۞إِنَّ قَٰرُونَ كَانَ مِن قَوۡمِ مُوسَىٰ فَبَغَىٰ عَلَيۡهِمۡۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡكُنُوزِ مَآ إِنَّ مَفَاتِحَهُۥ لَتَنُوٓأُ بِٱلۡعُصۡبَةِ أُوْلِي ٱلۡقُوَّةِ إِذۡ قَالَ لَهُۥ قَوۡمُهُۥ لَا تَفۡرَحۡۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡفَرِحِينَ

Lalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa."


وَٱبۡتَغِ فِيمَآ ءَاتَىٰكَ ٱللَّهُ ٱلدَّارَ ٱلۡأٓخِرَةَۖ وَلَا تَنسَ نَصِيبَكَ مِنَ ٱلدُّنۡيَاۖ وَأَحۡسِن كَمَآ أَحۡسَنَ ٱللَّهُ إِلَيۡكَۖ وَلَا تَبۡغِ ٱلۡفَسَادَ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

"Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna."


قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمٍ عِندِيٓۚ أَوَلَمۡ يَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَهۡلَكَ مِن قَبۡلِهِۦ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مَنۡ هُوَ أَشَدُّ مِنۡهُ قُوَّةٗ وَأَكۡثَرُ جَمۡعٗاۚ وَلَا يُسۡـَٔلُ عَن ذُنُوبِهِمُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

Ya ce: "An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai." Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba?



الصفحة التالية
Icon