يَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذٍ أَيۡنَ ٱلۡمَفَرُّ
Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"
كَلَّا لَا وَزَرَ
A'aha! bãbu mafaka.
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمُسۡتَقَرُّ
zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
يُنَبَّؤُاْ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذِۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ
Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
بَلِ ٱلۡإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ بَصِيرَةٞ
Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
وَلَوۡ أَلۡقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ
Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ
Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ
Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ
To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.