وَلَوۡ شِئۡنَا لَرَفَعۡنَٰهُ بِهَا وَلَٰكِنَّهُۥٓ أَخۡلَدَ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُۚ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ ٱلۡكَلۡبِ إِن تَحۡمِلۡ عَلَيۡهِ يَلۡهَثۡ أَوۡ تَتۡرُكۡهُ يَلۡهَثۚ ذَّـٰلِكَ مَثَلُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَاۚ فَٱقۡصُصِ ٱلۡقَصَصَ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ
Kuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni.
سَآءَ مَثَلًا ٱلۡقَوۡمُ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَأَنفُسَهُمۡ كَانُواْ يَظۡلِمُونَ
Tir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta.
مَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِيۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
وَلَقَدۡ ذَرَأۡنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ لَهُمۡ قُلُوبٞ لَّا يَفۡقَهُونَ بِهَا وَلَهُمۡ أَعۡيُنٞ لَّا يُبۡصِرُونَ بِهَا وَلَهُمۡ ءَاذَانٞ لَّا يَسۡمَعُونَ بِهَآۚ أُوْلَـٰٓئِكَ كَٱلۡأَنۡعَٰمِ بَلۡ هُمۡ أَضَلُّۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡغَٰفِلُونَ
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu.