وَنَجَّيۡنَٰهُ وَلُوطًا إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَا لِلۡعَٰلَمِينَ

Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai.


وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ نَافِلَةٗۖ وَكُلّٗا جَعَلۡنَا صَٰلِحِينَ

Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai.


وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَئِمَّةٗ يَهۡدُونَ بِأَمۡرِنَا وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِمۡ فِعۡلَ ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَإِقَامَ ٱلصَّلَوٰةِ وَإِيتَآءَ ٱلزَّكَوٰةِۖ وَكَانُواْ لَنَا عَٰبِدِينَ

Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu.


وَلُوطًا ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗا وَنَجَّيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِي كَانَت تَّعۡمَلُ ٱلۡخَبَـٰٓئِثَۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمَ سَوۡءٖ فَٰسِقِينَ

Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai.


وَأَدۡخَلۡنَٰهُ فِي رَحۡمَتِنَآۖ إِنَّهُۥ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai.



الصفحة التالية
Icon