Sa'an nan Muka biyar a bãyansu* da ManzanninMu; kuma Muka biyar da ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin zukãtan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbãnanci* wanda suka ƙãga, shi, ba Mu rubũta shi ba a kansu, fãce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabõda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinsu sakamakonsu kuma mãsu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.
____________________
 * Nũhu da Ibrahĩm da Annabãwan da ke bãyansu zuwa ga ĩsa ɗan Maryama.** Ruhubãnanci a Kiristanci kamar tasawwufi ne a Musulunci. Hana bidi'a yanã cikin jihãdi da tsaron addini bidi'a kuma kashe addini ne. Anã kashe bidi'a idan anã awon ayyuka da Littãfi kamar yanda ake hana zãlunci idan anã awo da sikeli kõ mũdu.


الصفحة التالية
Icon