وَٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَابَهُمُ ٱلۡبَغۡيُ هُمۡ يَنتَصِرُونَ
Da waɗanda idan zãlunci ya sãme su, sunã nẽman taimako (su rãma).
وَجَزَـٰٓؤُاْ سَيِّئَةٖ سَيِّئَةٞ مِّثۡلُهَاۖ فَمَنۡ عَفَا وَأَصۡلَحَ فَأَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yãfe kuma ya kyautata, to lãdarsa nã ga Allah. Lalle ne, Shĩ (Allah) bã Ya son azzãlumai.
وَلَمَنِ ٱنتَصَرَ بَعۡدَ ظُلۡمِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَا عَلَيۡهِم مِّن سَبِيلٍ
Kuma Lalle ne, wanda ya nẽmi taimakon rãmãwa a bãyan an zãlunce shi, to waɗannan bãbu wata hanyar zargi a kansu.
إِنَّمَا ٱلسَّبِيلُ عَلَى ٱلَّذِينَ يَظۡلِمُونَ ٱلنَّاسَ وَيَبۡغُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
lnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zãluntar mutãne kuma sunã ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bã tare da haƙƙi ba. Waɗannan sunã da azãba Mai raɗaɗi.
وَلَمَن صَبَرَ وَغَفَرَ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ
Kuma Lalle ne, wanda ya yi haƙuri kuma ya gãfarta (wa wanda ya zãlunce shi), to shĩ wancan aiki haƙĩƙa, yanã daga manyan al'amura (da Allah ke so).
وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن وَلِيّٖ مِّنۢ بَعۡدِهِۦۗ وَتَرَى ٱلظَّـٰلِمِينَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَ يَقُولُونَ هَلۡ إِلَىٰ مَرَدّٖ مِّن سَبِيلٖ
Kuma wanda (Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani majiɓinci bãyanSa, kuma zã ka ga azzãlumai, a lõkacin da suka ga azãba, sunã cẽwa, "Shin, akwai hanya zuwa ga kõmãwa?"