لِلَّذِينَ ٱسۡتَجَابُواْ لِرَبِّهِمُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱلَّذِينَ لَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُۥ لَوۡ أَنَّ لَهُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفۡتَدَوۡاْ بِهِۦٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ سُوٓءُ ٱلۡحِسَابِ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

Ga waɗanda suka karɓa wa Ubangijinsu akwai abu mafi kyau a gare su, kuma waɗanda suke ba su karɓa Masa ba, to, lalle dã sunã da abin da yake a cikin ƙasa gaba ɗaya da misãlinsa tãre da shi, haƙĩƙa, dã sun yi fansa da shi. Waɗancan sunã da mummunan bincike kuma matabbatarsu Jahannama ce, kuma tir da ita ta zama shimfida.


۞أَفَمَن يَعۡلَمُ أَنَّمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ كَمَنۡ هُوَ أَعۡمَىٰٓۚ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Shin, fa, wanda yake sanin cẽwa lalle abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya yanã zama kamar wanda yake makãho? Abin sani kawai masu hankali sũ ke yin tunãni.


ٱلَّذِينَ يُوفُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَلَا يَنقُضُونَ ٱلۡمِيثَٰقَ

Sũ ne waɗanda suke cikãwa da alkawarin Allah, kuma bã su warware alkawari.


وَٱلَّذِينَ يَصِلُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ وَيَخَافُونَ سُوٓءَ ٱلۡحِسَابِ

Kuma sũ ne waɗanda suke sãdar da abin da Allah Ya yi umurni da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã tsõron Ubangijinsu, kuma sunã tsõron mummũnan bincike.



الصفحة التالية
Icon