وَبَدَا لَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُواْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Mũnãnan ayyuka da suka aikata, suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi, na izgili, ya wajaba a kansu.


فَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَانَا ثُمَّ إِذَا خَوَّلۡنَٰهُ نِعۡمَةٗ مِّنَّا قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمِۭۚ بَلۡ هِيَ فِتۡنَةٞ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa'an nan idan Muka canza masa ita, ya sãmi ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: "An bã ni ita ne a kan wani ilmi nãwa kawai." Ã'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba su sani ba.


قَدۡ قَالَهَا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Lalle waɗanda ke a gabãninsu, sun faɗe ta, sabõda haka abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su da kõme ba.


فَأَصَابَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُواْۚ وَٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡ هَـٰٓؤُلَآءِ سَيُصِيبُهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُواْ وَمَا هُم بِمُعۡجِزِينَ

Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma ba su zama mabuwãya ba.


أَوَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni.



الصفحة التالية
Icon