وَإِذَا حُشِرَ ٱلنَّاسُ كَانُواْ لَهُمۡ أَعۡدَآءٗ وَكَانُواْ بِعِبَادَتِهِمۡ كَٰفِرِينَ

Kuma idan aka tãra mutãne sai su kasance maƙiya a gare su, alhãli sun kasance mãsu ƙi ga ibãdarsu.


وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٌ

Kuma idan anã karãtun ãyõòyinMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta ga gaskiya a lõkacin da ta jẽ musu, su ce, "Wannan sihiri ne bayyananne."


أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ إِنِ ٱفۡتَرَيۡتُهُۥ فَلَا تَمۡلِكُونَ لِي مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔاۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَا تُفِيضُونَ فِيهِۚ كَفَىٰ بِهِۦ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۖ وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Kõkuwã sunã cẽwa: "Yã ƙirƙira shi (Alƙur'ãni) ne?" Ka ce: "Idan na ƙirƙira shi ne, to bã ku mallaka mini kõme daga Allah. Shĩ ne Mafi sani ga abin da kuke kũtsãwa a cikinsa na magana. (Allah) Yã isa Ya zama shaida a tsakãnĩnada tsakãninku. Kuma shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."


قُلۡ مَا كُنتُ بِدۡعٗا مِّنَ ٱلرُّسُلِ وَمَآ أَدۡرِي مَا يُفۡعَلُ بِي وَلَا بِكُمۡۖ إِنۡ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ وَمَآ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٞ

Ka ce: "Ban kasance fãrau ba daga Manzanni, kuma ban san abin da zã a yi game da ni kõ game da ku (na gaibi) ba, bã ni bin kõme fãce abin da ake yin wahayi zuwa gare ni, kuma ban zama ba, fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa."



الصفحة التالية
Icon