قَالَ مَعَاذَ ٱللَّهِ أَن نَّأۡخُذَ إِلَّا مَن وَجَدۡنَا مَتَٰعَنَا عِندَهُۥٓ إِنَّآ إِذٗا لَّظَٰلِمُونَ
Ya ce: "Allah Ya tsare mu daga mu kãma wani fãce wanda muka sãmi kãyanmu a wurinsa. Lalle ne mũ, a lõkacin nan, haƙĩƙa, azzãlumai ne."
فَلَمَّا ٱسۡتَيۡـَٔسُواْ مِنۡهُ خَلَصُواْ نَجِيّٗاۖ قَالَ كَبِيرُهُمۡ أَلَمۡ تَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ أَبَاكُمۡ قَدۡ أَخَذَ عَلَيۡكُم مَّوۡثِقٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَمِن قَبۡلُ مَا فَرَّطتُمۡ فِي يُوسُفَۖ فَلَنۡ أَبۡرَحَ ٱلۡأَرۡضَ حَتَّىٰ يَأۡذَنَ لِيٓ أَبِيٓ أَوۡ يَحۡكُمَ ٱللَّهُ لِيۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلۡحَٰكِمِينَ
Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa. Babbansu ya ce: "Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta."
ٱرۡجِعُوٓاْ إِلَىٰٓ أَبِيكُمۡ فَقُولُواْ يَـٰٓأَبَانَآ إِنَّ ٱبۡنَكَ سَرَقَ وَمَا شَهِدۡنَآ إِلَّا بِمَا عَلِمۡنَا وَمَا كُنَّا لِلۡغَيۡبِ حَٰفِظِينَ
"Ku kõma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yã bãbanmu, lalle ne ɗanka yã yi sãta, kuma ba mu yi shaida ba fãce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba."