وَسۡـَٔلِ ٱلۡقَرۡيَةَ ٱلَّتِي كُنَّا فِيهَا وَٱلۡعِيرَ ٱلَّتِيٓ أَقۡبَلۡنَا فِيهَاۖ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ

"Kuma ka tambayi alƙarya wadda muka kasance a cikinta da ãyari wanda muka gabãto acikinsa, kuma lalle ne haƙĩƙa, mũ mãsu gaskiya ne."


قَالَ بَلۡ سَوَّلَتۡ لَكُمۡ أَنفُسُكُمۡ أَمۡرٗاۖ فَصَبۡرٞ جَمِيلٌۖ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَأۡتِيَنِي بِهِمۡ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ

Ya ce: "Ã'a, zukatanku sun ƙawãta wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyãwo, akwai tsammãnin Allah Ya zo mini da su gabã ɗaya (Yũsufu da 'yan'uwansa). Lalle ne Shĩ ne Masani, Mai hikima."


وَتَوَلَّىٰ عَنۡهُمۡ وَقَالَ يَـٰٓأَسَفَىٰ عَلَىٰ يُوسُفَ وَٱبۡيَضَّتۡ عَيۡنَاهُ مِنَ ٱلۡحُزۡنِ فَهُوَ كَظِيمٞ

Kuma ya jũya daga gare su, kuma ya ce: "Yã baƙin cikina a kan Yũsufu!" Kuma idãnunsa suka yi fari sabõda huznu sa'an nan yanã ta haɗẽwar haushi.


قَالُواْ تَٱللَّهِ تَفۡتَؤُاْ تَذۡكُرُ يُوسُفَ حَتَّىٰ تَكُونَ حَرَضًا أَوۡ تَكُونَ مِنَ ٱلۡهَٰلِكِينَ

Suka ce: "Tallahi! Bã zã ka gushe ba, kanã ambaton Yũsufu, har ka kasance Mai rauni ƙwarai, kõ kuwa ka kasance daga mãsu halaka."


قَالَ إِنَّمَآ أَشۡكُواْ بَثِّي وَحُزۡنِيٓ إِلَى ٱللَّهِ وَأَعۡلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

Ya ce: "Abin sani kawai, inã kai ƙarar baƙin cikĩna da sunõna zuwa ga Allah, kuma na san abin da ba ku sani ba daga Allah."



الصفحة التالية
Icon