وَقَالُواْ لِجُلُودِهِمۡ لِمَ شَهِدتُّمۡ عَلَيۡنَاۖ قَالُوٓاْ أَنطَقَنَا ٱللَّهُ ٱلَّذِيٓ أَنطَقَ كُلَّ شَيۡءٖۚ وَهُوَ خَلَقَكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Kuma suka ce wa fãtunsu, "Don me kuka yi shaida a kanmu?" Suka ce: "Allah, Wanda ke sanya kõwane abu ya yi furuci, Shĩ ne Ya sanya mu mu yi furuci, kuma Shĩ ne Ya halitta ku can da farko, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku."


وَمَا كُنتُمۡ تَسۡتَتِرُونَ أَن يَشۡهَدَ عَلَيۡكُمۡ سَمۡعُكُمۡ وَلَآ أَبۡصَٰرُكُمۡ وَلَا جُلُودُكُمۡ وَلَٰكِن ظَنَنتُمۡ أَنَّ ٱللَّهَ لَا يَعۡلَمُ كَثِيرٗا مِّمَّا تَعۡمَلُونَ

"Ba ku kasance kunã sani ba a ɓõye, cẽwa jinku zai yi shaida a kanku kuma ganinku zai yi, kuma fãtunku za su yi. Kuma amma kun yi zaton cẽwã Allah bai san abũbuwa mãsu yawa daga abin da kuke aikatãwa ba."


وَذَٰلِكُمۡ ظَنُّكُمُ ٱلَّذِي ظَنَنتُم بِرَبِّكُمۡ أَرۡدَىٰكُمۡ فَأَصۡبَحۡتُم مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

"Kuma wancan zaton nãku wanda kuka yi zaton shi, game da Ubangijinku, ya halakar da ku, sai kuka wãyi gari a cikin mãsu hasãra."


فَإِن يَصۡبِرُواْ فَٱلنَّارُ مَثۡوٗى لَّهُمۡۖ وَإِن يَسۡتَعۡتِبُواْ فَمَا هُم مِّنَ ٱلۡمُعۡتَبِينَ

Sabõda haka idan sun yi hakuri, to, wutar, ita ce mazauni a gare su, kuma idan sun nẽmi yarda, to, ba su zama daga waɗanda ake yardwa ba.



الصفحة التالية
Icon