أَفَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي كَفَرَ بِـَٔايَٰتِنَا وَقَالَ لَأُوتَيَنَّ مَالٗا وَوَلَدًا
Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya?"
أَطَّلَعَ ٱلۡغَيۡبَ أَمِ ٱتَّخَذَ عِندَ ٱلرَّحۡمَٰنِ عَهۡدٗا
Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?
كَلَّاۚ سَنَكۡتُبُ مَا يَقُولُ وَنَمُدُّ لَهُۥ مِنَ ٱلۡعَذَابِ مَدّٗا
Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa.
وَنَرِثُهُۥ مَا يَقُولُ وَيَأۡتِينَا فَرۡدٗا
Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai.
وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةٗ لِّيَكُونُواْ لَهُمۡ عِزّٗا
Kuma suka riƙi gumãka, baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.
كَلَّاۚ سَيَكۡفُرُونَ بِعِبَادَتِهِمۡ وَيَكُونُونَ عَلَيۡهِمۡ ضِدًّا
Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu.
أَلَمۡ تَرَ أَنَّآ أَرۡسَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ تَؤُزُّهُمۡ أَزّٗا
Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa?