أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰ
Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.
وَأَن لَّيۡسَ لِلۡإِنسَٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ
Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.
وَأَنَّ سَعۡيَهُۥ سَوۡفَ يُرَىٰ
Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi.
ثُمَّ يُجۡزَىٰهُ ٱلۡجَزَآءَ ٱلۡأَوۡفَىٰ
Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?
وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلۡمُنتَهَىٰ
Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضۡحَكَ وَأَبۡكَىٰ
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحۡيَا
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.
وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰ
Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
مِن نُّطۡفَةٍ إِذَا تُمۡنَىٰ
Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.