Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bãyan shẽkararsu wannan. Kuma idan kun ji tsõron talauci* to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalarSa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima.
____________________
* Idan kun ji tsõron talauci sabõda hanã mushirikai zuwa hajji sabõda fataucinku da su zai rage, to, bãbu kõme, arziki ga Allah yake, Yanã bãyar da shi ga wanda Yake so.


الصفحة التالية
Icon