannun Allah nã bisa hannayensu, sabõda haka wanda ya warware, to, yanã warwarẽwa ne a kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to, (Allah) zai kãwo masa ijãra mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Asalin mubãya'a daga bai'u ne, watau ciniki, wanda ya yi mubãya'a ga Limãmin Musulmi kamar yã yi ciniki ne yã sayar da ransa, dõmin ya karɓi Aljanna daga Allah a Rãnar Ƙiyãma. Mubãya'a ta farko,ita ce wadda aka yi wa Annabi a Hudaibiyya wani ɗan gari ne kusa da Makka a hanyar Jidda, tafiyar kwana ɗaya. An ce tanã cikin Hurumi, waɗansu sun ce bã ta cikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 512,
            "translated_text": "Waɗanda aka bari daga ƙauyãwa* zã su ce maka, \"Dũkiyõyinmu da iyãlanmu sun shagaltar da mu, sai ka nẽma mana gãfara.\" Sunã faɗã, da harsunansu, abin da bã shĩ ne a cikin zukãtansu ba. Kace: \"To, wãne ne ke mallakar wani abu daga Allah sabõda kũ, idan Yã yi nufin wata cũta agare ku kõ kuma (idan) Ya yi nufin wani amfãni a gare ku? Ã'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatãwa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, ya yi nufin tafiya Makka dõmin ya yi Umra sabõda mafarkin da ya yi cewa yã ga ya shiga Makka shi da Sahabbansa, sunã mãsu yin aski da saisaye na ibãda, sai ya ce wa ƙauyãwan da ke gefen Madina su fita tãre da shi dõmin kada Ƙuraishãwa su fãɗa shi da yãƙi,su tsare shi daga Ɗãkin. Kuma ya yi harama ya kõra hadaya dõmin mutãne su san bã yãƙi yake nufi ba. Sai waɗansu mãsu yawa daga ƙauyãwa suka yi nauyin fita, sukayi zamansu kuma suka ce: \"Zai tafi zuwa ga mutãnen da suka yãƙe shi a tsakar gidansa a Madĩna, suka kashe Sahabbansa. Ba zã mu bĩ shi ba dõmin mu halaka kanmu.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 512,
            "translated_text": "Ã'a kun yi zaton Annabi da mũminai, bã za su kõmo zuwa ga iyãlansu ba, har abada. Kuma an ƙawãta wannan (tunãni) a cikin zukãtanku, kuma kun yi zato, zaton mugunta, kuma kun kasance mutãne halakakku."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 512,
            "translated_text": "Kuma wanda bai yi ĩmãni da Allah da kuma Manzonsa ba, to, lalle Mũ, Mun yi tattalin wutã mai tsananin ƙũna, dõmin kafirai."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 512,
            "translated_text": "Mulkin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, Yanã gãfartawa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so alhãli kuwa Allah Ya kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 512,
            "translated_text": "Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi* dõmin ku karɓo su, \"Ku bar mu, mu bĩ ku.\" Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: \"Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka.\" Sa'an nan zã su ce: \"Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne.\" Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai kaɗan.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A bãyan sulhun Hudaibiyya Allah Ya yi wa Annabi alkawarin zai buɗe masa Haibara ya sãmi ganĩma mai yawa, amma kuma kada ya bari ƙauyãwan da aka nema su fita zuwa Makka, suka ƙi su fita tãre da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 513,
            "translated_text": "Ka ce wa waɗanda aka bari daga ƙauyãwa: \"Za a kira ku zuwa ga waɗansu mutãne* mãsu tsananin yãƙi (dõmin) ku yãƙe su kõ kuwa su musulunta. To, idan kun yi ɗã'a, Allah zai kãwo muku wata ijãra mai kyau, kuma idan kuka jũya bãya kamar yadda kuka jũya a gabãnin wancan, zai azãbtã ku, azãba mai raɗadi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Abũbakar zai kira su dõmin su yãƙi mutãnen Musailama, ko kuma su yãƙi Rũmu da fãrisa a bãyan rãyuwar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 513,
            "translated_text": "Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi a gidãjen Aljanna, kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya jũya bãya, (Allah) zai azabtãshi, azãba mai raɗãɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 513,
            "translated_text": "Lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yarda da muminai a lõkacin da suke yi maka mubãya, a* a ƙarƙashin itãciyar nan dõmin Yã san abin da ke cikin zukãtansu sai Yã saukar da natsuwa a kansu, kuma Ya sãka musu da wani cin nasara makusanci.<br \/>\n____________________<br \/>\n * A bãyan da Annabi ya sauka a Hudaibiyya, ya kirãyi Khuraish bn Umaiya el Khuzã'i ya aike shi Makka ya azã shi a kan rãƙuminsa dõmin ya gaya wa shugabanninsu cewa yãtaho Umra ne, bai zo da yãƙi ba. Sai suka sõke rãƙumin Annabi, kuma suka yi nufin kashe Khuraish amma Ahãbish suka hana su, ya zo ya gaya wa Annabi. Sa'an nan Annabi ya kira Umar bn Khattãb dõmin ya aika shi zuwa Makka, sai ya ce: \"Ya Manzon Allah inã tsõron raina ga Ƙuraishãwa, bãbu banĩ Adiyyin bn Ka'ab a Makka balle su kare ni daga gare su, amma inã nũna maka wani mutum wanda ya fĩ ni dangi a cikinta shĩ ne Usman bn Affãn.\" Sai Annabi ya kira Usman ya aike shi zuwa ga Abi sufyãn da shugabannin Ƙuraish, ya bã su lãbãrin cewa bai zo yãƙi ba. ya taho ne dõmin ziyãra kawai ga wannan Ɗãki dõmin ya girmama alfarmarsa. Ya rubũta masa takarda ya tafi da ita. Kuma ya umurce shi da ya yi bushãra ga Musulmi mãsu rauni, cewa cin nasara yã yi kusa, kuma Allah zai ɗaukaka addininsa. Usman ya fita ya tafi Makka ya iske cewa Ƙuraishãwa sun haɗu a kan hana Annabi shiga Makka. Abban bn sa'ĩd bn Asi ya haɗu da Usman a lõklcin shigarsa Makka, sai ya ɗauke shi a kan rãƙumarsa, ya bã shi maƙwabtaka dõmin kada a kashe shi, har ya kai takardar Annabi. Suka nãce cewa Annabi bã zai shiga ba suka ce wa Usmãn: \"Idan yanã son ɗawãfi sai ya yi,\" Sai ya ce bã zai yi ba sai Manzon Allah ya yi. Musulmi suka ce: \"Usmãn ya ji daɗi yã yi ɗawafi,\" sai Annabi ya ce: \"Ban yi zaton Usmãn zai yi ba.\" Sa'an nan lãbãri ya zo wa Annabi, cewa an kashe Usmãn sabõda haka Annabi ya ce: \"Idan sun kashe shi, sai mun yaƙe su.\" Wannan ya sa aka yi masa mubãya'a a ƙarƙashin itãciyar ɗalh mai kama da farar ƙaya. A bãyan haka Annabi ya aza hannunSa na hagu a kan hannunsa na dãma, ya ce: \"Gã hannun Usmãnu.\" Mãsu mubãya'a dubũ da ɗari uku kõ ɗari huɗu ne, da cewa za su yi yãƙi da Ƙuraishawa, bã zãsu gudu ba, sai dai su mutu. Daga nan shugabancin ya tabbata. Umar bn Khattãb yã sanya an sãre itãciyar nan dõmin mutãne sun fãra salla a ƙarƙashinta. Ba a yi yãƙi ba, sai aka yi sulhu. Annabi ya kõma a shekara mai zuwa yã yi Umra."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 513,
            "translated_text": "Da waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa da zã su karɓo su. Kuma Allah Yã kasance Mabuwayi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 513,
            "translated_text": "Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo su, kuma Ya gaggauta* muku wannan. Kuma Ya kange** hannãyen mutãne daga gare ku, kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya madaidaiciya.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Cin nasara makusanci, shĩ ne cin Haibara, a bãyan kõmawar Annabi Madĩna a ƙarshen zul Hajji. Sa'an nan ya fita wajen ƙarshen Muharram shekara ta bakwai. Aka samo ganĩma mai yawa. Waɗansu ganĩmõmi na waɗansu ƙasãshen da zã a ci a nan gaba har ƙarshen dũniya. Ganĩmar Haibara ita ce aka gaggauta. ** A lõkacin da Annabi ya fita daga Madĩna zuwa Hudaibiyya Allah Ya kange hannuwan Yahũdãwa daga iyãlan Musulmi na cikin Madĩna, in dã bã dõmin haka ba sai su je su fãɗa su da kashi da kãmu. Sai Allah Ya jefa tsõro a cikin zukãtansu."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 513,
            "translated_text": "Da waɗansu (ganĩmõmin) (5)da bã ku da ĩko a kansu lalle Allah Ya kẽwaye su da saninSa, kuma Allah Ya kasance Mai ikon yi ne a kan dukan kõme.<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Ganĩma da aka yi musu gaggãwa da ita, ita ce Haibara. Ganĩma wadda ba su da ĩko da ita, ita ce sauran ƙasãshen dũniya inda Musulmi suka ci, suka mallake shi, na ƙasar Rumãwa da farisãwa da Masar da sauransu."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 513,
            "translated_text": "Kuma dã waɗanda suka kãfirta sun yãke ku, dã sun jũyar da ɗuwaiwai (dõmin gudu) sa'an nan bã zã su sãmi majiɓinci ba, kuma bã zã su sãmi mataimaki ba."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 513,
            "translated_text": "Hanyar Allah wadda ta shũɗe daga gabãnin wannan, kuma bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah (ta taimakon mũminai akan mai zãluntarsu)."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 514,
            "translated_text": "Kuma Shĩ ne Ya kange hannayensu *daga gare ku, kuma da hannayenku daga gare su, a cikin Makka, bãyan Ya rinjãyar da ku a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Waɗansu Ƙuraishawa ne, sũ tamãnin, suka kewaye Musulmi a Hudaibiyya, da niyyar yaudara, sai aka kãme su, su duka, aka kai su ga Annabi, shi kuma ya yãfe musu, a bãyan ya nũna musu rinjãya. Wannan shĩ ne ya sabbaba yin sulhu."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 514,
            "translated_text": "Sũ ne waɗanda suka kãfirta kuma suka kange ku daga Masallacin Harami, da hadaya tanã tsare (sun hana ta) ta isa ga wurinta. Kuma bã dõmin waɗansu maza mũminai da waɗansu mãtã mũminai ba ba ku sansu ba ku tãkã su har wani aibi ya sãme ku daga gare su, bã da sani ba, (dã Allah Yã yi muku iznin yãƙi), dõmin Allah Ya shigar da wanda Yake so a cikin rahamarSa. Da (mũminai) sun tsabbace dã Mun azabtar da waɗanda suka kãfirta daga gare su da azãba mai raɗiɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 514,
            "translated_text": "A lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka sanya hanãnar ƙabĩ lanci a cikin zukãtansu hanãnar ƙabĩlanci irin *na Jãhiliyya sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa, kuma da a kan mũminai kuma Ya lazimta musu kalmar taƙawa** alhãli kuwa sun kasance mafi dãcẽwa da ita kuma ma'abutanta. Kuma Allah ya kasance Masani game da dukan kõme.<br \/>\n____________________<br \/>\n* A lõkacin da Ƙuraishi suka ga bã su iya yãƙi da Annabi, suka dõge da ƙabĩlancinsu, ta hanyar sulhu. Suka aika sahlu bn Amru da Huwaitib bn Abdul Uzza da Makraz bn Hafs bn Ahnaf dõmin neman sulhu bisa kada Annabi ya shiga Makka a wannan shekara, amma shekara mai kõmõwa ya je ya shiga Makka kwana uku, su kuma su fita har ya ƙãre Umra ya fita. Annabi ya karɓi sulhun. Aka ce Aliyu bn Abi Talib ya rubũta. Wajen rubũtun kuma aka so a yi tãshin hankali, dõmin ya rũbuta, Manzon Allah ya yi sulhu da Ƙuraishãwa, sai kuma suka ce ba su yarda a rubũta kalmar Manzon Allah ba. Sai Annabi ya sanya hannunsa mai daraja ya sõke kalmar da ake sãɓãni a kanta. Allah Ya saukar da natsuwa ga kõwa. ** Kalmar taƙawa ita ce kalmar shahãda dõmin ɗaukar alkawari da ita yanã lazimtawa mai ita bin umurnin Allah da dãɗi kõ ba daɗi ta haka sai natsuwa ta sãmu. Anã ce mata kalmar taƙawa dõmin da ita ake kãre rai daga bin shaiɗan. Ma'anar taƙawa, ita ce kãriya."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 514,
            "translated_text": "Lalle ne haƙĩƙa Allah Ya gaskata wa ManzonSa mafarkinsa da gaskiya: Lalle zã ku shiga Masallacin Harami, in Allah Ya so, kunã mãsu natsuwa, mãsu aske kawunanku da mãsu suisuye, bã ku jin tsõro, dõmin (Allah) Ya san abin da ba ku sani ba, sa'an nan Ya sanya wani cin nasara makusanci a bãyan wannan."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 514,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Ya aiki ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya dõmin Ya rinjãyar da shi a kan addinai dukansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai shaida."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 48,
            "page_number": 515,
            "translated_text": "Muhammadu Manron Allah ne. Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ'i mãsu sujada, sunã nẽman falala* daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin fuskõkinsu, daga kufan sujuda.** Wannan shĩ ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu, a cikin Injĩla ita ce kamar tsiron shũka wanda ya fitar da rẽshensa, sa'an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa'an nan ya daidaita a kan ƙafãfunsa, yanã bãyar da sha'awa ga mãsu shũkar' dõmin (Allah) Ya fusãtar da kãfirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gãfara da ijãra mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Neman falala da sana'ar hannunsu, kõ fatauci, ba su zama nauyi a kan mutãne ba, kõwanensu ya dõgara ga Allah,sa'an nan yanã rãyuwa a kan hãlãliyarsa. ** Kufan sujuda, shĩ ne hasken fuskõkinsu da annurinsu. fuska ita ce madũbin zũciya. Anã gãne zũciyar ƙwarai daga fuskarta. Bã ya halatta ga mutum ya riƙa darkãka gõshinsa ga ƙasã dõmin ya yi kwãdon salla. Wannan alãmar riya ce. Faɗakarwa. Nan ne ƙarshen dõgãyen sũrõri da ake cewa Muɗawwalãtu. An ƙãresu da sũrõri biyu, Ƙitãl dõmin yãƙi, da fat'h dõmin tsãrin gudãnar da siyãsa sabõda tsaron Addĩni. Bãyan haka kuma sai gajerun sũrõri, watau Mufassalãtu."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 515,
            "translated_text": "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da ManzonSa.* Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan yã nũna mana cewa bã yã halatta ga Musulmi ya yi wani aiki ko ya faɗi wata magana sai yã san hukuncin Allah a cikinsu. Kuma kada ya ƙãra wãyõnsa a kan abinda Allah Yã ce, kuma kada ya rage idan yanã da ĩkon cikãwa. Dukan wannan yakan ja Musulmi ga ɓãcin ayyukansa, watau ya yi ridda daga Musulunci."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 515,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku* bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ladubban zama da shugaba.Annabi shi ne kan shugabanni, sai dai ɗã'a gare shi wãjibi ne ga kõme, sauran shũgabanni kuwa ga abin da bai sãɓawa shari'a ba."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 515,
            "translated_text": "Lalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 515,
            "translated_text": "Lalle waɗanda ke kiranka daga bãyan ɗakuna, mafi Yawansu bã su aiki da hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 516,
            "translated_text": "Kuma dã lalle sũ, sun yi haƙuri har ka fita zuwa gare su, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri gare su, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 516,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi* Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Idan wani yã kai lãbãrin ɓarna, kada a yi aiki da shi sai bãyan an bincika an san gaskiyar al'amarin, kãfin a yi aiki da shi. fãsiƙi ga asalin kalma shi ne duka wanda ya karkace daga hanyar ƙwarai wadda aka sani. A nan, fãsiƙi, shi ne mai kai lãbãrin da yake akwai tãshin hankali a cikinsa, ko kuma abin tsõro dõmin ya sanya rũɗu a tsakãnin jama'a tun ba a san haƙĩƙanin al'amarin ba."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 516,
            "translated_text": "Kuma ku sani (cẽwa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Dã Yana bin ku ga (hãlãye) mãsu Yawa na al'amarin, dã kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Yã sõyar da ĩmãni a gare ku, kuma Yã ƙawãta shi a cikin zukãtanku kuma Yã ƙyãmantar da kãfirci da fãsicci da sãɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifõfin nan) su ne shiryayyu."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 516,
            "translated_text": "Bisa ga falala daga Allah da ni'ima. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 516,
            "translated_text": "Kuma idan jama'a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita.* Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan tsãri na sulhu a tsãkanin al'umma biyu mãsu faɗa, shĩ ne hanya mafi kyau wadda har yanzu wayon dũniya bai kai ga yin aiki da shi ba. Dã yanzu an zauna lãfiya, dã Majalisar Ɗinkin Dũniya na iya aiki da shi. haka Yake kuma ga sauran hukunce-hukuncen mutãnen dũniya. Shari'ar Musulunci sabõda ãdalcin da ke cikinta kuma wayon dũniya bai kai ta ga anã iya zartar da shi ba, shĩ ne ya sa ƙasãshen Musulunci ke kaucewa gare ta, dõmin son ran shugabanninsu. Allah Yã mayar da mu ga addininmu! Dukan Musulmin da ya kaucewa sharĩ'ar Musulunci, to, ya kauce ne dõmin ya sami damar yin zãlunci, kuma idan yã halatta kaucewar, yã zama bã Musulmi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 516,
            "translated_text": "Mũminai 'yan'uwan jũna kawai ne, sabõda haka ku yi sulhu a tsakãnin 'yan'uwanku biyu, kuma ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, a yi muku rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 516,
            "translated_text": "\"Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 517,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 517,
            "translated_text": "Yã kũ mutãne!* Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yã kirãyi mãsu ĩmãni a cikin wannan sũra sau biyar ga abin da ya keɓanta da su na umurni da hani kamar yadda Lukmãn ya kirãyi ɗansa wajen yi masa wasiyyõyi. Kuma ya kirãyi mutãne a wannan ãyã ga abin da ya haɗa mũminai da kãfirai wajen halitta, watau alfahari da dangantaka. Dangantaka bã ta ɗaukaka wanda taƙawarsa ba ta ɗaukaka shi ba, kuma bã ta rage wanda taƙawarsa ta ɗaukaka shi. Fĩfĩkon taƙawa, shĩ ne fĩfĩko tabbatacce."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 517,
            "translated_text": "¡auyãwa suka ce: \"Mun yi ĩmãni.\" Ka ce: \"Ba ku yi ĩmãni ba, amma dai ku ce, 'Mun mĩƙawuya, ĩmani bai gama shiga a cikinzukãtanku ba. Kuma idan kun yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, bã zai rage muku kõme daga ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 517,
            "translated_text": "Mũminan gaskiya kawai, sũ ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, sa'an nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihãdi da dũkiyarsu da kuma rãyukansu, cikin tafarkin Allah. Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 517,
            "translated_text": "Ka ce: \"Kuna sanar da Allah ne game da addininku, alhãli kuwa Allah Yã san abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Allah Masani ne ga dukan kõme?\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 517,
            "translated_text": "Suna yin gõri a kanka wai sun musulunta. Ka ce: \"Kada ku yi gõrin kun musulunta a kaina. Ã'a, Allah ne ke yi muku gõri dõmin Ya shiryar da ku ga ĩmãni, idan kun kasance mãsu gaskiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 49,
            "page_number": 517,
            "translated_text": "\"Lalle Allah yanã sanin gaibin sammai da ¡asa, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "¡̃. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: \"Wannan wani abu ne mai ban mãmãki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "\"Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?"
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, *da Samũdãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Rassi sunan wata rijĩya ce. Mutãnenta na zaune a gefenta da dabbõbinsu, sunã bauta wa gumãka, aka aika musu wani Annabi, anã ce da shi Hanzala bn safwan kõ kuma waninsa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Da ma'abũta ƙunci *da mutãnen Tubba'u,** kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ma'abũta ƙunci, mutãnen shu'aibu ne na farko. Bãyan an halaka su, sa'an nan ya tafi Madayana. ** Tubba'u, sarkin Himyar ne,a Yemen, yã musulunta amma mutãnensa suka ƙi bin sa ga addini, aka halaka su, shi kuma ya tsĩra. Shĩ ne sarki wanda ya sãɓãwa ƙã'ida; ya musulunta amma mabiyansa ba su musulunta ba."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 518,
            "translated_text": "Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "(Sai a ce masa): \"Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Kuma abõkin haɗinsa* ya ce: \"Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Malã'ika mai rubũtun aikinsa. Bã ya rabuwa da shi sai a hãlãye uku, wurin jimã'i da salga da wanka. Malã'ikan da aka haɗa shi da shi dõmin ya rubũta ayyukansa."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "(A ce wa Malã'iku), \"Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "\"Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "\"Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Abõkin haɗinsa* ya ce: \"Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Shaiɗanin da ke tãre dashi. A cikin hadĩsi an ruwaito cewa kõwa yana da Shaiɗani tãre da shi, sai dai idan ya rinjãye shi, da abin da Allah Ya aza masa, ko kuma shi sai shaiɗãnin ya rinjãye shi da bin son zũciyarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Ya ce: \"Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "\"Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama \"Shin, kin cika?\" Kuma ta ce: \"Ashe,* akwai wani ƙãri?\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan jawãbi na Jahannama yanã ɗaukar ma'anõni biyu. Ta farko tanã nũna ta cika ƙwarai, amma tanã kũkan a ƙara mata wani abu a cikinta. Wannan fassara ta yi daidai da ayãr da ta ce, \"Lalle na cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya.\" Sura ta 32, ãyã ta 13. Fassara ta biyu, ita ce Jahannama nã neman ƙãri tanã hushi sabõda mãsu sãɓawa umurnin Allah. Sũra ta 67 ãyõyi 6, 7 da 8."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "\"Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa)."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "\"Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, *kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Tsoron Allah a fake, shĩ ne a bauta masa, bã da riya ba, ɓayyane da ɓõye duka ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "(A ce musu) \"Ku shige ta da aminci, (5)waccan ita ce rãnar dawwama.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Kõ kuma ku shiga da sallama."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 519,
            "translated_text": "Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'?* (Babu).<br \/>\n____________________<br \/>\n * Sun nħmi wurin tsĩra, ba su sãmu ba, sabõda haka kãfiran yanzu ma ba su iya samun wurin tsĩra, sai dai idan sunkõma ga Allah ta hanyar ManzonSa kawai, watau taƙawa ga Allah ke nan. Anã kãre azãbarSa da ibãdarSa kamar yadda Yake so."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa)."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi* game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tasbĩhi game da gõdewa Allah a gabãnin fitar rãnã, shi ne sallar asuba, na gabãnin ɓacewarta, shi ne sallar Azahar da La'asar. Daga dare kuwa, shĩ ne sallar Magariba da Isha'i. Bãyan sujada, shĩ ne sallõli na nafila kuma ma'anarsa a nan tasbĩhi da tahmĩdi da kabbarõri a bãyan sallõli farillai talãtin da uku kõwace, sa'annan a cika ɗari da addu'ar da aka ruwaito a nan."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri *makusanci.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mai kira shĩ ne Isrãfĩlu a cikin ƙaho a Baitil Maƙadis dõmin a nan ƙasa ta fi zama kusa da samã."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari)."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 50,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani,* ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ya nũna ba a wa'azi da ilmin da bã daga Alƙur'ãni aka fitar da shi ba, sai fa idan bai sãɓawa abin da ke cikin Alƙur'ani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa)."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah)."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 520,
            "translated_text": "Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo)."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani)."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya)."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "An la'ani mãsu ƙiri-faɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Sunã tambaya: \"Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "(A ce musu): \"Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya)."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,"
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?"
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce \"Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,"
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: \"Bã zã ku ci ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: \"Kada kaji tsõro.\" Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: \"Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 521,
            "translated_text": "Suka ce: \"Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "(Ibrãĩm) ya ce: \"To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "\"Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom)."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "\"Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: \"Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!\""
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: \"Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,"
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 522,
            "translated_text": "Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: \"Mai sihiri ne kõ mahaukaci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Bã Ni nufin su sãmo Mini abinci, kuma bã Ni nufin su dafa Mini abinci."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 51,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã)."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Da wani littãfi rubũtacce."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda)."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Da rufin nan da aka ɗaukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa)."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Bã ta da mai tunkuɗẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 523,
            "translated_text": "(A ce musu): \"Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "\"To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "\"Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "(A ce musu): \"Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu *suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan ãyã tanã nũna yadda wani ke ceton wani sabõda kusanci dõmin a ƙãra daukaka mai ceton. Sharaɗin ceton shĩ ne wanda ake ceton yanã da nãsa ĩmanin. Wanda jinginarsa ta halaka bãbu mai cetonsa. Zuriya ta haɗa uwãye da almajiran mãlami sãlihi. Suna shiga a cikin cetonsa."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Suka ce: \"Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "\"To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "\"Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Shin zã su ce: \"Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ\"?"
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 524,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?"
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, cẽwa suke yi: \"Shi ne ke ƙãga faɗarsa\"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?"
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, Yanã da* 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Waɗansu Lãrãbawa sunãkiran Malã'ika 'ya'yan Allah mãtã, sunã kuma bauta musu dõmin su cece su daga Allah, suna yin gumãka da sũnansu."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?"
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!"
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake* Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).<br \/>\n____________________<br \/>\n  * (Ma'anar ita ce tsarkakewa kõ tasbĩhi, 'tsare sallõli, farillai, anã cewa' faɗin \"Subhãnal lãhi wal Hamdu Lillãhi\" a bãyan kõwane mazauni, dõmin ya zama kaffãrar wannan mazaunin."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 52,
            "page_number": 525,
            "translated_text": "Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalõkacin jũyãwar taurãri."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi *ya sanar da shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wahayin da ke zuwa ga Annabi bãbu ɓata a cikinsa dõmin Jibrilu mai kãwo shi ga Annabi, Malã'ika ne mai ƙarfi ƙwarai, wani Shaiɗãni bã ya iya taron sa dõmin ya musanya wahayin, kuma Annabi ya san shi sõsai, kuma idan ya kãwo wahayin, sai ya sauko kusa ƙwarai da Annabi, sa'an nan shi kuma Annabi ba rikitacce ba ne, yanã cikin hankalinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa)."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?"
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Lamirin Malã'ika Jibrila ne."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "A wurin da magaryar tuƙẽwa take."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "A inda taken, nan Aljannar makoma take."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Ganinsa* bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Lamirin Malã'ika Jibrila ne."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma* daga ãyõyin Ubangijinsa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Watau dai Alƙur'ani ya zo daga Allah ta hanya mafi aminci har ya sadu da mutãne dõmin su yi aiki da abin da ke cikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Shin, kun ga Lãta da uzza?(5)<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Watau kun bar Alƙur'ani kun kõma wa surkullen da kuke haɗãwa game da gumãka su Lãta da Uzza da Manãta. Kuna cewa sũ wakĩlan Mala'ikun da kuke bautã wa ne kuma su 'ya'yan Allah mãtã ne. Sunã cetonku daga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?"
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar(6) ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).<br \/>\n____________________<br \/>\n(6) Watau Alƙur'ani wanda Mala'ika jibrĩla ya zo wa Annabi da shi. Sun bar shi sun kõma wa tatsũniyõyi da gũrace-gũrace."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?"
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure)."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 526,
            "translated_text": "Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya)."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake* kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wanda yake mutumin kirki, Allah Ya san shi. Kada ku dinga tsarkake kanku da bãkunanku dõmin neman girma, kõ dõmin neman wani abu dabam."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?"
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?"
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?"
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?"
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?"
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?"
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 527,
            "translated_text": "Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Sũnan wasu taurãri biyu ne sunã fita a bãyan taurarin Jauza'a sunã tafiya daga kudu zuwa arewa karkace. Kabĩlar Lãrabãwa ta Khuza'a na bauta musu da umurnin Abu Kabshah, ɗaya daga cikin kãkannin Annabi na wajen uwa dõmin haka ne Ƙuraishãwa ke ce wa Annabi Ibn abĩ Kabshah, wanda ya ƙãga sãbon addinĩn da ya sãɓawa na ubanninsa."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Da waɗanda aka birkice *ƙasarsu, Ya kãyar da su.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mutãnen Lũɗu da aka birkice ƙasarsu da su."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake *yin shakka?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kamar abõkin magana kõ mai karãtu."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Makusanciya* fa, tã yi kusa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Makusanciya ita ce Ƙiyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Shin, kuma daga wannan (5)lãbãri kuke mãmãki?<br \/>\n____________________<br \/>\n (5) Al'ƙur'ãni."
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?"
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Alhãli kunã mãsu wãsã?"
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 53,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "To, ku yi tawãli'u (6)ga Allah, kuma ku bauta (masa).<br \/>\n____________________<br \/>\n (6) Anã yin sujadar karatu a nan, amma bã ta a cikin sujadai na tĩlas."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Sã'a ta yi kusa, kuma wata (7)ya tsãge.<br \/>\n____________________<br \/>\n  (7) Ƙuraishãwa suka nemi Annabi ya yi addu'a dõmin wata ya tsãge wani ɓangaren nãsa ya fãɗo a ƙasã; ya yi addu'ar, watã ya tsãge, wani abu daga gare shi ya fãɗo kamar yadda suka nema."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: \"Sihiri ne mai dõgẽwa!\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 528,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, \"Wannan yini ne mai wuya!\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: \"Shi mahaukaci ne.\" Kuma aka tsãwace shi."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), \"Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?"
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Sai suka ce: \"Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "\"Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?"
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 529,
            "translated_text": "Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar* ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mutãnen Sãleh sun nemi mu'ujiza da rãƙuma, a fitar da ita daga dũtse, sai aka fitar da ita, kuma aka raba ruwan sha a tsakãninsu da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,"
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?"
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. \"To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?"
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Kõ zã su ce: \"Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?\""
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Zã a karya* tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bushãra ce ga Annabi, cewa zai yi yãƙi da Kuraishi kuma zai rinjãye su. Sa'an nan yãkin ya auku a Badar."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. \"Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 530,
            "translated_text": "Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 54,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "(Allah) Mai rahama."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Yã sanar da Alƙur'ani."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Yã halitta mutum."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Yã sanar da shi bayãni (magana)."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Rãnã da watã a kan lissãfi suke."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku *kuke ƙaryatãwa?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Asalin lamiri \"ku\" yanã nũni ne ga nau'i biyu, watau mutãne da aljannu, sai dai bãbu lamirin abu biyu kawai a cikin Hausa, sai na jama'a. Jam'i a luggar Hausa ya fara daga biyu."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 531,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "Dukkan wanda ke kanta* mai ƙãrẽwa ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yanã nufin ƙasa."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ *mãsu nauyin halitta biyu!<br \/>\n____________________<br \/>\n* Mutãne da aljannu."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 532,
            "translated_text": "zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "Mãsu rassan itãce."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari."
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni."
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu."
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "Mãsu duhun inuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni."
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 533,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta."
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi."
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 55,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Idan mai aukuwa ta auku."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Idan aka girgiza ƙasã girgizwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Kuma kun kasance nau'i uku."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Watau mazõwa dãma*. Mẽne ne mazõwa dãma?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mazõwa dãma ko mãsu albarka waɗanda zã a baiwa takardunsu a dãma. Mazõwa hagu ko mãsu shu'umci waɗanda zã a baiwa takardunsu da hagu."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "A ckin Aljannar ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Jama'a ne daga mutãnen farko.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Jama'a daga mutãnen farko, sũ ne Annabãwan farko da kaɗan daga cikin mutãnen ƙarshe, shi ne Annabi Muhammadu, sallallãhu alaihi wa sallama. Bã a shiga cikin wannan kashi da aiki sai dai da zãɓin Allah. Kuma an rufe ƙõfarsa. Bãbu sauran wani annabi wanda zai zo da wani addini sãbo a bãyan Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 534,
            "translated_text": "Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?"
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wani ruwa mai gudãna."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Bã su yankẽwa kuma bã a hana su."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wasu shimfiɗu maɗaukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Sa'an nan Muka sanya su budurwai."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Ga mazõwa dãma."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?"
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Kuma sun kasance sunã cẽwa: \"Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "\"Shin, kuma da ubanninmu na farko?\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle mutãnen farko da na ƙarshe.\""
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 535,
            "translated_text": "\"Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "\"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "\"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã).\""
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "\"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "\"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "\"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako."
        },
        {
            "ayah_number": 57,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 58,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?"
        },
        {
            "ayah_number": 59,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 60,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa* ba,<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ãyã ta 60 haɗe take da ãya ta 61 watau, bã zã Mu kãsa musanya ku da waɗansu mutãne ba su tsaya matsayinku, sa'an nan kũ kuma Mu mayar da ku wata halitta."
        },
        {
            "ayah_number": 61,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 62,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 63,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 64,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 65,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 66,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "(Kunã cẽwa) \"Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!\""
        },
        {
            "ayah_number": 67,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "\"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!\""
        },
        {
            "ayah_number": 68,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?"
        },
        {
            "ayah_number": 69,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 70,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 71,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 72,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 73,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji."
        },
        {
            "ayah_number": 74,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 75,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri."
        },
        {
            "ayah_number": 76,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 536,
            "translated_text": "Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani."
        },
        {
            "ayah_number": 77,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja."
        },
        {
            "ayah_number": 78,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "A cikin wani littafi tsararre."
        },
        {
            "ayah_number": 79,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake."
        },
        {
            "ayah_number": 80,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta."
        },
        {
            "ayah_number": 81,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 82,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?"
        },
        {
            "ayah_number": 83,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa)."
        },
        {
            "ayah_number": 84,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 85,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani."
        },
        {
            "ayah_number": 86,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 87,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Idan kun kasance mãsu gaskiya ga da'awar rashin Tãshin Ƙiyãma, to, ku yi ƙõƙarin hana mutuwa ga mutãne dõmin ku hana cikar alkawarin tayarwa a bãyan mutuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 88,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,"
        },
        {
            "ayah_number": 89,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 90,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,"
        },
        {
            "ayah_number": 91,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma."
        },
        {
            "ayah_number": 92,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,"
        },
        {
            "ayah_number": 93,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi."
        },
        {
            "ayah_number": 94,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Da ƙõnuwa da Jahĩm,"
        },
        {
            "ayah_number": 95,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 96,
            "surah_number": 56,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka tsarkake* sũnan Ubangijinka, Mai karimci.<br \/>\n____________________<br \/>\n * A cikin rukũ'i anã tasbĩhi da cewa: \"Subhãna Rabbiyal Azĩm wa Bihamdih.\" Ma'anarsa Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma game da gõde Masa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Abin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 537,
            "translated_text": "Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 538,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi, Yanã sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta, kuma Shĩ yanã tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 538,
            "translated_text": "Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma zuwa gare Shĩ (Allah) kawai ake mayar da al'amura."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 538,
            "translated_text": "Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãza."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 538,
            "translated_text": "Ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma ku ciyar daga abin da Allah Ya wakilta ku a cikinsa (na dũkiya). To, waɗannan da suka yi ĩmãni daga cikinku, kuma suka ciyar, sunã da wani sakamako mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 538,
            "translated_text": "kuma me ya same ku, bã zã ku yi ĩmãni ba da Allah, alhãli kuwa manzonSa na kiran ku dõmin ku yi ĩmãni da Ubangijinku, kuma lalle Allah Ya karɓi alkawarinku (cẽwa zã ku bauta Masa)? (Ku bauta Masa) idan kun kasance* mãsu ĩmãni.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ya nũna bin umurnin Allah da nĩsantar abin haninSa shi ne bauta, dõmin Ya ambaci ciyar da dũkiya da yin jihãdi bauta ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 538,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda ke sassaukar da ãyõyi bayyanannu ga BãwanSa, dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai tausayi ne gare ku, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 538,
            "translated_text": "Kuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafĩfĩta girman daraja* bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ya nũna cewa sahabban Annabi sũ ne suka fi kõwane Musulmi a bãyansu daraja. Kuma akwai bambancin daraja a tsakãnin Sahabban farko da na bãya."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 538,
            "translated_text": "Wãne ne wanda zai ranta wa Allah rance mai kyau dõmin Allah Ya ninka masa shi (a dũniya) kuma Yanã da wani sakamako na karimci (a Lãhira)?"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 539,
            "translated_text": "Rãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) \"Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna.\" Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 539,
            "translated_text": "Rãnar da munafikai maza da munãfikai mãtã ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmãni: \"Ku dũbẽ mu, mu yi makãmashi daga haskenku!\" A ce (musu): \"Ku kõma a bãyanku, dõmin ku nẽmo wani haske.\" Sai a danne a tsakãninsu da wani gãru yanã da wani ƙyaure, a cikinsa nan rahama take, kuma a bãyansa daga wajensa azaba take."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 539,
            "translated_text": "Sunã kiran su, \"Ashe, bã tãre muke da ku ba?\" Su ce: \"Ĩ, amma kũ, kun fitini kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku game da Allah.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 539,
            "translated_text": "\"To, a yau bã zã a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bã zã a karɓa daga waɗanda suka kãfirta ba. Makõmarku wutã ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makõmarku ɗin nan tã mũnana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 539,
            "translated_text": "Shin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ* zukãtansu su yi tawãlu'i ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wanda yayi ĩmani da Allah amma bai bi umurninSa ba, sai zũciyarsa ta ƙeƙashe,ĩmãni ya fita sa'an nan kuma ya zama fãsiƙi mai fita hanyar gaskiya. Barin ciyarwa da dukiya dõmin jihãdi yanã nũna ƙeƙashħwar zũciya daga ĩmãni, sabõda haka faɗa da zũciya dõmin tsaron ĩmãninta shi ne jihãdi mafi girma."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 539,
            "translated_text": "Ku sani cẽwa Allah Yanã rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta.* Lalle Mun bayyanamuku ãyõyi da fatan zã ku yi hankali.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mai rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta da ruwa. Yanã rãyar da zukãta sabõda tawãlu'i ga ambaton Allah da bin umuminSa. Watau tawalu'i daidai yake da ruwa wajen rãyarwa ga matattu, sai dai kõwane da tãsa hanya."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 539,
            "translated_text": "Lalle mãsu gaskatãwa maza da mãsu gaskatãwa mãtã, kuma suka ranta wa Allah rance mai kyau, anã riɓanya musu, kuma suna da wani sakamako na karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 540,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da MazanninSa waɗannan sũ ne kamãlar gaskatãwa kuma su ne mãsu shahãda awurin Ubangjinsu. sunã da sakamakonsu da haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan su ne'yan Jahĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 540,
            "translated_text": "Ku sani cẽwa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 540,
            "translated_text": "Ku yi tsẽre zuwa ga (nẽman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna fãɗinta kamar fãɗin samã da ƙasã ne, an yi tattalinta dõmin waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzanninSa. Wannan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 540,
            "translated_text": "Wata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 540,
            "translated_text": "Dõmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar alfahari da abin da Ya bã ku. Kuma Allah bã Ya son dukkan mai tãƙama, mai alfahari."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 540,
            "translated_text": "Watau, waɗanda ke yin rõwa, kuma sunã umumin mutãne da yin rõwa. Kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne kaɗai Mawadãci, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 541,
            "translated_text": "Haƙĩƙa, lalle Mun aiko ManzanninMu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe,* a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin Allah Ya san mai taimakonSa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Littafi a nan anã nufin dukkan Littattafan samã da aka bãyar a bãyan Nũhu da Ibrahĩm. Ma'auni kuma, shi ne sharĩ'ar da ke cikinsu. Baƙin ƙarfe kuwa dõmin kãyan aiki na amfãnin sana'õ'i da cũtar da ke a cikinsa na makãmai da kuma amfãnin tsaron addini da jihãdi. Littafi da ma'auni ana aiki da su wajen awon ibãdar Allah da mu'ãmalõli a tsakãnin mutãne."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 541,
            "translated_text": "Kuma haƙĩƙa, lalle, Mun aiki Nũhu da Ibrahĩm, kuma Muka sanya Annabci da Littĩfi a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai nẽman shiryuwa, kuma mãsu yawa daga cikinsu fasiƙai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 541,
            "translated_text": "Sa'an nan Muka biyar a bãyansu* da ManzanninMu; kuma Muka biyar da ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin zukãtan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbãnanci* wanda suka ƙãga, shi, ba Mu rubũta shi ba a kansu, fãce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabõda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinsu sakamakonsu kuma mãsu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Nũhu da Ibrahĩm da Annabãwan da ke bãyansu zuwa ga ĩsa ɗan Maryama.** Ruhubãnanci a Kiristanci kamar tasawwufi ne a Musulunci. Hana bidi'a yanã cikin jihãdi da tsaron addini bidi'a kuma kashe addini ne. Anã kashe bidi'a idan anã awon ayyuka da Littãfi kamar yanda ake hana zãlunci idan anã awo da sikeli kõ mũdu."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 541,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da ManzonSa* Ya bã ku rabo biyu daga rahamarSa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Manzon Allah a nan, shi ne Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Anã umarnin ma'abũta Littãfi da su bĩ shi dõmin su sãmi rabo ninki biyu. Mãsu ĩmani a nan su ne 'Ahlul Kitãbi' na ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 57,
            "page_number": 541,
            "translated_text": "Dõmin kada (5)mutãnen Littãfi su san cẽwa lalle bã su da ikon yi ga kõme na falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so (wannan jãhilci yã hana su ĩmani). Kuma Alah Mai falala ne mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n  (5) Rashin saninsu ya hana su su bi Mahammadu ga sãmun falalar Allah; rabo biyu. Ga wata fassara, an ce harafin korewa ƙãri ne, watau ma'anarsa ita ce Allah Yã bãyar da rabo biyu ga waɗanda suka yi ĩmãni da Mazonsa, dõmin mutãnen littafi su san ba zã su iya hana abin da Allah Ya nufa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 542,
            "translated_text": "Lalle Alla Ya ji maganar* wadda ke yi maka jãyayya game da mijinta, tanã kai ƙãra ga Allah, kuma Allah nã jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan ƙissa tanã nũna cewa a Majalisar Annabi kõwa na da 'yancin shiga, namiji da mace, kuma ya faɗi abin da yake so, kõ da ya sãɓãwa abin da Annabi ya gani ƙãfin wani wahayi ya sauka. Gã wannan mace sunanta Khaulatu bnt Sa'alabah ta kai ƙãrar mijinta Ausu bn Samit wanda ya yi zihãri game da ita, watau ya ce idan ya kusance ta kamar ya kwãna da uwarsa ne. Ga al'adar lãrabãwa wannan bã saki bã ne, kuma ba ya iya kwana da ita har abada. Wannan shi ne takai ƙarã wurin Annabi har ta yi mahãwar da shi a kansa. Kuma wannan ƙissa tanã nũna gaskiyar Annabi, bai yi jawãbi ba ga abin da bai sãmi wahayi ba a kansa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 542,
            "translated_text": "Waɗanda ke yin zihãri daga cikinku game da mãtansu, sũmãtan nan bã uwãyensu ba ne, bãbu uwayensu fãce waɗanda suka haife su. Lalle sũ, sunã faɗar abin ƙyãmã na magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 542,
            "translated_text": "Waɗanda ke yin zihãri game da mãtansu, sa'an nan su kõma wa abin da suka faɗa, to, akwai 'yanta wuya a gabãnin su shãfi jũna. Wannan anã yi muku wa'azi da shi. Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 542,
            "translated_text": "To, wanda bai sãmu ba, sai azumin wata biyu jẽre a gabãnin su shãfi jũna, sa'an nan wanda bai sãmi ĩkon yi ba, to, sai ciyar da miskĩnai sittin. Wannan dõmin ku yĩ ĩmãni da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddõdin Allah ne. Kuma kãfirai, sunã da azãba mai raɗadi."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 542,
            "translated_text": "Lalle waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa, an wulãkanta su kamar yadda aka wulãkantar da waɗanda ke a gabãninsu, kuma lalle Mun saukar da ãyõyi bayyanannu, kuma kãfirai nã da azãba mai wulãkantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 542,
            "translated_text": "Rãnar da Allah zai tãyar da su gabã ɗaya, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata, Allah Yã lissafa shi, alhãli kuwa sũ, sun manta da shi, kuma a kan kõme Allah Halartacce ne."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 543,
            "translated_text": "Ashe, ba ka ga cẽwa lalle Allah Yanã sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata gãnãwa* ta mutum uku bã zã ta kasance ba fãce Allah Shĩ ne na huɗu ɗinta, kuma bãbu ta mutum biyar fãce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kãsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa fãce Shĩ Yanã tãre da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata a Rãnar ¡iyãma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kõme.<br \/>\n____________________<br \/>\n * A bãyan ƙissar zihãri, ya shiga maganar mãsu gãnãwa a cikin majalisa. Kuma ya nuna cewa ba a sifanta Annabi kõ a jingina wani abu zuwa gare shi sai idan abin nan yã fito daga Allah a cikin harshen ManzonSa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 543,
            "translated_text": "Ashe, ba ka ga waɗanda aka hane su ba daga ganãwar, sa'an nan sunã kõmã wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma sunã gãnãwa game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma idan sun zo maka sai su gasihe ka da abin da Allah bai gaishe ka da shi ba, kuma sunã cẽwa a cikin zukatansu: \"Don me Allah ba Ya yi mana azãba sabõda abin da muke faɗi?\" Jahannama ita ce mai isarsu, zã su shigeta. Sabõda haka makõmarsu ta mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 543,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan za ku yi gãnãwa, to, kada ku gãna game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma ku yi gãnãwa game da alhẽri da taƙawa. Ku bi Allah da taƙawa wanda zã a tattara ku zuwa gare, shi."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 543,
            "translated_text": "Gãnãwar daga Shaiɗan take kawai dõmin ya mũnanã wa waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli kuwa bã zai iya cũtar su da kõme ba fãce da iznin Allah. Kuma sai mũminai su dogara ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 543,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan an ce muka, *\"Ku yalwatã a cikin majalisai,\" to, ku yalwatã, sai Allah Ya yalwatã muku, kuma idan an ce muku, \"Ku tãshi\" to, ku tãshi. Allah nã ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajõji mãsu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kõme.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Bãyan ƙissar hukuncin gãnãwa cikin majalisa, sai kuma hukuncin zaunãwa kõ tãshi dõmin wani ya zauna. Kuma ana fifita mãsu ilmi da zama ga wurin da ya fi dãcewa da su."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan zã ku gãnãwa da Manzon Allah, to, ku gabãtar da 'yar sadaka* a gabãnin gãnãwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sãmi (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Hukuncin tãyar da mutãne dõmin a gãna da Manzon Allah, bã ya halatta sai a kan larũra mai tsanani sabõda haka aka sanya gabãtar da sadaka, sa'an nan aka sõke shi da umurni da tsaron salla dõmin wa'azin da ke cikinta da kuma bayar da zakka."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Ashe, kun ji tsõron ku gabãtar da sadakõki a gabãnin gãnãwarku? To, idan ba ku aikata ba, kuma Allah Ya kõmo da ku zuwa ga sauƙi, sai ku tsai da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa. Kuma Allah ne Mai ƙididdigewa ga abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Ashe, baka ga waɗanda* suka jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu ba, bã su cikinku, kuma bã su a cikinsu kuma sunã rantsuwa a kan ƙarya, alhãli kuwa sunã sane?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bãyan maganar mãsu tãyar da mutãne dõmin gãnãwa a cikin majalisa, sai kuma munãfikai mãsu mu'ãmala da kãfirai, kuma su je su zauna cikin majalisar Musulmi dõmin su ɗauki rahõtonsu zuwa ga maƙiyansu."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Allah Ya yi musu tattalin azãba mai tsanani. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sabõda haka suka kange (mũminai) daga jihãdin ɗaukaka tafarkin Allah. To, sunã da azãba mai wulãkantãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Dũkiyõyinsu ba su wadãtar musu kõme ba daga Allah, haka kuma ɗiyansu. Waɗannan 'yan wutã ne. Sũ, mãsu dawwama ne a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Rãnar da Allah ke tãyar da su gabã ɗaya, sai su yi Masa rantsuwa kamar yadda suke yi muku rantsuwa (a nan dũniya) kuma sunã zaton cẽwa sũ a kan wani abu suke! To, lalle sũ, sũ ne maƙaryata."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Shaiɗan ya rinjaya a kansu, sai ya mantar da su ambaton Allah, waɗannan ƙungiyar Shaiɗan ne. To, lalle ƙungiyar Shaiɗan, sũ ne mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Lalle, waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa waɗannan sunã a cikin (mutãne) mafi ƙasƙanci."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 544,
            "translated_text": "Allah Ya rubũta cẽwa,\" Lalle zan rinjãya, Nĩ da ManzanniNa.\" Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 58,
            "page_number": 545,
            "translated_text": "Bã zã ka sãmi mutãne mãsu yin ĩmãni da Allah da RãnarLãhira sunã sõyayya da wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa ba, kõ dã sun kasance ubanninsu ne, kõ ɗiyansu kõ 'yan'uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Yã rubuta ĩmãni a cikin zukãtansu, kuma Yã ƙarfafa su da wani rũhi* daga gare Shi, kuma zai shigar da su a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To, lalle ƙungiyar Allah sũ ne mãsu babban rabo.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Waɗanda suka tsare dõkokin Allah, Allah zai ba su ƙarfin rai ga zartar da al'amuransu da kyau, kuma zai wadãta su a dũniya da Lãhira. Asalin rũhi shine rai. Anã nufin rãyuwar ĩmãni da ƙarfin halin fuskantar gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 545,
            "translated_text": "Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah, alhãli kuwa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 545,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littãfi,* daga gidãjẽnsu da kõra** ta farko. Ba ku yi zaton sunã fita ba, kuma sun tabbata cẽwa gãnuwõwinsu mãsu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya jẽ musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu, sunã rushe gidãjensu da hannãyensu da kuma hannãyen mũminai. To, ku lũra fa, ya mãsu basĩrõri.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mazõwa Littãfi a nan, sũ ne Yahũdun Madĩna, watau Banĩ Nadĩr. ** Kõrewa daga ƙasã, Annabi yã kõre su zuwa Haibara a gargaɗar farko, Umar ya kõre su daga Haibara zuwa Syria a gargaɗa ta biyu."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 545,
            "translated_text": "Kuma ba dõmin Allah Ya rubuta musu kõrar ba, dã Ya azabta su a cikin dũniya, kuma a Lãhira sunã da azãbar wutã."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 546,
            "translated_text": "Wannan dõmin lalle su, sun sãɓa wa Allah, da ManzonSa alhãli kuwa wanda ya sãɓa wa Allah, to, lalle Allah, Mai tsananin uƙũba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 546,
            "translated_text": "Abin da kuka sãre na dabĩniya, kõ kuka bar ta tsaye a kan asallanta, to da iznin Allah ne, kuma dõmin Ya wulãkanta fasiƙai,"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 546,
            "translated_text": "Kuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganĩma ga ManzonSa, daga gare su, to, ba ku yi hari a kansa da dawãki ko rãƙuma ba amma Allah ne Ya rinjãyar da ManzanninSa a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 546,
            "translated_text": "Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga ManzonSa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na ManzonSa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya* (matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ɗan hanya, shĩ ne matafiyin da guzuri ya ƙãre masa, yanã neman taimakon da zai mayar da shi garinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 546,
            "translated_text": "(Ku yi mãmãki) Ga matalauta mãsu hijira waɗanda aka fitar daga gidãjẽnsu da dũkiyõyinsu, sunã nẽman falala daga Allah da kuma yarda, kuma sunã taimakon Allah da ManzonSa! Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 546,
            "translated_text": "Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a gabãnin zuwansu,* sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Muhãjirĩna sun yi hijira zuwa Madĩna daga Makka kõ waɗansu wurãre. Ansar, su ne mutãnen Madĩna. Waɗannan sũ ne ya kamãta a yi mãmãkin yadda suka taimaki addini a lõkacin tsanani. Muhãjirina sun bar gidãjensu da dũyarsu sun yi hijira, Ansarai sun raba dũkiyarsu da gidãjensu da iyãlansu sun bai wa Muhãjirĩna dõmin taimakon addĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 547,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cẽwa, \"Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 547,
            "translated_text": "Ashe, ba ka ga waɗanda suka yi munãfinci*ba, sunã cẽwa ga 'yan'uwansu, waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littafi, \"Lalle idan an fitar da ku, lalle zã mu fita tãre da ku, kuma bã zã mu yi ɗã'a ga kõwa ba game da ku, har abada, kuma lalle idan an yãƙe ku, lalle zã mu taimake ku haƙĩƙatan?\" Alhãli kuwa Allah na shaidar cẽwa lalle sũ tabbas, maƙaryata ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Bãyan ya nũna yadda Allah ke taimakon mai binsa da taƙawa. Kuma yanã nũna yadda Yake tãɓar da mai binSa da munãfinci."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 547,
            "translated_text": "Lalle idan an fitar da su, bã zã su fita tãre da su ba kuma lalle idan an yãƙe su bã zã su taimake su ba, kuma lalle idan sun taimake su lalle ne, haƙĩƙatan, zã su jũyar da bãyansu dõmin gudu, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 547,
            "translated_text": "Lalle kũ ne kuka fi bãyar da firgita a cikin zukãtansu bisa ga Allah, wannan kuwa dõmin sũ lalle waɗansu irin mutãne ne da bã su gãnẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 547,
            "translated_text": "Bã su iya yãƙar ku gabã ɗaya, fãce a cikin garũruwa mãsu gãnuwa da gãruna, kõ kuma daga bãyan katangu. Yãkinsu a tsãkaninsu mai tsanani ne, kanã zaton su a haɗe, alhãli kuwa zukãtansu dabam- dabam suke. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle wasu irin mutane ne da bã su hankalta."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 547,
            "translated_text": "Kamar misãlin waɗanda* ke a gabãninsu, bã da daɗẽwa ba, sun ɗanɗani kũɗar al'amarinsu, kuma sunã da wata azãba mai raRaɗi.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kuraishãwa da aka kashe a Badar."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 547,
            "translated_text": "Kamar misãlin Shaiɗan a lõkacin da yake cẽ wa mutum, \"Ka kãfirta,\" To, a lõkacin da ya kãfirta ɗin, ya ce (masa): \"Lalle bãbu ruwãna da kai. Lalle ni inã tsõron Allah Ubangijin halitta!\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 548,
            "translated_text": "Sai ãƙibarsu ta kasance cẽwa su biyun duka sunã a cikin wutã, sunã mãsu dawwama a cikinta. \"Kuma wannan shĩ ne sakamakon mãsu zãlunci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 548,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dũbi abin da ya gabãtar dõmin gõbe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Daga wannan ãyã ta l8 zuwa ƙarshen sũra, yanã bayãnin hãsalin darasin sũrar ne dunƙule, da kuma ambatar muhimman abũbuwan da ta ƙunsa dõmin wa'azi da farkarwa ga mai hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 548,
            "translated_text": "Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka manta Allah shi kuma Ya mantar da su rãyu, kansu. Waɗannan sũ ne fãsiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 548,
            "translated_text": "'Yan Wutã da 'yan Aljanna bã su daidaita. 'Yan Aljanna, sũ ne mãsu babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 548,
            "translated_text": "Dã Mun saukar da wannan Alƙur'ani a kan dũtse, dã lalle kã ga dũtsen yanã mai tawãli'u, mai tsattsãgẽwa sabõda tsõron Allah, kuma waɗancan misãlai Munã bayyana su ne ga mutãne, da fatan za su yi tunãni."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 548,
            "translated_text": "(Wanda Ya saukar da Alƙur'ani) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 548,
            "translated_text": "Shĩ ne Allah, wanda bãbu abin bautãwa fãce shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai Tsarẽwa, Mabuwãyi, Mai t஛astãwa Mai nuna isa, tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 59,
            "page_number": 548,
            "translated_text": "Shĩ ne Allah, Mai halitta, Mai ginãwa, Mai sũrantãwa. Yanã da sũnãye mãsu kyau, abin da ke a cikin sammai da ƙasa sunã tsarkake Shi, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 549,
            "translated_text": "Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩNa kuma maƙiyinku masõyi,. Kuna jẽfa sõyayya* zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku (daga gidãjenku) dõmin kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wani Sahãbin Annabi da ake cewa Hãtibu bn Abi Balta'a, ya rubũta takarda zuwa ga Ƙuraishãwa yanã sanar da su cewa Annabi na zuwa garinsu da yãƙi, sai Allah Ya sanar da Annabi tun manzonsa bai isa ba ga Ƙuraishãwa, sai aka mayar da takardar. Da aka tambayi Hãtibu dalĩlin yin ta,sai ya ce dõmin yanã da ɗiya da dũkiya ne a can, dõmin haka ya so ya gaya musu zuwan Annabi kõ da yake yanã da cikakken ĩmãmin cewa Annabi gaskiya ne, kuma zai rinjãye su duk yadda aka yi. Sai Annabi ya karɓi uzurinsa, ba a yi masa kõme ba, sai dai abin da Allah Ya hana; kada Musulmi su sãke wata ma'amala da kãfirai a ɓõye, ko a bayyane sabõda dalĩlan da aka faɗa a cikin sũrar."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 549,
            "translated_text": "Idan sun kãma ku, zã su kasance maƙiya a gare ku, kuma su shimfiɗa hannuwansu da harsunan gũrin ku kãfirta."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 549,
            "translated_text": "Zumuntarku bã zã ta amfãne ku ba, haka kuma ɗiyanku, a Rãnar Kiyãma. (Allah) zai* rarrabe tsakãninku, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Ga wata ƙirã'ã zã a fassara wurin da cewa: za a rarrabe tsakãninku;."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 549,
            "translated_text": "Lalle abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibrãhĩm da waɗanda ke tãre da shi a lõkacin da suka ce wa mutnensu, \"Lalle mũ bãbu ruwanmu daku, kuma da abin da kuke bautãwa, baicin Allah, mun fita batunku, kuma ƙiyayya da jiyẽwa jũna sun bayyana a tsakãninmu, sai kun yi ĩmãni da Allah Shi kaɗai.\" Fãce maganar Ibrãhĩm ga ubansa (da yace), \"Lalle za ni nẽma maka gãfara kuma ban mallaki kõme ba daga Allah sabõda kai.\" \"Yã Ubangijinmu! A gare Ka muka dõgara, kuma gare Ka muka mayar da al' amuranmu, kuma zuwa gare Ka makõma take.\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 549,
            "translated_text": "\"Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu fitina ga waɗanda suka kãfirta, kuma Ka yi gãfara gare Mu. Ya Ubangijinmu! Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima!"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 550,
            "translated_text": "Lalle, haƙĩƙa, abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku daga cikinsu, ga wanda ya kasance yanã fãtan (rahamar) Allah da Rãnar Lãhira, kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne wadãtacce, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 550,
            "translated_text": "Anã tsammãnin Allah Ya sanya, a tsakãninku da tsakãnin waɗanda kuka yi ƙiyayya da su, wata sõyaya daga gare su, kuma Allah Mai ĩkon yi ne, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 550,
            "translated_text": "Allah bã Ya hana ku, daga waɗanda ba su yãƙe ku ba sabõda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidãjenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu ãdalci. Lalle Allah Yanã son mãsu ãdalci."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 550,
            "translated_text": "Allah Yanã hana ku kawai daga waɗanda suka yãke ku sabõda addini kuma suka fitar da ku daga gidãjenku, kuma suka taimaki jũna ga fitar da ku, karku jiɓince su, kuma wanda ya jiɓince su, to waɗannan sũ ne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 550,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan mãtã mũminai suka zo muku, sunã mãsu hijira, to, ku jarraba su. Allah Shĩ ne mafi sani ga ĩmãninsu. To, idan kun san sũ mũminai ne, kada ku mayar da su zuwa ga kãfirai. Sũ mãtan bã su halatta ga aurensu, sũ kuma kãfiran bã su halatta ga auren mãtan. Ku bã su abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma bãbu laifi a kanku ga ku aure su idan kun bã su sadãkõkinsu. Kuma kada ku riƙe auren mãtã kãfirai, kuma ku tambayi abin da kuka ɓatar daga dũkiya, su kuma kãfirai su tambayi abin da suka ɓatar na dũkiya. Wannan hukuncin Allah ne Yanã hukunci a tsakãninku. kuma Allah, Masani ne, Mai hikima"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 550,
            "translated_text": "Kuma idan wani abu ya kuɓuce muku daga mãtanku zuwa ga kãfirai sa'an nan kuma kuka ɗauki fansa, to, sai ku bai wa waɗanda matansu suka tafi kwatankwacin abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma ku yi biyayya da taƙawa ga Allah wanda kuke mãsu ĩmãni da Shi, Shi Kaɗai."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 551,
            "translated_text": "Yã kai Annabi! Idan mãtã mũminai suka zo maka sunã yi maka mubãya'a a kan bã zã su yi shirki da Allah ba ga kõme, kuma bã su yin sãtã, kuma bã su yin zina, kuma bã su kashe,* ya'yansu, kuma bã su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirãwa** a tsãkanin hannuwansu da ƙafãfunsu kuma bã su sãɓa maka ga wani abu da aka sani na sharĩ'a, to, ka karɓi mubãya'arsu, kuma ka nẽmi Allah Ya gãfarta musu. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * A zãmanin jãhiliyya sun kashe 'ya'yansu mãtã ta hanya uku, ɗaya sabõda bãkance na addini, na biyu sabõda tsõron talauci; sunã turbuɗe 'ya'ya mãtã a bãyan sun shekara shida, na uku sabõda kunyar haihuwar mace, sai uwa ta yi rãmi, idan ta haifi namiji ta bar shi, idan kuma ta haifi mace, sai ta tũra ta a cikin rãmin ta turbuɗe.** Sunã tsintar yãro su mayar da shi ɗansu, haka kuma maza na yin tabanni, watau mutum ya mai da ɗan wani nãsa kamar yadda har yanzu kãfirai nã yin sa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 60,
            "page_number": 551,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku jiɓinci waɗansu mutãne* da Allah Ya yi hushi a kansu. Lalle sun yanke tsammãni daga (rahamar) Lãhira, kamar yadda kãfirai suka yanke tsammãni daga mazõwa** kaburbura.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Allah Ya yi Fushi ga duk wanda ya sani kuma ya ƙi aiki da saninsa kamar Yahũdãwa da miyãgun Mãlamai. ** Kãfirai ba su yarda da Tãshin Ƙiyãma ba, sabõda haka suke yanke ƙauna daga wanda ya mutu."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 551,
            "translated_text": "Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah alhãli kuwa, Shi ne Mabuwayi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 551,
            "translated_text": "Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Don me kuke faɗin abin dã ba ku aikatãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 551,
            "translated_text": "Ya girma ga zama abin ƙyãma awurin Allah, ku faɗi abin da bã ku aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 551,
            "translated_text": "Lalle Allah Yanã son waɗanda ke yin yãƙi dõmin ɗaukaka KalmarSa, a cikin safu kamar sũ gini ne mai ɗamfarar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 551,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa mutãnensa: \"Yã mutãnena! sabõda me kuke cũtar da ni, alhãli kuwa lalle kun sani cẽwa lalle nĩ Manzon Alah ne zuwa gare ku?\" To, a lõkacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukãtansu. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fasiƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 552,
            "translated_text": "Kuma a lõkacin da Ĩsã ɗan Maryayama ya ce: \"Yã BanĩIsrã'ĩla! Lalle nĩ Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bãyar da bushãra da wani Manzo da ke zuwa a bãyãna, SũnasaAhmad (Mashãyabo).\" To, a lõkacin da ya jẽ musu da hujjõji, suka ce: \"Wannan sihiri ne, bayyananne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 552,
            "translated_text": "Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya Jingina ta ga Allah, alhãli kuwa shĩ, anã kiran sa zuwa ga Musulunci? Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 552,
            "translated_text": "Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunansu alhãli kuwa Allah Mai kammala haskenSa ne, kuma kõ da kãfirai sun ƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 552,
            "translated_text": "Shi ne wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addĩnin gakiya, dõmin Ya ɗaukaka shi a kan wani addĩni dukansa kuma kõ dã mushirikai sun ƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 552,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Shin, in nũna muku wani fatauci wanda zai tsarshe ku daga wata azãba mai raɗaɗi?"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 552,
            "translated_text": "Ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku yi jihãdi ga ɗaukaka kalmar Allah game da dũkiyõyinku da rãyukanku. Wannan shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna da sani."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 552,
            "translated_text": "Sai Allah Ya gãfarta muku zunubbanku, kuma Ya shigar da ku gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, da waɗansu ɗãkuna mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar zama. Wannan shĩ ne babban rabo, mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 552,
            "translated_text": "Da wata (falala) da yake kunã son ta; taimako daga Allah da cin nasara wanda yake kusa. Kuma ka yi bushãra ga mũminai."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 61,
            "page_number": 552,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Ku kasance mataimakan Allah kamar abin da Ĩsã ɗanMaryama ya ce ga Hawãriyãwa, \"Waɗanne ne mataimakãna zuwa ga (aikin) Allah?\" Sai wata ƙungiya daga Banĩ Isrã'ĩla ta yi ĩmãni, kuma wata ƙungiya ta kãfirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi ĩmãni a kan maƙiyansu, sabõda haka suka wãyi gari marinjãya."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 553,
            "translated_text": "Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasã sunã tasbĩhi ga Allah, Mamallaki, Mai tsarki' Mabuwãyi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 553,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu,* wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Lãrabawa sũ ne mabiya al'ãdu, watau ummiyyũn daga ummu, watau uwa watau kamar yadda uwãye suka haife su dõmin bã su da wani littãfi da suke bi sai al'ãdunsu da hukunce-hukuncen shaihunansu."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 553,
            "translated_text": "Da waɗansu mutãne* daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Su ne Ajamãwan da zã su musulunta su bi Annabi tsira da aminicin Allah su tabbata a gare shi. Kõ kuwa duk wanda ya musulunta a bãyan sahabban Annabi. Wannan yanã nunã falalar sahabbai a kan waɗansunsu."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 553,
            "translated_text": "Waccan wata falalar Allah ce Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne Ma'abũcin dukan falala mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 553,
            "translated_text": "Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen* nan da suka ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Tir da wanda ya yi siffa da irin siffõfin Yahũdu daga Musulmi wajen ɗaukar karãtun Alƙur'ãni amma kuma bai yi aiki da shi ba. Yahaya bn Yamãni ya ce: \"Sunã rubuta nadĩsi bã su fahimtarsa, kuma bã su kula da ma' anarsa.\" Watau sunã wahala wajen ɗaukar ilmin da aka ɗõra musu ɗaukarsa amma kuma bã su yin amfãni da shi a wajen aikinsu da mu'ãmalõlinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 553,
            "translated_text": "Ka ce: \"Yã kũ waɗandasuka tũba (Yahũdu)! Idan kun riya cẽwa kũ ne zãɓaɓɓun Allah bã sauran mutanẽ ba, sai ku yi gũrin mutuwa* idan kun kasance mãsu gaskiya.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ba a sãduwa da Allah sai a bãyan mutuwa. Masõyi nã bũrin sãduwa da masõyinsa, kuma bã zai yi gudun sababin sãduwar ba."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 553,
            "translated_text": "Kuma bã zã su yi gũrinta ba har abadã sabõda abin da hannãyen su suka gabãtar. Kuma Allah ne masani ga azzãlumai"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 553,
            "translated_text": "Ka ce \"Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta, to, lalle ita mai haɗuwa da ku ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 554,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar* ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ba a hana Musulmi aiki ba a kõwace rãna, sai dai an hana duk wanda Jumu'a ta lazimta a kansa da ya yi wani aiki wanda bã na tattalin salla ba a rãnar Jumma'a, a bãyan kiran salla. Anã nufi da kiran salla na biyu a bãyan limãmi ya zauna a kan mumbarinsa, dõmin wannan kiran aka sani azãmanin Annabi da Abubakar da Umar. Amma kira na farko, Usman bn Affãn ne ya fãra shi dõmin farkar da mutãne, a bãyan sun yi yawa kuma sun kama sana'õ'i. Kuma a bãyan an ƙãre salla, sai a wãtse zuwa ga ayyuka da neman abinci. Bã a tsayãwa yin wata nãfila a bãyan sallar Jumu'a, sai dai an so yin raka'a biyu a bãyan fita daga masallãci kamar yadda Annabi ke yi. A farko, anã yin huɗubar sallar Jumma'a a bãyan salla har a lõkacin da ãyarin Dihyatul Kalbi ya kõmo daga shãm (Syria) da abinci,ya sauka a Baƙĩ'a, suka buga ganga, sai Sahabbai suka fita dõmin neman sayen abincin a gabãnin a ƙãre huɗubar suka bar mutum gõma shã biyu tãre da Annabi. Sai aka mayar da huɗubar a gabãnin salla. Kuma an fahimci cewa anã yin huɗuba a tsaye. Kuma ba a kafa Jumu'a, sai a kafaffen gari, amma Jumu'a nã ƙulluwa da mutum gõma sha biyu da lĩman."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 554,
            "translated_text": "Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 62,
            "page_number": 554,
            "translated_text": "Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: \"Abin da yake a wurin Allah ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrinmãsu arzũtãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 554,
            "translated_text": "Idan munãfukai* suka jẽ maka suka ce: \"Munẽ shaidar lalle kai haƙĩƙa Manzon Allah ne,\" Kuma Allah Yanã sane da lalle Kai, haƙĩƙa ManzonSa ne, kuma Allah Yanã shaida lalle munafukan haƙĩƙa, maƙaryata ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Munãfuki, a zãmanin Annabi, shine wanda ya bayyana Musulunci, amma kuma a ɓõye Shĩ kãfiri ne. A bãyan Annabi anã cewa munãfuki zindĩƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 554,
            "translated_text": "Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sai suka taushe daga tafarkin Allah. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 554,
            "translated_text": "Wancan, dõmin lalle sũ, sun yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sai aka yunƙe a kan zukãtansu. Sabõda sũ, bã su fahimta."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 554,
            "translated_text": "Kuma idan kã gan su, sai jikunansu su bã ka sha'awa kuma idan sun faɗa,* zã ka saurãra ga maganarsu. Kamar dai sũ ƙyami ne wanda aka jingine. Sunã zaton kõwace tsãwa a kansu take. Sũ ne maƙiyan, sai ka yi saunarsu. Allah Yã la'ane su. Yãya ake karkatar da su?<br \/>\n____________________<br \/>\n * Munãfukai sunã da kyawun sũrar jiki kuma sun iya magana da fasaha amma fa bã su da hankali sabõda ƙaryar da suke a kanta, sabõda haka sunã tsõron kõwane irin mõtsi ya zama a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 555,
            "translated_text": "Kuma idan aka ce musu \"Ku zo Manzon Allah ya nẽma maku gãfara,\" Sai su gyãɗa kãwunansu, kuma ka gan su sunã kangẽwa, alhãli kuwa sunã mãsu girman kai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 555,
            "translated_text": "Daidai ne a kansu, kã nẽma musu gãfara kõ ba ka nẽmamusu ba. faufau Allah bã zai gãfarta musu ba. Lalle Allah, bã zai shiryar da mutãne fãsiƙai ba."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 555,
            "translated_text": "Sũ ne waɗanda ke cẽwa \"Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su wãtse,\" alhali kuwa taskõkin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munãfukai bã su fahimta."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 555,
            "translated_text": "Sunã cẽwa \"Lalle ne idan mun kõma* zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Abdullah bn Ubayyi bn Salũl ya faɗi cewa \"Wallahi idan mun kõma Madĩna wanda ya fi ƙarfi, lalle zai fitar da wanda ya fi ƙasƙanci.\" Yanã nufin Ansãrai mutãnen Madĩna zã su kõri Muhãjirai. Yã faɗi haka a cikin wata tafiya ta jihãdi. Aka gaya wa Annabi, sai ya yi musu. Allah Ya kunyata shi."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 555,
            "translated_text": "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada dũkiyõyinku da ɗiyanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma wanda ya yi haka, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 555,
            "translated_text": "Kuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gãbanin mutuwa ta je wa ɗayanku har ya ce: \"Yã Ubangijina! Don me ba Ka yi mini jinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci dõmin in gaskata kuma in kasance daga sãlihai?\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 63,
            "page_number": 555,
            "translated_text": "Kuma Allah bã zai jinkirta wa wani rai ba idan ajalinsa ya je. Kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 556,
            "translated_text": "Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah. Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon yi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 556,
            "translated_text": "Shĩ ne wanda Ya halitta ku. Sa'an nan daga gare ku akwai kãfiri kuma daga gare ku akwai mũmini. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 556,
            "translated_text": "Ya halitta sammai da ƙasã da abin da yake hakkinSa. Kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku. Kuma zuwa gare Shi makõma take."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 556,
            "translated_text": "Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasã. Kuma Yanã sanin abin da kuke bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 556,
            "translated_text": "Shin, babban lãbãri bai je muku ba na waɗanda suka kãfirta daga gabãni, sai suka ɗanɗani uƙũbar al'amarinsu kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi?"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 556,
            "translated_text": "Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji bayyanannu, sai suka ce: \"Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?\" Sai suka kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah wadãtacce ne, Gõdadde."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 556,
            "translated_text": "Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: \"Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 556,
            "translated_text": "Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai labartawa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 556,
            "translated_text": "A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 557,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ayõyinMu, waɗannan sũne'yan wuta, sunã madawwama a cikinta. Kuma tir da makõma, ita."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 557,
            "translated_text": "Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 557,
            "translated_text": "Kuma ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo. Sa'an nan idan kun jũya bãya, to, abin sani kawai, akwai iyarwa bayyananna a kan ManzonMu."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 557,
            "translated_text": "Allah bãbu wani abin bauta wa fãce Shi. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 557,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi* a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Maƙiyi, shĩ ne mai hana mutumin da yake ƙiyayya da shi wani alheri ya sadu da shi. Idan son dũkiya kõ mãta kõ ɗiya ya hana mutum yin sadaka kõ fita zuwa jihãdji, to dũkiyar da mãtan da ɗiyan sun zama maƙiyansa ke nan."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 557,
            "translated_text": "Dũkiyõyinku da ɗiyanku fitina* ɗai ne. Kuma Allah, a wurinSa akwai wani sakamako mai girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Fitina, ita ce duk abin da zai cũci mutum ta hanyar da yake amincewa, cũtar ta dũniya ce kõ ta Lãhira. Cũtar Lãhira ta fi tsanani sabõda girman hasãrar da ke a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 557,
            "translated_text": "Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 557,
            "translated_text": "Idan kun bai wa Allah rance, rance mai kyau, (Allah) zai ninka shi a gare ku kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai yawan gõdiya ne, Mai haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 64,
            "page_number": 557,
            "translated_text": "Shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwayi, Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 558,
            "translated_text": "Ya kai Annabi! Idan kun saki mãtã, sai ku sake su ga iddarsu,* kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãshã bayyananna. Kuma waɗancan iyakõkin Allah ne. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Ba ka sani ba ɗammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bãyan haka.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Saki, shĩ ne warware ƙullin halaccin sãduwa da jũna a tsakãnin miji da mãta. Haƙƙi ne wanda Allah Ya saka ga hannayen maza ban da mãtã. saki ga idda, watau ya sake ta saki gudã a cikin tsarkin dabai shãfe ta ba dõmin sauƙin idda. Yanã haramta ga mijin da mãtar ya fitar da ita kõ ta fita daga ɗãkinta a lõkacin idda. fãruwar wani al'amari shi ne sõyayya a bãyan ƙiyayya da mayarwa a bãyan saki. Alfãsha a nan, tanã nufin faɗa da zãge-zãge a kan surukantã. Anã fitar da mai iddar saki sabõda alfãsha daga gidanta.Akwai saki na sunna kuma akwai na bidi'a, amma saki na sunna ɗaya ne, a cikin tsarkin da bã a shãfe ta ba kuma kada a ƙãra mata wani saki har ta ƙãre idda, sakin bidi'a kuwa shĩne uku gabã ɗaya kõ a cikin idda gudã, a cikin haila kõ jinin bĩƙi. Sakin bidi'a yanã 1azimta, Anã tĩlastã shi mayarwa ga wadda aka saki a cikin haila idan bai kai uku ba ga miji 'yantacce, kõ biyu ga miji bãwã."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 558,
            "translated_text": "Sa'an nan idan sun isa ga ajalinsu (na idda) sai ku riƙe su da abin da aka sani kõ ku rabu da su da abin da aka sani kuma ku shaidar da mãsu adalci biyu daga gare ku. Kuma ku tsayar da shaidar dõmin Allah. Wancan ɗinku anã yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance yanã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 558,
            "translated_text": "Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 558,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka yanke* ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Muddar idda ga wadda ta yanke ɗammãnin haila, sabõda tsũfa, watanni uku,kuma bã zã ta ƙãra kõme ba a kai. Wadda take akwai shakka a game da ita ga kõ akwai ciki kõ bãbu shi, to, zã ta yi iddar wattani uku kuma ta yi jiran watanni tara, watau ta yi watannin shekara, uku na idda, saurãn na fidda shakkãne. Haka ne hukuncin mai istihãla, watau jinin ciwo. Amma yãrinya mai shakkar ciki, sai ta zauna har shakka ta gushe. Yarinyar da ba ta fãra haila ba tana iddar wata uku. Bãbu bambanci a tsakãnin ɗiya da baiwa ga idda da watanni, amma ga idda ta tsarki, to, baiwã tana yin rabin na ɗiya ga saki da mutuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 558,
            "translated_text": "Wancan umurnin Allah ne, Ya saukar da shi zuwa gare ku. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sãkamako."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 559,
            "translated_text": "Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar* daga gwargwadon sãmunku. Kuma kada ku cũce su dõmin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abũta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shãyar da mãma sabõda ku, sai ku bã su tsãdõdinsu. Kuma ku yi shãwara a tsakãninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nũna talauci to wata mace zã ta shãyar da mãma sabõda shi (mijin).<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mijin zai fita ya bar wa mãtar da ya saki ɗaki ta zauna a ɗakinta har ta ƙãre idda. Anã ciyar da mai sakin kõme, amma bã a ciyar da mai sakin bã'ini sai idan tanã da ciki. Ijãrar shãyarwa tanã akan uba ga uwar da aka saki saki bã'ini kõ ga watarta, bisa ga yardar sassan biyu."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 559,
            "translated_text": "Sai mawadãci ya ciyar daga wadãtarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya bã shi. Allah bã Ya kallafa wa wani rai fãce abin da Ya bã shi. Allah zai sanya sauƙi a bãyan tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 559,
            "translated_text": "Kuma da yawa* daga alƙarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umurnin Ubangijinta da ManzanninSa, sai Muka yi mata hisãbi, hisãbi mai tsanani, kuma Muka, azabtar da ita azãba abar ƙyãma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * A bãyan da ya gama bayãnin saki da hukunce-hukuncen da suka rãtayu a gare shi, sai kuma ya gõya gargaɗi ga wanda bai bi waɗannan hukunce-hukuncen ba, ta hanyar tsoratar da shi da cewa Allah Ya halaka alƙaryu mãsu yawa sabõda sãɓã Masa ga hukunce-hukuncenSa ga ƙanãnan abũbuwa, balle mutum guda wanda ya sãɓã masa ga babban al'amari kamar aure da saki waɗanda rãyuwar ɗan Adam ta dõgara a kansu kuma ya yi bushãra ga wanda ya bĩ shi da taƙawa, ya fita daga duhun al'ãdu zuwa ga hasken sharĩ'arSa, kuma Ya yi wa'adi da bã shi sauƙin rãyuwa daga wadãtarSa mai yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 559,
            "translated_text": "Sa'an nan ta ɗanɗana masĩfar al'amarinta. kuma ƙarshen al'amarinta ya kasance hasãra,"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 559,
            "translated_text": "Allah Ya yi musu tattalin wata azãba mai tsanani. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abũta hankula, waɗanda suka yi ĩmãni! Haƙĩƙa Allah Ya saukar da wata tunãtarwa zuwa gare ku."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 559,
            "translated_text": "Manzo, yanã karãtun ãyõyin Allah bayyananu a kanku dõmin Ya fitar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidãjen Aljanna ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashnsu sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada. Haƙĩƙa Allah Yã kyautata* masa arziki.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Allah Yã kyautata wa wanda ya tsare sharĩ'arsa da kyau, awajen arzikinsa tun daga dũniya har ya zuwa Lãhira, dõmin Yã ce: \"Haƙĩƙa Allah Yã kyautatã masa (mai tsare sharĩ'ar) arziki,\" bã da Yã yi ƙaidin lõkaci kõ wuri ba."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 65,
            "page_number": 559,
            "translated_text": "Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma daga ƙasã kwatankwacinsu, umuruinSa yanã ta sauka a tsakaninsu dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõme, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõme da sani."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 560,
            "translated_text": "Yã kai Annabi! Don me kake haramta abin da Allah Ya halatta maka,* kanã nẽman yardar mãtanka, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.<br \/>\n____________________<br \/>\n * A cikin littãfin Buhãri an ruwaito daga A'isha, mãtar Annabi, cewa Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gareshi, yakan yi jinkiri a wajen Zainab bint Jahsh dõmin ya shã zuma a wurinta. Ta ce: \"Sai na shirya, nĩ da Hafsah: Duk wadda Manzon Allah ya shiga gurinta daga garemu, ta ce masa, 'Ina jin wãrin tsimi daga gareka! Kã ci tsimi! To, sai Annabi ya shiga ga ɗayansu, ta ce masa: \"Kã ci tsimi.\" Ya ce: \"A'isha! Nã shã zuma dai a wurin Zainab bint Jahsh, kuma ba zan kõma gareshi ba.\" Asalin abin, Annabi tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi,yã kasance yanã zagayãwa a gidãjen mãtansa a bãyan sallar la'asar dõmin ya gaishe su. To, sai ya sh ga ga Hafsah bãyan ya shiga ga Zainab, ta gaya masa haka. Kuma ya gaya mata nĩsantarsa ga zuma, kuma ya gaya mata lãbãrin cewa Abubakar da Umar, Allah Ya yarda da su, za su zama halĩfai a bãyansa. To, sai ta faɗi waɗannan lãbãru ga maƙwabciyarta A'isha. Wannan Ƙissa tana koyar da sauƙin halin Annabi a game da iyãlansa, da girmamawarsa a gare su."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 560,
            "translated_text": "Haƙĩƙa Allah ya faralta muku warware* rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * An rubũta yadda ake warware rantsuwa da kaffãra wadda aka ambata a cikin sũra ta5, ãyã ta 89. Anã kaffãrar rantsuwa da ciyar da miskĩnai gõma daga matsakaicin abinci, mũdu biyu ga kõwane, kõ tufãtar da su tufar da za ta ishe su salla, idan bai sãmu ba, ya yi azumin kwãna uku."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 560,
            "translated_text": "Kuma a sã'ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: \"Wãne ne ya gaya maka wannan?\" Ya ce: \"Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini.\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 560,
            "translated_text": "Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle Allah Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da sãlihan mũminai. Kuma malã'iku a bãyan wancan, mataimaka ne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 560,
            "translated_text": "Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya musanya masa waɗansu mãtan aure mafiya alhẽri daga gare ku, Musulmai mũminai mãsu tawãli'u, mãsu tũba, mãsu ibãda, mãsu, azumi, zawarõri da 'yammãta."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 560,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku* (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umunin su.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tsare kai da iyãli daga wuta yanã sãmuwa da shiryar da su da karãtu da nasiha a kan addini. Wannan yanã a cikin kyawun zamantakewa wanda sũrar ke karantarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 560,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka kãfirta!* Kada ku kãwo wani uzuri a yau. Anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa kawai ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kãfirai a nan, kafircinsu sabõda ƙin bin umurnin Allah game da kyawun zamantakewa da iyali yake. Laifinsu yã fi sauran laifuffuka dõmin yanã sabbaba yãmutsi a gida, har abin ya shãfi zurriya da ƙasã gabã ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 561,
            "translated_text": "Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi *da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, \"Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Allah Yã yi alkawarin bã zai kunyatar da AnnabinSa ba, haka kuma waɗanda sukayi ĩmãni tãre da shi, watau sahabbansa a Rãnar Kiyãma. Wannan shĩ ne dalĩlin da ya sa Allah Ya tsare Annabi da Sahabbansa daga bauta musu kamar yadda aka bautã wa waɗansu Annabãwa da Sãlihai waɗanda Allah zai tambaye su kõ sũ ne suka yi umurni da a yi musu bautar, sũ kuma su faɗi barrantarsu daga waɗanda suka bauta musu."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 561,
            "translated_text": "Yã kai Annabi! Ka yãki kãfirai da munãfwkai. Kuma ka tsananta a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce, kuma tir da makoma, ita."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 561,
            "translated_text": "Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka kãfirta*: mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu, sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyi biyu daga bãyinMu sãlihai, saisuka yaudare su, sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: \"Ku shiga, kũ biyu, wutã tãre da mãsu shiga.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Waɗannan misãlai biyu,mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu sunã nũna kusanci ga sãlihai bã ya isa ga addini sai kõwa ya yi abin da Allah Ya yi umurni da shi. Kuma anã kallafa wa mãtã da su kiyãye kyawun zamantakewa da mazansu. Kuma anã yi musu azãba sabõda sãɓa wa Allah ga barin haka kamar yadda ake ga mazansu."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 561,
            "translated_text": "Kuma Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka yi ĩmãni; matar Fir'auna,* sa'ad da ta ce \"Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurinKa a cikin Aljanna. Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutãnen nan azzãlumai.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wannan yanã nũna cewa kusantar kãfiri bã zai cũci mũminai ba. Sai dai Allah Yã hana aure a tsakãnin Musulma da kãfiri."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 66,
            "page_number": 561,
            "translated_text": "Da Maryama* ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da LittattafanSa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli'u.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wannan yanã nũna cewa rashin aure ga mãtar da ke iya tsare farjinta daga alfãsha kuma ta tsare addininta da taƙawa, bã zai cũce ta ba ga sãmun rahamar Allah a dũniya da lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "(Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannunSa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka?"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Sa'an nan ka sake maimaita, dũbãwa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa'ĩr."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga zamanta makõmarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Idan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Tana kusa ta tsãge domin hushi, ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama'a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, \"Wani mai gargaɗi bai je muku ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Sai su ce: \"I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce, 'Allah bai saukar da kome ba, bã ku cikin kõme sai ɓata babba.'\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Kuma suka ce: \"Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a cikin 'yan sa'ĩr ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Wato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ĩr!"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 562,
            "translated_text": "Lalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gãfara da wani sakamako mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa?"
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Shin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama, bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza?"
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Kõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba? To, zã ku san yadda (ãƙibar) gargaɗiNa take."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yãya (ãƙibar) gargaɗiNa ta kasance?"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Wãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã (Allah) ba, Mai rahama? Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Wãne ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikinSa? A'aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tãshin hankali."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya?"
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Ka ce: \"(Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da tunãni, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku!\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Kuma kace \"Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gareShi ne ake tãshin ku.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Kuma sunã cewa, \"Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu gaskiya ne kũ?\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 563,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana (gargaɗin).\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "To, lokacin da suka gan ta (azãbar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka mũnana, kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Ka ce musu \"Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi mana rahama, to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi?\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 67,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe, to, wãne ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga?\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ana so idan mai karatu ya kai ƙarshen wannan sũra ya ce: الله رب العالمين wato Allah Ubagijin halitta. An karanta wannan ãya a gaban wani kãfiri, sai ya ce zã mu fito da ruwan game da amfãni da dundurũsai da farħtani, sai ruwan idãnunsa ya faƙe."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Ga wanenku haukã take."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Mai zunɗe, mai yãwo da gulma."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri)."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: \"Tatsũniyõyin mutãnen farko ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 564,
            "translated_text": "Zã Mu yi masa alãma a kan hanci."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa)."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "\"Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: \"Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "\"Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Mafificinsu (hankali) ya ce: \"Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Suka ce: \"Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Suka ce: \"Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "\"Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Haka dai azãbar* take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Irin wannan azãba ce za a yi wa Ƙuraishãwa, dangin Annabi, kamar yadda aka yi wa mãsu gonar lambu, wãto da suka tũba aka musanya musu da abin da ya fi abin da suka sãba sãmu. Wato an gayã wa Annabi ne lõkacin da danginsa suka kangare, suka ƙi shiga Musulunci, aka yi musu azãbar fari, da rashin ruwa shekara bakwai, Allah Ya gaya masa cewa, zã su musulunta, alheri ya kõma musu. Ya kuwa kõma, kamar yadda Allah Ya yi alkawari"
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?"
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?"
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?"
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?"
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 565,
            "translated_text": "Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi)."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?"
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, \"Lalle ne shi mahaukaci ne!\""
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 68,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Kiran gaskiya!"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Mẽne ne kiran gaskiya?"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!"
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 566,
            "translated_text": "To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?"
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani)."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi)."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "A ran nan, mai aukuwa zã ta auku."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), \"Ku karɓa, ku karanta littafina.\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "A cikin Aljanna maɗaukakiya."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),"
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "(Ana ce musu) \"Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: \"Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!"
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!\""
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"Ĩkona ya ɓace mini!\""
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "(Sai a ce wa malã'iku) \"Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!\""
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!\""
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 567,
            "translated_text": "\"Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "\"Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn.\""
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "\"Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,"
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Da abin da bã ku iya gani."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Dã Mun kãma shi da dãma."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã."
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 69,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Daga Allah Mai matãkala."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 568,
            "translated_text": "Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Da matarsa da ɗan'uwansa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Da danginsa, mãsu tattarã shi."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Mai twãle fãtar goshi."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Sai mãsu yin salla,"
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne"
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu)."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!"
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?"
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 569,
            "translated_text": "Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita)."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 70,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)"
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "Ya ce: \"Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "\"Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "\"Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci).\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "Nũhu) ya ce: \"Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini.\""
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "\"To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni).\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "\"Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane.\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "\"Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 570,
            "translated_text": "\"Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga.\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna.\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya.\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "Nũhu ya ce: \"Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "Kuma Nũhu ya ce: \"Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 71,
            "page_number": 571,
            "translated_text": "\"Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "Ka ce: \"An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui'ãni), mai ban mãmãki.\""
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah.\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah.\""
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai.\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye.\""
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam.\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 572,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Kuma dã sun tsayu* sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Tsayuwa sosai wato su bautawa Allah kamar yadda Allah Ya umarce su, su yi Masa ɗa'a saboda Yã wadãta su."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu).\""
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah* ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Bawan Allah shi ne duk wani mai wa'azi yana kira zuwa ga Allah. Bã ya halatta a gare shi ya bar waɗanda yake yi wa wa'azi su kai fagen bauta Masa shi kansa. Sai ya gaya musu gaskiyar matsayinsa, kamar yadda Allah Ya faɗa wa AnnabinSa, kuma Ya umarce shi da ya gaya wa waɗanda yake yi wa wa'azi."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "Ka ce: \"lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri.\""
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "Ka ce: \"Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada.\""
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya maSa dõgon ajali!\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinSa ga kowa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya* gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * ldan Allah Yã aiko wani manzonsa da wani umurni ko hani zuwa ga mutãne to zai sanya mala'iku gaba gare shi da bãya gare shi suna gãdin sa dõmin kada wani Shaiɗãni ya kusance shi har ya sanya shi mantuwa ko kuskure, har ya iyar da manzancin nan kamar yadda yake."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 72,
            "page_number": 573,
            "translated_text": "\"Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Yã wanda ya lulluɓe!"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Lalle ne, a wurinMu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo* mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo** zuwaga Fir'auna,<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Wato Annabi Muhammad, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi.** Wato Annabi Mũsã, aminci ya tabbata a gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 574,
            "translated_text": "Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 73,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,"
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya"
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Da ɗiyã halartattu,"
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 575,
            "translated_text": "Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Sa'an nan, ya yi tunãni"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa,"
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Sai ya ce: \"Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "\"Wannan maganar mutum dai ce.\""
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Zã Ni ƙõna shi da Saƙar."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar!"
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna)."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "A kanta akwai (matsara) gõma shã tara."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: \"Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?\" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "A'aha! Ina rantsuwa da watã."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Da sãfiya idan ta wãye."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Mai gargaɗĩ ce ga mutum."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Fãce mutãnen dãma."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "A cikin Aljanna suna tambayar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Game da mãsu laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "(Su ce musu) \"Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?\""
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "Suka ce: \"Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "\"Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "\"Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "\"Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 576,
            "translated_text": "\"Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana.\""
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba."
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne."
        },
        {
            "ayah_number": 51,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Sun gudu daga zãki."
        },
        {
            "ayah_number": 52,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa"
        },
        {
            "ayah_number": 53,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 54,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce."
        },
        {
            "ayah_number": 55,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Dõmin wanda ya so, ya tuna."
        },
        {
            "ayah_number": 56,
            "surah_number": 74,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Bã sai Nã yi rantsuwa* da Rãnar ¡iyãma ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wasu na fassarawa: lna rantsuwa da Rãnar Ƙiyama. A ganina, da tabbatar da rantsuwar da kuma kore ta duka ɗaya ne, maƙasũdi dai jan hankalin mai karãtu ga abin da yake a ciki, na hikimar Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin* kansa ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kowane rai na zargin kansa idan bai yi aikin alheri ba, ko kuma bai yi fiye da wanda ya yi ba, ko kuma bai aikata wanda ya fi kyãwo ba a lokacin aikinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Yanã tambaya: \"Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?\""
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli)."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe)."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Aka tãra rãnã da watã"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Mutum zai ce a rãn nan \"Ina wurin gudu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "A'aha! bãbu mafaka."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba)."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Kada ka mõtsar* da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).<br \/>\n____________________<br \/>\n * Dangantakar wannan ãya da ta sama da ita, ita ce bambancin Annabi mai gaggawar karɓar umurnin Allah da ƙyamar kãfiri ga karɓarsa, da bayãnin sauƙaƙewar Allah ga mai bin umurninSa."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 577,
            "translated_text": "sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira)."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "kuma aka ce: \"Wãne ne mai tawada?\""
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa* take.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ranar kora mutane, kamar ana gargaɗa tumãki, zuwa ga tsayuwa a gaba ga Allah, dõmin hisabi."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!"
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!"
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?"
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)"
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;"
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?"
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 75,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ana son mai karãtu a nan ya ce: a ɓoye بلى وأنا على ذلك من الشاهدين."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 578,
            "translated_text": "Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "(Suna cẽwa): \"Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "\"Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki,"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Sunã mãsu zaman ginciri,* a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Kishingiɗa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki)."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "(A ce musu) \"Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 579,
            "translated_text": "Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 76,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "sa'an nan, da ãyõyi* mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Yã kamanta Manzanin Allah masu kãwo ayõyinsa da iskõki mãsu kãwo ruwa dõmin rahamar da ke cikin kowannensu."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "To, idan taurãri aka shãfe haskensu."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Kuma, idan sama aka tsãge ta."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Kuma, idan duwãtsu aka nike su."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Domin rãnar rarrabẽwa.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Yin hukunci a tsakanin tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?"
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 580,
            "translated_text": "Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Ga rãyayyu da matattu,"
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?"
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!"
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari."
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "(A ce musu) \"Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa.\""
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "(Ana ce musu) \"Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 47,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 48,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Kuma, idan an ce musu: \"Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 49,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 50,
            "surah_number": 77,
            "page_number": 581,
            "translated_text": "To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni"
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "A kan mẽ suke tambayar jũna?"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "A'aha! Zã su sani."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, a'aha! Zã su sani."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?"
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?"
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?"
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?"
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?"
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Sakamako mai dãcẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 582,
            "translated_text": "Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Lambuna da inabõbi."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Da yan Mata tsaraikun Juna"
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Da hinjãlan giya cikakku."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 78,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: \"Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Sunã cẽwa \"Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "\"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?\""
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Suka ce: \"Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!\""
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "To, ita kam, tsãwa guda kawai ce."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Sai kawai gã su a bãyan ƙasa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 583,
            "translated_text": "A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?"
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "\"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "\"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?\""
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Sai ya nũna masa ãyar* nan mafi girma.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ãyar Mũsã da ta fi girma ita ce sandarsa mai zama maciji ko hannunsa mai haske kamar tõcila idan yã sanya cikin hammata yã fitar."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Sai ya ce: \"Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka.\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Da duwatsu, Yã kafe ta."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "To, amma wanda ya yi girman kai."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya)."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "To, lalle ne Aljanna ita ce makõma."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?"
        },
        {
            "ayah_number": 43,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Me ya haɗã ka da ambatonta?"
        },
        {
            "ayah_number": 44,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake."
        },
        {
            "ayah_number": 45,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta."
        },
        {
            "ayah_number": 46,
            "surah_number": 79,
            "page_number": 584,
            "translated_text": "Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Yã game huska* kuma ya jũya bãya.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wani makãho, Abdullahi bin Ummi Maktũm ya je wurin Annabi dõmin ya musulunta, sai ya iske a lõkacin nan Annabi na ƙõƙarin shiryar da wasu manyan mutãne na Ƙuraishãwa, sai wannan makãhon ya yanke maganar Annabi da su, bã da saninsa ba, alhãli Annabi na bũrin su musulunta dõmin darajarsu ga idon mutãnensu. Saboda haka Annabi, (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ya ɓata Fuska, ya tafi dõmin ɓacin ransa, saboda rashin musuluntarsu. Bãyan haka Annabi nã girmama Abdullahi ƙwarai, idan ya je wurinsa sai ya ce masa \"Maraba da wanda Ubangijina Ya zarge ni sabõda shi.\" Kuma ya shimfiɗa masa mayafinsa, idan ya fita tafiya, yakan sanya shi riƙon garin Madina, ƙissar tana nũna girmamawar Allah ga Annabi da Ya ce: \"Ya game Fuska.\" Bai ce masa: \"Domin ka game Fuska\" ba, sai ya faɗa a cikin hali mai sauƙi.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Sabõda makãho yã je masa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Amma wanda ya wadãtu da dũkiya."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Kai kuma kã shagala ga barinsa!"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah)."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,"
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "A cikin hannãyen mala'iku marubũta."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!"
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye)."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari)."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Da inabi da ciyãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Da zaitũni da itãcen dabĩno."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Da lambuna, mãsu yawan itãce."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku."
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Da uwarsa da ubansa."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Da mãtarsa da ɗiyansa."
        },
        {
            "ayah_number": 37,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi."
        },
        {
            "ayah_number": 38,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne."
        },
        {
            "ayah_number": 39,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra."
        },
        {
            "ayah_number": 40,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 585,
            "translated_text": "Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 41,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Baƙi zai rufe su."
        },
        {
            "ayah_number": 42,
            "surah_number": 80,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu)."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Idan rãna aka shafe haskenta"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani)."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Rãƙuma mãsu ciki ɗan wata gõma."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan rãyuka aka haɗa* su da jikunkunansu.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ko kuma, aka haɗa kõwane mutum da irin mutãnensa a Aljanna ko a wuta."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta.<br \/>\n____________________<br \/>\n * A cikin zãmanin jahiliyya Lãrabãwa bã su son a haifa musu 'ya'ya mãta dõmin haka har sukan turbuɗe 'ya'yansu dõmin kada su yi abin kunya ko kuma su talauce wajen yi musu aure."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "\"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?\""
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su)."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan sama aka fẽɗe ta."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan Jahĩm aka hũra ta"
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan)."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã* ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Masu tafiya suna kõmawa bãya."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Mãsu gudu suna ɓũya."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Da dare idan ya bãyar da bãya."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Da sãfiya idan ta yi lumfashi."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, yã gan shi(5) a cikin sararin sama mabayyani.<br \/>\n____________________<br \/>\n  (5) Annabi ya ga Mala'ika Jibirilu ya san shi. Sabõda haka wani aljani bã zai yi kama da shi ba balle ya kãwo masa ƙarya."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma shi, ga gaibi(6) bã mai rowa ba ne.<br \/>\n____________________<br \/>\n   (6) Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cewa daga Allah yake, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Shin, a inã zã ku tafi?"
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 81,
            "page_number": 586,
            "translated_text": "Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Idan sama ta tsãge."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Kuma idan taurãri suka wãtse."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Kuma idan tẽkuna aka facce su."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Kuma idan kaburbura aka tõne su."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!"
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Mãsu daraja, marubũta."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Sunã sanin abin da kuke aikatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Bã zã su faku daga gare ta ba."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?"
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 82,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikẽli, suna ragẽwa<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mũdu."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 587,
            "translated_text": "Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Domin yini mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?"
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Wani ittãfi ne rubũtacce."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Sa'an nan a ce: \"Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi.\""
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?"
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Wani littãfi ne rubũtacce."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Muƙarrabai* suke halarta shi.<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Malã'iku masu daraja."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "A kan karagu, suna ta kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake."
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe."
        },
        {
            "ayah_number": 31,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci."
        },
        {
            "ayah_number": 32,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Kuma idan sun gan su sai su ce: \"Lalle waɗannan ɓatattu ne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 33,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 588,
            "translated_text": "Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 34,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya."
        },
        {
            "ayah_number": 35,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "A kan karagu, suna ta kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 36,
            "surah_number": 83,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Amsar tambaya \"na'am.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Idan sama ta kẽce,"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "To, zã shi dinga kiran halaka!"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Kuma ya shiga sa'ĩr."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Lale ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Da dare, da abin da ya ƙunsa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Da watã idan (haskensa) ya cika."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?"
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?"
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 589,
            "translated_text": "Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 84,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,*<br \/>\n____________________<br \/>\n   * Rãnar Ƙiyãma."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta* a cikinsa<br \/>\n____________________<br \/>\n * Rãnar Arafa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "An la'ani mutãnen rãmi.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mutãnen Najiran ne suka yi rãmi suka hũra wuta a ciki, dõmin su ƙõne wanda yã yi ĩmãni da addinin Masĩh Ĩsa dõmin su hana yãɗuwarsa. Suka umurci kõwane Musulmi ya jefa kansa a ciki, su kuma suna zazzaune suna kallo."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Wato wuta wadda aka hura."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa)."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Mai Al'arshi mai girma"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Fir'auna da samũdãwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa)."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 85,
            "page_number": 590,
            "translated_text": "A cikin Allo tsararre."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wannan ya yi kama da zuwan Annabi a cikin jahiliyya don ya haskaka duniya da ilimi kamar yadda girgije ke ba da ruwa saboda tsiron ƙasa, hantsar uwa ta ba da nono saboda jariri kuma maniyi ya zo lokacin Jima'i."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Rãnar da ake jarrabawar asirai."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah)."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Dõmin fitar tsiro."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Mai rabewa tsakanin ƙarya da gaskiya."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Kuma shĩ bã bananci* bane<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kãkãci."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 86,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri)."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 591,
            "translated_text": "Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Wanda zai shiga wutar da tã fi girma."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Kuma ya ambaci sũnan(5) Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.<br \/>\n____________________<br \/>\n  (5) Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Lalle ne, wannan* yanã a cikin littafan farko.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 87,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Zã su shiga wata wuta mai zãfi."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Game da aikinsu, masu yarda ne."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "A cikinta akwai marmaro mai gudãna."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "A cikinta akwai gadãje maɗaukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Da kõfuna ar'aje."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Da filõli* jẽre,<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Matãsan kai."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Da katifu shimfiɗe."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?"
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?"
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?"
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 592,
            "translated_text": "Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta."
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma."
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 88,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da alfijiri."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Da darũruwa gõma."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Da (adadi na) cikã da (na) mãrã."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Da dare idan yana shũɗewa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Iramawa mãsu sakon* ƙĩrar jiki.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Tsawo mai ma'ana."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya)."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi* suka yi gidãje)?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Wãdil-ƙura, sunan wuri ne kusa da Madina wajen Syria, wato Sham."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Da Fir'auna mai turãku."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: \"Ubangijina Ya girmama ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: \"Ubangijina Ya walãkanta ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!"
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!"
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai."
        },
        {
            "ayah_number": 22,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 593,
            "translated_text": "Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu."
        },
        {
            "ayah_number": 23,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!"
        },
        {
            "ayah_number": 24,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Yana dinga cẽwa, \"Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!\""
        },
        {
            "ayah_number": 25,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah."
        },
        {
            "ayah_number": 26,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa."
        },
        {
            "ayah_number": 27,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Yã kai rai mai natsuwa!"
        },
        {
            "ayah_number": 28,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira)."
        },
        {
            "ayah_number": 29,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya)."
        },
        {
            "ayah_number": 30,
            "surah_number": 89,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira)."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari* ba.<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Allah Ya ce ba sai Ya yi rantsuwa da Makka ba, sa'an nan zã a san darajarta a lõkacinda Annabi yake a cikinta, kuma shi yana da haƙƙin zama a cikinta mahaifansa da zurriyarsa duka, ko da yake zai yi hijira sabõda fitinar kãfirai mãsu halaka dũkiyarsu kan adãwa da shi. Dã sun yi amfãni da dukiyar ga ayyukan alheri, dã yã fi musu."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Da mahaifi da abin da ya haifa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Yana cẽwa \"Na* halakarda dũkiya mai yawa,\"<br \/>\n____________________<br \/>\n * Nã halaka dukiya mai yawa dõmin faɗã da addĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Da harshe, da leɓɓa biyu."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi* biyu ba?<br \/>\n____________________<br \/>\n* Hanyar alheri da ta sharri."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?"
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Ita ce fansar wuyan bãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Ga marãya ma'abũcin zumunta."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 594,
            "translated_text": "Waɗannan ne ma'abũta albarka*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da dãma, a Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci(5)<br \/>\n____________________<br \/>\n  (5) Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da hagu, a Lãhira."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 90,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "A kansu akwai wata wuta abar kullewa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Kuma da wata idan ya bi ta."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Da yini a lõkacin da ya bayyana ta."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Da sama da abin da ya gina ta."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Da rai da abin da ya daidaita shi."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Lalle ne wanda ya tsarkake* shi (rai) ya sãmi babban rabo.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Karɓar imãni da aiki da abinda ya ƙunsa tsarkake rai ne."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe* shi (da laifi) ya tãɓe.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Kãfirci turbuɗe rai ne da zunubi."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu)."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: \"Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!\""
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi)."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 91,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar)."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Da abin da ya halitta namiji da mace."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Kuma ya gaskata kalma* mai kyãwo.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Kalma mai kyãwo ita ce Kalmar shahãda da abin da ta ƙunsa na addinin Musulunci, wanda yake yinsa kamar yadda Allah Ya ce, ta hanyan ManzonSa, shi ne taƙawa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 595,
            "translated_text": "Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta)."
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya."
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne."
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka."
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa"
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma mafi taƙawa* zai nisance ta.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Mafi taƙawa da Mafi shaƙãwa suna ma'anar mai taƙawa da shaƙiyyi."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta."
        },
        {
            "ayah_number": 20,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka."
        },
        {
            "ayah_number": 21,
            "surah_number": 92,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi)."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da hantsi."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa)."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma lalle ta ƙarshe* ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ta ƙarshe, wãto, Lãhira; kuma ta farko, wato, dũniya."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?"
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 93,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya)."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 94,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 94,
            "page_number": 596,
            "translated_text": "Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 94,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Wanda ya nauyayi bãyanka?"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 94,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?"
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 94,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 94,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 94,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah)."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 94,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 95,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 95,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Da Dũr Sĩnĩna.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 95,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Da wannan gari* amintacce.<br \/>\n____________________<br \/>\n * Gari amintacce shi ne Makkah."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 95,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 95,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 95,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 95,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?"
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 95,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?*<br \/>\n____________________<br \/>\n * Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce بلى ,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Ya hahitta mutum daga gudan jini."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Ya sanar da mutum abin da bai sani ba."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu)."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Dõmin yã ga kansa, yã wadãta."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Shin, kã ga wanda ke hana."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Bãwã idan yã yi salla?"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?"
        },
        {
            "ayah_number": 12,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 597,
            "translated_text": "Ko ya yi umurni da taƙawa?"
        },
        {
            "ayah_number": 13,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?"
        },
        {
            "ayah_number": 14,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?"
        },
        {
            "ayah_number": 15,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa."
        },
        {
            "ayah_number": 16,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi."
        },
        {
            "ayah_number": 17,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Sai ya kirayi ƙungiyarsa."
        },
        {
            "ayah_number": 18,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma)."
        },
        {
            "ayah_number": 19,
            "surah_number": 96,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).<br \/>\n____________________<br \/>\n * Wato salla da sauran ibãdu."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 97,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 97,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari?"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 97,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 97,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 97,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 98,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 98,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Wani Manzo* daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki.<br \/>\n____________________<br \/>\n* Shi ne Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, dõmin bãbu wanda ya dãce da abin da ke cikin littafansu sai shi."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 98,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 98,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 98,
            "page_number": 598,
            "translated_text": "Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 98,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 98,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 98,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 99,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 99,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 99,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Kuma mutum ya ce \"Mẽ neya same ta?\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 99,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 99,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 99,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 99,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 99,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Sai su motsar da ƙũra game da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 599,
            "translated_text": "Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Aka bayyana abin da ke cikin zukata."
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 100,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?"
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?"
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi)."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "To, uwarsa Hãwiya ce."
        },
        {
            "ayah_number": 10,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?"
        },
        {
            "ayah_number": 11,
            "surah_number": 101,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Wata wuta ce mai kuna."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 102,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku)."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 102,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Har kuka ziyarci kaburbura."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 102,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "A'aha! (Nan gaba) zã ku sani."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 102,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Sa'an nan, tabbas, zã ku sani."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 102,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 102,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Lalle ne da kuna ganin Jahĩm."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 102,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 102,
            "page_number": 600,
            "translated_text": "Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku)."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 103,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Ina rantsuwa da zãmani.*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Wasu suna fassarawa da lokacin sallar La'asar da kuma marece. A kõwane dai, an bai wa lokaci muhimmanci, zãmani yana yanke wanda bai yanke shi ba. ba ya halatta ga mutum wata mudda ta zãmani ta wuce shi bai san amfãnin da ya sãma wa kansa a cikinta ba, kuma kõme ya sãmu idan ba addini ba ne, to, hasãrace."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 103,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Lalle ne mutum yana a cikin hasara."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 103,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara)."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 104,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa)."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 104,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 104,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 104,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 104,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?"
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 104,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Wutar Allah ce wadda ake hurawa."
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 104,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Wadda take lẽƙãwa a kan zukata."
        },
        {
            "ayah_number": 8,
            "surah_number": 104,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu."
        },
        {
            "ayah_number": 9,
            "surah_number": 104,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 105,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa* ba?<br \/>\n____________________<br \/>\n  * An yi Yãƙin Gĩwa shekarar haihuwar Annabi tsakãnin halaka su da haihuwarsa kwãna hamsin. Bayan shekara arba'in Annabi ya fara karantar da mutane. Ya karantar da su cikin shekara ashirin da uku, sa'an nan ya ƙaura. Bayansa da shekara hamsin waanda suka bi shi suka cinye duniya. Wannan yana nuna cewa mutane ba su samun daraja sai da riƙon addini da ilimi."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 105,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?"
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 105,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 105,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 105,
            "page_number": 601,
            "translated_text": "Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?"
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 106,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Sabõda sãbon ¡uraishawa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 106,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Sãbonsu na tafiyar hunturu da ta bazara."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 106,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka'abah)."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 106,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 107,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?"
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 107,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "To, wannan shi ne ke tunkue marãya (daga haƙƙinsa)."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 107,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 107,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "To, bone yã tabbata ga masallata."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 107,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 107,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu)"
        },
        {
            "ayah_number": 7,
            "surah_number": 107,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Kuma suna hana taimako."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 108,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Lalle ne Mu, Mun yi maka kyauta mai yawa."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 108,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke (baiko, wato sukar raƙumi)."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 108,
            "page_number": 602,
            "translated_text": "Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 109,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "Ka ce: \"Ya kũ kãfirai!\""
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 109,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "\"Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 109,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "\"Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 109,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "\"Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 109,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "\"Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake* bautã wa ba.\"<br \/>\n____________________<br \/>\n* Ãya ta 4 da ta 5 sun nũna addinin ƙarya yakan canza amma na gaskiya bã ya canzawa."
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 109,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "\"Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 110,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 110,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, ƙungiya-ƙungiya."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 110,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "To, ka yi tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 111,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka."
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 111,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra."
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 111,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "Zã ya shiga wuta mai hũruwa."
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 111,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta).*<br \/>\n____________________<br \/>\n  * Anã fassara shi da mai tsegumi, wãtau annamĩmanci; da Lãrabci anã ce wã mai annamĩmanci \"mai ɗaukar itacen wuta.\"."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 111,
            "page_number": 603,
            "translated_text": "A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma)."
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 112,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "Ka ce: \"Shi ne Allah Makaɗaĩci.\""
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 112,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Allah wanda ake nufin Sa da buƙata.\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 112,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba.\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 112,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi"
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 113,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "Ka ce \"ina neman tsari ga Ubangijin safiya\""
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 113,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Daga sharrin abin da Ya halitta.\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 113,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Da sharrin dare, idan ya yi duhu.\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 113,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri\""
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 113,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada.\""
        },
        {
            "ayah_number": 1,
            "surah_number": 114,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "Ka ce \"Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 2,
            "surah_number": 114,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Mamallakin mutane.\""
        },
        {
            "ayah_number": 3,
            "surah_number": 114,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Abin bautãwar mutãne.\""
        },
        {
            "ayah_number": 4,
            "surah_number": 114,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa.\"*<br \/>\n____________________<br \/>\n* Shaiɗan yakan ɓõye idan ya ji an ambaci sunan Allah, dõmin haka aka yi masa suna mai ɓõyewa, wãto bã ya zuwa wurin da ake karatu da wa'azi, kamar yadda bã ya zama cikin zũciyar mutum mai ibãda da gaskiya. Ibãda ta gaskiya ita ce wadda aka yi ta kamar yadda Allah Ya ce a yi ta. Banda ibãdar bidi'a, ba ta korar Shaiɗan. Kuma da sharaɗin a yi ibãdar da kyakkyawar niyya, dõmin aikin da bãbu niyya mai kyãwu game da shi ɓãtacce ne."
        },
        {
            "ayah_number": 5,
            "surah_number": 114,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane.\""
        },
        {
            "ayah_number": 6,
            "surah_number": 114,
            "page_number": 604,
            "translated_text": "\"Daga aljannu da mutane.\""
        }
    ]
}