وَإِن يُرِيدُوٓاْ أَن يَخۡدَعُوكَ فَإِنَّ حَسۡبَكَ ٱللَّهُۚ هُوَ ٱلَّذِيٓ أَيَّدَكَ بِنَصۡرِهِۦ وَبِٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma idan sun yi nufin su yaudare ka, to, lalle ma'ishinka Allah ne, Shĩ ne wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa, kuma da mũminai.


وَأَلَّفَ بَيۡنَ قُلُوبِهِمۡۚ لَوۡ أَنفَقۡتَ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا مَّآ أَلَّفۡتَ بَيۡنَ قُلُوبِهِمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ أَلَّفَ بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّهُۥ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yake cikin ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba, kuma amma Allah Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.


يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ حَسۡبُكَ ٱللَّهُ وَمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Ya kai Annabi! Ma'ishinka Allah ne, kai da wanda ya biye maka daga mũminai.


يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ حَرِّضِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ عَلَى ٱلۡقِتَالِۚ إِن يَكُن مِّنكُمۡ عِشۡرُونَ صَٰبِرُونَ يَغۡلِبُواْ مِاْئَتَيۡنِۚ وَإِن يَكُن مِّنكُم مِّاْئَةٞ يَغۡلِبُوٓاْ أَلۡفٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَفۡقَهُونَ

Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da mũminai a kan yãƙi. Idan mutum ashirin mãsu haƙuri sun kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan kuma idan ɗari suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu daga waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ, mutãne ne bã su fahimta.



الصفحة التالية
Icon