۞رَبِّ قَدۡ ءَاتَيۡتَنِي مِنَ ٱلۡمُلۡكِ وَعَلَّمۡتَنِي مِن تَأۡوِيلِ ٱلۡأَحَادِيثِۚ فَاطِرَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ أَنتَ وَلِيِّۦ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ تَوَفَّنِي مُسۡلِمٗا وَأَلۡحِقۡنِي بِٱلصَّـٰلِحِينَ
"Yã Ubangijina lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
ذَٰلِكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡغَيۡبِ نُوحِيهِ إِلَيۡكَۖ وَمَا كُنتَ لَدَيۡهِمۡ إِذۡ أَجۡمَعُوٓاْ أَمۡرَهُمۡ وَهُمۡ يَمۡكُرُونَ
Wannan daga lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci.
وَمَآ أَكۡثَرُ ٱلنَّاسِ وَلَوۡ حَرَصۡتَ بِمُؤۡمِنِينَ
Kuma mafi yawan mutãne ba su zama mãsu ĩmãni ba, kõ da kã yi kwaɗayin haka.
وَمَا تَسۡـَٔلُهُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Kuma bã ka tambayar su wata lãdã a kansa. Shĩ bai zama ba fãce ambato dõmin halittu.
وَكَأَيِّن مِّنۡ ءَايَةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ يَمُرُّونَ عَلَيۡهَا وَهُمۡ عَنۡهَا مُعۡرِضُونَ
Kuma da yawa, wata ãyã a cikin sammai da ƙasa sunã shũɗẽwa a kanta kuma sũ, sunã bijirẽwa daga gare ta.