وَقَالَ يَٰبَنِيَّ لَا تَدۡخُلُواْ مِنۢ بَابٖ وَٰحِدٖ وَٱدۡخُلُواْ مِنۡ أَبۡوَٰبٖ مُّتَفَرِّقَةٖۖ وَمَآ أُغۡنِي عَنكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٍۖ إِنِ ٱلۡحُكۡمُ إِلَّا لِلَّهِۖ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُۖ وَعَلَيۡهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ

Kuma ya ce: "Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam, kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara."


وَلَمَّا دَخَلُواْ مِنۡ حَيۡثُ أَمَرَهُمۡ أَبُوهُم مَّا كَانَ يُغۡنِي عَنۡهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٍ إِلَّا حَاجَةٗ فِي نَفۡسِ يَعۡقُوبَ قَضَىٰهَاۚ وَإِنَّهُۥ لَذُو عِلۡمٖ لِّمَا عَلَّمۡنَٰهُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu, ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma'abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba.


وَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَىٰ يُوسُفَ ءَاوَىٰٓ إِلَيۡهِ أَخَاهُۖ قَالَ إِنِّيٓ أَنَا۠ أَخُوكَ فَلَا تَبۡتَئِسۡ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: "Lalle nĩ ne ɗan'uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa."



الصفحة التالية
Icon