فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ فِي زِينَتِهِۦۖ قَالَ ٱلَّذِينَ يُرِيدُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا يَٰلَيۡتَ لَنَا مِثۡلَ مَآ أُوتِيَ قَٰرُونُ إِنَّهُۥ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٖ
Sai (¡ãrũna) ya fita a kan mutãnensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rãyuwar dũniya suka ce: "Inã dai munã da kwatancin abin da aka bai wa ¡ãrũna! Lalle shĩ haƙĩƙa ma'abũcin rabo babba ne."
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَيۡلَكُمۡ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّمَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗاۚ وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّـٰبِرُونَ
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai ha ƙuri."
فَخَسَفۡنَا بِهِۦ وَبِدَارِهِ ٱلۡأَرۡضَ فَمَا كَانَ لَهُۥ مِن فِئَةٖ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُنتَصِرِينَ
Sai Muka shãfe ƙasa da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba.
وَأَصۡبَحَ ٱلَّذِينَ تَمَنَّوۡاْ مَكَانَهُۥ بِٱلۡأَمۡسِ يَقُولُونَ وَيۡكَأَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ وَيَقۡدِرُۖ لَوۡلَآ أَن مَّنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَا لَخَسَفَ بِنَاۖ وَيۡكَأَنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Kuma waɗanda suka yi bũrin matsayinsa a jiya suka wãyi gari sunã cẽwa, "Wai! Allah Yanã shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bãyinsa, kuma Yanã ƙuntatãwa. Bã dõmin Allah Ya yi mana falala ba dã Yã shãfe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kãfirai bã su cin nasara."