وَكَذَٰلِكَ نُوَلِّي بَعۡضَ ٱلظَّـٰلِمِينَ بَعۡضَۢا بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Kuma kamar wancan ne Muke jiɓintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa.
يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَقُصُّونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِي وَيُنذِرُونَكُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَاۚ قَالُواْ شَهِدۡنَا عَلَىٰٓ أَنفُسِنَاۖ وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَشَهِدُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ كَٰفِرِينَ
Yã jama'ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jẽ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini nãku? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kãwunanmu." Kuma rãyuwar dũniya tã rũɗẽ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cẽwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai.
ذَٰلِكَ أَن لَّمۡ يَكُن رَّبُّكَ مُهۡلِكَ ٱلۡقُرَىٰ بِظُلۡمٖ وَأَهۡلُهَا غَٰفِلُونَ
Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai.
وَلِكُلّٖ دَرَجَٰتٞ مِّمَّا عَمِلُواْۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَٰفِلٍ عَمَّا يَعۡمَلُونَ
Kuma ga kõwanne, akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa.