ٱلۡـَٰٔنَ خَفَّفَ ٱللَّهُ عَنكُمۡ وَعَلِمَ أَنَّ فِيكُمۡ ضَعۡفٗاۚ فَإِن يَكُن مِّنكُم مِّاْئَةٞ صَابِرَةٞ يَغۡلِبُواْ مِاْئَتَيۡنِۚ وَإِن يَكُن مِّنكُمۡ أَلۡفٞ يَغۡلِبُوٓاْ أَلۡفَيۡنِ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

A yanzu Allah Yã sauƙaƙe daga gare ku, kuma Yã sani cẽwa lalle ne akwai mãsu rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, mãsu haƙuri, suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.


مَا كَانَ لِنَبِيٍّ أَن يَكُونَ لَهُۥٓ أَسۡرَىٰ حَتَّىٰ يُثۡخِنَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ تُرِيدُونَ عَرَضَ ٱلدُّنۡيَا وَٱللَّهُ يُرِيدُ ٱلۡأٓخِرَةَۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Bã ya kasancewa ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.


لَّوۡلَا كِتَٰبٞ مِّنَ ٱللَّهِ سَبَقَ لَمَسَّكُمۡ فِيمَآ أَخَذۡتُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta, dã azãba mai girma daga Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma.


فَكُلُواْ مِمَّا غَنِمۡتُمۡ حَلَٰلٗا طَيِّبٗاۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sabõda haka, ku ci daga abin da kuka sãmu ganĩma, Yanã halal mai kyau. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.



الصفحة التالية
Icon